shi!. Cak ta dakatar da kukan nata, slowly ta ɗago da kallonta ta saci kallonsa, dan tsoron haɗa ido da shi take yi ma.
"I don't know him, kawai naga mammyna tana da irin hoton ne, ta sanya cikin frame tare da rubuta love of my life a jiki"........ A takaice ya ce. "Are you Dr Hushaima's daughter?". Ya yi maganar da alamar mamaki a kan fuskansa, kuma da alama a ƙage yake da son jin amsa........ Kai ta jinjina mashi alamar e.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, lokaci guda ya ɗan ɗauke wuta, har wani irin huci mai zafin gaske ya furzar daga bakinsa, hannu yasa ya ɗan dafe gaban goshinsa, kamar ya shiga damuwa. Zuba mashi ido na ɗan lokaci ta yi, ganin bashi da alamar sake motsawa yasa ta ce. "Uncle should I go?".
Siririn ajiyar zuciya ya sauke, a sanyaye ya ce. "Just call me daddy"...... Tsare shi da ido ta yi, tamkar tana son karantarsa ne. Hakika ya shiga damuwa, yau ya shiga ɗakin aikin nasu ne yana binciken tsoffin hotuna sai ya kalli alamar an ja hoton an kusa ciresa, yasan kuma ita kaɗai ta shiga ɗakin shiyasa ya zo tambayarta, dan a dik hotunan dake ɗakin wannan kawai ta so cirewa, idan bata da alaƙa da hoton ba zata taɓa ba a cewansa. Dik yadda aka yi suna da alaƙa da ita, wannan hoto dai nasan kun fahimci daddyn Seraph ne a jiki, in kuwa haka ne kunga alama ta nuna su suka kashesa, ya ratso ta cikin aikinsu ne suka gama da shi, in kuma basu kashesa ba to dole ɗaya daga cikinsu ne shi, kila shima gangster ne.
Kada ku manta ba'a san ainahin face ɗinsu ba, kila ma Champion ɗin nan ne shi, dan haka kawai ba zai ce ta kirasa daddy ba, in ma bashi bane to da wuya idan ba Lion bane daddyn nata, akwai dai matsala, ku duba yadda ya ɗauke wuta a take daga jin yar wacece ita!.
"Daddy should I go?". Ta faɗa cikin shessheƙa. Wani irin yawu ya haɗiye mai sauti tare da sauke ajiyar zuciya jin ta kirasa da daddy, har cikin ransa ya ji sanyi. Hannayenta ya riko tare da cewa. "Kina karatu sosai ko?"....... Ta yi mamakin sauyawarsa lokaci guda! Amma sai ta basar da cewa yeah tana yi.
Jawota jikinsa gabaɗaya ya yi ya rungume, kanta ya fara shafawa a natse, cikin sanyin murya ya ce. "For give me"....... "Why are you asking me to forgive you, daddy?"..... Kai ya ɗan girgiza mata alamar babu komai tare da raba jikinsu, idanunsa da alamar ruwa a kwance a ciki ya saketa tare da cewa. "You can go! At anytime zan sake dawowa, ki natsu ki yi karatu sosai, don't let anyone to know daga in da kike ko wani labari a kanmu kin ji ko?".
Da kallo cike da mamaki ta bisa, ganin bashi da niyar sake yi mata magana ne yasa ta fita da sauri bayan ya buɗe mata kofa. Slowly ya ɗago idanu ya bi bayanta da kallo har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da tada motarsa, ya ja ya nufi gida. Yana parking a parking lot ɗinsu ya fito da sauri ya nufi elevator. Sama ya haura. Kai tsaye ya faɗa ɗakin aikinsu. A nan ya isko Lion and Scorpion suna aiki.
A tsakiyar room ɗin ya tsaya tare da cewa. "Lion kun samu saƙo?". Dikkansu suna kan aikinsu suka gyaɗa mashi kai, dan bala'i irin nasu a ɗakinma fuskoki a rufe tsabar rashin gaskiya da tantiranci. Karisowa ciki ya yi, a kusa da Lion ya zauna tare da fara pressing nasa computer........ "Ya batun wancan aikin?. Hope everything is going well?". Champion ya faɗa ba tare da ya kalli in da suke ba.
