sauran abin da ya rayu a gidan dan ya rama alkhairin mahaifiyarta a garesa, ta sadaukar da ranta a cetansa, yana kwance a gadon asibiti ya turosu.
Shi ne suka zo suka ɗauketa, sun sameta sume a cikin Jacuzzin, amma hayakin wutar tai mata illah, ga kuma wutar ta kakkama dik wasu robobi a cikin toilet ɗin ta cinye, ko jami'an da suka zo basu san tana ciki ba saboda wannan rufeta da ya yi...... To kun ji abin da ya faru! Yanzu mu koma kan labarinmu!.
Ta jima zaune a wajen tana shan kukanta, tana ganinsa ya sauko ƙasa, ya wuce kitchen ya sauke ruwan da ya ɗaura a pot, ya sanya rariyar tea ya tace ruwan a cup, sannan ya ɗauka ya koma sama ba tare da ya kalli in da take ba. Ganin ba zai kulata bane yasa ta miƙe ta koma cikin room ɗinta cike da kunci, tana son sanin ina mammy ɗinta, meyasa aka kawota wannan irin dream house da take mafarki kullum! Suna da arziki sosai, amma CRYSTAL PALACE ba dik kai ba, sai ta zama ƴar kauye a nan.
Saman bed ɗinta ta koma ta kwanta tana cigaba da kukanta babu mai rarrashinta, ga shi bauɗaɗɗen nata ya yi sama abinsa, yana zaune a balcony yana shan tea ɗin da ya dafa cikin kwanciyar hankali da natsuwa abinsa. Bayan ya kammala ya umarci robot dake aiki a gidan da su haɗawa yarinyar abinci, su tabbatar ta ci, sannan su bata magani kamar yadda yake a tsare, kuma su yi mata wanka, yana gama basu bayani ya ɗauki wani tail coat ya sanya a jikinsa bayan ya yi wanka ya cire waɗan can, ya fita ya bar gidan, ita kaɗai a dik wannan girman gidan kamar wata mayya, ba uwa, ba uba, ba kawa, ba aboki, babu kowa sai robot, wannan ma kawai ai tashin hankali, ga shi baƙon waje.
Haka robot ɗin nan suka hau aikinsu, tamkar mutane, suka shirya komai suka kai mata, maza ne su biyu. Tana kuka suka iskota. A saman table suka ajiye kayan abinci, ɗaya ya taka zuwa in da take, da hannu ɗaya ya ɗagota, bai direta a ko'ina ba sai a saman sofar dake kusa table ɗin.
Tana ta faman faɗin. "I don't want, please let me go"..... Ina babu wanda ya kulata, dan su ance su tabbatar sun bata abinci, dan haka a baki suka fara tura mata dole, abin da umarni suke karɓa, in kuma suka karɓa sai sun cika ko mutuwa ake yi.
Da taga babu sarki sai ALLAH sai ta hakura ta dinga karɓar abinci a natse kawai, ba sai an mata ɗure ba. Sosai ta ci kafin ta ce ta ƙoshi. Sai da suka tabbatar, sannan suka ɗauko magungunar, shi ma a baki suka bata ta sha, sannan ɗaya ya ɗauketa zuwa toilet, dan har da wanka aka ce su yi mata, tana cewa bata so, amma ina, ko a jikinsu, suka haɗa ruwan wanka. Dik tinaninta mutane ne shiyasa take ce masu bata so.
Tana ji tana gani yai mata zindir, ya jefata cikin ruwan katafaren glass Jacuzzi tamkar wata kayan wanki. Hannu yasa ya wanketa tas. Ai yau taga ikon ALLAH, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Mammy ɗinta, amma ina bata jinta.
Dawo da ita ɗakin suka yi bayan sun nannaɗeta cikin towel, a kan gado suka jefata kafin su kwashi kayan abinci su fice, sun gama aikinsu kenan. Fashewa da sabon kuka ta yi, ta kifa kanta da gwiwowinta tare da jawo bargo ta rufe tsiraicinta. Kyakkyawan ash hair ɗinta sai ɗigar ruwa yake yi.
Tin sautin kukanta na fita, har ya daina fita, daga karshe barci mai nauyi ne ya ɗauketa a wajen, bata san lokacin da ta kwanta kudundune a cikin bargon ba, ta hau barci, ta ci kuka ta ƙoshi ja'ira. To kun ji halin da Seraph ƴar Dr take a ciki, mu haɗa kayanmu mu koma Barrack.
