masu shi, tin suna 13 years, jikinsu bai yi wani kwari ba, a wata allurai kala uku masu karfi muke yi masu, wanda haka kuskure ne a fannin lafiya, ka sani na sani!".
A taƙaice Dr James ya ce. "Ko mu dakatar ko bamu dakatar ba dikkansu mutuwa zasu yi, already alluran ya kashe garkuwar jikinsu, dan haka ba zamu dakatar ba, gara kawai a cigaba har zuwa lokacin da zasu mutu, kuma ai idan suka zo mutuwa sun fi bada eggs dayawa, baka ga 50 eggs kowacce daga cikin matattun suka bayar ba?".
Dr Mark ya ce. "Yanzu ma ai sun fara mutuwa, one by one haka dikka zasu ƙare, yau biyar, wani watan ma biyar ko sama da haka zasu mutu, a haka zasu ƙare, dan haka ba wani zancen mu dakatar da yi masu allura, already su tasu ta ƙare". ........ Ya rabb, ku ji yadda suke magana tamkar ba ran ɗan adam bane suke mutuwa.
Shiru Dr Kamal ya ɗan yi, dik da cewa yana son aikin nan nasu, suna samun maƙudan kuɗaɗe, amma a yau yaran nan sun ɗan bashi tausayi, dan ya ga jikinsu ya fara lalacewa sosai da sosai, alluran ya gama kashe.
A haka suka shiga SECTION E. Sai suka shiga cikin wani ɗaki mai tarin glasai dayawa. Wajen tamkar lap ne haka, ga wasu halittu na ban mamaki dayawa a cikin glasses dake ɗakin, an yi glasses ɗin dogaye tamkar show glass haka, to a ciki ne waɗan nan halittu suke, tamkar suka ƙoƙarin yin wasu halittun ne.
Tin daga kan yanayin matakan tsaron da suka zubawa wannan ɗaki zaku san ba waje ne na wasa ba, zaku san wane ne mai bala'in haɗari. Gaban wani tangamemen glass mai girman gaske suka tsaya. Wani irin jibgegen halitta ne a ciki mai kama da dabba mai kuma kama da mutum, yana da wasu irin ƙulu manya-manya a tamolon kansa, idanunsa tamkar ball saboda girma, gwanin tsoro.
Wannan halitta ba komai bane face ɗaya daga cikin fitintinun da suke kirkirowa duniya, Dr James ya ja ragamar wannan project ɗin, shi ya harhaɗi kwayoyin halitta, su DNA ɗin nau'ikan dabbobi da mutane daban-daban, suka tacesu a lap, sannan ya fara kyankyasan wannan halitta, tin shekaru 8 baya yake yin wannan project ɗin, halittace mai matuƙar haɗari, yana daga cikin plan na WS dan hana duniya zaman lafiya, a wannan asibitin ba jarirai kawai ake kyankyasa ba, ba kuma magani kawai ake haɗawa ba, kazalika ba iya cututtuka kawai suke kyankyashewa ba, suna kyankyasar hadda dabobi, kai dik yadda kuke zaton asibitin nan ya zarce tinaninku, ku dai sai mun natsa cikin labarin.
Yanzu ba zaku gane me zasu yi wa duniya da wannan halitta ba, amma gaba zaku gane, yanzu haka renon halitta suke yi yana ƙara girma, a wannan ɗakin akwai nau'ikan halittu daban-daban, kowanne kuma da amfaninsa da dalilin yinsa.
Bayan sun duba halittar yana nan lafiya yana barci, sai suka ƙara gaba zuwa wajen wasu glasses ɗin, nan kuma wasu irin ƙananun halittu ne masu kamar ƙudaje a cike a cikin glasses ɗin, a gaban wajen suka tsaye, Dr James ya ce. "Waɗan nan halittu sun kusa barin wannan waje, a cikin week ɗin nan WS zasu karɓesu".
A tinaninku me za'ayi da su kuma?.
Jinjina kai Dr Kamal suka yi, suna ƙara yabawa kansu a wannan project ɗin, dan sun sha baƙar wahala. Sun yi yawo a cikin wannan ɗaki sosai, sun duba halittu daban-daban dayawa kafin su fito su nufi office ɗinsu. A office ba Dr James suka zauna, a tare suka yi breakfast around 11 na safe, sannan suka ɗan taɓa aiki zuwa 1 kafin Dr James ya ce bari ya duba Zinta a gida.
