Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kan fuskansa, ya watsa bayansa tare da bin fuskanta da kallo, babu haske sosai, bai iya banbance wacece bace, ya zaci ma ta Noor ce watau V. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi tare da matsawa da ita izuwa bakin dutse, ya ɗagata cak ya kwantar a saman dutsen, sannan ya ɗauki gel ɗinsa, ya wanke kansa sosai, ya yi wankansa, ya fito ya sanya bathrobe a jikinsa, ya ɗauki ƙaramin towel ɗinsa ya fara goge kansa. Bayan ya kammala ya ɗauki kayansa, sannan ya wuce abinsa, bai sake bi ta kanta ba. A lokacin 5:45 ta yi, lokacin sallar asuba ta kusa wucewa. A gaggauce ya shirya cikin tactical t-shirt and army trouser. Ya yi matuƙar kyau, ya ɗaure gashinsa domin ya je ya yi sallah, sai tashin kamshin turaren kamfanin su Noor yake yi, ya fito daga cikin tantinsa. Fitowarsa yasa dik sojojin dake wajen suka ƙame suka sara mashi, cike da jarumta ya taka ya nufi in da suke yin sallah. Nan ya iso su Zaynish dik sun yi wanka, Zaysh ɗan albarka yana koyawa Noor yadda zai yi alwala, Noor akwai barisa har ya haddace yadda ake yi. A wannan rana sun yi sallar asuba tare da Noor, sallarsa ta farko a arayuwarsa, lallai munai mashi fatan nasara tin da ya fara da sallar asuba, In Sha ALLAH tasa zata yi kyau, domin kuwa sallar asuba ba karamar sallah bace, ita ce sallar da in kana yinta a kan lokaci kafin fitowar rana ba zaka taɓa taɓewa ba a rayuwarka, a cikin salloli sallar laasar ce kawai ta fisa, sallar laasar karshe ce, idan kika rasa sallar laasar a kan lokacin tamkar kin yi asarar duniya ne da abin dake cikinta gabaɗaya. Ina son jan hankali mata masu jinkirta sallar laasar, ita ce kawai sallar da ALLAH yake rantsuwa da ita, wal asir, sallah ce da take ta musamman, mata ku kiyaye, kada rana ta faɗi baki yi sallar laasar ba. Bayan sun idar da sallah suka zauna yin askar, Leo and Zaynish suka yi karatun Alkur'ani mai girma. Sai da gari ya yi haske, sannan Leo ya umarci da a kira surgeon Manassa ta zo ta wanke hannun Zaynish ta yi trea ting ɗinsa. Da sauri Vash ya miƙe ya nufi tantinsu. Zaune ya iskota ita da Angelina suna shafa lotions a jikinsu, ga shi ya shigo ba excuse saboda bai yi tunanin zai samesu haka ba, dan yaga Manassa tana da son barcin safe, ya yi zaton ma barci suke yi, yasan Arya ce kawai mai tashi sassafe ko in ce asussuba, amma su Angelina suna kai 7. Yana shigowa da sauri ya juya masu baya yana faɗin sorry. Daga su sai towel da bai kai rabin cinyarsu ba, da kaɗan ya rufe mazaunansu, ga shi suna tsaye. Shi a matsayinsa na musulmi ya ji hakan tai mashi nauyi, su kuma da basu da addini sai basu wani damu ba, Manassa har da cewa. "Sir Arvash ya da juyawa haka?". "Zo ki duba Zaynish ya samu matsala a hannu". Yana gama faɗar haka ya wuce ba tare da ya sake juyowa ba. Kallon juna suka yi da Angelina, zazzaro idanu Angelie ta yi kafin ta ce. "Ke yi sauri ki zo ki je ki duba shi, wayyo, kome ya same shi?". A kiɗine ta yi maganar. Ganin ta shiga damuwa ne yasa Mannassa fara ƙoƙarin kwantar mata da hankali, ai