Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
samu number ɗinsa a phone na dad". Zamewa Arya ta yi ta koma saman bed ɗinta, ta zauna shiru, ita kanta bata san me yake yi mata daɗi ba, afkawa tai cikin tinanin da bata san na menene bane. Bata ankara ba sai ji ta yi an taɓata, da sauri ta ɗago kai, sun kewayeta suna kallonta cike da tausayawa. Manassa ce ta ɗan rungumota game da cewa. "Bloody you should stop thinking about this guy, we know he did wrong to you, amma tin da yanzu ɗaukar fansa ba zai yiwu ba ki bari mana akwai gaba ai". Nisawa ta ɗan yi before ta ce. "Ba zaki gane bane, zuciyata tafasa take yi idan na tina yadda na yi magana ya shareni, kina ganin kowa so yake yi in kula shi, amma shi wannan har ya samu nai mashi magana, ya walaƙanta ni, okey yanzu da students suna nan ma haka zan ji kunya a gabansu?". Tamkar zata yi kuka ta faɗa, da alama tana da riko da zafin zuciya. Hakuri suka dinga bata har ta hakura ta sauƙo, sannan suka koma kan abin da suke yi. Karfe 5 daidai suka fita zuwa mini gym ɗinsu dake ƙasa kusa da pool ɗin gidan. Sai da suka yi push-up guda 30, sannan suka fara ɗaɗɗaga ƙananan karafuna, dik sojojin dake gidan babu wanda yake ɗaga idanu ya kallesu saboda tsoron shiga matsala, amma kuma wlh dik sojan da ya yi aiki a gidan GAT sai ya so yaran nan kamar ya mutu, musamman Arya da V, suna da shegen shiga rai, sai dai soja ya yi ta dakon soyayyarsu ba samu zai yi ba. Dik in suka fito gabaɗaya hankulan sojojin nan tashi yake yi, su yi ta faman satar kallonsu, kuma dik masu tsaron gidan na GAT matasa ne masu ji da lafiya da karfi, kunga kuwa dole kunamar bindigarsu ta dinga harbawa idan suka gansu. 2 hours suka ɗauka suna gym, sai karfe 7 suka ɗan yi linƙaya cikin pool saboda gumin da suka haɗa na wahalar motsa jikin, sannan suka fito, jikinsu dik ruwa suka nufi cikin gida. A zahiri idan kuka ga soldiers ɗin nan zaku zaci ƙasa suke kallo, amma dikkansu harta waɗan da suke shawagi a tsakar gidan, na bakin gate dik kowani taku nasu Arya ɗaya a kan idanunsu, su kuwa bama su san suna yi ba, sai hira suke yi cike da kaunar juna suka wuce ciki. Zuna zuwa suka sake yin shiri cikin kaya iri ɗaya, sannan suka ɗan taɓa karatu kafin su je yin dinner. A ɓangaren Leo kuwa, ransa gabaɗaya a ɓace, dama ga wahalar da suka ci yau, tin da ya zo GIDAN SOJA bai taɓa cin wahala irin na yau ba, kai tsaye office na GAT ya nufa. Da ya je sai da ya tsaya a waiting room, ya tura saƙonsa na son ganin GAT, sannan ya yi zaman jiran a bashi izini. Izinin da bai samu ba kenan tsawon awa biyu, kuma GAT na zaune cikin office ɗin yana kallonsa ta camerar dake waiting room ɗin, so yake ya gwada hakurin Leo, dan yasan irinsu suna da zafin kai da rashin hakuri. Amma ga mamakinsa sai ya ga Leo ya jure zaman jira, in short ya gagara gane alkiblar Leo ɗin ne ma, kansa ta ɗaure gaskiya, sai ya ce bari sun kullah kenan, sai ya san shi ciki da waje. Bayan awa biyu yasa aka shigo mashi da Leo ɗin. A gabansa ya tsaya tare da sara mashi, jinjina kai ya yi kafin ya umarcesa da ya ajiye mashi makullin. Ba musu Leo ya ajiye. Shiru GAT ya yi yana jiran jin ko Leo zai yi mashi wani karin bayani, irin ya ce ya je ya ɗaukosu ya kaisu gida, amma sai ya ji shiru bai yi magana ba, hakan ba karamin mamaki ya sake baiwa GAT ba, wai wannan wani irin mutum ne?. Dan ya gwada shi sai ya ce. "You can go"........ Sara mashi Leo ya yi tare da juyawa ya fita. Da kallo GAT ya bisa yana mamakinsa, watau dai magana ce ba zai yi ba, to lallai yakamata a gyara mashi zama. Kasancewar lokacin dinner ɗinsu ya wuce sai Leo ya nufi room ɗinsu kawai, bai yi dinner ba yau saboda GAT. Can ƙasan maƙoshi ya yi sallama a lokacin shigarsa ɗakin, su Zaysh suna ta faman yin waya da gida, yau suna da damar kiran kowa da rana. Vash ne ya ce yau Friday zai yi sadaka, amma da ƴan room ɗinsu zai fara, to a ƙaidar GIDAN SOJA ɗin in dai zaka zo buɗe maka account nadaga cikin list na kuɗin da zaka kashe a farko, dan haka suna da account na ƙasar amma kamar students account. Dan haka dikkansu Vash ya basu kyautar 1k dollars, Noor ya ce ba zai karɓa ba, da Vash ya matsa sai ya ce ya baiwa Zaynash nasa, haka ya haɗawa Zaysh. Da yake Noor yana da kyawawan zuciya sai ya ce da Zaysh. "Bro ka kira Aunty Ummie mu gaisa, I really like her, Ina jin daɗin yadda kullum take ce mana mu kula da kanmu, mu ci abinci kuma mu yi barci a kan lokaci, tana da kirki sosai kuma tana sonmu sosai". Vash ne ya amsa da. "Gaskiya nima I really kike her, tana da kyakkyawan zuciya"......... Sosai Zaysh ya ji daɗin yadda suke yabon Aunty Ummie ɗinsa, sai ya samu kwarin gwiwar danna mata kira da sauri bayan ya duba time 4:40, yanzu ba jimawa suka dawo daga masallacin sallar la'asar, shi ne suka tashi Noor daga barci. Wucewa ciki Leo ya yi, kai tsaye ya nufi toilet dan shi bai samu sallar jam'i ba, GAT ya sanya shi zaman jira. Bayan ya yi alawala ya zo ya shinfiɗa dadduma ya tada sallah. Bugu ɗaya Ummie ta ɗauka, a lokacin ta gama sha kukan walaƙancin dangin miji, Auntynsu ne ta zo ta dinga zaginta wai taki haihuwa sai cinyewa ɗansu arziki take yi tana kiba, ta mata zagi ta uwa ta uba na cin mutunci, shi ne ta shiga ɗaki take ta faman kuka. Ganin call ɗin Zaysh yasa ta yi gaggawar goge hawayenta, har tana sauke ajiyar zuciya, dan a duniya idan akwai abin dake kwantar mata da hankali bayan karatun Alkur'ani to sai Zaysh, a kowani hali take ciki idan ta tuna tana da kani kamar shi wani irin farinciki take ji. Gyaran murya ta yi ta yadda ba zai gane tana cikin damuwa ba, sannan ta ɗauka tare da kara wayar a kunne. Cike da farinciki ya ce. "Assalamu alaikum Aunty"....... Sai da ta ɗan sake daidaita natsuwarta kafin ta amsa da. "Wa'alaikassalam Zaynish, ya yau ka kirani da rana? Baku aiki ne?". Tin daga maganarta ta farko ya gane tana cikin damuwa, amma sai bai nuna ba tin da yaga tana ƙoƙarin ɓoye mashi ne........ "Yau karfe 2 muke tashi horo, shiyasa na kiraki, ya gida ya kowa da kowa? Ina yayana? Jiya mun yi waya ma da shi"........... Take murmushi ya bayyana a kan face ɗinta, dan in tana magana da shi wani irin daɗi take ji, dik damuwarta ya gudu. "Kowa lafiya lou ya horon naku? Ina abokanka masu kirkin nan?". "Komai lafiya lou, ai su suka ce ma in kiraki, suna son gaisawa dake". Ya faɗa tare da ɗan cire wayar daga kunnensa....... "Ina son yin hira da su amma ban iya turancin sun nan ba, wayasani ma ko basa gane kwaɓata". Ta faɗa tana ɗan murmushi. One side smiling ya saki kafin ya ce. "Suna ganewa mana, ai kema kin iya turancin fa Aunty". "Uhm ni kada ka wani zugani, ina turanci a wanda bai je makaranta ba, kawai waɗan da ake yi a gari na tsinta na iya"...... Nisawa ya ɗan yi. "Kai Aunty, waye ya ce maki turanci wata tsiya ce da har sai an je makaranta