Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da thobe a jikinsu, while sun naɗe fuskokinsu da rawanin wanda yasa idanunsu kawai ake iya gani, idanun nasu farare tas da shi. Mutane uku ne, kuma da alama manyan mutane ne sosai, dan tin daga kan yanayin shigarsu, yadda suke a natse, amma bayan su na zaka iya gano komai dake bayansu ba sai haske kamar kantarki. Ɗan gyaran murya Dr James ya yi kafin ya ce. "Hope Mark ya iso ku?"..... Ɗaya na tsakiyan ne ya amsa da. "Ya iso mu, mun karɓi saƙo kuma muna godiya matuƙa, kuma zaku ga saƙonku yanzu". Jinjina kai Dr James ya yi. Da rufe bakinsu bai kai mintina biyu na sai computer ta yi ƙara. Yana zubawa alert ne ya shiga babban account ɗinsu na hospital ɗin wanda su dikka suke amfani da shi. Kimani dala miliyan 200 ne ya shiga cikin account ɗin. Hannu Dr James ya ɗaga ya jinjina masu alamar komai ya tafi daidai. Kai suma suka jinjina kafin na gefe ya ce. "A gaskiya waɗan nan kaya suna mana kaɗan, bamu ki kowani shekara mu dinga samun jarirai 500 ba, ku kara kokartawa". Cikin harshen turanci suke magana. Kai kawai Dr James ya jinjina masu alamar ya ji, daga haka suka yanke kiran. Suna yankewa sai ga wata kira ta shigo. Ɗaukar kiran ya yi, wasu mutane ne suma su biyu zaune a saman kujera, amma suma baka iya ganin background ɗinsu, suma dai fuskokinsu a rufe yadda zasu san ba aikin ALLAH suke yi ba. Dr Kamal ne ya ce. "Meke da akwai?"...... Ɗaya daga cikin mutanen ne ya amsa da. "Kaya muke so kimanin 300 a wannan shekara"..... "Zan iya". Shi ne abin da Dr James ya faɗa kawai kafin yasa hannu ya katse kiran nasu, sannan ya shigar da sunansu a list na masu son jarirai shekaran nan...... Ya rab, wai rai ne ake cikinsa yadda kuka san ana cinikin kayan sawa? Tambaya wai me ake yi da jariran ne? Uhm zan warware komai In Sha ALLAH. Yana katse kiran ya zauna tare da cewa Dr Kamal. "Yakamata ace izuwa yanzu dik shekara muna kyankyasan 1000, 150 zuwa 200 ya yi kaɗan, mu kanmu a nan muna da buƙatar guda 300 a kowani shekara, amma ka duba guda 55 kawai muka barwa kanmu, abin ya yi kaɗan". Jinjina kai Dr Kamal ya yi game da cewa. "Haka ne, matsalar mahaifar ce, yakamata mu kara mayar da himma, idan ta kama mu kara masu kuɗi mu koma saya 100 million dan mu samu sosai, yanzu mahaifareda muke da shi a ƙasa dik bai wuci 200 ba fa"...... Shiru Dr James ya yi, nazari ya fara yi kan yadda zasu bi ko ta halin ƙaƙa su samo mahaifa, ya ci alwashin kyankyashe jarirai 1000 a wannan shekara mai zuwa.. ALLAH sarki ƴan matan da ake cirewa kwai sun shiga uku, yanzu za'a haka takurawa eggs ɗinsu, zasu sake matsawa jikinsu da magunguna dan su dinga sakar masu kyau sasai, imagine ƴan mata guda 50 ne zasu bada eggs guda 1000, ya ALLAH waɗan nan yara sun shiga uku, wannan azzalumin Dr James ɗin yanzu zai yi ta danƙara masu allurai da magunguna, dole kowani wata jikinsu ya bada kwai sama da guda 10 zuwa 20, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Wlh da wannan shegiyar tiyatar da ake masu, a zura masu karfe a gaba a zuƙo kwayayyen ma ai kawai balai ne, bare magungunan da ake ɗirka masu, wannan tiyata ta fi komai wahalar da su, imagine karfe a gabanka, a zura har cikin cikinka, har wajen mahaifarka, a zuƙo ruwan eggs ɗinka, kai ya ALLAH ka tsaremu, ALLAH dik yadda zamani zata juya ALLAH ka taimaka mana ka barmu da imaninmu, kasa mu fi karfin suƙatanmu. Dr Kamal ne ya ce. "Bari ma in kira waɗan da muka bawa contracts na nemo mahaifar mu ji, shin guda nawa aka samo?"