jin kamar zata iya kiran sunansa a gabansa ta mashi magana, kalaman Seraphins sun ɗan shiga kanta sun hura mata kai.
Seraphina kuwa ta dage sai bata shawari take yi, ta dinga tunatar da ita littafin da suka karanta, yadda ake sace zuciyan namiji, dik Rimsha ta san komai, amma tsoron Aryan yasa ta mance komai. Sosai yau Seraphina ta sanyata gaba da shawari masu harfin da tasa ta fara jin kamar zata iya samun kan Aryan.
Sun jima suna hira har kusan mangrib, sannan suka sauƙo suka yi lunch a tare, suna kammala cin abincin sai ga message ɗin Aryan na cewa. "Yanzu ki dawo gida ina jiranki"....... Ai take hankalinta ya koma can, bare ma da ya ce yana jiranta, dik sai ta ji tana son ganin kanta a gida.
A gurguje ta miƙe tana sanar da Rimsha daddynta na jiranta, basu so rabuwa ba, amma haka suka hakura, Rimsha ta rakota main parlo tana cigaba da mata magiyar ta ɗan kara ko awa ɗaya mana, Seraphina ta ce. "My sis idan daddy ya yi kira zuciyata bata iya jira har sai na je na gansa, yana fa gida yana jirana, ki bari gobe ai zamu haɗe a school".
Dukan wasa Rimsha ta kai mata a baya tana faɗin. "Mara kunya, kalleta a wajen, ko kunyata baki ji kike rawan jiki kansa, wai ni me kika yi wa daddyn nan ne da ya mutu a kanki haka? Kullum yana gida tare dake". Cikin zolaya ta yi maganar tana murmushin da ya jima irinsa bai samu gurbi a zuciyata ba..... "Ai daddy ban yi mashi komai bama tukun nan, kin san yana taka mun burki, yana ɗan hanani wai sai mun yi aure, kin san me?". Ta faɗa tare da tsayawa a tsakiyar staircase na sauƙowa ƙasa.
Kai Rimsha ta girgiza alamar a'a bata sani ba. Cigaba Seraphina ta yi da cewa. "Daddy yana hanani nuna mashi love mai kyau sosai, ya ce sai mun yi aure, idan muka yi aure ko, daddy ba zai yarda ko waje ne ya fita ba, kullum zai zama yana gida manne dani, zan narka zuciyansa da soyayya"........ Shiru Rimsha ta ɗan yi, a cikin ranta ta ce ina ma ace ta samu mai sonta sosai, wanda take so sosai ita ma, wanda zata zautar da shi da wannan tarin soyayya da ta iya, ta narka zuciyansa da kaunarta, ta mallaka mashi kanta. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "ALLAH ya nuna mun aurenki da wannan daddyn dai kowa ya huta tin da kinki uncle Faryan ɗina, nima ki tayani da addu'ar ALLAH yasa uncle Aryan ya sakeni in samu wanda yake sona nike son shi, wanda zan zuba mashi dik wata soyayya da na iya, in zautar da shi da kaunata". Tamkar zata sa kuka ta kai karshen maganar
Dafa shoulder ɗinta Seraphina ta yi. "In Sha ALLAH my sister da uncle Aryan ɗinki zaki yi dik wannan kamar yadda nima da daddyna zan yi hakan, uncle Aryan zai soki, zai ƙaunaceki, zai zauce a kanki kamar yadda daddy ya mun, ki ɗauki shawarina da na baki please, zamu dace".
Kai kawai Rimsha ta jinjina, ita kaɗai tasan me a ranta, ita kaɗai tasan waye Aryan. Hannunta Seraphina ta ja tana faɗin. "Zo mu je ki rakani ni kam, daddy na jirana". Ta jata suka sauƙo ƙasa. Babu kowa a parlo sai Abba dake zaune saman sofa yana rike da sandarsa.
Cikin girmamawa Seraphina ta ce. "Abba zan koma"........ Kai ya jinjina mata. "Okey ki gaida gida sai na zo, ki faɗawa iyayenki fa ina nan zuwa mu gaisa".
Da okey ta amsa mashi, har zata fita ya kirata, kyautar wani kyakkyawan zobe ya bata yana faɗin. "First gift from your father in-law"........... Ni kam na ce Abba ya faɗi daidai, aikuwa shi father in-law ɗinta ne amma ta ɓangaren daddy Aryan namu ba.
