ba ɗaya ba, kowa gwani ne a ɓangarensu, amma Leo kat ne!....👌
Uniform ɗinsu yana mugun yi masu kyau, musamman tactical t-shirt and tactical trouse, ya ALLAH, idan suka sanya tamkar ka tsaya ka yi ta kallonsu kada ka dakata.
Suna fitowa harabar gidan sai ga wani soja ya shigo, a gabansu ya tsaya ya sara masu kafin ya ce. "Sir GAT na kiran sir Nooriel". Cike da mamaki Noor ya kalli Leo, sai kuma ya jinjina kai alamar he's coming. Juyawa sojan ya yi ya fita, shi kuma Noor ya ce da Leo. "Bro meyasa GAT yake nemana?".
Shiru Leo ya ɗan yi kafin ya ce. "Jeka ji mana"....... Kai ya jinjina kafin ya wuce ya tafi cikin tsananin takun jarumta. Bayansa Leo ya bi suka fito wajen harabar gidan, cikin barrack Leo ya shiga yana ɗan kewaye, ya zura hannaye a aljihu yana ɗan tattaki.
Shi kuwa Noor kai tsaye office na GAT ya nufa. Sai da ya yi excuse ya jira aka bashi izinin shiga. A natse ya shiga ciki, ya sha madarar mamakin ganin V a office ɗin, ita da Angelina suna zaune saman doguwar sofar dake cikin office ɗin, suna rike da wayoyinsu.
A gaban GAT ya tsaya tare da sara mashi, bai ɗauke hannu ba har sai da GAT ya jinjina kai alamar sarawar ta yi, sannan ya sauke hannunsa ƙasa. Satar kallon in da V take ya yi, hakika ta lashe zuciyarsa a wannan safiya, ta yi fitina cikin wani haɗaɗɗen gown da ya tsaya mata iya ƙasan cinya wajen gwiwa, ga rigar ya bi shape ɗinta, hannun rigar da chain ne, while kafafunta na cikin gucci ace sneaker da ya yi balai karawa dressing ɗin nata kyau, gata fara, shigar dark purple ba karamin fito da kyanta ya kara ba, shigarsu iri ɗaya da Angelina, sun gyara ash hair ɗin nan nasu, sai sheki yake yi, na gaban goshi ƴan guntayen nan suna kwance luff.
Yana sauke idanunsa a kanta sai ya ga shi take kallo tana yaba kyansa. Shammatar GAT ya yi ya ɗan mata alamar heart da hannu yana ɗan lumshe idanu irin ta haɗu ɗin nan. Kyakkyawan murmushi ta sakar mashi kafin ta haɗe babban yatsarta da manuniya tai mashi alamar perfect. Kashe mata ido ɗaya ya yi in a love mood, ya ɗan ciza laɓɓa alamar wankarta ta cijesa sosai.
Ita kuwa alamar sumbata tai mashi da ɗan bakinta. Daddy GAT yana can yana cike wasu forms yana jawa Noor aji, wai sai ya barshi a tsaye kafin ya umarcesa da abin da zai mashi, bai san nan suna shan sharholiyansu ba, soyewa suke a ɓoye a office ɗinsa.
Dik abin da suke yi Angelina na kallonsu, can ta matsa dab kunne V, a ɗan shagwaɓe ta ce. "V i wish in samu wanda zai kasheni da soyayya irin Romeo ɗin nan naki mana, ohhh shi***, V ya haɗu, ya iya love, ga jarumta, ga shagwaɓa, irin mijin da nike so, please help me find out someone like him". Tana faɗa tana ɗan ciza laɓɓa irin abin ya cizata ɗin nan.
