Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba dan haka ba shi ba zai zo wannan masarauta ba, ba zai sake zuwa kusa da mace ba, amma daddynsa ya ce ya ɗauki granny a matsayin shi ne, idan ya saɓa mata tamkar shi ya saɓawa. Amma fa dik da wanna wasiya baya wani bi, yanzu haka sai da tai mashi kira ya fi sau goma, yaki ɗagawa ma bare ya ji menene, sai da ta sanya aka rubuta mashi saƙon tana gadon jinya, sannan ne ya yi reply da yana zuwa, tin last month aka yi hakan sai yau yaga damar zuwa ɗan duniya. Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta ce. "Edward Harrison ba zaka mun magana bane yau ma?"..... Da kyar maganarta yake fita. Edward Harrison shi ne sunansa da suna sanya mashi, Harrison sunan babansa ne, basu san ya koma Muhammad ba. Lion da iskanci yake, akwai wata shekara da ya taɓa zuwa, tin da ya zo har ya ɗauki awa ɗaya a zaune ya koma bai yi wa kowa magana ba har dattijuwan, kuma tin daga wannan zuwa bai sake ba sai yau, shi ne take tambayar ko yau ma ba zata samu damar yai mata magana bane. Shiru babu alamar zai amsa mata, ganin haka yasa ta sake cewa. "Edward ina ganin kamar lokacin ɗaukakata izuwa sama ya yi, shi ne yasa na ce a kira mun kai". Ta dakata saboda yanayin jikin bata iya magana mai tsawo. Babu alamar Lion zai tanka mata bawan ALLAHN nan, ko motsi bai yi ba. "Idan ruhunana ya ɗaukaka zuwa sama Edward kai nike son ka zo ka ƙona gangar jikina, ka sheke tokata mai daraja". Ta sake yin shiru cike da sa ran zata ji muryansa, amma ina bai motsa ba. "Edward iyayenka Harrison da Robertson kawai dudu (ranan da suke bautawa suke kira da dudu) ya bani, yanzu kuma kai kaɗai suka bar mun, Edward ka yi magana mana in ji daɗi, ina jin kamar Harrison ne yake magana idan ka yi, ka bani kalamanka na karshe". "Zan tafi". Shi ne kawai abin da ya furta tare da miƙewa tsaye...... "Edward please ka fuskanci kakanka ku sasanta, ka mashi abin da.....". Kasa karisawa ta yi saboda ɗago idanun da ya yi a kanta, kara ɗaure fuska tamau ya yi, bai sake yin magana ba ya juya ya fita abinsa. Bai sake bi ta kan kowa ba, ya wuce ya shiga mota dan komawa, Iron Sovereign yana ta faman leƙansa ta view, yana gani Lion ya koma sannu bata haɗasu ba. Ko yaushe wannan gaba zata zo karshe kuma? Kowa sai ji da girman kai da zafin rai game da taurin zuciya. Wannan kenan a ɓangaren Lion, to mu leƙa ɓangarensu Seraphina. Har cikin gida Rimsha da Faryan suka ni Seraphina, sai murna take yi, ta kaisu wajen Madam suka gaisa, Faryan ya zauna a parlo yana ta bin Seraphina da ido, dik in ta gifta sai ya ganta, while ita kuwa sun shige ɗaki da Rimsha, sai kai komo take yi tana ɗaukiwa Rimsha kayan cima. Yau wunin farinciki suka karisa, sai ana kiran mangrib Faryan ya ce Rimsha ta zo su wuce gida, tamkar zata yi kuka ta ce. "Uncle yaushe zamu sake zuwa?". Shi ma da yake ya ga abin da zuciya ke so sai ya ce. "Ai bamu da nisa, dan haka zan dinga kawoki". Haba take ta fara murna. Dik abin da suke yi Aryan yana zaune gaban computer yana kallonsu, dik kalle mashi baby Cherry Bloom da Faryan yake yana ganinsa, kishi ya gama tsumasa, jikinsa har wani tsuma yi, ga shi ba wani dressing na suturta jiki sosai take yi ba, ya dinga kiran wayarta dan ya faɗa mata ta sanya wasu kayan, amma tana can an samu Rimsha wayar ma bata san in da yake ba. Bai tashi shiga damuwa ba sai da ya ji Rimsha ta ce da Seraphina su je cikin toilet su yi wanka, a boarding school haka suke yi, tare