Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
canza murya da gashin kai ba! Kamal ku baku san waye Haiza'an ba, na tabbata da ba zaku yi tantamar Zayra'an zai gane Lazy ba". Kai suka jinjina kafin Dr Kamal ya ce. "Dik ba wannan ne ma ya fi damuna ba, na damu sosai a kan IRON FIST, ka sani na samu mun sani aiki suke yi domin al'umma, a shirye suke su dakatar da nasarar da muke samu, ina tsoron abin da zasu iya aikatawa, kun san suna da mugun haɗari"....... Siririn tsaki Dr James ya ja. "Ba zasu iya yi mana komai ba, dik bala'i mutum ba zai taɓa iya gano WS-HOSPITAL ba! Ba'a haifi mahaluƙin da zai iya ganomu ko ya dakatar damu ba, dan nasara aka haifomu a duniya!". With his full confidence ya faɗa, yana jin tamkar dan su aka shinfiɗa kasar duniya!. Jinjina kai su Dr Kamal suka yi, dan suma sun san a irin tsaron mai masifaffen karfin da suke da shi sai dai in fita waje suka yi za'a iya kamosu, amma a cikin WS-HOSPITAL kam wane mutum ya iya kamasu, kofofin shiga masu shocking na lantarki, sai Dr James ya shigar da password shocking ke ɗaukewa, kuma shi kaɗai yasan password ɗin, ai kunga kuwa ba zasu kamu ba a ganinsu!. Haka suka cigaba da aiki suna tattaunawa game da nuna cewa IRON FIST ba su isa su dakatar da su ba, sun yarda da kansu kuma sun yi imani sune kawai masu nasara, dan nasararsu aka shinfiɗa duniya. A gefe kuwa, Sister Zinta ta koma ɗakin jariran, nan ta tarar Dr Kamal ya gaba duba boy ya bashi dik wani abin da ya dace, ta dawo rike da yaron tana lallaɓa shi tamkar kwai a faranti. Ita kuma sister Zinta ta ɗauki wannan haɗaɗɗen yaro mai blue eyes da aka kashe ɗan uwansa jiya, ta rungume yaron tana yabon kyansa, daga nan ta ce. "As from today this is my baby, kuma na bashi sunan Haiza'an". Ɗan zazzaro idanu a kanta suka yi, sister Maya ta ce. "Ina kika samu wannan suna mai shegen daɗin kuma, Haiza'an, sunan ya yi daɗi"...... Tana ɗan murmushi ta ce. "A laptop na my Dr na ga wani folder an rubuta Haiza'an shi ne kawai na ji sunan ya kwanta mun har cikin raina". "To waye ya ce maki suna ne? Kika sani ko wani abin ne?". Sister Maya ta faɗa.. tana saɓa babyn a saman shoulder ɗinta ta ce. "Koma dai menene sunan ya shiga raina sosai, koma ba sunan mutum bane, ko sunan wani abin ne ni dai ya mun, in na kira sunan daɗi nike ji, dan haka sunan babyn nan Haiza'an". Maya tana murmushi ta ce. "Kin san nima sunan ya kwanta mun a rai ya burgeni?"....... "Ai sunan yana da daɗi ne, daga yau sunan wannan baby Haiza'an, haka zaki dinga ce mashi"..... Suna murmushi gwanin sha'awa suka fara cire kayan jariran suna yi masu wanka. Bayan sun kammala suka sanya masu kayan sanyi saboda weather ta ruwan sama, a nan suka zauna zaman hira, sister Zinta ta sanar da sister Maya cewa ai sun kai babys ɗin ɗakin kula da su ne dan sun kamu da cuta, Maya ma ta gamsu da bayanin, sai suka hau addu'ar yaran su samu sauƙi. A can gefe kuwa 3D na zaune office ne Dr James suna tsara yadda zasu haɗa rigakafin cutar NEXAPOX-31 kafin su haɗa ainahin maganin cutar, Dr James ya fito masu da