To ta jikinsa ovaries yake.
A kowace wata, jikin mace yakan saki kwai ɗaya masu rabon twins biyu, daga cikin waɗannan ovaries ɗin kwan yake fitowa, shi kuma ake kira da ovulation, bari dai in kara maku yadda zaku gane, wata yana da kwanaki talatin ko? To ovulation watan sakin kwai yana faruwa ne kwanaki 14 kafin mace ta yi wani period ɗin, misali ace kina yin period 16 ga wata ace period ɗinki yana yin kwanaki 7 kafin ki kammala, idan an haɗa kinga mun samu kwanaki 23 a wata, to idan kin kammala jikinki zai huta na kwanaki 8 zuwa 9, sannan ki saki kwai a 2 ga watan da zamu sake shiga, kinga saura kwanaki 14 ki yi sabon period kenan, muna magana ne a kan idan 16 ga wata kike yin period ɗin, dan haka in 16 ga wata kike yi to 2 ga wata zaki dinga sakin kwai, fatan kun gane? To mu je zuwa, a sauƙaƙe kuma a gajerance nai maku.
Yauwa mace na sakin kwai sau ɗaya a wata na ce ko? To amma kwararrun likitoci irinsu Dr James suna iya tsokanar ovaries ɗin, sukan yi amfani da hormonal medications dan ovaries su fitar da ƙwai da yawa lokaci guda ba kamar yadda mace ke fitar da ɗaya kawai a wata ba.
And a ƙaida na kwan mace idan ya fito daga ovaries yana yin awanni 46 ne zuwa 48 idan ba'a sadu da mace ya haɗu da maniyyi ba sai ya lalace, shi yake zama period da muke yi a yau, idan ya lalace sai ya zama jini ya fita.
To bayan su Dr James sun baiwa waɗan nan yara magungunan dake sanya ovaries sakin kwai dayawa irinsu gonadotropins fsh and lh, waɗan nan magunguna suna motsa ovaries su samar da ƙwai dayawa suna barin kwan ya yi 24h, ya girma kenan, sai su yi masu egg retrieval wanda suka yi masu a yanzu kenan suka ciro kwayayen.
A likitance ana kiran hakan da egg harvesting, karin wani haske, idan eggs ɗin mace ya fito daga ovaries yakan bi wata ƙaramar hanya mai suna fallopian tube inda zai je wajen kusa da mahaifa ya tsaya, to a wannan lokacin idan mace ta sadu da namiji kafin 48h zata samu ciki, dan maniyin namiji zai haɗu da kwanta da nata maniyin sai su shiga mahaifa.
To amma idan bai haɗu da maniyi ba, ma'ana ba'a sadu da ita a waɗan nan lokutan ba, to kwan yana mutuwa ne after 48 hours ɗin, idan ya mutu kuma jikin mace zai fitar da shi ta hanyar haila, idan mace ta samu ciki kuma ovaries ɗinta suna taukewa ne su daina sakin kwai, shiyasa take daina yin haila da ciki, kwayayen haihuwarta shi ne yake zama hailar dama, idan babu su to babu haila ai kun gani!. Wannan shi ne abin dake gudana a wannan sashi na SECTION D, mu je zuwa dan ganin me suke yi da waɗan nan kwayayye kuma.
Tsab suka bi suna cirewa yaran nan kwayayyensu, virgin daga cikin yaran sun zubar da jini, wasu kuma a'a, bayan sun kammala suka tattare kwayayye suka komo da su cikin ainahin section D ɗin, suka rufe kofar da ya haɗa cikin section D da kuma in da waɗan nan ƴan mata suke.
Kowannensu aikinsa ya kama, yanzu ma bari mu bi Dr James dan muga me zai gudana a wannan waje, tin da dik yadda ya yi hakan dikkansu suke yi. Dik kwayayen da suka zo da shi wajen wani jiga-jigan freezer dake cikin wajen suka nufa, a nan suka shisshirya kwalaben eggs ɗin, sannan suka fito da wasu kwalaben da already suke cikin freezer, da alama ma sun jima. A taƙaice dai freezing ɗin eggs ɗin zasu yi.
Suka fito da waɗan da tin last month suka cirewa ƴan matan sannan suka cire kwan daga ruwan follicle a microsoft shi ne suka ajiye a cikin freezer, sai yau amfaninsu ya zo. Sister Lazy ana ta aiki ana satar kallon masoyi Dr James ɗin da ko sau ɗaya bai san tana yi ba, aikin dake gabansa kawai yake yi cikin natsuwa da taka tsantsar.
