ta jan Seraphina da hira har suka isa. Yana parking Rimsha ta kalli Seraphina, a sanyayye ta ce. "My star lady, kada ki manta idan kika yarda da uncle Faryan zamu kasance tare na har abada, zaki shigo cikin zuriarmu, zamu je school tare, shopping tare, mu ci abinci tare, komai tare zamu dinga yi".
Sosai waɗan nan kalamai suka yi tasiri a zuciyarta, sai take jin ta aminta da Faryan, amma kuma shi Aryan kada ku manta soyayyar tin yarinta tai mashi, pure soyayya kenan, hakika idan zata so Faryan yanzu sai dai dan kalaman da Rimsha ke yi mata, shi kuma Aryan sonsa yana ƙasan zuciyanta ne wanda ba zata iya haɗa shi da kowa ba, amma yanzu yarinta yasa ba zata iya banbantawa ba, a halin yanzu kowanne a cikinsu zata iya cewa tana so, amma kowanne da dalilin son nasa except daddy Aryan da pure love da babu dalili take mashi.
Zata so Uncle ne kawai dan irin kulawa da kuma nuna soyayya da yake mata, kunga su IRON FIST basu iya soyayya ba, daddy Aryan bai iya dik waɗan nan tausasawa ba, sai bada umarni ya iya, ko ta ce tana son abi sai dai ya kaita ta zaɓa, ya biya kuɗi, ba irin kyautar masoyan nan, ba kalamai irin na Uncle, shi dai umarni.
Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Zan yi tinani". Tana faɗa ta buɗe kofar motar ta fita. Da sauri Faryan ya buɗe shi ma ya fito. Zata wuce ya ambaci sunanta, juyo da kallonta a kansa ta yi. Wucewa Aisha ta yi ta basu waje.
Dawowa Seraph ta yi, a kusa da shi ta tsaya, tana kallon face ɗinsa ta ce. "Uncle gani"...... Ajiyar zuciya ya ɗan sauƙe kafin ya ce. "Nasan Rimsha ta faɗa maki ina sonki, haƙiƙa haka ne, ina sonki kuma ina fatan in ɗaukeki zuwa cikin zuriarmu, please kada ki ce a'a".
Shiru ta yi tana tinanin kalaman Madam dake ce mata dik wanda ya ganta sai ya zaci wata babba ce, sai a ɗauka 16 years take da shi, yanzu kowani namiji mai lafiya ya ganta sai ya sake ganinta, samari zasu yi tururuwan zuwa wajenta, dan haka ta kula sosai, a wannan lokacin komai zai iya faruwa da ita, wannan lokacin shi ne lokaci mafi haɗari ga rayuwar ɗiya mace, kada wasu kalaman soyayya su kwasheta ta faɗa cikin wani rayuwa, su nan turawa ne, ba ruwansu da sex after marriage, su before marriage suke yi, dik wani dokokin musulunci ba binsa suke yi ba, dan haka ta rike mutuncinta, kada ta kuskura ta bari wani namiji ya shiga gonar da ba nasa ba.
Waɗan nan kalamai ma Madam sun ratsa zuciyarta, hakika yanzu ta fara gasgata Madam, dan yadda ta ga kowa in ya ganta ya ce yana so, lallai ba shakka haka ne, suna mata kallon babba ne, alhalin 13 years kawai take da shi.
Juyawa ta yi ba tare da ta yi wa Faryan magana ba, ta wuce cikin room da zai sadata da elevator ɗinsu. Bayanta ya bi da kallo yana jin tamkar ya mallakawa kansa ita. Sai da ta ƙurewa ganinsa sannan ya shiga mota suka bar wajen.
Tana shiga gida ita kuma room ɗinta ta wuce, wayarta ta ɗauko ta hau kiran number Aryan tin kafin ta cire uniform, tana shigowa gida shi ne a ranta. Ga mamakinta sai ta ji wayansa a kashe, ta ɗan shiga damuwa na jin wayar a kashe, amma ta ajiye wayar ta hau cire uniform.