ake iyata? Yare ce fa kamar kowacce yare! Sai ki ga wani ga tarin ilimi sosai amma baya jin turanci, wani kuma sai ɗan banzan turancin amma kansa fanko ne, ƙasar da suka san ciwon kansu ma basa amfani da turanci Aunty, sai dai yaren ƙasar!". "Haka ne, to yanzu ina Noor? Basu waya mu gaisa"......... Miƙawa Noor ya yi, yana wani irin bosy smelling ya karɓa tare da karata a kunnensa. Cikin kwararriyar turancinsa ya fara ɗaga mata gaisuwa, daga nan suka ɓige da hira, Zaysh yana fassara mata wasu manyan kalmomi, idan tana son faɗar wani babban magana kuma sai ta faɗa da hausa ya fassara masu Noor da turanci". Sun jima suna waya kafin su yi sallama Noor ya kira Auntys ɗinsa shi ma, cikin ƙanƙanin lokaci ta waya suka saba da family ɗin juna, har in ɗaya ya kira gida a gidan kowa yana haba-haba ya haɗasu da abokansa su gaisa, sun zama kaman ƴan uwa na jini da dangin juna, dangin Leo ne kawai babu wanda ya sansu, ba su taɓa ganin ma ya kira gida a gabansu ba, amma su kowa a gidajensu yasan da ƴan ɗaki, sai dai kuma ahalin kowa basu san da Leo a ɗakin ba. Haka suka kasance cikin farinciki har dare, bayan sun yi dinner sun dawo, dikkansu suka yi wanka suka yi shirin kwanciya. Sai da suka sake kiran gida suka sha hira har zuwa 10 na dare, sannan ne ɗakin ta yi shiru tsit alamar sun yi barci. Leo yana kwance rike da waya yana chatting da gida, shi baya kiransu sai dai chat kawai, saboda shi ƴan gidansu ba zaman banza suke yi ba, dik suna da aikin dake gabansu, basu da lokacin ɓatawa wajen yin wasa saɓanin su Noor masu yi har da video call. So shi idan ya tashi yana dropping masu message ne, dik time da suka zo su yi reply, haka suke. Around 11 duniya ta yi shiru, kowa ya yi barci, kunna light na wayarsa Leo ya yi tare da sakowa kasar bed ɗinsa, kai tsaye bed na Noor ya nufa. Hannu yasa ya fara tashin Noor. Da yake ɗazu da rana ya sha barci sai ya farka a natse, slowly ya waro idanunsa a kan kyakkyawan fuskan Leo dake ta faman sheki. Ya yi mamakin ganinsa, hakan yasa ya tashi da sauri yana kai hannu saman ido. Mustsuke idanun nasa ya yi dan ya tabbatar da abin da yake gani. Tabbas Leo ne, cike da mamaki ya ce. "Bro what brought you here?"....... Baya kaɗan Leo ya ja tare da yi mashi alamar ya sauƙo ƙasa. Ba musu ya sauƙo yana cigaba da kallonsa. Hannunsa Leo ya kama suka nufi door. Noor bai musa ba ya fara binsa, buɗe kofa ya yi suka fita waje. Yana fita ya kashe light na wayansa ya zura a aljihu, a cikin duhu suka cigaba da tafiya har izuwa gym na barrack ɗin. Ko kaɗan Noor bai ji tsoro ba, bai kuma damu da ya tambayi ina za su je ba. Kasancewar Leo yasan gym ɗin tana can baya ne daga idanun mutane, sai ya kunna light na wajen, take haske ya gauraye wajen. Sake hannun Noor ya yi tare da ce mashi ya shirya. Sai a lokacin ya ɗaga idanu ya kalli Leo da kyau, muryansa na rawa ya ce. "Bro me za mu yi a nan?"........ "Training". A taƙaice Leo ya bashi amsa. Shiru Noor ya ɗan yi, yana son tambayar dalili amma yana shakka. Ɗaure fuska Leo yai alamar babu wasa a tattare da shi, sannan ya umarci Noor da ya wuce ya fara push-up, dan wlh ba za su yarda da wannan ragon tan nasa ya dinga sanyawa suna ɗaukar karshe ba, dole ya horar da shi horo na musamman wa shi kaɗai. Ganin babu arziki a kan fuskan Leo yasa ya wuce ya fara yi, waya Leo ɗin ya fitar ta duba time, sannan ne ya ce ya baiwa Noor 10 mins yai push-ups guda 100. Zazzaro idanu ya yi, a ransa ya ce to ai ko Captain almost 20 mins ya basu kuma har three times, shi kuma 10 mins at once? Gaskiya wannan zallar mugunta ce, ganin dai babu wasa a tattare da shi ne yasa bai yi gigin yi mashi magiya ba, sai kawai ya fara. Gefensa Leo ya tsata yana kirgawa, tin Noor na iya kirgawa har ya dawo yi kawai yake yi. Abin mamakin kuma shi ne sun fi tsoron Leo a kan Captain ma, dan kuwa dik wahala da gajiyar da Noor ya yi bai dakata ba, yana tsoron tsayawa ne. Haka ya dinga yi, tin yana daurewa har ya saki ya fara kuka, ko a jikinsa Leo kam, bai damu da kukan ba, sai ma rungume hannaye a kirji da ya yi yana kallonsa. Ko guda hamsin bai cika ba mintuna goman nan suka cika, nan fa Leo ya ce ya sake farawa daga farko, yau ba zasu tashi daga nan ba har sai ya yi guda ɗari a mintina goma. Haba kuka sosai Noor ya fara yi, hawaye bibbiyu, daga karshe majina da yawu dik suka fara zuba, Leo ko kaɗan bai ji kamar zai kyalesa ba, haka bawan ALLAHN nan ya dinga maimaita almost sau takwas, amma ya gagara yi a ƙasa da mintuna goma, dik wani sauran karfinsa ta kare, jikinsa ya jigata, kafafunsa da hannayensa kerma sosai suke yi, sai haɗa uban gumi yake yi. Shi kuwa Leo ya ce ko mutuwa zai yi yau sai ya yi a kasa da mintuna gomar nan, ko kwana ne sai sun yi a nan. Tin 11 ake abu ɗaya har karfe 1 sannan ya samu ya yi a ƙasa da mintuna gomar, sake cewa ya maimaita Leo ya yi, ya maimaita ya kuma yi a ƙasa da mintuna goma, da alama ta shiga kansa sosai wannan horo. A maimakon Leo ya barsa haka ya huta, sai ya sake sanya shi 100 sit-ups and 80 burpees, yaron nan kuka yake yi tamkar ransa zai fita, Leo bai ɗaga mashi kafa ba, har ta kai dakyar yake numfashi, har yana neman sumewa a wajen, amma Leo bai tausaya mashi ba har sai da ya yi waɗan nan training ɗin dikka. Around karfe 3 ya kammala cikin ƙaida, sannan ne Leo ya ce su tashi haka nan sai kuma gobe..... Babbar Magana, kenan Leo kullum dare zai dinga hora Noor? Lallai Noor yana cikin lukutar musifa, ga horon rana ga kuma na dare, bawan ALLAH ba hutu kenan. Gagara miƙewa a kan ƙafafuwansa ya yi, dan jikinsa dikka wani iri ɓari mai ban tausayi yake yi, idanunsa har sun kumbura, tsinin hancin nan nasa jajir kamar an shafa wani abin, ƙasan idanunsa dik sun yi jajir. Ganin ya gagara miƙewa ne yasa Leo tura wayansa a aljihu, sannan ya saɓesa a kafaɗa suka nufi waje. Kai tsaye room ɗinsu suka koma. A saman gadon Noor ya kwantar da shi tare da wucewa nasa bed ɗin. Har ya kwanta sai ya ji Noor na numfashi sama-sama tamkar zai mutu, hakan yasa ya sauko ƙasa, jakarsa ya ɗauko, tare da fito da wani drugs, sannan ya ɗauko bottle water, dan su da shi suke amfani, iya matsayin kuɗin iyayenka iya shagalinka!. Wajen gadon Noor ɗin ya dawo, miƙar da shi zaune ya yi tare da ɓalle drugs ɗin guda bibbiyu, ya ɓalle bakin robar ruwan, sannan ya bashi a baki. Dole ya buɗi baki ya karɓa, bayan ya sha Leo ya koma bed ɗinsa, ya mai da sauran drugs ɗin, ya kuma ajiye ruwan kafin ya haye ya kwanta. Shi ma Noor kwanciya ya yi, kusan a tare barci yai awon gaba da su. Washegari, yau ta kama Saturday, babu horo suna off. Tin da sassafe suka tafi yawace-yawacensu a cikin barrack ɗin, dan ba'a yarda su fita waje ba idan suna karar horo. Zaynash ya ce bari ya je yawo ta wajen dajin da suke zuwa horo ya gani, sai ya ɗauki camera ɗinsa wai zai ɗaɗɗauki