Lap gown and hand gloves suka sanya a jikinsu tin daga bakin kofa kafin su karisa cikin wajen, ga tarin computers daga gefe dayawa, kayan gwaje-gwaje suma akwaisu dayawa a ciki.
One thing about sister Maya and Zinta, dik cikin W-S-HOSPITAL ɗin nan sun fi kowa hakuri, hankali, natsuwa, kamala, kame mutunci da kuma kula da kansu, basa da faɗa, basa zuwa wajen hayaniya, akwai girmama manya, akwai tausayi da sanin darajar ɗan adam, sai dai kuma akwaisu da balain son yara, dik in suka ga yaro rasa natsuwarsu suke yi, su yi ta faman ɗauka, sun taɓa ganin jariri a hannun sister Lazy, suka dinga rokonta ta basu su rike, har da durkusawa ƙasa suka yi mata, ta ce masu babyn Dr mark ne, in suna so su je su rokesa, in ya yarda a basu to zata basu su rike.
Su kuma suna balain tsoron waɗan nan 3 doctors ɗin, dan haka suka hakura, amma har ruwan hawaye sai da suka yi, rauninsu shi ne yara.
Wasu kyawawan ƙananan transparent glass bottle suka ɗauko, a cikin wani katan baff, suka zauna a saman wasu chairs dake gaban manyan glass na chemical ɗin, a hankali suka fara ɗibar kowani chemical suna aunawa suna zubawa a cikin bottle ɗin daidai misali, sai sun auna kilonsa kafin su shirya shi cikin kwali, idan kwalin ya cika sai su ɗauka izuwa wajen da ake shirya chemical irinsa su hau shiryawa cikin glass ɗin.
Sun sanya eye protection a idanunsu kafin su fara aikin, suna yi suna hira a in da sister Maya ta ce. "Kin san wani abu sister Zinta?"...... Kai ta girgiza a lokacin da take ɗibar nata chemical ɗin. "Ina son DR MARK sosai, yana burgeni, amma ban san meyasa yake mugun bani tsoro ba, ko motsinsa na ji sai hantar cikina ta kaɗa".
"Uhm watarana komai zai wuce, mu dake mu yi aiki tukuru mu koma karkashin office ɗinsu, kin san basa ɗaukar wanda ba kwararre ba a karkashin office ɗinsu, shiyasa kika ga na kara dagewa dan in zama irin nurses da suke aiki tare da su, kamar dai wancan fitinanniyar Lazy, amma ke ina ga tsoron matar DR MARK kike ji shiyasa kike shankarsa over har haka"..................... "Hmmmm, bana tsoron matarsa, saboda ban taɓa ganin tana masifa ko wani abin mara kyau ba a cikin makarantar nan. Ni babban abin takaicina ma shi ne yadda basa ɗagowa su kalli mutum".
Zinta da shegen son gulma ce tai ƙasa-ƙasa da murya wajen cewa. "Kuma na ji an ce Dr James har hugging na Lazy yana yi, har kiss da sauransu".......... "Ina fatan shiruna ya zame mun alkhairi". A cewar Maya da bata cika son zaman gulma ba, dan ma dai Zinta best friend ɗinta ce yasa idan tana gulma bata tashi ta bar wajen, amma tana ƙoƙarin hanata gulmar, banda haka ita ba'a gulma da ita, kunji ta ce tana fatan shirunta ya zame mata alkhairi, dan tasan abin da Zinta bata sani bane, abin da ya fi kiss Dr James yake yi da Lazy, amma ba zata faɗa ba ko dan ma kada zuciyar Zinta ɗinta ya buga.
"Matsalata dake kenan Maya, komai sai ki ce kina fata shirunki ya zame maki alkhairi, to da kike wannan magana wani zanje in faɗawa ne? Ko dai kina tinanin wani na jinmu ne?"...... Kai ta girgiza tana cigaba da gwada chemical ɗinta, a natse ta amsa da. "Ba wani zaki faɗawa ba, kuma babu mai jinmu, kawai dai manta da maganar, ya batun shirin partyn da zamu yi next month na kammala karatun ajin farko?".