Gaban wasu manya-manyan freezer dake can jefe nesa da in da wajen freezer na kwayayen macen suke suka tsaya, kun san section D yana da balain girma, gari guda.
Wasu kwalaben suka ɗauko mai shake da sperm na maza dana mata. Suka isa gaban kwalaben dake ɗauke da mahaifan mata da suka shirya last time idan baku manta ba, sperm na maza dayawa ne a cikin kwalaben, dayawa sosai fa, kowani kwalbar dake ɗauke da maniyin akwai rubutun da suka yi a jikin kwalbar, a kallah kwalabe 50 haka suka fitar da su kamar yadda kwalaben kwayayyen matan ma yake 50.
Hallau yanzu ma dai bari mu bibiyi Dr James dan ya fi kowa kwarewa a kan aiki. Amma kafin mu tafi ina da tambaya, ta ya suke samun maniyin maza masu yawa haka? Ku duba yawan kwalaben fa! Which's means ba maniyin mutum ɗaya bane! To taya suke samunsu? Gara kwan mace suna iya tiyata su ciro bayan sun basu maganin da zai sanya su samu kwan dayawa, amma maniyin macen da maniyin ɗah namiji ta ya suke samosu? Gaskiya wannan ɓangaren akwai sarkakiya da ɗaure kai mai tarin yawa, yanzu dai muka fara shiga cikin labarin, koma dai menene zamu ji kuma zamu gani.
Wani karin haske, idan sun ciro sperm na maza fa sai sun kaisa lab sun tacesa, su cire masu karfi a gefe, su ware marasa karfi a gefe, dikka kuma suna amfani da su, sai dai kowanne da amfaninsa ne, amma idan muka shiga cikin zaku gane me suke yi da sperm mai karfi da mara karfi bayan sun banbantasu.
Dr James ne ya gyara hand gloves ɗin hannunsa, lokacin fertilization ya yi kenan, gaban wasu naurori ya tsaye, sannan ya ɗauki wata karamar na'ura mai kama da eyes care ya sanya a idanunsa, kamar glass haka na'urar take, wannan na'ura tana iya zuƙo komai ƙanƙantar halitta a wajen shiyasa suke sanyata, kamar microsoft take.
Sperm masu karfi da aka rubuta baby boys a jikin kwalbar ya ɗauko, a gaban petri dish ya tsaya, kwan mace ya fara zubawa a cikin petri dish ɗin kafin ya tultula maniyin dake cikin kwalba guda ɗaya gabaɗaya, ya haɗesu waje guda kenan. Wai na ce kun san a cikin dubban maniyi kaɗan ne ALLAH yake hukuntawa suke ɗauke da halittar yaro ko baku sani ba? Shiyasa Dr James ya zuba maniyin dikka dan yasan akwai mai amfanin a ciki wanda dik iliminsu wanesu su iya zaƙulo shi, wannan ilimin mai sama ne kawai! ALLAH ne kawai yasa wannene mai halittar yaro.
Bayan ya haɗasu sai ya sanyasu cikin incubator tare da saita yanayinta ya zamana kamar dai cikin mace, sannan ya barsu dan su haɗe da kansu dan ba'a isa a haɗesu lokaci guda ba, da kansu suke haɗuwa kamar yadda suke haɗuwa a cikin mace.
Bayan ya yi wannan sai ya ɗauko sperm marasa karfi sosai ɗin wanda aka rubuta baby girls a jikin kwalbar, Intracytoplasmic sperm injection ya ɗauko tare da fasawa ya tsira a cikin kwalbar sperm ɗin ya haɗa da allura ta microscope, bayan ya haɗa sai ya zuba maniyin kai tsaye a cikin kwan macen, ya yi mashi yadda yai wa sperm mai karfi na farko, wannan allura da yai wa maniyi shi zai sanya sperm ɗin ya yi kwari har ya bada abin da akeso tin da ba'a cikin mace suke ba, dole sai ana kara mashi karfi!.