Dik ɗakin shiru ya yi babu wanda ya amsa, sai can wayoyinsu ya yi ƙara ban da na Lion, a natse suka fito da wayoyin, sms aka yi masu. Buɗewa suka yi, a tare suka ɗago suka kalli Lion dake tsakiyansu yana pressing nasa computer........ Mai da kallonsu a kan sms ɗin suka yi, hoton wani dattijo ne mai zubin kamala da dattaku, fari tas da shi mai ɗan tsawo, shi ne Lion ya tura masu saƙon a wayansu.
Cikin wata iriyar muryan da ba zaka taɓa iya shaida voice ɗinsa ba Lion ya ce. "He will arrive in the Us tonight, he will check in at the Star hotel, and have dinner by the waterfront, by the end of the night, his fate will be sealed, he will not see the next day!"...... Kallon juna Champion and Scorpion suka yi.
"Guru kai ne a kan wannan aiki". Champion ya faɗa yana kallon Scorpion da suka fi kira da sunan guru, abin da yasa suke ce mashi Scorpion ma shi ne, kamar kunama yake, in dai ya kalli mutum sai gabaɗaya gangar jikinsa ya amsa kamar yadda in kunama ta harbeka sai gabaɗaya gangar jikinka ta amsa. Abin da yasa suke ce mashi guru kuma shi ne namijin gaske ne wanda gabaɗaya baya tsoron mutuwa, rungumar mutuwa yake yi a lokacin aiki, suka ce mutuwa da kanta shakkar ɗaukar guru take yi!.
"Tare zamu buga". Lion ya faɗa a sanyaye. Mamaki ne ya kamasu, dan sun san basu cika aikata aiki a tare ba, meyasa yau zasu yi a tare? Kaifin kwakwalwarsu da kaifinsu yasa mutum ɗaya a cikinsu yana iya jagorantar aiki dik girmanta, yau ace su uku dikka a aiki ɗaya? Lallai koma wanenen wannan babban kai ne!.
Shigar da hotonsa computer ɗinsa Champion ya yi domin ya duba waye shi? Yaki faɗa masu ya je wajen Seraph, ya bar abin a ransa dan yana jin kamar shi ne ke da kusanci da ita ba su ba ko in ce ya fisu kusanci da ita, dan haka a ransa ya kudurta niyar bata kulawa koda basu sani ba!....... Dik yadda aka yi shi ya kashe mata daddy ko kuma shi ne ma daddyn nata ɗan banza!.
Kammala bincikensa a kan hoton Champion, bayanai suka fito mashi kamar haka. Taimur Abbas Ali, dattijo mai shekaru 55 a duniya, preministar ƙasar India, dattijo mai mulki cikin gaskiya da amana, ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa musulman indiyawa, bashi da nuna banbanci ko kyara ga wasu addinan, akwai addinai dayawa a ƙasar, amma bai takura masu ba, ya bari suna yi kayansu, ɗan gwagwarmayar ne sosai, amma a yau so ake yi ya faɗi saboda gwagwarmayarsa kan ganin lallai sai Musulman kasar sun samu ƴanci suna rayuwa kamar kowanu Musulmi a duniya, shiyasa aka yi ca a kansa, har poisoning ɗinsa an so yi, amma ALLAH ya ketarar da shi, musulman indiyawa suna ji da shi, amma gwamnati ta basu kwangilar kashesa, kun ji kuma abin da Lion ya ce.
Jinjina kai Champion ya yi bayan gama karanta bayanai a kan dattijon, watau wanna babban aiki ne shiyasa Lion ya ce tare zasu yi, saboda akwai tsananin tsaro sosai, dole su mayar da hankali.
"Me plan ɗin?". Guru ya tambaya yana share bayanan da ya shi ma ya duba kan dattijon. Take computers dake gabansu ya yi ƙara alamar saƙo. Buɗewa suka yi a natse cike da kware, saƙo ne daga computer Lion, dik wani plan da ya shirya dan kashe mutumin ne ya basu jawabi. Natsuwa suka yi suna karantawa, plan A and B ne, basu taɓa tsara plan ya yi felling ba, amma dik da haka kullum sai sun tsara A and B saboda tsaro. Natsuwa suka yi suka karanta komai daki-daki kafin su goge saƙon, dan basu barin irin wannan shirin nasu gudun ɓacin rana.
