Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yawa ba bisa ƙa'ida ba, kuma ana bawa yara, mata, direbobi, musamman direbobi, za'a basu shi da sunan maganin hana barci, hakan na haifar da haɗasussuka a hanya, babban illar ce ga al'umma. Har kan Leo ya fara ciwo ganin waɗan nan ɓarna, amma ya daure suka je container na gaba. Suna buɗewa kwali-kwali na antibiotics ne a ciki, ana shigo da su suma ba bisa ƙaida ba, al'umma suna sha ba tare da sani ba. Kwayoyin suna cutar sosai, mutane su mutu cikin sauƙi, da ka yi zazzaɓi sai mutuwa. Time Leo ya duba a wayansa 2:30 ta yi. Cike da bada umarni ya ce su yi sauri gari ya kusa wayewa. Daga nan suka wuce container ta gaba. Suna buɗeta allurai ne dayawa a ciki, ai yana ɗaura idanunsa kan kwalaben alluran nan sai da ya ji gabansa ya faɗi. Soja da faɗuwar gaba ai kun san ba lafiya. Da yake basu da ishasshenlokaci a gurguje ya ɗauki alluran kwalba ɗaya ya zura a aljihunsa ya ce su mayar da saura su rufe tamkar ba'a taɓa taɓawa ba. Haka suka bi dik containers ɗin da suka buɗe, a kowani container sai Leo ya ɗauki abu ɗaya har suka isa kan miyagun kwayoyi, a nan ma ya ɗauki cocain ɗaya. Suka mayar da komai tamkar basu taɓa ba, sanna ya kwance karnikansa, ya ce Noor ya rike mashi ɗaya bari ya rike ɗaya, Noor ya ce. Shi wlh yana tsoron kare, basa haɗa hanya da kare, kada ku manta yana da cutar tsoro, tin ainahi haka yake da tsoron kare, kun gansa dai jarumi, wlh zai iya kama maciji, amma baya son kare ko kaɗan tamkar mai aljanu a kai. Miƙawa Zaynish igiyar karen Leo ya yi, ya karɓa ya rike, shi kuma ya riƙe ɗaya suka nufi hanyar komawa, yau ba barci akwai bincike kenan. Sun fara tafiya Vash ya karɓi igiyar karen hannun Leo dan ya taimaka mashi, saboda Leo ɗin ya fisu shan wahala, dik containers ɗin nan shi ya bubbuɗesu. Suna tafiya a hanya ne Vash ya ce. "Da mun cinnawa wajen wuta ai, komai ya ƙone su rasa shi"....... Nisawa Leo ya yi tare da cewa. "Ai bombing na wajen ba shi ne mafita ba, dakatar da masu aikata hakan ba shi ne ba, mu kama masu yi mu kashesu shi ne, idan har zaku rinƙa kama waɗan nan containers ɗin dik shime ne, in mun ƙona wasu waɗan nan yau, gobe zasu sake shigo da wasu, dan haka masu aikata hakan zamu raba da numfashinsu, shi ne ɓarna zata dakata!". Noor ya ce. "Gaskiya Avaris ta kai maƙura a wajen lalacewa"...... Leo ne ya amsa da. "A wannan case ɗin navy suna da babban kamisho, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar ƙasar nan, kome za'a shigo da shi daga waje ta ruwa ne, me amfaninsu da ba zasu dakatar da ɓarna ba? Ko dai dama an ajiyesu a bakin ruwan ne dan su dinga kamun kifi ko suna zaman kirga jiragen ruwan da zasu shiga su fita?". Cike da takaici yai wannan magana, ya rasa meyasa yake jin tsananin kaunar kasar Avaris.... Ni kam na ce saboda ƙasar mahaifinka ne mana, ai jininka suna ciki, dole ka so ƙasar. Zaynish ne ya ce. "Amma idan navy suna da laifi kaso 40 cikin ɗari na lalacewar ƙasar to fa ministar of foreign affairs yana da kaso 55 cikin ɗari, ministan tsaro yana da 75 cikin ɗari, sai number ɗaya na ƙasan yana da 100 cikin 100!". Kai Leo ya jinjina, su Noor dik kai suka jinjina, a dake Leo ya ce. "Ni ban yarda wani soja ya bani umarni a kan rashin adalci in masa biyayya ba!"