Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gwamma ba, halinsu sai su. Wucewa tantinsu ta yi, a lokacin Jehan da Manassa sun yi barci, while Angelina ta shigo tantin yanzu, sun kammala aiki da Zaynish, sai farinciki Angelina take yi saboda Zaysh ya yabawa aikinta, ya ce ta yi namijin kokari. Gyara shinfiɗarta ta yi ta kwanta tana kallon Arya da ta shigo yanzu, sai wani layi Arya take yi tamkar zata faɗi, jiki dik ya yi tsami. Sai da Arya ta duba Jehan, ta sumbaci yarinyar kafin ta kwanta a gefenta, ko sannu bata cewa Angelina ba. Ai tana kwanciya sai barci. Ita ma Angelina tana kwanciya sai barci. A can gefe kuwa, Noor yana ankare da komai, ya ga fitar Leo kuma yaga dawowansu, dama saboda jiran dawowansa yasa bai yi barci ba, dan haka yana ganin Leo ya dawo ya miƙe ya nufi tantin nasa. Baki ɗauke da sallama ya shiga cikin tantin, zaune ya isko Zaysh da Leo suna tattaunawa kan wannan hayaki, Leo yana aiki da laptop na Arya. A gefen Leo Noor ya zauna game da cewa. "Bro ina ka je?"....... Ba tare da Leo ya kallesa ba ya ce. "Idan na gama haɗa bayanai na tabbatar da abin da nike zargi zan faɗa maku in da na je, yanzu dai ya naku ayyukan?"....... "Komai na tafiya daidai". Suka haɗa baki wajen faɗe. Leo ya ce. "Zamu raba sojojinmu zuwa kaso huɗu, a cikin team 2 kowannenmu zai ɗauki mataimaki guda ɗaya, sannan 34 soldiers da suka rage zamu rabasu kaso huɗu". Jinjina kai suka yi, a daidai lokacin Vash ma ya shigo cikin tantin, a kusa da su ya zauna, maimaita abin da Leo ya faɗa yanzu ya yi dan Vash ya ji, sannan ya cigaba da cewa. "A team two muna da UNAYS, JURAIZ, AMEER AND FAHAD". Ya ɗan dakata yana dawo da kallonsa a kansu. Sai ya ce. "Zan yi aiki tare da Unays, Zaynish kana tare da Juraiz shi ne mataimakinka, Arvash kana tare da Ameer, Nooriel kana tare da Fahad, gobe da safe In ALLAH ya kaimu zan sanar dasu hukuncin da na yanke, sojoji 34 da muke dasu kuma kowannenku zai ɗauki sojoji 8 a karkashinsa, sojoji biyun da suke rage za'a barsu dan gadin sansaninmu". Jinjina kai suka yi, Zaynish ya ce. "Wannan hukunci ya yi"...... Noor ya amsa da. "Sosaima, hakan ya yi". Kai Vash ya jinjina, kasancewar Leo yana son yin aikin sirri shi kaɗai sai ya ce. "You can go"...... Da okey suka amsa mashi, a tare suka mimmiƙe kowa ya yi cikin tantinsa. Noor na shiga ya ɗauko blanket ɗin V daga cikin rucksack ɗinta, bai je in da take ba, ya shunfuɗa a ƙasa ya kwanta, ba zai kwanta da ita ba, ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, bai san bata da lafiya ba, ga barcin wahala ya ɗauketa, jikinta ya yi zafi raw tamkar wuta. Yana kwanciya ba jimawa barci tai awon gaba da shi, sansanin nasu ya yi tsit, dik sun yi barci sai sojojin dake wajen wuta da kuma Leo. ASUBA TA GARI. ------------------------🧠🔥 IRON FIST. The blood of power, the blood of authority and honor, the blood of bravery and leadership!!. Suna fira wajen CRYSTAL PALACE daddy Champion ya ɗauge saman motarsa, ya saukesa, wani irin niimantaccen iska ne ya fara ratsasu. Ai wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta ɗan rungumesa ba, ta manna mashi sumbata a cheek kafin ta sakesa ta miƙe tsaye, hannayenta ta buɗe tana shaƙar iska mai niima. Ta ɗan riko waist ɗinta kafin ta ce. "Daddy i wish Rimsha tana tare da mu a wannan waje, I wish tare muke jin wannan daɗi, da na yi farinciki, ita ma tana son irin wannan yanayin". Shi