Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daji, gaba daji baya daji, waje mai sunkuru da cikowar itatuwa, waje ne da ba zaka taɓa yarda halittar ɗan adam tana rayuwa a wajen ba, akwai alamar ban tsoro a wajen, ga wasu manyan tsaunuka da koguna a wajen. Noor ne ya ce. "Idan muka yi duba da tsuntsayen dake shawagi a sararin samaniyar kewayen hakan na nufin akwai tabkeken teku a wajen! Idan kuwa haka ne lallai ba shakka wannan teku dake kusa damu ta ratsa ta wajen".. Jinjina kai Leo ya yi alamar haka ne, in a cool way sosai ya ce. "Idan kuwa akwai taku a wajen to tabbas akwai wutar lantarki a waje, dik yadda aka yi akwai igiyoyin wuta sosai a wajen wanda su ne suka haka drone ɗin nan wucewa, lallai muna buƙatar sanin menene a wajen cikin gaggawa, dan ga dikkan alamu gagarumin abu ne a wajen"....... Jinjina kai Zaynish da Noor suka yi, su kuwa matan gabansu ne ya yi mummunar faɗuwa jin batun da mazan ke tattaunawa. Zaynish ya ce. "Idan muka yi duba da hayakin dake tashi ba hayaki ne na yau da kullum ba, lallai wannan hayaki gagarumin abu ne ake ƙonawa, ku yi duba da yadda yake tashi sama, a maimakon ya yi sama gabaɗaya, sai yana watsewa a cikin dajin, alamar abin da ake ƙonawa yana ɗauke da guba". Kai suka jinjina alamar haka, ba shakka a zancen Zaynish..... Jama'a ku tafawa renon AZURE, sun san aiki!. Leo ne ya ce. "Zaynish, Noor, ku kira Vash ina da magana daku a ɗaki"...... Da okey sir suka amsa, dawo da kallonsa a kan Arya ya yi. "Keep watching the place carefully, komai ƙanƙantar motsi ki sanar dani". Yana kai karshe ya miƙe daga kanta, cikin zafa ya nufi waje. Bayansa ta bi da kallo, bata iya zare idanunta ba har sai da Zaynish ya zo wucewa, sannan ta ɗauke kai. Sunkuyowa kanta Noor ya yi, cikin zola ya ce. "Brother ɗina yai maki kyau ne?". Ɗago da kallonta a kansa ta yi, zata mashi tsiwa sai taga yai mata mugun kwarjini, haɗiye maganarta ta yi, ta ɗan yi ƙasa da ido. Ɗagowa yai zai nufi waje raunatacciyar muryar V ta katse shi da cewa. "My Romeo". Ai ƙara ɗaure fuska ya yi, ya fice da sauri ba tare da ya kalli in da take ba. Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana ɗan shessheƙa, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita. Ita kuwa Arya ta cigaba da kallon aikinta, Manassa da Angelina suka zauna yin gulmar Leo da Zaynish, ba su yi gulmar Noor ba saboda kada V ta sauke haushi a kansu. A yayin da a waje kuma ruwan sama na zuba tamkar da bakin kwarya, while sojojinsu guda 34 ciff suna tsaye cikin ruwan kewaye da tantunansu dan bada tsaro, sun sanya army waterproof jacket. To mu leƙa sashen jigon labarinmu, mu ɗan duba su sister Maya sai mu sake dawowa, watakila kafin mu dawo sun gano wani motsi, su kuma lovers Romeo and Juliet kila zasu shirya. -------------------------🔥 WS-HOSPITAL.