Noor sarkin son jiki tuni ya kwanta mashi a jiki har da kukan shagwaɓa, yau ya tuna da su Aunty Lusi, yadda yake yi masu ya hau yi wa Leo yau, shi kuma ya daure yana ta biye mashi, dan Noor ya shiga ransa matuƙa.
A gefe guda kuwa su Arya bayan sun dawo da school sun yi lunch V ta ce zata tafi wajen daddy, da sauri Arya ta hanata ta hanyar cewa su je su buga basketball a wajen game ɗinsu. Ba dan ta so ba ta yarda, kuma babu rabon haɗuwarta da Noor nan kusa!.
Arya ta raba masu team, suna sanya sportswear iri ɗaya kaunin milk color. Arya ta ɗauki basketball ɗin nasu suka nufi wajen wasanninsu. Katafaren fili ne da GAT yasa aka ƙawata masu shi, kayan wasanni ne kala-kala a cike a ciki, akwai wajen football, basketball, snooker, har wajensu whots akwai, kwallon kwando da komai dai.
Raba kansu suka yi team biyu, Arya da Manassa, Angelie and V. Akwai wasu zaratan sojoji dake tsaron wajen wasan, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna suna satar kallonsu Arya. Ga shi sportswear ɗin nasu guntun wando ke zuwa tsala-stala cinyoyinsu dake wani irin glowing, very soft. Daga sama rigar tasu mai ƙaramar hannu ce, kayan dai yai masu kyau sosai.
Da suka fara ball ɗin dik in da suka yi idanun sojojin nan a kansu yake, musamman V da ko'ina yake cike dam, ai tana tashin kan mutane. Cikin nishaɗi suke wasanninsu cike da kaunar juna, Arya dai ta yi wa V wayau ta hanata zuwa ganin masoyi Leo.
A can cikin barrack kuwa zama Vash and Zaysh suka yi a saman wasu kujerun dake arear wajen horonsu. Suna zama Zaysh ya ce. "Bro kasan akwai mata a training ɗin nan?". Da sauri Vash ya amsa da. "Yeah, three days ago na haɗu da wata kyakkyawa a kusa da Senior staff side".
Shiru Zaysh ya ɗan yi kafin ya ce. "Ni kuma almost a month ago, mun yi karo da wata, kuma tin time ɗin ban sake ganinta ba"......... "Bar zancensu kira mana Ummie mu gaisa, na yi kewarta, jiya bamu yi waya ba"....... Watau idan kana da kyan hali kowa nemanka zai dinga yi!.
Wayansa ya je ɗaki ya ɗauko ya dawo, yana kunnata saƙon Ummie na shigowa. "Koman dare idan ka samu lokaci ka kirani". Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa, haka kawai ya ji faɗuwar gaba, cikin zafa ya laluɓo numberta ya danna kira.
A lokacin tana zaune saman kujerarta da ya gama shan wahala, dama ba wani qualityn kirki ba. Kiran na shigowa ta yi gaggawar ɗagawa, muryanta na rawa ta ce. "Hello"........ Sai da ya ji kirjinsa ta buga kafin ya amsa da. "Ummie lafiya?".
Kuka ta rushe mashi da shi, da kyar cikin kuka ta iya cewa. "Zaynish na shiga uku, yayanka aure zai kara, ƴan uwansa sun ce ya kara aure tin da ni bana haihuwa"....... Ɗan waro idanunsa a kan face ɗin Vash ya yi, idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, a duniya babu abin da ya tsana irin ya ga tashin hankalinta, yau da yana da dama babu wanda ya isa yasa mijinta ƙara aure, amma bashi da shi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da kyar ya saita natsuwansa tare da cewa.
"Ummie ki yi hakuri ki yi shiru mu yi magana kin ji?"....... Da kyar ta iya amsawa da. "Na gagara dannewa ne, Zay wai fa ƴar wannan gwaggon nasu masifaffiyar zai auro! Wannan yarinya mara kunya da ka taɓa wankawa mari lokacin da ta ce zata dakeni, ita fa suka ce ya aura! Wai ni me na yi masu ne? Meyasa suka tsaneni? Na yi wani laifi ne? Zay kada ka ɓoye mun, ka faɗa mun tsakaninka da ALLAH me laifina in gyara!". Tana kuka tamkar ranta zai fita.