"Na shirya mashi, amma kin san idan na tina karatun aji na biyun da zamu shiga aka ce ya fi kowanne wahala gabana faɗuwa yake yi? Ina jin kamar ba zan iya ba, yanzu wannan karatun ma da ya muka kare? Wahala kan wahala"....... "Zaki iya ƴar uwata". Ta faɗa cike da ƙoƙarin kwarara mata gwiwa...... "Ina sa ran na iya sosai"....... Da haka suka cigaba da hira suna shirya chemical ɗin nan har suka kammala, sannan suka fito, a lokacin yamma ta kawo kai, karfe 5 suke tashi daga aiki sai su koma wajen kwanansu na ɗalibai, za su shiga class daga 7 na safe zuwa 1 na rana, da sun fito zasu wuce wajen practical, karatunsu ba kamar na sauran likitoci bane, su special ne, suna karatu ana haɗa masu da aiki kullum dan su kware.
Kamar yadda AZURE BARRACK take yaye jami'ai gifted haka WS-HOSPITAL take yaye likitocin da babu irinsu a duniya, mayun bincike mayun aiki tamkar ba ƴan adam ba, a yanzu ba zaku gane komai ba, sai tafiya ta yi nisa damu a cikin WS-HOSPITAL zaku fahimci karatun! Mu je zuwa ku dai.
A lokacin da suka fito wajen lap ɗin almost 5:20, a gurguje suka yi shirin tashi, suka cire lap gown na jikinsu da hand glove ɗin, sannan suna shirya tsab. Dawowa wajen sashen su Dr James suka yi, a nan Sister Zinta ta ce. "Maya mu je ki rakani waiting room na Dr James".......... "Kin san halinsa ƙawata, shi baya son ya ce abu a saɓa mashi, ke kaɗai ya kira, idan ya ganmu tare ransa zai ɓaci, kinga hakan zai sa ma ki rasa damar da yake son baki, ba zan so ki rasa wannan dama ba, ki je ke kaɗai kin ji? Zan jiraki a section B".
Ta san maganar Maya gaskiya ce, ba'a mashi abin da bai ce ba, amma tana mugun tsoron zuwa ita kaɗai ne, dan shakkarsu take ji. Cigaba da kwarara mata gwiwa Maya ta yi har ta yarda zata tafi ita kaɗai, tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi waiting room ɗin nasa dake gefen office ɗinsa, kafin ka shiga office ɗinsa kofar room ɗin yana daga gefe. Ciki ta shiga bakinta a ɗauke da excuse.
Babu kowa a ciki sai wani irin ni'imantaccen kamshi dake tashi, ga sanyin Ac dake buga ko'ina, sofa set set guda ɗaya ne a cikin room ɗin, a tsakiyar sofas ɗin akwai wani lallausan Dubai rug a wajen, sai karamar dispenser, sai kuma wata karamar freezer daga gefe dan zuba drinks su yi sanyi, ga kuma wata karamar show glass mai ɗauke da glass cups masu kyau kuma very luxury. Ɗakin dai ya haɗu sosai.
A saman sofa ɗaya ta zauna, tin da suke basu taɓa shigowa sashen su Dr James ba, dan su aikinsu a wajen Chemicals yake, ta wannan ɓangare suka fi kwarewa, sai sun je aji biyu zasu koma sashen dabbobi, daga sashen dabobi dama sai babban sashe watau na su Dr James. Zaman good 30 mins ta yi, sai faman tinane-tinane take yi da kalle-kalle, ta yi tinani ya fi dubu kan dalilinsa na kiranta, amma ta rasa gane dalili, sai kawai ta yi shiru.