tsarin aikin da kuma jerin abubuwan da zasu buƙata domin haɗa wannan magani da kuma rigakafin. Suna ta faman karanta abubuwan buƙatar. Yau basu yi wani aiki sosai ba, around 1 suka je suka zuba jikin darling Dr James ya sake ɗaukansa video ya turawa World System, hakika bakina ya yi kaɗan iya zayyana maku bala'in da darling yake a ciki, ya rabb, ALLAH ya saka maka, ya bi maka hakkinka bawan ALLAH. Bayan sun duba shi suka wuce cikin ɗakin haɗa cutar NEXAPOX-31 ɗin, suka shirya kwalaben dake ɗauke da sinadarin cutar a cikin manya-manyan kwalaye, sannan suka shirya a wani ɗakin duhu dake kusa da wajen, daga nan suka fito suka nufi ɗakin kirkire-kirkiren halittunsu da ƙaƙale-ƙaƙalensu....... In Sha ALLAH a wannan kirkire-kirkiren zaku kirkirowa kanku bala'i shehu la'anannu kawai!. Wasu mugayen kwari dake cikin wasu glass suka sanya guard biyar majiya karfi suka ɗauka suka fitar masu da shi, kai tsaye a bayan motar da ake shirya jariran da Dr Mark yake fitarwa suka sanya katuwar glass ɗin. Kamar kullum Dr Mark ya ja motar ya fita da shi ta cikin wannan hanya da ta ɓulla cikin dokar dajin. Su kuma suka koma cikin asibiti, da alama an kammala wannan project na kwarin, za'a miƙawa masu shi. Ko wacce ƙasa za'a sakarwa waɗan nan kwari kuma? To koma wace ƙasa ce ALLAH ya kareku daga sharrin WS, dan waɗan nan kwari suka cijeka sai ka kwanta jinya na zazzaɓa mai mugun zafi ga ciwon kai, idan kana da rabo sai ka sha jinya ka warke, idan kuma ba saura kwana mutuwa zaka yi bayan shan azaba. Wunin wannan rana dai haka suka kasance, around 5:30 Dr Kamal and Dr James suka zo suka ɗauki sister Maya and Zinta. Yaran nan sam basa son tafiya su bar babys ɗinsu, amma ba yadda suka iya, sun gama yi masu wankar yamma suna wasanni dasu kawai 3D suka zo suka ɗaukesu, Maya har da guntun hawayenta wai bata son barin boy, ta ce zata tafi da shi Dr Kamal yaki yarda, ya yaudareta da kalamai har ta aminta ta biyosa suka tafi. Around 1 na dare Dr Kamal and Dr James suka sake fitowa suka baro ƴan matan nasu a cikin gida. Yau ranar haɗa drugs ne na jini da suka riƙa jariran jiya. Dan haka ba sai na sake yi maku bayani kan yadda suke haɗa magani da jinin ba, already kun sani, na ɓargo da ƙashi ne baku sani ba, idan na zo nan dallah-dallah zan maku. Amma yanzu dai sun haɗa maganin kamar yadda suka saba, suka shiryasu cikin sachet kamar ko yaushe. Sannan suka sa aka fitar masu zuwa ɗakin shiryasu a cikin kwalaye, sannan suka fitar zuwa General Hospital ɗin. Around 4 suka kammala, suka koma gidansu, sun isko su Zinta na barci, dan yau shayar da su maganin barci suna yi a cikin lemu da suka je yin lunch ba tare da su Zinta sun sani ba. Hankalin 3D ya fara tashi tin daren jiya da su Maya suka nemi titseyesu kan ina suka je, daga nan suka yanke shawarar rinƙa masu maganin barci cikin dare, dan basu son suga hankalin ƴan matan nasu a tashe, kuma ba zasu iya faɗa masu abin da suke yi ba. Bayan sun dawo wanka suka yi, suka shirya cikin wasu sleeping dress ɗin, a gefen matan nasu dik suka kwakkwanta tare da