Fitowa ya yi ya bar su Dr Kamal a office ɗin, ya nufi gida. Tin da ya sako kafafunsa a cikin parlon nan wani irin musulmin kamshi ta bugi hancinsa, shaƙa ya yi ya lumshe idanu tare da ƙarisawa ciki. A cikin ransa yake cewa a ina suka samu wannan kamshi mai daɗin haka? Ko'ina tsab-tsab, watau batu na gaskiya 3D akwai mugun tsabta sosai, basa shiri da ƙazanta ko datti waje, komai nasu tsab da yake likitoci ne.
Shi da kansa a yau ya shaida lallai yau mata na cikin wannan gida nasu, sama ya haye yana ta baza hanci yana shaƙar kamshi. A parlon sama ya isko Maya zaune tana karata wani littafi na lafiya da ta ɗauko daga room na Dr Kamal.
Tana ganinsa ta zube ƙasa tana ɗaga mashi gaisuwa. A dake ya amsa tare da cewa. "Ina madan ɗin take?"..... Tana ɗan sunkuyar da kai ta amsa da. "Tana cikin room"........ "Kun yi breakfast ne?".
Kai sister Maya ta gyaɗa mashi. "Mun sha tea"....... "Iya shi kawai?". Kai ta sake gyaɗawa. Ciki ya wuce yana tinanin ɗure zai yi wa Zinta yanzu, ga komai suna da shi, kitchen ɗinsu shaƙe da kayan abinci fa, ace tea kawai zasu sha, bai yarda ba.
Kofar room ɗinsa ya tura, wani kamshin na daban ne ta kai mashi karo a hanci, shaƙa ya yi tare da ɗan lumshe idanunsa kafin ya shigo, sister Maya ce fa ta zaɓo turarukan gida daga cikin turarukan dake ɗakin Dr Kamal, ta gansu kala-kala kwali-kwali, dan 3D akwai son kamshi da tsabta na faɗa maku, to wasu turarukan ma basu taɓa amfani dasu ba, basu san ya yake ba, ita kuwa tana zuwa ta dinga bincikawa tana taɓawa sai da ta ji wanda kamshin yai mata, sannan ne ta fito da shi, ta bi lungu da saƙo na gidan ta fesa, sannan ta ɗako wani daban ta fesa a ɗakuna.
Can ya hango sister Zinta kwance saman bed, kudundune a cikin bargo, idanunta a lumshe. Karisawa wajen ya yi, a gefen bed ɗin ya zauna tare da kai hannu ya janye bargon ƙasa, wutar ɗakin a kunne, ko'ina tankar........ Waro idanunta da suke jajir waje ta yi, kai tsaye sai kan face ɗinsa.
Tana ganinsa ta fashe mashi da kuka. Hannu bibbiyu yasa ya ɗagota sai saman laps ɗinsa, ɗan zubawa kayan jikinta idanu ya yi, rigar ta tafi da shi, rigace shara-shara maras nauyi sister Maya ta ɗauko mata daga ɗakinsu. Cike da kulawa ya ce. "Sorry princess of my heart". Ya faɗa yana taɓa goshinta da yau zafi sosai.
Kwantar da ita ya yi, ya miƙe ya fito waje, kitchen ya shiga, akwai manyan gas guda uku a cikin kitchen ɗin, sai glass na pots, sai kuma ƙaramin store na kayan abinci a ciki. Da kansa ya dafa mata indomie, ya soya two eggs da kyau, sannan ya haɗa mata tea mai kauri da zafi, ya jera a saman tray, ya ɗauko ya nufi room ɗin. A saman carpet ya ajiye tray ɗin kafin ya nufi wajen drawers dake ɗakin.
Wasu drugs ya ɗauko tare da kawowa saman carpet ɗin ya ajiye, ya nufi toilet. After 20 mins ya fito ɗaure da towel a waist ɗinsa. Shiryawa yai cikin pjs sky blue, ya dawo wajen bed ɗin, ƙarisa yaye mata bargon ya yi kafin ya ɗauketa cak. Bai direta a ko'ina ba sai a saman carpet ɗin, zama yai da ita a jikinsa, tana ta kuka.
