son GAT, kuma ta yarda zata bisa su je su rayu a gidan.
Daddynta ya gane tana wasa da hankalin GAT shiyasa tai mashi raɗa a kunne, dan haka sai bai yi magana ba, ya rungumeta kawai yana jin wani irin farinciki. Daga haka ya ce to su je su yi dinner, GAT ne ya ce ai shi wannan amince da ta yi yasa ya ƙoshi, ba zai iya cin komai ba. Cike da farinciki ta ce. "Bari in kawo maka green tea nasan zaka sha".
Daddy Noor dai goodnight yai masu ya miƙe ya fita abinsa, da sauri ita ma ta miƙe da nufin ta je ta kawo mashi green tea. Bayanta ya bi da kallo cike da tsantsar so da kauna yana tinanin irin mantar da ita komai da zai yi da soyayyarsa idan suka koma.
Yana zaune a wajen har ta dawo ɗauke da kyakkyawan plate and cup mai ɗauke da green tea. A jikinsa ta zauna tare da fara bashi tea ɗin a baki, ta ajiye plate ɗin a ƙasa. Ai manta komai daddy GAT ya yi, ya saki jiki sai yadda ta yi da shi, ya zama ɗan yaro a hannunta. In takaice maku dai wannan dare bai je ya yi wa su Arya goodnight da ya saba ba, bayan ya kammala shan tea ta fitar da cup ɗin, dawowa cikin ɗakin ta yi tare da zama a jikinsa.
Miƙewa da ita ya yi suka koma saman bed, ya zaune tare da jingina da jikin headboard na bed ɗin, ta kwantar da kanta a saman kirjinsa, hira suka fara cike da tsantsar so da kaunar juna, yana ta zuba mata salon soyayya mau narka zuciya, tin tana basarwa har ya fara kureta ta fara ƙoƙarin fito mashi da nata salon. E kam gidansu Noor ya ɗauki launin malam buɗe takarda. Bari dai mu je wani wajen mu dawo.
----------------------🔥
Zaune Seraphina take a saman gado, hannunta rike da waya tana dannawa, tin da aka sayi wayar nan yarinyar ga bata barshi ya huta ba, sai barci ne yake rabata da dannarsa. Madam tana parlo tare da ƴar kakkawar ƴarta, suna breakfast ne, a tunaninsu Seraphina bata tashi daga barci ba, shiyasa basu nemata ba, dan Aryan ya ce kada su bari wani abin ya taɓata, idan tana barci a bari sai ta tashi a yi dik abin da za'a yi, kada a tadata, shiyasa basu shigo room ɗin ba.
Ita kuma nan ta tashi har ta shiga buga game a waya. Tana sanye da sleeping dress, guntun wando zuwa cinya, da kuma ƴar vest, dikka farare kal, kyakkyawar ash hair ɗin nan nata dik a wargaje saboda barcin da ta tashi, ɗan pink lips ɗin nan nata a bushe alamar yunwa take ji, ko brush bata yi ba, dama Rimsha zata kira sai kuma ta tsaya buga game.
Ta yi nisa cikin game da take bugawa, ko kaɗan bata ji shigowarsa ba, kuma ya yi sallama, amma bata ji ba. A kusa da ita ya kariso tare da sanya hannu ya kwace wayar, cikin zafa ta yunkura zata bi wayar ta kwace. Tana ɗago ido ta ga mutum a tsaye, wani irin zabura ta yi tare da kurma ihu, baya ta ja tana faɗin. "Who are you?".
Zama a saman sofa Aryan ya yi tare da cewa. "Your daddy, baby taɓa wayarki ya yi yawa"....... Zuba mashi waɗan nan gulu-gulun eyes ɗin nata ta yi, bata yarda shi bane, amma kuma muryansa ne, yau da ainahin fuskansa ya zo mata, daga yau ba zai sake ɓoye mata kansa ba ya ce.
Ganin ta bushe da kallonsa ne yasa ya kyasta mata yatsunsa a kan fuska, zabura ta yi tare da cewa. "Is this a dream? The voice is for my dad, but your face isn't". Ta faɗa tana ɗan ja da baya. Dama yasan ba zata yarda lokaci guda ba, dan kada ku manta shekaru biyu kenan yanzu suna tare, kuma da wancan fuska ta san shi, rana tsaka ta gansa da wani face kun san ai za'a kai ruwa rana kafin ta yarda.
