Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗauka dama. Ganin kamar akwai matsala ne yasa Dr James ya ce su Dr Kamal su yi gaba yana zuwa, bari ya duba babyn, in bashi da lafiya ne sai ya ajiyesa ya ɗauki wani, da safe zasu duba lafiyansa. SECTION D ya dawo da babyn, su kuma suka wuce SECTION E da sauran na hannayensu dake ta faman barci. A saman gadon yaron ya kwantar da shi yana duba lafiyan jikinsa. Jikin yaron ya yi zafi sosai alamar bashi da lafiya, tin da yaga haka sai ya kyalesa, dan na faɗa maku basa amfani da jini mai rauni, idan jariri bashi da lafiya komai na jikinsa yana raunata, so jikinsa ba zai baiwa jininsa wannan sinadarin da suke da buƙata ba, ko sun razana shi sinadarin da suke so ba zai fita ba, sun yi asarar kashesa a banza kenan. Matsawa gaba Dr James ya yi, a gadon wani jariri ya tsaya, yaron idanunsa biyu yana wasa da ƴan kafafu da hannayensa, ya ALLAH, wlh ALLAH ya yi halitta a kan wannan yaro, da shi dana kusa da gadonsa, kamanninsu ɗaya sak, ya rabb, kyawawan gaske ne sosai, jajir da su, ɗayan babyn yana harci, while ɗayan idanunsa biyu. Yaron nan ya haɗu jama'a, idanunsa dara-dara farare kal a waje, kwayar idanunsa sky blue irin mai hasken nan, da yake dare ne ga idanun nasa a buɗe har wani kyalli yake yi, lips ɗinsa dark purple tamkar an sanya purple lipstick, yana ta zaro idanu waje yana wasa abinsa, tamkar a baka shi ka je ka ajiye ka yi ta kallo. Hannu Dr James ya sanya ya ɗauki babyn, ya kalli fuskansa da kyau kafin ya juya ya kalli fuskan babyn dake gadon kusa da wannan, tamkar an tsaga kara a kamanni, dik yadda aka yi da sperm na mutum ɗaya aka kyankyashi yaran, kuma yaran alama ya nuna sperm na ainahin European ne, dan turawa ne yaran, gashin kansu golden brown mai shegen kyau haka. Saɓa shi a saman shoulder Dr James ya yi, dama ɗaya zai ɗauka, su Dr Kamal sun tafi da huɗu. Bayansu ya bi yana ɗan jijjiga baby, dan yana ji an ɗaukesa ya fara ƙoƙarin kuka, da alama yunwa yake ji. A SECTION E ya isko su Dr Kamal suna tsaye da babys a hannu suna jiransa, yana zuwa suka kwantar da yaran a wannan gado na lantarkin. Suka kunna masu shocking ɗin. Take suka fara wani irin jijjiga, ya rabb, wannan baby ya zaro blue eyes ɗinsa waje tamkar kwayar zasu faɗi ƙasa, ya jisa a wani irin duniyar da bai taɓa ji ba, ya gagara gane menene ma a wajen. Ko gezau 3D basu yi ba, suna tsaye har sai da jikin yaran ya saki waɗan nan sinadaran, sannan ne Dr James ya matsa ya kashe shocking ɗin. Ai yana kashewa wannan baby mai blue eyes ɗin ya fashe da wani irin kuka har muryarsa tana wani irin garrrr-garrrr-garrr saboda tashin hankalin da gangar jikinsa ya shiga. Babu tausayu babu imani Dr James ya jefasu cikin ɗayar injin, yana jin yaron nan yana ihu, ko kyan yaron nan bai duba ya ce ya mashi kyau bari ya barshi ba, haka ya dannasu cikin wannan ball ɗin, suka mayar da marfi suka rufe. Suna rufewa kuka ɗaya mai ƙara yaron ya yi daga nan bai sake ba, injuna sun murɗe mashi wuya. Allahumma ajirni fi musibatin. Shiru 3D suka tsaya har lokacin tarar jini da ɓargo game da garin ƙashi da tsoƙa ya yi, suka ɗauki bokitansu suka zo suka tari komai kamar yadda suka saba, sannan suka wuce izuwa freezers room dan adana jinin......... Nasan jama'a kun ƙosa ku ji me suke yi da ɓargo da garin ƙashin babys ɗin ko? Tin da kun ji