A lokacin shi kuwa yana can yana barcin huce wannan zazzafar zuciyar, kuma koda idanunsa biyu ma ba zai ɗauki kiranta ba kuma ba zai je ɗaukota ba sai dai ta dawo da kanta, dan yau har ita haushinta yake ji, dik ya tsani kowa, Abba ya kara rikita mana zuciya da kwakwalwarsa, yana son mai da mana da shi ruwa mun samu mun kwatosa daga dokokin IRON FIST na babu mata a tsarinsu da kyar!.
Wanka ta yi, ta canza kaya, pjs ta sanya dan shan iska, ta fito parlo dan yin lunch, a nan ta isko Aisha zaune saman dinning, zama ta yi, masu aiki suka zuba mata abinci, sai suka fara ci a tare.
-------------------------🔥
Tafiya take yi tana ƴan waige-waige, bata ji motsin kowa ba sai ji ta yi kanta ya bugu da bayan mutum. Da sauri ta ɗago da kallonta dan ganin wanene? Daidai lokacin shi ma ya juyo slowly dan ya ga waye ya bugesa.
4 eyes suka yi da juna, wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haɗiya, ya ALLAH, sai ta tina ranar da ta fara ganinsa a school ɗinsu, ranar da ta matsa dab da shi irin na yau, ita kaɗai tasan me ta gani wannan rana.
Wani irin kallo mai kama da kina da hankali kuwa Leo ya wurga mata kafin ya ɗan ɗauke kansa yana ƙara ɗaure fuska. Ɗaure fuska tamau ita ma ta yi, a ɗan ƙule ta ce. "Nan wajen tsayuwa ne da zaka tsayawa mutane a hanya?".
Shiru babu alamar kamar ya jita, sai ma juyawa da ya yi, ya gyara hannayensa dake cikin aljihu, ya cigaba da kallon sabbin sojojin dake karɓar horon bar 1. Wani irin takaici ne ya turnuƙeta, a ƙule ta ce. "Nan cikin barrack muke ba wajen aiki ba, yanzu kai ba a sama dani kake ba, ɗiya ga GAT nike, dole ka mun biyayya".
Shiru babu alamar zai amsa mata, ganin hakan yasa ta ja dogon tsaki, a fusace ta juya ta nufi office na GAT, tana zuwa ta ce mashi tana son wannan Nirash ɗin ya kaita shopping yau, kuma idan ya kaita shi zai ɗauko kayan ya shigar mata cikin mota, idan ta dawo gida ma haka ya ɗauka ya shigar cikin gida.
Cike da mamaki daddy ya tambayeta meyasa? Sai ta ce ai ya cika girman kai da jiji da kai, tana son ta sauƙe mashi. GAT ya gano, dama shi yasan halin Arya bata son raini, dik yadda aka yi Leo ya nuna mata ƙasƙanci ne, haka take, bata ɗaukar raini, bata ɗaukar walaƙanci.
"Baby Nirash suka ƙarƙashin Mission ne, babu wani soja dake da iko da su kai tsaye, dole sai sun gama mission sun dawo cikin barrack da aiki shi ne nike da ikon sakasu komai, yanzu suna ƙarƙashin ministan tsaro da gwamnati ne, ba sojoji ne kamar sauran sojiji ba, saɓawa dokan soja ne sanyasu wani aiki, ko shi Noor da na bashi wannan aiki akwai dalili". Ya ɓoye mata cewa saboda Noor ƙanin matarsa ce, sai ya fake da cewa akwai dalili.
Sam bata ji daɗin waɗan nan kalamai ba, ta so daddy ya bata power ta wahalar da Leo, amma ba komai, zata gwada mashi ɗiyar GAT take.
