iyaye ayi nasara, ko nan gaba kada ka kuskura ka yi ƙoƙarin ja da maganansa, and okey zata rabaka da kowa lafiya"...... A duniya Lion yana kaunar daddynsa, yanzu haka maganar mahaifi da ya yi sai da idanunsa suka kaɗa suka yi ja, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ransa, ga Hoosainin daddyn nasa da ya renesa ma babu shi, wlh ba dan yana da karfin imani ba da ya jima da kauce hanya, dan dai tin da ya taso kalma ɗaya mahaifinsa yake yawan faɗa mashi shi ne dik wuya kada ya kuskura ya sauƙa daga turban koyarwa fiyayen halitta, mahaifinsa da second dad ɗinsa watau Hoosainin mahaifinsa sun jajirce wajen gina rayuwansa a kan turban musulunci, idan ya tina zai yi wani abin in ya tina tarihin Annabi Musa, Annabi Dawud, Annabi Isma'il, Annabi Isa, Annabi Nuhu, Annabi Muhammad (SAW) waɗan nan Annabawa tarihinsu daban yake, in ya tinasu sai ya fasa, dik wani gwagwarmayar da kake tinani ka sha a rayuwa to ko rabinsu ba ka kai ba. Annabi Nuhu ya fi dikkan Annabawa shan wahala a duniya, shekaru 950 ya yi yana wa'azi wa mutanensa, amma dik da haka suka ki musulunta, dik hakuri irin na Annabawa sai da Annabi Nuhu ya yi fushi ya roki ALLAH da ya halaka mutanensa, ALLAH ya ce ka kyara jirgin ruwan da zaka ɗauki ƙalilan ɗin mutanen da suka bika, saura zasu hallaka, imagine hakurin Annabi Nuhu, shekaru ɗari tara da hamsin yana masu wa'azi, amma daga karshe ma ce mashi suka yi mahaukaci ne bashi da hankali. Daga Annabi Nuhu sai Annabi Musa, ya sha wahala, ya azabtu kafin ya samu ya kwato mutanensa banu Isra'ila daga hannun mutanen Masar watau fir'auna, ya sha azaba bawan ALLAH nan, suka sha da kyar, suka tsallaka teku, amma me ya biyo baya? Yana cetansu daga azaba me suka ce mashi? Annabi Musa ya zo ya samesu suna sassaƙa gumaka, ya ce ya haka? Suka ce kai Musa mu fa ba zamu taɓa binka ba, ba zamu bautawa abin bautan naka ba, mu namu zamu sassaƙa yanzu! Imagine, mutanen da ka sai da ranka ka cecesu, ka wahala, ka juri yaki da dik wani barazana, babban mushiriki kamar Fir'auna ka kwatosu daga hannunsa, cikin kunci da azaba ya fito da su izuwa iskar ƴanci, amma me suka saka mashi da shi? Dik da haka bai yi fushi ba, ya cigaba da yi masu wa'azi, amma suka ki, sai wasunsu ne suka aminta, Annabi Isa, har ɓoye kansa yake yi a ɗaki saboda jefansa da kalmar mara uba da ake yi, bai yi wasa da yara kamar yadda kowani Annabi ya yi ba, ya rayu cikin ɗaki shiyasa ya taso baya son hayaniya kuma shiru-shiru, ya fuskanci ƙalubale da dama. Kai Annabawan ALLAH akwai hakuri jama'a, su ɗin karshe ne! Wani nan ko kyauta yai maka baka gode ba an dinga bala'i kenan, amma su ku duba, ALLAH ka bamu ikon koyi da su!.
So Lion yana mugun son daddynsa, baya barin mutun ya yi wasa da mahaifinsa, shiyasa ya takawa Aryan birki.
Miƙewa Aryan ya yi tare da cewa. "Ina zuwa, let me check them"..... Kai Lion ya jinjina mashi alamar to kafin ya ce. "Ka san yadda zaka yi da Abba, amma ko mutuwa zaka yi kada ka yarda da shiga cikin abin da ya shafi waɗan can halittu na mata, kasan dokar IRON FIST".