Su Dr Kamal ma dik haka suka yi nasu, aiki tukuru fa suke yi cikin taka tsantsan sosai, suka shirya sannan suka barsu a cikin incubator, zasu barshi ne ya yi kwanaki 3 zuwa biyar, a lokacin ne zai gama haɗewa da kwan yadda yakamata, sai ya zama zygote, a kwanaki na gaba daga sati biyu zuwa 4 daga zamansa zygote kenan, sai ya fara zama embryo, to idan ya fara zama embryo shi ne zasu dawo su canza mashi muhalli, dan idan ya zama embryo ya fara zama halitta, gudan tsoka kenan, kullum zasu zo su dinga dubasu dan su ga waɗanne ne suka fi karfi da lafiya suna ware kwalabensu gefe, masu raunin ma a gefe.
To idan ya ƙara kwanaki kamar biyu nan ne ake cirosa daga in da suka sanya, a wannan gaɓa idan mace za'ayiwa dashensa sai ta zo ayi mata aiki, shi ne zaku ji ana cewa an yi wa mace dashen cikin ko an haɗa kwayayen haihuwar mace da namiji an dasawa wata macen ta ɗauki cikin ta haihu, ba aiki ne na wasa ba, sai an yi da taƙa tsantsan, ba dik kai ne ke iya wannan aiki ba, bugu da kari ana iya samun matsala sosai, dandai su Dr James mayun doctors ne, sun kware, na ce maku a duniya irinsu basu da yawa, sun kuma saba wannan aiki sosai, shiyasa a wuni ɗaya suna iya haɗa kwai da sperm sama da 50 idan suka tashi aiki, dan haka ku gansu ne kawai ku barsu.
To su Dr James ba'a cikin mace suke dashen embryo ɗinsu ba, dan haka after 2 days suka dawo suka canzawa embryo ɗin wajen zama, suka yi dashensu a cikin waɗan nan mahaifa da suke sanyawa a cikin kwalabe masu kama da cikin mace, a ranar ma wuni suka yi suna dashensu, bayan sun kammala suka saita na'urar dake bawa cikin kwalbar yanayi daidai da cikin mace, suka shirya komai, sai da suka tabbatar komai na tafiya daidai sannan suka fito, Dr James ya wuce office ɗinsa tare da sister Lazy dake rike da takardun rahoton, dan ita aikinta a wajen shi ne suna aiki tana ɗaukar rahoton dik wani motsinsu, in sun kammala su duba rahoton dan su ga ko akwai wani matsala su yi gaggawar gyarawa.
A lokacin su kuma su sister Maya suna wajen nasu aiki, ba su kaɗai bane suke aiki a SECTION C, akwai nurses dayawa, amma su kaɗai ne masu amfani a labarin namu shiyasa nike magana a kansu kawai. Wasu shirga-shirgan guards ne suka shigo da wasu sabbin chemical a cikin manyan-manyan glass box. A jikin kowani box da sunan chemical ɗin a rubuce.
Mimmiƙewa dikka nurses dake wajen suka yi suna kallon box ɗin, taɓa sister Maya sister Zinta ta yi tare da cewa. "Yau kuma sabbin chemical muka samu, ya saɓa da waɗan da muka saba aiki da su, wannan kamar eesveratrol, nicotinamide mononucleotide, hyaluronic acid, retinoic acid and collagen peptides ne ai"..... Kai Maya ta jinjina game da cewa. "Su ne, sai mu hau shiryasu yadda yakamata ai". Kai sister Zinta ta jinjina, daga nan suka umarci saura nurses ɗin da su zo su fara ɗauko ƙananan bottle suna zubawa a ciki suna rubuta sunan kowanne da kilonsa sannan su shirya a muhallinsa.
Wai me ake yi da dikka waɗan nan chemicals ɗin ne? a ina suke samo sperm na maza? me suke yi da su? ina suke kai yawan uban sperm da kwayayen mace da dik wata sai sun cirewa mata ne? akwai sarkakiya da ɗaure kai a wannan ɓangare, na tabbata ba karamin ilimi zaku samu a wannan waje ba, bugu da kari zaku hankalta da abubuwa dayawa, sannan zaku gyara kurakuranku dayawa, zama nai sosai na shirya maku ingantaccen ilimi mai muhimmanci a wannan waje, i say it again, ban taɓa rubuta irin wannan labari ba, bana jin kuma har in gama rubutu a rayuwata zan sake yin littafi mai tarin iliminsa!!
A office ɗinsa Dr James ya zauna tare da karɓar takardan rahoton, ba tare da ya kalleta ba ya ce. "Go and call Zinta for me"........ Wani irin yawu ta haɗiye na takaici, yanzu ta gasgata cewa jiya shi ya kira Zinta kenan, ranta a matuƙar ɓace ta juya ta fito. Fuuu ta nufi section C, tana wani irin huci. Zata bar arear su Dr muryan Dr Kamal ya katseta da cewa. "Lazy call Maya for me". Takaici yasa bata kallesa ba ma ta amsa da okey tare da wucewa, suna neman sanya mata karamar hauka.
