Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kansa dake barazanar tarwatse mashi saboda tsananin ciwo da sara mashi da yake yi, musifar ta zarce tinaninsa. Sai da ya ɗauki good 5 mins a haka, ya saita natsuwansa kafin nan ya juyo, ya dawo ya sunkuyo kanta, ya sauke ajiyar zuciya ya fi sau uku, damtsen hannunta ya ɗan buga kaɗan game da cewa. "You really try, and i really appreciate". Sosai ta ji daɗi har cikin ranta ganin yau ya yabawa aikinta...... Ni kam na ce bama dole ya yaba maki ba, irin wannan ɓarna da kika bankaɗo ai wlh ba dik kai ba, za'a tara sojoji 1000 ba'a samu biyu masu kwazonki ba ɗiyar daddynta. Mai da kallonsa a kan laptop ɗin ya yi yana tunanin lallai zai yi aiki tare da Arya, dan ta fi dik mazan nan amfani, team 1 ne kawai suka ɗarata kwazo a wannan tafiya, amma dik sauran wlh ta fisu jajircewa, lallai zai yi aiki da ita, yana son mutum mai jajircewa. Cigaba da kallon wajen ya yi, a cikin wani tanti suka gano wani waje tamkar makaranta, ga board da komai, kuma ga alamar rubutu a jikin board ɗin, amma ya gogge ba su iya gane me ake karantarwa a wajen ba, amma tabbas makaranta ce wajen karantar da ƴan ta'adda. Babban abin da ya ƙara baiwa Leo mamaki shi ne yadda suke pacaka da ruwar roba bama pure water ba, sun fi bayin ALLAH na cikin gari yin rayuwar ƴanci da jin daɗi. Dik da basu ga ainahin cimarsu ba, amma sun fahimci cima mai kyau suke samu, dan sun ga buhu-buhun shinka ta waje, foreign rice kenan. Tin Leo na mamaki har ya daina, ɗan ƙara rage tsawonsa ya yi game da cewa. "Keep watching they're movements, idan wani sabon abu ya bayyana ki sanar dani, and dik abin da kika gani wanda bamu gani a tare ba make sure you write it down for me, bari in yi meeting da su Zaynish, i will be back in the next 2 hours". Ya kai karshen maganar game da miƙewa tsaye. Waje ya nufa cikin zafa. Bayansa ta bi da kallo tana jin tamkar ta jawosa ta dawo da shi ya cigaba da magana a kurkusa da ita kada ya dakata, amma ba yadda ta iya, tana gani har ya fita. Yana fita ta ce. "Jehan come close to me in baki yi barci ba". Da sauri ta ɗago kai jin ta ambaci sunanta, bata jin turanci, bata gane me Arya ta ce ba, sai da ta nuna mata alama da hannu sannan ta miƙe ta zo kusa da ita, a gefenta ta zauna, Arya ta ɗan jawota jikinta tana faɗin. "Zan koya maki computer my girl"...... Ita dai Jehan bata ji komai ba, kallon laptop ɗin kawai take yi. Arya kuwa ta cigaba da aiki, wani lokaci idan ta yi pressing wani abin sai ta cewa Jehan wannan abu kaza yake nufi, dik da yanrinyar bata jin yaren amma tana fahimtar nufin Arya tin da in tana mata bayani tana gwadawa da hannu. A can kuwa, Leo ya yi wa Noor message kan ya kira Vash and Zaynish su same shi a ɗaki yanzun nan. Ba'afi 5 mins ba sai gasu sun bayyana. Umarni ya basu kan su zazzauna, a dake suka karɓi umarni, suka zazzauna suna fuskantar juna. Cikin natsuwa ya zayyana masu dik abin da ya gani a cikin wannan daji ɓangaren aikin su Arya. Hakika hankulansu ya yi mugun tashi, amma sai suka daidaita natsuwarsu, Noor ya ce. "Okey, the reason why our seniors always saying North is different? Oh, kenan they already knows that akwai gagarumin matsala?". Vash ya amsa da. "Of course, but keep all this aside, let's focus on wancan hayakin, mu gano menene, wannan case ɗin babba ne, sai mun