Karɓa ta yi, diamond ring ne mai bala'in tsada, ta ji daɗi, a tsakiyar yatsanta ta sanya tana mashi godiya, yana kallonta ya ce. "Kin dace da ɗana sosai"..... Ita kam murmushi kawai ta yi game da wucewa tana kara yi mashi godiya.
A kofar parlo Rimsha ta tsaya suka ƙara yin sallama, sannan ta koma ciki Seraphina ya wuce, ko da ta dawo cikin parlo Abba baya nan, ta wuce room ɗinsa dan shirin zuwa masallaci. Sama ta haura ta nufi ɗakinta dan yin wanka ta yi sallar magrib
Benensu kai tsaye Seraphina ta wuce tana sauri sosai. Tana shigowa ta isko Madam a parlo. Oyoyo ta yi wa Madam game da zuwa ta rungumeta tana murmushi. Murmushi Madam ma ta yi tana faɗin. "An dawo?". Kai ta jinjina alamar kafin ta sake Madam ta miƙe da sauri ta nufi ɗaki tana faɗin. "Daddy na jirana".
Da kallo Madam ta bita tana murmushi. Tsayawa ta yi a kofar ɗakin ta yi sallama saboda ya hanata shigowa babu sallama dik da take ba musulma ba. Bata jira ya amsa ba ta faɗo cikin ɗakin.
Yana kwance a kan gado yana waya da guru dake ce mashi ya yi maza ya zo su yi shirin zuwa masallaci, shi kuwa ya ce yana ɗakin matarsa idan guru ya isa ya zo ya fito da shi.
Da gudu ta haye gadon tana faɗin. "Na yi missing ɗinka over my gentle chaos". Ta faɗa game da manna mashi sumbata a cheek ɗinsa. Zuba mata idanu ya yi ya kasa ɗaukewa, yaga ta ƙara kyau sosai ne.
"Daddy na maka kyau sosai ne da kake kallona haka?"...... Shiru bai amsa mata ba. Hakan yasa ta sake cewa. "Ni fa taka ce, ka kalleni da kyau ka sake kallo, kayanka kake kallo, mallakinka ne". A shagwaɓe sosai ta faɗa.... Shi kam ya rasa waye yake koyawa Seraphina manyance da iya magana, dik ta gama goge mashi hadda.
Dik abin da take faɗe guru na jinta, dik sai ya ji wani iri, a ransa ya ce. "A dole a gidan nan su dinga rasa natsuwar Champion ɗinsu, ashe dole dik after 1 hour ya gudu wajenta, irin wannan shagwaɓa mai narka zuciya da kalamai masu zafin nan, ai komai taurin zuciyarka sai ta narka maka shi, ka ji wani irin shagwaɓa mai melting heart, ya rabb, gaskiya nima ina buƙatar irin wannan kulawa da soyayyar, wai tayi kewansa over"........ Ni kam na ce to malam guru irin wannan kula da soyayar dai a waje ɗaya ake samunsa, a wajen mace kawai zaka iya samunsa, matan da kuke cewa basu da amfani, to dik duniya macece kawai zata yi maka irin wannan soyayya da kulawar, yauwa gara ma ka dawo cikin hankalinka, ko ya kuka ce jama'a?.
Zare wayar daga kunnensa Aryan ya yi, a daidai lokacin take cewa Aryan. "Daddy yau naga soft lips ɗinka ya ciza red sosai, kamar in yi kissing ɗinsa fa". Tana murmushi mai kwantar da hankali ga shagwaɓa, ko kunyansa bata ji kwata-kwata, ta tsaresa da waɗan nan dara-daran violet eyes ɗin nata tana wani turo baki.
Katse kiran ya yi game da dallah mata harara kafin ya ce. "Ban ce ki dawo da wuri ba? Me ya sanya kika je kika yi zamanki a can?". Yana ɗaure fuska sosai ya faɗa, sai kuma ya miƙe zaune yana kallonta.
Ɗan turo baki ta yi, ganin babu alamar wasa a tattare da shi ne yasa ta sauƙo ƙasan bed ɗin, a gabansa daidai in da ya sauke fararen kafafunsa ta tsugguna, hannayensa ta riko cikin nata, cikin girmamawa da sanyin murya ta ce. "Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, hira ce ta yi daɗi yasa na manta ka ce in dawo da wuri".
