Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, Through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave!". Bakinsu a haɗe suka rera wanna zazzafar taken nasu, dan yana rubuce cikin document ɗinsu, kafin su zo sai da suka haddace taken da dik wani dokan soja. Suna kai karshe suka daddage suka buga kafa ɗaya tare da sarawa manyan nasu. Watau tun da suka fara rera wannan take dik wani soja dake AZURE sai da ya miƙe ya kame a in da yake, wannan take nasu yana sanya sojojin su ji tamkar a filin daga suke, yana balain kara masu kwarin gwiwa, motsa zuƙata da gangan jikinsu da tsumasu yake, ga shi assembly hall ɗin akwai las speaker a ciki da in suna taken dik wanda yake cikin GIDAN SOJA sai ya ji, hakan zai sanya su mimmiƙe su tsaya cak game da sanya hannu a goshi alamar girmamawa ga GIDAN SOJA GIDAN WUTA!!!!. Idan aka kamaka ana rera taken baka miƙe ka ƙame saboda girmamawa ga taken ba ma sai ka sha horo sosai! Haddace taken wajibi ne a gareka!. Bayan sun kammala suna sauke ajiyar zuciya a hankali hankali ne Commander ya ce "Ina yi maku barka da zuwa AZURE BARRACK, Ina fatan zaku mai da hankali a kan aiki yadda yakamata?". Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, tamkar saƙaguna haka suka ƙame, doka ce baka isa manya suna magana ka yi magana ba tare da an baka izini ba. Kallon Captain Commander ya yi ba tare da ya yi magana ba. Da sauri Captain ya matsa gaba tare da fara magana cikin tsantsar jarumta. "Nasan kun san dokokin GIDAN SOJA, amma zan sake tinasar daku kafin mu bada umarnin zuwa mataki na gaba". Ya ɗan dakata yana kallonsu. Still ba wanda ya motsa a cikinsu. "Doka ta farko a GIDAN SOJA shi ne biyayya ga manyan Hafsoshi sojoji wajibi ne a kanku, bin umarnin manyan ba tare da gardama ba, ba shawara bace, wajibi ce! Ana buƙatar sojoji su kiyaye dokokin soja da na ƙasa bakiɗaya, abu na biyu shi ne shaye-shaye, an haramta amfani da miyagun ƙwayoyi da barasa a yayin aiki. An hana sata, cin hanci, fyaɗe, da sauran manyan laifukan da nasan kun sansu kuma kun karanta kundin dokokinmu, tunatarwa nike kara yi maku, dan a GIDAN SOJA dik wanda ya karya doka kun san sauran, to gargaɗi ne da jan kunne mai karfi a matsayin na sabbin sabbin ɗauka". Ya ɗan ja numfashi kafin ya cigaba. "Sai doka ta gaba shi ne yin aure ba bisa ƙa'ida ba. Sojoji suna da ƙa'idoji kan lokacin da za su iya yin aure, misali, a wani lokaci baya an tsare wata soja da ta amince ta auri mai bautan ƙasa (NYSC) ba tare da izinin manyanta ba, aka tsareta a prison na soja saboda ta karya dokokin soja kan aure, nasan kun samu wanna labarin a document ɗin da aka baku, sojoji suna da lokacin yin aure wanda sai sun karɓi umarni daga sama! Ba raɗin kansu suke yi ba". Dakatawa ya ɗan yi yana mai da numfashi kafin ya cigaba da cewa. "Horon fisika da na Ilimi wajibi ne a kanku, sojoji dole ne su halarci horo na jiki da na ilimi dan inganta kwarewarsu. Dole ne sojoji su kula da tsabtar kayan aikinsu da muhalli. Ana buƙatar sojoji su kasance a shirye dan kowane aiki a kowane lokaci. Yin