Kwanciya a jikinta V ta yi game da cewa. "We will talk later, yanzu kada ki katse mun jin daɗi". Ta faɗa tana ɗan fito da tongue ɗinta ta ɗan lashi lips ɗinta tana ɗagawa Noor gera guda. Yana ɗan tauna gefen lips ɗinsa yai mata wani alama da hannu wanda ta sanyata waro idanu waje a kan fuskansa, kashe mata ido ɗaya ya yi.......Wannan alama dai yai mata tafi karfin bakin STARLADY ɗinku shiyasa na gagara kwatanta maku alamar, Noor ya goge mun hadda ne gabaɗaya.
Daidai lokacin GAT ya miƙo mashi key ɗin mota, a dake ya ce. "Take them to shopping, make sure you take good care of them, and as from today kai ne zaka dinga kula da su, dik in da zasu je kai ma aminta kawai ka kaisu, ko a wajen mission na damƙasu a hannunka"..... Ba komai ne yasa GAT yai hakan na face dan yana auren Aunty Lisa, kunga yanzu ai sun zama ɗaya, Noor ƙaninsa ne, so yana ganin babu wanda ya cancanci kula mashi da su idan ba shi ba........ Ni kam na ce tab, V and Noor an samu promotion ai, kai kam daddy GAT sai dai mu ce sorry, sai kaga V da ciki zaka gane karatun, zaka gane kura ka baiwa ajiyar nama.
Team Noor muna cikin alkhairi dumu-dumu.
Sara mashi cikin zafin jini Noor ya yi bayan ya karɓi key ɗin......... "You can go with them now, this is my ATM, they know my pin". Ya kai karshe tare da miƙo mashi ATM card ɗinsa. Karɓa Noor ya yi, cikin zafa ya nufi waje.
Da sauri suka miƙe suka bi bayansa suna faɗin daddy sai mun dawo, hannu ya ɗaga masu cike da tsantsar kaunarsu.
A waje suka isko Noor, yana gaba suna biye da shi har wajen motar GAT, a nan suka tsaya suna ce mashi ya jira Arya da Manassa, suna zuwa yanzu. Buɗewa V gidan gaba na motar ya yi tare da ce mata ta shiga. Fakar idanun mutane ta yi, ta gaza hakuri har sai da ta ɗaga kafafunta ta shafi lallausan kumatunsa kafin ta shige ciki. Mai da kofar ya yi ya rufe yana kallonta, ya tsaya jiransu Arya, ita kuma Angelina ta shiga gidan baya.
A daidai wannan lokaci ita kuwa Arya tana cikin barrack tana faman yawon neman in da zata ga Leo, so kawai take yi ta ga fuskansa ko zata ji sanyi a ranta, ta damu sosai, tin dawowarsu Mission basu haɗu ba, sai dai hotonsa da take aukin kallah kullum.
While ita ma Manassa tana can yawon neman Vash dake cikin gidansu bai fito ba, ga nan Noor na tsaye yana jiransu.
----------------------------🔥
WS-HOSPITAL. Bari mu ɗan leƙa ya suke ciki mu dawo mu ga ya za'a ƙare da yaran GAT.
A wannan rana da yamma su sister Zinta sun gane ALLAH da girma yake, sun raina kansu, domin kuwa tin suna iya ƙoƙarinsu wajen yi wa yaran nan wanka har suka gaza, babys 30 suka samu suka yi wa wanka da kyar, sauran kawai suka jiƙa towel suka gige masu jiki, suka ce ba zasu iya wannan azaba ba.
Ga wannan baby sai kuma yake ta yi, Maya na ta fama da shi, ta sanya mashi suna darling, sai jijjiga shi take yi, idan ya yi shiru anjuma sai ya sake fara wani kuka.
Ana haka 3D suka shigo cikin ɗakin. A tare kirjin sister Maya and sister Zinta ya buga, sai suka tsinci kansu da faɗuwar gaba na ganin 3D, sai suke jin kamar ba alkhairi bane ya kawosu.
