Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin barcin ma sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi alamar ya fara samun peace of mind, ALLAH sarki, idan ya tina rayuwar iyayensa in bai zo ya ga second daddyn nasa ba baya samun natsuwa, ganinsa kawai shi ne kwanciyar hankalinsa, shiyasa ya gudu ya bar su Aryan tin asuba. "Ina sonka sosai Zayra'an, ina sonka fiye da kaina, ba wanda nike gani in ji daɗin rayuwata face kai da ƴan uwanka, ina rokon ALLAH ya bani ikon cika alkawarin dana ɗaukarwa ɗan uwana na kula daku". Ɗan motsawa Lion ya yi, hakan yasa ya zame hannunsa daga cikin na daddy, ya gyara kwanciyansa da kyau, ya cigaba da barcin da bai samu damar yi daren jiya ba........ Sake riƙo hannunsa gam daddy ya yi tamkar ance za'a rabasu ne, ya yi shiru yana ta kallon fuskan Lion. Slowly ya jingina kansa da jikin headboard na gadon, ya ɗan lumshe idanu cike da tinanika kala-kala. Barcin good 2h Lion ya yi, daddy na zaune bai motsa ba gudun kada ya tashesa. A hankali ya waro idanunsa da suke jajir saboda barcin bata ishe shi ba. Kai tsaye sai kan fuskan daddy..... "Dad". Ya furta yana miƙewa zaune, kallon farko ya zaci dad ɗinsa ne ba daddy ba. Slowly daddy ya yo ƙasa da kai yana faɗin. "Ka tashi?". Kai ya ɗan jinjina game da cewa. "What says the time?"...... Laluɓo waya daddy ya yi, ya kunna light ɗin screen.......... 4:00 PM. Iska mai ɗimi daga bakinsa ya furzar game da miƙa hannu ya jawo nasa wayan. "Daddy let me call Aryan, nasan yanzu yana can ya damu da rashin sanin ina nike". Cikin zolaya daddy ya ce. "Sai yanzu ka tina da shi kaima ai"..... Shiru bai yi magana ba, ya fara laluɓar number Aryan, ya danna kira. Sai dai a lokacin dik suna barci a kan gadon Seraphina, wayar tana silent basu ji ma, message Lion ya rubuta mashi kan yana lafiya kuma yana dawowa yanzu. Wayoyinsu kusan a haɗe yake, sun saita shi ta yadda idan ya turawa ɗaya saƙo dikkansu saura ukun zasu samu saƙon. Yana tura masu ya zuro kyawawan kafafunsa ƙasan bed ɗin, jikinsa dik a mace ya miƙe tsaye, toilet ya nufa, da kallo uncle Hussain ya bisa har ya shige katafaren toilet ɗin daddynsa, ajiyar zuciya Uncle ya sauƙe game da gyarawa ya kwanta. After 2 hours, Lion ne tsaye a tsakiyar master room na daddyn nasa, yana sanya botiran tail coat na jikinsa, ya rabb, kayan sun zauna a jikinsa matuƙa, tamkar dan shi aka yi su, yai wa kaya mugun kyau, ya tara kitson kansa ya ɗaure, jade eyes ɗinsa sun ciza sosai, kyawawan soft lips ɗinsa sun ciza pink matuƙa, fuskansa ya yi very fresh sosai, ya ƙara kyau da cikar haiba da kamala. Uncle dake zaune a kan gado yana kallonsa ne ya ce. "Zayra'an please ka dawo gidan nan da zama, tsawon shekaru 10 kenan yanzu ina binka kaki yarda, meyasa baka son zama a nan ɗin?".. Shiru ya yi bai amsa ba, har Uncle Hussain ya fidda ran zai amsa mashi ma sai kuma ya ji in a low way ya ce. "Nothing, kawai bana son gidan ne". "Please, even because of Nirash, ku dawo ku raya gidan nan, ku sake raya ruhin Haiza'an ɗina, ku farfaɗo da gidan"....... Nan ma shiru for good 3 mins ya yi kafin ya ce. "Zaka dawo mu zauna a tare a nan ɗin?"