fara gano hayakin mecece a wajen can before mu takalo faɗa da waɗan can riƙaƙƙun yan ta'addan". Jinjina kai suka yi, sun gamsu da kalaman Vash, dole su fara da batun hayakin nan, dan waɗan nan riƙaƙƙun ƴan ta'addan sai sun shirya masu. Gyaran murya Leo ya ɗan yi wanda yasa dik suka ƙara natsuwa suka kuma yi tsit. A natse sosai ya ce. "Zamu raba aikin nan yadda zai fi yi mana sauri da kuma sauƙi"......... Basu gane nufinsa ba, sai suka bisa da kallo suna jiran dogon bayani. "Kowani soja a cikinmu zai ɗauki jami'a ɗaya su yi aiki a tare, hakan zai tafi daidai, zamu tafi da fly drone ɗinsu na sirri, idan mun je wajen hayakin zamu rabu ne kashi huɗu, kowanne zai kama hanyar da zai bi, a kan hanyar da zai bi zai saki wannan drone, jami'ar da suke aiki da ita zata na duba mashi hanyar da yake bi ɗin tana bashi information a kai, hakan zai sa suma matan su bada himma, for now kunga su ukun dik basu bada himma ba, ɗaya ce mai fafutuka". Jinjina kai suka yi, sun yi na'am da wannan shawara....... A kan Noor Leo ya tsayar da idanunsa kafin ya ce. "Bayan aiki ban ce ku ɓige da wani abin ba, dan ma dai an ɗaura ne ba halin in haɗata da wani da na maka canji". Noor ya gane karatun, watau Leo ya gano cewa shi lover boy ne, shi ne har da yi mashi gargaɗi, siririn murmushi ya ɗan yi kafin ya ce. "Amma ai ya halatta idan ta binciko mun abu mai ma'ana in na ji daɗi in bata sumbata a cheek ko?"...... Kunnensa Zaynish ya kama, ya ɗan murɗa kafin ya ce. "Da a iya wannan zaka tsaya to da sauƙi, nasan halinka sarai, zama ka iya mantawa da aiki kuke yi ka zarce wani wajen, ni shawarata a rabasu, a haɗata da wani ɗin kawai tin da a bakin aiki muke, shi ma a haɗa shi da wata". Vash na murmushi ya ce. "Wannan shawara ta yi, kawai a rabasu"...... Buge hannun Zaynish Noor ya yi game da cewa. "In ga yadda za'ayi a haɗa matata da wani kato! Ni da kayana? A ina aka taɓa hakan?". Yana tamke fuska ya faɗa, wai dan ma su san ba da wasa yake yi ba. Shi dai Leo bai ce masu komai ba, ya jawo laptop ɗinsa, ya fito da sunan dikka sojojin da suka zo da su wannan Mission ɗin, sojoji bar one su 34 ne, sai bar 2 team 1 and team 2 su 8, sai kuma su Arya su 4, dik in an haɗa su 46 kenan. Fito da information a kan su Arya ya yi, ya zari V daga cikinsu ya turawa Noor Information ɗinta ta email ɗinsa kai tsaye ta sauƙa a laptop ɗin, a ƙasan information ɗin ya zayyana mashi aikin da zasu yi tare, dokokin aiki da tsare-tsaren da ya dace!. Kada ku manta team 1 dik suna da laptop a halin yanzu...... Daga nan ya zaƙulo bayanan Angelina ya turawa Zaynish da nashi bayanin shi ma. Fito da bayanan Manassa ya yi, ya san ba jami'a bace, surgeon division general ce, amma dik da takasance likitar sojoji a jikinsa yana jin tana da sani kan aiki irin nasu Arya, kuma ya san dik da take surgeon general to fa anbata horon kare kai, dan wannan dokar AZURE ce, harta likitocin sojoji suna karɓar hoto dan kare kansu. Dan haka sai ya ce. "Arvash kira mun Manassa yanzu"....... Miƙewa Vash ya yi, ya fito. Zaune ya iskota suna hira da Juraiz, ta ɗan saki jiki tana biye mashi, a tinanin Juraiz V ce ba Manassa ba, dan shi baya iya rabesu fa, shiyasa ya tsaya sai tsarata yake yi. Take kishin larabawan ta motsa, tamke fuska ya yi sosai game da cewa. "Ke! Sir Nirash na kiranki". Yana faɗa ya juya ba tare