...... Jinjina kai kawai Dr James ya yi, tare da jingina da jikin sofar ya shiga tsara irin yadda zai takurawa jikin ƴan matan nan su bashi eggs guda 1000 a ƙasa da watanni biyu, innallilahi wa inna ilaihir rajiun. Jama'a zaku yi mamaki idan na ce maku wannan computer da ake hada-hada da shi, ake saye da sayarwa daga ƙasashe da dama ta cikinsa, zaku yi mamaki idan na ce maku lallai mallakin daddyn Lion ne, da wannan computer ake iya buɗe dik wasu mataƙan tsaron hospital ɗin nan, da wannan computer ake juya dik wasu abubuwa, komai a kanta yake, dik wasu bayanai da abokan cinikayya, dik wata ɓarn da komai, tana da mahaukatan matakan tsaro wan daddynsu Lion da kansa ya sanya mata, baka isa bibiyar na'urar ba, kuma baka isa iya buɗeta ba, da karfin tsiya suka kwaceta daga hannunsa bayan sun sacesa, suka ɗauko har da Computer!. Shi ma Dr Kamal bayan ya gama kiran dik waɗan da suka baiwa contracts kan samo mahaifar mata, ya ji guda nawa aka samu, sai ya sanar da su yanzu ba 80 million zasu saya mahaifar ba, sun ƙara ya zama 100, a nemo masu kawai, yana gama basu bayani shi ma ya jingina da jinin sofa ya hau tunanin yadda zai angwance da Maya. A can Avaris kuwa dik ya haukata likitoci suna ta faman sace mahaifar bayin ALLAHN da basu ji ba basu gani ba, sun ji karin kuɗi, gari ya fara rikiciwa, kowacce mace ta zo asibiti ace mahaifarta ya lalace sai cirewa, wasu masu ciki ace ba zasu iya haihuwa da kansu ba sai aiki, daga yi masu aiki a sace mahaifa. Yanzu ta kowani asibiti a faɗin Avaris halin da ake ciki kenan, magana har ta fara yawa, dan har IRON FIST sun fara jin kishin-kishin ɗin maganar, amma da yake akwai wani babban aiki a gabansu sai basu mayar da hankali a kan wancan batu sosai ba. CRYSTAL PALACE.🔥 Lokacin da Aryan ya koma sai ya isko Lion cikin wata shiga ta alfarma, wani irin tsadaddun tail coat fari tas yasa mai kwalliyar zubin na sarauta, tin daga kan cover shoe dake kafarsa zaku san waje na musamman zai je. Ya cire bandejin dake forehead ɗinsa, amma bai cire na hannunsa ba, saboda ya fi jin ciwo a hannun nasa, na kai kaɗan ne. Sai tashin fitinannen kamshi yake yi. Cikin zolaya Aryan ya ce. "Yau mai girma granny zata yi babban bako kenan?"........ Guru dake zaune yana dannar waya ne ya amsa da. "Zaka bisa ne?"