Miƙewa tsaye ya yi, ya ɗan matsa gaba kaɗan dik da Vash baya jin yarensu, amma shi mutum ne mai son sirri da mugun zurfin ciki, yasan ko a yanayin maganarsa Vash zai fahimci wasu abubuwa.
"Ummie baki da wata matsala, ki natsu, kin manta kece kike ce mun ALLAH na jarabbatar mutanen kirki ne? Kin manta kece kike ce mun a kowani hali nike ciki kada na manta da ALLAH ne? Yanzu ki rufe idanunki, ki ambaci sunan ALLAH sau uku a jere kafin mu cigaba da magana"....... Shi ma dauriya ce kawai yake yi, amma zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje.
Cikin kuka ta amsa abin da ya ce, cike da yaki da yarda da ALLAH ta rufe idanunta ta ambaci sunan ALLAH sau uku a jere, take ta ji zuciyanta ya yi sanyi, dik wani raɗaɗi ya kau, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannu ta goge hawayeta. A natse ta ce. "Nagode wa ALLAH da ya bani ɗan uwa kamar kai".
Ajiyar zuciyan shi ma ya sauke kafin ya amsa da. "Nafiki farinciki idan na tuna kece ƴar uwata"...... Kara nisawa ta yi tare da cewa. "To na yarda, yanzu dai ka bani shawara ɗan uwana"....... "To shikenan, yanzu dai so nike ki kwantar da hankalinki, ki natsu, sannan ki bani aron kunnenki"........ Gyara zama da kyau ta yi, ta kara sauke ajiyar zuciya kafin ta ce. "Ina jinka rabin raina".
"So nike ki kara hakuri kan wanda kike dashi, ina ji a jikina wahalarki kaɗan ce ta rage, ki mai da komai ba komai ba, dik abin da za'ayi ki toshe kunnuwanki, ki rufe idanunki, kada ki taɓa nuna kamar kin san suna yi, ko ita yarinyar da zai aura kada ki taɓa nuna mata kamar kin damu, ki nunawa yaya kina supporting ɗinsa, zan tura maki kuɗi ku fara business, ki mai da hankali kan kasuwancinki, ki kuma cigaba da addu'a, ALLAH baya barci, kuma babu wanda zai baki haihuwa a duniyar nan face shi, tabbas kuma bai manta dake ba, amma dik da haka ki dage da addu'a, ki dage da tashi sallar dare, ki kai kukanki garesa, ki koma gefe ki huda ganye kina kallonsu, ina da tabbacin ALLAH zai dubeki da idanun rahama, sai warware mana dikkan matsalolinmu".
Sosai ta ji kwarin gwiwar kalamansa, amma sai ta ce. "A ina ka samu kuɗin da zaka bani in fara sana'a?"...... Bai ɓoye mata komai ba, ya faɗa mata kuɗin da Vash ya bashi, idan zai canza kuɗin ya turo mata sun kai 3M, jin kuɗin da bata taɓa ganin kwatansu bane yasa ta kiɗime, hankalinta a tashe ta ce. "Zay anya mutanen kirki ne kuwa? Kuɗi har miliyan uku zasu baka kyauta? Ni kam gaskiya ina tsoro, ka rabu da su to". Dik ta rikice.
Natsuwa ya yi ya kara yi mata bayani da kyau har ta fahimta, sannan ya ce zai tura mata 2.5 shi kuma zai bar sauran a hannunsa, ya ce ta samu sana'a mai kyau ta kama. Cike da murna ta ce mashi to zata sayi kayan gado da kujeru masu kyau ko da na 1m ne, dan ita ma ta sabonta ɗakinta kafin amarya ta zo.
Na'am ya yi da wannan shawara tata, daga nan ya ce ta nemo account ta turo mashi zai tura mata, ta dai tsaya a kan sana'ar da zata kama sosai, kada ta yi wasa!. Ai mancewa da batun kishiya ta yi, ta dinga murna, har da dariya mai sauti, daga nan ya koma ya haɗata da Vash, suka gaisa ta dinga yi mashi godiya cike da murna, mamaki Vash ya dinga yi a kan meyasa take yi mashi godiya har haka ne? Dan ya ɗan hawa Zaysh ɗan wannan kuɗi da bai wuci na kashewansu a wuni idan suka so ba!
Haka dai ya amsa da okey, daga nan Ummie ta yi masu addu'oin da ta saba, suka yi sallama, shi ma Zaysh suka yi sallama, ya koma ya zauna suka cigaba da hira da Vash.