suke wanka. Wannan abin ya yi matuƙar tayar mashi da hankali, jikinsa har wani tsuma yake yi, haka yana ji yana gani suka shiga toilet, babban abin da ya kara kiɗima shi ma yadda suka cire kaya a tsakar ɗakin, kuma ko kunyar juna basu ba, tambayar kansa ya fara yi menene amfanin boarding school ne ma a rayuwar ɗiya mace? Amsar da ya rasa kenan, amsar da ni kaina na rasa kenan, a zamanin yanzun nan menene amfanin boarding ga ɗiya mace, yadda zamani ta lalace, hmmm!. Kifa kansa a jikin table ya yi yana sauraran hirarsu har suka shiga toilet, basu aikata komai ba, wanka kawai suka yi suka fito, dik hirarsu yana ji, har suka gama suka shirya, Rimsha tasa abayar da suka sayo a shopping, Seraphina ma ta sanya abayar da ta ɗauka cikin sayayyar Rimsha. Daga nan suka dawo parlo suka hau hira da Faryan, suka bar wayoyinsu a ɗaki. Ai Aryan yana ganin su Rimsha sun tafi ya miƙe ya yi wanka, ya ɗauro alwala suka wuce masallaci, bayan sun yi sallar magrib da ishai suka fito shi sai ya wuce wajenta, guru na tsokanarsa bai tanka ba, saboda burinsa kawai ya je wajenta ya faɗa mata kada ta sake yin wanka da kowa. Zuciyarsa ta kara ninka tsanar Rimsha sosai, saboda ita ta ce su yi wanka a tare, sai ya ji yarinyar gabaɗaya ta fita ransa over. Bai san ba laifinta bane, ko bata ce ba Seraphina zata ce, saboda wannan ɗabiar ƴan boarding ne cire kaya gaban juna da wanka a tare, basu ɗaukesa a wani abu ba. A bakin door ya tsaya yana kallon yadda ta yi balain kyau cikin abayar, tana rike da waya suna chat da Rimsha, tana faɗa mata uncle Faryan sai yabon kyanta yake yi, sai zuba murmushi take yi an yaba kyanta. Unexpected ta ji ya kwace wayar. Da sauri ta ɗago kai, tana ganin shi ne ta saki ƙayataccen murmushi game da cewa. "Daddy shi ne ɗazun ka gudu ka barni ko?".......... A gefenta ya zauna tare da zuba mata ido bai ce komai ba. Gyarawa ta yi ta kwanto da kanta a saman laps ɗinta, ta juyo tana kallon kyakkyawan face ɗinsa da ya yi masifar yi mata kyau yau, yana ɗan ciza lips ɗinsa yana kallonta. "Daddy ka yi kyau sosai yau". Ta faɗa tana riko hannunsa. Nisawa ya ɗan yi tare da cewa. Likes comments and share fisabilillah. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1🔥 2025-12-8.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 42 & 43 "Daddy ka yi kyau sosai yau". Ta faɗa tana riko hannunsa. Nisawa ya ɗan yi tare da cewa..... "Dik kyan daddy bai kai rabin baby Cherry Bloom ba, kin fini kyau ai"........ Juyawa tai, ta kifa a saman mattress ɗin tare da kwantar da kanta da kyau a kan laps ɗinsa, tana ɗan wuwwurga kafafunta ta ce. "Daddy da gaske na fika kyau?". Shiru ya ɗan yi for almost 2 mins kafin ya ce. "Seraphina tashi mu yi magana". On a serious note yai maganar, hakan yasa ta miƙe zaune tana ɗan turo baki. Ɗan lumshe idanu ya yi saboda dafa laps ɗinsa da ta yi ta miƙe, zama ta yi suna fuskantar juna, ta natsu tsit. Hannunta ya kama cikin nasa, a natse ya fara gwada mata haramcin shiga toilet mutane biyu, ya ce haramun ne ma kallon tsiraicin juna. Ya so ce mata ma'aurata kawai aka halattawa ganin tsiraicin juna, amma sai ya fasa saboda shirmen da tai mashi ranar, kada tasa yau ma yai suɓutar baki, maganin kada ayi kada a fara, da yanzu yasan karamin aikinta ne ta jefa mashi tambayar da zai hana shi barci. Da yake tana son shi sosai, sai ta ce. "Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, dama a school ne muke yi tare har da su sister Aana idan muka yi lattin zuwa class, amma ba zan sake ba"...... Ajiyar zuciya ya sauke tare da sake hannayen nata kafin ya ce. "To kada ku sake". Faɗowa jikinsa ta yi tare da cewa. "Daddy baka zo kun gaisa da Rimsha bafa, ta zo har gidan nan"........ Ɗan ɗauke wuta ya yi na ɗan sekonnin jinta a jikinsa kafin ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, tsintar kansa yai a wani irin yanayi, ɗan gyaran murya ya yi kafin ya ce. "Cherry ba kin ce kina son daddy ya aureki ba?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e......... "To tashi in faɗa maki wani abin". Da sauri ta raba jikinta da nasa, tana kallon kyakkyawan fuskansa........ "Cherry, idan har kina son daddy ya aureki to ki daina hawa jikina". Cike da mamaki ta ce. "But daddy why? Are you not my daddy?"........ Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi, on a serious note ya ce. "Idan kina hawa jikina yanzu to aure zai haramta ne a tsakaninmu, ki bari sai mun yi auren tukun nan, ko oyoyo daga yau na hana, and in kina son in aureki ki dinga sanya ɗan kwali, ki kuma koyi sirri, kada ki sake faɗawa Rimsha abin dake tsakaninmu, dan babu kyau ki dinga faɗawa wata wani abu a kan mijinki". Ya so ce mata idan tana kwanciya a jikinsa tana jefasa cikin wani yanayi, amma ya yi saurin kama bakinsa gudun ta jefesa da wata tambayar da ba zai iya amsawa ba, dan Seraphina kam hankalin da sauƙi. Hannu ta sanya ta toshe baki, tana ɗan murmushi ta ce. "Daddy waye ya faɗa maka ina faɗawa Rimsha maganarka?"......... Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa ya watsa mata kafin ya ce. "Kina faɗa mata ko baki faɗa?"..... Ɗan turo baki ta yi. "Ai kaɗan nike faɗa mata ba dayawa ba"....... "Awwe ashe dai kina faɗar"....... Murmshi ta ɗan yi ta sanya tafukanta ta rufe fuska. Wani irin kallon kauna ya wurga mata da waɗan nan dara-daran eyes ɗin nasa. "Dubeta a wajen". Ya faɗa yana ɗan ciza harshe......... "Kai daddy kai daddy ka bari mana". Ta faɗa tana kai mashi dukar wasa a kirji. Wani irin yanayi mai mugun daɗi ya tsinci kansa a ciki, sai kuma ya miƙe ya koma saman sofa, ya zauna yana cigaba da kallonta, ALLAH ne kaɗai yasan irin son da yakewa babyn Cherry ɗin nan nasa, kome take yi kyau take ƙara mashi, yarinyar ga shiga rai. Haka suka kasance, har around 10 na dare, yai mata sallama ya fito, tamkar zata yi kuka, bata son rabuwa da shi, to amma ya zata yi? Dole ta hakura. Yana fita ta kira Rimsha, Rimsha na ɗagawa ta ce. "My Nisha kin san me?". Rimsha dake kwance a room na Faryan ta tada kai da laps ɗinsa suna kallo a laptop ɗinsa ce ta amsa da. "Ina zan sani tin da baki faɗa mun ba, meyafaru?". Cike da farincini ta ce. "Daddy ya ce idan ina son ya aureni wai in daina faɗa maki tsakanina da shi, kuma wai in daina hugging ɗinsa, mu daina wanka tare". Sai murmushi take yi ta faɗa, tamkar ba yanzu ya gama ce mata kada ta sake faɗa ba........ Miƙewa zaune Rimsha ta yi tare da cewa. "To amma waye ya faɗa mashi kina faɗa mun?"........ "Ni ma ban sani ba, kawai ya ce in daina faɗa maki ne"........ Dariya Rimsha ta yi tare da cewa. "Daddyn nan naki daga gani rigimamme ne, to ba zaki daina faɗa mun ɗin ba, mu ba aminai bane? Mun zama one blood ma yanzu". Tana murmushi ita ma ta ce. "Ai na ce mashi to ba zan sake faɗa maki ba, amma ba zan daina ba, kuma ba zai san na faɗa maki ba, yanzu ki bani shawarar yadda zan sa ya so ni sosai kin ji?"...... Satar kallon Faryan dake kallonsa ta yi kafin ta ce. "Ina room ɗin uncle Faryan, ki bari anjuma idan na koma ɗaki"........ Hararar wasa Faryan ya dallah mata kafin ya ce. "Me kuke ɓoyewa?"....... Da sauri ta ce. "Uncle wannan da muka je gidansu ɗazun ɗin ne fa! Star ladyta! Ka tina?". Da sauri ya ce. "Yauwa bani ita mu gaisa". Bata kawo komai a ranta ba ta miƙa mashi wayar, karɓa ya yi suka gaisa, bayan sun gaisa ya dinga yabon kyanta, sai murmushi take yi, daga bisani ya ce. Bai so daina kallonta ba, dole ce kawai tasa, amma please ta turo mashi pics ɗinta dayawa bari ya dinga gani. Cike da murna ta ce mashi to zata turowa Rimsha ta turo mashi, daga haka suka yi sallama, ya katse kiran tare da dawo da kallonsa a kan Rimsha da ta tsaresa da ido. "Kai Nisha wannan kawar taki akwai kyau, kina ga eyes ɗinta, i wish in sameta matsayin mata, kai Nisha ina ganin ina sonta fa". Hannu bibbiyu Rimsha tasa ta toshe baki tana murmushi kafin ta ce. "Uncle yau da kanka kake son mace?". Gerarsa irin na Aryan ɗin nan ya ɗaga mata, cikin salon son Seraphina dake ratsa zuciyansa ya ce. "Wlh wani irin sonta ne ya shigeni tin da na fara kallonta, please Nisha help your uncle kin ji? Kinga kawarki ce, zaki iya koya mata sona". Aikuwa cike da farinciki ta ce. "Uncle ko dan yadda ka kasance kai ɗaya ne mai sanyani farinciki a gidan nan dole in tayata samo zuciyar Seraphina, nima ina kaunarta sosai, zan so ta shigo zuriarmu kuma gidanka, ba zata yi wahalar samu ba, tana sona, tana da saukin kai, zata so dik abin da nike so, and zan baka numberta, kai ma ka dinga kiranta"....... Ya ji daɗin wannan kalamai, bai san time ɗin da ya bawa cheek ɗinta haɗaɗɗen sumbata ba, cike da farinciki ya ce. "In dai kika tayani shawo kanta nai maki alkawarin sabuwar waya da sabowar mota and laptop". Wani irin tsalle ta daka ta rumgumesa tana murna, shi ma rungumeta ya yi yana murmushi. A yayin da haka yake faruwa, shi kuma Aryan yana master room na Abba suna magana da Abba a kan Rimsha, bai samu damar sauraren voice na wayar da su Rimsha suka yi yanzu ba. Yana zaune a gefen gadon Abba, while Abba yana kwance saman bed. Dik abin dake faruwa Aryan ya zayyanewa Abba game da Rimsha, abin da ya gani da idanunsa na abin da aka koya masu a school. Daga karshe ya ce. "Abba aurar da ita zan yi, zan haɗata aure da Vash in the next 2 months masu zuwa!". Babu wasa a kan fuskansa. Miƙewa zaune Abba ya yi, hakika ya kiɗima da jin zancen nan, sai da ya fara maimaita hasbiyallahu wani'imal wakil kafa goma sannan ya ce. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, a zamanin nan na yanzu kawai ALLAH ne zai iya kare maka zuri'a, wannan wace iriyar musifa ce?". Shiru suka ɗan yi, can kuma Abba ya ce. "Aurar da ita ai ya zama dole ne, wannan musifa dole ai, sai ka shirya biyawa Vash ɗin sadaki, wata biyu ma ta yi nisa, gara a aura mashi ita nan da sati guda, dama zai zo ya yi kwana biyu kafin su tafi next mission kaga komai zai tafi daidai".......... "Haka ne Abba, amma a bari nan da two months ɗin". Aryan ya faɗa, so yake a ranar da za'a ɗaura auren a haɗa da nasa shi da Cherrynsa, shiyasa yake son nan da 2 months. Da farko Abba ya so ja, amma daga baya ya hakura ya bar batun, nan da wata biyu za'a yi bikin. Sosai Abba ya shiga damuwa, a daren ranar wlh bai rintsa ba, Aryan na fita Abban yasa aka kira mashi Rimsha, tana shigowa zata hau jikinsa ya ce ta zauna a ƙasa magana zasu yi, ai tana ganin yanayin fuskansa ta natsu tsit. A ƙasa ta zauna, ta sha jinin jikinta, fuskansa babu alamar wasa ya ce. "Tambaya zan yi maki, ki faɗa mun tsakaninki da ALLAH"...... Cike da mamaki ta ɗago ta kallesa, bai taɓa yi mata magana irin haka ba, amma sai ta ce to zata bashi amsa tsakaninta da ALLAH. Kai ya jinjina game da cewa. "Kin taɓa kwanciya da wani ɗa namiji ko kin taɓa da wata ɗiya mace?"