da ya kalli in da Juraiz yake ba. A hanzarce ta miƙe, bata lura da yanayin face ɗinsa ba, da sauri ta rufa mashi baya suka shiga tantin Leo. Kamewa ta yi ta sara mashi kafin ta ce gatan nan......... A dake ya tambayeta game da aiki irin nasu Arya shin tana da kwarewa a kai?..... Kai ta gyaɗa game da sanar dashi cewa dik abin da su Arya suka sani ita ma ta sani kamar yadda dik abinda ta sani a ɓangaren nata aikin suma sun sani. Ya ji daɗin jin hakan, sai ya ce. "You can go". Ya faɗa game da dawo da kallonsa a kan laptop ɗinsa. Take ya kwashi bayananta ya turawa Vash da bayanin yadda zasu yi aiki a tare........ Ita kuwa ta zo dab zata fita Vash ya ce. "Daga nan ki wuce cikin tantinku! Dare ya yi". Yana tamke fuska ya faɗa, babu wasa a tattare da shi. Cikin girmamawa ta ce. "Okey sir". Ta faɗa tare da ficewa. Duka Noor ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faɗin. "Ya da tamke fuska mutumin, ko dai ko dai?"..... Kara tamke fuskan ya yi. "Ko dai ko dai me?". Ya tambaya irin ban gane komai ɗin nan ba. Noor ya ce. "Ko dai kana ciki da sister ɗin tamu ce?"....…... Kai ya girgiza game da cewa. "Kawai dare ya yi ne, amma ni bana cikin komai"........ Zaynish ya ce. "In ta yi wari zamu ji"....... Murmushi Noor ya yi. "Kyalesa my Tiger, zai yi bayani ne". Cewar Noor ɗin. Leo dai aikinsa ya cigaba da yi a laptop ɗinsa, ya fito da email na Arya, ta nan ya yi mata hello game da cewa it's Nirash, dik wani information ki saka mun shi tanan, zan duba...... Sosai Arya ta ji babu daɗin ganin ya ce ta tura mashi ta email, hakan na nufin ba zai dawo tantinsu ba, ta so ne ya dawo ko kallonsa ta sake yi kafin ta yi barci, to amma ya zata yi? Haka ta danne tana shafa kan Jehan da ta tada kai da cinyarta tana aiki da hannu ɗaya, dik wani sabon abu da zata gani sai ta yi screen record ta tura mashi. Shi ma ya tasa laptop gaba yana aiki ba kama hannun yaro, tin yana ɗan jiyo hiransu Noor sama-sama na shakiyancin da suke yi wa juna har hankalinsa gabaɗaya ya bar kansu, bai ma san time ɗin da suka fice daga tantin kowanne ya wuce nasa tantin ba....... Wajen wuta Noor ya nufa, yana zuwa yasa hannu ya ɗauki V cak a yadda take zaune ɗin, ta baya ya ɗauketa. Bai direta a ko'ina ba sai cikin tantinsa. A tsakiyar electric mattress ɗinsa ya direta game da sauƙowa, ya zare rigan jikinsa ya ajiye kafin ya haye. Kwanciya ya yi a miƙe, cike da shagwaɓa sosai a muryansa ya ce. "My Juliet, tausa nike so, jikina na mun zafi". Miƙewa zaune V ta yi, ta haye kan flat tummy ɗinsa, damatsan hannunsa dake a murɗen nan ta fara matsa mashi da lausasan tafukanta tana faɗin. "Sorry my Romeo"........ Lumshe idanu ya yi laushin tafukanta na ratsa shi. Ganin haka yasa ta dage ta kara yi mashi sosai tana ta faman yi mashi sannu, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan mazaunanta ta baya yana aikin shafe mata su. Ta jima tana matsa mashi jikin kafin ya juya da ita, ta koma ƙasa shi ya dawo sama, kurawa juna ido suka yi, ya ɗan turo mata baki, a shagwaɓe sosai ya ce. "Julie, I'm in need of something very urgen". Tana binsa da wani irin kallon ƙauna ta amsa da. "What's that?"...... Sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya amsa da. "You"........... Lumshe ido ta ɗan yi game da sake buɗewa. "I'm yours already"..... "Sure?". Yana shagwaɓe fuska ya faɗa. Kai ta gyaɗa mashi alamar very sure ma kuwa. Sumbatar gefen kumatunta ya yi game da komawa gefe ya kwanta, sai ya kawota jikinsa ya rungume. Daga nan ya ce su yi barci. Ba musu ta lafe luff a kirjinsa, ba jimawa barci yai awon gaba da su. A ɓangare Leo da Arya kuwa, tamkar yadda dare yake matsayin rana a wajen ƴan ta'addan nan, haka yakasance a wajensu. Aiki suka sha har karfe 3, tana tare da laptop ɗinta shima yana tare da na shi, sai da nasa ta ɗauke caji ya kare, sannan ya hakura, yai mata dropping messages through sms kan da safe zasu cigaba, da yake dik suna da number abokan aikin nasu, sai ya laluɓo nata ya turo mata saƙon. Yana tura mata ya kashe wayar, yai addu'ar barci ya kwanta. Ba jimawa barci tai awon gaba da shi. Ita ma kashe nata laptop ɗin ta yi, dama ba caji sosai, batteryn solar takusa ɗaukewa, tana kashewa ta miƙe ta ɗauki Jehan da ta yi barci a jikinta ta kwantar da ita saman mattress, ta gyara ta kwanta a gefenta, already su Angelina sun jima da yin barci. Saura sojojin dake sansanin suna bakin wuta suna ta hira tamkar rana ce ba dare ba, su Juraiz dik sun shiga tantunansu. ASUBA TA GARI. MORNING D----O----L 🌅🔥 Asubarsu ta fara ne da farar asuba, shirin yin sallah suka yi, suka yi zaman karatun Alkur'ani mai girma kafin su yi askar ɗin safiya, Leo ya koyawa Noor karatun Alkur'ani na surori biyu daga ta ƙasa, ya fara ɗaukar haddarsu. Around 7 daidai suka tashi daga wajen sallar, suka nufi cikin tantunansu, a nan ne kowanne ya buƙaci ganin macen da zai yi aiki da ita. A can gefe kuwa, safiyar Arya ta fara ne da yi wa Jehan wanka, ta shafeta da mai, sai ta sanya mata kayanta tin da Jehan ɗin bata da kaya, wandon jeans baki da top fari, kayan sun ɗan yi mata yawa, amma haka ta sanya. Arya zata fita zuwa wajen koramarta Jehan ta ce zata bita. Hannunta takama suka nufi wajen koramar. Da zuwansu Arya ta shiga ruwa, Jehan ta tsaya bakin ruwa tana ta faman kallonta, tana murnushin dake kara mata kyau sosai. Watso mata ruwa a fuska Arya ta yi tana faɗin. "Zaki shiga ne?". Ta faɗa game da yi mata nuni da hannu ta alama tana ɗaga mata gera guda Da sauri Jehan ga jinjina kai, dan mayyar son ruwa ce. Alama Arya tai mata da hannu kan ta shigo, da sauri ta cire wandon jeans ɗinta, sai taki cire riga dan an fara kirgan dangi, girma ya fara zuwa, dik tana kunyar cire rigarta a gaba kowa, idan Arya zata yi mata wanka sosai take jin kunya, kawai daurewa takeyi. Arya ta fahimci hakan shiyasa bata takura mata kan ta cire rigar ba. Da rigar ta faɗo cikin ruwa. Angelina dake tsaye a can nesa ne take mamakin yadda Arya take wasa da Jehan, sun dai san Arya macece miskisla mai mugun shariya ga mutane, ko su da suke ƴan huɗunta ma bata sakewa da su har haka bare mutanen waje, makaranta wannan ba'a gani a waje sai dole, bata murmushi bata magana sai aiki, abin ya yi mugun basu mamaki, lallai sun yarda so gamon jini ne. ALLAH ne ya haɗa jinin Arya da Jehan. Jawota kusa da ita Arya ta yi tana faɗin. "Kada ki je ta bakin nan ruwa ya tafi mun dake". Riko hannun Arya ɗin ita ma ta yi suka cigaba da juyi a cikin ruwan..... Unexpected suka ji hayaniya ya fara tashi daga cikin sansaninsu, Arya na ƙoƙarin saurarawa ta gano menene sai ga Manassa da gudu tana faɗin. "Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu".......... Toh fah, Fulani sun biyo sahu, sun zo ɗaukar fansa. *Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.