Hannu yasa zai kamata ta yi saurin ja da baya tana zazzare ido, sai satar kallon kofar fita take yi, tana son dira kasan bed ta gudu. Yunkurawa ya yi zai kamota ta yi saurin dirowa ƙasa da gudun gaske. Miƙewa ya yi cikin zafa, taku ɗaya ya yi ya damkota ta waist ɗinta tare da sanya hannu ya toshe mata bakin da take ƙoƙarin zunduna ihun nan.
A saman bed ya zauna da ita tare da matseta da jikinsa sosai, ya rike hannayenta gam kafin ya ce. "Natsu ki ga wani abu". Ya faɗa tare da zame hannunsa daga bakin nata. Zuba mashi ido ta yi, kallon mamaki da firgici haɗe da ruɗani dik take binsa da shi. Shima ɗan zuba mata ido ya yi na a kallah minti ɗaya kafin ya fito da wancan face ɗin nasa ya sanya a fuskansa.
A maimakon ta natsu ta yarda da shi sai ta kara firgicewa tana ƙoƙarin guduwa, kankameta da kyau ya yi tare da fara ƙoƙarin shawo kanta. Da kyar ya samu ta yarda ta natsu kuma ta aminta da shi. Sai kuma me? Dariya ta fara yi tana faɗin. "Daddy I'm crazy, see me running away from you, ko ina zan je? My daddy you're so handsome over, oh my God, see beauty, amma daddy ka yi kama da Rimsha friend ɗita, bakinku da idanunku iri ɗaya, but ka fita kyau sosai". A ruɗe take maganar, ta ga kyan jinin ƙuraishawa dik ta rikice, zallar madarar kyan da babu mix!
Lokaci guda ya ɗan ɗauke wuta, kalaman Ammie ne suka dawo cikin kansa, in da take ce mashi. "Arya ba zaka taɓa iya barranta kanka da Rimsha ba, kai ubanta ne, dik wanda ya ganka ya ganta yasan kai mahaifinta ne, jini ba wasa ba, ka daina nuna tsana a gareta, ina mai tabbatar maka dik in da ka shiga in dai an sanku to fa sai an kira maka sunanta, ka sani da ku Rimsha ta yi kama yadda zai baku tabbacin ita ɗin taku ce ba ta mahaifiyarta ba, kamanninku ALLAH yasa mata ba kamanin uwarta ba, meyasa zaku cireta daga cikin ku?".
Shafa lallausan kumatunsa da Seraphina ta yi ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa, da sauri ya nisa tare da dawo da kallonsa da kyau a kanta.............. "Daddy tinanin me kake yi?".... Kai ya girgiza mata alamar babu komai. "No daddy, kana tinani mana, faɗa mun abin da kake tinani in tayaka tinani a kansa?".
Yarinya mai shegen wayau ga hankali da tinani. Sumbatar lallausan kumatunta ya yi tare da cewa. "Muje toilet ki yi brush queen of pressing phone"...... Turo ɗan bakinta ta yi tare da cewa. "Daddy ka bari in kira Rimsha to"..... Yana binta da wani irin kallo da idanunsa da yau suka yi zubin munafukai marasa gaskiyar nan ya girgiza mata kai alamar a'a bai yarda ba.
Shagwaɓa ta sanya mashi tana turo mashi ɗan bakinta, sumbatar ɗan bakin nata ya yi, wani irin yanayi ya ji lokacin da lips ɗinsa suka taɓa soft lips ɗinta dake da laushi kamar audiga, sai da ya ji shock a jikinsa, da sauri ya miƙe da ita tsaye tare da nufar toilet da ita. A gaban wash hand base ya sauketa tare da ɗauko brush ya hau zuba mata mayukan goge baki.
Tana turo baki ta ce. "Daddy i realized something"...... Da sauri ya kalleta yana jiran jin me zata ce ba tare da ya yi magana ba. "Daddy why, why baka son Rimsha? Anytime idan na ce zan yi magana da ita sai ka ce I should leave her, kuma idan ina faɗa maka hiranmu baka son ji, ka santa ne daddy da yasa baka sonta?".
Zazzaro mata idanu ya yi, bai yi tinanin Seraphina tana da wayo da kaifin kwakwalwar iya dogon tunani haka ba, yarinya sosai yake ɗaukarta. Gudun kada ta gane yasa ya ce. "Baby ni ban santa ba, kawai bana son ki dinga yin friends ne, koba ita ba haka zan yi wa kawayenki dan bana son abota".