ritaya daga aiki yana da tsari da dokoki da dole ne a bi. Sojoji da suka karya dokoki suna fuskantar shari'a a kotun soja dake cikin Barrack ɗin nan. Wannan shi ne dokokin GIDAN SOJA, fatan kun ji da kyau?". Ya kai karshen maganar yana rarraba idanunsa a kansu. Nisawa ya ɗan yi kafin ya cigaba da cewa. "A yau zaku karɓi manyan allurorin da ake yi wa dik wani sabon ɗalibin soja na kariya da sauransu, cikin alluran da zaku karɓa sun haɗa da allurar rigakafin cutar tetanus da diphtheria Tdap, waɗanda ka iya zama haɗari ga rayuwar soja, wannan allura ana yi wa sojoji a lokacin horo na farko kamar ku kenan, idan aka yi maku yanzu kuma sai bayan shekaru 10 za'a sake yi maku. Allurar na biyu kuma shi ne rigakafin cutar hepatitis A da B. Alluran yana kare hanta daga ƙwayoyin cutar Hepatitis A da B. Allura na uku shi ne allurar meningitis, watau meningococcal vaccine, yana kare kai daga cutar kumburin kwakwalwa watau meningitis, abin da yasa za'ayi maku shi dan horon da zaku fuskanta, gujewa ƙwaƙwalenku su kumbura ko su taɓu. Sai Rigakafin zazzaɓin cizon sauro watau yellow fever, yana kare sojoji daga wannan cutar da ake samu a yankunan tropic, musamman a Afirka da kudancin Amurka, so aikin zai iya kaiku ko'ina, dole ayi maku wannan alluran". Ya dakata yana ɗan nisawa. Commander ne ya karɓi zancen da cewa. "Waɗan nan su ne alluran da zaku karɓa a yanzu, dan haka ku shirya". Ya kai karshe yana dawo da kallonsa kan wasu zakwakuran sojojin dake gefe suna kallonsu, basu shiga cikin line ba, horarrun jami'ai ne ta ɓangaren harbi, basu da wasa. "Ku shigo da surgeons generals and nurses yanzu". Captain ya faɗa a dake. Daddagewa sojoji biyun nan suka yi suka sara mashi kafin su nufi gate na hall ɗin. Jim kaɗan suka shigo tare da malaman asibiti da surgeons brigadiers. Nan Captain ya umarci matasan sojojin nan da su gyara tsayuwarsu da kyau su kuma ɗage hannun rigarsu sama dan dikka alluran a damatsan hannu za'a daddanna masu. Haka kuwa aka yi, dik suka gyara suka tsaitsaya da kyau, nurses ɗin nan suka hau bin line by line suka fara yi masu alluran. Abin ku da jarumai, tamkar ba jikkunansu ake fasawa a danna alluran nan ba, suna tsaye kyam tsabar ma sun sanya aikin a ransu. --------------------🔥 A yayin da dikka wannan abin yake faruwa su kuma manyan zaratan general's na sojoji suna can cikin COMMAND HQ suna tattaunawa dangane da yanayin tsaron kasar Avaris, taro na gaggawa ne suka shiga. To mu leƙa Command HQ ɗin mana mu ga me suke tattaunawa, dan yana da amfani a garemu kwarai da gaske.. COMMAND HQ. Ɗakin meeting na sirri na AZURE, bangon ɗakin ma Soundproof, common view bulletproof ne wanda babu wani bullet da zai iya fasashi, dik da ya kasance ɗaki ne mai matuƙar tsaro, amma an saka bulletproof glass sosai saboda tsaro, ga na'urorin leƙen asiri da ke bin duk motsi waɗan dake ciki da waɗan dake waje ko in ce tunkaro ɗakin. Wurin yana da ƙofar shigowa ɗaya da kuma ɗakunan bincike guda biyu kafin a isa ciki. Kai bincike sosai fa ake yi kafin kowa ya shiga, ma'ana kafin manyan