ina, uniform ɗinta ta sanya a gaggauce, ta ce su je kawai. Shiryawa Manassa ta yi, ta ɗauki rucksack ɗinta suka fito. Kai tsaye in da su Leo suke sallah ta nufa, a lokacin dik sauran sojojin sun tashi, ya rage daga Leo, Noor, Zaynish, sai Vash, watau ƴan team ona kawai. Su Manassa na zuwa kallo ɗaya Leo yai masu ya ɗauke kansa game da miƙewa, ya nufi tantinsa bai yi magana ba. Ai Angelina bata san lokacin da ta ƙarisa gaban Zaynish ba ganin yadda hannunsa yake jini, dan Leo ya kwance mashi ɗaurin da ya yi wa hannu, yanka ce sosai aka mashi. Hannun nasa Angelie ta kama, tamkar zata yi kuka ta fara ce mashi sorry. Mamaki ne yakama shi, shi dai yasan ko sannu bai taɓa haɗa shi da waɗan nan yara ba, meyasa ta damu da shi har haka?. Ɗago kai ya yi slowly ya sauke idanunsa a kan Noor dake kallonsa shi ma. Kashe mashi ido ɗaya Noor ya yi yana sakin one side smiling. Matsawa Manassa ta yi game da riko hannun nasa, cikin raunin murya Angelina ta ce. "Manassa ki yi mashi a hankali kin ji?"......... Awwww, sai kawai Zaynish ya ji daɗi a ransa, to zuciya tin da ha dutse ba ai tana son mai kyautata mata ko. Ɗauke kallonsa daga kan Noor ya yi, ko sau ɗaya bai kalli Angelina ba, ya yi ƙasa da idanunsa, yana jin Manassa tana wanke mashi hannun, abinku da mazajen AZURE, ko kaɗan bai nuna kamar jikinsa akewa wannan abin ba, ya yi ƙasa da kai kawai. Sai faman ce mashi sorry Angelina take yi cike da nuna kulawa da tausayawaq , idan Manassa zata zuba mashi magani sai ku ga Angelina ta datse idanu tana faɗin ayi mashi a hankali. Miƙewa Noor ya yi game da cewa. "Let me check on my wife ina zuwa". Ya faɗa tare da nufar hanyar shiga tantinsa, dik in da zai wuce sojojin sai sun kame sun sara mashi. (Jiya na ji kunce Noor ne ya ɗauki mutanen nan dik, hala kun manta in da na ce dakatawa daga ɗaukar mutumin Leo ya yi ya nufi Noor yana faɗin ya faɗi kalmar shahada? Ya za'ayi Noor ya ɗauki mutane huɗu shi kaɗai fisabilillahi? Ku gayawa kanku gaskiya mana, ga Leo ga Zaynish dikka.) Gyara mashi hannu tsab ta yi, ta ɗaure da bandeji tare da ɗago kai ta ce. "Headlock sir"....... Kai kawai ya jinjina mata, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Thank you". Daga haka ya miƙe ya nufi tantinsa shi da Vash. Jim kaɗan ya fito ya shiga tantin Leo dan su yi bincike kan mutanen da suka kamo ɗin nan. While sun ɗaɗɗaure karnukansu a wajen da suke zama hura wuta. Gabaɗaya sojojin dake sansanin ne suka tattara a wajen da suke huta wutar nan except team 1 and matan, dan matan suna ɗaki, team 1 suna ɗakin Leo suna tattaunawa kan abin da suka yi daren jiya, suna shirya yadda zasu tsabtace ƙasar Avaris. Sojojin dake yi masu girki ne suka kammala game da fara raba masu, suna bin kowa su bashi na shi, sun kaiwa team one nasu a ɗakin Leo, while sun kaiwa su V nasu, sai suka nufi sauran sojojin dake wajen karnukan nan suka fara raba masu, kowa ya ga karnukan nan sai ya yi santinsu, sun haɗu matuƙa. Babu wanda ya lura da cewa Arya bata a cikin sansanin, dik suna ta harkokinsu, ita kuma tana sume kwance