Baby hannun Maya Dr James ya karɓa, basu yi wa kowa magana ba suka wuce wani glass wall room dake gefe guda. Ɗaki ne mai cike da na'urori kala daban-daban. Gabaɗaya hankalin sister Zinta and Maya ya tattara ya koma kansu, da yake glass wall ne suna iya hango me suke yi daga in da suke tsaye.
Kwantar da baby suka yi a kan wani ƙaramin bed, take yaron ya yi shiru tamkar sun rufe mashi baki. Wani na'ura mai matuƙar hasken gaske suka kunna mashi a kan fuska wanda yasa yaron ya datse idanunsa yana ɗan girgiza jikinsa kaɗan alamar baya son wannan haske.
Sosai hankalin su Maya ya tashi, da yake a wurin yau sister Maya ɗin ta fi rike babyn, sun fi shakuwa sai ta ji kirjinta na bugawa da karfi, jikinta ya fara kerma, ta dakata daga goge jikin sauran babys da take yi, gabaɗaya ta tsayar da kallonta a kan 3D take ƙoƙarin tura yaron nan cikin na'urorin dake jikin gadon da yake kwance.
Ko me zasu yi mashi kuma? ALLAH masani sai kuma alƙalamina.
Likes comments and share fisabilillah.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1🔥
2025-12-9.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 44 & 45
Scanning na ƙwaƙwalwar babyn suka yi, Dr James na kallon Dr Mark and Dr Kamal da suka tsare na'urar dake ɗaukar girman kwakwalwar yaron.
Kallon na'urar shi ma ya yi kafin ya sake kallonsu, a lokacin dik suka ɗago suka haɗa ido, wani irin kallo suka yi wa juna kafin Dr Mark ya fara kashe na'urar, sannan suka fitar da yaron.
Rungumesa Dr James ya yi izuwa wajen wani bed, kwantar da shi suka yi kafin su fara kokarin ɗibar jininsa. Dik abin da suke yi su sister Maya suna kallonsu, da yake sister Maya ta fi raunin zuciya har idanunta sun fara ruwan hawaye, dik ta kiɗime, saboda wannan ba side na aikinsu bane, amma dik da haka sun fahimci gwada yaron ake yi, kowacce a cikin ranta tana tambayar kanta meyasa suke mashi wannan uban gwaje-gwajen yana ɗan jariri?.
Bayan sun kammala suka fito da babyn, sister Zinta ya zo ya miƙawa baby, jikinta na ɓari ta karɓa, da karfi ta sauke ajiyar zuciya ganin yaron ya dawo lafiya lou. Ɗago ido ta yi karaf suka haɗa ido da Dr James, wani irin spark ta ji zuciyarta ya yi, ALLAH ya gani tana tsananin son wannan guy ɗin.
Ɗan shagala ya yi da kallonta na ƴan mintoci, sai da darling ya fara kuka ne ya fargar da yana kallonta, da sauri ya zare kallonsa daga kanta yana ɗan wani ƴan kame-kame kaman mara gaskiya. Dr Kamal and Dr Mark sai kallonsu suke yi suna sakin one side smilling na munafurci, sun san Dr James ya gama faɗawa, yana masifar son Zinta, amma yaki bada kai, sai ya dinga basarwa.
Baiwar ALLAH bata san komai ba, sonsa kawai ta sani. Ganin su Dr Mark suna kallonsa ne yasa ya wuce gaba, har ya kai kofa zai fita kuma sai kuma ya juyo, a kanta ya sauke kallonsa, while shi take kallo tana faman jijjiga babyn. "Idan mun tashi aiki ki sameni a office". Daga haka ya sa kai ya fice ba tare da jiran amsarta ba.
Sister Maya ce ta ce. "Sir please ayi hakuri a dawo mana da nurses ɗin can ko mutum 10 ne su tayamu aikin nan, akwai wahala, ba zamu iya ba". Cike da tsoro ta faɗa, muryarta na rawa.