Generals ɗin ma su shiga, sai an binciki ID, fingerprint, retina scan. Sannan ga wasu jiga-jigan sojoji guda biyu masu rike da jiga-jigan bindigogi suna tsaye a ƙofar ɗakin ta ciki da waje, ma'ana biyu ta ciki biyu ta waje, sai ka rantse da ALLAH sojojin nan basa numfashi saboda yadda suka kame kam. An kunna jammer na'urorin hana leƙen asiri, anti-drone radar, da surveillance 360 wacce ko yaya aka motsa dan leƙen sirrin cikin ɗakin sai an gano mutum, ko wata na'ura ka tura dan leƙen asiri jammer sai ta ganota. Daga nan zaku san ba ɗakin wasan yara bane a wajen! Kuma ƙananan kai basu zuwa wannan waje!. Manyan Generals na zaune a saman chair na table dake zagaye da ɗakin, irin round table ɗin nan ne, sannan a saman tables ɗin gaban kowani chair akwai sunan jami'in da zai zauna a wajen, wani ɗan karamin sing post ne da sunanyesu. Shugaban sojojin watau THE GENERAL OF THE ARMY THOMAS (G.A.T) yana zaune a tsakiya ta gaba, sauran Generals na a gefen dama da hagunsa bisa rank ɗinsu. A tsakiyar round na table ɗin ga jagorar rubuce-rubuce, da sashen bayanan leƙen asiri, da kuma wani soja mai ɗaukar hoto da recording idan an buƙata. Ƴan jaridu basu isa shiga wannan waje dan ɗaukar bayanai ba, sai dai su jira a waje idan an fito wani daga cikin General ya faɗa masu ga abin dake wakana dangane da tsaro ga kuma irin tattaunawar da aka yi!. Dikka dakakkun Generals ɗin dake wajen suna zaune ne cikin ladabi da biyayya game da nuna alamar girmamawa ga GAT dake wajen, kama daga kan lieutenant general, major general, brigadier General, General, dik suna cikin wannan ɗaki, kun san akwai bambanci tsakanin Lieutenant General da kuma Lieutenant, sannan akwai banbanci a tsakani Major General da kuma Major kawai, su waɗan da zaku ga General ya shigo cikin sunansu ana nufin su ne manya, misali Major General shi ne shugaban dik wasu Majors dake Barrack ɗin, kun gane ai? Wannan General ɗin na nufin mai wakiltan ko shuganan dikka Majors or Lieutenant ko dai wani runduna. Nasan kun gane nufina In Sha ALLAH. Zama yana tafiya cikin ladabi mai tsauri, dan kowa sai an bashi izini kafin ya yi magana. Wani kyakkyawan soja ne ya mike, hannu ya sanya ya buɗe taswirar kasan Avaris a gabansu. Katan taswira ne sosai wanda yake ɗauke da dukkan sassa na kasar, da yankuna da dama sai dai kuma a wasu yankuna akwai alamar jan marks, hakan alama ce da ke nuna yankunan da yan ta'adda su kaiwa kawainiya, su ake wa wannan mark ɗin. Still wannan kyakkyawan soja da ya buɗe taswira shi ya sake buɗe wasu takaddu a saman table ɗin. Takardun ne da suka fito daga hannun sojojin amma ta fannin kwararru kuma gifted waɗan da suke kamar jami'an leken siri na ƙasa, su horo na daban ake basu, ba zaku fahimci irin jami'an da nike nufi ba, dan ba kowa ya sansu ba, su ɗin sirrin ƙasa ne, amma bari mu kutsa ciki zaku gane irin jami'an sirrin cikin soja da nike magana. Duk wani soja da ke wajen a saman table a gabansa akwai coded notebook da pen da wani taswirar na manyan states na ƙasar, rahoton leƙen asiri, da hotunan jiragen