Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su tura masu in suna son ci su ƙoshi, ga wahalar horo, ga rashin muhalli mai kyau, gabaɗaya barrack ɗin sai a hankali bare kuma ɓangaren wajen kwanan ƙananan sojoji, makamansu tsofaffi matattu, horon ma ba cikakken horo ake basu ba face azabtar da gangar jikinsu, meyasa komai ya banbanta? Ko kuɗin da ake baiwa sojojinsu ya banbanta, salarinsu ɗaya, but why allowance ɗinsu yake banbanta sosai? Meyasa danger allowance, ration allowance, operation bonus na sojojin kudancin ƙasa ya banbanta dana arewacin Avaris? Barrack na kudancin ƙasar ka kalli yadda su Nirash suka rayu a ciki, cikin gata da kulawa, wasu sashe har AC ne da su, wajen kwana mai kyau, sojoji su rayu da kwargo da samun kula, ga natsuwa da sanin aiki, suna samu horo matuƙa, amma barrack na arewacin Avaris komai a lalace, dubi irin gadon da su Nirash suke kwana a kai a nan, to dubi irin gadajen dake barikin arewacin ƙasar! Komai a lalace cikin wahala da ƙunci. Hankalina ya yi mugun tashi sosai bro, kuma a haka ƴan arewacin suke rayuwa?". Shiru Aryan ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Gudanci basa tsoron mutuwa! Basu yarda a takasu ba! Sun san ƴancin kansu! Ba dai a cikin mission na su Nirash uku a kudancin ƙasan ɗaya a arewaci bane? Ga jira lokacin a nan ne zaka gane menene dalilin dikka wannan banbanci"....... Cike da mamaki guru ya ce. "Me haɗin mission na su Leo da banbancin dake tsakanin Arewacin Avaris da kudancin ƙasar?". Ciro wayarsa Aryan yai tare da yin playing na voice ɗin Seraphina dake waya da Rimsha a yanzu kafin ya amsa. "A cikin wannan mission ɗin zaka gane ainahin gaskiya, a nan zaka fahimci daga ina matsalar arewacin ƙasar ta fara ta kuma samo asali, yanzu dai ba sun je yaki da ƴan ta'addan dake haurowa kudancin ƙasar suna samu mafaka ba? To ka jira su juya mission kan arewaci zaka gano komai, dalilin kenan dayasa Lion ya ce kada mu sanya baki a mission ɗin, dan akwai abin da yake dubawa a mission ɗin". Shiru guru yai yana nazarin kalaman Aryan, lallai kuwa yanzu ba zai gane komai ba, sai su Leo sun juya Mission a kan arewacin Avaris. Nima na ce a yanzu ba zaku gane komai ba, amma mu je zuwa zaku gane. Miƙewa Aryan ya yi tare da nufar kofar fita yana cigaba da sauraren su Seraphina, yaran nan sai shirin ALLAH, hira suke yi sosai kan SSO, Rimsha ma ta ce ai ita babbar fan ɗinsu ce, musamman Admiral wanda ni da ku readers muka san shi da Lion kuma Zayra'an, sun mutu a kan SSO yaran nan, sai bawa Seraphina labari Rimsha take yi kan ranar ma SSO sun yi live da jami'an Paris, ta bibiyi live ɗin, har da cewa zallar ilimi da jarumta ce kawai yake magana a wajen. Seraphina ta ce. "Ni dai bana banbantasu tin da kullum da fuskokinsu a rufe, kawai dai nasan ina son SSO gabaɗayansu".... Rimsha ta amsa da. "Nima bana banbantasu, kawai dai nasan su uku ne, kuma dik ina kaunarsu, kin san dama jami'ai irinsu basa nuna fuskokinsu ga duniya saboda sun fiye yin aikin sirri, shiyasa suke nufewa, dan suna shiga ko'ina yin aiki, idan al'umma ta shaida kamanninsu ai kinga akwai matsala ko?". Seraphina ta amsa da. "Haka ne, suna da hujja ɓoye kamanninsu wa duniya, amma ina fatan ganin face ɗin ko ɗaya daga cikinsu ne ko sau ɗaya a rayuwata"...... Dariya Rimsha ta yi kafin ta amsa da. "Baki da hankali my star lady, a ina zaki samu damar ganinsu? Ki dai cigaba da yi masu addu'ar ALLAH ya cigaba da karesu yana dafa masu a dik in da suke". My people wai na ce ya kuke