Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suke Tajikistan & Afghanistan, kabilun da aka ce sun fi kowani kabilu kyau a duniya, kyau tamkar su suka baiwa kansu, ko halitta aka ce NIRASH ya yi wa kansa, dik buri irin na ɗan adam na tabbata ba zai yi wanda ya kai rabin nasa da ALLAH ya bashi tsantsar kyau ba, dik da haɗama irinta ɗan adam, saboda kyansa wasu kiristoci a primary school ɗinsu har ce mashi suke yi mala'ika ne shi, saboda basu san mala'ikan ba, dik in da ya yi Seraph zaku ji suna faɗi, watau mala'ika mai tsantsar kyau da haske. Kyansa ya ja mashi kalubale sosai wanda yasa ya kara ja baya da mutane yake rayuwansa shi kaɗai. Ƙabilun Pamiri su ne kabilun da suka yi kaurin suna wajen kyau a duniya, suna da hasken fata pure white sosai, sannan idanunsu dara-dara mai haske da zurfi ga su siren eyes, watau idanu masu kamar zanen kifi haka, sai dai yana da matuƙar wahala ku samu mai bakin ido a cikinsu, idanun pamiran people kala uku ne, olive green shi ya fi yawa a cikinsu, sai kuma ash, na karshe violet wanda daga cikinsu dama ya fara fitowa, yauwa ana samun masu brown eyes ma a cikinsu amma ba sosai ba. Kazalika su da wuya ki samu masu baƙin gashin kai a cikinsu, always gashinsu golden ne ko kuma ash color, sai brown da shi ma ɗaiɗaiku ne, suna da tsawo sosai ga cikar halitta, musulmai ne, dan haka NIRASH cikakken musulmi ne sosai. Tsayayyen namiji ga tsawo ga ƙira mai kyau. Amma mahaifiyarsa ce pamira ɗin ba mahaifinsa ba. Kamar yadda kuka ga fulani akwai na daji akwai na gari to suma kabilun Pamira su ne na gari, kamar yadda ake cewa fulanin daji bororoji to su kuma Pamira na dajinsu ana kiransu da tajik, to shi NIRASH mahaifiyarsa pamira ce ba Tajik ɗin ba. (Oh ni Star Lady yau kuma na zaƙulo maku ƙabilun da suka fi kowa kyau a duniya, bari mu yi labari a kansu dan ku ji yadda suke da komai nasu saboda ku samu karin ilimi, mu je zuwa, yau ta Afghanistan muka leƙa dan zaƙulo wasu sabbin abubuwan.) NIRASH ya fito ne daga babban gida mai ɗauke da family guda biyu, daga Big Bro ɗinsa sai Granny ɗinsu wanda baya a tare da su a gida guda, sannan su mazauna Us ne, bala'in son aikin soja ya kawoshi AVARIS, dan dik duniya babu makarantar horon sojoji da ake basu ingantaccen horo irin AZURE ɗin, shi ne yasa NIRASH ya zaɓi nan. Sauran bayani zaku ji a gaba. Note, dik wanda kuka kallah a AZURE babban kai ne, dan sai kana da hanya kake samu!. ------------------------🔥 Dawo da kallonsu a kan junan suka yi, ɗan daga kafaɗa Noor ya yi alamar anyway ba damuwa, dukansu wajen beds ɗinsu suka wuce, gabaɗayansu suma cire hulunan kansu suka yi, dukansu kowa da irin gyaran gashin kansa. Noor yana da gashi irin mai tsananin bakin nan, yana wani irin sheƙi, ga shi a kanannaɗe yadda kuka san indomie, kamar a nannaɗa mashi da gangan ne, irin nannaɗa sosai ɗin nan fa, kuma gashin tana da tsantsi sosai, Noor matashi ɗan baruwana, yana da hakuri, kuma yana da cutar tsoro, kamar akwai abin da ya taɓa faruwa da shi a lokacin da yake jariri ko yake cikin uwa, dan yana da irin saurin razana a abu, ko tsoratar da shi unexpected aka yi in ba'ayi sa'a ba yana iya sumewa ko ya kame, amma kuma yana da balain zuciya sosai, wannan ciwon tsoro nasa yasa mahaifinsa ya ce a kawosa AZURE, wai kila idan ya