ya tashin mata, tashin hankalin yasa zuciyarta ta buga bata haihu ba ta mutu, shi ne abin ya taɓa Noor. Su Lusi su suka renesa har ya girma, mahaifinsa yana mutuwar son ya haifi ɗa namiji wanda zai gajesa, ko bayan ransa zai tsaya ya kula da ƴan uwansa da kuma dukiyansu, amma sai ALLAH ya bashi ƴaƴa mata, a karshe ya samu namiji, ya yi matuƙar murna na samun Noor, sun renesa cikin gata da kulawar da ko kuda basu bari ya taɓa shi in suna nan!. Magajin billions of dollars ne nan.
Sai dai a lokacin da ya fara girma suka fahimci yana da tsananin tsoro, dan ko irin wasan nan da suke yi na razana mutum in suka yi mashi suma yake yi, daddynsa ya shiga tsananin tashin hankali, daga nan ya fara yawo da shi kasashe dan neman mashi lafiya, Amma ina sauki taki samuwa, daga karshe uncle ɗinsa ya bada shawarar a shigar da shi hukumar soja, idan ya kasance cikin maza zai samu jarumta.
Da farko daddynsa yaki, ya ce shi ba zai iya ganin ɗansa a wahala ba, sai daga baya da suka ga yana girma abin yana kara karuwa sosai, harta maganarsa ta koma ta mata, shi da ake son ya zana tsayayyen namiji da zai kula da dukiya, shi ne ya kare a mata maza ai kunga ba zaman lafiya, nan fa daddynsa ya aminta da a kaisa gidan soja mafi horon wahala.
Uncle ɗinsa ya nemo, a nan ya zaƙulo AZURE, take aka yi applying. Cikin ikon ALLAH, da yake kuma suna da abin hannu, ya samu. Ko da za'a kawosa nan ya sha kukan rabuwa da ƴan uwansa mata, suka dinga cewa babu mai yi masu parkin gashin kansu ya kitsa masu jelar, dan shi yake yi masu dama, na ce maku dik wani abin da ya shafi mata ya iya.
A takaice Noor maraya ne, babu uwa, bai sha nonon uwa ba, ga ciwon tsoro, ga shi cikin mata ya girma, ai ko daga nan zaku san Noor ya yi namijin kokari ma, rana tsaka ya tsinci kansa a wannan wahala! Ya jure gaskiya. Labarinsa a taƙaice kenan, saura bayani zaku ji a gaba. Me yasami mahaifiyarsa har ta firgita nakuda ya tashin mata unexpected? Wani irin tashin hankali ne yasa zuciyarta bugawa kafin ta haihu?.
--------------------🔥
Sun jima suna waya da Auntys ɗinsa kafin su yi sallama, ya ajiye wayar ya kwanta shiru yana tinani, da yanzu a gida yake yana kwance tsakaninsu, suna mammatsa mashi jiki cike da so da kauna.
Zuciyansa cike da wannan tinani barci ta yi awon gaba da shi. Shiru room ɗin ya yi alamar dik sun yi barci, sai Leo da ya miƙe ya nufi toilet. Alwala ya ɗauro ya dawo kan dadduma, nafilfili ya zo ya yi tare da addu'oi, sai around 1 sannan ya kwanta.
Washegari kamar kullum haka ta kasance masu. In takaice maku sai da suka jera kwanaki biyar suna sake maimaicin horo, suka sake karanta sirrin bindigar nan da kyau, tin ranar Monday suna abu ɗaya har zuwa ranar Friday. Yau gajeran lokaci ne, karfe 2 suke tashi a horo su je su huta.
A yau kuma Captain ya ce zasu motsa zuwa matakin horo na gaba, dan haka sai suka farka da wuri, karfe 5:30 ta yi masu a hall da suke haɗuwa kafin su fara training. Izuwa yanzu dik wata wahala ta bi jikinsu, basa gajiya sosai, kuma basa wani nauyin barci, harta Noor yanzu jikinsa dan dole ta fara karɓar horo, musamman da yana kasancewa kusa da Leo, yana samun kwarin gwiwa.