tinanin Seraphina zata yi a ranar da zata gane cewa daddy Aryan ɗinta ne ɗaya daga cikin SSO? Ya Rimsha zata ji idan ta gane uncle Aryan ɗinsu SSO member ne? Ya zasu ji ranar? A gefe guda kuma sun tsani IRON FIST, kai akwai cakwakiya fa, ku dai mu je zuwa. Ba ƙaramin daɗin sauraran hiransu Aryan yake ji ba, sai ma idan Seraphina ta yi magana tana ɗan shagwaɓe muryan nan, dik rasa kansa yake yi, sai ya ji tamkar ba'a duniya yake ba, tsabar daɗin hirarsu da yake ji har ya fito daga hotel ɗin bai sani ba, yana ta tafiya kawai abinsa. Da Seraphina ta ce. "Rimsha do you know something?". Rimsha ta amsa da aa. Seraphina ta ce. "Ina jin daddyna a raina sosai, tin shekaran jiya bai zo wajena ba, ina kewansa sosai, and bana son in ce ya zo saboda mom ta ce in daina takura mashi da yawan cewa ya zo zai daina sona sosai, amma ina cikin damuwa sosai, shi kuma yaki zuwa ban san meyasa ba". A shagwaɓe sosai ta karisa maganar. Ai sai ga malam Aryan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman hair ɗinsa yana watsawa, yana jin wani irin nishaɗi na musamman, kai shi kansa ba zai iya faɗa maku a wace duniya yake ba, ga shi sai tafiya yake ta yi ba tare da yasan in da ya dosa ba....... Rimsha ta amsa mata da. "Kawai ki kirasa ki ce kina kewansa, ai tin shekaran jiya ne bai zo ba, kinga ko mom ɗin ce nasan in kika faɗa mata ba zata hanaki kiransa ba tin da an jima, kawai ki kirasa". Ta amsa mata cike da son sanin tarihin Seraphina, ta san dai Madam ta ce mata marainiya ce bata da iyaye, to waye wannan daddyn? Gara mom da take cewa Seraph ta faɗa mata Madam Rohisha ce, amma dik da haka tana son sanin tarihinta, amma ta gagara tambayarta. Da sauri Seraphina ta ce. "I remembered something Rimsha, kin san da cewa daddyna yana kama dake? Your eyes and lips iri ɗaya da nasa, kuma skin ɗinsa up white ne irin naki"....... Ai da jin wannan magana Aryan bai san time da ya dawo cikin hankalinsa ba, ɗan zare idanu yai tare da kara natsuwa yana sauraronsu. A ransa ya ce lallai kin cika jinin IRON FIST, na kara shaidawa jininmu ce ke, kaga yarinya da basira, tab!. Ita kuwa Rimsha ta ce. "Kai anya kuwa kin gansa da kyau? Ko dan kina kewata ne yasa kike yi wa kowa kallon kama dani?"....... Da sauri ta ce. "No Rimsha, for sure yana kama dake, kinga ɗan bakinsa? Like yours, sai ma idan yana magana, dimple ɗinku iri ɗaya, his big-big eyes, kai kuna kama sosai. Shiru Rimsha ta ɗan yi kafin ta ce. "Kai anya ba uncle Aryan bane to? Dan dik cikin uncles ɗina mun fi kama da shi, dani da shi and Yah Vash dik da Ammie muke kama, su uncle Faryan kuma da Abba suke kama"........ "In kuwa haka ne to ina ga shi ne, but zan ɗauka maki pic ɗinsa idan ya zo, sai in tura maki ki gani idan shi ne". Seraph ta faɗa cike da mamaki. Tsayawa jikin wata karanta Aryan yai tare da gyara nose mask ɗinsa yana mamakin yaran nan, watau Rimsha har ta samu damar kallon fuskansa tasan da waye yake kama ko? Dole ya kara taka mata birki daga zuwa kusa da shi, ita kuma Seraph yasan maganinta ne, wayar ma zai kwace ya huta da bala'in da suke son jefasa, ka ji yara, shi yanzu idan su Ammie suka san shi ne Champion na IRON FIST Ina zai sanya kansa wai?. Yayi nisa cikin tinani bai san time da suka yi ending na call ɗin ba, sai jinsu shiru ya yi, katse kiran ya yi yana ƙoƙarin tura wayar a aljihu kenan guru ya iso wajen yana faɗin. "What brought you here bro? Ka sani dogon walking". Sai a lokacin ya ɗago kai ya fara kallon hanya, yayi nisa da hotel nasu, lallai jin gulma tai daɗi. Ɗan shafa kansa ya yi zai yi magana kenan daga gefensu suka fara jiyo hayaniya da ihun jama'a. Kallon juna suka yi, sai kuma suka sake kallon wajen, a natse suka fara takawa a tare suka nufi wajen dan su duba menene. Suna yin kwana suka isko wata matsakaiciyar kasuwa a wajen. A bakin gate ɗin suka tsaya tare kallon juna. Guru ne ya ce. "I think something bad is happening inside"........ "What am I thinking kenan". Aryan ya faɗa. Magana suka yi da ido ta hanyar cewa su shiga su duba. A natse suka fara takawa izuwa ciki. Tin daga nesa suke hango jama'a a kwakkwance a ƙasa kamar ba lafiya ba, kafin su farga sai ganin wasu tsageru suka yi a tsakiyar kasuwar suna gilmawa izuwa cikin shaguna hannunsu rike da bindigu zasu kai su goma, dikkansu fuskokinsu nannaɗe da rawani, sai jajayen idanu zaka gani. Kallon juna suka sake yi, Aryan ya ce. "I think they are armed robbers"..... Guru ya amsa da. "Dama waɗan nan ai daga gani ba tambaya ƴan fashi da makami ne".......... A daidai wajen wani shago suka tsaya, shagon irin na uztazan nan ne masu sai da su dabino, zamzam, bakaruwa ta makka, jallabiyoyi da rawani dayawa. Masu shagon din sun kwanta a kasan tebur dake cikin shagon, sun natsu tsit saboda harbin bindigun da armed robbers ɗin suke yi. Kusan a tare suka miƙa hannu suka zari rawani ɗai-ɗai, dik da nose mask dake fuskokinsu hakan bai hana sun kara naɗe fuskokinsu da kyau ba, kai tsaye suka nufi in da armed robbers ɗin suke. Sai faman fashi suke yi suna kwashe kayan al'umma suna wani irin muzurai tamkar kwarto a gidan General na soja. Kai tsaye wajen wani gaton shago na atamfofi Aryan ya shiga. Shi kuma guru ya wuce gaba. Manyan armed robbers biyu ne a cikin shagon, ɗaya na rike da bindiga yana wani zazzare idanunsa, ɗayan kuma na ta faman kwasan kaya, ga masu dukiya bayin ALLAH suka kwance luff a ƙasa, suna ji suna gani za'a kwashe masu halak ɗinsu, guminsu saboda tsoron wannan shegiyar kurmar abar da bata da sabo kuma bata jin yaren kowa face na kisa watau bindiga. "Siiiiiiiiiitttttt". Aryab yai wa guy dake rike da bindigar. Da sauri ya juyo da jikinsa da bindigar, babu tausayi ya nufi harbin Aryan, bai san Champion namu na amana Champion ɗin ne da gaske ba. Wata lace dage rataye a sama saitin kansu Aryan ya jawo tare da rufewa guy ɗin idanu, sannan ya kama hannunsa ya huya bindigar, a lokacin ya ɗana kunamarta zai yi harbi, Aryan ya tayashi danna harbi kai tsaye ya fasa kan mutuminsu dake ɗebar kaya yana zubawa a bugu. Sake hannunsa ɗaya daga jikin bindigar mutum ya yi yana ƙoƙarin buɗe lace na fuskansa, Aryan bai bashi wani dama ba ya kai mashi wata bahaguwar naushi a ciki, kafin ya gane me aka yi mashi ma Aryan ya kwaci bindigar tare da saitasa, take ya tarwatsa mashi ƙwaƙwalwa, a tsarin IRON FIST basa kama masu laifi, kawai idan suka isa waje kashesu dik suke yi, basa sa tsammanin ɓata gari zasu shiryu, kai bama sa basu dama, abin da suka sani kawai dik wanda ya kashe a kashesa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar dasu, dan haka basu da lokacin ɓatawa wajen baiwa makasa damar ko zasu gyaru. Ko da sauran ƴan fashin suka ji karar harbin da Aryan yai basu wani damu ba, saboda suna harba bindiga sama ai dan firgita jama'ar kasuwar, so sun zaci sama mutanensu suka harba, sai suka cigaba da jidan kaya suna zubawa a buhu tamkar halaliyarsu. Waje Aryan ya fito rike da bindigar, kowa ya gansa sai ya zaci armed robbers ɗin ne, dan ya nannaɗe