Ai gabaɗaya ta narka zuciyansa, ga girmamawa, ga soyayya kuma ga shagwaɓa, sai ya rasa me zai ce mata ma, ya tsareta da ido kawai, yana mata wani irin musulmin kallo mai narka zuciya.
"Please my whisper baby ka yi magana mana, na ce na zan sake ba, first and last i promise, ka ji nawan?". Tana turo baki ta faɗa, bata san dik ta rufe mashi baki ya rasa abin faɗe bane.
Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke game da riko hannayenta da ta kama nasa hannun da su. Ya ɗan matsa ƴan yatsunta cikin tafukansa har sai da ta ce wash......... Cikin wani irin low voice ya ce. "Komai zafin da na ɗauka sai dai in ban zo wajenki ba, komai ɓacin ran da nike ciki sai dai in ban haɗu dake ba, dik gudu suke yi, my cherry, kin san dik wata hanya da zaki bi dan ki faranta mun, nima yau zan sanyaki farinciki na musamman, jeki shirya, kada ki ci komai, yi wanka kawai ki shirya bari in yi sallar magrib da ishai ina zuwa in baki wata bazata".
Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi game da miƙewa tana faɗin. "Thank you so much my gentle chaos". Ta faɗa zata wuce. Miƙewa ya yi rike da hannayenta, ya ɗan kura mata idanu kafin ya ɗan rage tsawonsa, ya ɗan sumbaci gaban goshinta kafin ya saki hannayenta. Suna bin juna da kallon kauna ya wuce ya nufi benensu dan ana gab da kiran sallar mangrib. Yana fita ita kuma ta faɗa toilet cike da begensa da sabon soyayyansa.
A tinaninku bazatan me zai bata?.
----------------------
IRON FIST.
Mu ɗan koma baya kaɗan kafin mu cigaba. A ɗazun bayan Aryan ya kammala waya da Seraphins ya bata izinin tafiya, da suka gama wannan rikici da Vir ya bar wajen room na Lion ya shiga. Babu kowa sai ya fita zuwa ɗayan room ɗin, nan ya isko Lion tsaye yana shiri cikin tail coat fari tas, a gefen bed ya zauna yana faɗin. "Ina da tambaya".
Shiru Lion bai kulasa ba. A dake ya ce. "Wai wannan gida naka ne kai kaɗai ko namu?"...... Banza da shi Lion ya yi bai amsa ba. Ganin hakan yasa ya ce. "Ɓata bakina ma nike yi da na tsaya yin magana da kai a kan wannan issue, ina da right na yin abin da nike so a gidan nan, dan haka zan kawo sister ɗita wannan gida, ta zauna damu for some days, ba zata shiga harkarka ba, bama zata zo in da kake ba".
Tamkar babu Lion a ɗakin, ya cigaba da abin da yake yi, sai da ya kammala ne ya kalli in da Aryan yake. "Get ready to go to Dad's house now, there's something we need to check". Yana gama faɗa ya juya ya fice abinsa. Miƙewa Aryan ya yi, ya fito ya sanar da su Vir su shirya, sai ya dawo dan shiryawa.
After like 1 hour suka fito shirye cikin kaya iri ɗaya, tamkar ƴan huɗu. A main parlo suka iso Lion zaune, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya ɗaga kansa sama tamkar mai tinanin wani abin, ya yi shiru.
Ƙashin maƙogwaronsa Aryan ya ɗan taɓa kafin ya ce. "Let's go". Ba tare da ya yi magana ba, ya miƙe tsaye kafin ya waro jade eyes ɗinsa masu kama da sleeping eyes ɗin nan, yau sai ya yi kamar wanda yake cikin maye ma, dik yadda aka yi barci yake ji.
Jerawa suka yi zuwa main door na fita. Suka shiga elevator suka yi ƙasa, dik da suna sanye da wannan nose mask ɗin nasu na gado dik wanda ya gansu sai ya sake waigawa ya gansu, mazajen gaske.
*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*
Likes comments and share fisabilillah.
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-31.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
No editing.💔
E_____________ 73 & 74
A harabar benen nasu suka tsaya, key ɗin wata dalleliyar mota Lion ya fitar daga aljihun coat ɗinsa. Miƙawa guru key ɗin ya yi, dikkansu da kallo suka bisa suna mamakin ganin yau da motarsa na ainahi zasu fita.