A saman stage Captain ya tsaya, ya sanyasu rera taken gidan soja, bayan sun kammala ne ya kwashesu zuwa gym na barrack ɗin. Da yake yau ce ranarsu ta farko, sai ya ce.
"A yau zaku yi 200 push-up, 100 sit-ups, 80 burpees, 30 squats da kaya a baya, dik wanda ya kasa kammalawa a cikin mintuna 20, sai ya sake farawa daga farko". Sai ya rabasu team by team best on yadda suke 4-4 a ɗaki.
Kun san meyasa yanzu yake rabasu team-team? Dan ya lura idan ya rabasu ya sanya masu kamar gasa suna zagewa, babu wanda yake ɗaukar last, har Noor dagewa yake yi, kun san abu da gasa takan sa mutun ya yi har over acting ma.
Dan haka bayan ya rabasu team-team, sai ya ce. "Dik wanda ɗan team nasu ya yi karshen gamawa, to dinka team ɗin zasu sake farawa ne daga farko, team da suka yi karshe kuma, zasu yi frog jump 500 feets". Babbar magana.
Ai su Leo dik kai kallonsu a kan Noor suka yi, while shi ma su yake kallo, bawan ALLAH tin da yake bai taɓa push-up, ta ya za'ayi yau kawai ya fara kuma a zaci zai iya. Da sauri ya kawar da kallonsa daga kansu, dan yasan sai ya ja masu ɗaukar last.
Suna can suna tinani Captain ya ce. "Ready!....... Start"...…...... Cikin zafin nama kowa ya fara na shi, team ɗin su Unays sun zage, su ma su Zaysh sun zage sosai. Take suka fara haɗa gumi, amma dik da haka basu tsaya ba. Noor kam yana dai yi ne kawai, amma ba daidai yake yi bama, dan ko yadda ake ajiye hannu bai iya ba.
Da Captain ya ga dayawa daga cikinsu basu iya ba, sai ya ce wasu sojoji su koya masu. Cikin minti ɗaya wasu dakakkun sojoji suka yi wa wajen ƙawanya, take suka fara bankare su Noor, dan kun san koyarwa waɗan da suka sha horo kam ba a hankali zai biku ba. Tin Noor yana daurewa har ya fara kuka. Zaysh and Leo ne kawai suka iya jurewa, a wannan karon Unays ma bai iya ba, kuma bai iya jurewa ba, dan Unays ma dai renon ice cream ne, iyayensa manyan ƙusa ne a Naija, shi kuma Zaynash kun san dole zai iya, saboda wahalar da suka sha hannun Auntynsu, bawan ALLAH wuya tabi jikinsa already.
Shi kuma oga Leo yana da alaƙa kakkarfa tsakaninsa da AZURE wanda a nan ba zan faɗa ba, sai mun yi gaba, baa banza Captain Onbish yake jinsa a ransa ba, bugu da kari yana da alaƙa da manyan Generals na GIDAN SOJA ɗin, musamman GAT, wannan side ɗin na bari ne saboda wani sirri na labarin gaba zaku ji me alaƙarsu, amma suma basu san alaƙar ba fa, bugu da kari tin ainahi yana gym ba yau bane farau!.
Tin da Noor yake a gidan soja bai taɓa shan wahalar horo irin na yau ba, kafafunsa da hannunsa dik sun yi tsami, ya sha kuka sosai, ya kuma ci wahala, ya wahalar da team ɗinsa, dan sau uku su Leo suna maimaita wannan horo, tin suna hakuri har dikkansu idanu ya fara raina fata, yau harta Vash sai da ya yi ta kuka, Leo and Zaysh basu yi kuka ba kam, amma dai sun ɗanɗana a jikinsu, idanunsu ya yi jajir tamkar wuta, tin daga nan Leo ya kudurta a ransa cewa in dai haka ne daga yau Noor ba zai sake sanyasu faɗuwa ba, dan fa ba karya yau sun wahala, sama da 2 hours suna maimaita wannan horo, tin suna iyawa har dikkansu suka gaza, dik saura teams ɗin sun kammala horonsu sun bar wajen, amma su suna nan.