🔥 Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!.... Bayan sun kammala hiran, sai suka tashi, suka shiga baiwa jariran madara wanda nurses suke haɗa masu suna ajiyewa kowani baby a jikin bed ɗinsa. Suna baiwa yaran suna murmushi suna cigaba da baiwa junansu shawarin yadda zasu kara sace zuciyoyin 3D. A ɗayan ɓangaren kuma, 3D tsaye a cikin SECTION E, a ɗakin Drugs factory ɗinsu. Dr James tsaye gaban wasu injuna, yana sanye da kayan ƙariya, yau nose mask dake face ɗinsu irin manyan nan ne masu ɗauke da oxygen, hakan zai sanya ba zasu shaƙi numfashin Drugs factory ɗin ba, wannan oxygen ya wadatar da su. Dr Kamal ne ya ɗauko wannan jini dake bokiti, wanda suka sanya a freezer ta daskarar masu da shi, tin ɗazun dama suka ajiyesa a waje mai ɗumi, ya narke, a cikin wani tangameme faranti mai zurfi ya zuba jinin, wani karfe dake tsakiyar farantin ya fara jujjuyawa yana kwaɓa jinin, engine ne wajen. Almost 10 mins, wannan inji yana juya jinin jaririn, sai Dr James ya ɗauko wani ainahin sinadari a cikin kwalba wanda ake cewa collagen peptides ya zuba a cikin jinin jaririn. Collagen peptides sinadari ne dake ƙarfafa fata, hana wrinkles, da inganta laushin fata. Ya barshi kamar 10 mins injin na mixing ɗinsa, sannan ya sake ɗauko ainahin sinadarin retinoic acid ya zuba a ciki, manyan kwalabe ne sosai fa yake ɗaukowa, sinadarin retinoic acid yana sabunta fatar jiki, rage wrinkles, da hana tsufa. Bayan ya zuba injin ta yi mixing like 10 mins sai ya sake ɗauko, hyaluronic acid shi ma ya zuba a ciki. Hyaluronic acid ainadarin ne dake hana bushewar fata, yana sa fata ta yi taushi da ƙyalli tamkar glass, bayan ya zuba dakamar 10 mins shima sai ya sake ɗauko kwalbar nicotinamide mononucleotide ya zuba a ciki. nicotinamide mononucleotide sinadari ne dake sabunta kwayoyin halitta, watau cells da kuma kashe alamun tsufa. After 10 mins inji na mixing, suka haɗe da juna da jinin jaririn, sai ya sake ɗauko resveratrol ya zuba a ciki. resveratrol ana samun shi ne a cikin inabi, yana da tasiri wajen hana tsufa da kuma kare fata daga lalacewa, yana da matuƙar amfani a aikin 3D. Baya ga shi sai ya ɗauko coenzyme ya sake juyewa a ciki. coenzyme yana da matukar amfani wajen inganta kuzari a cikin jiki da kuma hana lalacewar fata, bayan shi ya ɗauko kwalbar epidermal growth factor ya zuba a ciki. Epidermal growth factor sinadarin ne dake sabunta fata a gaggauce cikin ƙanƙanin lokaci ya warkar da raunuka da dik wani tabo, ki koma tamkar ƴar tsana, babu tabo ko kaɗan a jikinki. Ya sake ɗauko stem cells watau ƙwayoyin halitta na asali ya zuba a ciki, in jin dai tana nan kunne tana mixing komai ta haɗesu su zame abu guda. stem cells yana sabunta fata da gyaran jiki gabaɗaya, daga shi sai ya ɗauko alpha lipoic acid ya sake zubawa, tsabar yadda injin ke mixing har wani hayaki-hayaki ne yake tashi daga cikin farantin, ga sinadaran da ake ta daddalawa a ciki. To alpha lipoic acid shi ma sinadarin ne dake rage kumburin fata da hana tsufa. Daga shi sai ya ɗauko babbansu kuma na ƙarshensu watau glutathione ya zuba. Wannan sinadarin yana sa fata tayi haske sosai, yana cire wrinkles, komai yawan tamu-tamun tsufarki zai yi fata-fata da shi ya mai da skin ɗinki very smooth tamkar yarinyar ƴar 13 years, yana da karfi sosai, a take yake cire tamu-tamun, sannan ya fi sauran dik sabonta fata da hana shi tsufa sosai. Yauwa kafin mu wuce gaba, dama na ce maku zan yi maku bayanin kan sinadaran dake cikin jinin jariri dan ku samu ƙarin ilmi kuma ku