Ganin tana cikin ɓacin rai ne yasa GAT ya ce. "Baby yakamata ki koya mashi hankali ne da kanki ba sai daddy ya shigar maki ba, ki kwaci ƴanci da kanki, ba ke mace bace? Ki gwada mashi dik wani jiji da kan namiji a gaban mace ba komai bane". Dan ya sanyaya mata rai ya faɗa.
Ta ji daɗin kwarin gwiwar da ya bata, a fusace ta juya ta fita, ko kaɗan bai damu ba, dan shi yana son ya ga yaransa suna yin abin da suke so, kuma suna kwatawa kansu ƴanci.
Tana fita suka ci karo da Manassa wacce ita ma bata jima da barin office na GAT ɗin ba, ta tsaya a gefen office ɗin tana chat da Vash, lokacin da Arya ta zo wucewa ranta a ɓace ne yasa bata ga Manassa ɗin ba, yanzu kuma daddy GAT ya kwantar mata da hankali, zuciyar ta ɗan yi sanyi.
"Bloody daddy ya ce mu je sir Noor ya kaimu shopping, suna wajen parking lot"....... Haɗe rai Arya ta ƙara yi kafin ta wuce gaba Manassa ta rufa mata baya.
A zaune suka isko su Noor suna jiransu, Arya na zuwa ta ce lallai sai V ta dawo gidan baya sun zauna su huɗu kamar yadda suka saba, ai Noor boy ɗin daddynsu ne, kuma driver ɗinsu, dan haka ba zata zauna a gidan gaba.
Yana jinsu bai ce ko ƙala ba, ita kuwa V ta ce ba zata koma baya ba, Angelina ta ce Arya ta kyaleta, ita kuwa Arya ta ce ba zata kyaleta ɗin ba. Ta zo ya buɗe gidan gaba na motar zata figota waje kenan daga bayansu suka ji an ce. "Me hakan?".
Da sauri suka juya, ganin Zaynish yasa Arya haɗiyar yawu, dan idan akwai wanda take tsoro a cikin sojojin team ɗinsu su biyo bayan Leo and Zaysh. Kun san dik cikin sojojin nan ma Zaynish ya fita daban, baya shiga harkar kowa, baya da yawan magana, ga ɗan banzan zafin rai, ba shiyasa basa shiri da Leo ba, to dik basu da sauƙin kai, kowa ji yake shi sarki ne, kunga kuwa ai ba zaman lafiya.
Sake V Arya ta yi, ta fi jin shakkar Zaynish ma sama da Leo, dan da suka je Mission tana ganin Leo yana hira da Noor, amma Zaysh kullum fuska a ɗaure, ba zaka taɓa ganin yana magana ba, kuma kullum kansa a ƙasa. Ja da baya ta yi, da sauri ta shiga gidan baya na motar Noor bai yi magana ba ya tada motar yana ɗagawa Zaysh hannu.
Kun san me? Zaynish baya banbanta su Arya, dan bai taɓa ɗaga idanu ya masu kallon tsab mai kyau ba, yanzu bai san ma wace daga cikinsu yai wa magana ba, ya ɗauka Arya V ce, saboda Noor kuma yai maganar.
To bari mu taƙaita wasu abubuwan. After some days.
A yau takasance ranarsu ta karshe a AZURE, dan yau zasu tafi Mission nasu na uku kuma a arewacin AVARIS, Tamkar yadda aka shirya masu komai a farko ne, sai dai a wannan karon an basu ƙarin makamai sosai, ƙarin abinci da ƙarin magunguna, bugu da ƙari an basu ƙarin kayan sakawa, watau uniform.
Leo ya buƙaci da a basu laptop ɗinau after nasu Arya, dan haka su ukun nan, Zaynish, Noor and Leo ɗin an basu laptop ɗai-ɗai, su Arya an basu postol gun. Sun shirya tsab, su kashe ko a kashesu, sun shiryawa mutuwa a kowani lokaci.