kan dutse yadda Leo ya kwantar da ita. ------------------------🔥 WS-HOSPITAL. Tsaye 3D suke a ɗakin kyankyasan jariransu, sun rabu suna aikinsu cike da kulawa da taƙatsantsan. While sister Lazy na biye da Dr James tana ɗaukar rahoton komai yadda yakamata. Freezer Dr Kamal ya nufa, kwalaben dake ɗauke da eggs ɗin da suka cire jikin yaran can ya ɗauko, wanda suka samu 50 eggs ɗin ya ɗauko, a natse ya koma wajen aikinsa. Buɗe kwalbar eggs ɗin ya yi, yana ƙoƙarin zubawa a cikin dish da zai haɗe da sperm da suka fito da shi. Ga mamakinsa sai ya ga eggs ɗin sun canza kala, mamaki ne yakama shi, sun yi wani iri sosai. Sosai Dr Kamal ya girgiza da yanayin waɗan nan eggs ɗin, ya yi dik gwaje-gwajensa the same thing yake bashi, ɗago kai ya yi, ya kalli Dr James dake faman zuba eggs ɗin hannunsa cikin dish. "Jammy, I think there is a problem, meyasa eggs ɗin nan suka canza kala? Na yi iya gwajina amma basu nuna mun wani dalilin canjin kalar ba". Zuciyansa na rawa ya yi maganar, saboda a tsawon shekarun da suke aikin nan bai taɓa ganin irin wannan abin ba, meyasa eggs ɗin suka canza kala? Ko dan sun cirosu daga jikin matattu ne? To amma gwajinsu bai nuna masu eggs ɗin suna da wani matsala ba, meyake shirin faruwa ne. Har yanzu sun gagara tinanin su hakura da waɗan nan eggs ɗin, basu taɓa tinanin ALLAH zai kamasu ta wata siga ba, kai bama su taɓa tinanin akwai wanda ya isa ya kawo karshensu a duniya ba, sun ɗauka a kullum sune da nasara. Dr Mark ne ya ce. "Kamal kana buƙatar wankin brain"........ Dr James da bai ko kalli in da suke bane ya amsa da. "Ku zubawa eggs ɗin sauran sperm na Haiza'an". Babban magana! Watau komai ta fanjama fan jam, shi baya tsoron komai. Dr Mark ne ya ce. "Ka manta zaka yi wa Zinta dashen sperm ɗin ne? Idan aka zubawa eggs ɗin zaka rasa"...... Ɗago idanu ya yi da sauri, da ya mance ai, da sauri ya ce. "Ku dakata, ku duba wani sperm ɗin, ku barmum wancan". Kai suka jinjina alamar to, a natse da taƙa tsantan suka fara aikinsu, zasu yi dashe yara 500 yau, sun ce nan da two months masu zuwa in suka sake cire eggs ɗin yaran sai su sake dashen wasu yaran ko da 300 ne, a wannan karon ba zai yiwu su kyankyashi yaran lokaci guda ba, dole a samu ratar watanni in dai suna buƙatar 2000 babys. Dr James ne ya gyara hand gloves ɗin hannunsa, lokacin fertilization ya yi kenan, gaban wasu naurori ya tsaye, sannan ya ɗauki wannan karamar na'ura mai kama da eyes care ya sanya a idanunsa, wannan na'urar ce dake iya zuƙo komai ƙanƙantar halitta a wajen shiyasa suke sanyata, kamar microsoft take. Sperm masu karfi da aka rubuta baby boys a jikin kwalbar ya ɗauko, a gaban petri dish ya tsaya, kwan mace ya fara zubawa a cikin petri dish ɗin kafin ya tultula maniyin dake cikin kwalba guda ɗaya gabaɗaya, ya haɗesu waje guda kenan. Bayan ya haɗasu sai ya sanyasu cikin incubator tare da saita yanayinta ya zamana kamar dai cikin mace, sannan ya barsu dan su haɗe da kansu dan ba'a isa a haɗesu lokaci guda ba, da kansu suke haɗuwa kamar yadda suke haɗuwa a cikin mace. Bayan ya