Idanun Dr Kamal a kanta ya amsa da. "Za'ayi hakan"........ Ta yi matuƙar mamakin jin kalamansa, bata taɓa zatan samun sauki daga garesa ba, ashe yana da saukin kai, sai ta ji wani irin sonsa ya shigeta, bata san time da murmushi ya kubce mata ba. Ni kam na ce yaro yaro ne, saboda dai akwai abin da suke so a wajenku ne, amma ban da haka ai ba zasu sauƙaƙa maku ba.
"Keep smiling beb". Dr Kamal ya faɗa tare da juyawa ya nufi kofar fita, kara faɗaɗa murmushinta ta yi, rufa mashi baya Dr Mark ya yi.
Suna fita Maya ta daka tsalle tare da haye jikin Zinta, cike da farinciki ta ce. "Sister ashe 3D suna da kirki, kinga sun amsa buƙatarmu a karo na farko a rayuwarmu"....... Zinta da gabaɗaya soyayyar Dr James ya gama narka zuciyarta ce ta amsa da. "Sun wuci haka, sister son Dr James yana neman yi mun illah".
Hannu Maya ta sanya ta karɓi darling, sumbatar yaron ta fara yi tana ta murmushi kafin ta ce. "Zai zama naki ne, ki kara dagewa, dan naga wani irin kallon da yai maki yanzu tin da muke a hospital ɗin nan ban taɓa ganin ya yi wa wani irin wannan kallo ba".…..... Tana murmushi ta ce. "Nima ban taɓa ganin ya yi irin wannan kallo ba, kina gani ya jima yana kallona, his eyes melt my heart all".
Rungumeta Maya ta yi, suka cigaba da tattaunawa suna farinciki. Da fitar su Dr James da kamar mintuna biyar sai ga nurses guda goma sun shigo, zazzaro idanu Maya ta yi kafin ta ce. "Lafiya?".
Ɗaya daga cikinsu ce ta ce. "Dr Kamal ne ya ce mu dawo nan, daga yau zamu dinga tayaku aiki". ...... Wani irin farinciki Sister Maya ta ji, ta kara rungume darling tana murmushi. Zinta ta ce to su tayasu su ƙarisa gyara babys ɗin, da sauri suka zo suka cigaba da aikin.
A can gefe kuwa, Dr Kamal and Dr Mark a tare suka karisa office na Dr James, zaune suka iskosa, ya kwantar da kansa a saman kujerarsa, ga hannunsa a kan laptop, da alama aiki yake yi ya shiga duniyar tinani. Taɓa shi Dr Kamal ya yi saboda bai ji shigowarsu ba.
Slowly ya sauƙo da kallonsa a kansu, nisawa ya yi kafin ya ce. "Soyayyarta yana nema yi wa zuciyata illa"....... Dr Kamal ya ce. "Ga alama nan mun gani". ..... Dr Mark ya ce. "To what are you waiting for?".
Cigaba da pressing na laptop ɗinsa ya yi tare da cewa. "Jira ya kare, daga yau na mallakawa kaina ita, dama tin asali kaina na halittawa ita, ba zan sake jira ba"......... Zama Dr Kamal ya yi a saman chair. "I love Maya, but ba yanzu zan mallakawa kaina ita ba, zan bari sai gaba". Dr Kamal ya faɗa.
Siririn tsaki Dr Mark ya ja tare da cewa. "Ya batun aikin W-S?". Shi bashi da lokacin mace a cewarsa.... Shiru Dr James ya ɗan yi kafin ya ce. "Aikinsu babba ne, dogon project ne, yanzu kuma wai jarirai 2000 suke da buƙata".