A ransa Leo ya ce lokacin gyarawa Noor zama ya yi, dan ba zai lamunta ba, babu abin da ya fi kona mashi rai irin last da team nasu ta ɗauka a yau, ya ji matuƙar zafin hakan. Da Captain yaga dik sun zube a ƙasa sun kwanta sai ya ce yau zai ɗaga masu kafa, amma wlh gobe dole sai sun kammala dukkansu a kan lokaci. Vash ya yi kuka har da majina, shi kan Noor ai faɗin irin kukan da ya yi ma ba zata yiwu ba, shi kuma Zaysh tin idanu na jajir har ta ciki da kwallah. Leo ne kawai bai yi kwallan ba, an dai ji jiki.
A tinanin vash za'a yafe masu sauran lokacin da ya rage ace su je ɗaki su huta tin da sun gaji, sai ya ga akasin haka, saura awa biyu lokacin sallar jumma'a ta yi, a yau in suka yi sallar jummaa shikenan horo sai gobe, na faɗa maku ranar Jummaa suna da gajeran lokaci ne.
A wannan awa biyu da suka rage Captain ya ɗaukesu suka nufi filin horo, ba zai iya yafe masu wannan awa biyun ba ko da zasu mutu. Dik sauran team sun kammala nasu har sun tafi horon sake koyan magana da ido.
Su kuma yanzu za su yi escape run, ɗaɗɗaure masu fuska da hankey aka yi, aka ɗaukesu a mota zuwa wani waje mai nisa da basu san ina aka nufa da su ba, kafafu da hannayensu dik zogi yake yi masu.
A wani waje mai cike da yashi aka saukesu, sannan Captain ya umarcesu da su koma sansani a cikin mintuna 70. Babbar magana, zazzare idanu suka fara yi, dan bama su san a ina suke ba, kallon juna suka fara yi, Captain kuma ya nemi waje saman bayan mota ya zauna, a natse ya ce lokacinsu ya fara daga yanzu.
Shiru suka yi suna ƙoƙarin ganin sun yi amfani da kwakwalwarsu......... (Dik yadda aka yi manyan sojoji suna tantama a kan kaifin kwakwalwar room 1 ne yasa suke son gwadasu, dan kuwa wannan horo sauran teams ɗin basu yi shi ba, akwai dalilin da yasa su aka masu hakan!.)
Sun ɗauki a kallah mintuna 5 a tsaye, sannan suka ɗan motsa, Captain ne ya ce masu. "In dai ɗaya daga cikinku bai isa sansani a ƙasa da mintina 70 ba to tabbas zaku sake farawa dikkanku, dan a cikin team kuke har yanzu".
Da jin haka yasa suka sake kallon juna. Leo kamar ba zai yi masu magana ba, amma da ya tuna ko ya yi kokarin ya koma bai kulasu ba in suka tsaya a baya shi ma za'a sake dawo da shi ne, tina haka ne yasa ya ware tafukan hannunsa yana rarraba idanunsa a kansu. Da sauri Noor ya matso ya ɗaura nasa hannun a kan nasa, Vash and Zaysh da sauri su ma suka ɗaura. Shiru Leo ya yi for 2 mins kafin ya ce masu. "Think with your brain". Yana kai karshe ya wuce gaba. Da sauri suka biyo bayansa.
Mamaki ne ya kamasu ganin daji ne a gabansu, bayansu duwatsu, gefen da gefensu bishiyoyi, da sauri Vash ya ce. "To ta wace hanya muka zo?"........ "Ta wannan dajin na gaban, cikin ciyayi kenan". A cewar Noor.