me suke yi da jini kam. Ni kaina na ƙosa in sanar daku amma a aikace ba'a labarce ba, na ƙosa ku sani dan irin abubuwan da dayawanku kuke amfani da shi ne, amma mu je zuwa, lokaci zai kaimu da ku ji komai!. Bayan sun adana su ɓargon yadda yakamata sai suka nufi SECTION D dan duba dashen da suka yi na eggs and sperms ɗin nan. Kewaye suka fara yi a cikin wajen suna dubawa, komai na tafiya yadda suke so. Sai dai abu ɗaya da basu yi tsammani ba, eggs da suka cire a jikin matattun yaran can sun fi kowani eggs a wajen karfi da kwari, sun fita daban da saura, da alama sun fi lafiya. A cewar Dr James jariran zasu fi kwari da lafiya, da alama zasu samu maƙudan kuɗaɗɗe da su. Fitowa suka yi bayan sun tabbatar da komai lafiya, suka nufi gidansu bayan sun je office ɗinsu sun cire kayan aikata ɓarnar nasu kenan, suka mayar da kayansu. Suna hanyar komawa gida ne Dr Kamal ya ce. "Waɗan nan eggs ɗin suna da karfi sosai"...... Dr James ya ce. "Sosai, nima na lura da hakan"....... Dr Mark ya amsa da. "Ina ganin mu sayar da babys ɗin kawai kada mu yi drugs dasu". Shiru Dr James ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Dama waɗan nan yadda suke da karfin nan manya ƙasashe zamu sayarwa, dama akwai ƙasar da ta nemi jarirai masu karfi a hannuna dan ta renesu ta mayar da su sojojinta, sai dai su jarirai dubu uku suke so"..... Dr Kamal ya ce. "Suna shirya yaki ta karkashin ƙasa kenan?". Dr Mark ya amsa da. "Zaka gane masu ne? Ai kasan haka suke, sai su reni jarirai a yadda suke son su kasance, su jefasu hukumar soja dan kawai kasashen duniya su razana da karfin sojansu, kaga yanzu akwai ƙasashen da idan aka ambaci sunansu to sai ka ji ana faɗin sojojinsu tamkar ba mutane ba, basu tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani". Dr Kamal ya amsa da. "To ai dama dole sojojinsu su zamana basa tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani, to mutane ne wanda sun taso ba su san komai ba face horon da aka basu, babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, shiyasa zasu iya fito na fito da kowacce ƙasa, basu san daɗin iyaye da ƴan uwa bane, basu san daɗin rai da rayuwa ba, abu ɗaya suka sani shi ne su kashe ko a kashesu". Jinjina kai Dr Mark ya yi. "Haka ne, dayawan manyan ƙasashe haka suke yi, shiyasa duniya take tsoronsu take tsoron sojojinsu, sojojinsu basu tsoron mutuwa, hasalima basu san me daɗin rayuwa ba bare su ji tsoron mutuwa, ba kana gani dik a wajenmu suke sayan jarirai ba, a renesu su zama sojoji, shekaru 17 zuwa 18 ya isa na renonsu". Shi dai Dr James ko ƙala bai sake ce masu ba tin da ya ce sayar da yaran zai yi a mayar dasu sojiji tin da eggs ɗin suna da karfi matuƙa, shi saboda yasan komai sai bai shiga hirar ba, su Dr Kamal ne ba komai suka sani ba, amma shi ya jima da sanin cewa manyan ƙasashe basu cika amfani da ƴan kasarsu matsayin sojoji ba, suna sayen jarirai ne su renesu su kuma horar dasu, so yasan komai. A gate ɗinsu suka tsaya suka yi knocking, da sauri wani guard ya zo ya buɗe masu. Ciki suka shiga Dr Kamal and Dr Mark suna cigaba da hiransu. Lokaci guda suka tsaya cak a lokacin da suka shigo parlo. Slowly Dr James ya sauke kallonsa a kan sister Zinta dake zaune saman sofa ta buga uban tagumi tana ruwan hawaye, while sister Maya na rarrashinta. Wucewa Dr Mark ya yi tin da shi bashi da