dai bai ce mata komai ba, sun zo sauƙa bridge ta hango irin turawa masu ice cream mai shegen daɗi a ƙananan motar nan, ai da sauri ta ce. "Daddy tsaya ka saya mana"...... Yana ƙoƙarin rage gudun motar ya ce. "In saya maki dai sarkin son zaƙi ba in saya mana ba". Dawowa mazauninta ta yi, ta zauna tana sakin one side smiling kafin kuma ta ɗan cukule fuska tana turo baki. Tsayawa ya yi, ya kira mai ice cream ɗin. Wani dattijo ne a irin waɗan nan motoci da ake haɗawa ɗin, ya zo da sauri, cikin girmamawa yana risinar da kai ya ce. "Wani irin za'a baka sir". Carap ta capke kafin Aryan ya yi magana ta ce. "Milk and mango flavor"...... Da okey dattijon ya amsa game da fara kokarin ɗauko roban zuba mata. Dakatar da shi Aryan ya yi yana harararta kafin ya ce. "Give her chocolate or strawberry"....... Turo baki ta yi. "Daddy irin wannan ice cream ɗin milky ya fi daɗi"...... Banza yai mata bai sake magana ba, dattijon ya zuba mata a robar ya miƙo mata, kin karɓa ta yi, ta make kafaɗa tana turo baki har da juyawa Aryan baya wai ta yi fushi. Hannu Aryan ya miƙa ya karɓa, sannan ya zaro kuɗi daga jikin kujerar motar, ya miƙawa mai ice cream ɗin dala 100. Dattijon ya ce. "Bani da canji". Aryan ya ɗaga mashi hannu alamar ya je kawai. Godiya ya dinga yi, Aryan ya tada motar da hannu ɗaya suka fara tafiya. Juya mashi baya ta kara yi tana kallon hanya, taki yi mashi magana. Oh manyan kasashen duniya sun cigaba, dare tamkar rana, ba rashin tsaro ba hayaniya, wlh ko'ina ka gani lantarki tankar kamar rana, abin gwanin ban sha'awa, ALLAH ka gyara mana kasarmu ta zama fiye da hakan! Ku ce Amin. Ya ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kafin ya tsai da motar a wani haɗaɗɗen waje da ake sai da flowers, kun san su ƴan rose ne, akwai iya baiwa flower muhimmanci. Wani haɗaɗɗen bunch of flowers ya saya tare da karɓa ya ajiye a gefensa. Ice cream dake ɗayan hannunsa ya kai saitin ɗan bakinsa, baya shan irinsu ice cream da kayan zaƙi, amma yau saboda ita zai sha........ Kaɗan ya ɗan lasa, sai ya ɗan tsuke fuska alamar batai mashi ba. Ɗan daurewa ya yi game da sake ɗeba mai ɗan yawa a bakinsa. Bai gaɗiye ba ya rike a bakin nasa, ya kai hannu ya jawota jikinsa, tana tirjewa aikuwa ya matse ɗan bakinta game da sunkuyowa kanta, ya tura mata ice cream ɗin dake bakin nasa cikin nata. Ji kake diff ta natsu ta daina ƙoƙarin kwace kanta, ta kwanta a jikinsa tana turo baki, sai kuma ta hau haɗiye ice cream, harda ɗan lashe baki. Zuba mata ido ya ɗan yi kafin ya ce. "Sarkin kwaɗayi, me na lashe baki kuma bayan kin ce ba zaki sha wannan ba?". Turo baki ta yi. "Saboda daga bakinka ya fito yasa na sha, ba dan haka ba bana so, test na bakinka ya kara mashi daɗi da armashi shiyasa, amma ni nasan strawberry bashi da wani daɗi"..... Ai gabaɗaya sawa ta yi ya ji shi a wani yanayi, wai dan daga bakinsa ya fito, kai wannan yarinya sai shiru. Miƙa mata ragowar ya yi yana faɗin. "Na hanaki shan milk baki ji ko?"