Kai ya jinjina alamar gamsuwa, sannan ya matsa kusa da Lion ɗin, rungumar Lion ya fara yi, hannu Lion yasa ya ɗan bubbuga bayansa alamar jinjina, sumbatar gefen kumatunsa Aryan ya yi, shi ma Lion sumbatarsa ya yi kafin su raba jikinsu da juna, ya matsa ya rungumi guru ma, suka sumbaci juna kafin ya fito. Kai tsaye benen su Seraphina ya nufa, dan ya duba ta tashi lafiya.
A lokacin da ya shigo tana tsaye a tsakiyar ɗakin tana rike da waya, sam bata ji shigowansa ba, sai ji ta yi ya kwace wayarta. Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa, ko da ya shigo ma sai da ya tsaya for good 5 mins yana kallonta, amma bata san ya shigo ba, sai da ya karewa surar jikinta kallo, tana sanye da shorts jeans zuwa tsakiyar santala-santalan cinyoyinta, daga sama ƴar riga da bata gama rufe cibiya ba mai dogon hannu kamar crop top haka, kun san shigarsu ai su, ba hankali aka sika ba, kafafunsa sanye da socks and bedroom crocs faro tas mai tsada.
Ash hair ɗinta a gyare, ya sha gyara wajen Madam, sai sheki yake yi, ga wani irin fitinannen kamshin dake fitowa daga jikin gashin ga kuma na jikinta, sai kamshin ya bada wani kala mai ɗaukar hankali. Sai da ya tsaya ya karewa jikinta kallo kafin ya shigo.
"Daddy kai ne?". Ta faɗa tana ɗan murmushi. Harara ya dalla mata kafin ya ce. "Baby anya ba zan hanaki waya ba kuwa? Baki iya amfani da ita ba"..... Zazzaro eyes ɗinta a kansa ta yi kafin ta ce. "Daddy me na yi kuma?"..... Ganin kamar zata faɗo jikinsa ta rungumesa ne yasa ya wuce saman sofa ya zauna yana faɗin. "Me ma baki yi ba? Haka ake amfani da waya ne? 24h baki komai sai pressing phone? On Monday zaku fara zuwa school, anya zaki yi karatun kuwa?".
Da sauri ta dawo kusa da shi, a gefen bed ta zauna suna fuskantar juna. "Please daddy kada ka rabani da wayar, i promise you that zan yi karatu sosai, kaga ai sss 1 zan shiga, dole in dage ko? Kuma dole sai da waya, and daddy ni karatu ma fa kawai nike yi da wayar, idan ka rabani da ita kaga karatuna zai ka baya tin da kamar lesson a gida nike yi da ita. Na yi alkawarin kula, zan warewa waya lokacin taɓawa daban, zan ware lokacin karatu"....... "Baby ni zaki yi wa kalaman yaudara?". Ya faɗa yana kallon idanunta a tsaitsaye, ga gashin idanun nata sun mimmiƙe, alamar kawai so take ta yaudaresa kada ya rabata da wayar, wai ita ma ta yi wayau, a haifeta a gabansu su sanya mata suna amma wai zata yi mashi wayau.
"Daddy trust me, kasan ai bana karya, kuma da gaske karatu nike yi a cikin wayar, and kaga wayar yana da amfani ko?"........ Miƙa mata wayar ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba, dan Seraph tana goge mashi hadda yarinyar nan.
Karɓa ta yi har da sauke ajiyar zuciya, a tinaninta ta mashi wayau ya yarda da ita, cike da wayau ta ce. "Daddy tin ɗazun ma karatu nike ta yi da wayar fa, kaga yana da amfani na ce maka, kamar uncle ɗina mai mun lesson yake". Wai irin ta sake sanyawa ya yarda da ita sosai ɗin nan............ Shi dai ido kawai ya zuba mata yana mamakin yarinyar nan, bata san kome take a wayar yana ganinta ba.