Ta gaji da zama da zuba idon ganin shigowarsa, amma shiru, sai a lokacin da cire tsammani, ta shiga wata tinanin, ta manta da zai shigo sai ta ji an turo kofar room ɗin. Tin daga ƙasa ta fara kallonsa, yana sanye da sportswear ba kayan aiki ba, da alama ya ɗan jima da tashi aiki, still fuskansa da nose mask, and ya ɗaura jacket a kan kayan saboda wani irin fitinannen sanyin da ake zubawa, kafarsa sanye da ankel socks and crops farare.
Ai yana shigowa ta miƙe tsaye a wani irin slow tana kallonsa, kowani motsi nasa a kan idanunta. Dr James irin mazan nan ne masu burge mata da shiga rai, ga shi da salo ɗan gaye.
A saman sofa ya kariso ya zauna, sai da ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya gama shan kamshinsa kafin ya ce. "Get out of my office!". A ɗan kaifafe ya faɗa, saboda ya ji haushin yadda ta kara 30 mins a kan lokacin da ya bata, shiyasa bai shigo da takardun da zai bata ɗin bama, ya ga lokacin da ta shigo ɗakin ta Camerar dake ɗakin, karfe 5:30 ta shigo, shi kuma 5 yasan suke tashi, kuma 5 ya ce ta zo ta same shi, shi ne zata ɓata mashi lokaci, ba zai ɗauki wannan iskanci ba.
Tsoro da shakkarsa yasa bata yi ƙoƙarin bashi hakuri ba, da sauri ta wuce ta fita. Tana fitowa suka ci karo da sister Lazy dake ƙoƙarin shiga office ɗinsa hannunta rike da tarin files na manyan ayyuka dana rahotannin dabbobi.
Tana ganin sister Zinta ta fito daga waiting room ɗinsa ta dakata tare da juyowa gareta, sai dai kafin tai mata magana Zinta ta wuce da gudu tana ƙoƙarin toshe bakinta saboda wani irin kukan da yake shirin kubce mata, ta ji zafin rasa wannan dama, tin bata wuci 16 years ba take dakon wannan dama, shekara biyu kenan tana aiki tukuru dan ta samu attention ɗinsa, yau ta samu amma ta sake rasawa, dole ta ji zafin wannan abu.
Da gudu ta nufi in da zata samu Maya. Zaune ta iskota rike da wani littafi tana dubawa. Da gudu ta zo ta ja hannunta tana faɗin. "Sister mu je"..... Maya na shirin tambayarta lafiya, amma ganin tana kuka yasa ta fasa tambayar tata tare da miƙewa kawai ta bi bayanta. Da gudu suka wuce sashen kwanan ɗalibai dake can nesa da lap ɗin, kuma shi ne section A a wajen, na ce maku sashe 5 ne a cikin wajen, sashen kwanan ɗaliban lafiya shi ne section A, sashen dabbobi shi ne section B, sashen chemical shi ne section C, akwai section D da section E wanda labari bai isar damu wajen ba bare mu san me a cikinsu.
Da gudu suka koma hostel ɗinsu. Ita kuwa sister Lazy da sauri ta shigar da takardun office na Dr, jikinta har tsuma yake wajen yin gaggawar fitowa ta bi bayan sister Zinta dan ta je ta ji me ya haɗata da Dr James da har zata shiga waiting room ɗinsa kuma ta fito tana kuka, ko dai akwai abin da yai mata ne?.
Kai tsaye sashen kwanan ɗalibai Lazy ta nufa, sai huci take yi, dan a duniya idan ana son aga fushinta wata ta raɓo Dr James, a cewarta zata iya kisa a kansa.
A lokacin da ta shiga room ɗinsh suna zaune sister Zinta na faɗawa Maya abin da ya faru sai ganin Lazy a kansu suka yi, cike da tsoro suka mimmiƙe tsaye, ɗaure fuska tamau Lazy ta yi, in a harsh way ta ce. "Ke me ya kaiki room na Dr James?"....... Tsuru-tsuru da idanu Maya ta yi, dan akwaita da tsoro sosai, gara ma sister Zinta da ɗam kwarin zuciyarta.
