Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma babu alamar zai amsa Noor. Shiru ya tsaya zuciyansa sam babu daɗi na abin da Leo yake yi masu, amma ya zasu yi? Dole sai hakuri. Ko sunan Leo ɗin fa basu sani ba, kuma wai suna ɗaki guda. Jin shiru yasa dad ya ce. "Are you okay pleasure?". Da sauri ya amsa da. "Yes dad". Ya faɗa yana juyawa ya bar wajen. "Is there any problem?". Dad ya tambaya, da sauri ya girgiza kai alamar a'a, sai ya haye bed ɗinsa ya kwanta zuciya babu daɗi. Haka suka cigaba da hira da daddyn nasa har barci ya ɗauke su Zaynash, sun shafe 2 hours suna hira, da alamar shakuwa da kaunar juna matuƙa a tsakaninsu. Sai can suka yi sallama, ya katse kiran tare da kashe wayar bakiɗaya, daga nan ya hau barci shi ma. Ɗakin ta yi tsit alamar dik sun yi barci harta Leo ɗin ma. --------------------------🔥 NEW YORK. CRYSTAL PALACE. Ayi hakuri da zaman da zan yi wajen bayanin inane CRYSTAL PALACE, zan yi hakan ce dan ba zan sake bayani a kanta ba, kuma zan yi hakance dan na tabbata ba kowa yasan irin ginin da nike nufi ba har sai na yi bayani, bugu da kari CRYSTAL PALACE tana da alaƙa da kusan kowa dake a cikin wannan littafi, dik wata rikici daga cikinta yake fitowa, shiyasa dole zan daure in sha wahalar typing dan fayyace maku tsarinta dallah-dallah!. CRYSTAL PALACE. Watau duniyar glass masu bala'in kyau da kyalli game da ɗaukar hankali, duniya ce guda mai zaman kanta, cikin CRYSTAL zaku rantse da ALLAH kasa ce or gari mai zaman kanta, wajen da ke haskakawa kamar rana, amma mu shiga cikin domin ku ganewa idanunku. Katafaren yankin da na tabbata baku taɓa cin karo da irinsa ba. Wasu irin jiga-jigan hyper glass skyscrapers a wajen, gine-gine masu hawa 30 zuwa 50, dik na glasses masu canza launi bisa yanayi gari, suna ƙyalli kamar lu'u-lu'u, tare da golden edges. Akwai manya-manyan solar gardens, lambunan zamani masu amfani da hasken rana, sannan suke canza launi da dare su bada sky blue light mai ƙara ƙawata wajen da ɗaukar hankali. CRYSTAL PALACE gamayyan gidaje ne masu hawa 30 zuwa 50 da a ƙallah zasu kai 20 a wajen, dikka ƴan haya ne cike a cikin, idan har aka kama maku kuɗin da suke biyan hayan kowani hawa ɗaya a shekara ya isa sayen katafaren gida na alfarma a Abuja Naija, sannan dik kuɗaɗɗen suna tafiya ne wani asusu guda ɗaya, haka na nufin mallakin mutum ɗaya ne. Akwai infinity sky villas, wasu box masu zubin gidaje ne masu shawagi a iska, haɗe da smart levitation technology, ba kamar gidajen zama bane, a'a, su na yawon shaƙatawa ne a sararin samaniya, idan kun gaji da zaman cikin gida kuna da damar fita ki yanki ticket ku shiga wannan karamun box zai yi sama daku kamar ƙaramin jirgi, sai dai a iya sararin samaniyar CRYSTAL yake tsayawa baya zuwa wani wajen. Ga watsu rantsasstsun neon quantum roads, titunan da ke haske bisa tafiyar mutane da motocin zamani. Ga wasu magnetic highways, hanyoyin mota da ba sa buƙatar taya, sai fasahar levitation. A saman waɗan nan tituna akwai wasu jiga-jigan Guards madaka ƙarti dake kai komo suna shawagi dan tabbatar da tsaro, kuɗin da ake biyan waɗan nan Guards ɗin kawai arzikin wani kamshaƙi ne a Naija. Sannan akwai hanyoyi a sama, sky walkways, hanya ce da ta fita daga wannan gini izuwa wannan amma ta sama, kowani hawa akwai hanyoyin da suka sada gine-ginen, ba sai ka sauƙo kasa ka sake hayewa sama idan zaka je wajen mutum ba. Akwai ƙayatattun wuraren hutawa a ciki irinsu ethereal beach, wani nau'in teku da ke canza launi a bisa lokacin dare