Cike da faɗa ta afko cikin section C, tana tafiya kamar zata faɗi ƙasa, wannan idan iskar mota ya zo tsab zai wuce da ita, ga wani kafurin high heel da ta kwama a kafa, sai ya sanya tana tafiyar ƴar tsana, tana wani cokala kafa, ni kam na ce ki dai tafi a hankali, a rage saurin kada a faɗi ƙasa, to naga kafafun ne sirara kamar na sauro, ga takalma yasa ta yi sama can ai kunga dole in faɗi haka.
Tana sanyo kafafunta a cikin side ɗin sai da kowacce nurse ta natsu tsabar kowa yasan balainta, sai ƙoƙarin hura siririn hancin nan take yi abu ya ci tura yaki huruwa. Kai tsaye cikin chemical set ɗin ta shiga. Cikin gadara da bada umarni ta ce. "Ke Maya ki je Dr Kamal na kiranki, ke kuma Zinta ki biyo bayana". Tana kai karshe ta juya fuuuu kamar wata kumfar teku ta wuce gaba.
Tana fita nurses ɗin suka fara gulmarta, dan babu wanda yake sonta a hospital ɗin nan, miƙewa Maya ta yi, muryanta na rawa ta ce. "Sister Zinta a tinaninki meyasa Dr Kamal yake nemana?"..... Zinta da hankalinta ya gama tashi ne ta amsa da. "I don't know what to say now gaskiya, kawai ki je da wuri, dan basa son ɓata lokaci su". Tana kai karshe ta bi bayan sister Lazy da sauri, kirjinta sai bugawa yake yi da karfi-karfi, tana fatan alkhairi ne yasa wanna aljanar zata kirata, baiwar ALLAH bata san cewa Dr James ne yake kiranta ba.
A tare da Maya suka fito, can a bakin side na office ɗinsu 3D (3 Doctors) ɗin nan suka hango Lazy a tsaye tana cika tana batsewa tana jiransu. Jikinsu dik a mace tamkar waɗan da kwai ya fashewa a ciki suka nufi in da take. Tin basu kariso ba ta juya ta wuce ciki fuuuu, bayanta suka bi, Sister Maya ta wuce office na Dr Kamal, ita kuma Zinta ta bi bayan sister Zinta zuwa office na Dr James.
A tinaninku meyasa 3D suka buƙaci waɗan nan innocent nurses ɗin? Muje zuwa, Star Lady taku ta amana ina tare daku, sai mun warware komai a tare! Mu leƙa team DEATH OR LIFE (DOL) mu dawo mu ji meyasa 3D ɗin nan suke kiran ƴan matanmu.
------------------------🔥
DOL.🔥
Har dare ya tsala suna wajen a zazzaune, idan wutar ya mutu su kara wasu kirare su hura hutan, babu alamar barci a tattare da su, domin a horon bar 2 an horasu da yunwa da rashin barci, sai su yi kwanaki uku basa barci, kazalika suna 24h babu abinci dik dan su saba, so yanzu ya zame masu jiki, yunwa da rashin barci ai abokin aikinsu ne.
V tin tana dan ja baya, tana rike da hannun Romeo ɗinta suna hira har ta saki jiki ta kwanto jikinsa tare da miƙe kafafu suna hira, dik wani motsinta a kan idon Juraiz, har ga ALLAH yarinyar ta tafi da imaninsa. While Arya na ɗaki, ta gama iya dube-dubenta, daga karshe ta rufe laptop ɗin, ta ci abinci kaɗan sannan ta kwanta dan yin barci. Manassa na waje bakin kofa tana latsa waya.
Bayan Agelina ta gama waya da Aunty Lisa sai ta dawo wajen ta zauna, matsawa kusa da ita Unays ya ya yi, cikin salo ya ce. "Hy, good evening". Kallo ɗaya ta ɗan mashi tare da ɗauke kanta kafin ta amsa, dan ma dai yana gaba da ita ne da ba zata amsa ba. Ƙoƙarin janta da hira ya yi, amma ta basar da shi, saboda yaran GAT akwai jan aji wlh, V ce dai mai saukin kai.