Wani irin kallo ta wurga mashi mai kama da na tuhuma kafin ta ce. "Daddy is seems like you're hiding something, you look like Rimsha! And you don't.......". Da sauri ta danna mata brush a baki, yanzu ya fahimci yarinyar nan ba dai wayau ba, ka ji wani kaifin tinani da basira, har ta fara ɗagosa, ya yi nadamar nuna mata ainain face ɗinsa, ya nuna mata ne kuma ba dan komai ba sai dan kada shakuwarta da wancan face ɗin nasa ta yi yawa ta yadda hakan zai zame mashi matsala a nan gaba, amma gashi yana shirin kwantowa kansa ruwa, a ransa ya ce dole ya rabata da Rimsha ko kuma ya sanya aje ayi wa Rimsha surgery a canza mata kamanni, dik sai ya ji zafin yadda yarinyar ta ɗauko kamanin dangin ubanta bata yo uwarta ba.
Goge mata baki yake yi amma ya luluƙa duniyar tinani, dan har sai da ta ce. "Daddy is okey". Cire brush ɗin ya yi yana kallon kyakkyawan fuskanta ta cikin mirror, dika-dika tsayin Seraphina ko kirjinsa bata kai ba, shiyasa yake kara ɗaukarta a yarinya kamar sosai. Ɗauraye mata bakin ya yi kafin ya ce ta yi wanka ta zo. Daga haka ya fito waje zuciyarsa cike da tunanin meyakamata ya yi dan cire mata zargin yasan Rimsha da take yi.
A saman bed ɗinta ya kwanta yana tinanin har barci ta yi awon gaba da shi. Lokacin da ta fito daga wanka ya yi barci, a kusa da shi ta tsaya tare da zubawa kyakkyawan fuskansa ido na ɗan lokaci, kamar zata tashesa sai kuma ta fasa, yanzu ɗan zamanta da Madam har ta kara natsuwa da hankali, ta fara sanin daidai da ga daidai ba. Madam Rohisha musulma ce cikakka, dik wani ɗabi'u da abin da ya dace da musulmai shi take koyawa Seraphina.
Yanzu haka ta cusa mata kaunar son rufe jikinta, shiyasa ma kuka ji bata ce yau Aryan yai mata wanka ba, Madam ta faɗa mata jikinta sirrinta ne, kada ta bari kowa ya ganin mata, hakika Madam tarbiya take bata irin yadda uwa take baiwa yarta, amma kuma sai wanda Seraphina ta yi ra'ayi take ɗauka, ga ɗaura ɗankwalinan ba yadda Madam bata yi da ita ba amma yarinyar nan taki, haka take sakin gashi abinta, ko toilet haka take shigewa.
Closet ɗinta ta nufa dan ta shirya. Wandon jeans guntu zuwa gwiwa ta sanya da riga mai kamar hannu, ta wuce wajen Madam ta gyara mata kai, sai tashin kamshi take yi ta dawo room ɗin. Da Madam ta ce ta zo ta yi breakfast sai ta ce tana zuwa. Ta zo ta zauna a saman side sofa tana ta faman kallon kyakkyawan fuskansa.
A daidai lokacin wayansa dake cikin aljihu ta fara kara, hakan ya yi sanadin farkawansa, a kan fine face ɗinta ya sauke idanunsa. Ba tare da ya ɗauke kallonsa daga kanta ba ya ciro wayarsa daga aljihu, ko bai diba ba yasan Lion or guru ne suke giransa, su biyu ne kawai suke da wannan number da aka kira yanzu watau sim 2 ɗinsa.
Idanunsa a kanta ya yi picking tare da karawa a kunne, sannan ya ɗaura yatsansa ɗaya a saman lips ɗinsa yana mata nuni da ta yi shiru. Slowly ya motsa kyakkyawan soft lips ɗinsa wajen cewa. "What's going on? Meyasa kake tambayar ina nike?"....... Ɗan bakinsa kawai Seraphina take kallo, ya yi magana amma ba zaka taɓa cewa ya motsa lips ɗin ba.
Shiru ya ɗan yi for almost 1 minute kafin ya sake cewa. "Give me some minutes I'm coming". Yana gama faɗar haka ya ciro wayar tare da katse kiran. Miƙewa zaune ya yi idanunsa dik barci, har sun yi ja. Kasan bed ɗin ya sauƙo tare da cewa. "Baby zan dawo anjuma". Ya faɗa yana ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinsa dake ɗan murɗa mashi a hankali-hankali. Bai jira amsarta ba ya yi saurin ficewa. Kai tsaye ya koma benensu da sauri, dan yadda ya ji muryan Lion tamkar akwai matsala.