Shammatarsa ta yi ta sake snapping ɗinsa pic har guda biyu bai sani ba. Sai dai tana ɗauka ya miƙa hannu ya kwace wayar tare da cewa. "Me kike yi da pics ɗina? Kin ɗau na farko bai isheki ba sai kin ƙara ne?"...... Ai a zabure ta miƙe ta faɗa jikinsa da nufin ta kwace wayar, tamkar zata yi kuka ta ce. "Daddy ni ban yi snapping ɗinka ba, give me my phone".
Shi kuwa ɗaga hannunsa sama ya yi yana kallon hoto, sai ya danna delete zai goge. Wani irin zabura ta yi game da miƙewa a jikin nasa zata kwace ta hanasa gogewa. Baya ya yi da hannun nasa, binsa ta yi dole sai ta kwace, idanunta sun cika tab da kwallar yaudara tana son karya mashi zuciya irin ya kyale mata ɗin nan.
Daidai kyakkyawan gefen face ɗinsa ta kwanto mashi da kirjinta tana miƙa hannu zata kwace wayar. Hannunsa ɗayar yasa ya tallabo waist ɗinta ta baya wajen mazaunanta, da ɗayan hannunsa kuma ya danna delete ya goge hoton, ya koma kan ɗayan ma ya goge. Take ta ɗauke wuta, tamkar ta yi sumar tsaye, shiru bata motsa ba. Sauke hannunsa ya yi, sai yanzu ya lura da yadda ta kwanto jikinsa. Take ya ji ya ɗan ɗauke wuta shi ma, a hankali ya ɗan yi ƙasa da ita yana jin tamkar kada ya raba jikinsa da matasan tula-tulan nata dake saitin face ɗinsa, amma ya ɗan yi ƙasa da ita.
Wai irin ta yi fushin nan ne fa taki motsawa. Dawo da ita daidai suna fuskantar juna ya yi, ya ɗan kwantar da ita gefe yana tallabe da bayanta da hannunsa ɗaya. Zubawa face ɗinta idanu ya yi, ta datse idanu tana hura kumatu, ga hawayen da suka cika mata ido sun fara zubowa, ta ji zafin goge hotunan da ya yi, ta ci alwashin turawa Rimsha hotun nan yau, amma ya ɓata komai, abin da ya fi bata takaici ma shi ne yadda ya ganota, yanzu tasan zai rabata da wayarta ne ko kuma ba zai sake yarda da ita ba bare ya bata daman zama da shi har ta samu damar ɗaukarsa wani hoto.
Shi kuwa slowly ya sunkuyo da kansa a kanta, a gefen wuyanta ya ɗan kwanto da kansa, a hankali ya fara shakan kamshin shampoo na gashinta mai daɗin kamshin dake kwantar da hankali, sai ya rungumeta sosai a jikinsa, kawai ingiza shi zuciyansa take yi da ya yi kissing ɗinta, gudun kada yai hakan ne yasa ya kwantar da kansa a gefen wuyanta.
Jin sauyawar numfashinta ne ya sanya shi ɗago kai, sai ya ga kuka take yi sosai, nisawa ya yi tare da zuro tongue ɗinsa waje, hawayen nata ya fara lashewa wanda ya sanya ta dakatar da kukan cak. Da sauri ta waro idanunta waje, kai tsaye sai a cikin nasa idanin very close to her haka. Ɗan zabura ta yi, lokaci guda kuma ta ji tsoro ya shigeta, bata san tsoron me ba, kawai ta ji tsoro ne.
Cigaba da lashe hawayen nata ya yi bai damu da tana zazzare mashi idanu ba. Ɗan lasar lips ɗinta ya yi da ya gama lashe hawayen, sannan ya dawo da kallonsa gabaɗaya a kan idanunta, suna fuskantar juna, suna shakar numfashin juna. Saura kaɗan ta saki mashi fitsari a wando, take jikinta ya soma kerma, zazzare idanu ta cigaba da yi a kansa.