Takura mata Unays ya dinga yi da ƙoƙarin sai ta kula shi, ita kuwa tana amsa shi sama-sama, sai ya yi magana uku take amsa ɗaya, a gaskiya Unays karya ne mace ta ce bai haɗu ba, cikakken namiji ne, ga kyau, chocolate da shi, but Angelina bata nuna kamar ya haɗu mata ba.
Sai da 12 ta buga ne, cike da bada umarni Zaynish ya ce. "Dik matan nan ku tashi ku tafi ɗaki". Abin ku da shi musulmi ne, kuma yasan darajar mace. Ɗago ido Noor ya yi ya kallesa, sai ya ga Zaynish baya kallonsa, haka na nufin ba dan saboda Noor ɗin na baiwa flower ruwa shi da V ya yi maganar ba, hasalima shi bashi da matsala da soyayarsu, kawai dai yaga bai dace matan suna cikinsu a wannan lokacin bane.
Ganin ba da wata manufa Zaysh ya yi maganar bane yasa Noor ce mata ta tashi su shiga ɗaki. Matsawa ta yi, sumbata ya bashi a kumatu kafin ta miƙe tsaye, miƙewa Angelina ma ta yi, suka nufi hanyar komawa tantinsu. Dab zasu shiga ciki V ta ji an rike hannunta ta baya, tana juyowa ya jawota jikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke, wucewa ciki Angelina da Manassa dake zaune a wajen suka yi.
Haɓar V Noor ya ɗago, cikin zafa ya haɗe bakinsu, hot kiss ya shiga bata, mayar mashi da martani ta fara yi, yasa hannu ya fara shafa tula-tulanta yana lumshe ido. Ita kuma ta kankameshi ta baya tana tura mashi tongue ɗinta.
Sun ɗan ɗauki lokacin a haka kafin ya saketa tare da ce mata goodnight, ya faɗa still yana matsa tula-tulanta bai saki ba. Juyawa ta yi da sauri ta shige cikin tantin nasu, shi kuma ya juya ya koma wajen da suka hura wutan. Tin da ya zo wajen suke kallon juna da Zaysh kaman wasu munafukai, magana da ido suke yi.
Kashewa Zaysh ido ɗaya ya yi kafin ya koma wajen zamansa ya zauna, harara Zaysh ya watsa mashi tare da ɗauke kansa, ya cigaba da dannar wayansa. Haka suka kasance har wayewan gari, basu rintsa ba. Da sassafe su Arya suka tashi, one by one suka fito waje, nan suka isko sojoji masu yi masu girki sun hura wuta. Wucewa Arya ta yi izuwa wajen koramar dan ta yi wanka, tana sanye da white bathrobe.
Tana wucewa sai ga Angelina ta fito rike da waya a hannunta, daidai lokacin Leo ma ya fito sanye da sleeping dress ɗinsa, ya ɗaura towel fari a kansa, bai bi ta kan kowa ba ya wuce wajen karamar baya shi ma. Wucewa Angelina ta yi izuwa wajen da ta ga sojojinsu na zazzaune, tana sanye da kayan jiya bata canza ba.
Daga ɗan nesa da sojojin ta tsaya tare da ɗaga wayarta ta kama ɗaukar su Unays hoto, dik suna zazzaune, basu sani ba, ta ga su Unays an mata kyau yau, sai kawai ta tsaya kashe masu hotuna tana murmushi.
Daga bayanta ta ji an ce. "Aiki ya sameki kema, kin faɗa irin cutar V ko?"..... Ba tare da ta juya ba ta amsa da. "To ke Manassa wai ina ruwanki da mu ne? Ke dai ba kin ce Arya zaki biyewa ba? Babu namijin da ya kai ku yi soyayya da shi ko? Na tabbata watarana zaku faɗa tarko ne!"...... Brush ɗinta Manassa ta sanya a baki ba tare da ta sake cewa uppan ba ta wuce izuwa wajen wani dogon bishiya dake gefen su Unays ɗin tana goge bakinta.
Harara Angelina ta bita da shi kafin ta cigaba da ɗaukarsu hoto. Ita kuwa Arya tana zuwa wajen koramar ta ware igiyar bathrobe ɗinta, ta zaresa ta ajiye a gefe, ya rage daga ita sai pant and bra da yake suna sakawa yanzu. Saboda santin da take ji ne yasa ta rufe idanu ta faɗa cikin ruwan dake kwance ƙasar koramar wai dan ma kada sanyi yasa ta fasa shiga.