Da sauri Zaysh ya ce. "Kenan sai mu bi tayan mota ai".........Murmushi Noor ya yi tare da cewa. "Yes mun samo hanya, cikin sauki ma zamu koma"....... Vash ne ya amsa da. "Ashe ma ba wani wahala zasu ruɗamu". Murna suka fara yi sun samu mafita, har da wucewa gaba suka fara neman tayar motansu.
In a cool way Leo ya ce. "Before they brought us here, they kept driving around in circles to confuse us about the route, so following the tire tracks isn't the solution!!"....... Take murnarsu ya koma ciki, watau kenan sun shirya wahalar da su.
Noor ne ya ce. "Brothers me abin yi to?"...... Vash ne ya amsa da. "Gaskiya our senior are very smart, wato suka yi ta kewaye da motar dan sun san zamu ce zamu bibiyu taya"........ Zaysh ne ya capke da cewa. "Jahili baya yin AZURE BARRACK, dik wanda ka gani a nan ɗan baiwa ne!".
Noor ne ya ce. "Mu yi ta tafiya kawai zamu samu hanya"....... Zaysh zai yi magana suka ga Leo ya juya ya koma baya in da Captain yake zaune a saman mota. A ɗan nesa ya tsaya tare da kurawa motar idanu na 1 minute kafin ya juya ya dawo in da suke, gaba ya yi, kallon juna suka ɗan yi kafin su rufa mashi baya. A bakin fita dajin gaban nasu ya tsaya, ya ɗan lumshe idanunsa yana tinanin in da gate na parking lot na barrack ɗinsu yake, da ya tina gabas take fuskanta, sai ya tina motar da kawosu tana fuskantar yamma ne, hakan na nufin da suka fito barrack daga gabas sun juyo yamma ne, in kuwa haka ne barrack ɗinsu yana ta gabas ne. Bashi da tabbaci, amma yana tsammanin haka ne.
Dan haka cike da yakini da yarda da kai ya wuce gaba tare da cewa su Noor su yi sauri dan lokacinsu ya ja. Zuba mashi idanu suka ɗan yi suna mamakin hanyar da ya nufa, dan su dai iya kallonsu basu ga alamar barrack ɗinsu a wajen ba. Amma sai suka yi hakuri suka bisa. Tafiya suka fara yi tin suna hira jefi-jefi kafafunsu na yi masu zafi har suka yi shiru.
Sun yi tafiyar good 40 mins kafin su isko hanyoyin sun rabe biyu, tsayuwa suka yi a wajen suna kallon Leo, shi kuma ƙoƙarin tinano yanayin hanyoyin da suka bi a lokacin zuwa ya yi, dik da cewa idanunsu a rufe, yana iya tina kwana nawa suka yi a lokacin da suke cikin mota, tabbas kwana biyar suka yi, a farkon kwanansu sun fita barrack ba jimawa ne, kuma shi kaɗai ne kwanar tsakani da ALLAH sauran kwanan dik an yi ne dan a rikitasu.
Idan kuwa haka ne to kwana zasu yi, ɗayar hanyar zasu bi, kuma daga in da suke babu nisa da barrack. Dan haka sai ya bi hanyar da ta rabe ta yi kwanar. Jikinsu dik ya jigata, da kyar suke tafiya a yanzu. Sai dai duna yin kwanar basu wuce tafiyar 10 mins suka yi ba sai ga barrack ɗinsu sun hango. Ai tsabar murna Noor bai san lokacin da ya wastsake ba, cikin farinciki ya rungumi Vash, sai suka daure suka ɗaga kafafu dan karisawa.
Suna isa rooms ɗinsu suka wuce, dan lokacin sallah saura ƴan mintuna. A gurguje suka yi wanka, ga shi ba ruwan zafin gasa jiki, wlh dik wanda ya gansu yasan a tsananin gajiye suke. Noor dai ko wanka bai yi ba, gado ya haye, ya kwanta abinsa, tin da bani horo a gaba ai sai barcin huce gajiya.