fahimta da kyau, dan haka kafin mu ce zuwa gaba ku ji me 3D zasu aikata, bari in baku wannan bayani. A jinin jariri akwai sinadarin hematopoietic stem cells kamar da na faɗa a haba, to hematopoietic stem cells sinadarai ne dake samar da sabbin ƙwayoyin jini red & white blood cells. Ana amfani da su wajen warkar da cututtuka kamar ciwon sankara, sannan suna wanke tsoffin jini. Na biyu a baya na ce a jinin jariri akwai sinadarin mesenchymal stem cells su kuma waɗannan ƙwayoyin halitta suna taimakawa wajen sabunta fata, ƙashi, da sauran sassan jiki, dik tsufarka zaka zama sabon matashi mai ji da karfi da lafiya tamkar ɗan yaro under age. Na uku a jinin jariri akwai erythropoietin, shi kuma sinadarin da ke taimakawa wajen samar da jan jini red blood cells, kun san jan jini daban yake, masu shi daban suke, da lafiya da karfi. Na huɗu akwai fetal hemoglobin. Wannan nau'in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da ƙarfin ɗaukar iskar oxygen fiye da na manya, idan ka yi amfani da maganin 3D hmmmm, karfi da lafiya kam a dai yi shiru kawai. Na biyar akwai alpha fetoprotein, wannan sinadari ne da ake samu a cikin jinin jariri, wanda ke sabonta garkuwar jiki, idan kin tsufa garkuwar jikinki ta raunata ta yadda kowani cuta zai iya yi maki shigar farad ɗaya, to wannan sinadari na sabonta garkuwar jiki, ki zama tamkar yara. Na shidda akwai Interleukins & growth factors, waɗannan sinadarai ne dake ƙarfafa garkuwar jiki da kuma sabunta ƙwayoyin halitta. To su ne a jinin ɗan jariri wanda sai sun razana jaririn suke samo jikinsa ya sakarwa jininsa waɗan nan sinadaran ta yadda in sun marƙaɗa shi sun matso jinin zai zo ɗauke da sinadaran!. To mu cigaba da bibiyar 3D yau mu ga abin da ya turewa buzu naɗi, amma kafin nan ina da tambaya! Mun gama jin na jini, to shi kuma ɓargon ƙashin fa? Me suke yi dashi? A gaskiya shi fitina da balainsa ya fi na jini, a hankali zamu iso garesa, zaku ji komai, haɗarinsa yawa ne da shi, shiyasa na ware mashi lokaci na musamman. Bayan kamar 30 mins da kammala zuba sinadaran injin na mixing Dr Mark ya tsayar da injin, komai ya haɗe sosai. Dr Kamal ya ɗauko color ɗin da suke buƙata, white suka sanyawa haɗin, take da injin ya sake mixing komai ya zama fari tas tamkar farin fenti, ba zaku taɓa cewa akwai jini a ciki ba, Dr James ya ɗauko fm, sinadarin dake kashe ƙarnin jini da dik warin wasu sinadaran, ya zuba a ciki, suka ɗauko wani powder mai kamshin inabi da sauran kayan itatuwa suka zuba a ciki. Injin ya sake mixing sosai kafin su sake kash injin. Sannan suka danna wani madanni, gabaɗaya farantin ya yi sama, ya juye maganin cikin wani abu tamkar ball, daga nan suka kunna wasu injuna dake gaba guda biyu kafin su kunna makunnin wannan ball ɗin. Nan take ball ɗin ya fara motsawa yana sama ya ɗan yi ƙasa. Matsawa kaɗan suna yi izuwa karshen injinan suka tsaya, a wajen akwai wani katon baff a bakin karshen injunan. Sun rungumo hannayensu a saman kirji, idan suna aiki ba'a magana, babu wanda ya ce da wani ƙala, kowannensu yana lissafin kan yadda zasu ƙara inganta aikin nasu ne. After 30 mins da tsayuwarsu a wajen sai ga bakin injin ya buɗe, you can't