Daga nan suka shiga gudanar da aiki. Gabaɗaya Champion ya manta da Seraph again, ya kama aikin ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai.
A tinaninku wani irin plan Lion ya shirya dan kashe wannan mutumi? Za su yi nasara ko a'a? Me kuke tinani a wannan ɓangare? Uhm da aiki babba a gabanmu, kwata-kwata ban taɓo dalilin kirkiran wannan labari da na yi bama, amma mun kusa isa wajen, zan so kowa ya karanta wannan ɓangare dan abu ne da zai shafi kowa da kowa musamman mata, ALLAH dai ya yi mana mai kyau!.
----------------------------🔥
AZURE.
Bayan sun ci sun ƙoshi V ta ce su je wajensu Arya. Cike da farinciki suka miƙe zasu haura sama kenan suka jiyo tsayuwar motocin GAT a harabar gidan. Ai mantawa da su V ta yi, da gudu ta nufi door tana faɗin. "Aunty I'm coming"..... Su dai kome ta yi burgesu take yi, dan haka suka bita da kallo.
Daidai lokacin su Arya suka sauko da gudu, suna sanye da sleeping dress, silky short trouser and vest daga ta sama. Ai a mikiyan su Lisa suka bisu da kallo, ai sai suka rikice, a take a wajen suka rasa wacece V a cikinsu. Ba dan V kayan jikinta daban da nasu yake ba da wlh ba zasu gane ta ba, dan hankalinsu ba zai basu cewa V bata kai su tsawo ba.
GAT na shigowa parlo suka rungumesa da karfi suna mashi oyoyo, ai gyara tsayuwa su Lisa suka yi suna kallonsu, gwanin burgewa. Rirrikosu GAT ya yi yana yi masu oyoyo ɗin shi ma, a haka suka kariso tsakiyar parlon. Sai a lokacin ya lura da su Lisa a tsaye, ɗan sake su V ya yi, idanunsa a kan Aunty Lisa ya ce. "Welcome".
Fuskokinsu a ɗauke da murmushi suka amsa da. "Thank you daddy!"..... "Where's your dad?". Ya tambaya yana kamo V dake ƙoƙarin zamewa, so take ta gudu ɗaki dan ta ga call ɗin Noor ya shigo wayar Angelie dake hannunta. "Daddy yana cikin room". Suka bashi amsa kusan bakinsu a haɗe.
Yana satar kallon suran jikin Aunty Lisa ya ce. "I hope you're enjoying this moment and hope you take your dinner?"...... Da sauri suka amsa da. "Yes daddy, we really love this house, especially da yakasance our beautiful princess tana ciki". Lisa ta faɗa tana nuna mashi V da hannu.
Da yake yasan a yaran nasa V da Angelie ne masu saukin kai sai ya yi zaton ko V ta saki jiki da su ya kyautata masu ne yasa suke yabonta, and yasan ta fi sauran saurin shiga rai, ko kusa ko alama bai gane dalilinsu na kiranta beautiful princess ba. "Let me see your dad Ina zuwa". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan V da gabaɗaya ta gama ƙosawa daddy ya saketa ta gudu ɗaki, ta yi picking call na Noor, dik da tasan batun waya zai yi mata, amma ta matsu ta ji voice ɗinsa.
"My baby naga kina sauri ki gudu sama hope lafiya?". GAT ya tambayeta..... A ɗan shagwaɓe ta ce. "I want to go to toilet daddy"..... Da sauri ya saketa yana faɗin. "Run my baby"...... Kashe mata ido Angelie ta yi, dan ya ga call ɗin ita ma, da gu V ta nufi sama tana maidawa Angelie martani da ɗaga mata gera guda.
Harara Arya ta bisu da shi dan dik abin da suke yi ta gansu. Sama GAT ya nufa yana faɗin bari ya duba daddy Noor yana zuwa. Wucewa Arya da Manassa suka yi izuwa room na daddyn nasu ba tare da sun kalli in da su Lisa suke ba. Angelie ce ta ce. "Aunty Lisa ku zo mu je room ɗinku ko?". Da okey suka amsa, ta wuce gaba suk rufa mata baya. Yanzu Angelie ta gane suna da alaƙa da mutumin da V take so watau Noor, shiyasa ta matsu ta koma room ta ji bayani daga bakin V, ita kuwa V sai addu'a take yi kada su Aunty Lisa su sanar da Noor ga in da ta fito.