Hannu tasa ta goge hawayen dake zuba mata, cikin girmamawa ta ce. "Shi ne yai inviting ɗina zuwa wajen........". Bata iya karisa maganar ba sakamakon wani bahagon marin da Lazy ta sauke mata, cikin fushi ta ce. "Ke har kin isa Dr James yai inviting ɗinki zuwa wajensa? Wacece ke? Dame kike taƙama?".
Note, yauwa na ji kuna cewa dikka malaman asibitin nan kamanninsu ɗaya, ba haka na ce ba, ce maku ma yi suna ɗan kamanceceniya, amma kowacce da irin halittarta da kuma yanayin kamanminta, kyan fuskarta da kyan jikinta, ko yanayin hasken skit ɗinsu ya bambamta, kawai dai shekarunsu ne dikkansu ɗaya watau 18 years, in da suke kamanceceniya kuma shi ne yanayin jiki, ƴan caras-cas dasu zubin ƴar tsana na ce maki.
Dafe kuncinta sister Zinta ta yi, idanunta suka kara kawo ruwa sosai, bata da bakin iya ramawa saboda sister Lazy a karkashin office ɗinsu Dr James take, dole ne su yi mata biyya. Zazzaro fararen idanunta Maya ta yi, tana son ja da baya sister Lazy ta cakumo wuyar rigarta, cikin faɗa ta ce. "Kece kike zugata ta shiga gonata ko? An faɗa maku Dr James mara aji ne shi da zai kula irinku? This should be the first and last da zan sake ganinku a arear da yake, ku ba a section B kuke aiki bama? Me ya kaiku side ɗinsu?!". Ta faɗa tana shaƙe mata wuya.
Gagara amsa mata suka yi, cakumo wuyar rigar Zinta ma ta yi, tsabar mugunta ta haɗa kansu ta gwara da juna kafin ta ce. "Dik wacce ta sake shiga gonata sai na lahira ya fita jin daɗi!".
Su kuwa tsabar tsoronta babu wacce ta iya koda kara ne, dik da sun ji zafin buga masu kai ɗin da ta yi, amma suka shanye har sai da ta gama zazzaga masu jajjagen balain nata, ta kwashi kafafunta mai kama da na sauro ta nufi waje fuuuuu, sannan ne suka zazzauna a gefen bed ɗinsu tare da rushewa da kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsu suna luguiguita gaban goshinsu, sannan ne suka yi shiru, suka rungumi juna cike da takaici da danasanin zuwa side ɗinsu Dr James.
Almost 30 mins suna a haka kafin su miƙe zuwa toilet ɗinsu, abinku da ɗaliban lafiya, ko'ina a cikin toilet ɗin nasu tsab-tsab har sheki yake yi, fuska suka wanke a wajen wash hand base, sannan suka fito, saman gado suna koma, kowacce ta fito da littafanta ta fara nazari kan Chemicals da suke karanta a yanzu, babu wacce ta sake cewa ƴar uwarta uppan suka shiga karatu.
Ita kuwa Aunty masifatu kanwar jarabatu watau sister Lazy kai tsaye room ɗin Dr James ta nufa tana ta wani uban huci, ran ƴan mata ya ɓaci.
TO MY PEOPLE ME KUKE TINANI A WANNAN ƁANGARE? MU JE ZUWA!.
CRYSTAL PALACE.🔥
Zaune Seraphina take a saman gadonta, tana rike da waya tana dannawa, ta shiga world live a wayar tana dudduba labaran duniya dan jin me yake gudana. Lokaci guda ta zunduma ihu tare da miƙewa tsaye.
Da gudu Madam da ɗiyarta Aisha suka shigo dan jin meyasamu Seraphina take ihu kuma, a tsakiyar gado suka iskota tana murmushi ta kurawa waya ido, cikin kiɗina Madam ta ce. "Babyn daddynta lafiya? Wannan ihun fa?".