wani business dasu, ya nufi ɗakinsa abinsa. Kallon juna Dr Kamal and Dr James suka yi. A tare suka tako zuwa in da suke, bai yi magana ba, hannun yasa ya ɗauki Zinta cak suka wuce room ɗinsu. Sai faman tirjewa take yi tana faɗin ya saketa ita kam. Bai direta a ko'ina ba sai a saman gadonsun, a lokacin 5 na asuba ta yi. Fashe mashi da sabon kuka ta yi, zama a gefen gadon ya yi tare da jawota jikinsa yana kokarin rarrashinta. Ai tana zuwa jikinsa sai ta ji karnin jini, kun san shi wani shegen abu ne da baya ɓuya dik da suna cire kayansu su sanya na aiki a jikinsu, amma sai ya kama fatansu ƙarnin, bare ma ace jinin ɗan mutum, shiyasa suke yin wanka idan sun gama zaluncin nasu ai. Ta yi mamakin jin karnin jini a jikinsa, amma sai ta kawar da tinanin da cewa. "Ni ka sakeni"....... Saketa ɗin ya yi yana faɗin. "Menene yafaru kike wannan kuka haka? Yaushe kika tashi daga barci?"........ Tana turo baki ta ce. "Ina ka je? Wajen sister Lazy ko?". Tana dallah mashi hararar da bata san tana yi ba ta yi maganar. Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke, shi ya zaci ma wata matsala ce babba, nisawa ya ɗan yi. "Baki ga mu uku muka dawo bane?"...... Tana kallonsa bata yi magana ba..... "Mun je duba babys ɗinku ne basu da lafiya, akwai babyn da hancinsa yake bleeding shi ne muka je basu magani da taimakon gaggawa, ai kinga ma dikkanmu muka fita a tare ko?". Ajiyar zuciya ta sauke, sai yanzu ta gane dalilin dayasa yake karnin jini, watau babys ɗinsu ba lafiya har da mai bleeding, jinin ya taɓa shi kenan, to yanzu zuciyanta ya yi sanyi. Tafukanta tasa ta rufe fuska tana ɗan murmushi ga hawaye a fuska, wani irin kallon kauna ya bita da shi, har cikin ransa ya ji mugun daɗi ganin tana kishinsa. Dogon hancinta ya ɗan ja game da cewa. "Bari in yi wanka in shirya zuwa office". Ya faɗa yana miƙewa.... Da sauri ta ce. "My Dr nima zan fita aiki yau, ina son ganin babys ɗinmu"...... Kai ya jinjina mata game da cewa. "Ki shirya to mu fita a tare". Cike da murna ta tashi, jiya da bata ga jariran nan ba dik ta damu. After some hours. Rike da hannunta suka fito parlo, yana sanya da kayan aikinsa, ita kuma kayan da ya bata shi ta sanya, doguwar riga zuwa gwiwa, ta kamata sosai a in da ta fito mata da shape na jikinta matuƙa. A parlo ya isko su Dr Mark sun shirya, sister Maya ta yi wanka ta nufi sashin gidansu dan shiryawa zuwa aiki. Gaba Dr Kamal and Dr Mark suka yi, Dr James and sister Zinta suka rufa masu baya. Suna shiga sashen asibitin ya saki hannun district Zinta game da cewa. "Jeki wajen babys ɗinku, anjuma ina zuws"...….... Tin da suka shigo sauran nurses ɗin suke ta faman kallonsu cike da mamaki. Ita kuwa ko a jikinta, ta matsa ta yi hugging ɗinsa game da sumbatar gefen cheek ɗinsa. Kama nata kumatun ya yi shima ya sumbata kafin su yi sallama ta wuce ta bufi SECTION D. Tana shiga taga ɗakin ya ɗan canza mata, durkutsawa sauran nurses ɗin suka yi suna ɗaga mata gaisuwa, fuska a ɗauke da fara'a ta amsa kafin ta ƙariso ciki, cike da mamaki ta ce. "Sister Nazy meyafaru? Ina sauran babys ɗinmu? Naga sun ragu ne". Daidai lokacin sister Maya ta shigo, ita ma durkutsawa ƙasa suka yi suka hau gaisheta. Wacce aka kira da Nazy ce ta amsa da. "Aunty Zinta basu ragu ba, dama haka suke"...... Kai Zinta ta shiga girgizawa alamar a'a kafin ta ce. "Ba haka