Tana hayewa sama ta faɗa balcony, zama ta yi saman chair dake wajen ta fara ƙoƙarin kiran numbersa kenan kiransa ta sake shigowa. Sai da ta saita natsuwarta kafin ta yi picking.
"Hello". Ta faɗa a shagwaɓe. Nisawa ya ɗan yi tare da satar kallon Leo dake kokarin sanya botiran sleeping dress ɗin jikinsa. "Barka da dare". Ya faɗa tamkar mai raɗa dan kada Leo ya jiyosa.... "Barka dai, fatan ka koma lafiya?".
"Lafiya". Ya amsa tare da ɗan yin shiru, sai kuma ya ce. "Kin manta baki karɓi wayarki ba! Ga shi gobe da sassafe zan bar barrack ɗin nan, sai ya kenan?"... Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Ba kai ka sanyani na manta komai ba".... "Like how?". Ya tambaya...... "Like the way you did mana, ka sanya na manta kaina ni wacece, na mance a wata duniya nike, ai ka yi freshing brain ɗina my heartbeat".
Ɗan waro eyes ɗinsa ya yi, shagwaɓar nan tata ta tsuma zuciyansa, ta yi melting heart ɗin nasa, in a cool way ya ce. "Me na yi maki wai?"....... "Uhm baka san a lokacin da ka matso kusa dani ka yi freshing komai ɗina ba ko?"..... Shiru yayi, lallai yarinyar nan tana son wuce dik lissafinsa, tana faman goge mashi hadda. Satar kallon Leo ya yi kafin ya ce. "Kina da zola, yanzu dai faɗa mun ya za'ayi da wayar nan?".
Turo baki ta yi tamkar tanaa gabansa, a ranta ta kuduri niyyar sanya shi sakin jiki ya yi hira da ita dolensa ko yaki ko ya so. Dan haka sai ta ce. "Da sassafe mu haɗu ka bani wayar kawai"..... Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Okey goodnight".......... "Uhm komai naka daban ne, to mu haɗu a Whatsapp". Bata jira amsar shi ba ta katse kiran. Mamakin yarinyar ne ya rufesa, a ransa ya ce ƴar karama da ita sai karfin hali. A fili kuma ajiye wayar tasa ya yi irin zai shareta ɗin nan.
Amma sai ya gagara, dan kuwa tin da ta ambata mu haɗu a Whatsapp gabaɗaya ya ji hankalinsa ya tattara ya koma kan Whatsapp ɗin nasa, hannunsa sai kaikaiyi yake yi, burinsa ya kunna data. Siririn tsaki ya ja tare da jawo wayar tasa again. Wunna light ɗinta ya yi tare da kunna data. Aikuwa yana kunnawa sai ga saƙonta ya shigo, haka kawai ya tsinci kansa da saurin buɗewa.
"Baka son yin magana dani ko my heartbeat? Laifin me na yi maka? Ko baka son mace irina ce? Baka son yin abota dani? Me na gaza da shi a cikin abubuwan da kake fatan abokiyarka ta mallaka?". Shi sakon da ta fara turowa. A ƙasan kuma sai ta sake cewa. "Ɗan hakinka da baya son buɗewa ya yi maganar nan kada ka bari in kama shi, dan ba zai maka kyau ba!".
One side smiling ya ɗan saki tare da fara typing reply kamar haka. "Gaskiya bana son mace irinki!". A gajarce ya rubuta ya tura mata. Ai tin bai gama cire yatsarta a wajen ba ta fara yi mashi ruwan emoji na hawaye kala-kala. Ya fi emoji 100 ta tura mashi. Da sauri ya hau typing. "Oh sorry, lafa haka nan, da wasa nike".
Yana tura mata ta turo mashi emojin shagwaɓa tana turo baki. Sake sakin one side smiling ya yi kafin ya hau serious typing na amsarta kamar haka. "Kina dikkan abin da kowa zai ji yana son alaƙa dake, kawai ban sanki bane yasa, kin ki faɗa mun wacece ke? Daga ina kike? A ina kika sanni? Idan kika bani amsa zan saki jiki mu yi hira, kuma zaki zama ƙawata". Lokacin da ya tura mata daɗi yasa ta miƙe ta ɗan daka tsalle tare da komawa ta zauna, sannan ta fara typing.