believe what i saw my people. Ya ALLAH, a jere drugs suka fara zubowa a cikin wannan baff ɗin, yadda kuka ga ake arranging magunguna a cikin saches ɗinsu, haka waɗan nan magunguna suka fito daga cikin injin, ko kasheki za'ayi idan ba'a gabanki aka haɗa wannan magani ba ba zaki taɓa cewa akwai jini da waɗan nan sinadaran a ciki ba, pure magunguna ne a ciki farare ƙal..... Kin taɓa jin maganin hana tsufa? mai da tsohuwa yarinya. To waɗan nan magunguna ba komai bane face magungunan mai da tsohuwa yarinya, maganin gyaran jiki, skin ɗinki ya zama irin na waɗan can na kwana, maganin glowing, lightning, glass skin da sauransu, zai sabonta maki halitta cikin ƙanƙanin lokaci. Shiyasa basa karɓar sperm da eggs na munana sai kyawawan mutane, dan dik wanda ya sha maganin ya zama yaro, ya kuma yi kyau sosai, shiyasa dik nurses dake cikin wannan asibitin suke da mugun kyau, dan sperm and eggs na kyawawan gaske ake ɗaukowa! Fatan yanzu kun gane dalilin da yasa dole sai na kyawawa!. To ina matan littafin nan masu shan maganin gyaran jiki? Masu shan maganin ƙarin haske, su skin care manya! To koma dai me ga abin da kike sha nan, mu munga komai, munga dik abin da 3D suke haɗawa, dan haka mu bamu a wannan layin na su glowing, ko ya kuka ce mutanen kirki?..... Watau ni kaina ina kiɗimewa idan na tina abin da suke haɗawa da wannan ɓargon ƙashin jariran fa, mun dai ji na jini, ko ya na ɓargo da kuma shi kansa garin ƙashin da tsoƙa ɗika yake? Yanzu shikenan jarirai guda biyar ɗin nan sun tafi har abada? Haka zasu cigaba da salwantar da rayuwan jarirai? Suna niƙasu tamkar masara! Tamkar ba rai bane da su? Wannan wace iriyar balai ce, rai fa, su ɗauka su saka cikin inji ya niƙa ya fitar masu da jini daban, garin tsoka da ƙashi daban, ɓargon cikin ƙashi daban, rai fa, ran ma na jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, la haula wala ƙuwata illah billah, allahumma ajirni fi musibatin, wannan musifa ina zamu tsaya da ita? Ba dole jama'a su dinga ganin tashin hankali da musifu ba, ace ƴan ɗan adam akewa wannan ɗibar albarka, ya ALLAH. Bayan magungunan sun gama zuba ne 3D dikka suka ɗebo ruwa a boket duka zuba cikin farantin da ya haɗa maganin da farko, sannan suka kunnasa, farantin ya yi sama, ruwan ya zuba cikin ball, daga nan suka sake tsayawa a gefe. After 30 mins sai ga magunguna da basu kai ka farko ba sun fara fitowa, watau marasa karfi sosai aka yi yanzu da ɗaurayar inji. Waɗan nan marasa karfi sosai ɗin sai kun sha sosai yake biyan buƙata, kuma shi ne mai arha daidai talakawa!. A baff daban marasa karfin suka zuba, dan da na farko ya gama fitowa sun janye baff ɗin gefe, sai suka sanya wani. Bayan komai ya gama fita sai suka haɗa karfi suka cicciɓi baff ɗin magani mai karfin suka fito dashi wajen ɗakin, suka koma suka ɗauko mara karfin suna fito da shi waje. (Ni na rasa ma wani irin suna zan baiwa wannan ɗaki saboda musifar dake cikinsa, kai ya ALLAH. To bari dai mu bashi sunan ɗakin niƙa jariran, tin da babban abin da suke yi a ciki kenan. A wajen ɗakin niƙa jariran suka dire baff dikka biyu ɗin, magunguan yana dayawa, ga baff ɗin da girma, sai da suka yi da gaske suka iya