suke ba, gaskiya sun fi haka sosai ma". Sister Maya da ta shigo yanzu ne ta ce. "Ai dama su 55 ne, na taɓa ƙirgasu a lokacin da muka fara aiki a nan"...... Jama'a ku ce wow, ku tafawa sister Maya!. "Yauwa kin kirgasu ko?". Sister Zinta ta faɗa. Kai sister Maya ta gyaɗa alamar e kafin ta ce. "Gaskiya an ragesu, ha haka suke ba, waɗan nan ai basu wuci 30 ba a nan"....... "To mu kirgasu mu gani". Cewar sister Zinta. Na'am suka yi da zancenta, dan haka sai suka fara ƙoƙarin kirga babys ɗin. Suna kirgawa babys 30 ne ciff, kunga daren jiya ma sun ɗauki biyar. Zazzaro idanu sister Zinta ta yi game da cewa. "Sister Nazy ina sauran babys ɗin?". A kiɗime ta yi maganar. Zazzare idanu dikka nurses ɗin suka fara yi, tsabar babu ƙwaƙwalwa a kansu wai basu san cewa an kwashi yara 25 ba, kuma kullum suna kwana tare da su su tashi da su. Dage mata suka yi a kan lallai su basu san an ɗauki babys ɗin nan ba, su dai kawai suna yi wa yara wanka. Hankalin sister Zinta idan ya yi dubu ne ya tashi, cike da tashin hankali ta ce. "Bari in sanar da Dr James, kila su sun san in da yaran suke"...... Na'am suka yi da zancenta, dik hankalinta ya yi tsananin tashi, tana kiɗime, fitowa ta yi da sauri ta nufi sashin 3D, ita kuma sister Maya ta wuce ta ɗauki ɗan babynta da ta maye gurbin darling da shi wanda yake da rabon kwanaki nan gaba jiya 3D basu niƙa shi ba. Tana ɗaukansa sai ta ji jikinsa da zafi, hakan yasa ta yi gaggawar ɗagowa tana kallon su sister Nazy da suma ita suke kallo, tambayarsu ta yi me ya sami babyn, nan ma idanu suka fara zarewa suma faɗin basu sani ba. Siririn tsaki ta ja game da saɓa babyn a kafaɗa ta fita izuwa office na Dr Kamal dan ta bashi ya duba mata lafiyar yaron. Ita kuwa sister Zinta a kiɗime ta shiga office na Dr James, bata ko bi ta kan office ɗin PA sister Lazy ba, da sauri ta wuce. Tsaye ta iskosa yana ƙoƙarin cire coat ɗin jikinsa ya sanya surgical gown, dan akwai matar da aka kawo daga geferal hospital ɗinsu dake saman WS-HOSPITAL, in baku manta ba ai General hospital ɗin Avaris ce a samansu Dr James, su kuma suna ƙarƙashin ƙasa. To an kawo matar ne zasu cire mata mahaifa, in baku manta ba a farko labarinmu da farkon ganinmu da 3D suna cirewa wata mata mahaifa ne, to ashe daga cikin wannan General hospital ɗin ake shigo masu da matan suke cire masu mahaifa sai a sake fitar da su. Idan mace bata da lafiya, in suka ce tiyata za'ayi mata, bayan anyi mata allura da sunan za'ayi mata tiyatar, in ta yi barci sai su sauketa ƙasa izuwa wajen 3D ta sihirtaccen hanyarsu, 3D kuma su yi mata aiki su cire mata mahaifa, idan sun gama su kaita wannan ɗaki d suke shirya drugs ɗin da suke haurarwa saman nan, fatan kun tuna ɗakin?. Idan suka kaita wannan ɗakin suka ajiye to zasu yi wa babban likitan General hospital ɗin message, shi zai shigo da yaransa su ɗauketa su haurar da ita sama, sai a mayar da ita ɗakin tiyata na General hospital ɗin, su yi kamar su suka yi mata aiki suka cire mata cuta. Wannan mata da kuka gani a farkon labarinsu da 3D suka cire mata mahaifa ma ai daga wannan General hospital na Avaris ɗin ta fito, baiwar ALLAH bata sani ba kawai aka cutar da ita, aka shigo da ita wajen 3D bayan an yi mata alluran barci da sukan za'ayi mata ciyata a cire mata ƙarin mahaifa, shikenan aka kawota 3D suka rabata da mahaifarta. Kun san