"Baby, watau ni ne baki yarda dani ba ko? Ban isa in hanaki abu ba ko? Bincike kike yi a kaina? Baki tinanin hakan zai iya affecting rayuwata ne? Baki san dik abin da ake ɓoyewa yana da haɗari bane? Baki yarda da daddynki ba? Ke fa yakamata ki rufe asirin daddynki, amma kece kike ƙoƙarin ɗaukana hoto dan ki turawa duniya ko?". Ya ɗan dakata yana jinjina kai.
Gagara motsawa ta yi, jikinta dik a mace, ba zata iya yin magana ba. Kara matso da face ɗinsa dab ita sosai ya yi, kara zaro mashi ido ta yi, shi kuma ya ɗaure fuska tamau tare da cewa. "Ban yi zaton zan ce ga abin da nike so ki yi gaban kanki ba, idan kina son sanin waye ni why ba zaki yi facing ɗina ki tambayeni ba? Meyasa zaki tambayi wata bare? Good!". Ya faɗa tare da saketa, a hanzarce ya miƙe, jefa yai da wayarta a saman bed.
"Ki nuna hotona a koma ina ne ki tambayi waye ni idan kin yi ra'ayi, amma ki sani ko mutuwa na yi a kan hakan kece sila". Yana kai karshe ya nufi hanyar fita da sauri tamkar zai tashi sama...... Shiru ta yi tamkar mara lafiya, ta zuba mashi ido har ya fice. Yana fita ne ta samu damar fashewa da kuka, a ranta take jin bata kyauta ba, meyasa zata nemi dole sai ta binciko waye shi tin da ba zaluntarta yake yi ba? Meyasa idan tana son sani ma ba zata tambaye shi ba kamar yadda ya ce ba?.
Da sauri ta miƙe ta ɗauko wayar tata. Jikinta har yana rawa wajen laluɓo number ɗinsa. Kira ta fara danna mashi tana ruwan hawaye. Na farko ta kira har ta katse ba'a ɗaga ba, na biyu kuma yana shiga ya katse kiran, na uku ma haka, da ta takura mashi sai ya kashe wayar gabaɗaya, ta kira ta ji switch off.
Take jikinta ya kara mutuwa, ta yi nadamar ɓata mashi rai har ya yi fushi da ita. Da gudu ta fito ta nufi room na Madam tana kwala mata kira. A lokacin Madam tana cikin toilet, hakan yasa ta zauna a gefen gadonta tana jiranta.
Tana zama sai ga wata mata ta shigo room ɗin bisa jagorancin Aisha, matar ma tare take da wata budurwa wacce a kallah zata kai 23 haka. Cike da mamaki Seraphina ta bisu da kallo kafin ta ce. "Aisha who are those people?".
Kallon tsab matar ta yi wa Seraphina kafin ta ce. "Wannan ita ce yarinyar kenan?". Da alamar walaƙanci da ƙasƙanci a maganar matar. Jinjina mata kai Aisha ta yi kafin ta ce. "Ita ce mai gidan". Taɓe baki matar ta yi tare da cewa. "Ina Aunty Rohisha ɗin ne?".
Aisha ta amsa da. "Tana toilet"...... Ganin yadda matar ta kalleta ya sa Seraphina ta ɗan sha jinin jininta, a sanyaye ta ce. "Good morning".
Matar ta amsa a takaice tare da wucewa ta haye saman bed ɗin Madam ta yi kane-kane har da miƙe kafafu tamkar wata ballagaza ta zauna a kasuwa. Matashiyar yarinyar dake tare da ita ce ta kariso wajen Seraph, sai da ta dallah mata wani irin harara kafin ta ce. "Give me a way to pass".
Cike da mamaki Seraph ta kalli filin dake gadon, dik bai isheta hanyar wucewa ta haye saman gadon ba sai in da take? To amma da yake ba bakuwar zafi bace sai an taɓota sosai sai ta miƙe ta basu waje, ta koma saman sofa ta zauna, ita ba don tana son faɗawa Madam halin da take a ciki bama da ta bar room ɗin.