"Promise me that in na faɗa maka wacece ni ba zaka fasa abotarmu ba?"..... Kai ya jinjina tamkar yana a gabanta kafin ya hau typing na ya ɗauki alkawari.......... "Vanisha by name, daughter of GAT, na sanka ne since ban wuci 9 years ba a jinin robar man shafawarmu, kullum da tinaninka nike kwana kuma nike tashi, na ji a raina kamar kai ba a zahiri kake ba shiyasa da na ganka na rikice, please kada ka yi breaking promise da ka ɗauka mun, na zaɓi in faɗa maka gaskiya ne kawai dan nasan dik alaƙar da aka kulla a kan ƙarya bata ƙargo, nasan zaka fahimceni kuma ka mun uzuri". Tana gama rubutawa ta tura mashi kirjinta na dukan uku-uku, cike take da fargabar amsar da zai biyo baya, kada ya ce ya karya alkawari, ina zata sanya ranta in hakan ta faru? Safe kirjinta ta yi tana jiran amsa daga garesa, har ƴar gumi ta haɗa.
Shi kuwa a lokacin da saƙonta ya shigo mashi, natsuwa ya yi ya karanta da kyau. Ai yana zuwa in da ta ce ƴar GAT take bai san time ɗin da ya miƙe zaune ba. Wani irin waro idanunsa a kan wayar ya yi, sai yake ganin kamar bai karanta daidai ba, hakan yasa ya faro karantawa daga farko. Tabbas abin da ya karanta a farko shi ne.
Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan.
Me kuke tinanin zai faru? Zai bata amsa ko yaya? Zai cika alkawarin da ya ɗauka? Zai take zokar AZURE ne ko dai zai bi doka ya gogeta daga babin rayuwansa?.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP
STEP 1________🔥
13-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
NOTE. FIVE LIONS babu complete ɗinsa, yanzu nike posting ɗinsa, yanzu aka fara!
E_____________12
Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan. Gagara danna reply ya yi, dan ya shiga ruɗani.
Wai na ce kun san me ake cewa GAT kuwa? To Nigeria ma bata da muƙamin GAT, sai a manyan ƙasashe ake bada irin wannan muƙami, amma bari in yi maku yadda zaku fi ganewa kila ku gane dalilin Noor na shiga ruɗani da tashin hankali. A Nigeria muƙamin General shi ne babban kuƙami, amma a lokacin da ƙasa zata shiga yaƙi akwai wani muƙami da ake bayarwa wanda ya ɗara General mai ɗauke da 5 stars, wannan muƙami ana kiransa da field marshal, ana bada shi ne kawai a lokacin da ƙasa zata shiga yaki da wata ƙasa, rundunar da zasu jagoranci ƙasar babban da aka fitar shi ake baiwa muƙamin field marshal, bayan yaki ana cire muƙamin dan ba'a amfani da shi. Dan haka Naija dik girmanta bata da GAT!. Irinsu US sau sauran manyan ƙasashe ke amfani da GENERAL OF THE ARMY.
Bari in kara yi maku bayani dan ku fi ganewa da kyau, ku san muƙamin da ake magana a kai. General of the Army yana da 5 stars ne da eagle ɗaya, daga shi sai General mai 4 stars kawai, sai Lieutenant General mai star uku kawai ba wani rank, Sai Major General mai stars 2, Brigadier General mai star ɗaya, Colonel bashi da wani star, Lieutenant Colonel shi ma ba star ba eagle, Major shi ma ba wani star, Captain yana da stars 2 kamar Major General kenan, akwai First Lieutenant mai star ɗaya, Second Lieutenant bashi da star, Sergeant Major of the Army bashi da star, Command Sergeant Major bashi da stars shi ma, Sergeant Major, First Sergeant, Master Sergeant, Sergeant First Class, Staff Sergeant, Sergeant sune suke kasancewa drivers na manyansu ko masu baiwa wani babba tsaro! Corporal, Specialist, Private First Class, Private PV2, Private PV1 dik waɗan nan basu da star, waɗan nan sune muƙaman soja gabaɗaya, to dik waɗan nan da na kirga maku fa a ƙarƙashin GAT suke, kun ga kuwa dole dik wanda ya ji sunansa in yasan me suna take nufi dole ya girgiza!.