...... A zabure ta zazzaro idanu a kansa, ganin ya kara murtuƙe fuska ne yasa ta yi ƙasa da kai game da cewa. "A'a Abba, ban taɓa wlh"..... "Ki mun bayani da kyau!". Ya faɗa in a harsh way, dan yana da mugun zafi, yanzu ne ma da tsufa tasa ya ɗan yi sanyi, amma da! Tab!......... Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Wlh Abba ban taɓa aikata ko ɗaya daga ciki ba, amma roommate ɗinmu suna yi, classmates ɗinmu ma suna yi, ni da Seraphina ne bamu taɓa yi ba". Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Meyasa kuke wanka a tare a toilet ku dayawa matsayinku na matasan ƴan mata?"........ Jikinta ne ya soma rawa, cikin sanyin murya ta ce. "Abba wani lokaci ne idan mun yi lattin zuwa class muke wanka tare dan mu yi sauri, amma bayan haka ALLAH babu wani abin"...... Daga kalamanta yasan iya gaskiyarta take faɗe, dan haka sai ya ce ta tashi ta tafi ba tare da ya faɗa mata hukuncin da uncle ɗinta ya yanke kan aurar da ita ba...... Da sauri ta miƙe ta fito, a ransa ya ce yakamata ya fahimtar da Aryan cewa Rimsha bata taɓa aikatawa ba, dan ya kara tsanarta sosai, a bayanan da ya yi wa Abba ma ya yi kamar ya yarda ta taɓa aikatawa. Abin da yasa Aryan ya ce ta taɓa aikatawa kuma shi ne, ya fahimci bayanin Seraphina a baibai, da ta ce mashi sister Aana ta ce ita kirjinta basu girma ba, ba zasu yi komai da ita ba, kirjin Rimsha ya fi nata girma, to shi ne yake tinanin kenan tin da na Rimsha yafi nata girma suna aikatawa da ita kenan ai, bai san ba haka bane, bai fahimta bane, shi ne har da ƙara tsananta zai aurar da ita. Kwana tinane-tinane Abba ya yi, ya yi nadamar turata boarding school tana ɗiya mace, a zamanin yanzu da komai ya lalacen nan, gaskiya ya yi babban kuskure. Wannan damuwa ta hanasa rintsawa, washegari da sassafe ya haɗa kan Faryan da Harleen ya ce su rakasa benen kusa da su aje batun nemowa Aryan da Harleen auren Aunty Lusi da Aunty Luna, dan fa bai manta da zancen ba. Faryan ɗan auta kam ba ta shi ake yi ba, shi ance da sauran shi, basu san shi yana can yana ƙoƙarin sace zuciyar Baby Cherry bloom ɗin Aryan ba, ya samu numberta wajen Rimsha, jiya sun kwana chatting while Aryan sun kwana aikin IRON FIST, bai bi ta kan wayar Seraphina ba bare yasan abin da suke tattaunawa, ita kuwa tana nan Faryan ya tsarata son ransa, ya zuba mata kalaman da ta dinga murmushi har ta yi barci fuska ɗauke da murmushi. ....... Hmmmm ga shi da Aryan da Faryan sun fi shaƙuwa da juna, Aryan ya fi kaunar Faryan fiye da Harleen, akwai case kenan. Faryan sai dariya yake yi yana murna za'ayi wa Harleen auren dole, baya murnar za'ayi wa Aryan auren dole, amma yana murnar na Harleen, dan dama yana son a kuntatawa Harleen ko dan kuntatawa Rimsha da yake yi. Shiga ta mutunci suka yi, Abba thobe and bisht ya sanya, ya naɗa rawani, while Harleen and Faryan tail coat suka sanya. Kai tsaye suka nufi benensu Noor, sai haɗe rai Harleen yake yi. Ko da suka je daddyn Noor baya nan, amma sun samu uncle da su Aunty Luna, kuma sun karɓesu hannu bibbiyu saboda kirkinsu, yadda suka mutuntasu yasa Abba ya ji ya ƙara kwaɗayin su haɗa zuri'a, musamman yadda Aunty