...... "Kai daddy kai daddy, to ai wannan bashi da yawa, and ni ka faɗa mun meyasa ka ce in daina shan milk kaki". Ta faɗa tana miƙewa zaune. Kama hannunta ya yi ya damka mata ice cream ɗin kafin ya ce. "Gaba zaki san dalilin hanaki sha milk, yansu dai karɓi ice cream ɗinki ki shanye". Make mashi kafaɗa ta yi. "A'a daddy, ni in dai ba na bakinka ba to ban so"..... Wani irin hararar kauna ya wurga mata kafin ya ce. "Wannan already ya taɓa bakin nawa, please my cherry ni bana shan zaƙi, karɓa ki sha kayanki"...... Har lokacin bata kula da rose dake gefensa ba, ta sake make mashi kafaɗa kan ba zata karɓa ba. "Karɓa in baki wani gift". In a low way ya faɗa...... Tana turo baki ta karɓa tana kallonsa. "Close your eyes". Ya faɗa ta hanyar motsa laɓɓa kawai ba tare da fitar wani sauti ba. Da sauri ta datse violet eyes ɗinta. Rose ɗin ya fito da shi kafin ya ce. "Open your eyes". Ai tana sauke kallonta a kan rose ɗin nan bata san lokacin da ta kai hannu ta karɓa ba, da sauri ta ɗan rungumesa tana murmushi. Raba jikinsu ya yi kafin ya ce. "Sha ice cream ɗinki bari mu je wajajen yawo sosai". Ya faɗa yaka ƙoƙarin tada motar. A shagwaɓe ta ce. "Daddy ni kam ka bar kaini ko'ina mu je mu hau fly board please"........ Ɗan zaro mata idanu ya yi, sai kuma ya ce. "Fly board a daren nan? Baki tsoron ruwa ko?"........ Kai ta gyaɗa. "Yes daddy, ruwa is the most favorite thing da nafi so, please mana my gentle chaos". Ta marairace fuska tamkar zata sa mashi kuka. Zai yi magana ta rigasa, ta dinga mashi magiya har sai da ya aminta, haka ya juya kan motar suka koma beach na cikin CRYSTAL PALACE. A in da ya faka motarsa ɗazu yanzu ma ya faka, ya fito ita ma ta fito, yarinyar nan sanyi tamkar zai busar da ita amma take kiran su hau fly board. A bakin ruwan ya tsaya tare da kira guard dake tsaron wajen, ya ce su haɗa mashi flye board bari ya hau da matarsa. Sun yi mamakin ganin da daren nan zasu hau, around 1:30 yanzu, amma basu da zaɓi ya wuci bin umarni, haka suka shirya mashi. Hannu yasa ya ɓalle botirin after dress na jikinta, ya zare rigar gabaɗaya, ya ce ta ɗaure gashin kanta da veil na rigar. Ba musu ta yi a hanzarce. Hawa kan fly board ɗin ya yi, ya ɗaure kafarsa da kyau kafin ya miƙo mata hannu, kama hannunsa ta yi, ta hau ita ma ta gabansa, sai ta juya ta ƙanƙame shi ta baya, shi kuma ya riko waist ɗinta ta saman mazaunanta da kyau, ta ɗan ɗaga hannunta ɗaya sama tana murnushi, daɗi kamar ya kasheta. Ni ban ma san ya zan kwatanta maku fly board ɗin nan da hausa ba, matsalata ban iya kwatance bane. Bari dai in gani ko zan iya, kada ku mun dariya. Yauwa fly board zaku gansa a cikin teku, masoya suna hawa su ta yawo a saman ruwa, kai wannan kwatance na rasa ta ya zan yi fa......... 💔😭😂 Haba juyi ya fara yi da ita a cikin ruwan, tin suna baki-bakin gadar beach ɗin har suka fara natsawa can tsakiyar ruwan, daɗi kamar ya kasheta, sai ma sun tashi sama sosai, sai ta ɗaga hannu tana ƴar ƙara, fatanta ta ganta a tsakiyar teku zata je garin da rana yake fitowa, ya ALLAH, a wannan rana ta san ko rintsawa ba zata yi ba. Kara ƙanƙame shi da hannu ɗaya ta yi, tana cigaba da ɗaga ɗayan hannunta tana murmushi, shi kam kallo fine face ɗinta kawai yake yi, yana jin tamkar ya haɗe bakinsu, yadda suke a tsakiyar ruwan nan gasu a saman iska, iska mai daɗi sai kaɗa su yake yi, gabaɗaya ya canza mashi yanayin mood ɗinsa, ya shiga romantic way, yana ɗan lumshe ido. Suna saman iska ta ce. "Daddy barci kake ji ne?". Da yake hasken dake baki-bakin gadan na haskasu sosai. Kai kwai ya iya girgiza mata alamar a'a, gabaɗaya ya rasa natsuwansa, barema yadda kirjinta ke haɗe da nasa. Hannunta da ta ɗaga sama ta sauke game da ɗaurawa a kan kyakkyawan cheek ɗinsa kafin ta ce. "Daddy naga eyes ɗinsa tamkar kana jin barci". Nisawa ya ɗan yi game da juya fly board ɗin suka nufi bakin beach ɗin, dan tana neman jefasa cikin wani al'amari, gara ma kawai su sauƙa. Kukan shagwaɓa ta saka mashi tare da cewa. "Daddy kada ka saukeni yanzu"........ Ko sannu bai iya ce mata ba, wasa ya kare, sauketa ya yi shi ma ya sauka. Ya kama hannunta sai cikin mota, sai kuka take yi yai banza da ita. Da gudun gaske ya tada motar suka nufi benensu. Yana tsai da motar ya fita game da fito da kayan da suka yi shopping, ya kama hannunta sai cikin elevator. Suna haurawa ɗaki ya wuce da ita, bai yi mata magana ba ya ajiye mata kayanta ya nufi waje. Yana fita ya rufe kofar fita gida nasu, ba mai iya sake fita ko shiga. Daga nan ya wuce benensu yana jin cikinsa wajen mararsa na murɗa mashi sosai. Ita kuwa ta zauna a bakin gado tana cigaba da kukan shagwaɓarta har da cewa daga yau ba zata sake kula shi ba. A hankali ta kwanta kan gadon tana ta faman kunkuni har barci ya saceta a wajen. Shi kuwa Aryan gida ya koma, zaune ya isko Lion a tsakiyar bed yana rike da laptop yana bibiyar su guru da suka fita aiki yau, ya sanya bluetooth a kunne suna magana da juna. Ai Aryan na shiga ya haye gado ya kwanta ba tare da ya yi wa Lion magana ba. Ya kwanta ruff da ciki yana dafe mararsa da hannu ɗaya, serious ciwo marar tasa take mashi, in ta murɗa sai ya datse idanunsa. Kallo ɗaya Lion yai mashi ya ɗauke kansa, ya cigaba da abin da yake yi na ƙoƙarin kwatantawa su Vir location da containers ɗin suke..... Tsabar yarda da kansu da IRON FIST suka yi babu bindiga babu wuƙa a hannunsu, daga su sai key ɗin motar da suke driving guru and Vir suka tafi. Kuma cikin daji can border da ƙasar suka kutsa. Tin da suka sako hancin motarsu cikin wannan dajin suke sharara gudu, guru yake driving dan dik cikinsu ya fisu iya mota sosai, Vir ya kwantar da kansa a jikin kujerar mota yana danna waya, hankalinsu a kwance mutanen nan, tamkar basu san cewa waje mai haɗari zasu shiga ba. Jikin motarsu ta gaba akwai camera, ta wannan Camera Lion yake kallon kan hanyar da suke a laptop ɗin gabansa.......... Suna dab da isa wajen containers ɗin ɗaya daga cikin motocin da suka ɗauko container ɗin driver ɗin ya zare kansa daga layin da motocin suka jeru su 5 suna ƙoƙarin shigowa cikin ƙasar. Canza hanya wannan container ta yi, kuma ba kowa bane driver ɗin wanna mota face Dr Mark, in baku manta ba ai ya fito da kwari cikin mota mai ɗaukar container. To tin shigowarsu Vir wannan dajin Camera da 3D suka sanya a kofofin shige da fice na dajin ta nuna masu cewa mota ta shigo, da Dr James ya bibiyi su Vir sai ya gane motar jami'ai ne, dan da motarsu na SSO suka fito sakamakon kada ma ƴan sanda su taresu a hanya su ɓata masu lokacin. Ganewa da Dr James ya yi cewa jami'ai ne dik da bai san su waye ne a cikin motar ba, sai ya ce kira Dr Mark a waya, ya ce mashi ya canza hanya akwai matsala a wajen, to shi ne ya zame kansa daga cikinsu. Tsabar 3D sun shahara dik wasu dajukan da suke bi dan aikata ɓarnarsu a hanyar shige da fice sun sanya Camera dan gudun raja irin ta yau, watau ko an so kama su ba zasu kamu ba, Dr James munafuki yana tsaye gaban computer yana kallon komai yana baiwa Dr Mark information kamar dai yanzu. Robar ruwa Vir ya ɗauko, ya fasa ya ɗaɗɗakawa cikinsa rabi sannan ya rufe sauran. A daidai lokacin suka yi kiciɓus da containers ɗin, da karfi direbobin dake jan motocin containers ɗin suka ja birki har motar karshe ta