Cikin salo ya fara rarrashinta ta yadda dole ta yi shiru ba dan ta shiryawa hakan ba. Ya ɗauko fuck ya fara naɗar indomie ɗin yana bata a baki, da farko taƙi karɓa, amma da ya jawota jikinsa, cikin sanyin murya ya ce. "Idan baki ci ba zan ƙara yin abin da na yi". Sai ta buɗe baki ta fara karɓa. Da ta ce yai mata zafi idan ya ɗebo sai ya hura mata da bakinsa yai sanyi, sannan ya bata.
Haka ya dinga bata har sai da ta ci kusan rabi, sannan ta ce ya isheta, ya ɗauko tea ya bata, shi ma kusan rabi ta sha, sannan ta ce ta ƙoshi, ya ɓalle magungunan da ya ɗauko, ya bata ta sha, ya ɗauketa cak sai kan gado. Bayan ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, a gaban gadon ya tsugunna game da ce mata. "Zan koma office, sai yamma zan dawo, akwai wani abin da kike so?".
Kai ta girgiza bata yi magana ba, sumbatar ɗan bakinta ya yi tare da miƙewa ya nufi closet ɗinsa, ya shirya cikin suit, ya ɗaura rigar aikinsa a kai, ya fito ya koma office. Ya wuce Maya a parlo yarda ya barta, ta dukufa a karatu haiƙam. Yana fita ta miƙe da sauri ta koma cikin ɗakin dan duba sister Zinta ɗinta.
Bari mu leƙa DOL mu dawo.
DEATH OR LIFE (DOL).
Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana ɗan shessheƙa, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita, da gudu ta miƙe ta yo waje, su Angelina na kiranta amma taki tsayawa, a tsakiyar tantunansu ta zube gwiwowinta cikin ruwan saman, yau tana jin kamar mutuwa zata yi.
While su kuwa su Leo suna zauna a cikin room na Leo. Da Noor, Leo, Vash and Zaynish, Leo ne ya dubesu da kyau kafin ya ce. "Bani son dikkan sojojinmu su san me yake faruwa yanzu, zamu fita izuwa wancan wajen da hayakin yake, zamu je mu duba menene, sai mu dawo mu san irin shirin da zamu yi masu".
Jinjina kai suka yi, Zaynish ya ce. "Ina tinanin wata ma'aikata ce a wajen ko wani abin makamancin haka, duba da irin kurɓataccen bakin hayakin dake tashi, dole wasu sinadarai ne a haɗe a wajen".
Kai suka jinjina, Leo ne ya jawo laptop ɗnsa ya kunna, a tsanake yake fito da taswirar dajin, cikin sanyin murya ya ce. "Wannan waje yana ta yamma da Avaris ne, a yammar ma ba tsakiya ba, ya gota ta gudu kaɗan, yamma maso kudu kenan".......... Zubawa taswirar idanu suka yi, suna sauraron bayaninsa.
Noor ne ya amsa da. "Wani lokaci yakamata mu tafi?"....... Shiru suka ɗan yi, can Leo ya ce. "This coming two days". Kai suka jinjina alamar to, a sirrance suka tsara komai, basu bari sojojinsu sun sani ba.
A can gefe kuma Angelina sun kamo V suka dawo da ita, sai kukan dai take ta faman yi. Zaman rarrashinta suka yi, da kyar barci ya saceta saboda ta ci kuka ta ƙoshi. Bayan ta yi barci Anglina ta fito da laptop ɗinta, ita kuma Dr Manassa ta ɗauki wayarta ta koma saman mattress ɗinsu ta zauna.
Angelina na buɗe laptop ɗinta sai ga saƙon ɓoyayyen email ya shigo mata, da sauri ta shiga kan saƙo. Ɗan zazzare idanu ta yi a kan saƙon, dogon note ne kamar haka. "Assalamu alaikum my flowers, how's your day and hope you're enjoying this rain weather?. From the very first moment I looked into your eyes, I didn't just see beauty, I saw strength, discipline, and a calm fire that only a true soldier carries, you wear your courage with grace, and your confidence with elegance, your beauty isn't only in your face, it lives in your voice, your posture, and the way you stand firm even when the world tries to shake you, you are a warrior with a gentle soul, in a life where we are trained to face chaos, you are the calm that steadies my mind, your presence brings me peace in ways no battlefield ever could, when I think of rest, safety, and quiet strength, I think of you, we both know the weight of this uniform, we understand sacrifice, loyalty, and silence, yet with you, I feel understood without speaking, protected without armor, you remind me that even soldiers deserve softness, love, and a place to breathe, so today, I lay down my pride and speak from my heart, I have fallen in love with you, not out of weakness, but out of certainty, i choose you, not just as a fellow soldier, but as the woman who calms my storms and strengthens my spirit, If love is a battlefield, then you are the only one I would gladly stand beside in peace and in war"............ Aa lallai, irin waɗan nan kalamai haka, e lallai mun shaida soldiers deserve love and peace, jama'a saƙon na sojoji ne fa, Unays ko Juraiz waye da wannan kalaman masu melting heart ɗin?.