ɗauka. Suna ajiyewa Dr Mark ya kira guards madaka karti su uku suka zo suka ɗauki baff ɗin, amma kafin su ƙirasu sai da suka rufe kofar ɗakin niƙa jariran da matakan tsaronsu na wutar lantarki, babu wani mahaluki da yake shiga masu wannan ɗaki, su kaɗai suke shiga, saboda su kaɗai suka san ɓarnar da suke yi a ciki. Bayan guards ɗin suka bi izuwa wani katafaren ɗaki mai girman gaske, kwalayen magunguna ne cike a cikin ɗakin, a nan guards ɗin suka sauƙe baff ɗin dikka biyu, akwai ma'aikata mutum 10 a ciki, aikinsu kawai shi ne shirya magungunan a cikin kwalaye ƙanana kafin a shiryasu cikin manyan cartons. Saman haɗaɗɗun chairs da aka tanada masu suka zauna, suka zuba idanu suna kallon yadda ma'aikatan nan ke aiki da jikinsu wajen ganin sun shirya komai yadda yakamata a kan lokaci. Suna sanya magunguna marasa karfi a kwali daban, mai launin white and ratsin ash, su muma magunguna masu karfi kwalinsu farine tas. Sai around 10 na dare 3D suka je suka yi wanka, suka shirya cikin shiga iri ɗaya, white pj's, basu ko ci abinci ba suka dawo ɗakin aiki. A lokacin ma'aikatan sun shirya cartons 20 na masu karfi, 10 na marasa karfi, kowani carton kuma yana ɗaukar kwali ƙanana na maganin guda 25. Umarni Dr James ya baiwa guards uku da su fitar masu da cartons 30 ɗin dikka da aka shirya waje. Cikin ƙanƙanin lokacin suka fitar da shi suka ajiye a tsakiyar SECTION E ɗin, sannan suka koma bakin aikinsu. Wayansa Dr James ya ɗauka, password na tsaron lantarki dake jikin wani kofa dake fuskantarsu ya cire. Yana cire password ɗin shocking na wajen ya mutu, tangameme kofar karfen dake wajen ya wangale kansa. Da kansu 3D suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna shigarwa cikin wannan ɗakin. Cikin ƙasa da 10 mins suka kammala, a lokacin 12 na dare ya yi. Bayan sun kammala shigar da komai kaf, sai suka rufe kansu a cikin ɗakin, suna rufewa lantarkin wajen ta kawo, shocking ya dawo, dik wanda yakuskura ya zo jikin kofar bushewa zai yi, dan wasu irin mahaukatan shocking ne a wajen. Wuta na kawowa ɗakin naga wani haɗaɗɗen katafaren ɗaki ne, ga sofa set, AC, TV, tamkar office na wani hamshaƙin muƙamin gwamnati, komai na cikin ɗaki fari ne tas, an zuba maƙudan kuɗaɗɗe ba karya, ya ALLAH. Dr Kamal and Dr Mark ne suka wuce suka yi zamansu a saman sofas ɗin. Shi kuwa Dr James wayarsa ya shiga latsawa kamar na 5 mins, sai ga pop dake ɗakin ta gefen hagu ya fara motsawa, jim kaɗan wajen ya buɗe tamkar kofa, sai ga tsani an juro da shi ciki. Miƙewa su Dr Mark suka yi, suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna haura tsanin, kowannensu kwali bibbiyu yake ɗauka su haye tsanin. Suna hayewa hudawa suka yi cikin wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa, tamkar store ne, empty yake, a nan suke shirya magungunan. A cikin ɗakin wani babban likita dake sanya cikin kayan aikinsa ne a tsaye, ya rungume hannayensa a kirji yana kallonsu suna shigo da drugs ɗin. Wannan likitan shi ya zuro masu tsanin, shi Dr James ya turawa saƙon sun iso, shi ne ya buɗe wajen ya sako masu tsani dan su haura. Wai kun san tsadar magungunan kuwa? To ko shugaban ƙasa ba na kowani ƙasa ne