..... Dikkansu basu fahimcesa sosai ba, Vash ya ce. "Kana nufin ba zaka yi wa AZURE biyayya ba?". Kai ya jinjina. "Ba AZURE ba, dik duniya babu wanda ya isa in yi mashi biyayya kan cutar da al'umma! Wlh yadda na yi rantsuwa da ALLAH kafin in saka wannan kakin kan zan kare rayuka, dukiya, ƙasa bakiɗaya, to billahil lazi babu wani mahaluki da ya isa ya tilastani ya bani umarnin in yi shiru ana cutarwa! Sai dai a kasheni a kan haka, amma wlh dik masu ɓarna sai na dakatar da su, Navy sun yi alƙawarin kare bakin ruwa, ba zasu bar dik wata cutarwa ta ruwa ta shigo ƙasa ba, amma me muka kama yau? Ina suke da har suka bar hakan ke faruwa? Okey baa basu izini ba ko?". Cike da takaici ya kai karshen maganar. A yadda ya yi magana yasa su Zaynish sun ji lallai ko zasu mutu ba zasu marawa karya baya ba, lallai zasu aiki dan cika alƙawarin da suka ɗauka. Cike da taƙaici Zaynish ya ce. "Hakika ba zamu zama karnukan farautar manyanmu ba! Lallai ba zamu karɓi umarnin rufe bakinmu a lokacin da ake zalunci ba, ba shakka sai dai a kashemu amma a kan gaskiyanmu!!". Noor ya ce. "Dama ai mu mutuwa ba wata aba bace a wajenmu, sai da muka tabbatar cewa mutuwa ta fi takalmar sakawarmu sauƙi a wajenmu kafin mu yarda mu sanya wannan kaki, dan haka mu matattune dama, lallai zamu tsaya a kan gaskiya!". Vash ya ce. "Ba zamu taɓa bari a cigaba da cutar da al'umma ba, zamu zama sojoji na farko da suka fara gyarawa kowa zama a ƙasar nan!"....…. Leo ya ce. "Idan sun san wasu ai basu san wasu ba, ba zamu ki karɓar umarninsu ba, dan umarninsu doka ce, amma muna da damar yin abin da muke so a bayan idanunsu ba tare da sun sani ba ai, daga yau babu wani ɗan ta'adda da zamu sake kamawa mu mayar barrack, dik kashe shegu zaku yi". Zaynish da ya fito daga Afirka me bai sani ba? A ƙule ya ce. "Abinda ko mun sha wahala, mun je yaki, a yakin har mu rasa ƴan uwanmu sojoji, mu sha wahala mu kama ƴan ta'addan mun kaisu ma bayan kwanaki sakesu ake yi wahalarmu ta tashi a banza, dan haka ina tare da kai, dik a daji zamu kashesu kisa mafi walaƙanci, mu jefa gawarwakinsu cikin manyan tekuna, in mun koma mu ce dik sun gudu, that's all". Noor ya ce. "Wannan umarni da ƙananan sojoji basa samu yasa suke shan wahala, suna filin daka amma wai suna jiran manya daga sama su basu izinin harbi, sai su tsaya ayi ta harbinsu! Abin taƙaici, amma zamu gwada masu kwarewa a kan aiki, zamu canza hukumar soja na duniya bakiɗaya". Vash ne ya ce. "Ni wani kafurin ne ma ya kawo dokar idan kana filin daga ma sai ka nemi izinin harbi?"....... Zaynish ya ce. "Kafuran suna dayawa ai, amma zamu kafa tarihi a hukumar soja wanda ko mun mutu ƴan baya zasu yi amfani da salonmu, zamu canza hukumar soja a duniya bakiɗaya kamar yadda Noor ya ce, zamu bawa duniya mamaki, sai mun ɗara FIVE LION In Sha ALLAH". Leo ne ya ce. "FIVE LIONS, kai watau AZURE ta jima tana yaye gwarazan maza fa"......... Noor ne ya ce. "Ni fa ina ganin IRON FIST ma daga AZURE suka samu horo, dan wani lokaci aikinsu yana mun kama da namu fa".......... Vash ne ya amsa da. "Ban san meyasa nike son tarihin FIVE LIONS har cikin raina ba, sojojin da suka shiga tarihin duniya a lokacin baya, sojojin da suka bada mamaki". Leo ya ce. "Ina tinanin AZURE ta hora IRON FIST gaskiya, saboda nima irin aikin da suke yi yana bani mamaki, amma ni fa ina ji a jikina IRON FIST ba mugaye bane kamar yadda duniya ta ɗauka, kawai gwamnatin duniya ne ta nunasu matsayin azzalumai saboda suna rusa zaluncinsu"........ E mana, jama'a jinin IRON FIST yana magana, kaifin kwakwalwarsu gado ce, kun ji yana hasashen ba mugaye bane. Noor ya ce. "Ai manyan duniya zasu aikata fin haka ma, da zarar ra'ayinka ya sha banban da nasu to fa kai ne ɗan ta'adda kuma mugu, su kuma asalin ƴan ta'adda mugayen basa kiransu da hakan saboda ra'ayinsu iri ɗaya"...... Kai kawai Zaynish ya girgiza, daga nan bai sake yin magana ba, ya yi shiru, suka cigaba da hira suna tafiya, sai da suka kusa isa wajen tantunansu ne Noor ya ce. "Zaynish lafiya ka yi shiru?". Nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Babu komai bro". Noor bai yarda ba, ya matsa ya rike Zaynish tare da tsayar da shi suna fuskantar juna, suka dakata da tafiya, cike da kulawa ya ce. "Bro, now we're one family, bamu da iyaye da ƴan uwa a nan, bamu da kowa, why not ba zamu haɗa kanmu, mu rungumi juna