Note, Seraph shekarunta 10 a duniya yanzu, yarinya ce sosai.
-------------------------🔥
GIDA SOJA!. AFTER ONE MONTH.
A wannan wara ɗayan dik horon da aka yi masu a farko-farko ne ake ta maimaita masu dan ya bi jikinsu da kyau, ba'a ɗaura sabon horo ba, tin suna iya mantawa har wannan horo na farko ya ratsa jikinsu sosai. Shiyasa na tsallake tin da ba zan yi ta rubuta maimaicin horo ba!.
A yau Monday watansu guda kenan a GIDAN SOJA, a yau zasu fara shiga horo sabo kashi na biyu.
Kamar kullum karfe 5:30 na asuba, bayan sun yi sallar asuba, dik sun hallara a wannan fili, a yau dai Noor ya fito, dan za su shiga sabon horo, a wata guda da suka wucen nan dik kullum sai Captain ya tashesa da duka, amma yau da yake za'a shiga sabon babi ya daure ya taso.
Sun kasance a cikin layi kamar kullum. Cikin zafin nama Captain ya tako, ya iskosu a wajen. Saman stage ya haye tare da ɗan yin gyaran murya. Da sauri suka haɗe natsuwatsu tare da buga kafa, suka sara mashi. Jinnina kai ya yi kafin ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya.
Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, united as one, well never fall. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, a thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, our oath is strong, we'll see it through. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".
Suna kai karshe ya ce. "Kamar yadda kuka sani ne, a yau zamu sabonta maku horo, zamu matsar dashi izuwa matakin gaba, ina fatan kun shirya?". Ya kai karshe da alamar tambaya. Wani irin kamewa suka yi alamar sun shirya ba tare da magana ba.
Rarraba idanunsa a kansu ya ɗan yi kafin ya ce. "A yau zaku fara ne da endurance run for 10km". Babbar magana, gudu fa ba tafiya ba, na 10Km da matsala. Dayawa daga cikinsu sun ɗan ɗauke wuta, amma ganin babu fuskan wasa yasa suka daure.
Maryan Captain ne ya katsesu da cewa. "Lokacinku ya fara daga yanzu, kada ku manta lokacinku yana kirgawa ne! So attention".
Wani irin tsaki Noor ya ja tare da rike kai, har ga ALLAH ya gaji, ba zai iya jura ba fa. Ganin matasan sun fara gudu sun bar shi a wajen ne yasa yai gaggawar bin bayansu da ɗan gudunsa, kada a barsa a baya.
Gudu na tsawon kilomita goma ba tare da tsayawa ba. Dik wanda ya yi baya, sai ya sake farawa daga farko. Babbar magana, kuma kun san dik wanda ya yi baya sai ya faro ɗin nan ne, babu tausayi.
Haba haka suka zage dantse suka fara gudu babu wasa. Sai dai bayan kamar minti 30, gwiwowinsu sun fara raunata, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dan ma wai a wata ɗayan can sun ta maimaita horo sun ɗan samu karfi da kwari ne, da sai yaya kenan?.
Noor da ya tabbatar da gaske idan ya yi baya zai sake komawa daga farko, kuma ko mutuwa yake yi ba zasu yafe mashi ba, kilomita goma ba biyu kamar ta baya ba, yaushe zai koma baya ya sake dawowa, ai sai ya zage, yasa dikkan karfinsa wajen gudu. Da yaga kamar ba zai iya bama sai ya kwarara zuciyansa tare da yin shahada ya kama hannun Leo.
Ko kaɗan Leo bai kalli in da yake ba, amma da ya fahimci Noor baya son faɗuwa ne yasa ya kama hannunsa sai ya juyar da hannun nasa ya rike Noor ɗin da karfi suka fara gudu sosai a tare, hakan ya yi mugun karawa Noor kwarin gwiwa ba kaɗan ba.
Lamarin da ya yi mugun baiwa su Zaysh mamaki kenan, how comes Leo zai kama Noor? Kai kamar a mafarki?. Shi kuwa Leo ganin Noor ya dage sosai ne yasa ya kara kankame hannun nasa.