yakin maƙiyan ƙasa da ƙasa, wannan kyakkyawan sojan ya sake budewa. Bayan ya kammala buɗe su gabaɗaya sai ya koma saman kujerarsa ya zauna ya kame ƙam, dukansu suka kara natsuwa sosai. Cikin nuna tsantsar isa da girma G.A.T ya mike tsaye, yana miƙewa duka sauran sojojin suka kara nutsuwa sosai. Ɗan gyaran murya yayi cikin kwararriyar turancinsa ya fara magana a natse bayan ya kunna mic dake gabansa, ya kuma kunna recording system na sirri dan su ajiye tarihin kowane zama. "Ina yiwa kowa da kowa barka da zuwa wannan taron, na san kunsan abinda ya tara mu anan, dan dik karshen sati muna yi, domin sanin halin da kasar mu take ciki da kuma sanin irin nasaran da muka cimmawa, kamar dai kullum zamu fara gabatar da abunda ya tara mu ba tare da ɓata lokaci ba, ina son bayanai daga bakin kowannenku, ina son jin wani nasara aka samu da kuma cigaba da muka kara samu a yankunan da ƴan ta'adda sukayi wa kasan nan kawanya". Ya ɗan dakata da yin maganar yana bin fuskokin kowannensu da kallo. Dukansu sun wani natsu suna bin shi da kallon suma, wasu da kallo mai cike da tuhuma, wasu kuma da kallo mai cike da tsantsar ƙauna. In faɗa maku gaskiya? Kowa ya ga GAT sai ya sake kallonsa, kyakkyawan dattijo ne ajin farko, fari tas tamkar ka taɓa jini ya fita, ga balain kwarjini da farin jini, dik in da ya je ana sonsa kuma ana haukar tsoronsa, fuskansa babu alamar wasa ko fara'a, amma a haka kowa son shi yake yi, yana da jajircewa matuƙa a kan aikinsa, idan ya wurgawa mutum waɗan nan dara-daran eyes ɗin nan nasa wlh sai ka ji fitsari ya kubce maka, eyes ɗinsa suna da zurfi da firgitarwa, gasu milk color mai ɗan duhu, kwayar kuma tiger brown, a shekaru zai iya kai 45 to 47 years haka, amma idan kuka gansa wlh ba zaku bashi even 30 yrs ba, yana da kyan jiki matuƙa, ga gashin kansa bakinkirin babu alamar furfura, ba dan na san shekarunsa na gaskiya ba da na ce karya ne bai wuci ɗan 25 ba! Saboda jajircewansa a kan aiki ya tara uban makiya da masoya, babu mai shege mashi gaba bai takesa ba, baya hawa tsarin kowa, sai dai a hau nasa!. (WANI IRIN RAWA KUKE TINANIN ZAI TAKA A WANNAN LITTAFI BAYAN WANNAN YABO DA YA SHA DAGA GARENI?) Cigaba ya yi da cewa. "Ina fatan samun sakamako mai kyau daga gare ku a wannan zama, lokacinku ya fara daga yanzu!". Yana kai karshen maganar ya koma ya zauna a saman kujerarsa. Yana komawa ya zauna wani dakakken soja ya mike wanda akalla zai iya kai shekaru 40-45, fuskansa a ɗaure tamau babu alamun wasa a tattare da shi, ga razani da kwarjini irin na sojoji a tattare da shi, BRIGADIER GENERAL AMEEZAN (BGA) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakimsa. Mic dake gabansa ya kunna, sannan ya fara da cewa. "A gaskiya a nawa ɓangaren an samu cigaba sosai, an samu nasara, mun kashe ƴan'ta'adda a cikin wannan satin a kalla sunkai talatin zuwa arba'in, sannan mun tashi guraren da suke zama, mun hana su zaman gari mun hanasu zaman daji, mun dai samu nasara sosai......". Ya ɗan dakata yana kallon fuskokin sauran sojojin, ya fahimci wasu suna kallon shi ne