wani abu? Ko hukuma zata shekara tana binciken General hospital ɗin nan ba zata taɓa samun wani abin zargi ba, ku lura da irin tsarin da aka yi mana, ɓarkar tana ƙarƙashin ƙasa, ko kin ce a wannan asibitin aka cire maki mahaifa wlh ba za'a taɓa yarda ba, saboda babu alamar abin zargi a wajen, ba wanda zai zaci cutarwar tana ƙarƙashin ƙasan hospital ɗin, sai ranar da ALLAH ya yi asirinsu zai tonu ne kawai za'a ga abi da ba'a taɓa tsammata ba. A kiɗime sister Zinta ta ce. "My Dr kazo ka gani babys ɗinmu babu wasu, su 55 ne dama, yanzu kuma saura 30, bamu ga 25 ba". Tsabar kiɗimewa har haɗewa words ɗinta yake yi..... Wani irin rass Dr James ya ji gabansa ya faɗi, tin da suke babu wata nurses mai kula da babys da ta taɓa kirga adadin yaran da suke kaiwa wannan ɗakin har su gama kwashesu, yau ɗaya an samu haziƙan da suka kirga babys ɗin tin a farko kawosu, lallai kuwa akwai matsala....... Nima na ce matsala kam ba karama bama. *Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.* Likes comments and share fisabilillah. QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-29.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 69 & 70 WS-HOSPITAL. Daurewa ya yi game da fara pretending, ya nuna kamar bai gane me take magana a kai ba, a dake ya ce. "Waye ya ce maki 55 babys ne a wajen dama?". Karisowa in da yake ta yi, ta riko hannunsa tana faɗin. "They're 55 sir, we already caunt them since before"....... Nan fa ya ji kansa ta ɗan buga, bai taɓa zatan irin wannan rana ba a rayuwansa, so bai shirya mata ba. Shiru ya ɗan yi yana tinanin solution, katse mashi shirun ta yi da cewa. "Ko dai wani ya sace babys ɗin ne? Na shiga ukuna!". Ganin yadda hankalinta ya yi mugun tashi ne yasa ya jawota jikinsa, bai san lokacin da bakinsa ya kubce wajen ce mata. "Meyasa kika damu da yaran da ba naki ba?"....... Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa. "Because i love them all, ina jin kamar babys ɗina ne, please my Dr, help me to find them out". Ɗan gyaran murya ya yi, ya daidaita natsuwansa kafin ya ce. "Ba jiya na ce maki wasu babys ɗin basu da lafiya ba?"........ Kai ta jinjina alamar e. "To shi ne aka kwashesu kada su raɓawa sauran yaran dake da lafiya ciwo, akwai wata sabuwar cutar da ta shigo mana ne, yanzu muna ƙoƙarin shawo kan cutar, maganin cutar kuka ga mun yi wa wannan darling ɗin naku ai, yanzu saura kwanaki kaɗan mu gama haɗa maganin cutar, daga nan darling zai dawo wajenku, sauran yaran ma za'a dawo da su, amma yanzu a kowani lokacin zamuna zuwa mu bincika yaran, dik wanda ya kamu da cutar zamu kwashesu mu kaisu safe room dan tsaron lafiyarsu har su samu lafiya". Ya faɗa hakan ne kawai dan bashi da mafita, kuma bai yi tinanin lallai zasu jira ranar da zai dawo masu da babys ɗin kamar yadda ya ce ba, a tinaninsa iya son fatar baki kawai suke yi wa yaran, so yana ganin ai zasu mance da yaran kafin nan da kwanaki. Ta aminta da zancensa, dan ta tina ai babyn da Maya take kiransa my boy ma sun same shi da zazzaɓi, hakan na nufin jariran basu da lafiya da gaske kenan, ajiyar zuciya ta sauke game da ɗan sakesa kafin ta ce. "My Dr, ka kula da babys ɗin sosai har zuwa su samu sauki sai ka dawo mana da su, da yamma idan muka tashi aiki ma zamu je mu dubasu". Kirjinsa ne ya ɗan amsa jin ta ce da yamma zasu je su duba babys ɗin, amma