Abin da ba'a taɓa ba wai Noor ya zo na farko, sai yau shi da Leo su ne farkon isa wajen, tsalle ya dinga yi yana murna tamkar wani karamin yaro, kamar ma bai gaji ba fa, dik kuma daɗin Leo ya taimaka mashi ne yasa bai ji wahalar gudun ba. Shi kuwa Leo robar ruwan da aka ajiye masu a wajen ya ɗauko tare da ɓalle bakin ɗaya, tin da ya kafa a ɗan bakinsa bai zare ba sai da ya sanye tas, ya yi jifa da robar, sannan ya sake ɗauko wani, ya ɓalle ya sha rabi, zai rufe rabin Noor ya karɓa ya kafa a bakinsa, tas ya shanye, sai murmushi yake yi ya zo na ɗaya, a ransa yau ya ɗanɗani irin farincikin da ake ji a dik lokacin da aka yi nasara, sai ya ji yana sha'awar ya yi ta yin nasara a rayuwansa. Da bashi da wani tunani a gaba a rayuwansa, amma dalilin wannan abin Leo yasa ya fara tinanin cigabansa.
One by one matasan dik suka iso wajen. Wasu sun iso a tare da Captain, wasu a bayansa. Yau babu wanda bai iso a kan lokacin ba, bayin ALLAH sun fara saba horon ne. Captain bai bari sun huta ba, yana isowa ya ce maza su shirya su kama hanya, ya nuna masu wani hanya a wajen, ya ce su je.
Ba musu suka kama hanya, da sauri Noor ya bi bayan Leo, a kusa da shi ya tsaya, dik in Leo ya cire kafa a wajen shi kuma zai sanya. A haka suka isa wajen wani katafaren yashi mai kama da ruwa, irin yashi mai mugun laushi dake lumar da abubuwan nan ne.
Waro idanu suka yi suna kallon wajen cike da mamaki. Muryan Captain ne ya katse masu kallon nasu da cewa. Zaku rarrafa daga farkon yashin nan, ku yi iyo a cikinsa ku fita ta other side ɗin. Zazzare idanu suka yi, gabaɗaya horonsu ya canza fa, yanzu dik girman yashin nan zasu yi iyo a ciki? Kai, lallai yau gwiwowinsu zasu cire, da matsala gaskiya.
Suna can suna tunanin mafita Captain ya fara kirga masu lokaci, ga shi ya ce mintina 10 kawai garesu, wanda bai fito a 10 mins ba zai faro. Cikin zafin nama suka faffaɗa, dayawansu sun ji sabon wahala, dan a tunaninsu karamin aiki ne, sai da suka faɗa suka ji lumewa ƙasa suke yi, suna ƙoƙarin ɗagowa amma ƙasar na sake yin ƙasa da su.
Still Noor yana kusa da Leo. Sai dai bai fargaba ya ga Leo ɗin ya fara yi mashi nisa, hakan yasa ya kara zafin nama ya matsa kusa da shi. Da Leo ya ga haka sai ya kama hannunsa da kansa, suka fara iyo a tare, yadda kuka san a cikin teku suke........ Note kowani horo da nufin yinsa da kuma dalilin, ba in da ba'a turasu kama masu laifi, dan haka dole gwiwar kafafu da hannu su yi kwari!.
A wannan karon ma Leo, Noor, Unays, Zaynash ne suka yi farko-farkon fitowa. Ya ilahi suna fitowa, wani irin daɗi da Noor ya ji, bai san lokacin da ya daka tsalle ya rungumi Leo yana murnushi ba. Da karfi ya ce. "Thank you so much brother, I really love you".
Haka kawai Leo ya tsinci kansa da tsananin farinciki ganin yadda Noor yake murmushi saboda shi. Ganin Leo bai amsa shi bane yasa ya sake shi yana kara faɗaɗa murmushinsa. A daidai lokacin su Vash suka fito. Cike da farinciki Noor ya ce. "Brothers na shiga sahun ƴan farko".
Zuba mashi idanu Vash, Unays, Leo and Zaysh suka yi, suna ta mamaki yadda yake murya. Shi kuwa yau ya gane watau zuwa na ɗaya fa duniya ne, akwai mugun daɗi, kai kanka a farinciki na musamman zaka tsinci kanka.
Shi kansa Captain farinciki ne ta lulluɓe zuciyansa, sai ya guduri niyar faɗawa Leo ya ja Noor a jiki tin da idan suna tare yana zagewa ya yi nasara, dan suna son ya yi nasara. Da wannan tunani a ransa ya haɗa kan waɗan da suka yi nasara suka nufi wata hanya, waɗan da ba su nasara ba kuma ya kyalesu tare da sauran sojojin dake wajen kan su mayar da su su sake!.