ko rana, ba kato sosai bane, an yisa ne dan mazauna CRYSTAL ɗin su mori kuɗin hayansu da kyau. Ba iya su aka tsaya ba, akwai cloud nine resort, wurin hutawa mai shawagi a saman gajimare! Amma shi ma a iya sararin samaniyar CRYSTAL ɗin ne. Lunar reflection park, wani kaɗaɗɗen lambun da ke hasken launin wata, saman lambun wasu kyawawan taurari ne aka yi kwalliya da su dake ƙarawa wajen kyau. Akwai Crystal sphere arena, wajen taruka, wasanni, kallon cinima dan kallon film ko wani abin, da wajen nishaɗi da aka yi amfani da fasahar hologram. Irin solar da ake amfani da shi a CRYSTAL yana bada wutar lantarki ba irin solar da aka sani bane, domin kuwa su haɗe yake da views ɗinsu, idan rana ta daki glasses na windows ɗin sai wutar lantarki ta samu, batiransu na chanji wanda yasa ko dare ce wuta bata taɓa ɗauke masu. Babu ƴan aiki a CRYSTAL PALACE, domin kowani gida akwai robot dake aiki bisa umarnin mazauna wannan gida. Akwai SOLARIS CORE, wani katafaren gini ne wanda ya kasance cibiyar kasuwanci, a nan kasuwansu yake, super market kala daban-daban a ciki dan yin shopping ba sai sun fita waje ba. Dan a kara ƙawata CRYSTAL PALACE kawai sai aka yi wasu floating luxury malls a saman, idan kana so zaka iya zuwa can ka yi shopping ɗinka hankali kwance. KAI TURAWA FA SUN CI GABA, YANZU NASAN WASU SUNA NAN SUNA TINANIN ANYA AKWAI DIK ABIN DA NA KIRGAN NAN A GASKE KUWA? TO DIK AKWAISU SARAI, IN BAKU JE IN DA SUKE BA KUN KARANTA A NOVEL ƊINA, SHIYASA NA DAURE NIKE MAKU BAYANINSU DALLAH-DALLAH DAN KU GANE, NAIJA MA MUKE DA KANANAN GINE-GINE IRIN ESTATE BARE SU? AI SUN SHAHARA A GINE-GINE SHIGEN CRYSTAL PALACE TIN TINI. Ga wani katafaren elysium cloud lounge, wajen cin abinci ne a sama mai balain kyau da ɗaukar hankalin wanda aka tsara shi sosai. Yanayin tsarin tsaron wajen, akwai irin drone security ɗin nan, ƙananan jirage dake kula da tsaro dare da rana, da zarar sun ga wani motsin da basu yarda da shi ba zasu hau kara take Guards su ɗauki matakin gano meke gudana ko wace barazana ke zuwa. Ga irin bio scanning entryways, babu wanda zai shiga yankin ba tare da kowa dake cikin gidansa ya gane waye ya shigo CRYSTAL PALACE a yau ba! Dan akwai tv da aka haɗa da bio scanning ɗin a kowani gida dake wajen. Dik da haka akwai quantum shielding system, tsarin wall da aka kewaye wajen mai amfani ne da wutar lantarki dan kare yankin daga barazana ta waje, ko jingina daga waje ka yi da jikin bango sai ka ji shocking, kuma bulletproof ne wall ɗin, ga wani katafaren CRYSTAL PALACE HOSPITAL a takaice mu ce CHP, hospital ne dan kula da lafiyarsu, asibiti ne wanda shi ne na huɗu a duniya wajen karfi da kayan aiki game da manyan jiga-jigan likitoci. Gate guda biyar ne na shigowa CRYSTAL, wanda kuma dikka gate ɗin suna da mahaukatan tsaro na ban mamaki, ba sai na faɗa maku haɗuwar gidajen dake cikin CRYSTAL ba, saboda makurar haɗuwa ne, dik wanda kuka gani cikin CRYSTAL babban kai ne, ya kai yadda ba'a tinani, wane karamin kai da iya kama haya a cikinsa. To a duniya gabaɗaya irin CRYSTAL PALACE guda huɗu ne kawai, kun taɓa jin labarin THE LINE NA SAUDIYA AND THE CIRCLE NA DUBAI? to su ne guda biyun CRYSTAL cikon na uku sai kuma wani a nan cikin US ɗin shi ne na huɗu, sai dai THE LINE AND THE CIRCLE kunga mallakin gwamnatin kasashen ne, kuma bama a fiddasu ba, shi kuma CRYSTAL mallakin wani mutum ne wanda su kansu mazauna wajen basu san ainahin mai wajen ba, dan an ce ya fi shekaru 10 da mutuwa, wasu sun ce yana prison and ɗauresa