wajen horon nasu hoto, in sun yi passing out ya kaiwa Ummie ta ga wuraren, dan haka sai ya nufi ma'ajiyar kekunan horonsu, ya ɗauko keke guda ya haye kai, sanye yake da three quarter jeans baki da lallausan t-shirts ash color, ya yi kyau sosai, sai ya ɗaura army p-cap a kansa. Vash kuma fita ya yi dan ya samu damar kallon sauran matasan sojojin. Noor har yanzu yana ta faman barci wahala, Leo yana kwance saman gado bai sauƙa ba tin bayan sallar asuba da ya dawo, idanunsa biyu kuma!. A natse Zaysh yake tuƙa kenan nan nasa yana ɗan kalle-kalle, ya sanya helmet a kansa wanda ya ɗauka a jikin keken, kowani kenen akwai hular kwanon a ɗaure a jikinsa, dan dokace basa hawa keke babu shi. Wata doguwar hanya ya miƙa, nan yaga matasa dayawa a kan keken, wasu suna dawowa, wasu kuma suna tafiya, a ransa ya ce yau ba training sai yawo, watau kowa ya je ganin wuraren da muke zuwa horo dan ya ɗauki hoto ya ajiye tarihi. Yana sharan wata kwana da zata sada shi da cikin dajin suka ci karo da wata keke da ta sharo kwana ita ma, hakan yasa sarkan keken ya zube ƙasa, saura kaɗan su faɗi daga shi har wancan ɗaya mai keken. Amma suka yi saurin sanya kafafunsu a ƙasa. Kusan a tare suka ɗauko ƙasa, ya tsayar da kekensa a gefe, shi kuma wanda suka yi karon ya tsugunna yana ƙoƙarin gyara sarkar keken nasa da ta zube. Da yake yasan shi ne da laifi da ya shiga kwanar da gudu, sai ya yi saurin tsugunnawa a wajen tare da kama sarkar yana faɗin. "Sorry bari in gyara maka".......... Miƙewa tsaye ya yi ya bar mashi sarkan ya gyara. Tsab ya mai da shi ya gyara tare da rike kan keke ya miƙe tsaye, a sanyaye ya ce. "Sorry ba da gangan na yi ba, na shiga duniyar tinani.......". Bai iya karisar da maganar ba ganin cewa macece ba namiji ba. Zazzaro ido ya yi, ta cire hukar kwanon kanta, ta kuma ɗan buɗe zip na ƙatuwar jacket ɗin jikinta da ya hana ake iya kallon kirjinta har a gane macece, daga ta ƙasa wandon jeans dogo ne a jikinta, kafafunta da Boot bakake, hannunta da army hands gloves, ba ta yadda zaka iya gane macece har sai da ta cire hular kwanin dogon gashin kanta da kyakkyawar face ɗinta ya bayyana. Ai kusan suman tsaye ya yi a kallonta, ga shi da helmet a kansa mai cover, bata iya ganin face ɗinsa, hakan yasa ya zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu, bai iya ɗauke kallonsa daga kanta ba, sai da ya ga ta motsa ta miƙa hannu zata karɓi kan kekenta da ya rike ne yasa ya farga, da sauri ya ɗauke kallonsa daga kanta tare da fara juye-juye yana neman namijin, dan bai gama yarda ita ce mai wannan keken ba yafi tinanin da ya tsugunna gyara sarkan ne namijin ya gudu mace ta zo. Kun san a matasan sojojin harda mata? Ban taɓo maku ɓangarensu bane saboda labari bai biyo ta nan ba, amma harda matasan mata dake sha'awar shiga aikin. A ransa ya ce. "Yanzu wannan kyakkyawan mai zubin taliyar ma a training na soja take kenan? To yanzu wannan ba zata karye bane ma?". A fili kuma karɓar kan kekenta da ta yi ne ya dawo da shi daga tunanin da ya afka. Ya gagara sake yi mata magana, yana gani ta mayar da helmet ɗinta a kanta, sannan ta gyara ta haye kan keken ba tare da ta yi mashi magana ba. Sai da ta gyara hands glove na hannunta kafin ta fara tuƙa keken ta bar wajen. Mutuwar tsaye ya yi yana kallonta har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo nasa keken, ya hau ya cigaba da tafiya zuciyansa cike