fuska da rawani, cikinsu kai tsaye ya shiga, kafin ma ya isa guru ya kashe mutum 4, kafin su farga an kashe masu bindigun 10 dikka saura masu kwasan kaya su zuba a buhu. Nan suka farga da cewa su Aryan fa ba mutanen ba ne su bane, nan suka fara ƙoƙarin kokawa da su. Ganin haka yasa su Aryan suka jingine bindigun hannunsu, marasa bindigun ma sun kai su 10, dik sun fito tsakar kasuwan suka yi wa su Aryan zobe. Tini su Aryan suka ajiye bindigu suka hau gwada masu jami'an SSO suke, kuma IRON FIST renon AZURE suke. Dik wanda suka yi wa duka ɗaya sai ya baje a ƙasa, baya sake tashi, dama dik kayan maye ya cinye dik wani quality nasu. A daidai wannan lokaci jiniyar motar ƴan'sanda ya fara karaɗe ko'ina a arear alamar suna zuwa. Cikin zafin nama su Aryan suka ɗauki bindigunsu, dik suka harbe armed robbers dake baje a ƙasar, basu bar ko mutum ɗaya da rai ba, sannan suka yasar da bindigun suka gudu ta tsakanin shaguna, suka haye katangar kasuwar suka dira ta baya. Ba zasu yarda a gansu ba ai, kada ku manta jami'an SSO suke, suka kuskura suka haɗu da ƴan'sandar nan to za'a samu matsala, dan ƴan'sansa zasu ce su buɗe fuskokinsu, su kuma ba zasu yarda ba, idan aka matsa zasu haɗa da ƴan'sandan dik su kashe ne, so gara su gudu kawai. Basu zame ko'ina ba sai hotel ɗinsu, suna shiga suka hau haɗa kayansu, barin AVARIS a yau ya kamasu, idan ba haka ba sai an san SSO suna ƙasar AVARIS, dan dik waɗan dake kasuwar sun ga kalar fatarsu ai, zasu faɗa, kuma ma dole za'a nemesu tin da sun kashe almost 20 armed robbers, kunga kuwa nemansu wajibi ne. Sun yi sa'a time da suka koma hotel ɗin Lion ya farka, yana zaune tsakiyar bed rike da waya yana ƙoƙarin kiransu kenan sai gasu nan. Ba tare da ɓata lokaci ba suka sanar mashi ga abin da suka aikata, harara ya dallawa Champion ba tare da ya yi magana ba. Guru ne ya ce. "Bro no time". Shi ma hararar ya samu babu alamar Lion ɗin zai yi magana, har suka gama shiryawa bai kulasu ba, sai da guru ya haye saman bed ɗin ya jawo hannunsa yana faɗin su je, sannan ne ya ce. "I can't go anywhere"....... Aryan dake ƙoƙarin jan luggage box ɗinsu ne ya dallawa Lion harara kafin ya ce. "Do you heard what you said kuwa?". Shiru babu alamar zai sake tanka masu, sai ma gyarawa da ya yi ya kwanta abinsa. Cikin fushi Aryan ya yi tsalle ya dira a tsakiyar gadon, dan in sun biyewa Lion wlh tsab zai ja masu aiki, dan wani lokaci Lion iskancinsa yawa ne da ita, sai ka kai zuciya nesa zama da shi. Hannun rigar jikinsa Aryan ya naɗe tare da sunkuyawa ya cicciɓi Lion sama sai saman shoulder ɗinsa yana faɗin. "Ba zan iya juran iskancinka na wannan lokacin ba"...... Guru da iskanci shi kuma ya yi saurin damke hannayen Lion dukka biyu ya dawo da su ta bayan wuyan Aryan ya rike gam wai dan ma kada ya ce zai kwaci kansa, da hannu ɗaya Aryan ya rike Lion, ɗayan hannunsa kuma ya ja luggage box ɗinsu suka fito parlo. A tsakiyar parlo Aryan ya sauke Lion tare da cewa. "Lets go"...... Wani irin kallo ya dallah masu da waɗan nan shaggun sharp eyes ɗin nasa masu rikitarwa kafin ya juya zai koma ciki, watau idan kana neman ɗan duniya ka samu Lion ka gama, tin da sun nuna a ƙage suke su bar hotel ɗin shi ne sai ya kuntata masu, ga shi ba zasu iya matsawa ko nan da can su barshi ba, iskanci kala-kala cike da cikinsa guy ɗin nan. Ai cikin zafa Champion ya damko wannan tuntun jekar kitson nasa yana faɗin. "Baka isa ba"...... Da sauri guru ya tare gabansa yana faɗin. "Bro please". Wani irin kallo Lion ya dallah mashi kafin can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "Give me a way to pass"...... Jan tuntun gashin nasa da karfi Aryan ya yi har sai da Lion yai baya, dawowa ta gabansa Aryan ɗin ya yi, ya zamana su ukun suna fuskantar juna. Aryan ne ya ce. " Likes comments and share fisabilillah. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1🔥 2025-11-25🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________24 & 25 Wani irin kallo Lion ya dallah mashi kafin can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "Give me a way to pass"...... Jan tuntun gashin nasa da karfi Aryan ya yi har sai da Lion yai baya, dawowa ta gabansa Aryan ɗin ya yi, ya zamana su ukun suna fuskantar juna. Aryan ne ya ce. "Lion please don't play with us here, kaga kai ka iya ɗaukar kasada na wuce misali, to wannan zai yi affecting namu sosai ne, zai ɓata mana mission ɗinmu". Hararansa Lion yai kafin ya ce. "I think zaka cigaba da nuna ka isa dani ne". Yana ɗaure fuska ya faɗa. Aryan zai amsa guru yai saurin rigasa da cewa. "Ina babu wannan magana, yanzu dai let's go". Ya yi saurin faɗar hakan ne saboda yasan Aryan in ya buɗe baki zai lalata komai ne. Kun san me ne? Lion ya tsani a nuna mashi iko, shi ma Aryan baya yarda a nuna mashi kamar bai isa ba. Yanzu da Aryan ya ce Lion ya tashi su tafi sai Lion ɗin ya ga kamar Aryan ya nuna mashi iko shi ne yaki tashi, shi kuma Aryan ya lallaɓashi yana ganin kamar ai ya bashi girma ne, idan suna gida yadda kuka san maguna haka suke da faɗa, amma idan suka je office girmama juna suke yi, dan rank ɗinsu daban-daban. Da kyar suka shawo kansa, sannan ya yarda suka bar hotel ɗin. Amma basu bar Avaris a lokacin ba, sai can yamma jirgin da suka yi booking ya tashi, sun dai bar hotel ɗin ne suka yi nisa suka kama wani. By 4 na yamma jirginsu ya ɗaga zuwa US. To safe journey our IRON FIST KUMA SSO. --------------------------🔥 DEATH OR LIFE TEAM.🔥 A bakin wani katafaren dajin dake kudu maso yamma na AVARIS jirginsu ya tsaya, dikkansu using parachute suka yi wajen sauƙa, dan jirgin bata sauƙa ba, mazan ne suka fara sauƙa domin daji ne. A natse one by one suka diro ƙasa. Dikkansu idan ka kallin fuskokinsu aikin ne kawai a ransu, babu wasa a tattare da su, musamman Leo, Noor, Zaynish, Arya, Unays, Juraiz and V, waɗan nan su daban ne, burinsu su kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinsa ba a AZURE, a tarihin manyan da suka gabata a AZURE kafin su zo, sun karanta akwai wasu team masu suna F-L-F da su ne suka kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba, amma sun bar AZURE yanzu, kai AZURE da kanta ta basu sunan F-L-F, su biyar ne a team ɗin, labarinsu sai da ya karaɗe duniya, tin daga kansu kuma ba'a sake wasu jami'an da suka yi rabinsu ba, to kudirin su Leo su bugesu, ya zamana sunan team ɗinsu DEATH OR LIFE ya zamana shi ne a sama da kowani suna. Bayan sun kammala dirowa dikkansu, jirginsu ya tashi sama ya barsu a wannan ƙungurmin dajin. Gyara rucksack na bayansu suka yi, Leo ne ya fara wucewa gaba, ko tsoro babu ya kutsa cikin dajin nan. Bayan su 12 nan kada ku manta an haɗasu da ƙananan sojoji dake bar 1, an ƙara masu 12 soldiers. Zaynish ne ya rufawa Leo baya cikin takun jarumta, while sauran sojijin zuƙatansu ya matuƙar kaɗawa da wannan ƙungurmin daji, amma ganin Leo ya yi gaba yasa suka ɗan samu kwarin gwiwa. Arya ce ta rufawa Zaynish baya tana riko igiyar rucksack ɗinta da kyau, ga wannan sheggun tauraran takalmar nasu da ko