cike da tuhuma wasu kuma suna kallon shi cike da gasgata shi. Bai damu ba ya cigaba da cewa. "Mun raka yan ta'adda a guje tamkar karnuka, mun hana su sukuni, babu abunda zamu ce sai dai godiya ga sojojin mu da suka sadaukar da rai domin bawa wannan kasa kariya, amma mun rasa sojoji a kalla zasu kai goma, ina jajanta wannan al'amari". Ya kai karshen magana tare da buɗe takardar dake gabansa, rahoto ne na shaidan aikin da yake ikrarin sanyi. Tunda ya fara magana har ya kai karshe akwai wasu generals na sojoji guda biyu da ke zaune a gefensa, sai kallon juna suke suna sake kallon shi, da alamar shakku a kan fuskokinsu, amma babu wanda ya tankasa, dan babu wanda yake magana idan ɗaya yana magana. Gaban General of the army ya turo wannan rahoton nasa yana kara ji da kansa a matsayin sunyi aikin ƙwarai, sai ya koma ya zauna. Wani dakakken soja ne ya sake mikewa cike da nuna tsantsan jarumta. MAJOR GENERAL RAHEEL (MGR) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakakinsa. A kaifafe ya fara magana kamar haka. "Gaskiya ne BGA, ana samun cigaba sosai a ɓangaren tsaro saɓanin baya, a nawa yankunan da nake wakilta an samu nasarori da dama, mun kama ƴan ta'adda sun kai goma sha biyu, muna fatan mu cigaba da samun nasara haka har mu karar da su". Shima ya kai karshen maganarsa tare da buɗe takardun dake gabansa na rahoton shaidan abinda ya fada ya turata izuwa ga GAT. 1 by 1 haka gabaɗaya sauran sojojin suka mike sukai jawabansu. Sai soja guda ɗaya ne bai tashi ba, wani kyakkyawan matashin soja da akalla zai kai shekaru talatin da uku zuwa da biyar a duniya, fari tas da shi, kyakkyawan gaske. Yana zaune shiru yana binsu da ido saboda shi sabo ne a karin girman, satin da ya wuce ya taka matsayin irin nasu bisa ga jajircewa da kokarinsa, karfi da aikinsa ya bashi wannan matsayi, so bai fara aiki ba tukuna, cikin satin nan zai fara aiki shiyasa bai bada rahoton shi ba. Tattara dukkan bayanansu GAT ya yi sannan ya mike ya rufe masu taron a zuwan zai duba rahotannin nasu sannan kuma zai zurfafa bincike saboda tabbatar da gaskiya suke faɗa ko ba haka ba, a bayaninsa na rufe taron ya kara masu karfin gwiwa, ya nuna musu su kara jajircewa dan tabbatar da tsaron wannan ƙasa, ya ja kunnensu sosai ya kuma tsawatar musu a kan su tsaya suyi aiki, su kawo karshen ƴan ta'adda, ya kwarara musu gwiwa sosai sannan ya rufe musu taro da addu'a irin tasa. Bayan rufe taron shi ya fara fita kafin dukkan sauran sojojin su rufa mishi baya. Suna fitowa BGA ya tsaya gaban ƴan jaridu domin basu rahoton abin da suka tattauna a yanzu, ya sanar da su cewa ana kara samun nasara ɓangaren tsaro, sannan ya kara da cewa an yi nasarar kama wasu daga cikin ƴan ta'adda, daga karshe ya rufe masu da cewa ƙasarsu ta kusa tsabtata daga datti ƴan ta'adda, sun kusa kawo karshen ta'addanci da duk wani tada kayan baya, yana masu albishir da za'a samu zaman lafiya mai ɗorewa, ransu fansa ne a kan wannan ƙasa. Yana gama zuba musu kalaman nasa da kowani ɗan ƙasa yake fatan ji, sannan ya wuce zuwa office ɗinsa dake