Aisha ma waje ta samu saman sofa kusa da Seraphina zata zauna kenan muryan matar ta katseta da cewa. "Ke wuce ki fita a nan"........ ALLAH sarki, suna nunawa Aisha kyara ne dan marainiya ce Madam ta ɗauko take reko, abu ba abu ba sai su ce mata maganar family ake yi.
Wannan mata kanwar Madam ce uwarsu ɗaya ubansu, wannan budurwar ƴar kuma ƴarta ce, basu da mutunci ga shegen son duniya, sun ji Madam ta samu matsugunni a CRYSTAL PALACE ne shiyasa suka ce suma dole su zo aci arziki da su, yanzu dai wai sun dawo gidan da zama.
Miƙewa Aisha ta yi zata fita fita jiki ba kwari Seraphina ta riketa tare da cewa. "For what reason zata fita? Is it your room? Su waye ku nema da zaku zo ku samemu a ɗakin mom ɗinmu ku ce ta fita? Is it your room?". A kule ta faɗa tana kallon matar, jinin IRON FIST basa ɗaukar rainin wayau, da farko ta ɗauka bakin arziki ne shigasa tai masu shiru, amma da ta ga basu san arziki ba shi ne ta gwada masu jinin IRON FIST take.
Budurwar ce ta amsa da. "Ke baki da tarbiya ko? Babban mata zaki faɗawa haka? Bata haifeki bane? Ko a gidanku babu manya ne?"..... Wani irin mugun harara Seraphina ta dallah mata kafin ta ce. "Keda gidanku suke da manyan ai naga basu baki tarbiyar adalci ba, kuma basu koya maki yadda ake magana ba". Ta faɗa tana zazzare mata ido, irin ta san bafa tsoronta take ji ba.
Kallon juna yarinyar da mamanta suka yi, sun gano Seraphina ba wacce ake takawa ta taku bane. Daidai lokacin Madam ta fito daga toilet, ta yi wanka har ta shirya a ciki dan da kayanta ta shiga, cikin arabian dress ta shirya.
Ganin suna musayar yawu yasa Madam ta yi saurin cewa. "Safiyya me haka? Daga zuwanki? Ke ba zaki canza hali bane wai?".
Wannan budurwar ce mai suna Suhana ta ce. "Mommy Ummina bata da laifi, wannan yarinyar ce ta zageta"...... "Ya isa haka Suhana, babyn daddy me yakefaruwa ne?"...... Sake hannun Aisha Seraph ta yi tare da miƙewa ta isa gaban Madam, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Mommy daddy yana fushi dani, ya tafi cikin fushi, kuma ina ta kiransa baya ɗauka, daga karshe ma ya katse kiran".
Riko shoulders ɗinta Madam ta yi. "Jeki room ɗinki ina zuwa sai ki faɗa mun me kika yi mashi ya yi fushin dan mu san daga in da zamu fara gyara, Aisha ku je da ita". Ta kai karshe tare da saketa. Da sauri ta juya ta nufi waje ba tare da ta sake kallon in da suke ba, Aisha ta rufa mata baya.
Suna fita Madam ta kalli Safiyya tare da cewa. "Ke baki da hankali ko? Sai kin ɓata mana dik wani shirinmu a kansu kin sa asirinmu ya tonu ko? Yanzu idan kuka fara nuna mata kiyayya kuka ja aka koremu ba shikenan komai ya lalace burinmu ba zai cika ba ko! Meyasa baku da tinani ne?".