....... Da sauri Aryan ya girgiza kai yana faɗin. "Tab! Zuwa RING OF POWER ai sai shi ɗin! Mutanen da in sun gammu tamkar su zare mana ranmu, dan dai kawai ba yadda suka iya damu ne". Ya kai karshe tare da wucewa ciki, saboda ya tina baya, da alamar sosuwar rai a kan fuskansa. Guru ne ya ce. "Let me see him"..... Lion dai bai ce komai ba, ya ɗauki wayansa ya fito waje. Kai tsaye sama ya haye, sai wajen sauƙar private jet ɗinsu, sai tashin kamshi yake yi, yau fuskansa ta banbanta da kowacce rana, yana ɗaure tamau tamkar hadari, idanunsa sun nuna alamar yau babu mutunci. Jiga-jigan guards 8 ne a saman wajen su ke kewaye da jet ɗin, dikkansu cikin bakaken suit masu balain tsada, babu alamar wasa a kan fuskan kowannensu. A tsakiyar wajen ya tsaya, sai kuma ya juyo baya. Yana juyowa guru da Aryan suka zo suka yi hugging ɗinsa, rungumesu shi ma ya yi, still bai yi magana ba, babu ma alamar zai motsa kyawawan laɓɓan nasa. Sun ɗauki 5 mins a haka kafin ya sakesu ya nufi cikin jet ɗin nasu. Cikin zafin jini guards ɗin suka take mashi baya izuwa cikin jirgin, sai da ya shiga ya zauna sannan guards biyar suka shiga tare da shi. Kansa a ƙasa yana kallon wayarsa, amma a zahiri su Aryan yake kallo, yana mugun son mutane biyun nan, a duniya a yanzu dai wlh daga Leo ɗinsa sai su yake so, kai baya ma iya banbanta su ya fi so ko Leo. Idan baku manta ba a farkon littafin nan na faɗa maku Leo yana da kaka, amma kakan nasu basa tare da su? To suna da kakanni mace da namiji, amma da mutum ɗaya suke magana, basa yi wa ɗayan magana, hasalima basa zuwa in da ɗayan yake saboda laifin babansu da ya shafesu. Amma mu bi Lion zaku gani!. jirginsu na ɗagawa basu dira a koina ba sai a birnin ELDORIA cinin ƙasar AVARIS. Ya ilahi, kunga wani irin mahaukacin cikar da international airport na ƙasar ta yi da dubban jama'a da motoci kuwa? Ƴan jaridu ta ko'ina, jama'a manya-manyan a ƙasar dik sun ziyarci wannan airport ɗin, Prime Minister na Avaris da kansa ya dira a wannan Airport ɗin domin tarbar Lion da ya zo masu a matsayin Prince ɗinsa. Jerin comboi na motoci dankara-dankara kawai sai da aka jera motoci guda hamsin ciff waɗan da suka zo ɗaukarsa, sojoji, ƴan sanda, da dik wasu kaki sai da suka dira a wannan airport ɗin, jiniya tamkar filin yaki zasu tafi, motocin sojoji 10 ciff suka zo dan takewa motocinsa baya. The only Prince of RING OF POWER kenan........ Tin da ya sako kafarsa a step na jirgin nan ta koina aka fara kashe mashi pic. Manyan mutane dake tare gefe guda suna jiransa ne suka fara gyara tsayuwa dan ya fito su gaisa. Sai dai tin da ya fito kansa a ƙasa, bai ɗago ba, yana wani irin taku cikin zafin jini, guards biyar ɗinsa suka take mashi baya suma cikin tsananin jarumta, kai tsaye wajen tsadadden motar dake fara tas a cikin jerin bakaken motocin dake fake dan shi ya nufa, gabaɗaya numbobin motar an rubuta PRINCE OF RING OF POWER a jiki, da alama mallakinsa ne kawai motocin, shi kaɗai akewa comboi. A jikin motar ya tsaya tare da juyowa, har lokacin kansa a ƙasa, Prime Minister ne ya fara nufosa cike tsaro da girma, guards ɗinsa suna take mashi baya shi ma. A gaban Lion ya tsaya, hannu Lion ya bashi suka yi musabaha, sannan ya juya ya shiga motarsa, bayan Prime Minister bai sake gaisawa da kowa ba, kuma akwai manya sosai da suka halacci wajen saboda shi, ko meyasa yaki amsa masu?. A jere motocin suka tashi, kai tsaye sai katafaren MASARAUTAR BARTHARUN wacce suke kira