jawosu jikinsu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da su. While shi kuma Dr Mark yana can yana kwasan hanya zai fitar da kaya daga cikin ƙasan ta ɓarauniyar hanya. D-------O-------L🔥 Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna. Kiran Ummie ne ya shigo wayar Zaynish. Ciro wayar ya yi daga aljihunsa. Kashe kiran ya yi game da kiranta. Bugu ɗaya ta ɗauka, kara wayar a kunne ya yi game da cewa. "Assalamu alaikum". A yadda ya yi magana ko Angelina dake kusa da shi bata ji me ya ce ba. Daga ɗayan ɓangaren Ummie dake zaune saman sabbin sofa set ɗinta da ta yi wa kanta ne ta amsa da. "Waalaikumussalam ɗan uwana"....... "Ina wuni Aunty Ummie?"........ "Lafiya lou Alhamdllh ya aiki da abokan aikin naka?"....... "Suna nan lafiya, ya gida da Yaya Faisal? Ya dawo ne?". Kai ta ɗan girgiza kafin ta ce. "A'a bai dawo ba, ya dai turo mana saƙo jiya, ina su Noor? Kwana biyu ban jisu ba?"..... Kallon in da Noor yake ya ɗan yi kafin ya ce. "Suna nan lafiya, Aunty Ummie kina mana addu'a sosai ko? Kin san yanzu addu'a kawai muke da buƙata". "Sosaima, kullum sai na yi maku, ALLAH ya kare mun kai, yaushe zaka dawo ka fara aiki a nan dan ka ɗauka mana fansa? Ka kore mana ƴan ta'addan nan?"......... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Sai mun kammala wannan FIVE MISSION ɗin, a wannan lokacin ne muke da zaɓi, ko mu zauna a Avaris mu yi aiki ko kuma mu yi applying Nigeria or Niger dik wanda kika zaɓa mun, so in mun gama FIVE MISSION muna dan ƴancin zaɓar ƙasar da muke son yin aiki". Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Zan yi tinanin in da zaka yi aiki, amma yanzu dai yaushe zaku gama?"...... "Very soon In Sha ALLAH, ke dai ki cigaba da yi mana addu'a". "In Sha ALLAH addu'a kam ba fashi, yanzu dik ajiye wannan magana, batun aure na kiraka mu yi"...... Kada ku manta ita bata san sun tafi mission ba, ya ɓoye mata dan kada ya ɗaga mata hankali, yanzu ta ɗauka suna barrack ne shiyasa ta ɗauko mashi batun aure. Ƙasa ya ƙara yi da murya wajen cewa. "Kai Aunty Ummie, na faɗa maki bani da zaɓi a kan mace, kawai ki bani dik wacce tai maki, ki zaɓota, na baki wuƙa da nama, ko wacece kika kawo zan aureta, na yi alkawari, amma ki kawo wacce zata girmamaki fiye da yadda zata girmamani, wacce zata soki kamar yadda nike sonki, wacce zata maki biyayya tamkar yacce zata mun, wacce zata kula dake tamkar yacce zata kula dani, idan ba mai wannan ɗabi'u ba bana so kada ki kawota!"...…. Murmushi ne ya kubce mata, cike da farincikin irin yadda ya bata muhimmanci a rayuwansa ta ce. "Ina wacce ka ce ka taɓa gani? Wacce ka fara jin sonta a ranka? Bana son ka rasa soyayyarka ta farko". Nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Ban san in da take ba, na faɗa maki tin daga ranar ban sake ganinta ba, dan haka ni nama mance da ita, kawai ki nemo mun taki"......... "To shikenan zan kuwa nemo maka haɗaɗɗiya, kana zuwa hutu sai aure kawai"........ Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce. "A'a, mu ai muna da lokacin yin aure, sai mun samu umarni daga sama, idan kin samo matar ki sanar dani sai in shigar da buƙatar auren a tsare, idan manyanmu sun yarda shikenan in na dawo sai ayi komai". Da to ta amsa kafin ta ce. "To ka kula da kanka, ka ci abinci ka yi ibada mai kyau, a dik in da kake ka sani ALLAH yana ganinka, kada ka cutar da kowa, ka zauna da kowa da zuciya ɗaya, hakance zai sanya ba zasu iya cutar da kai ba, a dik in da kake ka tausayawa mace, kaga mai raunice, ka tausayawa kanka, ka tina kai maraya ne, baka da kowa sai ni, ba zan iya jurar rashinka ba, ka tina hakan, ka rinƙa addu'a da alwala kafin kwanciya barci, ALLAH ya yi maka albarka". Hakika kunnuwansa sun yi mugun sabo da jin kalaman Aunty Ummie na nasiha kullum, har ya haddace, dan haka da In Sha ALLAH ya amsa mata. Sai ta sake cewa. "Ina sonka sosai rabin raina". Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, bai san daɗin iyaye ba, amma a kanta yasan ainahin menene soyayya, ta sadaukar da komai saboda shi, lallai soyayyarta ce ake cewa true love........ "Nima ina sonki sosai Aunty Ummina, ba zan taɓa son wani abu rabin son da nike yi maki ba, ki kula da kanki, dik abin da yake damunki ki yi gaggawar sanar dani kin ji?". Da okey ta amsa mashi, daga haka suka yi sallama, ya shiga gallery ɗinsa, hotunanta ya fitar ya fara kallon yana tina yarintarsa, lallai Aunty Ummie ita ce komai ɗinsa, tai mashi komai, a rana sai ta kirasa sau biyar ko mantawa bata yi, ga hidimar shago dana gida, amma baya sanya ta manta da shi, kome ta ɗauka zata kai baki sai ta tina shi, ta ce shin shi ya ci ko bai ci ba? Yana samun irin abin da take ci ko baya samu? Dik ta damu. Ya jima yana kallon hotonta kafin ya ɗan nisa, unexpected wayan nasa ya kubce ya faɗi ƙasa a gabansa. Da sauri Angelina ta ɗauko mashi wayan, kurawa hoton da yake kallo ɗin ido ta yi. Bata san lokaci da ta ce. "Wow, she's so beautiful"........ Slowly ya ɗago kallonsa a kanta wanda tin da ta zauna a wajen ko sau ɗaya bai ganta ba, har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta furta words kan hoton. Murmushi ta ɗan yi game da miƙo mashi wayar tana faɗin. "Is she your sister?". Ta faɗa tana mai da kallonta a kansa......... Bai amsa mata ba, kuma bai karɓi wayar ba. Bata damu da bai amsa ba ta sake cewa. "You look alike, amma tafika kyau saboda ta fika hasken fata, and ta fika big-big eyes, wow ta yi kyau sosai, anya ba zan cewa daddyna ya auro mana ita ba? Ta yi kyau sosai, na ji ina sonta". Har cikin ransa ya ji Angelina ta burgesa, dik wacce zata so Aunty Ummie, hakika zata sace zuciyansa. Ganin bai karɓi wayar bane yasa ta zaci ya ji haushin abin da ta yi ne, sai a lokacin ta tina ashe oganta ne, taɓa wayansa ba da izininsa bama ta yi laifi, da sauri ta ce. "Sorry sir, it can't happen again". Ta faɗa tana sake miƙo mashi wayar, cikin muryar girmamawa tai maganar. Hannu yasa ya karɓa yana ɗauke kallonsa daga kanta. Ƙasa ta yi da kai, haka kawai sai ta ji murmushi ya kubce mata ganin yau ɗaya ya ɗaga ido ya kalleta, abin da bai taɓa yi a, ba zata mance wannan rana ba, kuma