da tinanin dama akwai kyawawan ƴan'mata a barrack ɗin nan kenan? Kaga wata zaka ce an kure halitta a kanta! STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1________🔥 6-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________7 A can gefe kuwa Leo sai da ya gama kwanciyansa ya miƙe ya yi wanka, shirinsa ya yi cikin ƙananan kaya masu kyau, yau ɗin ma dai ripped jeans ɗin ne, da alama ripped sun fi yawa a cikin kayansa, kyansa ya kara bayyana, amma kuma ya ɗan rame kaɗan alamar wahala a tattare da shi. Har zai fita daga room ɗin sai kuma ya dawo ya hau shin Noor daga barci, dan yana son koyawa yaron komai a tsari. A firgice Noor ya tashi yana ambatar sunan daddynsa, da alama mafarkinsa ya yi, wlh ba dan GIDAN SOJA ba ba'a tashin Noor daga barci, saboda ciwon nan nasa, yana firgita, amma yanzu har ya fara sabawa da tashin nasa da ake yi. In a cool way Leo ya ce. "It's breakfast time, get up and let's go eat"........ Jin voice ɗin Leo yasa Noor sauke ajiyar zuciya, a natse ya ɗago jajayen idanunsa a kan Leo ɗin, tamkar zai yi kuka ya ce. "Please brother let me sleep, I really want to sleep". Da kyar yake maganar. Sosai Leo ya ji tausayin yaron ya kama shi, sai ya ji yana buƙatar jin labarin Noor, kamar zai fita, sai kuma ya fasa, komawa saman bed ɗinsa ya yi, ya zauna tare da jawo jakarsa, buɗewa yai. Biscuits manya-manya masu daɗi ya ciro kwali biyu, da hannu ya yi wa Noor alamar da ya zo. Ba musu ya sauƙa ya je, gefensa ya nuna mashi, zama ya yi yana ta faman daka hamma. Miƙa mashi biscuits guda ɗaya Leo ya yi, ba musu ya karɓa yana cigaba da kallonsa. Ɗan nisawa ya yi kafin a natse ya ce. "I want to know your history, who are you? Why don't you want to focus on the work that brought you here?". Da sauri Noor ya waro idanunsa a kan Leo ɗin, lokaci guda ya ji murmushi ta kubce mashi, wani irin musulmin daɗi ya ji, wai yau Leo ne yake kula shi haka? Har yana neman jin tarihinsa? Bai san cewa dikkansu a ɗakin sarai Leo yana karantarsu ba, dik wani motsinsu yana sane da su, shi mutum ne da ya tsani haɗa hanya da dolaye marasa basira, sai da ya gama karantarsu tsab a ɗakin sannan ne kuka ga ya ɗan fara kula Noor, ya fahimci a ɗakin dikka babu dolo sai dai rashin mai da hankali a kan aiki, amma dikkansu akwai kaifin basira. Shi Noor na daban ne a cikinsu, kwakwalwansa tana da saurin gudun tinani, akwai wani baiwar da ALLAH ya ajiye a tattare, kawai tsabar sangarta ne da shiririta da ƴan uwansa mata da daddynsu suka yi mashi har tai mashi over yasa baya taɓa abin arziki, amma da zai taimaka mashi wlh za'ayi alfahari da shi a hukumar soja, zai kafa babban tarihin da zai yi wuya a sake samun wanda zai sake kafa irinsa. Shin kun yarda da zancen Leo dake cewa Noor zai kafa babban tarihi? Wace iriyar tarihi kenan? Wace iriyar baiwa ce a tattare da Noor? Mu je zuwa. Gyara zama ya yi, take ya ji barcinsa ta gudu, a natse ya ce. "My name is Nooriel Fayruz Zaheeran, ainahina European ne, mahaifina European ne, mahaifiyata ƴar kabilar scandinavian ce a kasar Mexico yankin Amurka kenan, amma mu mazauna CRYSTAL PALACE ne a cikin Us, mahaifiyata ta rasu a ranar da nike shirin zuwa duniya, na taso a tare da sisters ɗina mata su uku, sune komai nawa, sai daddyna". Nan ya kwashi dikkan labarinsa, yadda daddynsa ya kwallafa rai kan neman ɗah namiji, dukiyar da ake jiran ya kula da

Chapter 12 of 95