life in prison, dan haka yanzu wajen tana karkashin kulawar wani ne daban, to koma dai menene mu je zuwa dan abin dayawa. A takaice yadda Crystal yake kenan. Gidajen cikin CRYSTAL ɗin nan dikka an kama hayansu, babu empty, kada ku manta gidaje ne guda 20, kuma dikkansu benaye ne masu hawa 30 zuwa 50, amma dik wasu manya dake jin kansu a ƙasar sun kama haya suna ciki da family ɗinsu, dan yanayin tsaruwar wajen da kuma karfin tsaronsu, dan ko tsuntsuwa bata isa wucewa ta sararin samaniyarsu ba na'ura zata harbota ko ta kaɗata wani waje, zallar basira da technology aka zuba wajen tsara wannan gini, shiyasa ya fita daban......... Wannan ma na takaita maku haɗuwar CRYSTAL PALACE wlh. ----------------------- Kai tsaye mu wuce Crystal Palace Hospital, watau CPH. A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka yi mata mugun nauyi, tana son motsa jikinta amma ta gagara, da kyar ta yi karfin halin waro idanunta waje. Ya subhanallah, idanun nata sun yi jajir sun kumbura matuƙa, sun zama abin tsoro. Zazzarosu sosai ta yi tana bin in da take da kallo, ganin bata gane ko'ina bane wajen yasa ta ɗan motsa lips ɗinta da suka yi mata nauyin tsiya, tongue ɗinta tamkar an ɗaɗɗauresa, da kyar ta iya cewa. "Mammy, mammy where are you?". Shiru babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta yunkura zata miƙe, sai ta ƙasa, a nan ta ji alamar jikinta a ɗaure yake, ƙoƙarin sauƙo da kallonta izuwa jikin nata ta yi, a daidai lokacin aka turo kofar room ɗin wanda hakan yasa ta wurga eyes ɗinta can. Wani mutum ne ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin drip guda biyu. Sanye yake da tail coat, kafafunsa na cikin wasu haɗaɗun cover shoes masu tsadar gaske, fuskansa a sanye da nose mark, kansa sanye da hat, gabaɗaya kayan jikinsa bakake ne harta socks dake kafafunsa. Yana shigowa ya sauƙe kyawawan dara-daran eyes ɗinsa a kanta, while ita ma shi take kallo, dik da yana sanye da nose mask hakan ba zai hana ka gane cewa haɗaɗɗe bane. Yana da tsawo sosai, ga cikar halittar, dik in da ake neman namiji wannan ya kai. Ganin idanunta biyu yasa intently ya iso gaban bed ɗin, a gefe ya ajiye drip ɗin kafin ya mai da kallonsa a kanta da kyau. Can ƙasa ya ce. "Had luck". Ya faɗa yana kai hannu zai riko nata hannun. Da sauri ta janye baya, da kyar ta iya sake cewa. "Who are you and where is my mammy?". A maimakon ya amsa mata sai ya kai hannu ya kama nata, a natse ya zare mata drip da ya kare yana faman jan jininta. Bayan ya cire ne ya zauna saman sofar dake kusa da ita, bai sake yi mata magana ba, da ganin haka ita ma bata sake yi mashi magana ba, ta yi shiru tana tinanin ina mahaifiyarta take?!. Daga karshe ta yunkura, a hankali ta miƙe zaune a tsakiyar haɗaɗɗen bed ɗin da ba zaka taɓa cewa na majinyata bane. Ƴan kafafunta ta yi ƙoƙarin zurowa ƙasa, sai dai ina, gadon yana da tudu bata iya taɓo ƙasa ba, ɗan shagwaɓe fuska ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, kai kallonta a kansa ta yi, ya sunkuyar da kai shiru tamkar ba mutum a cikin ɗakin. Turo baki ta yi tare da gyarawa ta matsa bakin bed ɗin sosai. Dirowa ƙasa da karfi ta yi a in da ta tafi gabaɗaya zata faɗi ya miƙe kafansa ɗaya ya tareta, ashe dama yana kallonta, da ta faɗo forehead ɗinta zai bugu da tiles ɗin ne, sai ya tare kan nata ya bugu da kafarsa. Slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta, bai yi magana ba yasa hannu ya kama nata hannun, da hannu ɗaya ya ɗagata tare da miƙewa tsaye ya jefata kan gadon. A kan