Tin da ta fara karantawa take murmushi har ta kai karshe, da sauri ta ce. "Manassa come and see something"......... Sauƙowa ƙasa Manassa ta yi, ta zo da gudu dan ta gani.
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-18.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 55 & 56
Tin da ta fara karantawa take murmushi har ta kai karshe, da sauri ta ce. "Manassa come and see something"......... Sauƙowa ƙasa Manassa ta yi, ta zo da gudu dan ta gani. A gaban laptop ɗin ta tsaya ta bayan Angelina, a natse ta fara karantawa.
"Assalamu alaikum my flower, kin wuni lafiya? Fatan kina enjoying wannan yanayi na ruwan saman?. Tun daga farkon lokacin da na kalle ki, ban ga kyau kawai ba, na ga ƙarfi, ladabi da jarumta, ga natsuwa dake cikin zuciyar soja na gaskiya, kina ɗaukar jarumtarki da kima, kuma kina cike da kwarin gwiwa, kyanki ba a fuska kaɗai yake ba, yana tattare da muryarki, tsayuwarki, da yadda kike tsayawa daram ko da duniya na ƙoƙarin girgiza ki, ke jaruma ce mai zuciya mai taushi, a rayuwar da aka horar da mu mu fuskanci rikici da hatsari, ke ce nutsuwar dake kwantar min da hankali, kasancewarki kusa da ni ya kawo min salama fiye da duk wani filin daga, idan ina tinanin hutu, kariya da ƙarfin zuciya game da natsuwa, to ke nake gani, dikkanmu mun san nauyin wannan uniform ta soja, mun san ma'anar sadaukarwa, aminci da natsuwa, amma tare da ke, ina jin an fahimce ni ba tare da na yi magana ba, ina jin kariya ba tare da makami ba, kina tuna min cewa ko sojoji ma suna buƙatar peace, soyayya da wuri na numfashi mai kyau, saboda haka yau, na ajiye girman kai na, na furta maki daga zuciyata cewa na kamu da sonki, ba dan rauni ba, sai dan tabbaci, na zaɓe ki ba kawai a matsayin abokiya soja ba, sai dai a matsayin macen dake kwantar min da guguwata kuma ke ƙarfafa ruhina, idan soyayya fagen daga ce, to ke kaɗai ce wacce zan tsaya a gefenta da yardar rai, a zaman lafiya da a lokacin yaƙi"......... To jama'a ga shi nan na fassara maku kalaman na jiya, gaskiya kun sakani dariya jiya, to anyway ga shi nan dai na fassara.
Bayan ta gama karantawa ne ta ɗan rungumo Angelina tana murmushi, a sanyayye ta ce. "Angelie ki amince mashi, waye ne ma? Kuma kaman soja ne ko? Ya iya kalamai"......... Kai ta jinjina. "Soja ne, a cikin sojojinmu yake, ina tinanin ma shi ne wanda yake mun magana, ba shi ne wanda ɗazun ya ce zai ɗauka mun V ba".
Ɗan zazzare idanu Manassa ta yi. "Wow he's so handsome ai, chocolate guy, ya haɗu, look at his eyes, his gorgeous body, ta ko'ina ya haɗu"...... Nisawa Angelina ta yi. "Ni ina da wanda nake so, bawai Unays bai haɗu bane, ya haɗu, but ina da wanda zuciyata ta kamu da sonsa tin farkon mission ɗinmu".
Ƙara rumgumeta Manassa ta yi, tana murmushi ta ce. "Ke wanenen wannan?. Shi ne baki taɓa faɗa mun ba?"..... Murmushi ita ma ta ɗan yi. "Hmmmm ya haɗu over, shi ma fa soja ne, hoooooo Manassa i love him from the button of my heart, everything about him is special, his movement, his speech, his walking, his energy, his looking, the way he's working, the way he's praying har yasa na ji ina sha'awar addinin da suke yi, baki ga idan suna addininsu ina fita in tsaya ina ganinsu ba? Everyday shi ne yake tsayawa right side na sir Nirash idan zasu yi addini, i love his natsuwa over".