daki wacce ke kusa da ita. Horn suka fara dannawa su Vir cike da takaicin tare masu hanya da suka yi. Kashe motar guru ya yi, suka ɗan kalli juna, Vir ya ƙara kwantar da kansa a jikin kujerar motar, basu yi alamar zasu motsa daga in da suke ba. Ganin haka yasa driver ɗin container gaba ya buɗe ya diro ƙasa, wani shirgegen kato da shi, ga tsawo ga ƙiba, jikinsa a murɗe sosai kamar ɗan dambe, yana wani nishi tamkar wanda ya yi gudu. Cikin takun dake nuna namijin gaske ne ya nufi motar su Vir. Sake kallon juna suka yi kafin su buɗe kofar motocin a tare su fito, lokacin chaskalewa ya yi. Wannan driver na zuwa ya dunkule hannu zai kaiwa guru punch a fuska, ai cikin zafa guru ya rike hannunsa. Vir ya daka tsalle ta kan motar ya kai mashi wani bahagon punch a bayan kunne, Vir bahago ne kaman Lion, sun fi amfani da hannun hagu sama da dama. Ai wannan driver ji ya yi duniya ta tsaya mashi cak, ya ji dukan hannun maza, gabaɗaya jijiyoyin dake baiwa jikinsa jini tsayawa suka yi cak, lokaci guda ya durkushe a kan kafafunsa, jini ya fara fita ta hancinsa saboda duka a bayan kunne ba wasa ba, ko kai da kanka kasa hannu ka ɗan danna bayan kunnenka ta ƙasa gefen kumatu sai ka ji azaba bare IRON FIST su kai maka naushi a wajen ai dole a samu tsayawar jijiyoyon jini. Ganin haka yasa sauran direbobin dik suka diro waje, ɗaya ya gudu da yake ya san basu da gaskiya, biyu kuma suka tsaya, dikkansu kartin maza ne masu rai da lafiya madaka karti, sun horu iya horuwa. Da zafansu suka nufo su Vir, suna wani dam-dam-dam a ƙasa. Tsayuwar jarumta IRON FIST suka yi. Guru ya ce. "Vir ba zan barka ka ji da su in kamo wanda ya gudun nan ba kuwa?". Kai Vir ya jinjina. "Jeka kamo shi bari in ɗan basu a jikinsu". Shoulder ɗinsa guru ya buga tare da wucewa ya bi bayan motarsu ya nufi hanyar da wancan driver ɗin ya bi ya gudu. Shi kuma Vir ya gyara tsayuwa yana jiran direbobin su iso. *Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.* Likes comments and share fisabilillah. QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A LADY TEEMA. STEP 1🔥 2026-01-02🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 77 & 78 *FOLLW MY TIKTOK ACCOUNT 👇* https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP *FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL ACCOUNT* 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ------------------------🧠🔥 IRON FIST. The blood of power, the blood of authority and honor, the blood of bravery and leadership!!. Da zafansu suka iso garesa, tamke fuska Vir yai, duka ɗaya ba ƙari yai wa kowannensu, dikkansu kowanensu ya bage a ƙasa, gyara hannun rigansa Vir ya yi kafin ya nufi wajen containers ɗin, ya kai hannu ya gyara bluetooth na kunnensa kafin ya ce. "Our Lion what's next?". Lion dake faman kallon Aryan dake juyi a saman bed ɗin ne ya amsa da. "Seize the container, ku kira guards ɗinmu su ɗauki containers ɗin zuwa gidan Uncle na bayan gari, we're coming in the next few minutes". Yana gama magana ya juyo ya ɗan riko Aryan yana faɗin. "Brother what's wrong with you?". Da farko Lion ya ɗauka iyashege ne yake damun Aryan yasa ya zo ya kwanta mashi ruff da ciki, sai yanzu ya fahimci da gaske cikinsa na ciwo shiyasa ya rikosa. Da gudun gaske guru ya bi ɗayan driver ɗin da ya gudu. Sun ɗan yi gudu mai nisa suka yi kiciɓus ɗa wata container, Dr Mark ya faka container ya fita yana jiran call