Wani katafaren fili aka kaisu a yau ma, sai ya raba su team by team, bari mu ɗauki team room number 1 and room 2 mu yi bayani a kansu. Captain ya yi gyaran murya tare da cewa. "Room 1 kune a matsayin zakwakuran sojoji kun zo kama manya ƴan'taadda a filin daga, team room 2 act like gangster now, room 1 ku kama room 2 ba tare da kun kashesu ba, ku gwada dabarar yaki mu gani".
Shiru suka yi suna tunanin ai ba'a koya masu wannan horon ba. Tamkar Captain ya gane me suke tinani sai ya ce. "Ba'a yi maku practical a kan abin da ba'a koya maku ba, a cikin horon da kuka yi akwai wannan, ku fara zaku fahimta".
Shiru suka sake yi, basu taɓa sanin dik wani rarrafe ko lankwashe-lankwashe da ake sanyasu wani nau'i ne na dabarar yaki ba, su sun ɗauka kawai dan jikinsu ya yi kwari su yi karfi ne, shiyasa suke ganin ai ba'a koya masu ba.
Filin yana da maɓoya sosai ta yadda gane mutun abu ne mai wahala, akwai tankuna da drones na tsofaffin bayan motocin yaki. Captain ne ya ce. "Room 2 you have two run now, room 1 ku kuma ku yi shirin kai wa gangsters farmaki".
Room 2 ne suka fara kallon juna, to su da ba ƴan ta'adda ba ya za'ayi su iya acting kamar su fisabillilahi? Basu san an koya masu salon ƴan ta'addan bama, dan wani lokaci kafin ka kama ɗan ta'adda sai ka maida kanka irinsa shiyasa ake koya masu irin salonsu.
Wasu empty pistol gun Captain ya baiwa su Leo a matsayinsu na waɗan da suka zo kama gangster's.
Sauran sojojin kuma ya ce dik su koma baya, bari room 1 And 2 su gwada aiki.
Baya su Leo suka juya har sai da ƴan room ɗin su Unays suka ɓuya, sannan ne Captain ya ce su juyo. A natse ya ce. "A nan wajen zaku gwada kaifin ƙwaƙwalwa mu gani, ku kama ƴan uwanku ba tare da bindiga ba, kuma kada ku bari su dakeku, sai dai ku ku dakesu, amma ban da dukan da zasu ji ciwo".
Kallon juna suka ɗan yi, Zaysh ne ya ce. "Brothers let's walk slowly kamar yadda muke tafiya a daji yayin fitar da kanmu, muna tafiya a hankali dan kada mu bugu da itace ko wani dutse".
Kallon juna suka ɗan yi, sai Leo ya wuce gaba, bayansa suka biyo, hannu ya ɗaga masu wanda yasa suka tsaya, da hannu ya yi masu alama da su rabu ba tare da ya juyo da kallonsa a kansu ba. Baya Captain ya koma tare da rungumo hannaye a kirji, shi da sauran sojojin suka zuba masu ido.
Sanɗo suka fara yi rirrike da bindigun da aka basu. Rabuwa suka yi kowa ya kama laluɓe, a yau kowa kaifin kwakwalwarsa ta kwacesa. A yayin da suke zuwa su kuma su Unays suna kara ɓoyewa ne. A hankali Leo yake tafiya har ya shiga bayan wasu matattun motocin yaki da wasu kwantaunars, a nan ya ɗan tsaya shiru tamkar mai tinanin wani abin, sai kuma ya ɗan rintse idanunsa tare da kasa kunne sosai.
Lokaci guda ya waro idanunsa waje, cikin zafa ya juya gefensa tare da sanyawa Unays dake laɓe bayan wata mota bindiga a kai, da numfashin Unays ya yi amfani wajen gane yana wajen, kun tuna horon da aka basu a daji na su dogara da numfashin juna? Ashe ta shiga kansu da kyau.
Yana sanyawa Unays bindiga ya yi zafin namar damkoshi ta wuya-wuya suka fito harabar wajen, daidai lokacin Zaysh ya fito da nasa ya kama shi ma. Wani irin dogon ajiyar zuciya Captain ya sauke alamar ya ji daɗi, saura Noor da Vash dake laluɓe. Kun san da cewa Noor yana da bala'in kaifin ƙwaƙwalwa, ga shi dai baya son horon, amma wlh ya naɗi komai a kansa. Dan haka shi ma da numfashinsa yai amfani wajen kama shi, yana fitowa shi ma Vash ya fito ya kama nasa.