* Likes comments and share fisabilillah. QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-30.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 71 & 72 D-------O-------L🔥 "Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu". Siririn tsaki Arya ta ja tare da kama hannun Jehan suka fito daga cikin ruwan, bathrobe ɗinta ta sanya game da ɗaukar sauran kayanta suka nufi sansanin nasu. Sai dai suna isa suka isko gabaɗaya fulanin a tare waje guda, sun durkusa a kan gwiwowinsu, dik sun yi tsuru-tsuru da idanunsu da suka yi jajir, ido ya raina fata, sun ci jibga a hannun sojojin AZURE. Zaynish ne ya umarci sojojinsu da su tattabkesu da bulala, su zanesu da kyau sai sun gane wajen wuta suka kawo kansu. Aikuwa sojojin suka ciro zabga-zabgan bilalu suka rakasu, suka fara basu a jikinsu, suka daka masu tsawa kan su taru waje guda, sannan suka dinga zane masu jiki har wajen huts ɗinsu suka je suka kamo waɗan da suka gudu suka dawo da su, zanesu da kyau suka yi, Leo yana ɗaki ko leƙowa bai yi ba, Noor ma yana ɗaki da V dake barci, while Vash yana ta baya yana waya da su Ammie. Shi ma Zaynish ya fito yana waya da Aunty Ummie ne Fulanin suka iso kansa da sanduna, wai zasu dakesa, aikuwa ya ce bashi da lokacinsu, ya umarci sojojinsu da su zanesu, kada su harbesu da bindiga ko su ji masu ciwo, a'a, bulala zasu masu shi ne daidai da su, dan rashin duka ne yake damunsu. Ganin dik suna durkushe a tsakiyar tantunan nasu suna kuka ne yasa Arya dawo da kallonta a kan Manassa kafin ta ce. "Waɗan nan ne suka zo kashe mu ɗin?"...... Waige-waige Manassa ta fara yi..... "Yeah su ne". Tsaki Arya ta ja game da wucewa cikin tantinsu tana jan hannun Arya, dan in ta tsaya tana iya sumar da mutum, dik takaici ya rufeta. A gurguje ta shirya dan tasan Leo na jiranta, a hanzarce ta ɗauko breakfast ɗinta suka ci tare da Jehan, ta dinga baiwa yarinyar a baki har sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta ci nata, bayan sun kammala ta ɗauko biscuit daga rucksack ɗinta ta baiwa Jehan kan ta ci, sannan ta jawo laptop ɗinta. A gefenta Manassa da Angelina suka zauna, Angelina ta ce. "Manassa ina son sir Zaynish fiye da yanda kike tinani, ya haɗu fiye da yadda kike tinani, jiya kin san har mafarkinsa na yi?". Wani irin harara da Arya ta dalla mata bata san ma ta yi shi ba, ta ɗauke kallonta daga kansu ta mayar kan laptop ɗinta. Manassa ta ce. "Gaskiya ya haɗu, amma fa zaki sha bakar wahala a kansa, dan naga ko kallon mutane baya yi, ga fuskansa kullum a tamke"...... Angelina zata sake yin magana Arya ta katseta da cewa. "Aiki nike yi, kuna damuna da shirmen banza, ku je waje idan hira zaku yi". Harararta Angelina ta yi game da cewa. "Bari ki ga wani abu Manassa, ke kula Arya ki yi abin dake gabanki babu ruwanki damu". Ta faɗa tare da jawo wayarta. Number Aunty Ummie ta fitar, kira ta danna mata tana cewa Manassa. "Sister ɗinsa ce, daren jiya sun yi waya, bana jin yarensu but na fahimci sun shaƙu sosai, tana da kyau matuƙa, kin ganta kuwa? Kamar tauraruwa, har cikin raina ina sonta sosai". Angelina ta faɗa a lokacin da wayar ya fara ringing. Zazzaro idanu a kanta Manassa ta yi. "Ke ina kika samo nunber sister ɗinsa kuma?". Cike da mamaki