da RING OF POWER. Masarauta ce mai ɗimbin tarihi wacce ita ke juya Avaris a yau, su da saurata suke mulki ba siyasa kai tsaye ba. Kamar England, kunga suma da sarauta suke mulkar ƙasa, sarauta ce mai power a ƙasar. To haka Avaris ma, RING OF POWER ita ke da karfi a ƙasar fiye da politics. Masarauta ce da dik wani jarumi ko mai mulki da ya fara mulkan Avaris daga cikinta ya fito, masarauta ce da ita ta kafa Avaris da kewayenta, masarauta ce da ita ta jagoranci mahaukatan mayakanta da basu ɗauki rai a bakin komai ba suka yi faɗa suka kwatowa Avaris ƴanci a hannun turawar mulkin mallaka, shiyasa masarautar take da karfi sosai, ita ta sama masu ƴanci. Kakan Lion namiji shi ya jagoranci mayakansa suka yi fito na fito da Burtaniya a lokacin yana matashi, shiyasa dik wanda ya fito daga wannan masarauta mutanen Avaris mugun girmama shi suke, ana ji da shi, to Lion shi ne the only magajin da masarautar take da shi, shi ne yarima mai jiran gado, Nirash bai san da su a duniya ba, kazalika suma basu san da shi ba, Lion dai shi ne yasan komai, kuma kunga na faɗa maku ya ki faɗawa Leo tarihin iyayensu. Masarautar tana da balain girma, tana da fuskoki biyu da fadoji uku, tana da tarihin mayaka da dawakai, sune suka zo na biyu a duniya a masarautar dake da yawan dawakai da mayaka, su in zasu yi yaki a kan dawakai suke yi, suna da karfin masifa tamkar dawakan nasu, kakansu Lion har yanzu shi yake mulkar masarautar, kuma babansu Lion da Hussaininsa su biyu ya haifa a duniya, amma dik ya rasasu, tin suna raye ma suka bar masarautar. Daddyn Lion zuciyar balai ne da shi, akwai saurin fushin masifa, baya ɗaukar nonsense, baku ji shiyasa su Dr James suka ce sun ci bakar wahala kafin su samu damar kama shi ba? Mutun ne mai haɗari, ya gaji jarumta daga mahaifinsa. Saboda wannan zafin zuciya da ɗan banzan girman kai nasa ya ɗebesa suka yi faɗa da mahaifinsa, shi kuma mahaifin nasa ya yi amfani da power ɗinsa na mulki ya hukuntasa, ya jefasa a kurkukun masarautar tamkar ba ɗan sarki ba, ya ce sai daddyn Lion ya durkusa ƙasa a gabansa ya bashi hakuri, shi kuma daddyn Lion ɗin ya ce da ya bashi hakuri gwara ya sanya takobi ya datse wuyansa ko kuma ya rataye kansa. Kafiyar bala'i daddyn Lion yake da shi, ga shegen zafin kai, aikuwa Iron Sovereign watau King ya ce shi kuma sai daddyn Lion ya ce mashi sorry, ya ɗauki tsawon wata ana ganawa daddyn Lion ɗin azaba, amma taurin zuciyarsa da taurin kansa tasa ya ce sai dai ya mutu a azaba amma ba zai bada hakuri ba. Da mahaifinsa ya ga haka yana tsoron rasa ɗansa sai ya fito da shi, ya ce ya koresa ya bar mashi masarauta cike da sa ran daddyn Lion zai bashi hakuri komai ya wuce. A maimakon ya bada hakurin, sai ya ce tafi nono fari! Wlh yaki bada hakuri, ya gwammaci ya bar family da gatansa ya tafi saboda furta kalmar sorry kawai, ya ce ba'a mahaifi wanda zai bawa hakuri ba! Aka ce ɗan nagada ya fi ɗan na koya, shi ma kakansu Lion ɗin fa haka yake, a lokacin yakin kwato ƴanci da turawa da turawan suka kama shi, a kan ya basu hakuri ne ya gwammaci dik azaban da suka