haka kawai har cikin ranta ta ji Aunty Ummie ta shiga ranta, ta yi matuƙar burgeta, har ta ji cewa lallai tana son yin magana da ita. Zanen heart ta yi a ƙasa tare da zana dogon kifiya a tsakiyar heart ɗin kafin ta yi rubutu da yaren daddynta a saman heart ɗin, a ƙasa kuma da turanci ta rubuta. "Zuciyata ta makance kan mutum ɗaya, ta rufe ruff kan mutum ɗaya, bana ji, kuma bana ganin kowa sai shi, shi kaɗai ne zaɓina, shikaɗai nike gani in ji daɗi, i love you forever and ever"...... Ta gama rubutun tare da miƙewa ta bar wajen, ta koma kusa da Manassa ta zauna zuciyarta cike tab da tsananin begensa, tana fatan ace ya ga wannan zane. Shi kuwa cigaba da dannar wayansa ya yi ba tare da ya sake ɗagowa ya kalli in da take bama bare ta ji sanyi a ranta. ------------------- Tsaye Lion yake a tsakiyar room ɗinsa rike da rigar pjs ɗinsa daya cire, ya kunna light bolb da suka ɗaura a saman tantin wanda ke amfani da solar, haske ya gauraye ko'ina a cikin ɗakin, yana ƙoƙarin ɓalle botiran rigan zai sanya a jikinsa ya fita. Bakinta a ɗauke da excuse Arya ta shigo cikin tantin rike da hannun yarinyar nan, zata fita ne yarinyar ta ce sam ita ba zata zauna a ɗakin ita kaɗai ba, shi ne Arya ta kamata suka taho tare. Sake hannunta Arya ta yi game da kamewa ta sarawa Lion tana ɗan yin ƙasa da kai, gabanta sai faɗuwa yake yi na ganin kyakkyawan kakkarfar surar jikinsa, his sixpack was so Masha ALLAH, dole nema ya tafi da tinanin dik wacce ta gansa, gabaɗaya sai ta nemi natsuwarta ta rasa, ai a miliyan ta ɗauke kallonta daga kansa game da sauƙe hannun nata ƙasa. "Sir akwai abin da yakamata ka zo ka gani, dan bayani da baki ba zai yiwu ba". A dake ta faɗa cikin girmamawa. Kai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Sake sara mashi ta yi kafin ta kama hannun Jehan su nufi waje tana ɗan waigosa. Cikin tantinsu suka koma, ta zauna a gaban laptop ɗinta game da cewa Jehan ta zauna a saman electric mattress ɗinsu. Hayewa kai Jehan ta yi tana kallon Arya cike da so, tana son Arya sosai.... Cigaba da abin da take yi Arya ta yi, ita kaɗai a cikin tantin, su V dik suna wajen wutar da suka kunna. After 5mins da kiransa sai ga shi ya shigo sanye da pjs ɗin da yake rike da shi ɗazun, hannunsa rike da wayansa yana pressing, da alama saƙo yake rubutawa. A dab saitinta ta baya ya ɗan tsaya, sai da ya kammala rubuta saƙon da yake yi ya tura sannan ya sunkuyo kanta game da maido da kallonsa kan laptop ɗin. Kallon 1 minute ya yi wa laptop ɗin sai kuma ya kai hannunsa sama mouse ɗinta, already hannunta na kai. Ai wani irin yanayin da ta ji ya ziyarce a lokacin da skin ɗinsa ya taɓata ba zai misiltu ba, da sauri ta janye hannunta tana sauke numfashi a hankali-hankali, ga daddaɗar kamshin perfume ɗinsa na kamfanin su Noor dake ta faman tashin kofofin hancinta. "Wannan ina ne?". Ya faɗa a natse yana mai da kallonsa kan face ɗinsa, ta tsare ƙashin wuyan nan nasa da kallo. Ɗan ɗauke kallonta ta yi game da cewa. "Jiya V ta tura drone mai ɗan girma wajen ne sai suka harbesa, shi ne na tura ƙarami