yi wannan sai ya ɗauko sperm marasa karfi sosai ɗin wanda aka rubuta baby girls a jikin kwalbar, Intracytoplasmic sperm injection ya ɗauko tare da fasawa ya tsira a cikin kwalbar sperm ɗin ya haɗa da allura ta microscope, bayan ya haɗa sai ya zuba maniyin kai tsaye a cikin kwan macen, ya yi mashi yadda yai wa sperm mai karfi na farko, wannan allura da yai wa maniyi shi zai sanya sperm ɗin ya yi kwari har ya bada abin da akeso tin da ba'a cikin mace suke ba, dole sai ana kara mashi karfi!. Su Dr Kamal ma dik haka suka yi nasu, aiki tukuru fa suke yi cikin taka tsantsan sosai, suka shirya sannan suka barsu a cikin incubator, zasu barshi ne ya yi kwanaki 3 zuwa biyar, a lokacin ne zai gama haɗewa da kwan yadda yakamata, sai ya zama zygote, a kwanaki na gaba daga sati biyu zuwa 4 daga zamansa zygote kenan, sai ya fara zama embryo, to idan ya fara zama embryo shi ne zasu dawo su canza mashi muhalli, dan idan ya zama embryo ya fara zama halitta, gudan tsoka kenan, kullum zasu zo su dinga dubasu dan su ga waɗanne ne suka fi karfi da lafiya suna ware kwalabensu gefe, masu raunin ma a gefe. To idan ya ƙara kwanaki kamar biyu nan ne ake cirosa daga in da suka sanya, a wannan gaɓa idan mace za'ayiwa dashensa sai ta zo ayi mata aiki, ba aiki ne na wasa ba, sai an yi da taƙa tsantsan, ba dik kai ne ke iya wannan aiki ba, bugu da kari ana iya samun matsala sosai, idan aka samu matsala kuma shikenan sun yi asarar kwayayen fa. Bayan sun kammala, suka fita a tare, Dr James yana duba time a agogon hannunsa. 5:40 na yamma, kai tsaye cikin SECTION D ɗin suka ƙara kutsawa, wajen babys suka je, kewaye suka yi, suka duba lafiyar yaran sosai. Sai da suka tabbar suna lafiya, Lazy na ta faman ɗaukar rahoto. Fitowa suka yi, a tare suke ɗaura kafafunsu a ƙasa suna sake ɗagawa. Kai tsaye death room suka nufa, abin da yasa suka sanyawa ɗakin death room shi ne wanda ya shiga baya fitowa da rai, a nan kuma suka kai darling, basa kai mutum wajen sai makamancin abin da suka yi wa darling ya faru da shi, wani lokaci suna yin gwajin wata cuta a jikin yara su kaisu nan, ba a kan darling bane farau, ko idan suka gwada ya yanayin aikin kwarin da suka kirkira ta hanyar sakarwa jaririn suka cijesa, suna kirkirar kwari mai cizon mutane su sanya masu guba a cikin jini, su gurɓata jikin mutum, so suna gwada wannan project ɗin ma a kan jariran da suke kyankyasa. A taƙaice dai dik wani project da suka yi suna gwaji a kan jariran sai su kawosu death room su ajiyesu dan ganin irin karfin cutar. A halin yanzu ba sai na warware maku me dame suke gwadawa a kan jariran nan ba, gaba zaku gani da idanunku, dan suna dayawa. And masu cewa rashin imanin su Dr James ya yi yawa ko dai suna tsafi ne, a'a, basu da haɗi da tsafi, basa tsafi ko kaɗan! Kirkiran cuta da magani, sai kyakkyasar jarirai su fitar Black Market, su yi maganin hana tsufa da jinin jarirai kawai suke yi, zallar bushewar zuciya ce ba tsafi ba, to zuciyar da babu ALLAH a cikinta me ma ba zasu aikata ba? Ai dik randa aka ce ka saki ALLAH wlh babu wanda