sha horo ya shiga cikin maza cutar zata rabu da shi, dan an nemi magani har an gaji ba sauki. Bugu da ƙari Noor yana da yanayin mata sosai. Dan a gidansu dikka mata ne, shi kaɗai ne namiji, shiyasa harta maganarsa zaku ji sautinta kamar ta mata saboda sabo da zama a cikinsu, ga shegen son jiki, dik dai wani halin mata sai ka same shi da su, babu abin da bai iya ba wanda mata suke yi, shi ne karami a gidansu, dik matan sun girmesa . Ɗaya na gefen Noor shi ne ZAYNASH, shi gashin kan nasa ya cika kansa sosai, bashi da tsawo sai cika da laushi sosai, ga shi irin light brown ɗin nan ne, guy ɗin bashi da saukin kai ko kaɗan, amma yana da hakuri da jurewa dakon abu, sai dai akwai zuciyar balai idan aka taɓasa, sannan in aka kuresa ya fara faɗa bai san dainawa ba. Mahaifansa ƴan ƙasar Niger ne a Africa. (Ina mutanena ƴan Niger? Ku zo ga ZAYNASH naku ne ɗan Nijer! ) kyakkyawan gaske ne, mahaifiyarsa buzuwa ce, mahaifinsa bahaushe, kun san suma ba baya ba wajen kyau da kamala. Uhm ZAYNASH ɗan gasa kenan, yana da bala'in kishi, baya son ya ga wani ya wucesa, shiyasa a makaranta baya bawa wasu damar zuwa first class, bashi da matsala da kowa, amma kada ka nuna mashi iko ko ka fishi, ba zaku shirya ba, yana da ƙoƙarin matua, dik dan farincikin family ɗinsa yake yi, saboda su ya shiga aikin soja!! Daya na gefen kuma gashin kanshi yana da cika sosai sai dai shi yana da tsantsi sosai yana kwance har gaban goshinsa, ga shi bakinkirin, sunansa ARVASH MUHAMMAD KHAIZA'AN, shi ɗan baruwana kenan, komai ka ke yi sai dai ya bika da ido kawai, ga shi da zurfin cikin balai, hakuri da juriya dik ya haɗa. Dukkansu huɗun nan karshen haɗuwa ne, idan ana maganan haɗuwa aka zo nan to fa sai dai a rufe baki, very classy da su, ga class da girmama kai, musamman NIRASH and NOOR, kyansu na daban ne, halittarsu ta sha bamban da tasu. Dikkansu fatarsu tana tsananin sheki da kyau except ZAYNASH dake da African skin, su ukun nan dik suna amfani ne da STAR BODY LOTION OR SOAP shiyasa yanayin kyan skin ɗinsu iri ɗaya, shi kuma Zaynash da namu man yake amfani!. Bari in takaice maku labari haka suka kwana cikin ɗakin nan ba wanda ya sake yiwa Leo magana, kuma shima baiyi masu magana ba, amma fa sunyi gulman shi sosai, musamman gashin kansa yanda basu taɓa ganin irinsa a zahiri ba, suka dinga yabon gashin sosai har Noor yana cewa dama ace ya samu irin wannan gashi ai da ya more. ----------------------------🔥 4:30AM watau asuba. Wani irin busa ne ya karaɗe gabaɗaya barrack din, tamkar busar ƙaho, wannan busa tayi sanadiyyar farkawa kowanensu, su Noor a tare suma suka farka, sai dai ga mamakinsu sai suka samu Leo a zaune a saman gado yana rike da wayarsa yana latsawa alamar tun ɗazun ma ya tashi koma dai bai yi barcin ba ma kwata-kwata, sun ɗan yi mamaki. NOTE: A gidan soja a lokacin horon matasan sojoji ba'a basu waya har sai sun kammala horo sun fara aiki za'a maido masu da wayoyinsu, sai dai suna iya kiran gida sau ɗaya ko biyu a sati amma ba da wayoyinsu ba, wasu ƙasashe suna basu wayoyinsu su kira gida, wasu kuma ana kira masu ne da wayar securitys officers, amma rike waya ba'a yarda ba, to amma ni na saka suna tare da wayoyinsu saboda wani dalilina kuma wannan part ɗin sai da wayoyi a hannunsu zan samu damar yin wani abu