Kara zazzare idanu Manassa ta yi, tana ɗage gera ta ce. "You mean sir Zaynish?"........... Gyaɗa kai ta yi sama alamar yeah shi fa....... Manassa ta ce. "Yeah, sir Zaynish karshen haɗuwa ne shi ma, especially his hair, African hair ɗinsa akwai ɗaukar hankali, yana da yawa kuma ya cika kansa"...... Jama'a kunsan gashi buzaye ai, akwai kyau, ashe kalle mana gashin Zaynish namu suke yi.
Angelina zata yi magana Arya dake fama da aiki ne ta rigasu da cewa. "Rubbish! Ku ba zaku daina ɓata lokacinku a kan maza ba ko? Ba za ku kama abin dake gabanku ba ko?"........ Harararta Angelina ta yi. "To tin da ke baki da lokacinsu sai aka ce maki muma haka ne? Mu muna son maza, especially kyawawa, ina son sir Zaynish, a kansa zan iya komai, abeg maintain word and mind your business!". Ta kai karshe tana murguɗa mata baki.
Kunsan Arya da karfin hali, hata ɗaukar raini, aikuwa tana juyowa ta kaiwa bakin Angelina bugu da karfi wanda sai da tasa ta saki karar da bata taɓa zatan zata yi ba. Ai a miliyan ta miƙe ta yi kan Arya, da sauri Arya ma ta miƙe tana faɗin. "Zaki sa hannunki a jikina ne?".
Angelina bata yi magana ba, tana zuwa ta damketa da faɗa, suka fara kokawa da karfi tamkar basu san juna ba, kome suka samu bugawa juna suke yi, da sauri Manassa ta taso ta fara ƙoƙarin rabasu, amma abin ya ci tura, hakan yasa ta fita da gudu sai ɗakin Leo, ta ce su zo su raba mata su Angelina suna faɗa.
A lokacin suna tsaka da tattaunawa kan wannan tafiya da zasu yi. Leo ne ya ce Vash ya je ya rabasu kuma ya kawo mashi su nan. Miƙewa ya yi, Manassa ta yi gaba ya rufa mata baya, har lokacin faɗa suke yi sosai, Arya ta jiwa Angelina ciwo a baki na punch ɗin da ta dinga kai mata.
Yana zuwa ya damkesu da hannu ɗaiɗai ya rabasu, sai huci dikkansu biyu suke yi. ....... "Dik ku je sir Nirash yana kiranku". Vash ya faɗa a dake. Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa gaba kafin Angelie ta rufa mata baya, V dai tana ta barcinta.
Juyawa shi ma ya yi zai fita, a sanyayye V ta ce. "Sir Arvash"....... Tsayawa yai tare da juyowa, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa........ Cike da zolaya ta ce. "A ranar da muka fara haɗuwa ka ce kana sona, nai maka kyau, amma yanzu meyasa ko magana baka mun? Ko kallona baka son yi?". Ƴar ƙaniyar yarinya, tafa san meyasa yake dik wannan, na farko ta ce mashi ita ƴar GAT ne, kunga ko a nan ɓangaren soja tafi karfinsa, na biyu ga aljanar da take mashi, aljanar tasa ta ce in ya kula wata mace sai ta kashe macen, kunga kuwa ba zai so a kasheta ba ai.
Amma hakika nin gaskiya Vash yana son Manassa, irin sosai ɗin nan, kawai dai waɗan nan iya shege biyun da ta yi mashi ne yasa ya ja baya.
"Da farko da na ce ina sonki ma wasa nike yi, shi ne kawai!". Ya kai karshe tare da yunkurawa zai juya....... "Ban yarda wasa kake yi ba, dan na ce ni ƴar GAT shi ne zaka gujeni? Ba zaka iya fuskantar kowani haɗari a kan macen da kake so ba? Kai ba soja bane"........ Dakatawa ya yi, slowly ya ɗago eyes ɗinsa a kanta, lallai tayi gaskiya, yakamata ya fuskanci kowani irin haɗari ne a kan soyayyarsa, bai kamata ya janye dan GAT ba, to amma ita aljannar kuma fa? Idan ya ce zai iya ja da GAT zai iya ja da aljanar da baya kallo ne? To ace shi musulmi ne ya riki ayoyin ALLAH, ita Manassa idan ya fara soyayya da ita aljanar ta zo mata me zata karanta ta tsira tin da ba addini ne da ita ba?.