"Are okey?". Leo dake kwance rike da waya ne ya tambaya cike da mamaki. Da sauri Noor ya diro kasan bed ɗinsa, V ta yi mashi message ya kai 5 bai iya buɗewa ba bare amsawa. Da zafin nama ya haye bed ɗin Leo, dik hankalinsa a tashe, muryansa na ɗan rawa ya ce. "Bro tashi ka ji wani abu?".
Da ido Leo ya bisa ba tare da ya motsa ba. Sanin halinsa yasa ya fara bashi labari kawai ba tare da ya jira ya tashi ɗin ba. Sai da ya kammala har karshe cike da sa ran zai ga ruɗu a kan fuskan Leo, sai ya ga ya ja siririn tsaki yana dallah mashi harara. Take ya ji jikinsa ta ɗan saki, sai kuma ya ce. "Bro ko baka ji da kyau bane? Ɗiyar GAT fa na ce!".
"Then so?". Leo ya faɗa yana cigaba da dallah mashi harara. Shiru Noor ya yi, kwakwalwansa ta shiga doubting, anya Leo yana kan saiti kuwa? Ana maganar GAT yana faɗin then so what? Anya lafiyansa lou kuwa?.
Katse mashi tinani Leo y yi da cewa. "Bana hanaka jin tsoron wani ɗan adam ba? Baka ji ko?". Leo ya faɗa tare da miƙewa zaune....... Kada ku manta Noor yana da cutar tsoro a cikin kwakwalwansa, dole ya yi wannan rikicewa, dik da ya zama soja ba wai cutar ta rabu da shi bane, time to time tana tashi, idan ta tashi kuma yana rikicewa ya dinga jin tsoron abu, haka idan ya firgita sosai abin yana motsa mashi.
Sake maimaitwa Leo ya yi cewa. "Bro I'm talking about GAT ooooo". ....... "GAT shi ba mutum bane? Ba haihuwarsa aka yi kamar sauran mutane bane? Ko shi faɗowa ya yi daga sama da yasa ya fita daban?". With full confidence Leo ya faɗa, dan shi wlh baya tsoron wani abin halitta face ALLAHN da ya haliccesa, ga shi da saurin fusata, dan a yanzu haka ya fusata na ganin yadda Noor ya tsorata a kan wani halitta, ya sha faɗa mashi ALLAH kawai ake tsoro haka ba wai halittar ALLAH ba, amma Noor baya ganewa, ALLAH sarki bai san cewa ba laifin Noor bane, cuta ce.
Gabaɗaya kan Noor ya shiga ruɗani, sai yake jin kamar shi ne kunnuwansa basa jiyo mashi abin da Leo yake faɗe da kyau, in ba haka ba yana ganin ba zai yiwu wani ya faɗa magana da ta saɓa ta girmamawa ga GAT ba!.
Call da ta shigo wayar Noor a yanzu ne yasa Noor dawo daga duniyar tinanin da ya afka, kallon wayar hannun nasa ya yi, V ce take kira, da sauri ya ɗago ya kalli Leo, while shi ma Leo ɗin shi yake kallo.
"Bro ina tsoron ɗaukar wayar......". Ya faɗa a raunace. Wani irin kallo da Leo ya dallah mashi ne yasa ya gagara karisa maganar. A sanyaye Leo ya ce. "A ina ka taɓa ganin soja da tsoro ko fargaba? GAT da kake magana ka rikice daga jin sunansa ɗin sai da ya jajirce ya cire dik wani tsoron abin halitta kafin ya taka matsayin da yake, idan ka zage watarana kai zaka ɗaura 5 star with eagle a gaban rigarka da taken GAT ɗin". Ya ɗan dakata saboda ɗan sara mashi da kansa yake yi, Noor yana son ja mashi dogon surutu.
Still dai babu alamar Noor zai kwarara kan nan nasa, ganin haka yasa Leo ya jawosa jikinsa, cikin hikima da dabara ya fara karfafa mashi gwiwa yana gwada mashi lallai dikkan wani abin halitta bai isa ya yi maka komai ba matuƙar ka yarda da ALLAH, dan haka ba GAT ba ko bakin sniper or machine gun bai isa yai maka komai ba, dan haka ya karfafa kansa.
One thing da na manta ban faɗa maku na, su Noor ba musulmai bane,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 95