face ɗinta ya tsayar da idanunsa, still dai babu alamar zai yi magana. Yanayinsa yadda kuka san wani shahararren gangster haka. Komawa ya yi ya zauna tare da ciro wayansa daga aljihu, intently ya fara latsa wayar yana typing message. Ɗan zuba mashi idanu ta yi, sai kuma ta turo baki, take dara-dara violet eyes ɗinta suka cika tab da kwallah, a fili ta ce. "Where are you mammy? I'm so scared here, come and take me away from here". Cikin kwararriyar turancinta ta yi maganar, voice ɗinta ba dai daɗi da sanyi ba, ga zallar madarar shagwaɓa. Yana jinta sarai, amma ko motsi bai yi ba, yana cigaba da latsa wayarsa. Ganin babu mai kulata ne yasa ta lallaɓa ta koma ta kwanta shiru. Kyakkyawar yarinyar karshen haɗuwa, gashin kanta light ash very silky haka, ga wani irin sheki da yake yi, violet eyes ɗinta dara-dara farare tas da su. ----------- silent for almost 40 mins ne ya biyo baya kafin wasu nurses guda biyu suka katse masu shirun ta hanyar shigowa. Ɗaya hannunta rike da wata ƴar CPH-note-b, ɗayar kuma hannunta rike da babban leda mai shaƙe da magunguna. A gaban bed ɗin suka tsaya, mai rike da magungunan ne ta miƙawa guy ɗin tana faɗin. "Here's her drugs, make sure she's taking it on time". Hannu yasa ya karɓi magungunan ba tare da ya kalli in da suke ba, ita kuma ɗayar nurse ɗin miƙa mashi note-b ɗin ta yi, saƙon sallama ne, takarda ce mai ɗauke da sunan CRYSTAL PALACE HOSPITAL da sauran bayanan yarinyar, me dalilin kwanciyarta, kwananta nawa, kuɗin da aka cajesu, kai komai dai, a karshe time da date da aka sallameta. Sannan takardan nashi ne, dan idan ba mazauna CRYSTAL ba babu wanda yake da irin takardan, din in zaka kwanta jinya sai ka zo da notebook ɗin, a nan za'a cigaba da yi maka rubuce-rubuce har ranar sallama!. Nan ma karɓa ya yi, ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye, gentle ya tako zuwa gaban bed ɗin. Hannu ɗaya yasa ya ɗauki yarinyar sai saman shoulder ɗinsa, bai bi ta kansu ba ya nufi waje. Yana fitowa wasu jiga-jigan guards masu zubin gangsters su uku suka take mashi baya da gudu. Kai tsaye wajen wani dankareren mota ya nufa, tin kafin ya iso wasu guards madaka karti dake kusa da motar suka ɓalle mashi back door. Ciki ya jefa yarinyar kamar yaki, sannan ya shiga gidan bayan shi ma. Da sauri suka mayar da door ɗin suka rufe, da wani irin gudun karti suka nufi sauran motocin dake wajen, da gudun gaske suka ja motocin suka kutsa cikin C-P (CRYSTAL PALACE) Ita dai taga ikon God, sai kawai ta hau binsu da kallo, tam daina magana tin da har yanzu ba'a samu mai iya amsa mata ba. Ɗaya daga cikin shahararrun ginin da ya fi ƙawatuwa a wajen suka nufa, shi hawa 10 ne kawai, sannan shi gabaɗaya glass nasa sky blue ne babu mix. A parking lot na gidan suka paka motocin, da gudu wasu kartin guards dake shawagi a gidan suka nufo motocin. Nasa suka fara ɓuɗewa kafin na kowa. Fitowa ya yi cikin zafin nama, yasa hannu ya ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa, hannunsa ɗaya rike da drugs ɗinta. Ita dai shiru kawai ta yi tana kallon ikon God. Kai tsaye elevator ya nufa, daga kan yadda yake tafiya zaku san lallai wannan shahararren gangster ne, tafiyarsa babu wasa ko sanyin jiki. Hawa na biyar ya haye. A wani katafaren parlo mai tsananin kyau ya dakata. Shiru ya ɗan tsaya kamar na 1 minute, sai kuma ya nufi wani door dake fuskantosa. Yana zuwa ya ɗan taɓa handle na door ɗin sai ga shi ya buɗe kansa. Wani katafaren sleeping door ne, katon bed ne kawai a ciki, yana shinfiɗe