Ganin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Kasan ba zaka iya sona da gaske bane kasa na fara sonka? Ka cutar da zuciyata? Haka addinin naka ya koyar ka cutar da mutum?"......... Nisawa ya yi tare da ɗago da idanunsa sosai a kanta. Rasa me zai ce mata ya yi, sai kawai ya juya zai fita. Kukan munafurci ta fashe mashi da shi, har da tsuggunawa ƙasa.
Cak ya dakata tare da juyowa, ya ALLAH, zuciyansa na sonta, ba zai iya wucewa ya barta tana kuka ba, dawowa ya yi, a gabanta ya tsugguna tare da sanya hannu ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, hankey ɗinsu na sojoji ya fitar, a natse ya goge mata hawayen munafurcin da ta ƙaƙalo, cikin sanyin murya ya ce. "Sorry, amma a halin yanzu ba zan iya baki amsoshinki ba, tabbas ba karya bane ina sonki, amma ba zan iya soyayya dake yanzu ba, ba kaina nike jiyewa ba, ke nike jiyewa, so please ki bani lokaci zan nemo mafita". Yana kai karshe ya miƙe ya fita.
Ai yana fita ta miƙe tsaye, ta rike waist ɗinta ta fara tikar rawar da babu kiɗa, haka take so dama, ta yi ta wahalar da shi, ita tana da imanin cewa dik abin da namiji ya same shi a sauƙaƙe baya taɓa ɗaukansa da daraja, shiyasa take son sai ta ganawa zuciyar Vash namu azaba kafin ta bada kai, a zahiri gata Manassa kuma tana sonsa, a baɗini gata aljana da ta haramta mashi son kowa. Kai yaran GAT sai shirin ALLAH.
Sai da ta yi rawarta mai isarta, sannan ta ɗauko wayarta, ta hau rubuta mashi saƙon cewa a madubin ganinta na aljanu ta ga ya kula wata yarinya yau, lallai ya sani dik abin da ya faru da wannan yarinya shi ne sila, ya shirya ba zata bar wannan yarinya ba, ai ta faɗa mashi dik macen da ya kula sai ta kasheta. Tana gama rubuta mashi ta tura sai ta hau cigaba da taka rawarta tana nishaɗi.
A can kuwa Leo ya baiwa Arya da Angelina punishment na frog jump, saboda baya son irin wannan ɗabia, ace suna ƴan uwa kuma suna faɗa, ba zai ɗauki wannan iskaci a team ɗinsa ba. Abin ku da soja a cikin ruwan sama ya sanyasu tsallen kwaɗon fa, ga dukan ruwa ga wahala.
Dikkansu sai da suka yi frog jump 100 suna kewaye tantunansu su sake dawowa, abinku da renon AZURE basu nuna wahala ko gajiya ba, amma sun ji a jikinsu kasancewar a cikin ruwan sama ne hakan ta faru. Dalilin wannan wahalar da Angelina da ya Leo ya yi ne yasa Unays ya ƙara ƙullatansa, ya ce ba zai kyalesa ba sai ya ɗauka mata fansa.
After some hours, garin ya yi shiru, iska mai sanyi ya sauƙa saboda ruwan da aka sha, dajin ya ƙara kyau da zama kore shar, ruwan sama ya ɗauke ɗiff, matasan sojojin da suka yi sallar magrib da ishai sun hura wuta suna zaune ƙarƙashin bishiya suna hira suna shan ɗumi, dik suna sanye da army jacket da takalmar aikinsu, while team 1 suna cikin ɗaki a zaune suna tsara yadda komai zai tafi, suna tsara a daren nan zasu saci jiki akwai in da zasu je su duba wani abu. Sojojin dake masu girki sun girka sun gama, sun zubawa kowa a plate, sojojin dake kewaye da wutan da suka kunna suna cin abincinsu.
While su Arya ma suna cin nasu abincin a ɗaki, amma V kwance take saman gado, ta yi wanka tana sanye da sleeping dress ɗinta masu kyau, taki cin abinci, idanunta har sun kumbura saboda kuka, tana kudundune a cikin army blanket ɗinsu. Sai rarrashinta Angelina take yi, amma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 67 Chapter of 95