Ɗan zare idanu Dr Kamal yai kafin ya ce. "Apart from 500 da muka basu last two months ago? To me zasu yi da su?"........... Siririn tsaki Dr James ya ja kafin ya ce. "Sabuwar addinin da suke son kirkiranwa duniyar nan ne suke plan a kansa, zasu reni waɗan nan babys ɗin, su koya masu abu guda, watau addinin da suke so, idan yaran suka kai 18 years sai su bayyanasu a duniya, zaku ji ana cewa wasu sabbin mutane sun bayyana da sabon addini, mutane da dama zasu bi wannan addinin saboda hujjojin da suka shirya, sun shirya ɓatar da hankali mutane, kun tina project da suka sanya muka kai masu kan tattara bayanan jama'a?".
(Kun tina su Lion sun faɗi cewa a plan na WS akwai fito da addini guda ɗaya? Kuma akwai satar bayanan mutane dan ayi amfani da kwakwalensu? To ga maganar ya fito a bakin Dr James kun ji.)
Jinjina kai Dr Kamal and Dr Mark suka yi, cigaba ya yi da cewa. "To da wannan zasu yi amfani wajen dakushe tinanin mutane, zasu canza masu ra'ayi ta dole, zasu juya abubuwa da dama, nan da shekaru kaɗan ne, yanzu wuyarta kyankyasan babys ɗin ne, sun hura mun wuta, suna neman ɗaura mun pressure kan nan da next year in basu 2000 babys, ga waɗancan mutane dake son 1000 babys, sannan WS again sun ce suna buƙatar babys mata zallah guda 1000 nan da 2 years masu zuwa, abubuwan sun yi mana yawa, ga ƙarancin mahaifa, dole mu san tsarin da zam yi a shekara mu samu koda 2000 babys".
Dr Kamal ya ce. "Su waɗan can me zasu yi da babys mata? Sun manta dokarmu ne? Bamu kyankyasan mata mu sayar, maza kawai muke sayarwa, ko mu da muka kyankyashewa kanmu mata ai da akwai dalili, dan su mana aiki ne, meyasa zamu karya dokanmu a kan wannan aiki?". ........ Siririn tsaki Dr James ya ja kafin ya ce. "Kasan sun ce mai gidansu dijjal ya kusa bayyana, shi ne suke buƙatar babys mata dan su raina mashi, hanya suke share mashi ai".
One thing about this 3D, Dr James shi ne kaɗai yasan dik wani sirri na kasuwancinsu, kuma shi kaɗai yasan su waye WS, dik abokan kasuwancinsu shi kaɗai yasansu, kuma shegen wayau ne da shi, yasan da cewa su Dr Kamal abokansa ne kawai da suka haɗu a makaranta, shiyasa yaki yarda ya haɗasu da abokan kasuwancin nasa wai dan ma kada watarana su ci amanarsa, ba komai yake buɗe masu ba, ko computer daddyn Lion shi kaɗai yasan password ɗinta, shiyasa kuka ga komai shi ne ke masu bayani.
Haka suka cigaba da tattaunawa suna tsara yadda project ɗin zai tafi har ya basu abin da suke da buƙata.
--------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
Bayan Lion ya kammala wayarsa da Mr president cikin room ɗinsa ya dawo, a kusa da guru ya zauna tare da miƙa hannu ya bugi heronsu. Da sauri zakin ya ɗago kai, wani irin mugun kallo Lion ya kurga mashi kafin ya nuna mashi hanyar sauƙa daga gadon da hannu ba tare da ya yi magana ba.
Ai a kule hero ya ɗago hannu zai kai mashi yagushi a jiki da waɗan nan shegun faratunan nasa guru ya tare. Shi kuwa Lion da ya tsaya yana jiran ya kawo hannun ne ya sake watsa mashi harara, da alama yau zazzafar faɗa suke yi, kun san wani lokaci idan ta kwaɓe masu faɗa sosai suke yi, kuma dan balai Heron ya fi son Lion, kuma Lion ɗin ne mai bashi mugun wahala a gidan.
Mari Lion ya kai mashi a fuska tare da ɗaure fuska sosai, ya sake nuna mashi hanyar sauƙa. Hannu guru yasa yana ɗan shafa wuyan heron alamar rarrashi kafin ya nuna mashi hanyar sauƙa.