....... Rass uncle Hussaini ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya daure da cewa. "Zan yi tinani, amma idan na aminta zan dawo mu zauna gabaɗaya zaka dawo?". Kai kawai ya jinjina ba tare da ya sake yin magana ba. Shiru uncle yai yana tinanin yadda zai dawo gidan su haɗe waje guda, da kuwa abin zai yi making sense. Katse mashi tinani Lion ya yi da cewa. "Bye uncle"....... "Bye my beloved son". ....... Daga haka bai sake magana ba ya fice waje, ya bar uncle, dik lokacin da yake so zai iya tafiya, shi dai ya koma benensu. Yana fitowa waje wasu karfin jami'an SSO suka nufosa da gudun gaske, hannu ya ɗaga masu tin ma basu ƙariso ba, baya son hayaniya da gayya, baya cikin wani good mood sosai. Sauƙowa kasar wannan baranta ya yi, ya nufi gate na fita, da kafa zai koma benensu ba sai ya ɗauki mota ba, dama da kafa ya zo. Kafin ya fito sai da ya sanya wannan haɗaɗɗen nose mask ɗin nasu a face ɗinsa, sannan ya fito ya nufi benensu, a cikin ransa yana jin kamar zai iya dawowa gidan nasu da zama. Dik in da ya zo ƙetarawa sai waɗan nan jiga-jigan jami'an sun kame tamkar basa numfashi sun sara mashi, bai ɗago ya kalli kowannensu ba, bai tanka kowannensu ba, ya wuce kai tsaye ya nufi benensu. ----------------------🔥 KHAIZA'ANS HOUSE. Sai da aka zubawa Rimsha ruwa 3 bottle kafin su samu kanta ta farfaɗo, da kuka ta farfaɗo tana faɗin. "Abba yanzu uncle Aryan ɗin ne mijina?".... A lokacin Abba baya kusa, sun baro room ɗinsa da ita, Faryan ya ɗauke zuwa room ɗin Ammie. Rungumota Ammie ta yi, ta hau rarrashinta tana bata baki, sai dai ina Rimsha taki yin shiru, in short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana wannan kuka na ta shiga uku, dik Abba bai san tana yi ba, a rana ta huɗu ne ta kama Monday, a wannan ranar da asuba Faryan ya ce ta shirya ya kaita school. Jin cewa aurenta ba zai hanata school bane yasa ta ɗan saki jiki, burinta dik ta je makaranta su haɗu da Seraphina ta faɗa mata abin da aka yi mata, dik tayi sanyi baiwar ALLAH, daga umm sai uhm-uhm ta zama, bata hira, ta takura kanta sosai, amma yau da zata je school har da ɗan murmushinta. Ta shirya tsab cikin uniform ɗinta, har ta rame uniform ɗin yai mata yawa. Faryan na tsaye a parlo ta fito rike da rucksack ɗinta, karɓa mata ya yi yana faɗin. "Mu je in kaiki da wuri, Abba na jirana zamu je mu ɗauki amaryar Yah Harleen". Kallonsa ta yi, muryarta a dashe sosai ta ce. "ALLAH yasa tana da kirki"....... Da amin ya amsa game da riko hannunta, suka nufi waje yana kara yi mata nasiha, yana tausan zuciyarta, yana faɗa mata kalamai masu daɗi, yana tunatar da ita ALLAH ya ce Annabi ya ce, a haka suka nufi school ni kuma na nufi DOL kafin mu dawo mu bisu school ɗin. --------------------🔥 D-O-L Nutso take yi a cikin ruwan cike da farinciki, yana tsoma gashin kanta can kasan ruwa tana ɗagosa ruwan dake biyo gashin ya ƙara wanke mata fuska, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba. Shi kuwa tamkar gunkin da aka sassaƙa haka yake tsaye a cikin ruwan ware kitson kansa dan ya wanke golden hair ɗinsa. Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana ɗan juyawa, ɗagowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi........... Likes comments and share fisabilillah. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-22.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️ E_____________ 59 & 60 DEATH OR LIFE. (DOL) Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani. Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba'a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za'a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen. Al'ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za'ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?. Amma shi rigakafi za'a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za'a biku ko'ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za'ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye. Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama'ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza. Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka. Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buɗe container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai ne a cikin wannan container, waɗan da basu san me Tramadol ba, wani maganani ne da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta, amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, in kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai. Leo sai da ya ɗan girgiza ganin waɗan nan uban tulin kwalin Tramadol ɗin nan, katon container irin wannan cike da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buɗe container. Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiransa da maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwandon sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fahimci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!. Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba. A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu, amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki. Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe lokaci guda ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake in na ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali!. Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al'umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al'umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuɗi. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando! Idan kuwa kinƙi dakatar da shi to fa ɗan karfin da yake da shi ɗin zaku rasa, dan in yana da sauran shan ruwa a gaba bai mutu ba, to at the end abar tasa mutuwa zata yi ta daina aiki, kinga kuwa bai samu power ba wanda yake da shi kun rasata. Wata ma sai kuga ita ke sayawa mijin man power, su man power manya, zakuwa ki ga man power. Wlh mata tin wuri idan zaku tattara mazajenku ku turasu gudun motsa jiki da gym kullum dan su samo power ɗin asali is better for you, gym yana sanya jikin namiji ya yi karfi, dik wasu matattun jiyoyi zasu miƙe, yana ƙara girman gaban da kukewa haukar neman har kuke kai kanku ga halaƙar in da zaku rasa ɗan wanda kuke da shi. To maza, gym yana ƙara girman gaba da kuke so ɗin, ba sai kun sha man power ba zaku samu ingantaccen power da babu mix, sannan gym yana ware ƙasusuwan gaɓɓai yasa su yi kwari sosai, yana ƙara lafiya da daidaita zuciyar ɗan adam, kai in taƙaice maku kai da kanka in ka fara zaka ji jikinka ya canza, ya yi maka daɗi da sauransu. Mata ku tura mazanku gym ko dan su dinga ɗaukarku kamar ƴan baby suna jefawa gado kamar matan novel, da zarar yana gym komai girmanki zai ɗaukeki cak, to kashinsa ya yi kwari, amma yanzu kun kyalesa dik man gyaɗa da gishiri ya kashe dik wani karfin da yake da shi, ga wata musifa wai man power, ba dole a samu tangarɗa ba!. (Kuma mata masu shan hips and breasts enlargement yake kome? Ku jira, zan bangaɗo maku dame ake haɗasa, naku na nan tafe, ai nai alƙawarin sai fa na faɗi komai dake cutar da bayin ALLAH!) Container na gaba kuma maunguna ne irinsu