yake iya jurar sayen maganin dik bayan wata ɗaya yana sha ba, suna da tsada, dan kwali ɗaya ƙarami mai ɗauke da drugs ƴaƴa kwara 6 kawai ya kai 1M, in dai kana son mai da kanka yaro matashi kuwa dole ka dinga sha dik tsadarsa. Amma ai kunga sun yi marasa karfi sosai watau ɗaurayar inji, waɗan nan basu da tsada sosai, carton ɗaya baya wuce 100k, kunga a karton kuma kwali 25 ne a ciki, zai kama kowani kwali 4k kenan, kunga shi da sauƙi a kan masu karfi. Marasa karfin ne ƴan iyayi yaran malan Shehu suke kashe kansu da wahalar sai sun saya su gyara jiki, ayi glowing da lightning, ayi ta zuba kuɗi, ba'a ci ba a tsaya dole sai an gyara skin, bayan ga kayan gyara da Manzon ALLAH ya faɗa, wanda littafan musulunci suka koyar, dik bai maku ba. Idan baki san kayan gyaran da Manzon ALLAH ya faɗa, littafan musulunci suka koyar ba In Sha ALLAH a karshen littafin nan na yi alkawarin zan rubuta!. My people you can't believe what I saw there. Bayan sun kammala shirya drugs ɗin, Dr Kamal and Dr Mark suka tsaya tattaunawa da wannan babban likita dake tsayen, shi kuma Dr James ya nufi kofar da zata fidda shi daga ɗakin. Ya ilahi, yana buɗe kofar kun san me a wajen?. Katafaren asibiti ne na al'umma a tsakiyar birnin Avaris, babban asibitin gwamnatin na ƙasar ne! In baku fahimta bari in maku gwari-gwari. Kenan WS-HOSPITAL a tsakiyar al'umma take ba tare da kowa ya sani ba, sai dai tana underground ne, nasan dayawanku suna tinanin a dokar daji WS-HOSPITAL take, aikuwa gata a tsakiyar gari, a garin ma a babban birnin Eldoria, kasar da aka haifi daddynsu Lion, bugu da ƙari ƙarƙashin asibitin gwamnatin ƙasar, dik wannan haɗuwa da tsayuwar WS-HOSPITAL a ƙarƙashin ƙasa yake. Jama'a WS sun zarce yacce kuke tinani, manyan kai ne da kamasu abu ne dake kamar wuya, ai tin da kuma ji Lion da kansa ya ce kamasu abu ne mai balain wahala, daga nan zaku game ba ƙananan kai bane, sun zarce tinaninku, ku duba yadda suka shinfiɗa gini a ƙarƙashin ƙasa tamkar ba za'a mutu ba fisabilillahi, suke baiwa ƙarƙashin ƙasa wutar lantarki kusan gabaɗaya na birnin Avaris, shiyasa a ƙasar ake wahalar rashin wuta, to ashe ga in da wutar take tafiya, ba'a iya ɗauke wuta a WS-HOSPITAL ko na second ɗaya, saboda abubuwan da suke sanyawa a freezers irinsu sperm, eggs, blood da sauransu. Dole wuta lantarki tai yawa a wajen, ga nan jama'ar Avaris kullum cikin ƙorafin babu wuta, da an kawo da an ɗauke, kuma Avaris tana daga cikin ƙasashen da ta fi tsaranta karfin wutar lantarki, suna da uranium, amma ace kullum suna kukan rashin wuta, ashe da in da ake kai wutan a bar jama'a a gantale. Har fa hanyar yadda motoci zasu iya shiga underground ɗin a wannan gini an shinfiɗata, sai dai motocin in zasu shiga sai sun yi tafiya mai nisa zuwa cikin daji, a can aka yi wani waje da aka haɗa, aka yi shinfiɗaɗiyar titi har cikin WS-HOSPITAL, ta nan Dr Mark yake fito da motar jarirai idan an saya a wani waje, hmmmm babu wanda zai taɓa expecting akwai hanyar zuwa ga 3D palace a cikin wannan asibiti ta gwamnati...... Hmmmmm, shiyasa a wannan asibitin ba ko'ina ake barin mutane su shiga ba, wannan ma iya abin da kuka gani yanzu ne, ainahin