Luna ta gwada masu kulawa, da kanta ta kawo masu ruwa da abin taɓawa, ta zauna tana ta kula da su, uncle ɗin Noor ma akwai kirki da son mutane. Ya zauna kusa da Abba sai jansu da hira yake yi, musamman ma da ya ji ai maƙotansu ne, sai ya saki jiki da su sosai, ya girmama Abba sosai, ba ƙaramin daɗi Abba ya ji ba, hakan yasa ya furta buƙatarsa ga uncle kai tsaye. Aikuwa cike da murna uncle ya ce ai wannan ba wani abu bane, dan suna addini daban-daban ba zai hana su auratayya ba matuƙar su Aunty Luna suna so, bari yayansa ya dawo zasu yi magana, zasu tattauna, kada Abba ya wani damu zai ji amsa mai daɗi. Sosai Abba ya ƙara girmana dattakunsu, ya yi matuƙar farinciki, ya masu godiya sannan ya ce idan ba damuwa Aunty Luna su gaisa da Harleen, fuska ɗauke da fara'a ta ce ba komai, ta miƙe ta fita zuwa balcony, kin bin bayanta Harleen ya yi har sai da Abba ya ce. "Ka je tana jiranka". Sannan ya miƙe yana haɗe rai ya fito balcony ɗin. Tana tsaye tana kallon cikin CP ya ƙariso wajen. Bai ce mata sannu ba sai da ita ta ce mashi. "Hy". Sannan ne ya amsa game da ce mata. "Well-done". Daga haka bai sake magana ba, har suka ɗauki 20 mins a wajen, sannan ya wuce ya dawo parlo, ga mamakinsa sai bai samu su Abba a wajen ba, sun koma gida. Siririn tsaki ya ja tare da bin bayansu, ita kuwa Aunty Luna ko a jikinta, sai ma son shi da ta ji ya shigeta, dan tana son namiji miskili, bata san wannan ba iya miskili bane, ɗan duniya ne. A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana barin gidan Abba ya koma wajen Lion. A lokacin Lion ya dawo daga Ring Of Power, yana tsaye a balcony sanye da pj's farare ƙal, ya saki kitson dake kansa wanda suka ƙasa mashi matuƙar kyau, hannunsa rike da cup of americano yana sha, ya zura hannu guda cikin aljihu, yana kallon yadda CRYSTAL PALACE ke a cikin dare, yana da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haske ta ko'ina tamkar rana, wani irin ni'imantaccen iska na kaɗawa a hankali-hankali wanda ke kaɗa kitson kansa suna motsawa, iskan gwanin daɗi. Wajen sky blue light ne, hakan ta ƙara fito da tsantsar kyan fuskansa, waɗan nan jade eyes ɗin nasa sun kara wani irin cool sun ciza, zaku ce barci yake ji, in baku manta ba shi da Leo idanunsa sun yi zubin sleeping eyes ai, to da yake yanzu yana cikin kwaciyar hankali sai idanun suka ƙara zama sak sleeping eyes sosai, pink lips ɗin nan nasa ya ciza kala matuƙa, yana ɗan ciza laɓɓan nasa a hankali alamar yana tinanin wani abin. Aryan ya ɗan jima yana kallon haɗuwar Lion, da dai ya ga bafa zai gaji da kallon kyan nan nasa ba sai ya kariso wajen, a kusa da shi ya tsaya, hannu yasa ya fara tattare kitson dake kan nasa, yana tarawa wajen guda kafin ya ce. "What a special day today! My man yana cikin farinciki"....... Aryan ya san idan Lion yana cikin farinciki ne yake sake kitson kansa a watse. Shiru babu alamar Lion zai yi magana. Ɗaure mashi gashin Aryan ya yi game da cewa. "Yakamata mu binciki meyasa ake cire mahaifar mata a asibitoci a hankalin yanzu? The case is getting out of hand, anywhere ka juya wannan magana ake yi, i think there is something behind all this". Kai Lion ya ɗan jinjina ba tare da ya yi magana ba, hannu Arya ya miƙa ya karɓi Americanon dake hannunsa, sipping ya ɗan yi tare da cirewa, ya nisa before ya ce. "A Avaris abin yafi worst! But why, meyasa dik wata musifa a wannan ƙasar tafi yawaita kuma mutanen cikinta suka fi shan wahala". Sai da

Chapter 52 of 95