A wannan tafiyar ma daddyn Noor ya zo yai masu sallama, Aryan and guru sun zo, amma Leo bai zo ba, Abba da kansa ya zo this time, ya zo kuma tare da Rimsha, Aryan ne ma ya ce Abba ya je da ita dan ta ga Vash, aure tsakaninsu ba fashi. In ƙara taƙaice maku dai a yau jirginsu ya ɗaga zuwa arewacin AVARIS, an umarcesu da kada su bar ɗan ta'adda ko guda ɗaya ya yi saura, su kama kowa, su ruguje komai nasu, sun kuwa karɓi umarni.
A wannan karon Ummie ta zo, tana cikin damuwa sosai, saboda yanzu dangin mijin nata sun sake sakota a gaba ganin Zaynish an ɗauki lokaci bai dawo ba, har dukanta ranar amarya ta yi, shi kuwa Faisal yana can yana faman neman yadda zai yi ya rufe masu asiri, yana ta addu'ar ALLAH ya bashi sa'a ya samo gold ɗin nan.
Baiwar ALLAH ko da ta zo bata faɗawa Zaysh abin dake faruwa ba, ta ɓoye, sai ta nuna mashi tana cikin matuƙar farinciki sosai, ya ji daɗin ganinta, ya rungumeta yana jin tamkar kada su rabu, amma ina, lokacin da Captain yai kira dole ya rabu da ita, yana ɗaga mata hannu suka shiga cikin jirgi, ita ma sai ɗaga mashi hannu take yi.
Sai dai ta faɗa mashi cewa ta samu ciki amma cikin ya zube, bata faɗa mashi cewa amarya ce ta daketa har cikin ya fita ba, ta dai ce mashi ta samu ciki amma bai zauna ba. Ko Faisal ɗin bata faɗa mashi sanadin zubewar cikin ba, dama yana zuwa ganin gida dik karshen wata, tin kafin ya zo cikin ya zube, ya kira abokinsa likitan da ya taimaka masu har suka samu cikin, ta je asibitin yai mata wankin cikin, ko da karshen wata Faisal ɗin ya zo taki faɗa mashi ga dalilin zubewar ciki.
Da ya tambayi dalili ta ce faɗuwa ta yi kan dutse, ya dinga faɗa, ya ce in ALLAH ya basu wani cikin ko tsinke bai yarda ta ɗaga ba, ya dinga faɗa har kamar zai doketa, abin da suke wahalar nema tsawon shekaru ALLAH ya kawo ta yi sakaci da shi har ya fita, ya faɗa ya nanata. Sai hakuri ta dinga bashi.
Ita kuwa amarya ƴar banza, har yau cikin da take ta ikirarin tana da shi ɗin yaki bayyana, idan baku manta ba almost 8 to 9 months kenan yanzu, ba ciki ba labarinsa, ko ina cikin ya yi?......... 👀
Anya ma ba shiyasa ta zubarwa da Aunty Ummi nata cikin ba? Dan tasan ita bata da shi, jama'a ku duba mun wannan lamari fa!
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-11.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 47
Karfe 4 na yamma daidai jirginsu ya ɗaga sai arewacin AVARIS! Sai farinciki suke yi zasu tafi babban mission, while basu san abin dake wajen ba, su dai suna murna kawai.
WS-HOSPITAL.
Cikin kwanaki ƙanƙanin su Maya suka yi mugun sabo da babys ɗin nan, abinku da suna yi wa yaran wanka kullum, su shafesu da mayuka, su gyarasu, basa hutawa aikinsu kenan, shiyasa suka yi mugun sabo da su, kun sansu kuma da shegen son yara, sai yara suka shiga zuciyarsu, shi darling dama ba'a magana, dan wlh wani irin mugun so suke yi wa babyn nan ba kaɗan ba.