---------------------🔥
Haka rayuwar matasan sojojin nan ya cigaba da tafiya har suka ɗauke basic training na tsawon watani, a nan manyansu suka ga room 1, room 2 zuwa room 3 suka da kaifin ƙwaƙwalwa da kwarewa, dan haka sai aka fara basu horon jami'an na musamman, misali kamar a Nigeria ce jami'an NDA haka, su jami'ai ne da kwarewarsu ya zarce yadda ake tinani, dan shi horonsu ma na shekaru biyu ake yi masu, amma a Nigeria horon yana iya kai shekaru uku, sai dai su AVARIS a shekaru biyu jami'i ya zama kwararre, basa ɓata lokaci kuma basa ɗaukar wasa. Dan haka su Noor suka shiga fagen horon jami'ai na musamman da iya gwabzawa a ƙasa da ƙasa, ga karatun da suke karɓa tamkar a school, har yau Unays, Zaysh, Leo basa shiri, kuma har yau Leo bai yafe dukan da aka yi wa Noor ba, sauran jami'ai sun yi passing out a watanni shidda nan, su kuma an matsa da su gaba, wani wajen da aka kaisu ba mai iya samun damar ganinsu, ko fitowa basa yi, barci a ƙurarren lokaci tashi a farkon lokaci, komai an ninka masu ukun na baya.
A ɓangaren su Arya ma hakan ce, sun dukufa a kan aikinsu babu kama hannun yaro, sun mayar da hankali sosai.
To zan ɗan taƙaice training ɗin nan ne ba dan komai ba sai dan labarin yana gaba, manyan abubuwan da yakamata ku sani suna gaba ne, kada mu ja lokaci a horar da su! Dan tafiyar bama a fara ba! Shiyasa zan taƙaice maku shi amun afuwa!.
A ɓangaren Ummie, cikin ikon ALLAH ta kama sana'a da kuɗin da Zaysh ya bata, ALLAH ya zubawa abin albarka, tana samu sosai, dan haka bata damu da auren da mijinta ya ƙara ba, an yi auren an luma kawo yarinyar gidan an haɗasu, ba kalar rashin mutuncin da yarinyar bata yi mata, amma ko kaɗan bata damuwa da ita, ta mai da hankali kan kasuwancinta, tana kuma yin waya da ɗan uwanta yana kwantar mata da hankali, har yanzu dai ciki shiru babu shi babu labarinsa, bata nuna damuwarta, tana dai cigaba da addu'ar ALLAH ya bata mai albarka!.
Zaysh dik in ya samu wani kuɗi sai ya ƙara mata, yanzu tana da babban shagon sai da abayoyi, kishiyar tata bata da burin da ya wuce ta ga shagon ya durkushe, ta yi balal'in duniyar nan kan lallai mijin ya buɗe mata nata shagon, ya ce shi bashi da kuɗi, ita ma Ummie ba shi ya buɗe mata ba, ɗan uwanta ne, to shi ne take ta ƙulla makircin yadda zata yi shagon ya durkushe komai ya kare dan mugunta da bakin hali, kuma wlh Ummie bata rageta da komai ba fa! Har kyauta tana yi mata, kawai dai mugun hali ne.
--------------------🔥
Yau ta kama ranar Friday, sai shirye-shirye Ummie take yi, ranar Monday zata je kasar Avaris passing out na Zaysh, dan zasu fita, tin da ya tafi bata sake sanya shi a idanunta ba sai waya kawai, kunga kuwa sai murna ai yanzu.
Kaya akwati guda ta shirya, kuma ita kaɗai zata tafi, dan mijinta bashi da halin biyan kuɗin jirgi, ita ɗin ma Zaysh na zai biya mata, ya ce kada ta taɓa kuɗin shagonta, shi ma kuma Vash ne ya bashi kyautar kuɗi ya ce ya yi shirin passing out ɗinsu, shi ne ya tura mata ta zo. Danginsa sai zaginta suke yi, wai yawo zata je, dama sun ƙala mata sharrin bin maza, wai idan ba bin maza take yi ba a ina ta samo kuɗin buɗe shagon nan nata?. Ita dai bata ce masu komai ba, suka ce ai sun san basu da komai, marayu ne, waye ya bata kuɗi?.