Manassa ta tambaya..... Yatsa Angelina ta ɗaura mata a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru, shirun ta yi a daidai lokacin Aunty Ummie ta ɗaga kiran tana sallama. Cikin harshen turanci Angelina ta ce. "Hello Aunty"...... Mamaki ne ya ɗan kama Aunty Ummie jin turancin turawa, sai kuma ta tina kila daga wajen aikin su Zaynish ne, dan haka sai ta natsu sosai saboda ta iya fahimtar turancin, kunga ba wani iyawa sosai ta yi ba. Cike da girmamawa sosai Angelina ta ce. "Good morning Aunty"....... "Morning how was your night?". Cikin rawar murya Aunty Ummie ta faɗa....... Angelina na murmushi ta ce. "Cool. My name is Angelina, from AZURE barrack, babban friend ɗin sir Zaynish, shi ne ya ce in kiraki mu gaisa". Cike da tsoron abin da zai je ya zo na karyar da ta yi mashi ta yi maganar. Aikuwa washe baki Aunty Ummie ta yi, abinku da jininmu mutanen amana, kun sanmu da alkunya, Aunty Ummie ta ɗauka budurwarsa ce ya ce ta kirata, ta ɗauka kunya ce yasa Angelina bata ce ita budurwarsa ba ce, aikuwa ta yi matuƙar farinciki, ta tarbi Angelina da kalamai masu daɗi, cikin zolaya ma ta ce. "Ko dai kece surukar tawa?". Angelina murmushi sosai tamkar ba zata dakata ba, ta ji matuƙar daɗin yadda Aunty Ummie ta karɓeta, sai ta ce. "Eh...... A'a..... Kawai na kira ne in gaidaki, muna aiki, in ba damuwa zan iya dinga kiranki muna gaisawa Aunty?". Aunty Ummie ta ɗauka Angelina kunyarta take ji yasa take mata kwana kwana, bata san nan yaran GAT basu san kunya ba, kawai tsoron Zaynish take ji yasa taki sakan jiki su sha hira. Cike da nuna kulawa Aunty Ummie macen kirki ta ce. "Ko baki kirani bama ni zan dinga kiranki ina jin ya kike! Tin da daga ke har shi kunki faɗa mun kece surukata to ki kula mun da shi sosai, kada ki bari komai ya damesa, sannan ki saki jikinki, ni Auntynku ce gabaɗaya, dake da shi dik ɗaya na ɗaukeku". A goggece ta yi turancin, amma zaka iya fahimta sosai. Ta faɗa a cikin ranta tana cewa. "Watau already yana da budurwarsa, kunya ce yasa yaki faɗa mata, amma da jiya ta ce zata samo mashi mata shi ne kenan yau yasa budurwar tasa ta kirata, lallai ma, to tasan me zata yi mashi ɗan ƙaniya". A fili kuwa murmushi kawai take yi tana sauraran Angelina ɗin. Angelina ta fahimci turancin Aunty Ummie sosai, sai ta ce. "Thank you so much Aunty, i really appreciate"....... Cike da zumuɗi Aunty ta ce. "Ki tura mun hotunanki ta Whatsapp mana, ina son ganinki kanwata". Sosai ta ji daɗi game da rungume Manassa da ta kafeta da kallo tana faɗin bari ta tura mata yanzu, ita ma Aunty Ummie sosai ta ji daɗi, da haka suka yi sallama cikin mutunta juna da girmamawa. Whatsapp Angelina ta shiga, a take ta zaɓo hotunanta tsala-tsala masu kyau ta tura mata guda biyu, sai ta ɗauko wanda suke su huɗu gabaɗaya ta tura mata game da ce mata su ƴan huɗu ne ga sauran sisters ɗinta. Aikuwa Aunty Ummie na online, da sauri ta buɗe hotunan, har hannunta na rawa wajen ganin ta buɗe. Ya rabb, tana yin tozali da ɗiyar GAT ta ji Angelina ta kwanta mata a rai, yarinyar ta haɗu, bata damu da yanayin shigarta na ƙananan kaya ga kai ba ɗan'kwali ta saki gashi har baya ba, ita dai yarinyar ta kwanta mata tin da Zaynish da kansa ya ce ta kirata ai shikenan. Tana buɗe hotonsu su huɗu sai ta ruɗe, a take a wajen ta ce lallai Zaynish ya samu mata,

Chapter 86 of 95