Su kuma suka shirya suka tafi masallaci, Leo ya shirya cikin wasu tsadaddun ripped jeans blue mai bala'in kyau, daga sama ya sanya polo shirt fari tas, still ya sanya army p-cap, amma ya juya p-cap ɗin dan ya iya yin sallah. Ya tara kitson kansa ya ɗaure a baya, ya tura jelar cikin p-cap ɗin, sai tashin daddaɗar kamshi perfume na kamfaninsu Noor yake yi. Watau yau Leo ya fito a ainahin ɗan duniyarsa, ripped jeans ɗin nan ta kara mai da shi irin shahararrun ƴan iskan nan ne, irin jeans ɗin nan ne masu zubin crazy, but ripped ba'a yayyage take skint a waje ba, tana yayyagen amma daga ciki an sanya wani tadin jeans ɗin, yagi-yagin ya zama kamar kwalliya ce kawai.
Dadduma ya ɗauka ya fita zuwa masallacin, su kansu Zaysh da suke maza sai da suka kallesa suka kara, daga karshe ma zuba mashi idanu suka yi har ya fita. Sannan suka karisa nasu shirin, Zaysh kayanmu na hausawa ya sanya, kyakkyawar jumpa milk color da ta sha guga sosai. Vash ya sanya three-pieces suit. Ya yi matuƙar kyau, amma sai santin kayan Zaysh yake yi, wai shadda tai mashi kyau, Zaysh ya ce su je masallaci su dawo zai bashi kyautar kala biyu, ya zaɓi wanda yake so, sai murna yake yi.
------------------- After 40 mins.
Bayan sun yi sallah sun fito, za su nufi dining hall, a kan hanyarsu na zuwa suka ci karo da GAT da ya fito daga office ɗinsa, sai sauri yake yi, ai take kowa ya kame suka hau sara mashi. Har ya wucesu kuma sai ya dawo, a gaban Leo ya tsaya, dama tin ɗasun da ya kalli yadda suka yi suka dawo gida yake ta faman kallon Leo a video ɗin, dan yaga shi yai masu jagora.
Key ɗin hannunsa ya miƙawa Leo, a natse ya ce. "Ka je sashin horar da jami'ai na musamman ka ɗauko mun yarana ka kaisu gida". Yana gama faɗar haka ya wuce bai kara wata magana ba. Mamaki ne ya kama Leo, to shi a yaushe ya san yaransa fisabilillahi? Bai san hakan ma dik gwada shi yake son yi dan ya tabbatar da cewa da gaske da ƙwaƙwalwa Leo yake aiki ne ko kuwa! Watau ya gano yaran da kansa, ya yi tinani da brain ɗinsa.
Ya ɗan jima a tsaye kafin ya juya ya nufi harabar office na Seniors ɗin nasu. A hanya ya haɗu da Captain, sara mashi ya yi, har zai wuce Captain ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, ya ɗan yi mamaki. Katse mashi mamakin Captain ya yi da cewa. "A lokacin da ba lokacin horo ba ka ɗaukeni matsayin brother"....... Watau a lokacin horo kuma ba sani ba sabo.
Jinjina kai ya yi tare da bashi hannu suka gaisa........ "Ina zaka je?". Captain ya sake faɗa...... Sai da ya ɗan yi shiru na ƴan sakani kafin ya ce. "GAT sent me to pick up his children from school and take them home"....... Jinjina kai Captain ya yi, shi ma zuciyarsa cike da mamakin yadda aka yi su Leo suka dawo, a tarihin AZURE team biyu ne suka taɓa haye waɗan nan gwaji dik da akwai wasu masu zafi a gaba, amma tin a farko babu wata wahala sun fara wucewa, gaskiya su ɗin ƴan baiwa ne.