ɗazun dan in ga me yake ɓoye. Waɗan nan mutane sune abin dake wajen". Cike da mamaki Leo ya sake mai da kallonsa kansu. Wajen tamkar rana, wutar lantarki zaku zaci rana ne, tantuna ne dayawa a kafe a wajen, wlh ya fi sansanin soja haɗuwa, ga wayarin na wutar lantarki da aka yi, amma su sojoji an basu kaya masu amfani sa solar, a wani sashe na wajen mutanen ma gini ne na ɗaki da block da sementi, ta ko'ina matasa ne suke yawo rike da muggan makamai masu rai da lafiyan da babu irinsu a hannun sojoji. Abin mamaki kuma wlh dik matasan nan yara ne da basu kai 20 years ba, suna sanye da rawani a fuska da jallaniya a jikinsu, wasu kuma da irin pakistan riga da wandon nan, sai sha'aninsu suke yi a wajen tamkar a cikin gari. Riƙaƙƙun ƴan ta'adda ne dake arewacin ƙasar waɗan da suka samu lasisi a ta'addanci, waɗan da manyan ƙasar ke ɗaure masu gindi, suke jin tamkar sun fi karfin kowa da kowa. Motsa done ɗin Leo ya yi, ya fara controlling ɗinsa yana bin sassan wajen, ta ko'ina matasa ne ke shawagi, a kallah zasu kai matasa 300 kam. Gabaɗaya mamaki ya hana Leo yin dogon tinani a kansu, mai da kallonsa a kan kilomita nawa ne tsakaninsu da mutanen ya yi, a gaskiya suna da nisa sosai. Cigaba da kutsawa lungu da saƙo na wajen ya yi, fili ne mai girman gaske, tamkar gari, ga lunguna da wajajen ɓoya ba adadi. Juya akalar drone ɗin Leo ya yi ya nufi wani wajen wanda ya ga lantarki yafi yawaita a wajen dan yaga menene. Bolb na wuta ya yawaita a wannan waje. Tura drone ɗin ciki ya yi dan yaga menene. Ya ilahi ya lillahi, ai Leo bai san lokacin da ya zabura ya miƙe tsaye daga sunkuyon da yake ba. Jama'a, ta'addaci ya yi mugun karfi a arewacin kasar fiye da yadda kuke zato, wannan ɗakin cike yake tab da computers masu inganci, karfin intanet dake wannan waje kusan za'a ce yafi na cikin gari karfi, ashe shiyasa suka iya gano drone na farko suka harbesa, lallai ƴan ƙasa sun yi mugun sake ta'addaci ya yi girman da in ba ALLAH ba babu mai iya kwatarsu. Wannan abu ya yi matuƙar gigita Leo, kuma ƴan ta'addan aka horar kan sanin computer da iya sarrafata. TO WAYE YA HORAR DA SU A WANNAN FANNI?. A wannan waje suna da likitocinsu, suna da masu yi masu girki, suna da dik wani abin da ɗan adam zai buƙata dan more rayuwa, dik yadda kuke tinaninsu wlh sun zarce hakan, wannan shi ne ainahin taddacin arewacin ƙasar ba wata rufa-rufa ko sakayawa, ƴan ta'addan suna rayuwar jin daɗi da ƴanci fiye da ƴan ƙasa, abinci available, ga likita, kuma kullum ƙara yawa suke yi, ga karfin internet da aka ja masu har cikin wannan kungurmin dajin, shiyasa zasu kafa waya su yi video son ransu, su saki baya slow na network saboda karfin intanet na kasar rabi dik su aka baiwa, idan sun tashi zuwa yin ta'addaci sai su tura kalilan daga cikinsu da su matsa daga in da suke zuwa gaba ta bakin fita cikin gari su kafa wasu tantunan, sai su yi shiri su shiga gari, su kashe na kashewa su kwashi na kwasa, su dawo dasu sansanin da suka kafa, bayan kwanaki biyu in komai ya lafa su zaɓi waɗan da aka tsara masu kan ba yanzu