bene hawa na 4 kusa da office ɗin GAT, ya yi amfani da elevator dan haurawa sama. Sauran Generals duka kowanne ya wuce nasa office. Su kuma ƴan jaridu suka fita suka sanar da al'umma halin da tsaron kasar take ciki. (A gaske haka tsarin yake, haka ƴan jaridu ke yawon faɗa mana halin da ƙasa ke ciki bayan manyan sun faɗa masu son ransu, uhm a wannan karon komai zan rubuta shi ne yadda yake In Sha ALLAH, sai ɗan gyara dan armashin labarin da kuma jin daɗin masu karatu!.) -------------------------🔥 A gefe guda kuma an kammala yiwa dukkan matasan sojojin nan allura, nan captain ya bukaci da kowa ya wuce ɗakinsa dan ya huta alluran tabi jiki, za su fara karɓan horo cikin kankanin lokaci. Cikin natsuwa suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya suka nufi inda ya kasance ɗakunansa suke. A tare wasu matasan sojoji su uku suka nufi inda ya kasance ɗakinsu, suna tafiya ne a natse kasancewar yau suka fara sanin juna a assembly hall, da alama dukkansu sunyi maraba da juna, daga yanayin yadda suke tafiya za ka fahimci cewa lallai sun fahimci juna. Room number 1 shi ne ɗakin da suka shiga, dik da kasancewar sun san babu kowa a ciki, hakan bai hana ɗaya daga cikinsu daka sallama ba. Sai dai ga mamakinsu kuwa suna sanya kai a cikin ɗakin suka yi arba da mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. Sun yi matukar mamakin ganinsa dik da cewa sun san mutane huɗu ne a kowani ɗaki, amma sai suka kawar da mamakinsu su ka karaso ciki. Ɗaki ne na matasan sojoji, gadaje ne guda huɗu a ciki, akwai komai na bukata, kowane ɗaki akwai toilet nasa a ciki, toilet guda biyu, gadon nasu irin sama da kasa nan ne, irin gadon ƴan boarding school, ya yi kyau sosai gadon, kowane gado yana shimfiɗe da zanin gado da bargo na lulluɓa, duka kalan uniform nasu na sojoji ne, ga karamin freezer. (Kada ku manta ba wai iya makarantar soja bane kawai a wajen, fili ne na yaye kwararrun jami'an da manyan kasashe suka aminta da kwakwalwarsu, waje ne na yaye gifted a ɓangaren kwakwalwa, karfafa a ɓangaren jiki, zaku gane nufina idan tafiya ta yi nisa, amma kafin nan me kuke tinani a wannan gida na soja? Ya ɗakunan kwanciya na sojijin kasarku yake? Irin na AZURE BARRACK ne?.) Wannan matashi dake tsaye yana goye ne da katan jakansu irin na sojoji a bayansa, da alama kayansa ne a ciki, hannunsa rike da takarda yar karama kaman yana karantawa, kansa sanye da army p-cap. Kusan a tare waɗannan matasa 3 da NOORIEL, ARVASH da ZAYNASH, kusan a tare suka yi mishi sannu, sai dai ga mamakinsu bai amsa su ba. Kallon juna sukayi cike da mamaki, dan dukansu a lokacin da suka fara gabatarwa da juna kai a assembly hall lokaci guda suka sake suka amsa wa juna kasancewar sun san ba su da kowa a nan, kuma wlh jininsu yai mugun haɗuwa cikin ƙanƙanin lokaci tin kafin ma su gane ɗaki ɗaya suke kuma rukuni ɗaya zasu karɓo horo, amma how comes shi suke mishi magana ya ƙi amsa musu?. NOORIEL ne ya gagara hakura da alama shi yana da zalama da son mutane sosai, karisawa gaban matashi ya yi, ya tsaya suna fuskantar