Wucewa Leo ya yi ya nufi wajen motocin. Duba key dake hannunsa ya yi, ta Pagani huayra lmola ce, yasan mota sosai shiyasa ya gane key ɗin wacce ce. Kai tsaye ya nufi motar, bai ɓata lokaci wajen shiga ba, ya ajiye daddymarsa a saman seat na motar, a natse ya tada ta ya nufi barin wajen.
Sai da ya tafi kaɗai ya fara tinanin ina nema school ɗin kwararrun jami'an yake? Kwararru ma ta wani ɓangare ne? Dan kwarewar ai kala-kala ce. Hakan yasa ya tsaya tare da tambayar wasu zaratan sojoji dake ta faman sarawa motar a tinaninsu GAT ne a ciki. Sauke glasa ya yi tare da sara masu, sannan ya yi masu sallama. A mutunce suka amsa, a natse ya tambayi ina ne school na yaran GAT.
Ba ɓata lokaci suka sanar da shi ai suna ɓangaren computer ne, su kwararrun jami'ai ne ta ɓangaren computer. Godiya ya yi masu tare da jan motar ya wuce, da kallo suka bisa suna manakin irin tsantsar kyan da yake da shi, basu taɓa kallonsa a barrack ɗin ba sai yau.
Kai tsaye gate na school ɗin ya nufa, ya yi mamakin ganin babu students. Yau jummaa tin 1 suka tashi, yanzu kuma 2:30 ta yi, students dik sun watse, GAT ya shiga meeting ne ya makara zuwa ɗaukar yaran nasa, ga shi kuma bai basu driver ba saboda tsananin son da yake yi masu, komai da ya shafesu da kansa yake zuwa ya yi, dan in yasa ayi masu sai ya ga ba'ayi masu yadda ya dace.
Rarraba idanunsa ya fara yi tin da ya shiga school ɗin, makarantar tana da girma sosai, zaka ce ba'a cikin barrack ɗin ma take ba saboda girma. Yawo ya fara yi a ciki yana neman ta ina zai gansu ne wai. Can ya hango wata studens sanye da uniform ɗinsu, tana duke a kusa da filin wasanninsu, jan motar ya yi ya karisa wajen. Jin motsin mota yasa ta ɗago kai slowly.
Ya subhanallah, ALLAH ya yi halitta a wannan waje, ƴar yarinya ce da bata wuci 13 years ba, tana sanya da mini sket zuwa santala-santala cinyoyinta, black color ne sket ɗin, sai top daga sama white color, haka uniform ɗin nasu, tana da gashi mai tsananin kyau, bakinkirin, ta ɗaure shi kashi biyu, ta zubo jekar ta gaba gar kasan kirjinsa, ga jekar gashin an ɗaure da ribon kalar uniform ɗin, kafafunta sanye da boot fari tas, tana goye da jaka black color.
Ganin motar yasa ta ɗaure fuska sosai, tamkar bata taɓa sanin menene dariya ba, da ta haɗe ran ma ta fi kyau. Da sauri ta bar wajen ta shiga wajen wasannin. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa, kuma ya gane ita ce ƴar GAT, dan ga kama nan a kan fuskansu. Jan motar ya yi ya bi bayanta har zuwa wajen wasanin cike da mamakin meyasa ta ga motar gidansu kuma bata tsaya ba? Bai san yaran nan sun fi ubansu murɗaɗɗen hali ba.
A ɗan nesa da su ya faka motar tare da fitowa, ya jingina da jikin motar a ransa yana jin ba zai iya juwa ya yi masu magana ba, ɗan ɗagowa ya yi ya kalli yarinyar, sai ya ga ashe su biyu ne a wajen, ɗaya tana ƙoƙarin ɗaure igiyar boot dake kafafunta, ɗayar kuma hannunta rike da basket ball.