zai kaika rashin imani, zallar zalunci ne, kuma haka zaku yi hakuri ku karanta, nasan da zafi, amma darasin ciki zaku duba, littafin ZAKUNA BIYAR na faɗa na ƙara faɗa littafi ne dake tamkar rayuwarmu a yau!. A gaban kwalbar da darling yake a ciki suka tsaya, Dr James ya kama jarkar madararsa dake jikin glass ɗin, ya tuge robar dake jiki, sai ya yi mashi worming na madarar tare da mayar mashi. Ɗan zuba mashi idanu suka yi. Ya rabb, wasu irin ƙuraje manya-manyan sun fito mashi a jiki, wasu ƙurajen sun farfashe suna fitar da farin ruwa, fuskansa ta kumbura matuƙa, ƙuraje har kan hanci da idanunsa, bakinsa da ya kumbura sosai ma ƙurajen sun fito sosai a wajen. Dik rigima da kukan nan nasa ya yi tsit, ya rabb, shi kaɗai yasan irin azaban dake jikinsa, jikin nasa tamkar wuta saboda zafi, fatarsa dik ta wani irin ƙoƙe, kyakkyawan ash hair ɗinsa irin na Seraphina ya zama tamkar an zuba mashi suwan starch, gashin ya ƙandare, ya mimmiƙe tsaye tamkar bayan bushiya, idanunsa sun rufe saboda kumburi, kunnuwansa dik sun ƙara girma sosai. A taƙaice ya canza daga halittar ɗan adam, imagine fa, shi fa ruwan cutar da kanta suka zuba mashi a jini, ai dole ya canza daga halittar ɗan adam. Waya Dr James ya fito da shi, video ya ɗaukesa short na second 30, saving ya yi tare da wucewa gaba, su Dr Kamal suka rufa mashi baya. Office ɗinsu suka koma, a gaggauce suka yi shirin tashi a aiki, har karfe 6 ta cika yau basu tashi da wuri ba.......... Fitowa ya yi zai nufi gida, a dake ya kalli Lazy game da cewa. "Dik rahoton yau ki mun submitting a office zan duba da safe, rahoton aikin dashen da muka yi ɗazun ki ajiye mun shi a sama dan da shi zan fara da safe". Tana kallon face ɗinsa ta ce. "Zan je US gobe"........ Kai ya ɗan jinjina tare da cewa. "Kin shirya amsar da zaki baiwa su Zayra'an kenan? Ko dai kin shirya fito na fito da su ne? Ko dai yanzu kin daina tsoron karonki da su ne?". Wani irin faɗuwar gaba ta ji, rabonta da su Lion tin ranar da ya zo gidanta a WASHINGTON, ya yi yunkurin ƙasheta, ta tsira da kyar. Tin a wannan lokaci bata sake ganinsa ba, bata san ya yazama yanzu ba, ba lallai ta iya ganesa bama idan ta gansa, sai dai kar ku manta da ita sak yake kama kafin ta yi surgery, lallai in ta gansa ko dan wannan kamanni zata ganesa. Amma fa bata san Leo yana raye ba, ta zaci ya mutu........ Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Na tabbata ba zasu iya ganeni ba, zan je US gobe, kuma zan taka har CRYSTAL PALACE dik da ba za'a barni in shiga ba, amma zan nemi ganin yarana Zayra'an bin Haiza'an, Aryan bin Khaiza'an, Mahvir bin Ali, Hunaish bin Omar, zan je in ga ya suka zama yanzu, zan roki alfarman a kiranmun Zayra'an, nasan har yanzu yana tare da su Aryan, dan nasan Hussain ya masu huɗubar su kaunaci juna, zan je da suffar mabaraciya ko wani suffa, na tabbata Zayra'an ba zai yasar da halin Haiza'an ba, tabbas yana da tausayin marasa galihu, idan na je da suffar tausayi zai saurareni har ma ya bani sadaka, a nan zan samu damar magninsa, zan ga ya ɗana ya zama". A yadda