A taƙaice Aunty Safiyya ta ce. "Kai Aunty Rohisha, ni fa yarinyar ne take bani haushi, na tsaneta daga kallon farko, na kasa ɓoye tsanar ne yasa na nuna halin"...... Nufosu Madam ta yi tana faɗin. "Gara ki koyi danne abu, dan wlh a kan wannan yarinyar babu irin matakin da ba zasu ɗauka ba, zai ma koremu a gidan nan, kada ki manta saboda ita ya ɗaukomu dan ta yi farinciki, dan haka dik abin da kake son cimmawa a hankali zaka bi da shi har ka cinma, bugu da ƙari ina son ki san cewa gidan nan gabaɗaya kewaye yake da camarori, cikin bedrooms ɗinmu ne kawai babu camera, amma bedroom na Seraphina akwai ɓoyayyen Camera, ranar da na shiga unexpected ina ɗaga kai jikin bulb na wuta ta ƙasa naga karamar camera, da alama basa son Seraphina tasan da camerar ne a wajen yasa ya ɓoye, amma sauran ɗakunan gidan babu, su parlo, kitchen har balcony dik akwai Camera, dan haka ku yi taƙa tsantsan, ku kuji shiga harkar Seraphina a gaban camera".
Kai suka jinjina alamar gansuwa, sannan Suhana ta ce. "Mom gaskiya CRYSTAL PALACE duniya ne kuma karshe ne, amma kuma gaskiya suna ji da yarinyar nan sosai, dubi irin daular da aka zuba mata, sannan Camera ta ko'ina dan kula da dik wani motsinta, tsaro sai ka ce zasu iya hana mala'ikan mutuwa ɗaukar ranta in ya zo?". Tana ɗaure fuska alamar hasada dan bata samu irin hakan ba ta faɗa.
Madam zata yi magana Aunty Safiyya ta rigata da cewa. "Gaskiya Aunty Rohi kin iya ɓadda kama, ni ba dan na ji muryanki bama ba zan gane ke bace, kin iya sanya fuskar boge wlh, kuma kowa ya ɗauka fuskanki ce fa". Ta kai karshen magana suna murmushin dake kama dana mugunta. Madam ta ce. "To ya zan yi, biyan buƙata yafi kwana masallaci, dole in yi basaja, dole in ɓadda kama in shiga jikin Seraphina dan cikar burina".
Shiru Aunty Safiyya ta yi tana tinanin makudan dalolin da ta karɓa kan ta fito masu da Seraphina daga CRYSTAL PALACE, a ranta ta fara tsara yadda zata shawo kan lamarin, ta samu ta ja Seraph wajen CP ɗin. Watau sun san a cikin CP dai kam basu isa shiga su ɗauketa ba, dole sai an fito da ita waje, lallai kuwa akwai gagarumin matsala, meyasa suke neman Seraphina? Su waye su? Madam Rohisha da ɓadda kama for what? Meyasa ta shiga rayuwar Seraph? Me manufar su Safiyya? Zasu yi nasara ko kuwa?. Uhm mu leƙa WS-HOSPITAL mu dawo.
---------------------------🔥
WS-HOSPITAL.
Bayan wani lokaci, zan yi skipping na labarin ne kaɗan saboda wani dalili da a gaba zaku gane!.
Gabaɗaya 3D haɗe suke a cikin section D suna duba lafiyar jariran dake cikin cikin uwar da suka kirkira da kansu, yaran sun fara wayo, dan wajen transparent ne kana iya ganin yadda suke rayuwa a ciki, suna motsawa a hankali tamkar yadda suke motsi a ciki uwa, kallonsu daga ta waje abin sha'awa da ɗaukar hankali, dikkansu kuma lafiyayyu ne sosai, dan in baku manta ba su Dr suna tace maniyin namiji su cire mara karfi sai su kara mashi alluran karfi dan ya zama daidai da wancan.
Bari in baku wani haske a nan yadda zaku fi fahimta, nasan kunsan halittar mace da namiji ba ɗaya ba, mace tana da rauni, namiji ya fi karfi, to wannan maniyi mai karfi shi ne na ɗah namiji, wanda bashi da karfi sosai kuma shi ne na ƴa mace, to in baku manta ba na faɗa maku su basa kyankyashe mata ai, maza kawai suke kyankyasa, shiyasa suke karawa maniyin karfi da allurai domin ya basu ɗah namiji ba mace ba, fatan kun gane?.