a wajen. Meyasa ake hanasu wayoyinsu a lokacin horo? ana hanasu wayoyinsu ne saboda abu biyu, na farko dan kada su fitar da sirrin irin horon da ake yi masu, watau su ɗauki video ko hotuna, shiyasa da wuya ku ga video ɗin yadda ake ainahin horar da sojoji, ainahin horonsu ba wai tsallake dutse, ko gudu or iyo cikin ruwa ba, ainahin horon ɓoyesa ake yi matsayin sirri, sai ka shiga zaka sani, zan rubuta yadda rayuwar sojoji suke a gaske da dik wata wahalar da suke sha da komai dai, ba zan rage komai ba! Zaku san su waye soldiers ba sunansu da kuke ji kullum ba, akwai abin da zan ɗan sakaya, abu na biyu da yasa ba'a basu waya shi ne zai ɗauke masu hankali daga kan horon da suke yi, musamman karatu da nazarin makamai da suke yi, yana ɗauke masu hankali. Dan haka kada ku manta da na faɗa maku ni zan barsu tare da wayoyinsu ne saboda labarina ya tafi mun yadda nike so, bana son abin da ba haka ba in saka maku shi tin da baku sani ba sai ku ɗauka gaske ne, shiyasa na faɗa maku ba'a basu wayoyi ni ne kawai na basu fatan kun game?! -------------------------🔥 ARVASH ne ya ce. "Wannan wani irin ƙara ne ya tashi mutane ba lokacin tashi ba?". ZAYNASH ne ya kalli ARVASH idanunsa dik barci ya ce. "Awww kai nan baka san gidan soja ka zo ba ne kake tambayar me ya tasheku yanzu? Tab lallai ma, watau lokacin tashi bai yi ba, to ai a wannan gidan babu zancen lokacin tashinka, ba kamar gidanku bane da zaka yi barci lokacin da ka ga dama ka tashi lokacin da ka ga dama, nan lokacinsu zaka bi, dallah tashi ka yi abin da za yi yanzu, karfe biyar da rabi za ka fara karɓar horon, GIDAN SOJA GIDAN WUTA kake!! Kai baka karanta a document na biyu da aka bamu bane?". Ɗan turɓune fuska Noor dake jinsu ya yi yana ɗan miƙa kafin ya ce. "Ni wallahi daddynmu ne ya matsa mun gabakiɗaya akan wannan aiki, wai na taso cikin mata, na taso a rago shi ne fa kawai ya ce sai na shiga aikin soja, gaskiya ni barci bai ishe ni ba". Ya faɗa tare da koma ya kwanta. ZAYNASH da yake kokarin fitowa ƙasa daga gadonsa ne ya ce. "Kwanciya ko? Hhhhh yaro man kaza, kwanta bari Captain ya shigo cikin ɗakin nan sai ka gane annabi isa ba ɗan ALLAH bane manzon ALLAH ne, sai yafi maka sauƙi ka tashi da kafarka ka je wajen training akan ka bari ya zo ya same ka". Yana rufe baki VASH ya karɓa da cewa. "Kyaleshi, idan Captain ya shigo zai nuna mashi a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba a gidansu ba". Ya faɗa tare da dirowa kasan gadon ya nufi in da ya kasance toilet ɗinsu. Kwanciyansa Noor ya koma yayi yana cewa. "Bazan tashi yanzu ba, sai anjuma, dik abin da zaku yi sai dai ku yi, ba Captain ba komawa zai zo sai nayi barci na, a gidan mu karfe takwas nike tashi, dan haka sai takwas ɗin ta yi zan tashi". Ya faɗa tare da jawo bargo abinsa. A cikin ƙasa da mintuna arba'in da biyar suka yi wanka suka shirya cikin ƙananan kaya yanda zai musu daɗin karɓan horo, sannan suka fito, suna fitowa suka nufi inda ya kasance masallaci, a nan suka yi sallah sai dai kafin su fita sun yi ƙoƙarin tayar da Noor daga barci, amma yaki tashi, ya ce su barshi, haka suka rabu da shi, dan a gidan soja dama ba'a taimakon juna ai a lokacin horo, barin mutum zaka yi jikinsa ya gaya mashi. So sun fita suka bar Leo a tsakiyar gadonsa yana zaune yana latsa