take furta ɗanta ko kunya bata ji ba, da confidance take ambatar ɗanta ne. Jama'a mu faɗa mata ubanta Lion zai ci ne ko mu kyaleta? Mu faɗa mata ko da wani irin suffa ta zo mashi ba zai saurareta bane ko mu yi shiru? Mu faɗa mata dalilinta yasa Lion bai ɗauki halin Haiza'an na taimako ba, Lion bai yarda da kowa ba a rayuwansa face su Aryan, ko dame ka zo ba zai yarda da kai ba. Jama'a waye yake jiran ganin ranar da zasu haɗu? Waye yake jiran ganin ta je masu a wata suffa sun yi 4 eyes da Lion? Lazy bata da hankali, lallai bata san zakin da Haiza'an ya bari ba. Jama'a kun taɓa tinanin meyasa daddyn Lion bai bari Lazy ta yi renon Lion ba? Kun taɓa tinanin meyasa ya barshi a wani waje a renesa? Hussain ɗinsa ya renesa, kun taɓa tinanin dalili? Uhm jama'a ku ƙara jinjinawa daddy Lion!. Shi kansa wannan zaki nasu Lion da suke kira Hero da kuke gani kula da rayuwan Lion yake yi! Amana aka bashi, wannan Hero akwai tarihi a kansa, kafin ka fara taɓa Lion lallai sai ka fara kashe Hero!. Kai Dr James ya jinjina game da cewa. "Ni kaina ina son sanin ya Zayra'an ɗin nan yake, idan kin samu dama ki ɗauka mana hotonsa, dan ina mahaukacin son ganin bayan da Haiza'an ya bari". Murmushi ta ɗan saki, a wautarta wai yau Dr James ya nemi alfarma a wajenta, cike da yanga ta ce. "Tabbas zan ɗauko maka hotonsa"...... Kai ya jinjina game da cewa. "Safe journey". Da okey ta amsa, sai murna take yi yau ya tsaya sun yi magana, a cikin ranta ta ci alwashin samo mashi hoton Lion, bata tinanin zasu iya yi mashi wani abin, ko da yake yaran basa a gabanta ai, bata damu ba, duniyarta kawai take ci. Me amfanin irin wannan rayuwa? WS sun ce zasu bata matsayi a duniya, zata yi suna, ba kuɗin bane ya dameta, ta zama shugaba shi ne burinta, ga shi bata zama shugaba ta kare a aiki da su Dr James. Amma a tinaninku meyasa bata zama wata mai mulki ba bayan wannan abin da ta yi wa WS?. Kai tsaye gidansu Dr James ya nufa, yana shiga ya haura sama, gidan yana nan tsab-tsab yadda ya same shi ɗazun. Kai tsaye room ɗinsa ya nufa, a natse ya tura door ya shiga. Zaune ya isko sister Maya a saman side sofa, tana karanta littafin nan na ɗazun, while sister Zinta na zaune a gefen bed sanye da rigar ɗazun, suna hira jefi-jefi. Ganinsa yasa sister Maya miƙewa tana faɗin. "Zan je cikin asibiti in duba babys ɗinmu, sai kin zo". Zuwa ta yi ya raɓa shi ta fice. Tsayawa a tsakiyar ɗakin ya yi game da zubawa sister Zinta idanu. Da yake suna da kunya na jinin gado sai ta gagara iya ɗagowa ta kallesa, ta yi ƙasa da kai tana ɗan ɓoye fuska. Gentle ya tako in da take. A gabanta ya ɗan tsugunna, kyakyawawan hannayenta ya riko, ya zubawa face ɗinta idanu. "Welcome sir". Ta faɗa can kasa...... "Are you okey now?"