Kamar kullum, sun kammala yi wa babys ɗinsu wanka, sister Maya tana zaune rike da darling tana mashi wasa, yaro ya fara wayau, kamanninsa da Seraphina sai ƙara bayyana yake yi sosai, sai ma idan ya yi shiru yana wasa, ya ALLAH, kamar ka sacesa ka gudu da shi.
Tongue ɗinta sister Maya take ta faman zura mashi a cikin baki yana sha, in ya fara tsotsa da ta cire zai fasa kuka. Sai mumushi sister Zinta take yi tana kallonsu, while ita ma tana rike da baby ɗaya daga cikin yaran nan.
A lokacin kuma 3D suna cikin wani room a na ban mamaki a wani wajen da daga gani sirrintaccen waje ne, bakina ya yi kaɗan ya iya zayyana maku yadda wannan ɗaki yake, amma tin daga kan matakan tsaronsa, yadda yake da kofa mai amfani da tsaron wutar lantarki, babu wanda ya isa shiga wajen ba tare da izinin 3D ba, kana taɓa kofar wlh mutuwa zaka yi, lantarki ne zai jaka, zaku rantse da ALLAH lantarki kasar gabaɗaya aka karar da shi a wannan hospital ɗin, ta ko'ina haske sosai.
A cikin wannan ɗaki gabaɗaya wasu mahaukatan injuna ne wanda zaku zaci factory ne, engines masu karfi, waɗan da suke sarrafa abubuwa, akwai ɗakuna dayawa a cikin wajen wanda ganinsu kawai tashin hankali.
Kewaye 3D suke ta faman yi a cikin wannan ɗaki suna duba yadda ake aiki, waɗan nan injuna suna ta faman haɗa chemicals na wannan cuta tasu mai suna Nexapox-31, a wannan waje ake haɗa shi ana zubawa a kwalabe manya-manyan, nan ne matakin karshe kenan, bayan an ɗauko chemicals da su Maya suka haɗa, sai aka ɗauki asalin kwayar cutar da aka ruɓar, to a nan ake gaurayasu, cutar ya yi green sosai da sosai gwanin ban tsoro ma da tada hankali, daga yanayin ruwan cutar idan ka gani kasan wannan bakin zalunci kawai aka haɗa, sai ka ji karjinka ya buga.
Komawa 3D suka yi office na Dr James, saboda sun duba cutar, abin da ya kawosu yi kenan. Can cikin meeting room ɗinsu suka shiga, a saman sofas suka zauna, shi kuma Dr James ya miƙe, computer ya buɗe tare da cire mata password, danna wasu lambobi masu zubin na sirri ya yi.
Jim kaɗan aka ɗaga kiran nasa, a tinaninsu Dr Kamal zasu ga mutane kamar yadda kowa yake bayyana idan zasu yi waya ta kasuwanci, sai suka ga akasin haka, domin kuwa wani irin duhu ne bakinkirin ya mamaye ko'ina a cikin computer.
Rarraba idanunsu suka yi suna jiran ganin haske ya bayyana mutum ya bayyana, sai suka ji shiru, can kuma suka ji wata fasasshiyar murya an ce. "Hello".
Kara zazzaro idanu suka yi, babu dai alamar mutane a wajen. Da suka zuba idanu sosai a saman computer ta gefe sai suka ga an rubuta WORLD SYSTEM, sun sha madarar mamaki, bayan shekaru 3 suna ta jin sunan WS a bakin Dr James sai yau suka taɓa ganin yana waya da su. Sun so ganin fuskokinsu, dan suna zargin kamar ba mutane bane ma, amma sai dai ina, bayan Dr James babu wanda ya sansu a duniya!. Watau su Dr Kamal dik rashin imaninsu sun jinjinawa WS har suke ganin kamar ba mutane bane su ɗin, tab! Babbar magana!!.