wayansa, basu yi mashi magana ba shi ma bai yi masu ba!. Sai dai ga mamakin su kuma shine ya riga su zuwa masallaci, a can suka iskoshi, da yake hanyar zuwa masallacin yana da yawa, sai suka yi tinanin kila yanke ya bi. Karfe biyar da rabi daidai suka fito daga masallaci, suna fitowa gabaɗayansu suka nufin wani tapkeken fili, dama already sun sani ba yau bane farin zuwansu gidan soja, wata ɗaya da ya wuce sun yi cike-ciken form da zasu yi, sannan sun zauna na sati ɗaya a nan a nunnuna masu abubuwa kafin su koma su yi shirin zuwa karɓar horo, so sun san komai kuma yana cikin tsarin da aka tsara musu kafin a dauke su, ba saɓa lokaci! Babu wasa da aiki! Babu karya doka. GIDAN SOJA GIDAN WUTA, WAI ME KUKE TINANIN ZAI FARU NE?. NASAN HAR YANZU BAKU FARA FAHIMTAR KOMAI BA, TO KU YI HAKURI KU CIGABA DA BIBIYA, NAN GABA KAƊAN ZAMU ISA IN DA ZAKU FARA GANEWA! YANZU FARKO NE SAI NA DAURE NA YI MAKU NAYANIN KOMAI YADDA ZAKU FAHIMTA! DAN GABA KU JI DAƊI!. *Wannan littafi na ZAKUNA BIYAR tin daga page 1 na step 1 har zuwa karshen step 1 sadaukarwa ne ga mutanena na ƙasar Niger, ƴan Niger ƴan amana, ƴan Niger sun mun abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba, Niger gidan karaminci da mutunci, gidan amana da kyautatawa, kai ƴan Niger baki na ya yi kaɗan wajen iya faɗan alkhairanku, kun mun na gani! Ban san da me zan biyaku ba shiyasa na yi maku wannan sadaukarwan, ALLAH ya kara maku lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali da farinciki, jin daɗi da walwala mara yankewa har illarh Masha ALLAH, hakika ina kaunar mutanen ƙasar Niger kauna sosai mara misiltuwa, much love.*🌹♥️ STAR LADYN TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. 2-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________3 5:30AM AGOGON AZURE BARRACK TA BUGA. Gabaɗaya matasan sun haɗe a filin nan, da yake akwai tsari da natsuwa sai dik suka shiga cikin layi mai kyau. Kowannensu yana abin da yake yi, ZAYNASH and VASH hira suke ta yi da juna gwanin burgewa, tamkar sun jima da sabawa da juna, shi kuma NIRASH sai duba wata ƴar takardan hannunsa yake yi yana tsaye a can jefe bai shiga sahun layi da su ba. Sai lokacin da Captain ya kariso wajen ne NIRASH ya nufo in da sauran matasan suke, a gaba ya tsaya tare da rufe takardan hannun nasa, da yake ƴar karama ce sai ya turata cikin aljihu, dik suka mayar da hankali kan Captain dake tsaye a gabansu. ------------------🔥 Yana tsaka da barcin da ta ɗauko ɗanɗano da daɗi, har mafarkin sisters ɗinsa yake yi, ya saba kwanciya a saman laps ɗinsu yai barci har ya tashi ba zasu saukesa ba, yau yana kewa, gadon gidan soja bata yi kama da cinyar sisters ɗinsa ba. Ya yi nisa a cikin mafarkin da yake yi tamkar saukar aradu haka ya ji an takasa da wannan shegiyar takalmar tasu, da karfi Commander ya takasa har sai da ya faɗo ƙasan gadon. Ko a fuska kuka ga commander kuka ga Captain kun san Captain Onbish ya fi imani da tausayi, Commander ko kaɗan babu ALLAH a lamuransa, bakin mugu ne da ya ga jiya ya ga yau a GIDA SOJA, in taƙaice maku shi ya horar da su Captain Onbish ɗin ma! Kunga kuwa dole wannan ba zai yi tausayi ba!. Ƴar kara Noor ya saka tare da waro idanunsa. Ganin mutum a tsaye a kansa fuska babu alamar annuri yasa yai mahaukacin razana, dan shi fa