gana mashi, daga karshe duka datse mashi yatsun kafafu, amma dik da haka yaki bada hakuri, yasan halinsa kuma yake ƙoƙarin tursasa mahaifin su Lion da ya basa hakuri. In takaici maku labarin dalilin kenan da yasa daddyn Lion ya komawa US da zama, daga bayan Husaininsa ya ji ba zai iya zama ba, ya rufa mashi baya, dan kamar chewing gum suke! Mahaifiyarsu ta yi ta baiwa Iron Sovereign hakuri kan wai ta bada hakuri madadin ɗan nata, ya yafe mashi, amma sai ya ce yana son ɗansa da bakinsa ya furta wanda kuma shi kansa yasan abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba. Har daddyn Lion ya koma ga ALLAH bai taɓa furtawa wani kalmar sorry ba, kuma tin da ya bar masarautar bai sake waiwayarsu ba saboda bala'in zuciya, sai wani lokaci da mahaifiyarsa bata da lafiya, a lokacin Lion yana da 5 years a duniya, shi ne ya ɗauko shi suka zo, bai je in da Iron Sovereign yake ba, ya duba mamarsa kawai ya bar masarautar abinsa. KUN JI TARIHIN DADDYN LION A TAƘAICE KO?. To Lion ya zo masarautar sau uku bayan babansa ya bar duniya, ɗaya tare da su Aryan ya zo, biyun shi kaɗai, kuma dik yana zuwa ne saboda kakarsa da ita kaɗai ta taimaki mahaifinsa, lokacin da mahaifin Lion ya bar masarautar granny ɗin tasu ce kawai ta ɗebi gwala-gwalai ɗinta ta bashi, ta ce ya je ya saidasu ya rayu cikin farinciki da walwala, shiyasa dik abin da Lion yake yi idan granny ta yi kira zai amsa, yanzu ma ita ta kirasa kan ya zo. And mahaifinsa kafin ya rasu ya faɗa mashi ya kula mashi da mahaifiyarsa, kullum maganarta kawai yake yi, ita kaɗai ta tsaya mashi, ita ɗin uwa ce da kowa zai yi burin samun irinta, so shiyasa Lion yake tare da ita. Abin da yasa baya zuwa wajen kakansa namiji kuma, kakan nasa ya ce ba zai karɓi Lion a matsayin magaji ba har sai ya zo ya durkusa a gabansa ya bashi hakuri, watau ya yi abin da babansa bai yi ba kenan, idan ya yi haka zai karɓesa a matsayin magaji. Shi kuwa Lion ya fuskanci kakan nasa ido da ido ya ce waye ya ce mashi shi Zayra'an yana neman a karɓesa a matsayin magaji? Baya da buƙatar sarauta a rayuwarsa, kai family ma kanta baya buƙata bare wata sarauta, wlh shi Zayra'an da ya bada hakuri, da ya furta kalmar sorry gwara ya kashe kansa. Babbar magana, King ya ga wanda ya fi daddyn Lion izza da isa, watau dik da yasan kashe kai ba kyau amma da ya bada hakuri gwara ya kashe kan nasa. To shi ne suka raba jaha da Iron Sovereign ɗin, saboda ya ce ba zai bada hakuri ba, shiyasa kuma kuka ga Lion ya tsani kalmar sorry, ya ce ba zai taɓa furtawa ba! Kuma waɗan da suke tare da shi ma ba zasu furta ba, yanzu ko kashe Leo zaku yi ba zai taɓa ce maku sorry ba, sun ce da zu furta wannan kalma gara a kashesu! Tin da a kan kalmar aka kori babansu daga dangi, to ba zasu furta ba!......... E to akwai kura, mah people me kuke tinani ne wai?. Tin da suka danno hancin motocinsu cikin katafaren gate na farko na masarautar na fara ganin wasu irin kyawawan mutane masu cikar kyau da haiba, sai dai fa mutanen suna da abin al'ajabi, dik wanda zaku kallah a cikin masarautar yana sanye ne da wata iriyar