Wannan mota dad da kansa ya saya masu su huɗun iri ɗaya, to tin bayan rasuwar dad ɗin suka rufe motocin, dik wani abin da zai sanya a gane suna da alaƙa da Haiza'an sai da uncle yasa suka ajiyesa, dalilin kenan da yasa basa fitowa da Hero, domin kowa ya ga wannan zaki sai ya gane zakin Haiza'an ne, dan wannan zaki ya shiga tarin dad dama duniya bakiɗaya, kuma a jikin Zakin a gaban goshinsa akwai rubutun sunan dad da aka yi mashi da wuta, shiyasa kowa ya gansa zai gane na dad ɗin ne, shiyasa ko waje basa leƙowa da shi, yana gida.
Sun yi mamakin ganin zasu fita da wannan mota, motocin nasu dik plate numbersu sunan Haiza'ans family ne a jikinsa, shiyasa suka jinginesu. Tin da suka ga Lion zai fita da wannan mota suka fahimci ya shirya fito na fito da duniya bakiɗaya kenan, lallai kuwa akwai kura, uncle da duniya ta ɗauke ya mutu yana ƙoƙarin tada tarzoma kenan, zai sanya IRON FIST su bayyana a duniya, zasu jingine aikin SSO kenan ko yaya? Ya Aryan zai yi da Seraphina da ta tsani IRON FIST? Me Khaiza'ans family zasu ce? Abba zai yarda da cewa Aryan shi ne Champion na IRON FIST?.
Fito da motar guru ya yi, Lion ya shiga gidan gaba, Aryan da Vir suka shiga gidan baya. Kai tsaye HEART OF CRYSTAL PALACE suka nufa. Tin daga kan securitys dake tsaron CRYSTAL PALACE har izuwa kan jama'ar dake ciki sai da suka zubawa motar nan ido, musamman suna Haiza'an dake gaban motar. Mota na farko kenan da dad ya fara sayawa ƴan matasansa a lokacin.
Da yake gate ɗin gidan dad automatic ce, suna isa gate ɗin ta yi scanning motar, ganin babu abin haɗari a ciki yasa gate ɗin ta wangale masu kanta. Ciki suka kutsa, kai tsaye suka nufi marking lot, bayan sun paka motar kusan a yare suka fito.
Cikin main parlo suka nufa, a jere suke sanya kafafunsu a ƙasa suna ɗaukewa. Suna shiga main parlo suka rabu, kowannensu ya yi nasa hanyar. Kai tsaye cikin ɗakin dad ɗinsu Lion ya nufa, tin da dad ya rasu Lion bai taɓa shiga wani ɗaki a gidan ba face na daddyn nasu, ɗakin mom ɗinsu yana nan yadda ta barshi, bai taɓa shiga ba, baya sha'awar ganin ko kofar ɗakin bare ya shiga.
A saman bed ɗin daddy ya jefa wayansa game da cire tail coat ɗin jikinsa ya jefa kan gadon, ya bar iya long sleeve shirt na ciki, toilet ya shiga, jim kaɗan ya fito fuskanta da ɗan danshin ruwa, balconyn daddy ya nufa, tsayawa ya yi yana kallon cikin CRYSTAL PALACE ɗin, a hankali ya ɗan lumshe idanu yana tina da idan ya shigo gidan da fuskan daddynsa yake fara cin karo yana tsaye a balcony, ko yana zaune a kan sofar dake wajen.
A hankali iska ta fara kaɗa shi tana kaɗa kitson dake kansa, sai ya ji wani irin daɗi na ratsa shi. Ya ɗan jima a tsaye a wajen kafin ya juyo ya dawo cikin ɗakin. Haka kawai yau ya ji yana sha'awar yi wa daddyn nasa bincike a ɗaki, abin da bai taɓa yi ba, dan kullum ya zo daga toilet sai gado kawai yake amfani da su.
Drawers na wajen mirror ya buɗe, babu komai a ciki, rufesu ya yi ya nufi wajen closet na daddy, kusa da wani tangamemen wardrobe ya tsaya, komai yana nan yadda yake, kayan daddy dik baa taɓa komai ba tamkar yana raye.