ba?". Matsawa Vash ya yi, ya dafa kafaɗar Zaynish yana faɗin. "Ka faɗa mana damuwarka mu yi maganinta a tare"...... Baya Leo ya koma ya jingina da jikin wata bishiya yana kallonsu bai yi magana ba. Nisawa Zaynish ya yi kafin ya fara basu labarin yadda ƴan ta'adda suka kashe mashi dangi, iya shi da sister ɗinsa kawai suka rage, ya basu labarin komai bai rage ba. Sun yi matuƙar tausaya mashi, Noor ya rungumesa game da cewa. "As from today we're your family also, ba kai da Aunty Ummie bane kawai, akwai mu, we are brothers now! Zamu tsaya da kai dik wuya dik daɗi, promise that kaima kana tare damu"........ Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume Noor. "We're brothers now!". Matsawa Vash ma ya yi, suka rungumi juna. Shi dai Leo yana gefe yana kallonsu bai tanka ba....... Wani irin haushi karnukan hannunsu suka fara yi, hakan yasa Noor janye jikinsa a miliyan ya ja da baya, ya tsorata da kukan karen. Ɗago kai Leo ya yi yana faɗin. "Me yake damun karnikan?". Ya faɗa tare da kuna light ɗin hannunsa a kansu. Shiru Leo ya ɗan yi game da cewa su Noor su yi shiru, dan karnuka basa haushi banza, bare ma karnukan da aka baiwa horo irin wannan....... Tsit suka tsaya karnukan na cigaba da daka haushi. Lokacin guda cikin zafa Zaynish ya ture Leo tare da damke wukar da wani mutun ya zo ta baya zai daɓawa Leo ɗin. Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu. Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. "Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye"....... Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu. Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen. Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji. Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa. Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa. Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha...... Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba. Zaynish bai iya faɗa da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu ɗaya yake faɗa shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar ɗaga Noor ya daki mutumin. Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne. Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi. Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka........ Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. "Dik ku kashesu, ba za'a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba"........ Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. "Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta'adda bane kawai!". Noor dake haki kaɗan-kaɗan ne ya ce. "Ina zargin navy ne!"...... A natse Zaynish ya amsa da. "Tabbas na zargi hakan nima"....... Vash ya ce. "Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?". Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. "Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki"..... Zaynish ya ce. "Okey, watau sun ga shigarmu wajen?"...... Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. "Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami'an?". Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son ƴan Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama'a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?".. A taƙaice Leo ya ce. "ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko'ina akwai gurɓatattu"....... Vash ya ce. "Basa tsoron mutuwa"........ Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. "Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da suka aikata". Noor dake ƙoƙarin haɗe guys ɗin can ya ɗauresu da belt ɗinsa da ya kwance ne ya ce. "Ni fa ina son addinin nan naku, saboda naga akwai adalci sosai a cikinsa, kome zaku faɗa bisa adalci kuke faɗa". Ai da sauri Leo ya ce. "Are you sure kana son shiga?"