labarin yana book 2 jama'a, ALLAH yasa kanmu ya iya ɗaukar wasu abubuwa, kai ya ALLAH ƙazantar dake duniyar nan, ALLAH ne kaɗai zai iya maganin komai! Ni dai yanzu addu'a ta ɗaya, ALLAH ka bamu cikawa da kalmar shahada da ni da mutanena na kirki, In Sha ALLAH wlh mutuwar shahada zamu yi my people!. Amma ku daga ganin iya hospital na World system kun san ba mutane ne da zasu kamu ta sauƙi ba, basu fito ba sai da suka shirya, kai akwai abubuwa idan muka natsa cikin labarin nan, baku ha komai ba. Cikin asibitin Dr James ya shiga, kewaye ya fara yi yana duba yadda ɗakunan da majinyata suke yake, babu abin da zaku ɗaga a asibitin nan ku kirasa mai kyau sosai, komai a gurɓace a lalace da yake government hospital ne, amma ku duba irin aljannar duniyar da suka shinfiɗa a ƙarƙashin ƙasa dan biyar buƙatar kansu kawai, ya ALLAH gwamnatin Avarsi ku ji tsoron ALLAH, ita duniya dai wuni muka zo yi, kowa zai koma ga ALLAH, tabbas zaku tsaya ne a gaban ALLAH da abubuwan da kuka shuka a duniya, ku tuba tin kuna da sauran lokaci. Ya jima yana kewaye cikin asibitin nan, wani sashe ma idan ya shiga yawu yake tofarwa saboda lalacewar asibitin, daga karshe ya koma wannan private room ɗin, suka koma cikin WS-HOSPITAL ɗinsu, dan abin da ya kawosu kawowa kenan maganin, daga wannan asibitin kuma za'a fitar da magungunar ne zuwa ƙasashen ketare, manyan dattawan alhazawa da masu mulki ake sayarwa magungunan. Can na tina lokacin da su oooo suke cewa basu son bakaken fata, wai fararen fata suke so, su jikinsu baya tsufa, bakaken fatanmu su yi ta tada hankalinsu suna damuwa a kan su suna tsufa! Su yi ta sha'awar jikinsu ooo, wai yana da kyau basa tsufa, my sister zauna yadda ALLAH ya ajiyeki shi ne ya fi maki alkhairi, baki san me yake behind rashin tsufar nan ba! MAGANIN MAI DA TSOHUWA YARINYA! MAGANIN HANA TSUFA! HMMMMMMM. Saura mu ji me suke yi da ɓargon ƙashin da kuma shi kansa garin ƙashi da tsokar jariran kuma!. Kai tsaye SECTION D suka wuce, Dr Mark ya koma room ɗinsa ya kwanta tin da shi babu ruwansa da love. To mu ɗan koma baya kaɗan a kan su Zinta kafin mu cigaba. Bayan sun kammala baiwa babys ɗin nan madara mai ɗumi, zama suka yi a gefen gado, sister Zinta ta buga uban tagumi tamkar mai tinanin wani abin. Taɓata sister Maya ta yi tare da cewa. "Tinanin me kike yi?". Nisawa ta ɗan yi. "Darling nike tinani, sister ina jin tamkar bashi da lafiya, anya ba zan fita in je in duba shi ba kuwa? Zan binciko shi a gidan nan, nasan wani ɗakin suka kaisa"........ Shiru sis Maya ta yi, sai kuma da yake soyayyar ƙanin nasu ya rufe masu idanu sai ta ce. "Mu je mu duba shi, na tabbata yana kusa da mu". Kai sister Zinta ta jinjina, sai kuma ta ce. "Sister kina ganin da gaske alluran magani suka yi mashi?". .... Kai tsaye Maya ta girgiza kai alamar a'a kafin ta amsa da. "Wlh ba magani bane, cuta ce, baki ga yanayin kalar ruwan ba? Kin lura akwai chemicals da muka haɗa a cikin cutar da yake ikirarin maganin ne?". Jinjina kai sister Zinta ta yi. "Tabbas cuta ce, amma koma menene zan ɗaukosa, zan gwadasa, in dai cuta ce tabbas zan yi mashi magani, ai mu muka haɗa chemicals ɗin, dik kuma mun

Chapter 64 of 95