Nisawa Lion ya ɗan yi, hannu ya kai zai buɗe wannan wardrobe ɗin, sai taki buɗewa, zuba mata idanu kaɗan ya yi, nan ya fahimci haɗe take da na'urori, sai da password zata buɗe. Ɗan ɗage kafaɗunsa ya yi alamar anyway, sai ya wuce drawer ta gaba. Hannu ya kai jikinta take ta buɗe kanta. Wasu tsala-tsalan tail coat masu masifa tsada ne a shirye a ciki, a jikin hanger aka shiryasu tamkar mai shi yana raye.
Kallo ɗaya ya yi masu ya ɗan ɗauke kai, har zai wuce kuma sai ya lura ai ba iya faɗin wardrobe ɗin ba kenan, tana da zurfi amma a wajen da su coat ɗin nan suke ya yi kaɗan ace iya zurfinta kenan, what's behind?. Bai yi wani dogon tinani a kai ba ya matsa gaba, dan bai son ciwon kai, saboda yana tinanin dik kaya ne a cike a cikin ko'ina, dan yasan halin daddyn nasa ɗan kwalisa ne, gadon ɗaukar wanka suka yi.
Wucewa gaba ya yi, ya dinga yawo a wajen, ko wucewa ya zo yi kusa da wardrobe in dai ta ɗan yi scanning ɗinsa sai kofar ta buɗe, bai damu ya dudduba me a ciki ba, wasu drawers ɗin ma takardu ne a cike a ciki ba kaya ba, amma bai mai da hankalinsa ba, wucewa kawai yake yi.
A cikin ransa ya ce. "Ina computer dad? Da wannan computer yake controlling HAIZA'ANS AIRLINE da sauran abubunsa"....... Kada ku manta na ce maku computer hannun Dr James ita ce computer dad.
Fitowa daga wajen ya yi, ya dawo tsakiyar ɗakin. Yana tsayawa sai ga Vir ya shigo yana faɗin. "Nan ka yo?"..... Bai yi magana ba, ya dai bi Vir da ido. Saman gadon dad Vir ya zauna yana cigaba da kallon Lion ɗin.
Aryan kuwa kai tsaye room na mom ya nufa, domin kuwa ya jima yana son zuwa room ɗinta ya yi bincike, amma bai samu dama ba, abubuwa sun masu yawa, kafin su kammala wannan wannan zai sako kai, ko lokacin kansu basu da shi........ Yana tura kofar yana da kura ta buɗesa, dan kuwa ana gyara ko'ina a gidan banda ɗakin nan, Lion ya hana a taɓa ko kofar ne, shiyasa uban yana da kura ya buɗe koina.
Kamar Aryan zai juya sai kuma ya daure ya fara tattare yanar yana shiga ciki, dik in da ya taka sai shaidar kafansa ya bayyana saboda kura da ta yi yawa.
Gadonta, drawers komai yana nan yadda ta fita ta bari, har bedsheet baa taɓa ba. Ɗan girgiza kai Aryan ya yi game da cewa. "Sai an share room ɗin nan an gyara zan dawo, dattin ya yi yawa". Ya faɗa game da ƙoƙarin juyawa zai fita.
Idanunsa ne suka sauƙa a kan gadonta, ya ga alamar tudu a bakin gadon, alamar wani abin ne da kura ta rufe sosai, kamar ba zai je wajen ba, sai kuma ya daure ya karisa. Hannunsa yasa ya zaƙulo abin dake wajen, kura ya zama tamkar ƙasa mai laushi aka zuba a wajen.
Ya yi mamakin ganin wayarta ce, kenan tashin hankali yasa a lokacin da ta shigo ɗakin ta manta waya? Karkaɗe wayar ya yi game da ɗauka ya fita, rufo kofar ya yi ya nufi room ɗinsu na gidan, a nan ya ɗauki towel ya goge wayar, sai ya yi ƙoƙarin sakata a caji, amma babu caza, addu'a yake ALLAH yasa wayar bata mutu ta daina aiki gabaɗaya ba, ALLAH yasa ta tashi.
A aljihunsa ya sanya wayar kafin ya fita ya nufi ɗakin dad. Ko da ya je bai sanar da Lion ya ga wayan mom ba, yana son ya fara binciken komai da kansa kafin ya sanar da Lion........ In short sun yi kewaye sosai a gidan, amma basu bi diddigi ko bincike-binciken abubuwan ba, sun dai duba komai yana nan, babu abin da zasu buƙata ko da zasu dawo gidan.