....... Kai ya gyaɗa a lokacin da yake ɗago guys ɗin ya saɓa a saman shoulder ɗinsa. "Ina son shiga, bro kyawawan halayenku sun ratsa zuciyata, ibadarku, komai naku akwai kyau, ina son shiga"........ Da sauri Zaynish ya ce. "A'a to sauƙe waɗan nan mutane ka karɓi shahada yanzu". Jinjina kai Leo ya yi tare da sauƙe mutumin da ya ɗauka a ƙasa, ya zo ya rungumi Noor yana faɗin. "Ba zamu iya jiran sai mun isa sansani ba, yanzu kawai ka furta shahada".. Ba karamin daɗi Noor ya ji ba ganin suna ta murna dan zai shiga addininsu, aikuwa hakan ya ƙara mashi kwarin gwiwa, sai ya sauƙe mutanen, Leo da Zaynish har suna haɗa baki wajen karanto mashi shahada, ya maimaita, ya ALLAH, su kaɗai suka san irin daɗin dake ransu, rurrungumesa suka yi, Vash mai karnuka ma zuwa ya yi zai rungumesa Noor ya ja da baya yana faɗin. "Bro, ba da dogs ɗin nan ba, ka bari sai mun koma sansani ka". Murmushi Vash ya saki yana ja da baya. ALLAHU AKBAR, yau Noor ɗinmu ya zama musulmi, ya rabb, yau ranar murnace a garemu mu team NOOR. Haka suka kwashi mutanen, a lokacin 5 na asuba ta yi, gari ya fara haske, kai tsaye suka ƙarisa wajen sansaninsu, cikin dabara suka shiga sansanin, in baku manta ba ai fitar sirri suka yi, kai tsaye tantinsa Leo ya ce su kai mutanen, already biyu daga cikinsu sun mutu, ɗaurin goro yai masu ya barsu a ciki. Ya fito da sauri ya nufi wajen tekun nan dan ya yi wanka su yi shirin sallar asuba, lokaci ya yi, while a daidai lokacin ita ma Arya ta fito dan ta je ta yi wanka, ita tana son yin wanka a lokacin da jama'a suke barci, dan yana son shiga gefen tekun nan wajen ƙorama ta yi wankarta, bata son shiga toilet ɗinsu na nan sansani. Zuciyarta cike da tinanin su Leo basu dawo ba, dan ita tasan basa nan, ta damu sosai, kai tsaye cikin tabkin wajen ƙoramar ta nufa, hannunta rike da soap ɗinta and gel, ta ratayo towel ɗinta a wuya, while tana sanye da pjs a jikinsa, su V dik suna barci, saura sojojin wasu suna wajen wutar da suka hura, wasu kuma suna cikin tantunansu. Da yake wajen akwai duhu saboda duwatsun ƙoramun, sannan gari bai waye sosai ba, dan 5:20 ne a yanzu, so hakan yasa bata ga Leo ya cikin ruwan ba. A saman wata karamar dutse ta tsaya, ya cire pjs ɗin jikinta kaf, ta ware dogon silky ash hair ɗinta da ya kai mata har ƙugu, ya rage daga ita sai wani ƙaramin vest zuwa cibiya wanda bashi da hannu, daga ƙasa pant fari tas mai kyau. Zama ta ya bakin dutsen tare da sanya dogon kafarta dake ɗaure da diamond chain mai kyau a cikin ruwan, ita tana saka chain da waist beat dan kwalliya, amma su V basa sakawa. Ajiye kayanta da towel ɗin a saman dutsen ta yi, ta ajiye su gel ɗinta ma. Ɗan rintse idanu ta yi tana faɗin shiiii alamar ruwan da sanyi, sai kuma ta ɗan ja tsaki game da cewa. "Ko ina su sir Nirash suke? Sun samu nasarar abin da suka je nema? Ina masu fatan cin nasara". Ta sake jan tsaki tare da datse idanunta, da sauri ta faɗa cikin ruwa tana faɗin shiii sanyi. Dik abin da take yi a kan idanun Leo, amma ita bata farga yana cikin ruwan ba, da yake yana can tsakiya. Linƙaya ta fara yi yana juyi a ciki tana jin daɗin ruwan............ Nima na juya alƙalamina dan ba'a kansu kawai zan ƙare page ɗin ba, zamu dawo anjuma mu ga ya zasu kaya a cikin ruwan nan, ga Noor ya musulunta, Zaynish da yankar wuƙa a hannu, ga haɗaɗɗun karnuka guda biyu da muka samu, ga waɗan nan miyagun da muka kama, kai ga-ga ɗin ma yawa me da shi fa. Bari dai mu je mu dawo. --------------------------🔥 CRYSTAL PALACE. "Daddy please talk to me, baka da lafiya ne?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Hannunsa yasa ya laluɓo nata hannun, ya ƙanƙame cikin nasa, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Stop crying kada abin ya mun yawa kin ji my Cherry?". Ajiyar zuciya ta sauƙe, da kyar ta iya cewa. "Daddy na bari, amma ka faɗa mun me yake damunka ne, baka da lafiya ne?"