Idan kunga yadda jariran nan ke motsawa sai sun burgeku, a yanzu sun kai watanni bakwai, sun zama halittar mutun, a kallah zasu kai jarirai 150 a wajen, dikka kuma maza ne, babu mace ko ɗaya, sannan dikkansu farare ne tas da su, da alama sperm ɗin sai an zaɓa ake saya, ba kowanne ake saya ba.
Dr James ne ya ɗan tsaya a gaban na'urar kwalba guda, hannu ya ɗaura a saman oxygen control na jikin gwalbar, kashe wajen ya yi, hakan yasa iska ta daina shiga cikin kwalbar, komai ya tsaya jim. Idanunsa a kan wata ƴar madaidaiciyar touchscreen computer dake jikin kwalbar wanda suke amfani da shi dan duba bugawar zuciyar jaririn, yanayin da yake ciki da sauransu, so ya zuba ido a wajen yana kallon yadda computer ke harbawa da karfi-karfi, zuciyar yaron tana bugawa da karfin gaske ne, saboda rashin iskar shaƙar numfashinsa.
Slowly ya dawo da kallonsa a kan jaririn, nan ya ga yaron ya fara motsawa da karfi alamar yana neman iskan shaƙa, ya ware ƴan yatsunsa dake ƴan ƙanana sosai yana ƙoƙarin mikar da kafafu, jikinsa babu kwari bare ya yi wani yunkuri. Mai da kallonsa a kan computer Dr James ya yi, nan ya ga zuciyar yaron ta tsananta bugawa da karfin gaske.
Dawo da kallonsa a kan kwalbar ya yi, unexpected ya ga jaririn ya waro idanu waje, azaba ta yi azaba, babu iska babu shaƙar numfashi ai kunga babu azabar da ta kai wannan. Nisawa ya yi tare da dan lna oxygen control ɗin ya kunna mashi. Haba ai har sai da computer ta yi ƴar kara alamar bugawar zuciyar yaron ta dawo, slowly jaririn ya maida ƴan yatsunsa ya dunkule su kafin ya ɗan juya tamkar yadda suke juyawa a cikin uwa.
Yana juyawa cibiyarsa dake manne da uwa ne ya ɗan naɗe mashi wuya. A daidai lokacin su Dr Kamal suka iso wajen, in a low way Dr James ya ce. "Kamar wannan project ɗin ya fi dik waɗan da muka yi a baya kyau! Karfi da kuma lafiya!".
"Meyasa ka ce baman?". Dr Mark ya tambaya. "Saboda yaran suna da karfi da lafiya, a ƙaida jariri baya iya rayuwa babu iskan oxygen na second 30, amma yaron nan ya kai 1 minute babu iska, kuma da na dawo da iskar bai shiga wani yanayi ba, yakamata nan da 30 days mu yi test na brain and heart ɗinsu dan tabbatar da ingancinsu".
Dr Kamal ne ya ce. "Gaskiya yaran suna da lafiya sosai, nima na shaida duba da yadda suke motsawa da karfi, bamu taɓa kyankyasan yara masu karfi da lafiyarsu ba"....... Dr Mark ne ya ce. "To ko dai akwai jinin FIVE LIONS a jikinsu ne?"........ Siririn tsaki Dr James ya ja tare da wucewa gaba bai sake magana ba, Dr Kamal ne ya ce. "Ga dikkan alamu har yanzu FIVE LION suna ranka Mark". Ya faɗa tare da bin bayan Dr James.
Bayansu Mark ya bi yana faɗin. "Dole FIVE LIONS su tsaya a raina, kuma nasan suna ranku, dan ba'a taɓa shegun jami'an da suka kusantomu irinsu ba, jami'an da suka shirya mission a kanmu, jami'an da basa tsoron mutuwa, jami'an da basu ɗauki ransu a bakin komai ba".
"Hmmm". Kawai Dr Kamal ya ce, na ciki na ciki, su kaɗai suka san me yake a cikin ransu. Kai tsaye wani ɗaki dake a cikin section D
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 95