sai ya danne. Kai ya jinjina kafin ya sumbaci cheek ɗinta. Murmushi ta ɗan yi game da juyawa, tana murna ta nufi hanyar fita. Bayanta ya bi da kallo har ya fice, nisawa ya ɗan yi game da girgiza kai yana furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa. Tana fita ya kammala shirinsa tsab. Sannan ya fito ya nufi ɗakin da zasu yi wa macen tiyata. A nan ya isko su Dr Kamal suna jiransa a waiting room. Yana zuwa suka ƙarisa ciki. Wata macece kwance a kan gadonsu na tiyata, tana sanye da blue gown irin wanda ake sanyawa waɗan da za'ayiwa tiyata, an shirya komai tsab, daga ganin wannan mata zaku san irin matan nan ne na kauye da basu waye sosai ba, basu san komai ba, cutarta aka yi da sunan ciwo za'a cire mata a mahaifa, kunga za'a cire mata shi gabaɗaya. Cike da taka tsantsan suka fara aikin. Da yake sun kware kuma sun saba yi sai basu ɗauki wani dogon lokaci ba suka kammala komai, bayan sun gama Dr Mark ya ɗauki wata glass ball aka sanya mahaifar a ciki, sannan ya fita da mahaifar ta wata kofa. Su kuma Dr Kamal ya hau haɗa gyara wajen, Dr James yai mata ɗinki tsab, sannan ya ɗauki paper da pen, a natse ya yi rubutu the seme rubutun da ya yi wa matar farko da aka cire mata mahaifa. Ya rubuta a dinga kula da ita sosai, a bata cima mai kyau har zuwa ta samu sauƙi, ta dinga shan abu mai ɗan ɗimi. Ya rubuta magungunar da yakamata a bata kafin ajiye paper kusa da hannunta, ya ƙara gyarata kafin ya kira nurses su fita da ita. Shi kuma ya bi bayansu Dr Mark. A in da suke ajiye mahaifar suka nufa, a nan suka je Dr James ya sanya cikin kwalbar, ya saita na'urar dake jikin kwalbar ta fara bada yanayi daidai da cikin mace, suka tabbatar komai yana tafiya daidai, sannan suka nufi in da suka yi sashen eggs ɗin nan. Kewaye suka fara yi a wajen suna duba dik wasu motsin eggs ɗin. Dr Kamal ne ya ce. "Wai ina Lazy ne yau? Bata bimu ɗaukar rahoto ba".......... Dr James da ya ɗan yi shiru for 2 mins ne ya amsa da. "Ban taɓa sanin Lazy bata da hankali ba sai yau, wai US zata je". Zazzaro idanu Dr Mark ya yi. "US kuma?". Suka haɗa baki da Dr Kamal wajen tambaya. Kai ya jinjina masu alamar e kafin ya ce. "Kila ajalinta ke kiranta, dik da Hussain baya raye, na tabbata su Zayra'an suna da labarin abin da ta aikata bayan mahaifinsu, na tabbata kafin Hussain ya mutu ya basu labarin komai, tabbas sun san cewa Farooq na WS yana rufe, na tabbata suna can suna neman Farooq ɗin kamar hauka, kunga in suka kamata tasan me zai biyo baya". Dr Mark ne ya ce. "Wai dama Lazy tasa aka kama Farooq?"...... Kai Dr James ya jinjina game da cewa. "Ita tasa aka kamasa, a lokacin da aka kama Haiza'an aka tafi da shi ta kira Farooq a waya ta shirya mashi gadar zare da sunan an far masu ya kawo masu ɗauki, yana zuwa aka kama shi, na tabbata Mahvir ba zai kyaleta ba, kai su Zayra'an ba zasu taɓa yafe mata ba". Murnushi Dr Kamal ya yi. "Ai dik a tsananin yunwace suke da nemanta, ta kai kanta ga mutuwa"...... Dr Mark ya ce. "Ba zasu iya ganeta ba fa". Siririn tsaki Dr James ya ja. "Sai dai idan bata ci karo da Zayra'an Bint Haiza'an ba, ina da tabbacin jinin Haiza'an zasu ganeta tsab, domin su baiwa da ita aka haifesu, kyauta ce daga ALLAH ba daga wasu ba, kuma Lazy ta manta abu guda, jinin uwa fusgan ƴaƴa yake yi, bugu da ƙari ta canza komai amma bata

Chapter 84 of 95