Sun ɗauki a kallah 3 hours a gidan kafin su nufi gida, suna komawa kuma ɗakin aikinsu suka shiga, aikin awa ɗaya suka yi, a nan Lion ya ce akwai wasu containers da ake shirin shigo dasu cikin ƙasar daren yau, ya yi bincike ya gano ta ɓarauniyar hanya za'a shigo da su, dan haka Vir and guru su dakatar dasu, su kwace containers ɗin dan su san me aka ɗauko a ciki, sannan su kashe dikka direbonin containers ɗin, mutum ɗaya kawai zasu barshi da ransa, su mashi ɗaurin goro su dawo da shi zuwa ɗakin azabtar da mutanensu.
A kan haka suka tsai da matsaya yau, daga nan Aryan ya gudu wajen Seraphina. To mu koma kan labarin.
Wanka Seraphina ta yi, ta shirya cikin crazy jeans baki, da polo t-shirt fari tas, ta je Madam ta gyara mata gashi tana tambayarta a daren nan kwalliyar me haka?. Cike da soyayya ta ce. "Daddy ne zai zo, shi ya ce in shirya".
Madam ta ce. "To ki zo ki ci abinci kafin ya zo ɗin"......... Ta maƙe kafaɗa tare da cewa. "Kai mom daddy ya ce kada in ci komai sai ya zo"....... Madam tana murmushi ta ce. "To daddy's girl, ajira ya zo ya baki a baki ko?". Ta faɗa a lokacin da take kammala gyara mata gashin ta ɗaure suka koma kan gado. Juyowa ta yi ta rungumi Madam tana murmushi.
Daidai lokacin Suhana ta shigo cikin ɗakin, wani irin kallon rainin wayau ta yi wa Seraphina, haushin Seraph take ji dan ta fita kyau da komai. A walaƙance ta ce. "Ke tashi ki fita daga ɗakin nan zamu yi magana ya dangi".
Seraphina da bata barin ko ta kwana ta amsa da. "Ɗakinki na shiga ne?". Ta faɗa tana tamke fuska tamau, irin ba wasan nan....... "Rashin kunya zaki mun ne? Am i your mate?"........ Taɓe baki Seraphina ta yi, ta mata kallon uku goma kafin ta amsa da. "To sannu dabino sarkin shekaru".
A fusace Suhana ta ɗaga hannu zata mareta Madam ta yi gaggawar rike hannun nata, babu wasa a kan fuskanta ta ce. "Kada ki kuskura Suhana, kada ki yarda ki yi gigin ɗaura hannunki a jikinta"......…. Cike da takaici Suhana ta ce. "To kenan Aunty sai in tsaya wannan ƴar kucakar yarinyar tana faɗa mun magana?".
Kallon uku saura kwata Seraphina ta yi mata, bata sake tanka mata ba, dan kuwa tasan in dai batun duka ne to mutum ɗaya ne kawai zai daketa ta haɗiye ta yi shiru, shi ne kuma daddy Champion, bayan shi wlh ko Madam ta daketa ba tare da kwakkwarar dalili ba sai ta rama, dan ba'a haifota dan wani ya taɓa lafiyarta ba! Tana ji da kanta da kuma jikinta, she respected herself! So dariya ma Suhana ta bata wai zata dage.
Miƙewa ta yi ta sauƙo ƙasan gadon Madam, sumbata ta mannawa Madam a cheek game da cewa. "Than you mom, ina ga daddy ya dawo bari in je". Ta faɗa game da baiwa banza ajiyar Suhana. Madam ta saki hannun Suhana tana ta faman murmushi suka yi sallama.
Seraphina na fita Madam ta ce. "Baki da hankali ne zaki ce zaki ɗaura hannunki a jikinta? Me ta yi maki? Baki duba yanayin jikinta bane? Kina ɗaura hannunki a jikinta wlh sai kin yi nadama, dan kuwa ko taɓata kika yi jikinta na nuna alamar hakan, bare mari, tsab yatsunki zasu bayyana a kan fuskanta, kin san waye daddyn da take kiran nan kuwa? Kin san a kanta zai iya komai ko baki sani ba? Zai iya ɗaure dikka zuri'armu, dan haka ki bi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 88 Chapter of 95