ya manta a GIDAN SOJA yake. Ihu ya kurma sai kuma lokaci guda ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya kame ko ya suma, kar ku manta irin ciwon da yake da shi. Daddynsa ya ɓoyewa GIDAN SOJA wannan batu, kuma magana ake ta ba dik kai ke zuwa wannan gida ba, kunga magana ake ta daddynsa na da daloli, dan haka ba zasu zurfafa ba!. A maimakon Commander ya tausaya mashi ganin ya suma, sai ya sake sanya kafarsa ya take nasa kafafun yana ce mashi ya tashi ya fita wajen horo cikin ɗaga murya. Sai dai dik tsawar da ya yi a banza, dan Noor bai motsa ba. Hakan yasa ya ɗan duƙa a gabansa, nan ya tabbatar da ya suma. Siririn tsaki ya ja tare da kwalawa wasu jaratan sojoji biyu kira, dama tare suke bin ɗaku-ɗakuna suna tashin sauran basu tashi ba!. Da wani irin gudu kamar gangsters waɗan nan sojoji suka shigo room ɗin. Da hannu ya nuna masu Noor game da cewa. "Ku zuba mashi ruwa kafin ku ɗaukesa zuwa wajen horo". BABBAR MAGANA, watau ba ɗaga kafa babu tausayi!. Da sauri soja ɗaya ya matsa kusa da shi, hannu yasa ya cicciɓesa sai saman shoulders ɗinsa. Shi kuma Commander ya fita zuwa sauran ɗakunan dan tabbatar da kowa ya fita. Waɗan nan sojoji babu tausayi babu tausayawa suka kai Noor wajen babban tap na barrack ɗin. A kan fuskansa suka kunna tap ɗin. Ai ruwan nan na taɓa fatansa a wani irin gigice ya farka yana ambatar sunan Aunty Lusi, da alama ta fi kula da shi a gidansu. Janyesa daga wajen tap ɗin suka yi ganin yana neman sake rasa numfashinsa, suka tsayar da shi a kan kafafunsa, sai ƙoƙarin tangaɗi yake kamar zai faɗi. Sai dai yana waro idanunsa take ya shiga natsuwarsa, dan ganin waɗan nan sojoji yasa ya tuna ashe fa GIDAN SOJA yake, sai ya ji ya kara tsanan aikin fiye da yadda ake zato. Basu bari ya samu damar tinani ba ɗaya ya daka mashi tsawar da ya sanya shi firgita, in a harsh way suka ce ya wuce wajen horo kafin jikinsa ya gaya mashi, bashi da zaɓin da ya wuci ya wuce da sauri, dan bai ga alamar wasa a wannan waje ba! Waɗan nan sojoji tsab zasu iya cinyesa ɗanye a cewansa. Haka ya wuce zuciyansa na tsananta bugu da razana saboda tsawan da suka yi mashi ya tsorata sosai. Shi ko wanka bai yi ba, ga jikinsa a jike da ruwa, babu damar ya koma ɗaki bare ya canza kaya!. --------------------🔥 Cikin kakkaifar murya Captain ya ce da matasan. "Ready!!". Take dik suka buka ƙafafuwan a kasa, at the same time suka ɗaga hannu suka sara mashi alamar gaisuwa. Kai ya jinjina masu haɗe da sake cewa. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya. Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!". (My people ya kuke tinani idan za'a rera taken nan da gangar ƴan BB? Uhm.) Jinjina kai Captain yai tare da cewa. "Kamar yadda kuka sani ne dole yau zamu fara horonmu, yakamata tin last week zamu fara amma abubuwa suka ɗan shiga cikin lamarin wanda already kun sani ba sai na tsaya dogon bayani ba, yanzu zamu fara da matakin farko, dole ne ku yi tafiya da sauri cikin tsari na tsawon mil biyu domin gwada ƙarfin jiki a fannin safiyar nan, so get ready again!". Ya kai karshe yana rarraba idanunsa a kansu, da yake wajen akwai haske sosai. Sai da ya tabbatar da kowa ya hallara a wajen, aka kira sunan kowa dake rubuce a document, suka amsa, sannan ya ɗan yi gyaran murya. Kara haɗe natsuwarsu