....... Kai ta jinjina mashi alamar e......... "Came on". Ya faɗa tare da ɗan miƙewa ya rungumeta yana ɗan shafa bayanta, hannayenta tasa ta yi hugging ɗinsa tightly. A tare suka sauke ajiyar zuciya, ya ɗan saketa tare da cewa. "Let me bath"....... "Should I help you?". Ta faɗa can ƙasa. Kai ya ɗan girgiza. "Ki huta ina zuwa". Daga nan ya fara rage kayan jikinsa, yana yi yana ƙura mata ido, ita kuwa ta yi ƙasa da kai. Cire kayan ya yi, ya rage daga shi sai shorts, cikin toilet ya nufa. Nisawa ta yi tare da kwanciya tana jin sabon sonsa na shigarta. ----------- silent. After some hours, zaune yake a saman bed ɗinsu, sanye da pjs ash color a jikinsa, ya tasa laptop a gabansa, while sister Zinta na kwance a gefensa, ta tada kai da cinyarsa, shi kuwa yana ta aiki, ya mata girki da kansa, ta ci ta ƙoshi, ya mata wanka da kansa, suka sanya kaya iri ɗaya, ya kwantar da ita, yana shafa kanta yana aikinsa har barci ya ɗauketa, watau wani irin so yake yi wa Zinta na wuce misali, ko motsawa ta yi har cikin ransa yake ji. Video call ya danna a laptop ɗin nasa, ringing ya fara yi, jim kaɗan aka ɗauka. Wani kyakkyawan fuska ne ya bayyana a gaban screen ɗin, kyakkyawan mutum ne, matashi ne da ba zai wuci 25 years ba, suna mugun kama da Dr James sosai, kamar an tsaga kara. "Good evening bro". Dr James ya faɗa. "Evening ƙanina, ya aiki?". ............ Kai jama'a ƙaninsa kuma? Wannan matashin yana nufin ya fi Dr James shekaru? How? Wai kun gansa kuwa? Ɗan yaro fa, amma wai shi ne yayan Dr James? Abin da mamaki. "Cool bro, ya naku aikin?"....…. "Muna da kai ai dole komai ya tafi daidai". Bro ya faɗa..... Kai ya ɗan jinjina yana murmushi kaɗan-kaɗan........ "Ya batun waɗan can kwarin?". Brother ya tambaya..... "They're ready, ko yanzu kuke da buƙata zaku samesu, amma ni bro ina son sanin me World system zata yi da waɗan nan kwari? Me zaku yi da shi?". Siririn one side smiling brother ya saki kafin ya ce. "Wata ƙasa zamu ladabtar, sun kawo mana taurin kai da tsaurin ido ne, shiyasa muke san yi masu azaba ta wannan hanya, mu sakar masu kwarin da zasu cijesu suna sanya masu guba a jiki"...... "To shi kuma NEXAPOS-31 fa? Sai yaushe zaku yi amfani da ita?"........ Shiru brother ya ɗan yi. "A sabuwar gwamnati, sai gab zaɓe, amma kasan bamu da tabbas, idan aka ɓata mana rai a yau muna iya sakinta wa duniya, kawai dai mun fi son sai an yi zaɓene, idan aka samu sabuwar gwamnatin sai mu kiɗima hankalin duniya!". "To amma bro kwanaki ka ce mun kuna shirin canza yanayin duniya bakiɗaya, kuna shirin extreme climate crisis, kun saka na kirkiro maku kwayoyin cutar da zasu sanya mutane mugun zazzaɓi mai tsananin karfi da zafi, kuma mun fitar maku da kwayar cutar, amma baka sake magana a kai ba". Kai brother ya ɗan jinjina. "Already wannan magani naka ya isha ga al'ummar duniya, sai dai yana cikin asibitoci musamman asibitocin gwamnati, ba mun yi amfani da kwali da kalar maganin da gwamnati take rabawa kyauta ne ai, ka kwashe asalin ingantattun magungunar, ka shigar da namu, kasan mutane da son banza, tin da an ce na kyauta ne zasu dinga karɓa suna sha, basu san shawowa kansu suke yi ba, to tuni har maganin ya fara bazuwa". One side smile Dr James ya saki kafin ya ce. "Naga wasu likitocin sayar da maganin kyautar ma suke yi ai suna karɓar kuɗaɗe". ......... "Basu san marasa kyau ɗin bane ai,

Chapter 78 of 95