diazepam, rohypnol, valium, magungunan bacci da kwantar da hankali a cewarsu, ana shigo da su da yawa ba bisa ƙa'ida ba, kuma ana bawa yara, mata, direbobi, musamman direbobi, za'a basu shi da sunan maganin hana barci, hakan na haifar da haɗasussuka a hanya, babban illar ce ga al'umma. Har kan Leo ya fara ciwo ganin waɗan nan ɓarna, amma ya daure suka je container na gaba. Suna buɗewa kwali-kwali na antibiotics ne a ciki, ana shigo da su suma ba bisa ƙaida ba, al'umma suna sha ba tare da sani ba. Kwayoyin suna cutar sosai, mutane su mutu cikin sauƙi, da ka yi zazzaɓi sai mutuwa. Time Leo ya duba a wayansa 2:30 ta yi. Cike da bada umarni ya ce su yi sauri gari ya kusa wayewa. Daga nan suka wuce container ta gaba. Suna buɗeta allurai ne dayawa a ciki, ai yana ɗaura idanunsa kan kwalaben alluran nan sai da ya ji gabansa ya faɗi. Soja da faɗuwar gaba ai kun san ba lafiya. Da yake basu da ishasshenlokaci a gurguje ya ɗauki alluran kwalba ɗaya ya zura a aljihunsa ya ce su mayar da saura su rufe tamkar ba'a taɓa taɓawa ba. Haka suka bi dik containers ɗin da suka buɗe, a kowani container sai Leo ya ɗauki abu ɗaya har suka isa kan miyagun kwayoyi, a nan ma ya ɗauki cocain ɗaya. Suka mayar da komai tamkar basu taɓa ba, sanna ya kwance karnikansa, ya ce Noor ya rike mashi ɗaya bari ya rike ɗaya, Noor ya ce. Shi wlh yana tsoron kare, basa haɗa hanya da kare, kada ku manta yana da cutar tsoro, tin ainahi haka yake da tsoron kare, kun gansa dai jarumi, wlh zai iya kama maciji, amma baya son kare ko kaɗan tamkar mai aljanu a kai. Miƙawa Zaynish igiyar karen Leo ya yi, ya karɓa ya rike, shi kuma ya riƙe ɗaya suka nufi hanyar komawa, yau ba barci akwai bincike kenan. Sun fara tafiya Vash ya karɓi igiyar karen hannun Leo dan ya taimaka mashi, saboda Leo ɗin ya fisu shan wahala, dik containers ɗin nan shi ya bubbuɗesu. Suna tafiya a hanya ne Vash ya ce. "Da mun cinnawa wajen wuta ai, komai ya ƙone su rasa shi"....... Nisawa Leo ya yi tare da cewa. "Ai bombing na wajen ba shi ne mafita ba, dakatar da masu aikata hakan ba shi ne ba, mu kama masu yi mu kashesu shi ne, idan har zaku rinƙa kama waɗan nan containers ɗin dik shime ne, in mun ƙona wasu waɗan nan yau, gobe zasu sake shigo da wasu, dan haka masu aikata hakan zamu raba da numfashinsu, shi ne ɓarna zata dakata!". Noor ya ce. "Gaskiya Avaris ta kai maƙura a wajen lalacewa"...... Leo ne ya amsa da. "A wannan case ɗin navy suna da babban kamisho, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar ƙasar nan, kome za'a shigo da shi daga waje ta ruwa ne, me amfaninsu da ba zasu dakatar da ɓarna ba? Ko dai dama an ajiyesu a bakin ruwan ne dan su dinga kamun kifi ko suna zaman kirga jiragen ruwan da zasu shiga su fita?". Cike da takaici yai wannan magana, ya rasa meyasa yake jin tsananin kaunar kasar Avaris.... Ni kam na ce saboda ƙasar mahaifinka ne mana, ai jininka suna ciki, dole ka so ƙasar. Zaynish ne ya ce. "Amma idan navy suna da laifi kaso 40 cikin ɗari na lalacewar ƙasar to fa ministar of foreign affairs yana da kaso 55 cikin ɗari, ministan tsaro yana da 75 cikin ɗari, sai number ɗaya na ƙasan yana da 100 cikin 100!". Kai Leo ya jinjina, su Noor dik kai suka jinjina, a dake Leo ya ce. "Ni ban yarda wani soja ya bani umarni a kan rashin adalci in masa biyayya ba!"