waje guda suka yi, da karfi Captain ɗin ya ce masu start. Sai da suka sake sara mashi kafin su fara tafiya cikin tsari da natsuwa amma da sauri, a lokacin su Zaynash basu lura da Noor a wajen ba, dan a baya ya tsaya da ya zo. Sai daka hamma yake yi, saboda shi har ga ALLAH barci bai ishe shi ba, ba dan wannan Commander maras imanin nan ba ALLAH da ba zai tashi ba. Hannayensa NIRASH ya zura cikin aljihun wandonsa suka cigaba da tafiya har na tsawon wannan bil biyun, suna tafiya wasu suna hira, wasu suna cewa ashe ma aikin sojan ba wahala, shi ne sai tsoratasu ake yi, ashe iya wannan ɗan tafiya ne, ai wannan sai su kwana suna yi. Haka a tinanin Noor ma shikenan zasu koma ɗaki su yi barci daga wannan ƴar tafiya, sai kuma me? Suna kai daidai gaɓar mil biyu wata hanya ta rabe a wannan waje, nan fa Captain dake biye da su amma ta gefe ba'a cikin layinsu ba ya umarcesu da su sauka daga kan wannan hanya su bi ɗayar. Nan da Noor ya gane lallai already wannan hanya an shiryata ne ma dan horar da su, shi fa wlh bai shirya aikin soja ba, kawai daddynsa ya ja mashi balai yana zaune cikin sisters ɗinsa gwanin burgewa, da yanzu ko shirin tashi barci bai yi ba. A daidai wannan lokacin ne kuma su Zaynash suka lura da shi, da sauri suka isa in da yake, Vash ne ya fara cewa. "Noor yana ga jikinka dik ruwa? Baka canza kaya ba! Kana son mura ta kamaka ne?". Zaysh (Zaynash) ne ya ce. "Meyasa baka cire wannan kaya ba? Zaka yi ciwo!". Cike da kulawa game da tausayawa haɗe da gaskiyarsu suka faɗa. Amma Noor sai ya dallah masu harara, a fusace ya ce. "Kada ku sake yi mun magana, mugaye kawai, ai kun san me aka mun da zaku wani zo ku nuna kuna sona!". Da sauri Zaysh ya ce. "Wlh bamu san me aka yi maka ba". Vash ya amsa da. "Noor muna sonka mana"...... A kufule ya amsa da. "Da kuna sona da baku bari waɗan can azzaluman sun azabtar dani ba, dan haka karku sake yi mun magana". Ya kai karshe tare da wucewa. Captain dake kallonsu ya so yi masu magana a kan cewa ba'a tsayawa magana da juna haka, amma kasancewar ranarsu ta farko ce sai ya kyalesu. Jiki ba kwari suka bi bayansa, dan wlh ya basu tausayi tin ma basu san me matsalarsa ba. Tafiya mai ɗan nisa suka yi a wannan hanya da suka sauka kafin su isa wani tapkeken fili mai girman gaske wanda ya fi hall ɗinsu sau goma, fili ne mai cike da duwatsu, tsaunuka da shinge, daga karshen filin wani dogon bene ne mai step-step sun kai 100 zuwa 150, tsawon staricase ɗin nan ya yi mugun basu mamaki, kuma ba ɗaki bane, just steps ɗin ne kawai aka yi har sama, kuma saman ma babu komai, dan horon gwarin gwiwa kawai aka yi wanna bene. A bakin wannan fili Captain ya umarcesu da su dakata, dik tsayawa suka yi suna mai da nunfashi a hankali-hankali. Sai dai Captain bai bari sun huta ba ya yi cauting from one to 3 ya ce su je da gudun gaske su isa wancan steps ɗin. Da yake har yanzu da ɗan sauran karfinsu sai suka kwasa da gudu sosai, Noor shi ne na karshen zuwa wannan waje, dan tsabar ragwanta da barci da yake kansa, ga ruwan da ya sha, while NIRASH and ZAYSH sun rigasu isa wajen. Shi kuma Captain cikin zafa ya ɗan taka har ya isa wajen, hakan ya basu damar ɗan hutawa kafin ya iso. Dan yana zuwa ya umarcesu da su tattakawa su haura wannan steps har sama a cikin

Chapter 4 of 95