maciji suka taka ya taku kenan. Sojoji 8 ne suka rufawa Leo baya, saura suka tsaya suna kallon Noor, ba yadda za'ayi su tafi su barshi tin da shi ne assistant ɗin Leo, dole su bashi tsaro ko da su zasu mutu. Shi kuwa ya tsaya kallon V da ta ɗan turo baki tana ƙoƙarin sassauta ɗaurin da ta yi wa igiyar rucksack ɗinta, ya tamke mata ciki sosai. Bayan ta ɗan sukurkuta ne ta ɗago kai, haɗa idanu suka yi, one side smilling ya ɗan sake mata kafin ya miƙa mata hannu. Da sauri ta miƙo mashi, kamata yai suka nufi bayansu Leo, da sauri su Angelina suka rufa masu baya, sannan sauran sojijin bar 1 ɗin suka rufa masu baya....... Su leo sun yi nisa a tafiya, sai da suka ɗaga kafa kafin suka cin masu, sun yi tafiyar good 30 mins kafin su isosu, nan ma a bakin wani ruwa suka iskosu a tsaye, ruwa ne mai ɗan yawa sosai kamar kogi, amma ba ruwan gudu sosai bane, yana tsaye haka, ga wasu dogayen bishiyoyi bakake a wajen, daga gefe akwai duwatsu da tsaunika. Ɗan kewaye Leo ya fara yi a wajen yana dubawa, da sauri sojoji 5 suka rufa mashi baya dan bashi tsaro. Shi kuwa Noor ɗan matse hannun V a cikin nasa yai, hakan yasa ta ɗago eyes ɗinta a kansa. Can ƙasan maƙoshi ya ce. "Bani rucksack ɗinki in rike maki"...... Kamar yasan ta ɗan gaji, da sauri ta zame hannunta daga nasa. Zuba mata idanu yai, dama ya fahimci ta gaji ne yasa ya ce ta kawo ya haɗa da nasa ya rike masu. Ganin tana ta faman kwancewa ne yasa ya matsa dab ita, bata ankara ba sai jin hannunsa ta yi a saman cikin nata, yana kallon cikin eyes ɗinta ya fara kwance mata jakar, ai wani irin romantic mood V ta faɗa, while shi ya jima da faɗawa tin da ya riko hannunta a bakin dajin. Wani irin harara Arya ta dallah masu tare da wucewa ta fara kewaye wajen ita ma. Kwance mata jakar ya yi, da kansa ya sauke mata shi ƙasa daga bayanta, sai ya ratayosa a hannun damansa saman shoulder ɗinsa, ya zura hannayensa a cikin aljihu yana kallon yadda ruwan kogin yake motsawa a hankali-hankali, ga dabobin daji marasa haɗari suna zuwa shan ruwa a wajen, iska na kaɗa bishiyoyin dake wajen, yanayin weather wajen akwai daɗi. A daidai lokacin Leo ya dawo wajen, kusan a tare suka dawo da Arya, ba tare da Leo ya kalleta ba ya ce. "Ki duba mana network na wannan waje akwai karfi ne?". Ya faɗa tare da matsawa ɗan gefe ya fara kwance igiyoyin rucksack ɗinsa shi ma, ya sauƙe ƙasa, dan wajen tai mashi, yana fatan su samu network mai kyau a wajen, dan su Arya su yi aikinsu a natse, su tura drones na camera dan gano ainahin in da miyagun suke. Sauke rucksack ɗinta Arya tai tana dallah mashi harara ta ƙasan ido, a ranta ta ce ba dan ka zo a oganmu ba da ka gane baka da wayau, amma yanzu ma nasan maganinka, da Arya kake yi, sai na wahalar da kai ta gefen aikina. Tana fito da laptop ɗinta tana tinanin kalar wahalar da Leo da zata yi a dajin nan, zata yi ta bashi wrong information sai ya ji azaba. Kunna laptop ɗin nata ta yi ta fara duba network na drone ɗinsu. Sun kuwa yi sa'a, dubawar farko suka samu network mai karfi sosai a wajen, ɗagowa tai ta kalli Leo tare da cewa. "There is a strong network here"....... Kai kawai ya jinjina tare da ɗago da eyes ɗinsa a kan sojojin dake wajen. "Ku kafa mana tantina a nan". Daga haka bai sake magana ba, ya fara fito da important kayan da zai buƙata a yanzu. Ya miƙa masu nasa tantin, ya nuna masu in da yake buƙatar su kafa mashi, ɗan nesa dasu kenan. Da sauri suka karɓa cikin girmamawa. Miƙewa yai ya nufi wajen tsaunikan da wani

Chapter 34 of 95