Da sauri ya ɗauke kallonsa a kansu, amma ya sha mamakin ganin kamar kamanninsu ɗaya su biyun. Dan ya tabbatar kallon gefen ido ya sake binsu da shi, nan fa ya kara shiga mamaki ganin da gaske ne a kan fuskokinsu babu wani banbanci, sun yi mugun kama na wuce misali. Like seriously! Wow, abin da mamaki. Jingina sosai yai da jikin motar yana mai da kallonsa ƙasa, babu alamar zai yi masu magana.
Wasu ƴan'mata guda biyu ne da suka shigo wajen basket ball ɗin a yanzu suka sanya yai gaggawar ɗan raba jikinsa da jikin motar, dan ta witsiyar ido ya gansu, sai yaga tamkar almara ce ko inuwarsu Arya ya gani.
Nan fa ya ji kamar kwakwalwansa ta ɗan juya, a cikin ransa ya ce kenan ƴaƴan GAT Quadruple ne? Kuma dikka mata masu tsananin kama da juna? Kai bai taɓa ganin haka a zahiri ba. Amma sai ya fiske tare da mai da kallonsa ƙasa.
Wacce ke rike da basketball ɗin ce ta ce. "Arya time is going let's finish this game before that ya kariso". Kalamanta ya nuna basu san da Leo a tsaye a wajen ba. Arya dake faman ɗaure igiyar boot na kafafunta ne ta ɗago da kai. "Angelina dad can't come now, because he has a meeting, so we have a lot of time da zamu buga game ɗin nan slowly".
Uhm Angelie, Arya, Manassa and Vanisha, ƴaƴa ne ga GAT namu, ƴaƴan da kenan ya mallaka a rayuwansa, ƴan huɗu ne watau quadruples, sun taso ne cikin tsananin kula da soyayyar mahaifi, bai taɓa bari sun yi kuka ko sau ɗaya na rashin wani abu ba a rayuwarsu, yana sonsu fiye da yadda yake son kansa, basu da mahaifiya, daga su sai uban masu aiki dake kula da su, ma'aikatan gidan GAT sun haura 15, kuma dik saboda farincikin su Arya ya zuba su. Sun taso sangartattun yara waɗan da basa ji kuma basa ragawa kowa, ranon soja ne su ɗin, basu ɗaukar rainin hankali, musamman Arya, asalin sunanta DINEARIS, suna ce mata Arya ne kawai saboda wani dalili na daddynsu da yasa ya ɓoye ainahin sunansa.
Yaran nan sun gado madarar kyau ne daga mahaifiyarsu, tamkar ku sacesu ku gudu ku je ku ajiye ku yi ta kallo, komai nasu iri ɗaya ne sak, sai banbancin halaye, dan Arya ita ce babba, kuma tafi kowa jiji da kai a ganin jama'a, amma a zahirin gaskiya tsantsar kamun kai ne da gudun rainin wayau, shiyasa bata kula kowa, ko ɗaga ido ta kalli mutane bata yi, ƴan uwanta sai daddynta kawai take kulawa.
Sai mai bi bata Manassa, ita ma tana da halin shariya, amma ita kuma akwai son gulma sosai, dik wani news na gulma to a zo wajenta amma akwai shegen tsoro. Ta ukunsu Angelina, ita ƴar baruwana ne, kowa nata ne, sai zafin ran balai idan ta ga ana zaluntar wasu, wani lokaci bata da hakuri kuma bata da daɗin sha'ani, dan bata barin ko ta kwana, na karshensu kuma autarsu ita ce Vanisha, suna ce mata V, yarinya son kowa kin wanda ya rasa, shagwaɓaɓɓiya number ɗaya, ga zallar iya soyayya, akwaita da son karanta labaran soyayya, ga son kallon film da ake mutuwa kan soyayya, kullum maganarta ɗaya yaushe masoyinta zai bayyana, tana da fara'a sosai, dik cikin Quadruple ɗin ita kaɗai ce mai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 95