na Dr James. Burki guru ya ja yana kallon container ɗin. Ganin wancan driver ɗin yana ƙoƙarin gudu ne yasa guru ya rufa mashi baya. Dab guy ɗin zai faɗa ruwan dake wajen guru ya kama shi, ya haɗa hannayensa ta baya ya rike da hannunsa ɗaya, sai ya kwashe kafafunsa sai da ya zube ƙasa. Belt ɗin wandonsa guru ya zaro, ɗauri goro yai mashi a hannu da belt ɗin kafin ya sake shi yana mai da kallonsa a kan wannan container ɗin. Sai kuma ya taɓa bluetooth dake kunnensa, a natse ya ce. "Our Zayra'an na haɗu da wata container da aka ratsa ta wata hanya da ita, meyakamata in yi? Babu driver a cikinta". Dr Mark dake laɓe yana kallon Vir ne ya maimaita sunan. "Zayra'an!". Ya faɗa yana zazzaro idanu. Jikinsa na rawa ya fito da wayansa, kai tsaye Dr James ya dannawa kira. Bugu ɗaya Dr James dake rungume da Zinta suna baiwa flower ruwa ne ya ɗauki kiran. Cikin mayen soyayya ya ce. "Hello, Mark lafiya?". Murya na rawa Dr Mark ya ce. "Zayra'an seized our container!"....... Ai a wani irin zabure Dr James ya saki Zinta game da miƙewa zaune, lokacin guda ya ji wani irin zafi room ɗin ya ɗauka, wani irin yawu ya haɗiye har maƙoshinsa ya yi sama ya sake yin ƙasa, kan kace me zufa ta fara keto mashi a gefe da gefen fuskansa. Miƙewa ya yi ya nufi toilet dan kada Zinta ta ji me zai ce. Sai da ya saita natsuwansa kafin ya ce. "Mark, make sure basu ganka ba, ka bar wajen yanzu! Dan idan har Zayra'an Muhammad Haiza'an ne zai kamaka a wannan waje da kake laɓe, dan haka ka gudu". Da okey Dr Mark ya amsa, daga in da yake laɓe yana iya kallon guru, ya ɗauka shi ne Lion, lallaɓawa ya yi, ya gudu ba tare da guru ya gansa ba. Ya yi gudu mai nisa kafin ya ce da Dr James. "Na bar wajen, but kayan fa?"....... Dr James ya ce. "Wani kaya ana maganar rayuwarmu, Mark ka tabbatar Zayra'an Muhammad Haiza'an ne?". Dr Mark ya ce. "Tabbas shi ne, ai shi kaɗai ne Zayra'an kai tsaye haka"...... Shiru Dr James ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Kenan kana nufin Zayra'an jami'an SSO ne? Kenan sune SSO da gwamnatin Amurka ke alfahari da taƙama da su? Kai Mark ka bar wannan dajin yanzu!". A ɗan kausashe ya yi magana ta karshe. Dr Mark hakika ya tsorata, ai kara gudu ya yi wajen barin dajin....... Shi kuma guru Lion ya ce mashi. "Ka kama container ka kashe driver ɗin". Ya faɗa a lokacin da yake ɗago Aryan, ya juyo da shi suna fuskantar juna, sai ya ɗan shafa kumatunsa yana faɗin. "My heartbeat what's wrong with you?". Cike da kulawa yai maganar, da zarar Aryan na cikin damuwa Lion ya rasa natsuwarsa kenan, yadda kuka san zuciyoyin identical twins haka zuciyoyinsu ke a haɗe, idan ɗaya na cikin damuwa ɗaya baya samun kwanciyar hankali. Gagara yin magana Aryan ya yi, yana kallon Lion kawai, sai kuma ya rufe idanunsa ruff, kwantar da shi Lion ya yi, ya sauƙa ƙasan gadon. Waje ya nufa, jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da wata ƴar karamar na'ura. Saman bed ɗin ya hauro yana kallon fuskan ɗan uwan nasa. Jama'a an faɗa maku a banza ne idan Lion yana cikin damuwa suke rasa sukuninsu? Dik su damu, ko ba zai kulasu ba sai sun mashi magana? Ba'a banza bane, idan basu da lafiya haukace kawai baya yi a kansu, ko barci baya yi har sai ya tabbatar sun samu lafiya sosai, sun fita daga haɗari yake kyalesu, kunga kuwa dole su damu idan bashi da lafiya shi ma. Kama hannun Aryan ya yi, ya sanya yatsansa ɗaya a

Chapter 91 of 95