..... Dikkansu basu fahimcesa sosai ba, Vash ya ce. "Kana nufin ba zaka yi wa AZURE biyayya ba?". Kai ya jinjina. "Ba AZURE ba, dik duniya babu wanda ya isa in yi mashi biyayya kan cutar da al'umma! Wlh yadda na yi rantsuwa da ALLAH kafin in saka wannan kakin kan zan kare rayuka, dukiya, ƙasa bakiɗaya, to billahil lazi babu wani mahaluki da ya isa ya tilastani ya bani umarnin in yi shiru ana cutarwa! Sai dai a kasheni a kan haka, amma wlh dik masu ɓarna sai na dakatar da su, Navy sun yi alƙawarin kare bakin ruwa, ba zasu bar dik wata cutarwa ta ruwa ta shigo ƙasa ba, amma me muka kama yau? Ina suke da har suka bar hakan ke faruwa? Okey baa basu izini ba ko?". Cike da takaici ya kai karshen maganar. A yadda ya yi magana yasa su Zaynish sun ji lallai ko zasu mutu ba zasu marawa karya baya ba, lallai zasu aiki dan cika alƙawarin da suka ɗauka. Cike da taƙaici Zaynish ya ce. "Hakika ba zamu zama karnukan farautar manyanmu ba! Lallai ba zamu karɓi umarnin rufe bakinmu a lokacin da ake zalunci ba, ba shakka sai dai a kashemu amma a kan gaskiyanmu!!". Noor ya ce. "Dama ai mu mutuwa ba wata aba bace a wajenmu, sai da muka tabbatar cewa mutuwa ta fi takalmar sakawarmu sauƙi a wajenmu kafin mu yarda mu sanya wannan kaki, dan haka mu matattune dama, lallai zamu tsaya a kan gaskiya!". Vash ya ce. "Ba zamu taɓa bari a cigaba da cutar da al'umma ba, zamu zama sojoji na farko da suka fara gyarawa kowa zama a ƙasar nan!"....…. Leo ya ce. "Idan sun san wasu ai basu san wasu ba, ba zamu ki karɓar umarninsu ba, dan umarninsu doka ce, amma muna da damar yin abin da muke so a bayan idanunsu ba tare da sun sani ba ai, daga yau babu wani ɗan ta'adda da zamu sake kamawa mu mayar barrack, dik kashe shegu zaku yi". Zaynish da ya fito daga Afirka me bai sani ba? A ƙule ya ce. "Abinda ko mun sha wahala, mun je yaki, a yakin har mu rasa ƴan uwanmu sojoji, mu sha wahala mu kama ƴan ta'addan mun kaisu ma bayan kwanaki sakesu ake yi wahalarmu ta tashi a banza, dan haka ina tare da kai, dik a daji zamu kashesu kisa mafi walaƙanci, mu jefa gawarwakinsu cikin manyan tekuna, in mun koma mu ce dik sun gudu, that's all". Noor ya ce. "Wannan umarni da ƙananan sojoji basa samu yasa suke shan wahala, suna filin daka amma wai suna jiran manya daga sama su basu izinin harbi, sai su tsaya ayi ta harbinsu! Abin taƙaici, amma zamu gwada masu kwarewa a kan aiki, zamu canza hukumar soja na duniya bakiɗaya". Vash ne ya ce. "Ni wani kafurin ne ma ya kawo dokar idan kana filin daga ma sai ka nemi izinin harbi?"....... Zaynish ya ce. "Kafuran suna dayawa ai, amma zamu kafa tarihi a hukumar soja wanda ko mun mutu ƴan baya zasu yi amfani da salonmu, zamu canza hukumar soja a duniya bakiɗaya kamar yadda Noor ya ce, zamu bawa duniya mamaki, sai mun ɗara FIVE LION In Sha ALLAH". Leo ne ya ce. "FIVE LIONS, kai watau AZURE ta jima tana yaye gwarazan maza fa"......... Noor ne ya ce. "Ni fa ina ganin IRON FIST ma daga AZURE suka samu horo, dan wani lokaci aikinsu yana mun kama da namu fa".......... Vash ne ya amsa da. "Ban san meyasa nike son tarihin FIVE LIONS har cikin raina ba, sojojin da suka shiga tarihin duniya a lokacin baya, sojojin da suka bada mamaki". Leo ya ce. "Ina tinanin AZURE ta hora IRON FIST gaskiya, saboda nima irin aikin da suke yi yana bani mamaki, amma ni fa ina ji a jikina IRON FIST ba mugaye bane kamar yadda duniya ta ɗauka, kawai gwamnatin duniya ne ta nunasu matsayin azzalumai saboda suna rusa zaluncinsu"........ E mana,

Chapter 73 of 95