Daidaita natsuwarsa Dr James ya yi kafin ya amsa masu hello ɗin, sannan ya ce. "Nexapox-31 is ready, ko a wannan sabuwar shekara da zamu shiga zaku iya sakinta wa duniya"....... Shiru aka ɗan yi na a ƙallah 2 mins, can wannan fasasshiyar murya ya sake cewa. "Wa sabuwar gwamnati muka shiryawa, sai bayan zaɓe, me karfin gudun aikinsa? Hope ya fi cututtukan da muka saya a baya?".
With full confidence Dr James ya ce. "Wannan ya fi dik wata cuta da ta bayyana a baya! Wannan tana tafe da su DNA, cuta ce daka iya fata-fata da ɗan adam, wannan cuta idan kana da rabon rayuwa ma ka rayu to zaka rayu ne babu kunnuwan jin magana, dan sai ta yi fata-fata da kai, bugu da ƙari wannan cuta tana ɓoyewa ne a cikin jiki na tsawon sati biyu, sai ta shiga jiki a hankali ta lalata dik wani garkuwar jiki, sannan take bayyana, a lokacin ko ni dana kirkireta yin maganinta zai ban wahala, dan wannan sati biyu da ta yi ta kashe komai na jikin ɗan adam, hakika ban taɓa yin project mai bala'in wahala da karfi irin wannan ba, so ku kwantar da hankalinku, komai zai tafi yadda kuke so".
Shiru aka sake yi na kamar 2 mins, sannan wannan murya ta sake cewa. "Muna son ganin yadda take aiki a jikin mutum, na san ba zaku rasa jarirai a ƙasa ba, ku gwada mana example a kan ɗaya daga cikinsu"........ Kai Dr James ya jinjina alamar to, daga nan ji kake ɗiff sun katse kiran.
Nisawa Dr James ya yi tare da zama kusa da Dr Kamal, a sanyayye ya ce. "Wasu mutane sun kirani jiya, wai suna son babys guda 50 zasu yi sadaukarwa". Ya faɗa yana ciro wayansa........ Cike da mamaki Dr Kamal ya ce. "Ban gane sadaukarwa ba?"...... Dr James yana pressing wayarsa ya amsa da. "Kasan yanzu duniya ta cigaba, irinmu masu kyankyasan jarirai mun fara yawaita, abin ya fara girmama a duniya, so yanzu dik jiga-jigan kungiyar matsafa ta duniya sayen jarirai suke yi dan sadaukarwa, sun daina amfani da yaransu na jini, sai dai su saya kawai su je su kaisu".
Dr Mark ya ce. "Na gani last week wai an kama wata mota cike da jarirai zata fita AVARIS, sai maganar ake yi, daga karshe aka gano manyan kungiyoyin tsafi ce ta sai jariran za'a fita da shi a kai masu, a lokacin na yi mamaki, dik tinanina mu kaɗai muke kyankyasan jarirai, ashe an fara samun ilimin a duniya".
Dr Kamal ya ce. "Duniya ta cigaba, matsafa sai sharholiya, kuma zasu karu a duniya, dan dama kasan wasu saboda bada jininsu ne yasa suke tsoron shiga kungiyar, saboda suna jin ba zasu iya bada ƴaƴansu ba shiyasa ba zasu iya shiga ba, amma yanzu lafiya lou, dik manyan kungiyar tsafi yanzu sayen jarirai suke yi"........ Dr James ya ce. "Ba kowacce kungiyar tsafi take da karfin sayen jariran ba ai, kun sani ba ƙananan kuɗi bane, sai manyan jiga-jigan ƙungiyoyin da suka haɗa ƙasashe waɗan da manya a duniya ke ciki sune suke da karfin sayen jarirai, ko last year babys guda 50 da na cire a yaran da muka kyankyasa wani shahararren kungiyar matsafa na sayarwa".