....... Ɗan matse hannunta a cikin nasa ya yi, yana ɗan lumshe idanu ya ce. "Ban taɓa maraicin uwa ba sai yau, ban taɓa jin zafin rasa Ummiena ba sai yau, my Cherry please ina son farinciki na musamman ta ɓangarenki kin ji?". Ya faɗa tare da juyo da jikinsa ya kwanta a miƙe. Hannunta ɗaya ta ɗaura a kan lion chest ɗinsa. "My gentle chaos, zan yi dik iyawata wajen ganin na wanzar da farinciki a tattare da kai, yanzu dai faɗa mun baka da lafiya ne?". Ta kai karahe tana ɗan sunkuyo da kanta a kansa kaɗan, ta ɗan ɗaura goshinta a kan nasa......... Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Lafiyata lou, kawai ina cikin damuwa ne, na tina Ummieta". "Daddy na yi alƙawarin sanyaka farinciki tamkar yadda Ummie take sanyaka"......... Ɗan miƙewa ya yi, ya koma yai kwamciyar ruf da ciki, ya ɗago kansa suna kallon juna, zallar madarar kaunarta ne kwance a cikin kwayar idanunsa, in a low way sosai ya ce. "Are you sure?". Ya faɗa yana ɗage mata gera guda. ALLAH sarki har ya mance me Abba yai mashi, masoyiya ta kwantar mashi da hankali. Tafukanta ta ware, kumatunsa dikka biyu ta tallabo, tana murmushi ta ce. "I'm very sure my gentle chaos". Ta faɗa tana ɗan matse kumatun nasa....... Zuba mata idanu ya yi yana jin wani irin tsantsar kaunarta na ratsa mashi zuciya, haɗe fuskokinsu ta yi, ko kunyar kallon cikin kwayar idanunsa bata yi, a shagwaɓe ta ce. "My gentle chaos ina sonka sosai". Wani irin kallon kauna ya ɗan bita da shi kafin in a low way sosai ya ce. "Love you more, from the button of my heart, love everything about, coz you're special". Ɗan ɗagowa ta yi, ta sumbaci gefen lallausan kumatunsa, tana murmushi. Hannu yasa ya shafi soft cheek ɗinta game da lumshe idanu, a cikin ransa yana jin zai samu hanyar rabuwa da Rimsha, shi bama wai rabuwa da ita ba, bai damu ba dan bai ɗauketa mace ba, bai yarda matarsa bace dama, amma dai koma me yana tsoron ɓacin ran Seraphina sosai, shiru ya yi yana tinani, can ya tina why not ya haɗa guru da Rimsha? Saboda Abba yana da abu guda ɗaya, idan Rimsha da kanta ta same shi ta ce bata son Aryan lallai zai yarda ya raba wannan aure, hakan kuma ba zata faru ba har sai Rimsha ta faɗa son wani. Da alama hanya ce ta haɗuwarta da guru wannan aure nasu, tabbas zai ɗauketa ya kaita gidansu, ta rayu a cikinsu matsayin sister ɗinsa, daga nan guru zai fara sonta, idan soyayyarsu tai zurfi Rimsha ba zata iya rabuwa da shi ba, tabbas zata faɗawa Abba bata son shi, shi kuma zai raba wannan aure nasu, daga nan shi kuma Aryan ɗin bayan ya saketa ya aura mata scorpion ɗin, tabbas zai wahalar da ita ta yadda ba zata taɓa jin son shi a ranta ba, hakan zai sa ta fara son guru da wuri ayi komai a gama. Lallai wannan shawara ta yi, tina haka yasa ya sauƙe dogon numfashi....... Lallai nima na shaida, wannan wata hanyace ta haɗuwar Rimsha da guru, ko kuma Lion da Rimsha ba........... 👀 Cikin zolaya ya ce. "My Cherry yanzu idan na ce mata biyu zan aura zaki yarda?"........ Zazzaro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta tamke fuska tamau. "No daddy, ni kaɗai zaka aura, babu wani mata biyu!". Tana hura dogon hancinta ta faɗa, zallar kishinsa ya gani kwance a cikin kwayar idanunta tin ma bata san menene auren ba. Kai ya jinjina tare da cewa. "Yadda kike son kawarki Rimsha ɗin nan ba zaki yarda ku auri miji ɗaya ba?"........ Siririn dariya ta ɗan yi kafin ta ce. "Mijina ni kaɗai ne, ita ma mijinta ita kaɗai zata aura!". ....... "But why?". Ya tambaya cike da mamaki, dan ya zaci sai wacce tasan aure take kishin mijinta ai. Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi game da cewa. "Daddy ba kace in daina maganar da bata dacen can ba?". Kai ya jinjina alamar haka ne ya hanata, ohk sai yanzu ya gane nufinta, watau ba zata yarda

Chapter 76 of 95