Da gudu ta diro ta zo ta rungumi Madam tana faɗin. "Mom ki zo mu yi murna, ana hira da Admiral, my hero, jarumin da babu biyunsa a duniya, kinga hira da shi ake yi a kan IRON FIST ɗin nan da suka addabi al'umma, an miƙa masu case ɗin ne su kamosu, mom admiral basu taɓa karɓar aiki kuma su faɗi ba, yanzu karshen IRON FIST zai zo, zasu daina ta'addanci da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba". Dik a kiɗime take magana tana haɗe words, daɗi yasa bata san ma me take faɗe ba.
Kun san waye wannan da Seraphina ta ruɗe a kansa? Gaskiya bai taɓa karɓar aiki kuma ya faɗi ba, kwararre ne, jami'in SEAL U.S Special Operations ne, idan ana maganar Seal a waje to ba'a kiran dik wani jami'i, Seal yana nufin SE Sea ruwa kenan, A Air sama kenan L Land kasa kenan, a takaice SEAL na nufin Sea, Air, and Land. Su ɗin sojoji ne da ke iya yaƙi a ruwa, sama, da ƙasa, Su ne ƙwararrun sojojin U.S Special Operations da aka basu horo mai tsanani sosai da babu biyunsu, su zasu iya aiki a kowanne irin muhalli, teku, kogin, bene, cikin ruwa, kan ƙasa, da kuma ayyukan da ake tsallaka cikin jirage ruwa da sama, ba kamar sauran sojoji suke ba, a sauran sojoji zaku ga na ruwa daban, na ƙasa daban, Air Force ma daban, kuma kowannensu da irin horon da ake bashi, to su haɗe masu horon dikka ake yi a masu, imagine!
Baa ɗaukar mutum horon Seal sai idan ya karɓi horon aikin soja, dan haka kawai ba zai iya karɓar horon seal ba, ba kowa yake iya haye horon ba ko da ya karɓi horon soja, za'a ɗauki mutane 50 amma da kyar 5 suke iya hayewa basu mutu ba, a horon suke mutuwa, manyan tekuna ake jefasu a masu horon sojojin ruwa, sanna a masu horon sojojin sama, azo a masu horon sojojin ƙasa, ga training na sirri da ake basu kan kwarewa a ɓangaren fasaha da sarrafa computer, wlh dik US su ne jami'an da babu biyunsu, kuma basu da yawa saboda ba kowa yake iya tsallake horonsu ba.
To shi wannan guy da Seraphina take haukar cewa yana burgeta shi ne O-9 Vice Admiral na Seal Special Operations, mutum ne da babu wanda yasan fuskansa, kullum suna sanye da covering nose mask, kuma idan ba babban aiki irin kama IRON FIST ba ba zaku gansu a hira da wasu ba, basa shiga jama'a saboda suna ɓangaren jami'an sirrinsu ne, shiyasa basu bari an san face ɗinsa ba.
Su uku ne mafiya kwazo a hukumar Seal, wanda matsayinsu yake tafe a jere. Da O-10 Admiral mai matsayi kaman ace GAT a hukumar sojan ƙasa, sai O-9 Vice Admiral mai magana a wannan hira ta yanzu da Seraphina take gani, sai kuma O-8 Rear Admiral upper half, su ukun nan daban suke, kuma ba'a taɓa kallon complete face ɗinsu ba, tin Seraphina bata yi wayau sosai ba take kaunarsu a jami'an Seal, dan time to time tana bibiyarsu a wayar mom ɗinta, tana mugun son jarumai ne yarinyar.