zasu sakesu ba, su kutsa dasu cikin daji su kaisu babban sassani wajen babban shugabansu. Saura kuma su barsu a wannan karamin sansani da suka kafa su karɓi kuɗin fansa, waɗan da aka wuce da su babban sansani sai su haura watanni 6-7 a wajen, wasu ma ko an kawo kuɗin fansa basa sakesu, saboda ba'a basu umarnin su sake su ɗin ba, daga sama ake juyasu suma, haka zasu ajiye mutane suna lalata da su, basa zuwa kama mutane haka kawai sai an gama tsara masu ga waɗan da zaku kama, idan kun kamasu ku ware kaza ku turasu babban sansani, kaza ku karɓi kuɗin fansa daga ƙaramin sansani, dik karshen wata waɗan da suke basu umarni suna kiransu su yi lissafi da su, dama already sun san adadin kuɗin da suke baiwa masu basu umarni dik wata. Dik watan ALLAH akwai adadin kuɗin da suke baiwa manyan ƙasar masu ɗaure masu gindi, miliyoyin miliyoyi suke basu, su kuma manyan su basu kayan aiki, bindigu masu inganci, kayan abinci, kayan more rayuwa da kuma wayoyi masu tsada, sannan ga kayan shaye-shaye da suke basu kala-kala, komai ana zuwa da jirgi helicopter a sauke masu kayan abinci, jirgin bata sauƙa ƙasa, a sama take tsayawa ta sake masu makamai da kayan abinci game da dik abin da zasu buƙata. ----------------------- Bin dik wani lungu da saƙo na wannan ɗaki da drone ɗin Leo ya yi, basu gane cewa drone bane, dan na faɗa maku kamar ƙuda yake....... Ya jima a wannan ɗaki yana kallon irin manyan ingantattun kayan aikin da suke da shi kafin ya fita ya sake shiga ɗakin kusa da wannan. A nan kuwa mata ya gani, mata dayawan da a kallah zasu kai 250 haka, dik sun yi shunfuɗa dun kwakkwanta. Fita ya yi ya cigaba da yawace wajen da girmansa ya zarce yadda kuke tinani, nan yaga wasu matan suna zaune bakin wuta suna girki sanye da manyan hijabai har ƙasa, daga gani ba tambaya kasan waɗan nan sun zama ƴan gida, sun yi jimawar da duniya ta manta da su a wajen, sun sadaukar da rayuwarsu sun mance da iyalansu ma bakiɗaya, ALLAH sarki, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ALLAH yai maku sakayya, ya bi maku hakkinku, dan na tabbatar kuna da yara da ƴan uwa. Leo bai san lokacin da ya ɗaura ɗayan hannunsa a kan bakinsa ba, ya kusa suman tsaye saboda tashin hankali, yana jin ta'addanci ta'addanci bai taɓa zaton karfin ta'addancin ya kai har haka a arewacin ƙasar ba, a wannan waje yaushe ƙananan sojoji ƴan bar one zasu iya fito na fito da su? Tsakiyar wannan dokar daji, gaba daji baya daji, ba zaka taɓa zatan akwai ran ɗan adam a wajen ba, ia ilahi, sun kafa wajen kafawar da suna iya ganin dik motsin da zai shigo masu, kafin sojojin su iso in da suke already suna ganinsu ta computers ɗinsu, kafin sojojin su farga sun kewayesu sun masu rubdugu. Wannan ai sai sojojin da suka samu horo biyu suka amsa sunansu sojoji, sannan a haɗa da air force, a masu ɓarin makauniya na wuta sama da ƙasa, ai masu ruwan boma-bomai sau ɗaya shi ne za'a iya masu ba'a zauna tura ƙananan sojoji masu tasowa ana kashesu a banza ba. Miƙewa tsaye gabaɗaya Leo ya yi tare da juyawa Arya baya, ya ɗan dafe

Chapter 85 of 95