Yana saƙo kafarta cikin main parlonsu sai ga Leo tare da hero sun fito, Leo yana shirye cikin shigar ƙananan kaya, wandon ripped jeans baki, da polo shirt fari, ya ɗaura winter jacket a sama, ya yi masifar kyau, still dai yana sanye da nose mask a face ɗinsa, kafafunsa cikin socks kuma cikin boot kalar rigarsa, sai tashin kamshi yake yi.
Yana ganin Champion ya ce. "Bro dama wajenku zan je, jibi zan koma, zan je shopping yanzu"..... Guru dake kallon heronsu ne ya amsa da. "Take my ATM card". Ya faɗa yana ciro card ɗin daga aljihunsa ya miƙa mashi. Karɓa ya yi tare da sa kai zai wuce, da sauri zakin ya bi bayansa. Champion ne ya yi wa zakin magana da wani yare, ya ce. "Hero zo mu tafi ka bar Leo ya fita".
Kun san me? Iya wuya basa taɓa yarda su fita da zakin nan waje, kullum yana cikin gida, ɓoyesa ma suke yi saboda wani dalili nasu na kansu, akwai masu kiwon zaki sosai, ko gidansu Noor akwai damisar da suke kiwo, kuma idan zasu fita shan iska a cikin CP suna fita da shi lafiya lou, amma zakin IRON FIST baya leƙa ko kusa da elevator bare fita, kuma wannan zakin tin Leo yana jariri yake tare da su. Mutumin da ya reni Lion kamar shi ya basu zakin, kun san sun girma ne a hannun wani tsohon soja, bari zasu baku tarihinsu da kansu, zaku ji daga ina suka samo karfin zuciya da jajircewa kan duniyar nan, daga wanda ya rikesu har suka girma ne!.
Da gudu hero ya bi Aryan suka wuce ciki. Kai tsaye room na aikinsu ya shiga, dan yasan a nan zai isko su Lion. Kamar kuwa ya sani, zaune ya iskosu gaban computer suna ta aiki. A gaban nasa computer ya je ya zauna tare da miƙa hannu ya taɓa mouse ɗinta. Take ta kawo haske, nan ya ga tarin bayanai da Lion ya tura mashi kan WORLD SYSTEM.
Bayanai ne kamar haka, a natse ya fara karantasu a cikin ransa ni kuma na rubuta maku a zahiri.
Shirye-shirye WORLD SYSTEM ga duniya a cikin waɗan nan shekaru mafi kusa dake zuwa, babban shirinsu na farko shi ne cure duniya ta zama abu guda ɗaya, su fitar da shugaban ƙasa guda ɗaya addini ma guda ɗaya, hakan ba zai faru ba sai sun shafe dikkan addinai na duniya, sannan hakan ba zai faru ba sai sun rage population na al'ummar duniya, dan haka dole su kirkiro ta'addanci, cututtuka, ambaliyan ruwa, girgiza ƙasa, canzawar yanayin sararin samaniya dan a samu yawaitar faɗuwar jirage sama. Babban aikin da suka ɗauko dan rage yawan al'umma a yanzu ya haɗa da, digital identity harvesting, satar bayanan nutane a yau, da yawancin na'urori da apps ana tattara bayananka a ɓoye kama daga kan DNA, yatsanka, kalmomin da kake faɗi, inda kake tafiya, ana amfani da shi wajen gina maka digital clone dan su iya yi maka amfani nan gaba ba tare da izinin ka ba, bafa amfanin kirki zai maka ba, a'a za'a juya kwakwalwarce a lokacin da zasu fito da addini guda ɗaya wa duniya, ba zaka iya yi masu gardama ba, dan sun sace komai naka an juya maka ƙwaƙwalwa.
Shirinsu na biyu shi ne, mind control & neuro weaponry, fasahar sarrafa hankalin mutane, a baya ba na ce za'a sace bayananku ba? Idan aka gama sacewa sai a fara project kan yadda za'a fara sarrafa hankulan mutane, za'a fara sarrafa mutum daga nesa ta hanyar microwave, EMF, ko chip a kwakwalwa, sauya maku tunani, saka tsoro ko ƙiyayya cikin mutane dan ɗora su akan tafarki ba daidai ba, ku yi ta tsanar juna kuna kashe juna, kuma ko ya za'ayi maku bayani ba zaku fahimci kowa ba, dan abin da aka cusawa kwakwalwarku kenan ku tsani ƴan uwanku, ku ta kisa babu gaira babu dalili, ba zaku taɓa sanin cewa ana amfani da ƙwaƙwalwarku ake cusa maku tsanar juna da son kashe mutane ba, ku dai gaku nan ne kawai zaku ta kisa, kuna sace ƴan uwanku, babu tausayi babu imani!.