Cikin zafa ya diro ƙasa tare da girgiza jikinsa da karfi, ya wani buɗe, kai ya ilahi, a gaskiya zakin nan ƙato ne, ga uban gashin da suka bar mashi a jiki wanda ya ƙara mashi girma da kyau, dik bayan watanni shida suna bashi alluran kashe mashi hakwara, hanasa cizo da sauransu, and suna ciyar da shi nama sosai, shiyasa ya yi kato matuƙa, wannan ka ci karo da shi ai sai ka kwanta kawai ka ce ka mutu.
Ko kallon in da yake Lion bai yi ba, ya gyara ya kwanta tare da jawo bargo, ya lumshe jade sleeping eyes ɗinsa, a cikin ransa ya fara karanto addu'ar barci. While shi kuma guru ya kashe masu light na ɗakin, ya kunna dim kafin ya kwanta shi ma, ya jawo wayansa ya fara pressing. Shi kuma hero ya kwanta a kasa saman carpet dake gaban bed ɗin nasu.
After some minutes barci yai awon gaba da su dikka. A lokacin shi kuwa Aryan yana can yana ganawa waɗan nan mutane uku azaba, can underground room ya kaisu, ɗaki ne da su kaɗai suka san in da yake a faɗin ƙasar, a nan suke kashe na kashewa, su hora na horarwa, su ganawa wanda zasu ganawa azaba azaba.
Dik wani nau'i na kayan azabtar da mai laifi akwaisa a wannan ɗaki. Ba yadda bai yi da mutanen nan kan su faɗa mashi meyasa suke bibiyar rayuwar Seraphina ba, amma sunki faɗa mashi, har kunne ɗai-ɗai ya yanke masu, amma suka kafe fir cewa wlh su basu san komai ba, kawai an kirasu ne a waya aka basu wannan aiki, basu san wanda ya basu ɗin ba.
Aryan bai yarda da su ba, dan haka cikin fushi ya datse maƙogwaron ɗaya daga cikinsu, ya razana biyun da su faɗa mashi su ma ko su baƙonci lahira. Ƙoƙarin fahimtar da shi suka yi kan cewa su basu san komai ba, amma ina bai yarda ba.
Kuma da gaske ne basu san komai ba, kawai contract aka basu na su kawota, su kuma suka baiwa Aunty Saffiya suka cire nasu kamisho. Harta number da aka kirasu aka basu aikin ɓoyayyar number ce.
Karɓar wayoyinsu Aryan ya yi, faceluck ne security ɗinsu, dan haka ya saita fuskokinsu ya buɗe wayoyin, ciki ya shiga ya fara bincike. Da yaga number ɓoyayyar number ce, sai ya shiga message ɗinsu, nan ya ga an tura masu dala miliyan 50 kan su kawo Seraphina.
Lokaci guda ya wani irin zabura ya miƙe tsaye yana kallon sms ɗin. Zazzaro eyes ɗinsa a kan screen na wayar ya yi, ya ilahi, hasbiyallahu waniimal wakil ya maimaita sama da sau 30 kafin ya ɗago da kallonsa a kansu.
Lallai ba shakka da wannan account ɗin aka turawa mommynsu Lion kuɗi, kuma da wannan account ɗin aka turawa Dr Hushaima kuɗi, dama ya ɓoyewa Lion cewa da wannan account da aka turawa Dr kuɗi da shi aka turawa mom ɗinsu kuɗi, akwai abubuwan da Aryan ya ɓoyewa Lion sosai dangane da case ɗin daddynsu, saboda kada zuciyar Lion ta buga, yana tsananin sonsa sosai, so ya gwammaci ya rufe abin shi kaɗai kada ya rasa ɗan uwan nasa.