da wani haɗaɗɗen bedsheet na alfarma white kala, da one side sofa. Sai kofar toilet and balcony wanda dik da glass aka yi su kun sani. A saman bed ɗin ya direta tare da ɗaura drugs ɗinta a gefenta, daga haka ya juya bai sake kallon in da take ba. Parlo ya fito, kai tsaye ya nufi wani madaidaicin door dake fuskantar ɗakin da ya fito. Wani haɗaɗɗen dry kitchen ne a wajen, da alama babu kowa a gidan sai shi kaɗai. Kyakkyawan pot ya ɗauko daga cikin pot set ɗinsa, ruwa ya zuba a ciki tare da buɗe drawers na sama ya ɗauko wani ɗan karamain bottle, wani green leaf ya ɗebo daga ciki, ya zuba cikin ruwan pot ɗin, sannan ya ɗauko wani bottle na honey. Kaɗan ya zuba zuman a ciki, ya kunna gas, a kai ya ɗaura tare da nufo waje. Yana fitowa ita ma ta fito daga room ɗin da ɗan gudunta tana faɗin. "Mammy I don't want to stay here, please come and take me away from here". Tana kuka sosai da hawayenta. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, sai ya nufi wani siririn hanya dake kusa da glass wall dining room dake cikin parlon. Da kallo ta bisa, a ranta ta ce ko dai baya magana ne?. A fili kuwa hawaye na cigaba da tsere a kan fuskanta sosai. Tana ganinsa ya yi amfani da remote wajen sauƙo da staircase daga sama, sannan ya haura sama abinsa ya kyaleta tsaye kamar wata doluwa. Zaman dirshan ta yi a ƙasa tare da sanya hannayenta dikka biyu ta fara watsa kyakkyawan ash hair ɗinta tana cigaba da kuka. Lokaci guda kuma ta ɗan kwaɓe fuska tana ɗage hanci sama wai jikinta na tsamin datti, dan yau kwanakinta uku a asibiti bata yi wanka ba, kuma babu wanda ya yi mata, tin da suka kawota ma shi sai jita ya je, tana sume aka kaita, daren jiya ta farfaɗo tana kuka kenan aka yi mata alluran barci, bata tashi ba sai ɗazun. Farfaɗowarta jiya yasa aka kirasa a waya ya zo, tin kuma da ya fita wajenta jiyan sai yanzu ya koma ya ɗaukota da likitocin suka sanar da shi ta samu lafiya zai iya tafiya da ita. Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Wannan yarinya ba kowa bace face ƴar Dr Hushaima ALLAH jiƙan rai, da alama kuma wannan mutumi shi ne bahagon murɗaɗɗen mutumin da Dr ta taimaka dik da ban sani ba, hasashe nake yi, naga halinsu na rashin magana iri ɗaya ne da wancan, to wai ma su waye su ne?. To yanzu dai mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi yarinyar Dr ta tsira?. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. 4-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________5 Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi ta tsira?. A lokacin da Dr ta fita ɗakin da gudu ta nufi room na ƴarta a lokacin shi ma ya miƙe daga gadon, in baku manta ba ai bata yi mashi alluran barci ba, so idanunsa biyu, yana jin dik abin dake faruwa. Fitowa daga room ɗin ya yi ta hanyar dafa bango, dan jikinsa dik babu karfi ko kaɗan, da kyar ma yake iya motsawa, amma saboda yasan musifar da yake a ciki sai ya yi tinanin dik yadda aka yi shi ake nema yasa aka shigo gidan again. Cigaba da tafiya ya yi har zuwa wajen staircase, zai taka stair ɗin kenan su Eagle suka banko parlo door. Ganinsu yasa ya fasa sauƙa, dan jikinsa babu wani karfin da zai iya kwatar kansa, sai ya matsa baya, a maimakon ya koma room ɗin can sai ya kara gaba, a nan ya ci karo da room na ƴarta, buɗe door ɗin ya yi ya shiga ciki. Yana sanya kai daidai lokacin yarinyar ta farka, ta zauna a saman bed tana faɗin. "Mammy I want to dring water". Laluɓar hanya a cikin duhu ya yi izuwa wajen switch, sai da ya kusa kewaye room