Bayan mijinta bata faɗawa kowa ga wanda ya bata ba, ta koma gefe ta yi shiru tana kallonsu.
Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa.......
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1________🔥
10-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
E_____________9
Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa. "Lafiya kika shigo mun parlo yau kuma?".
"Lafiyar ce ta kawo haka"........ Ɗan zare ido Ummie ta yi, sai kuma ta basar da cewa. "Okey me yake tafe dake?"..... Shiru yarinyar ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Albishir na zo yi maki, abin da kika kasa bawa mijinmu yau ALLAH ya bashi a jikina". Ta faɗa tana shafa shafaffen cikin nata. Wata figaggiya da ita kamar kazar mayu, wannan idan babban mota ya zo da gudu iskansa tsab zai kaita ƙasa, ba welcome bare goodbye, tana nan kamar namiji ya ɗaura zani!.
Ajiyar zuciya Ummie ta sauke, take murmushi ya bayyana a kan face ɗinta, a sanyayye ta ce. "Kai Alhamdllh, ALLAH mai kyauta mai kari, UBANGIJI ya saukeki lafiya, amma na tayaki murna, banda abinki da rigima ai nima bani na hana kaina ba, ALLAHN da kika ce ya baki shi ɗin ne dai mai bayarwa, kuma shi ne bai bani ba, a haka kuma ina gode mashi ina karawa, amma wlh na yi murna da ALLAH ya bamu ta wajenki, ai dik ɗaya ne!". Da iya gaskiyarta ta yi maganar, dan ALLAH ya ɗaura mata jaraban son yara, yara makota dik a wajenta suke wuni, dan haka bata bakinciki da wannan ciki, wlh idan aka haifa zata rike tamkar nata In Sha ALLAH baiwar ALLAH.
Wani irin ɗaure fuska amaryar ta yi, dan ita ba ta kawo mata labarin dan ta yi murna bane, burinta ta kuntata ma, amma sai ga shi tana murmushi. Cike da takaici ta ce. "To ai ba ɗanki bane, nice uwarsa, kada ki taɓa sa ran zai zo ko da kusa dake ne"......... Sosai Ummie ta ji kirjinta ya buga, sam bata ji daɗin hakan ba, ta zaci ai zasu haɗa kai su reni yaran ne!
Ganin fuskanta ya canza yasa amarya jin daɗi, burinta ya cika ta kuntata mata, dan ta kara mata takaici ma sai ta ce. "Idan fitsari banza ne kaza ta yi, ki haifi naki, nawa basu da alaƙa dake juya kawai, almost shekaru 5 kenan yanzu da aurenku ko ɓari baki taɓa yi ba, wai har mazan da kike bi ma babu wanda ya iya yi maki cikin ne? Sai kuɗi kawai suke baki? Ko da yake kece juya, ko zasu dinga kwana a kanki ba samun cikin zaki yi ba". Ta kai karshen maganar tare da juyawa tana wani hura hanci, ta nufi waje.
Tsaye Ummie ta yi, take wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska, da gudun gaske ta shige cikin ɗaki, babu abin da ya fi bata takaici irin ƙazafin zina da suke mata, a dik san da suka ce maza take bi suke bata kuɗi sai ta sha kuka, ga shi yau tsawon wattanni 8 bata samun damar hira da Zaysh, dan tin da suka shiga horo na karshe-karshen nan ba'a basu waya ba, an karɓi wayoyinsu, sai ranar Sunday yake kiranta da wayan securitys officers, kuma mintina biyar ake basu su gaisa da gida su ji idan kowa yana lafiya, baya ga haka basu da wani lokaci ɓatawa, dan a watannin karshen nan horo wuta-wuta ake basu babu kama hannun yaro.
Kuka ta ci mai isarta, sannan ta miƙe ta ƙarisa shirinta, wunin ranar haka ta wuni cikin ƙunci, sai can yamma ta nufi shagonta dan su yi lissafi gobe zata yi sammakon tafiya Abuja, daga nan zata hau jirgi zuwa Avaris, ta so zuwa Niger wajen ƴan uwanta na kauye ta kai masu abin arziki tin da ta ɗan samu rufin asiri, amma ba dama, sai ta ce bari ta bari sai ta dawo daga Avaris ta sauƙa ta can!.