Tabbas Aryan yasan cewa an yi wa daddyn Lion tiyata an ɗebi sperm ɗinsa, domin kuwa shi ne mutum na karshe da ya yi magana da daddyn, a lokacin da ya kira table phone nasu dake parlo a gida, lokacin suna yara da basu wuci 10 to 12 years ba, Lion yana sama yana karatu, shi kuma da wani babban amininsu mai suna MAHVIR wanda suke ce mashi VIR ko Barde, suna zauna a parlo suna buga game na ludo.
Da table phone ɗin yai ƙara Aryan ne ya je yai picking, a lokacin ba zai iya tantance a wani hali daddy yake a ciki ba, amma tabbas yana tsaka mai wuya, a wannan lokacin ne daddy ya faɗawa Aryan abubuwa dayawa, ciki har da tiyatar da suka yi mashi, ya ce yasan kashe shi zasu yi, ba zai rayu ba, Aryan ya faɗawa Zayra'an ya ɗauki Nirash su dikka su gudu, mom ɗinsu ta ci amanarsu, a wannan rana ne suka san cewa mom ce ta jefasa cikin wannan hali.
A wannan rana daddy ya faɗawa Aryan abubuwa da dama, sai dai a lokacin saboda ƙarancin shekaru Aryan bai damu da son sanin su waye suka yi mashi hakan ba, kuka kawai yake yi yana tambayarsa ina yake yanzu.
Da gudu Vir ya yi kansa yana tambayarsa lafiya? Aryan bai iya amsa mashi ba, hakan yasa Vir ya yi sama da gudu ya kira su Lion da guru dake ɗaki.
Kafin su sauƙo wayar ta katse, daddy ya katse kiran, da alama kwace wayar daga hannunsa aka yi, lokacin da suka sauƙo ne Lion ya rungume Aryan yana tambayarsa menene yake faruwa. Da kyar Aryan ya faɗa mashi yadda suka yi da daddy, mom ya sayar da daddy gabaɗayan shi, dan haka ya umarci da su gudu yanzu, dan mom tana hanyar dawowa. So a wannan rana ba komai ya faɗawa Lion ba, dan abin zata mashi yawa, ace mahaifiyarka ce zata aikata wannan zalunci, dan haka sai ya rufe wasu maganganun ya barwa kansa sanin wasu abubuwan.
Cikin abin da ya rufe har da wannan account ɗin, da Lion yasan cewa da wannan account da aka turawa mom ɗinsu kuɗi da shi aka turawa Dr Hushaima hakika da Lion zai kashe Dr da Seraphina da kansa, saboda tsananin takaici, amma yanzu Lion yana ganin kamar wasu ne suka baiwa Dr contract na daban dik ba tafiya ɗaya bane.
Sosai Aryan ya gigita gani dik account ɗaya ne. Cikin tsananin fushi ya ɗauki wuƙa ya datse maƙogwaron dikkan maza biyun, jikinsa na wani irin tsuma, kirjinsa na tafarfasa, a fili ya ce. "Koma wanenen lokacin waiwayarka ya isowa IRON FIST, tabbas ni kaɗai na isheku koma su wanenen ku!!".
A wajen ya bar gawarwakinsu, ya fito ya shiga motarsa, dan yasan suna da masu tsabtace masu wajen. Kai tsaye ya nufi komawa gida, sai hasbiyallahu waniimal wakil yake nanatawa a cikin ransa, dan kirjinsa na dab da tarwatsewa zuciyarsa ta fito waje tsabar tashin hankali.
Yana a kan hanyar komawa ne aka kira wayar wancan mutumin, dama ya tawo da wayoyin. Picking ya yi tare da karawa a kunne. Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Ɗauko yarinya ɗaya kawai ya gagareku, to idan ba zaku iya ɗaukota ba ku sare mana kanta, kwakwalwarta da kuma eggs ɗinta ƙawai muke da buƙata ba wani abin ba.......". Wata mahaukaciyar birkin da Aryan ya taka sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 95