Amma kun san wani abin mamaki? Wannan da ake live da shi ɗin fa ba kowa bane face Aryan, a idanun duniya su ne seal, a bayan duniya sune IRON FIST, yanzu gwamnati ta gagara kama IRON FIST shi ne aka damƙa masu case ɗin, dan an san dik US babu jami'ai masu aiki da cikawa biyun, to my people ya kuke ganin wannan wasa zata kaya? Zasu gagara kama IRON FIST ne su zamana karo na farko a rayuwansu sun faɗi a mission? Ko kuma zasu kama kansu ne a matsayinsu na IRON FIST? Ga shi dai sun karɓi mission ɗin, sun kuma rattaɓa hannu! Me kuke tinanin zai faru? Zasu yi aiki da basira a wannan ɓangaren ne ko kuwa dai ya zasu yi?.
IRON FIST a bayan fage, US SEAL SPECIAL OPERATIONS a idanun duniya, jami'an da duniya ke girgiza da jin sunansu, gaskiya su Lion akwai ƴan rainin wayau, to yanzu ya zasu gudanar da wannan mission fisabilillahi? Gasu can a AVARIS suna gudanar da bincikensu a kan aikinsu na IRON FIST, sun hau live sun sanar da sun karɓi aikin kama IRON FIST, kai ana wani iya shege a littafin FIVE LIONS, nima zan so ganin ta yadda zasu kama kansu kam!.
Da yake dik wanda ya kwana a Us ya tashi yasan su waye Seal Special Operations (SSO) bari in taƙaita masu sunan, kowa yasan su waye jami'an SSO, hakan yasa Madam ta ce. "Kai Alhamdllh, lokacin kawo karshen waɗan nan IRON FIST ɗin ya yi babyn daddynta".
Matsawa Seraphina ta yi, ta shige jikin Madam tana gwada mata yadda SSO suke magana a live, live ɗin da ya tara manyan jami'ai daga sassar duniya, manyan shugabanni, kowa kawai burinsa yai magana da su, su kuma da Aryan ne da guru a wajen suke magana, Lion yana barci, bai ma san ana yi ba, kuma shi ne admiral ɗin da ya rattaɓa hannu a kan misson na kawo karshen IRON FIST a duniya, amma kunga ɗan duniyan barcinsa yake hankali a kwance, sun je yawo ne suka dawo, yanzu ba jimawa dawowarsu daga Arewacin ƙasar Avaris, sun je binciken da suke yi ta bayan fage, dik a gajiye ya dawo shiyasa yake barci.
Idanu Madam ta zuba tana ganin yadda manya ke magana, idan Aryan zai yi magana sai kowa ya haɗa natsuwansa, gasu ƴan gayu ne ƴan kwalisa, akwai shegen iya ɗaukar wanka su ukun nan, kuma kaya iri ɗaya suke sanyawa, komai ɗinsu iri ɗaya, zo ku ga yadda ake magana cike da jarumta ga sharp voice, sannan ga class da tsantsar natsuwa sai IRON FIST.
Da sauri Seraphina ta ce. "Mom ki bani wayarki in kira daddyna in faɗa mashi ya kunna world live ya ga SSO suna magana, bana son kiransa da wayana dan kada live ɗin ya katse, ina son in faɗa mashi kuma ina kallon live".
Da yake na faɗa maku dikkansu fuskokinsu a rufe sai bata gane Aryan ba, kuma iya face ɗinsu ne a Camera, sannan suna sanye da p-cap daga shi har gurun. Ita ma Madam bata gane Aryan bane, da yake ita dama bata san ainahin face ɗinsa ba, Seraphina kawai ya nunawa, idan zai shigo gidan kuma shi yasan hanyar da yake shigo kai tsaye sai room na Seraph kaman wani aljani.
Da sauri Madam ta bata wayar, shigar da number Aryan da ya bata ta yi, jikinta har yana rawa wajen shigarwa, sai ta ga ashe Madam tana ma da number, danna mashi kira ta yi. Suna tsaka da live ɗin sai ta ga vice admiral ya miƙe tare da barin wajen, turo baki ta yi tare da cewa. "Mom ina vice zai je?".