Project ɗinsu na uku shi ne, kashe hanyar abinci, bayar da abinci da ruwa da magani marasa kyau a ɓoye, nan gaba kaɗan aiki zai yanke, makarantu babu, asibiti ba za'a ɗauki ma'aikata ba, babu aikin yi dai a taƙaice, hakan zai sa al'umma su koma kan harkar noma da kiwo, dole su koma sana'ar hannu, shiyasa WORLD SYSTEM ta fara kashe ɓangaren sana'ar hannun ba tare da kowa ya sani ba, zasu baku iri mai gurɓata ƙasar noma da muhalli su ce ya fi kyau ku shuka, da zarar kun fara shukasa shikenan ya kashe naku irin, ko kun shuka naku ba zai fito ba, a lokacin da zasu fito da addininsu guda ɗaya wa duniya zasu ce ku yi imani da shi ko su hanaku abincin nomawa, dama irin da kuke shukawa nasu waye ne? Ko ku yi masu biyayya ko yunwa ta kasheku! Baku da mafita, kuma ga shi su nasu irin bashi da ƴaƴa bare idan kun shuka ku sake shukawa, sau ɗaya zaku shuka, idan zaku sake wani sai dai ku saya daga wajensu. In banda munafurci me na kashe ƴaƴan irin nasu idan ba wani munafurci suka shirya maku ba?.
Makiyaya ma ba'a barku a baya ba, yanzu haka WOLRD SYSTEM tana ƙoƙarin kirkirar namar da za'a dinga haɗawa da technology pmh, zasu ce maku wannan nama yafi, zasu yaudareku ku karɓesa, zasu yi maku saukinsa, ku kuma zaku so banza, daga nan ku zubar da batun kiwata naku dabbobin, zasu rabaku da dabobinku ta hanyar kashe wasu, su ƙone wasu, su sace wasu, daga karshe su hanaku namansu da suke sayar maku a sauki da aka kirkiresa da technology ne ba namar da ALLAH ya bamu ba, dole idan kuna son nama ku yi biyayya a garesu. Wannan abu bata shafi musulmi ko kirista ba, mai kuɗi ko talaka, zaku sha mamaki a lokacin da masu kuɗin da kansu zasu fara nadamar bautawa waɗan can tsinannun, dan kwantan ɓauna suke yi masu a yanzu, babu wanda zai iya gane hakan.
To abu na gaba shi ne, geoengineering, gine-ginen masana'antu dake kwanto ɓaraka wa duniya bakiɗaya, zasu yi gwanjo na jirage da ke fitar da hayaki, zasu kirkirosu ne su sayar da su a arha, jiragen su yawaita, a daina hawa motoci sosai, amma abin da baku sani ba shi ne waɗan nan jirage da zarar sun tashi sama canza yanayin sama suke yi, suna bada chemtrails a sama dan canza yanayi, wannan yanayi shi zai ƙirƙiro fari, ambaliya, da kuma girgizar ƙasa masu girma a jere a jere, wannan fasaha ce ta cikin geo weaponry, ta haka ruwa zai ɗauke a yankuna, koguna su ƙafe, rashin ruwa rashin abinci, dik abin da kuke zato ya wuce nan........ My people a koda yaushe, ko bana raye idan kun tina da Princess Teema or Star Lady ku mun addu'a, sannan ina rokon da ku tayani addu'ar samun damar kammala rubuta wannan littafi.
Aryan na kammala karanta wannan bayanai Lion ya sake turo mashi wasu kamar haka. A dik cikin ƙasashen dake duniya AVARIS ce kasar da ta fi cancanta a garesu su fara aiwatar da wannan project ɗin, kasar tana da dik abin da suke buƙata, shiyasa suka sanyawa ƙasar ido, fitinar yau daban ta gobe daban, kuma abin mamakin shi ne manya masu gudanar da wannan tsari cikin barisa da hangen nesan mafiya yawa daga cikinsu ƴan Avaris ɗin ne, saboda ƙasa ce dake da tarin ƴan baiwa, suke basu tsari da abin da ya dace. Yanzu dole mu fara aiki a kan Avaris kafin mu cinwa WORLD SYSTEM.