shiga ta ban mamaki, wasu irin king tail coat suke sanya da. Kuma abin mamaki mazan masarautar su suke yin kitso, mata kuma sai su ɗaure gashin kansu gida biyu su sako jelar ta saman kafaɗa. Ashe ga daga in da su Lion suka gado kitso a kai, daga wajen daddynsu suka gada, shi kuma daddyn nasu kunga daga nan Masarautar ya girma da shi kenan, al'adarsu ce, dole maza suna kitso mai shegen kyau, sai su ɗaure jelar gashin su yi tuntu da shi. Wasu kuma kitso baya wuce dogaye kwara uku suke yi, sai su yi amfani da kitson su ɗaure gashinsu da shi su yi tuntu, style na kitso dai kala-kala, kuma da yake gashinsu yana da tsantsi da kyau, baki da sheki ba karamin kyau kitso yake yi masu ba! A kaf masarautar babu mai golden hair sai Lion, kada ku manta shi ma a wajen mom ɗinsu da ta fito daga kabilar Pamira ya gado golden hair ba daga wajen daddynsu ba. So shi kaɗai ne mai kalar wannan gashi, shiyasa ya kara fita daban a cikin daban na mutanen masarautar. Yana da causin dayawa, da sauran ƴaƴan ƴan uwan Iron Sovereign, amma dai shi kaɗai ne magaji. (Kun san me? Mutanen Ring Of Power nan sun tuna mun da mutane Birnin Black World na littafina na RAWANI ZALINCI! Mutane Big Bro Black Tiger namu, su kuma irin shigar Annabi Isa suke yi, amma su basa kitso a kai, su kuma wannan masarauta maza da kitso ita ce al'ada, mata kuma da tara gashin a ɗaure! Wlh sun tuna mun Black Tiger ɗinmu na amana!.) One thing about mutanen Ring Of Power rana suke bautawa ba ALLAH ba, so ba musulmai bane, harta kakan Lion ba musulmi bane, yanzu haka basu san Lion Musulmi bane da abin ya tsananta, shi daddyn Lion ALLAH ne ma ya tsaga da rabon musuluntarsa, ALLAH ya tsaga bai da rabon wahala, da ya bar masarautar ne ya samu damar musulunta ta dalilin mom ɗin su Lion ɗin, kun san ba zai auri musulma yana matsayin mai bautar rana ba ko? To dalilinsa kenan na musulunta a farko, ita ta koya mashi komai na addini kafin addinin ta tsara shi ya shiga neman ilimi gadan-gadan, dan haka family ɗin Lion masu bautawa rana ne, kuma basu san shi musulmi bane! Bama su san daddynsa ma ya musulunta ba, and Lion bai taɓa zuwa masarautar ya kwana ba, idan ya yi wuta ne ya yi awa biyu a ciki ya koma, da sun san Musulmi ne ai da bala'in sai ya fi haka, rikicin ba zata kare ba!. Tin da motocinsu suka shigo dik wani mai rai ya natsu tsit, kowa ya shiga taitayinsa, dan ba'a taɓa wanda ya taɓa fuskantar Iron Sovereign ya faɗa mashi magana kai tsaye ba sai Lion, ko daddynsa a lokacin da ya yi taurin kai wlh baya fuskantar baban nasa gaba da gaba ya faɗi magana, sai dai ya faɗa a bayansa a mayar mashi. Amma shi Lion ido cikin ido ya dubesa ya ce. "Da in durkusa in baka hakuri gwara na kashe kaina! Kuma ni ban ce maka ina da buƙatar a karɓeni a matsayin magaji ba! Bani da buƙatar sarauta a rayuwata, haka kuma bani da buƙatar family!". Wannan magana ta yi matuƙar gigita Iron Sovereign, domin babu wanda ya taɓa kallon cikin idanunsa ya bashi martani, Lion ne na farko, kuma daga kansa baa sake samun wanda ya yi hakan ba! To wannan dalilin yasa kowa yake