A tsakiyar wajen suka tsai tsaya kusa da Leo. Da ido Captain yai amfani wajen cewa room 2 su kwaci kansu. Ai suna gane karatun suka juya suna fuskantar su Leo gaba da gaba, kafin Leo yai wani motsi Unays ya ɗaga kafa yai ball da bindigar da Leo ya nuna shi da shi, sama bindigar ta yi, tana dawowa Unays ya caɓeta tare da nuna Leo ɗin da ita yana wani irin murmushi wai irin ya yi nasarar nan.
Ɗan buɗe idanunsa Leo ya yi yana ɗan mamaki, dan shi bai zaci su Unays zasu kwaci kansu ba. Sai kuma ya ɗan fiske. Unays kuma mamaki yake yi yadda aka yi kafafunsa suka yi sama sosai, watau horon rarrafen nan tasa kafafuwansu sun kara kwari matuƙa, lallai kuwa gaskiyar Captain ne an koya masu dabarun yaki a cikin wannan horo su ne basu ankara ba.
Matsar da bindigar saitin forehead ɗin Leo Unays ya yi, yana cigaba da wani irin murmushi. Cikin zafa Leo ya ɗan kauce tare da yin ƙasa kaɗan, ya kama hannun Unays mai rike da bindigar, ya murɗe hannun baya, ai bai san time da ya saki bindigar ya fasa kara ba. Kasa ta faɗi.
A maimakon Leo ya ɗauka, sai ya barta a wajen, suka hau gwabzawa da hannu, while su Noor ma suna fafatawa. Cikin ƙasa da minti biyar room 1 suka lallasa room 2 suka yi laushi. Dik sun kai abokan faɗar nasu ƙasa saura Noor da suke ta fafatawa, shi gaskiya bashi da karfi, amma ya dage don ya zo na farko, ai ya ɗanɗani daɗin zuwa na farko yanzu baya wasa.
Tsaitsayawa su Leo suka yi suna mayar da numfashi, while su Unays suna baje a ƙasa suna nishi sama-sama. Captain ne ya ce. "Nan fagen yaki ne, kuna iya taimakawa ɗan room naku, dan ko a daji ne zaku taimaka mashi daga abokan gaba".
Ai tin bai gama rufe maki ba Zaynash da Vash suka yi kan su Noor, take suka kai guy ɗin ƙasa. Hannu suka dunkule suka bugi na juna, amma ban da Leo dake tsaye a gefe yana rike da waist ɗinsa, tafawa suka sake yi cike da murnan sun yi nasara. Shi ma Captain murna ya yi sosai, dan bai san meyasa team nasu Leo suke mugun burgesa ba, musamman Leo and Noor, yana jinsu har cikin ransa.
Hutawa ya basu dama su yi na kamar mintuna biyar, aka basu ruwan sha kafin su wuce su koma dan yin lunch and sallah, dan time ya yi.
Kai tsaye masallaci musulman cikinsu suka wuce. Bayan sun yi sallah suka haɗu a dining hall ɗinsu. Kamar yadda suka saba cin abinci suka ci, suka ƙoshi nak, sannan aka basu hutun 30 mins, a nan suka yi zaman hira, shi kuma Leo ya fito da wannan book ɗin ya fara karantawa. A kusa da shi Noor ya zauna, yanzu ya daina zama kusa da su Zaysh.
Dik abin da Leo yake yi yana kallonsa, so yake ya dinga kwaikwayonsa saboda rayuwar Leo ɗin tana burgesa, amma bai yi magana ba har 30 mins ta cika, a nan aka kwashesu zuwa wajen gwajin makamai. A yau handling heavy weapons aka sanyasu, manyan bindigu aka basu su rike, aka ɗeba masu lokaci, nasan dayawanku baku san cewa bindiga tana da nauyi ba ko? To nau yi gareta, musamman idan akwai bullets a cikinta, shegen nauyi ne da ita, ai ko da iya rike bindigunsu aka barku ba karamin aiki bane, amma haka suke wuni dakon kayansu bayin ALLAH.