Ko da ta zo fita sai da amarya ta yaɓa mata magana, wai dan ta ji tana da ciki ne dik ta shiga damuwa har da kuka ido ya kumbura, ita dai bata ce komai ba ta fice abinta. Sai habaice-habaice amarya take yi.......... Ita dai bata dawo gidan ba sai dare, a shagonta ta yi sallar mangrib da ishai suka yi lissafi da yaron shagon, sannan ta sayi abinci a restaurant ta dawo da shi. Tin da ta shiga ɗaki ta rufe kofa bata sake fitowa ba, dama mijin ba'a ɗakinta yake ba.
A ciki ta ci abincinta ta ƙoshi, daga nan ta kwanta abinta, da assusuba ta tashi ta ja akwatinta, mijin nata kuma yana nuna mata tsantsar so da kulawa, dan kuwa har tasha ya rakata da sanyin asuba, sai faɗi yake yana nanatawa kan ta kula da kanta. Da motarsu ya zo tashi ma, ya ƙanƙame hannunta yana faɗin zai yi kewanta sosai, ita ma har kwallah ta yi tana faɗin zata yi kewansa, dan tana mugun son shi, kuma tasan yana kula da ita, yana gwada mata kauna, kome yake faruwa ba yin kansa bane, ta sani kuma ta yi mashi uzuri, bata hukunta shi da laifin danginsa ba!. Ko kaɗai bai taɓa yi mata ƙazafin zina ba, masu yi ma idan ya ji ba karamin faɗa suke yi da shi ba, shi ya aminta da ita, danginsa ne dai sai shiru!.
A haka suka rabu cike da kaunar juna, ya koma gida ita kuma motarsu ya tashi sai Abuja, daga nan ta hau jirgin Mexico wanda already mijin nata ya wuce gaba wajen shirya mata komai, zata sauƙa a can, gobe ta hau jirgin Avaris kai tsaye, already an shirya jirgin da zasu tafi Avaris ɗin a Mexico, jirgi direct daga nan Naija zuwa Avaris ne babu, sai an yi masu juye a Mexico, shiyasa!.
TO UMMIE SAI DAI MU CE SAFE TRAVELS!.
----------------------🔥
AZURE.
BIKIN KARRAMA MATASAN SOJOJI KO ACE PASSING OUT.
Barrack ɗin gabaɗaya ya canza, an sake mashi fenti, dik wasu sojojin dake waje sun dawo barrack, hakan yasa barikin ta cika da dubban zaratan sojoji, ta ko'ina su ne ke ta faman shawagi.
Ranar passing out, wannan rana ce da za su saka kakin soja da cikakken kima and ƴanci, su tsaya a bainar jama'a a matsayin sabbin sojojin ƙasa, kada ku manta su ba kamar sauran sojoji bane, sun shiga horo na musamman a babi na biyu, kunga dole bikin karramasu ya zama gagarumin biki sosai!.
Tin sati biyu da suka wuce aka fara preparation for the ceremony. Yau takama Monday kuma ranar da za su fito daga ɗakin horon da aka shigar dasu bayan shekaru biyu suna gwabzawa da fama. Da safiyar wannan rana, sojojin sun tsananta kai komo a cikin barikin, kowa ka ɗaga ido ka gani sai ka firgita, suna wani muzurai tamkar zasu cinye mutum ɗanye!.
Katafaren hall na GIDAN SOJA an ƙawata shi matuƙa, an shirya kujeru da dik abin da za'a buƙata, gefen iyaye da dangi daban, an shirya shi matuƙa, gefen manyan general's na sojoji an ƙawata shi, gefe guda kuma ga matasan sojojin da suka fara horo tare da su suka yi passing out a zone one, ga wasu sojojin da aka shirya masu rike da bindigu sun kai su 50 a layi, a can ta tsakiyar hall ɗin wasu dakakkun sojoji su 10 ne a tsaye a tsakiyan wajen cikin ƙamewa da nuna kwarewa a kan aiki.
A kusa da side nasu General's an shirya gefen iyalansu, dan suma zasu ziyarci wanna biki. Ga kayan ciye-ciye da aka shirya masu rai da lafiya. Komai yana nan bisa tsari.
Basa wasa da lokaci, dan haka karfe 3 na yamma kowa ya hallara a wannan waje, dangin matasan sojojin dik sun hallara, watau tin ana iya kirga motocin dake danno hanci cikin barrack ɗin nan har aka daina, domin kuwa AZURE ta ga manya-manyan ƙusoshi da ake da su a ƙasa da wajen ƙasar, waɗan da ba'a taɓa tunanin ganinsu ba, musamman CEO na STARS BODY LUSH, dayawa sun yi mamakin ganinsa a wajen, sai tambayar kansu suke yi me ya kawo shi nan kuma?.