shakkar Lion, idan ya zo waje dik wani halitta mai rai natsuwa yake yi. Suna parking na motocin aka buɗe mashi kofa, take busa ya karaɗe ko'ina a cikin masarautar, The Crown Sentinel ya iso, ta ko'ina taken girma ake mashi, dik wasu bayi da kuyangu zubewa ƙasa suke yi a in da suke suna bashi hanya har sai ya wuce. Wlh The Iron Sovereign yana mugun son Lion, kawai ɗan banzan girman kansu na gado ne yasa yake ganin ba zai iya janye batun sai Lion ya bashi hakuri zai karɓesa matsayin Crown Sentinel ba, amma da ya ji ya zo ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da leƙasa ta view ɗin ɗakinsa saboda yana cikin room ɗinsa can saman bene mafi tsawo a masarautar. Kai tsaye babban sashen masarautar Lion ya nufa, in da uwar gida kuma amarya take kenan, kuma ita kaɗai ce matar sarkin, dan su a al'adarsu mace ɗaya suke aure, shiyasa yake da ita kaɗai. Tin daga nesa ake zube gwiwowi a kasa ake kwasar gaisuwa, idan sun durkusa ma sai sun kifa kansu a ƙasa, al'ada ce haka suke yi wa Iron Sovereign ɗin nasu, so shi ma Lion kamar haka suke girmama shi. Kai tsaye cikin katafaren ginin ya shiga. Dik masu gadi a wajen sai da suka zube ƙasa, tare da guards ɗinsa suka shige, sai da ya zo kofar babban parlonsu ya ɗagawa guards ɗin hannu alamar su tsaya. Tsayawa suka yi shikuma ya wuce ciki. Yana shigowa wasu mata suka fara buɗe shi da hayaki wai na addu'ar da aka yo daga rana, Lion zai yi albarka. Ai yana ɗago idanu gabaɗaya matan suka dare suka bashi hanya, wasu har da faɗuwa a garin gudu, ƴan hayakin ƙaniya, ashe wargima waje yake samu, har da wani munafikin fure a kan tiren hayakin da wani munafikin tiraren wuta na tsinke. Dama sai da matan suka ce su suna tsoron yi mashi wannan hayaki, amma granny ta kafe lallai su yi mashi ai ita ta ce. Wai tana jin kamar ba zata sake ganinsa bane, shiyasa tasa a nema mashi rahama daga rana, ai mashi addu'a, dan tana ganin kamar ganin karshe zata yi mashi. Ta tsufa sosai da sosai, komai yi mata ake yi, zata kai 65 years a duniya, to tana jin kamar lokacin tashin ruhinta sama izuwa wajen hasken ranar da suke bautawa ya kusa, dan su basu yarda da akwai mutuwa ba, sun ce tashi sama ruhunsu yake yi, ya shiga cikin hasken rana ya zauna, to kunga wanda ya mutu baya dawowa bare ya dawo ya basu labarin ba haka abin yake ba sun canza salo da dabara, and su a nan gawa konawa ake yi, hasa binnewa, idan ruhu ya tashi sama ya shiga hasken rana, sai shi kuma gawa a konesa a hure tokar ta tabi iska. Kafin Lion ya yi magana ko mutum ɗaya bata rage a cikin room ɗin ba, dik sun fice da gudu. Takowa ya yi izuwa gaban gadon da granny ɗin nasu take kwance. A gefe ya zauna tare da yin ƙasa da kai. Da sauri dik kuyangun dake hidimta mata a cikin ɗakin suka nufi waje, dattijuwar tana ƙudundune cikin bargo kato na alfarma, ga king bed ɗin nata ya yi wani irin masifaffen haɗuwa. Ɗakin haske tankar tamkar tsakiyar rana suke saboda kwayayyen chandeliers na alfarma dake haske ko'ina. Shiru bai iya yin magana ba, yana dai duke da kai, umarnin daddynsa kawai yake bi,

Chapter 51 of 95