Ɗago kai Aryan ya yi bayan ya kammala karanta wannan jawabi, sai ya ce. "Bro i saw one message this morning cewa an samu sabbin ƴan ta'adda da suka fito a kasar Avaris two days ago, ƴan ta'adda ne masu haɗarin da suka fi waɗan da suke cikin ƙasar a yanzu". Ya yi magana dikkansu shi da guru kallonsu a kan Lion suna jiran jin me zai ce, ni kaina ina jiran jin me Lion zai ce, dan nasan zancensa gaskiya ce zai faɗa, fasa kwai zai yi.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP
STEP 1🔥
2025-11-21.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________20 & 21
Lion bai yi magana ba for almost 5 mins, sannan yai masu dropping messages na bayanai a computers ɗinsu. Sun san bayayin dogon magana, dikkansu basa tsawaita magana, amma na Lion and guru is worst, magana ta minti ɗaya ba zasu iya yin bayani ba, sun gwammaci zaman typing su tura ba magana ba, shi Champion idan ta kama yana daurewa ya yi magana har na mintuna biyu.
Already sun saba dama dik abin da suka tambaya a rubuce yake turo masu amsa, suma a rubuce suke tura tambaya, sai basu wani damu ba, a natse suka buɗe message ɗin kamar haka.
"Kun taɓa ganin yadda ƴan ta'adda suke fitowa dan kansu kawai ne? Ƴan ta'adda! Wasu jama'a ce da ake kirkirarsu musamman dan a fitinawa al'umma, kun taɓa tambayar kanku ina iyaye da ƴan uwan waɗan nan ƴan ta'adda? Kun taɓa tambayar kanku meyasa ƴan ta'adda suke da horo kan sanin makamai tamkar yadda sojoji suka sani? Za'ayi musayan wuta da ƴan ta'adda da sojoji, idan bullet ɗinsu ya kare a ƙasa da minti ɗaya suke sake sanya bullets a bindigunsu tamkar yadda aka horar da sojoji sanya bullets a bindingu cikin gaggawa, kun taɓa tambayar kanku ya aka yi suka iya dikka wannan? Ko dai a kullum kuna rigingimu tsakaninku da ƴan uwan da kuke tare da su cewa sune ke kasheku?".
Wani dogon note ya sake tura masu kamar haka a kasan wannan. "Terrorists! Kalma ce wacce aka kirkira, ƴar ta'addan dake Avaris waɗan da ake ta ikirarin sun addabi al'umma dikkansu kauyawa ne, dakikai ne da basu taɓa shiga class ba, ya aka yi suka iya karatun sanin makamai karatun da ya fi kowanne wahala? Sanin ita kanta bindiga ba karamin wahala bace, ya aka yi suka san dikka wannan? Ya aka yi suke da bindigun da suka fi na sojijin Avaris karfi da sabonta? Ta ina suke samo makamai masu karfi da kayan aiki tamkar jami'ai? Sun fi wasu jami'an ma kayan aiki in gantattu! Why?"
Amsa, a bayan kowani ɗan ta'adda ko ɓarawon daji akwai manyan dake bashi umarni kuma dake koya mashi aikin ta'addanci, ƙalilan ne daga cikin ƴan ta'addan suka fito daga kasar Avaris ɗin, kalilan ɗin kuma jahilan ciki aka kwasa game da yi masu karya da sunan jahadi suke yi wa musulunci, da rashin iliminsu aka yi amfani wajen sanyasu aikata abin da suke yi! Amma ainahin ƴan ta'addan idanu baya ganinsu, mutane ne da aka kirkiresu, tsawon shekaru aka horasu, mutane ne da basu da wani dangi bare su san daɗi dangi har su ji tausayi, basu da iyaye, su kawai an kirkiresu ne saboda taaddaci da kashewa, shiyasa ba zasu ji tausayin kowa ba, ba zaku taɓa gane kan wannan rigima a yanzu ba, sai bincike ya natsa damu cikin WORLD SYSTEM komai ya yi nisa zaku gane mecece ainahin ta'addanci, su waye ainahin ƴan ta'addan da ake dangatawa da musulmai alhalin basu ma da addini kwata-kwata, dik wanda yake matsayin member na wannan taaddancin bashi da addini wlh! Ko kiristoci na kwarai basa kisa haka ɗai, saboda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 95