Dr Mark ya ce. "Haka ne sai manyan kungiyoyi, dan har yanzu ina ga akwai kungiyoyi masu bada jininsu ko in ce ahalinsu ga tsafi, har yanzu cigaba bai zo masu cewa saye kawai zasu yi ba, su zuba kuɗi su samu kuɗi"......... Wani shu'umin one side smiling Dr James ya saki kafin ya ce. "Zamu ɗaga farashin kowa jariri this coming year, daga miliyan 100 zuwa 150, saboda naga yanzu dik sun fara wayewa, kowa baya son wani abin ya samu zuri'arsa, sai dai su saya jarirai, dan haka zamu ƙara masu kuɗi sosai, dan ai kungiyar tsafi akwai makudan kuɗaɗen jini na fitar hankali, dan haka dole mu kara, kai Dr Kamal nabaka nan da one month ka tabbatar ka kawo mana mahaifa guda 500, dik yadda za'ayi ma ayi, idan kashe mata za'ana yi ana cirewa, idan satowa za'ana yi ba tare da saninsu ba, kai koma me za'ayi masu ayi, mu dai mahaifa muke da buƙata!!".
Jinjina kai Dr Kamal ya yi, a dake ya amsa da. "Yazama dole mu samo, amma eggs da muke da su a ƙasa ai basu wuci 200 ba, yakamata mu samu wasu"....... Kai Dr James ya jinjina kafin ya ce. "Tin kwanaki uku da suka wuce na sanya aka yi wa ƴan matan da muke da su dikka alluran gonadotropins wasu kuma follitropin alfa gonal-f, a wannan wata zasu bamu eggs da dama, dan na tsokani ovaries na jikinsu sosai, zasu bada abin da ake so matuƙa.
Dr Kamal ne ya ce. "Waɗan nan allurorin basu yi wa jikin mace yawa ba kuwa? Kada ya lalata masu jinin jiki gaba mu rasa daga in da zamu na samun eggs ɗin"........ Ba tare da shayi ko ɗar bare tausayi ba Dr James ya ce. "Dole zai lalata dik wani kuzari nasu, zai gurɓata jinin jikinsu gaba kaɗan, kowani wata sai an yi masu shi, sai an tsokani ovaries ɗinsu sun fitar da abin da bashi suke fitarwa ba, su fitar da overdose, ai kunsan dole ya lalata masu jiki, amma ba yanzu bane, zasu iya ƙara shekaru 5 gaba suna bamu eggs, daga nan ovaries ɗinsu zai raunata, ya daina ma bada eggs ɗin gabaɗaya, a wannan lokacin amfaninsu ya ƙare, sai dikkansu mu kashesu at once". Babu ɗigon imani a kan fuskansa ya faɗi wannan magana, mata rai 50 kake lissafin wannan allura zai lalatawa rayuwa, baka ji komai a ranka ba, har kake lissafin zaku kashesu gabaɗaya idan suka daina maku amfani suka daina baku abin da kuke buƙata. Already yasa an fara renon wasu matan a wani killataccen waje tin shekaru 5 baya, ba tare da saninsu Dr Kamal ba yasa ake renon yaran wasa idan waɗan nan sun lakace sun daina bashi eggs ya kashesu to ga wasu nan ya kyankyasa ana renonsu sai ya maye gurbi, shegen plan ne da shi.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan musifa dame tai kama, ran ɗan adam tamkar ran kiyashi, ba'a ɗauki mutum a bakin komai ba, ko da yake tin da ka iya kwantar da ƙananan yara, ka buɗe gabansu ka saka masu wannan karfe ka ciri eggs ɗinsu a can cikin cikinsu ai babu abin da ba zaka iya ba bakin shaiɗani, yadda ake cire eggs na mace ya tsaya mun a rai ni kam, ƴan matan dake virgin, basu san komai ba, ba'a taɓa buɗe wannan hanya ba, da yake kai ƙanin ifiritu ne, tsinanne, haka kake danna masu wannan karfe a ciki,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 57 Chapter of 95