Ruwan a daidai kirjinta ya tsaya da ta tsugunna a ciki, kana iya hango tudun tula-tulanta a waje, ruwa ta fara ɗeba a tafukanta tana watsawa a fuskanta tana ɗan tsuke baki saboda sanyi, ga ruwan koramar daga sama yana zuba ta baya bayanta, sun kafa tantin wajen da zasu yi wanka fa, amma tsabar iskanci irin na Arya a nan take son yin wanka.
Da yake ta rigada ta shiga sai ta fara jin daɗin ruwan, tsoma kanta a ciki ta yi tare da ɗagawa da sauri ruwan ya biyo gashinta ya hau wanke mata fuska. Cike da farinciki tasa hannu tana sharce ruwan face ɗin nata, slowly ta buɗe idanu kai tsaye sai a kan Leo dake tsaye yana ƙoƙarin kwance igiyar bathrobe na jikinsa.
Ai bata san time ɗin da ta zunduma ihu ba, ya yi mugun bata tsoro, bata ji motsin mutum ba, bata ma kawo a ranta akwai wanda ya ga wannan koramar a cikin sojojinsu ba, ta zaci ita kaɗai ta ga abinta shiyasa ta zo shanawa a wajen taki zuwa toilet da suka kafa.
Ko a jikinsa wai dan ta yi ihu, hasalima bai ɗago ya kalleta ba ya cigaba da kwance igiyar, ya buɗe rigar ga shi yana fuskantarta, daga shi sai shorts irin matsastsun nan da kana iya ganin shatin halittansa, daga sama babu ko single ne, faffaɗar lion chest ɗinsa a waje, ko kaɗan bai damu ba, ita kuwa ta yi suman tsaye a cikin ruwan, ga shi ta kudurtawa ranta ba zata fita ba tin da ta rigasa zuwa, sai dai shi ya hakura ta gama. E kam akwai case, zan ga da ita da shi waye zai hakura ya barwa ɗaya wajen
Likes comments and share fisabilillah.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1🔥
2025-11-27🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________28 & 29
Zame rigar ya yi tare da ajiyewa a gefe saman wani dutse. Ai kasaƙe Arya ta yi tana kallonsa, ta kuma gagara daina kallon nasa dik da rikitata da ya yi. Cikin zafin nama ya motsa izuwa dab bakin ruwan, sai a lokacin ta lura da sojojin huɗu dake bayansa wanda sun juya mashi baya suna rike da bindigu dan bashi tsaro.
Ƙara rage tsawonta ta yi ta hanyar ƙara natsawa cikin ruwan saboda ta ɓoye kirjinta, dik da take bata da addini lallai bata yarda a kalle private part ɗinta ba, musamman kirjinta, a cewarta dik wanda ya kalli tsiraicinka ya gama da kai, kuma ba zai sake kallonka da wata daraja ba, kuma zancenta haka ne, ni ban ga amfanin fitar da surar jikin da wasu ƴan matan suke yi ba, dik ranar da namiji a waje ya kalli albarkatun da ALLAH yai maki shikenan kuma, ALLAH baya kuskure, ba a banza ya ce mata ku suturta jikinku ba, amma wasu suna ganin kamar wayewa ce su bar ko'ina a buɗe, wlh dik namijin da yasan ciwon kansa ya fi son macen dake cikin hijabi, yana son sanin ainahin abin dake a cikin hijabin ne.
Ko sau ɗaya Leo bai ɗago ya kalleta ba, ya shige cikin ruwan abinsa, sai dai bai tsaya ta kusa da ita ba, saboda ita tana tsoron can tsakiyar ruwa, ta baki-baki ta tsaya, shi kuma wajen yai mashi kaɗan tin da ruwan ko waish ɗinsa bata kai ba.
Can ya shiga har sai da ya kai in da ruwan ta zo daidai kirjinsa. Gagara motsawa Arya ta yi tamkar wacce ta sume, slowly ta juyo bayanta ta ɗan saci kallonsa. Wankansa yake yi cikin kwanciyar hankali, kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta dafe tare da jan dogon numfashi kafin ta furzar a hankali, a idanunta kawai ta fara kallon irin yadda ya cire rigar a gabanta, ya ilahi, ita kanta ta shaida Leo ya haɗu matuƙa, jikinsa tamkar madara, ba tabo ba ciwo sai wannan tsage na gerar tasa da ta ƙara mashi kyau sosai.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 95