ɗin kafin ya gano switch ɗin. Kunna light ɗin ya yi, take haske ya gauraye room ɗin. Da sauri Seraph ta ɗago kanta ganin haske tana faɗin. "Mammy a little water......". Bata iya karisa maganar ba ganin mutum a tsaye ga bandeji a hannu, bugu da kari bata iya ganin face ɗinsa. Wani irin razana ta yi tare da zazzaro voilet eyes ɗinta a kansa. Wani irin kallo ya bita da shi, wanda ita bata san yana kallon nata ba saboda nose mask ɗinsa, ga p-cap daga cikin hular jacket ɗinsa. Cigaba da zazzare ido a kansa ta yi, tana kallonsa from up to down. A daidai lokacin ya ji motsin mutanen, a tinaninsa suna shigowa room ɗin ne, sai dai kuma a lokacin suka wuce da Dr zuwa ICU ɗinta. Jin motsinsu yasa ya daure tare da takowa izuwa wajen bed ɗin nata. Hannunsa ɗaya mara ciwon nan ya sanya tare da ɗaukar yarinyar, tana ƙoƙarin kurma ihu ya yi amfani da hannunsa mai ciwon ya rufe mata bakda tafukansa. Wajen view ɗinta ya dawo, da kyar ya iya buɗewa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya dake suka fita ta view ɗin, a saman wani ɗan dakali a wajen ya zauna da ita a jikinsa. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi da iya karfinta, ganin zata iya ja su faɗi kasa tin da wajen ba wani mai faɗi bane, irin dakalin nan ne da ake yi na saman window ɗin toilet ko na ɗaki hakan nan ne, to a wajen window toilet suka zauna, ganin zata ja su faɗi ne yasa ya sanya hannunsa ya zame hular jacket ɗin kansa, ya ɗan kawar da p-cap na kansa gefe dan ta samu damar ganin idonsa, sai ya zame hannunsa daga bakinta ya ɗago haɓart suna fuskantar juna. Wani irin zaro ido waje tai tamkar kwayarta zasu faɗo ƙasa a lokacin da ta ga jajayen idanunsa tamkar wuta, dik da bata kalli face ɗinsa gabaɗaya ba ta wani irin mahaukacin razana, take ta kame waje guda kamar ta sume, dan numfashinta ya ɗauke, idanunsa sun yi wani irin ja tamkar jini ne a ciki, dik wanda ALLAH ya bashi ikon haɗa ido da wannan guy a wannan lokaci ko bai suma ba kaɗan ne zata rage mashi saboda firgici. Ganin ta ɗauke wuta ne yasa ya mayar da hulansa, slowly ya kwantar da kanta a gefen chest ɗinsa, ya ɗan rintse idanunsa saboda tsananin zafin da hannunsa yake yi mashi, alluran kashe zafin ta fara sauƙa, kun san dole akwai zafi. Yana jin motsin yaran Eagle suka shigo room na yarinyar. In takaice maku labari har suka kashe Dr yana wajen da yarinyar, ba zai iya zuwa ya ceci Dr ba, saboda shi kansa taimako yake nema a yanzu. Jin shiru alamar sun bar ɗakin yarinyar yasa ya kokarta ya miƙe da ita, daga alama shahararren ɗan ta'adda ne, yadda yake da dauriya da karfi kamar wani doki, dik yadda aka yi ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba. Da kyar ya lallaɓa ya kama room view suka komo cikin ɗakin, ya so dira ƙasa ya bar gidan, amma ha zai iya dira da ita ba, kunga ga ciwo a hannu, ga kuma nauyinta, jikinsa ba karfi, idan suka dira a tare zata iya jin ciwo koma ta bugu a in da ba zata rayu ba, shi ma kuma haka. So dole ya mayar da ita cikin ɗakin, bata ko motsi. Cikin toile ya kaita, a cikin jaccuzi ya kwantar da ita tare da fitowa, dispenser dake room ɗin nata ya ja zuwa toilet ɗin, da kyar ya ɗaukesa ya ɗaura a saman Jacuzzin, ya rufeta, sannan ya fito, ya koma ta view, ya dinga lallaɓawa a hankali ya sauƙo, a lokacin sun kunnawa gidan wuta sun fita. Shi ma fita ya yi. Yasan da wuya wutar ta kamata, dan a cikin Jaccuzi ya kwantar da ita, ga disperser ɗin da ya ɗaura mata, shiyasa washegari ya tura yaransa su ɗaukota da dik

Chapter 8 of 95