juna, cikin ɗan nuna alamar rashin jin daɗin amsa musu da bai yi ba ya ce. "Amma dai ba ka ji mu bane muna yi maka magana baka amsa ba ko?". Babu alamar gayen zai tanka mishi, sai ma raɓawa gefensa da yayi ya wuce, a saman gadon da ya kasance ita kaɗai ce a cikin ɗakin saura biyu duka ɗaya kan ɗaya ne, ita kaɗai ce babu na biyu akanta. A samanta ya ɗaura takardan dake hannunsa, sannan ya kwakkwance igiyar jakar dake bayansa tare da sakko da ita, ya ɗaura jakar itama a saman gado, bai ko kalli in da suke ba. Abin ya basu mamaki sosai, sun san cewa a lokacin da suka zo wannan barrack ɗin, sun ajiye jakunkunansu a ɗakin, ba suje assembly hall da su ba, amma shi kaman bai yarda da su ba, da jakarsa ya tafi. Sororo NOORIEL ya tsaya ya saki baki yana kallonsa cike da mamaki, basu tsammace hakan ba. Shi kuwa yana ajiye jakarsa ya cire p-cap dake kansa. Yana cire hular kyansa ya bayyana, kyakkyawan gaske ne, shekaru ba zai wuce 24 ba, launin fatansa irin pure with ɗin nan ne tamkar madara, yana da dara-daran idanu milk color, idan kuka ga idanun nasa zaku zaci baya kallo sosai saboda yanayinsu kalar cool zubin sleeping eyes kuma. Ba abin da ya fi baiwa matansan mamaki kamar gashin kansa, gashinsa irin golden ɗin nan ne wanda ake kira da (blonde hair.) mai balain kyalli da ɗaukar hankali, ya yi mugun kyau sosai, ya kuma sha gyara sai kyalli yake yi, ga wasu kitson kalba manya-manyan da ya zuba a kan nasa, basu taɓa ganin irin gashin a zahiri ba gaskiya sai yau, bugu da kari da kitso a kansa, hakan ya yi mugun tafiya da imaninsu, and gashin da kitson ya yi balain kara mashi kyau sosai, ai sai suka saki baki suna kallon kyan gashin nan. Shi kuwa, jawo jakansa ya yi ya hau buɗewa, abubuwan da zai yi amfani da su ya ciro, kama daga kan towel, brush, mangoge baki, wani set of lotions na Companyn STARS BODYS LOTIONS, company ne da kaff duniya basu da na biyu a mayuka da sabulan gyaran jiki, ciro lotions da kuma perfumes kala daban-daban masu daɗin kamshi ya yi. Ya kwashesu ya yi hanyar toilet da su. Da kallo suka bisa cike da mamakin yanayin kyakkyawar surar jikinsa, da alama ya jima yana gym ba sai yanzu zai fara ba, kurawa gashin gerarsa idanu NOORIEL ya yi har ya shige toilet, gerarsa yai matuƙar burge Noor, abin da yasa ya burgesa kuma shi ne, a jikin gerar ta gefen dama akwai tsagu guda biyu da suke tamkar yankan wuƙa aka mashi, hakan yasa ya raba gerar biyu daga ta karshe, ta kara mashi tsantsar kyau matuƙa, ba shi ya raba ba, ciwo ya taɓa ji a wajen sai ta zama haka, gwanin burgewa, idan kuka kalli guy ɗin a farko zubin tantiran ƴan duniya ne da shi, amma asalin halinsa shi kaɗai ya santa!. Uhm NIRASH MUHAMMAD HAIZAAN inkiya LEO kenan, jajirtaccen matashi kaifi ɗaya, bayi da wasa kuma baya ɗaukar wasa, mutum ne da abin dake gabansa kawai yake yi, baya shiga harkar kowa kuma ya tsani a shiga tasa, ya fi son zama shi kaɗai, bashi da magana kuma baya son ana magana a kusa da shi, jinin jarumta ne ke guda a jikinsa, ya fito ne daga kaɓilar Pamiri People

Chapter 3 of 95