Iyayen Unays sai mamakin ganin daddyn Noor suke yi, dan labarinsa suke ji, yau kuma gasu ga shi, abin like wow. Kyakkyawar waje aka ware mashi shi da family ɗinsa su Aunty Lusi, dikkansu burinsu su ga Noor, rabonsu da shi shekaru biyu da watanni kenan, sun yi kewansa sosai, a lokacin da ya shiga horo na musamman ko sun zo basa samun damar ganinsa, dan a wannan lokaci babu wanda ya isa ya gansa. Shiyasa nima na tsallaka maku wajen, a horonsu na musamman ba'a yarda ko iyaye su ga mutum ba, daga kai sai Captain and Commander! Babu ma wanda yasan duniyar da ake horo na musamman ɗin, amma dai a underground ake yi!.
Iyayen Vash ma sun hallara a wajen, da 3 uncles ɗinsa, dan shi shi kaɗai mahaifinsa ya haifa, ba kani ba kanwa!.
Kowa ya bayyana, dik sun zauna sun natsu tsit, Ummie ma ta baro hotel da ta sauƙa ta iso barrack cikin shigarta na tsadadden abayarta, da yake sun fito daga horo an basu wayoyinsu, tin da Ummie ɗin ta taso yana waya da ita, shi ya shige mata gaba wajen samu ta iso lafiya, ya roki Captain alfarmar da a kama mata hotel, da yake yanzu Captain ya zama abokinsu sai ya aminta, ya tura yaransa biyu aka ɗaukota a airport, aka kaita hotel, da zata zo barrack ta kira Zaysh a waya, ya sanya ta ɗauki abin hawa ta ce a kawota AZURE kowa yasan wajen! Kun ji yadda aka yi ta zo.
Waje ya yi tsit kowa sai rarraba ido yake yi suna jiran bayyanar sojojin. Su V da suka sha kwalliya na wucewa tsara, tamkar zasu tafi gasar kyau, suna zaune a side na family ɗin senior staff, su passing out ɗinsu sai next week, ba tare za'ayi da na su Leo ba, saboda abin zai yi yawa!. Wani kafurin Italian gown mai tsantsan kyau da ya bi shape ɗinsu, ya fito da su tamkar ka sace su ka gudu da su, ga ash hair ɗin nan nasu da ya sha gyara, waɗan nan gajeru na gaban goshin sun ƙara fito da tsananin kyansu!.
Dik wasu manya a Avaris yau sun bayyana a AZURE, president, vice president, governors, ministers, kai kowa ya hallara, shiyasa tsaro ya yawaita, helicopter sai shawagi suke yi sama, ga su eagle and jet dake kewaye dan tabbatar da tsaro.
Wani irin bit ne ya karaɗe gabaɗaya hall ɗin, ga take GIDAN SOJA ɗin dake tashi ya bi tare da bit ɗin, wanda ya sanya gabaɗaya hall ɗin aka ƙara natsuwa tsit. A jere matasan sojojin nan suka fara shigowa, suna taku cikin tsantsar jarumta, gabaɗayansu sanye suke da sabbin kakin soja da ya kara masu kwarjini na musamma, kakin soja firgita makiya kenan!.
Cikin zafin jini suka tako har izuwa saman stage in da aka tanada masu dan tsayuwa kowa ya gansu!....... Ni da kaina na ce ya ilahil alamina, watau dik wanda ya sansu a shekaru biyu baya a yanzu ba zai taɓa ganesu ba, zun zama wasu irin dakakkun maza, lafiyayyun cikakkun maza majiya karfi! Dik da a cikin kaki suke idan kuka gansu ku kun san ba horon wasa suka karɓa ba, fuskokinsu tamkar waɗan da aka aikowa da saƙon cewa wuta zasu shiga, babu wasa ko alamar fara'a a kan fuskokinsu.
Daddyn Noor ai bai san lokacin da ya mike tsaye yana kallon ɗansa ba, a tsaye yake, babu wasa a kan fuskansa, dik yadda suke zaton ganinsu sun zarce hakan, tin daga kan tsayuwan Noor daddynsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 95