"Kai babyn daddynta akwaiki da rigima, to gama wayar mana sai ki fara neman jin ina zai je". Madam ta bata amsa cike da mamakin halin Seraphina da shegen son jaruman mutane...... Tin ɗazun Aryan ya yi picking call ɗin yana jinta tana zubawa Madam shiriritarta, da ya ga alamar ta mance da ta kirasa sai ya ce. "Baby what's going on?".
Murmushi ta yi tare da ƙara manna wayar a kunne da kyau, cike da farinciki ta ce. "Daddy ka kunne wayarka ka duba Us military world live yau my hero's suna live"...... Mamaki ne ya kama shi, shiru ya ɗan yi kafin a ransa ya de. "Blood is thicker than water, watau Seraphina bata sansu bama sonsu take yi, bata taɓa ganin Lion and Guru ba, amma suna cikin ranta sosai, bare shi da ta san face ɗinsa, tana tsananin son shi sosai, ALLAH mai iko.
Sayayyar voice ɗinta ne ta katse shi da cewa. "Daddy baka jina ne? Please ka je ka gansu, jarumai ne, zasu kawo mana karshen IRON FIST masu kashe mutane fa"...... Face ɗinsa ne ta ɗan canza, a sanyayye ya ce. "Baby baki son IRON FIST ne?"........ Da sauri ta gyaɗa mashi kai tare da cewa. "I hate them daddy, mugaye ne, suna kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, daddy su fa suka kashe mom and daddyna, don sune terrorists na ƙasar nan, nasan for sure su suka kashe mammyna!". Ta kai karshen maganar idanunta na cikowa da kwallah.
"Is okay baby, Don't cry, I agree that you don't like IRON FIST, but don't cry over them, I'm going to hang up now, I'll call you back later, I'm doing something right now". Ya kai karshen maganar da alamar damuwa a tattare da shi, bai ji daɗi ba yadda kowa yake masu kallon manyan ƴan ta'adda.
"Daddy make sure you watch the live ka ji?"....... Da sauri ya amsa da okey tare da katse kiran. Nisawa yai tare da ɗan jingina da jikin sofar parlon ɗakin da suka kama, yai shiru yana tunanin kukan Seraphina, da yanzu yana CP babu abin da zai hana shi zuwa gareta ya rarrasheta, yasan sai ta yi kuka tin da tai maganar iyayenta, shiyasa yai saurin katse kiran dan kada ya ji kukanta, yasan Madam zata rarrasheta shiyasa bai damu sosai ba. A fili ya ce. "Zayra'an baka yi wa Seraphina adalci ba ko kaɗan, me laifinta zaka ce baka sonta a kusa da kai? Ka manta hakkinta dake kanka? Ka manta ita ɗin amana ce a kanka da ALLAH zai tambayeka ka rike amanar? Ya ka yi da ita? Gaskiya baka kyauta ba!.....".
Jin motsin fitowa ne yasa yai shiru tare da ɗago kai ya kalli kofar shigowa, guru ne ya fito yana zura hannayensa a cikin aljihun pj's ɗin jikinsa. A kusa da Aryan ya zauna, cikin natsuwa da sanyin murya ya ce. "What are you thinking bro?".
Ɗago idanu a kansa Aryan ya yi tare da cewa. "Nothing, ka gama magana dasu ne?"...... Kai ya jinjina alamar yeah, sannan ya ce. "Bro akwai gagarumin matsala a arewacin Avaris, musamman da muka je barrack na arewacin ƙasan, wai menene banbancin arewaci da gudancin ƙasar? Meyasa commond hukuncinsu daban-daban, kundin dokoki jahohinsu da hukuncinsu daban-daban, meyasa? Horon sojojinsu daban-daban, a barrack na gudancin nan ka duba yadda suka hora su Nirash! Komai a wadace, ga tsari da muhalli mai kyau, meyasa barrack na arewaci da yunwa ma ake hora sojojin? Abinci kaɗan za'a basu sai dai su kira iyayensu daga gida
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 95