A yanzu good 30 mins suka ɗauka wajen rike bindigun nan, daga nan aka ware 30 mins again aka koya masu magana da idanu ga junansu, idan sun shiga wata matsala ga dabarun da zasu isarwa da juna saƙo ba sai sun yi magana kowa ya jisu ba, Captain ya basu kalaman sirri ga junansu, wanda dik in da suke idan suka ambaci wannan kalma an san so ne, sannan kowani room ya basu kalaman sirrin gane juna ko a cikin duhu ne.
Yau sai da suka yi sallar al'asar sannan suka bufi class ɗinsu. Shi ma yau sabbin makamai za'a koya masu, sun natsu tsit suna rike da notebook and pen. Cike da tsantsar jarunta Captain ya shigo ɗauke da katuwar littafin makaman nasu.
A saman table ya ajiye littafin kafin ya juya ya kallesu da kyau. Sai ya juya ya fara rubutu a board ɗin, yau ya koya masu yadda bindigun suke, wajen bullet, yadda ake goge bindigar da dik wata sirrin bindiga. Wannan ɓangaren ba zan rubuta maku shi dallah-dallah ba, dan ban san iya ina rubutuna zai tsaya ba, akwai ɓata gari, ba ta yadda za'ayi in fitar da sirrin komai! Hakan na kamar cin amanar ƙasa ne! Dan haka ita bindiga sirri ce, kawai dai yau Captain ya yi masu darasi kan dik wata sirri na bindiga, ya bage masu komai!.
Awa uku tsu suka ɗauka suna karatu, dan yau babban aiki ne, kuma kasancewar sun yi wannan dogon karatun yasa karfe biyar yau suka tashi daga horo, Captain ya ce wannan abin da aka koya masu yau yana buƙatar dogon nazari da natsuwa dan ya shiga kansu, saboda a wannan gaɓa ne idan suka yi kuskure kaɗan bindigar kan iya ja masu matsala har ta yi kisan kai, dan haka su kula sosai.
Dan haka karfe 5 suka koma rooms ɗinsu, basu sake fita ba sai lokacin sallah musulman cikinsu suka fito suka nufi masallaci, basu dawo ɗaki ba sai da suka yi sallar isha'i, suka ci abinci, sannan suka dawo. Wanka suka yi, kowannensu ya yi shirin kwanciya, sannan suka ciro wayoyinsu suka hau kiran gida, yau har da Zaynash, ya fito da wayansa a gabansu bai ji kunya ba, ya kira Ummie ya haɗata da su Noor suka gaisa. Still dai Leo bai yi masu magana ba, suma basu yi gigin kai mashi waya ba.
Noor ya dinga murna yana faɗawa daddynsa yau ya yi kokari ya zo na ɗaya, shi ma daddy murna ya dinga yi. Sosai suka sha hira, daga nan ya kira Aunty's ɗinsa mata su uku, Luna, Lusi, Lisa, hira suka dinga yi, ya dinga yi masu kukan ya yi kewarsu, ashe dama su suka kara shagwaɓa shi suka mai da shi na mata, suma kukan kewansa suka dinga yi, wai baya nan yanzu ba wanda suke yi wa tausa. Shagwaɓa ya dinga zuba masu suna biye mashi.
Ai idanu su Zaysh suka zuba suna kallonsa cike da mamaki, wai kato da shi yana abu kamar mata, sai ma da yake magana da su Aunty Luna, wlh zaku ɗauka macece take magana, har murya, ya canza voice ya koma sak su, cike da yanga. Dik abin da suke yi Leo yana jinsu amma bai tanka ba.
Wai waye NOOR. Mu ɗan ji waye shi kaɗan. Ya fito ne daga babban family, sune mamallakan STARS BODY LUSH, Companyn da ya fito na farko a duniya, mahaifinsa yana da wasu mahaukatan kuramen kuɗi, su shidda ne a family ɗinsu sai, daddynsu, Lisa, Luna, Lusi, sai Uncle ɗinsu ƙanin daddynsu wanda shi ma babban mutum ne, Noor bashi da mahaifiya, ta rasu a lokacin da take nakudansa, daga karshe aiki aka yi aka cirosa, bai sha nonon uwa ba sai madara, yana ɗaya daga cikin abin da ya kara mai da shi haka, ga cutar tsoron dake damunsa.
Akwai abin da ya faru da mahaifiyarsa a lokacin da take da cikinsa ne, wanda wannan firgici yasa nakuda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 95