Wasa-wasa dik in da suka san zasu sami Lion sai da suka duba, babu shi babu alamarsa, har karfe biyu na rana, damuwar rashin sanin in da yake ne yasa Aryan bai je wajen Seraphina ba.
Around 2:30 na rana Abba ya kira Aryan, ya ce dik abin da yake yi ya bari ya zo yanzu. Dole ya bar komai ya nufi gida. Ga mamakinsa yana shiga gida sai ya isko su Abba dikka a parlon Abba dake sama.
One by one ya fara kallon family, a kan Abba ya tsayar da kallonsa, Abban na hakimce saman gado, ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana rike da scepter ɗinsa, fuskansa a ɗaure tamau yau, babu alamar wasa. Da shigowar Aryan kowa ya ƙara natsuwa tsit, Rimsha na cikin mayafin amare, da alama da gaske Abba sai da ya ɗaura wannan aure.
Zaman Aryan ya yi a kan side sofa yana mai da kallonsa a kan Ammie wacce da ka ganta kasan tana cikin tsananin tashin hankali. Shiru ne ya ɗan biyo baya a parlon, can Abba ya katse shirun da cewa. "A yau ina tsananin farincikin wannan al'amari da ya faru, a yau na aurar da ƴaƴana biyu, ALLAH Alhamdulliha".
Shiru suka yi suna kallon Abba, a kan Harleen Abba ya tsayar da kallonsa. "Anjuma da daddare zamu je ɗauko matarka, idan ta zo sai in haɗaku in faɗi abin dake bakina"...... Ya ɗan nisa tare da tsayar da kallonsa a kan Aryan.
"A wannan rana irin ta yau, umarni nike baka ba shawara ba! Ga Rimsha nan amana, ita ɗin ba mata bace kawai a gareka, kanwace, ƴar uwace, jininka ce, ka riketa amana tamkar yadda mahaifinta ya rikeka, ya kula da kai, haka zaka riketa"..... Tashin hankali!! Me nike shirin ji? Kirjina sai da ya buga da karfi, nasan kuma naku ya buga da karfi, Aryan kuma, Rimsha matarsa? What?!.
Wani irin tamke fuska Aryan ya yi, zai yi magana Abba ya rigasa da cewa. "Ban gama magana ba! Ina farincikin sanar da kai yau na mallaka maka sister ɗinka, matarka, jininka, wannan aure da kai aka ɗaura shi ba da Vash ba, sadakinka ka biya da kanka!"...... Babbar magana! E lallai Abba ya cika ɗan duniya, watau sadakinsa da kansa ya biya.
Abba ya duba ya ga babu mai iyawa da Rimsha sai Aryan ne, saboda bata jin magana, Aryan ne zai gyara mata zama, shiyasa ya haɗa wannan aure. To amma Aryan ba Uncle ɗinta bane? Kai ni Queen Of Surprise kaina ya ƙulle fa.
Miƙewa tsaye Aryan ya yi, in a harsh waye ya ce. "Ni ka aurawa wannan abar? Lallai kuwa ka saya mata tikitin tafiya lahira ne!! Kuma wlh ba zan zauna da ita ba, a yanzu na sak.......". Tsawar da Abban ya daka mashi ne yasa ya dakatar da maganar. A fusace Abba ya miƙe tsaye, jikinsa har kerma yake yi, ya nuna Aryan da sandar hannunsa, babu wasa a tattare da shi, a fusace ya ce. "Wlh, wlh, wlh, dik ranar da ka saki Rimsha, ba zan taɓa yafe maka ba in bana raye, in kuma ina raye ka sani sai dai kan nemi wani uban ba dai ni Khaiza'an ba, aurenka da ita babu saki, kuma daga yanzu ka ɗauketa ku wuce gidan naka!!".
"Ba zan ɗauketa ba Abba! Lallai ba zan saketa ba kamar yadda ka faɗa, amma kuma ka sani ka jefa rayuwarta cikin ukuba da azaba ne, ba zan taɓa sonta ko in zauna da ita ba!".......... Ammie ce ta miƙe, jikinta na kerma ta ce. "Aryan please ka yi shiru, mahaifinka ne fa!".
A fusace ya kalleta, cikin zafin zuciya ya ce. "Ki mun shiru, ba dake nike magana ba, na tabbata da mahaifiyata ce take tsaye a nan ba zata ce in yi shiru ba, ba zata yi shiru tana gani a zalunceni ba, yau da Ummie tana nan babu wanda ya isa ya cutar da rayuwata, amma saboda bake kika haifemu ba shi ne kika zuba ido yai mana abin da yake so, meyasa baki sa anyi har da Faryan ba? Saboda shi ɗanki ne?".......... Shiru Ammie ta yi tana jin zafin kalamansa, amma ta daure saboda tasan yana cikin ɓacin rai ne, da zafi abin da Abba yai masu, sun san babu wanda Aryan ya tsana biyun Rimsha, amma Abba ya haɗa wannan aure, shi ma yasan bai nemi zaman lafiya ba ai.
Abba ne ya ce. "Ohk, ni ne na cuceka kenan? Ni Aryan kake faɗawa na cuceka?!". Cikin faɗa ya faɗa. Mimmiƙewa su Faryan suka yi, Rimsha dai tin lokacin da Abba ya ce da Aryan ga matarka Rimsha, tin daga wannan lokaci da ta ɗaga mayafi ta kwala ihu ɗaya bata sake motsawa, Abba ya jefata cikin balain da yasa numfashinta ɗaukewa ta sume.
A fusace Aryan ya ce. "Abba......". Ammie ce ta yi ƙoƙarin sake dakatar da shi, saboda tasan hali, kuma tasan kome zai ce Abba fa magana ɗaya yake, in dik duniya zasu haɗu babu wanda ya isa ya sanya shi canza magana, ko ana mutuwa, ko wannan magana zata zama silar jefa rayuwar wasu a haɗari to fa ya yi ta ne, babu canji! Dan haka tsayawa ja in ja babu wani abin da zai ƙara masu, gara ta daure ta danni Aryan ɗin kawai.
"When I'm talking to my father, I don't need anyone to interrupt me, just get out of this room now!". In a harsh way ya faɗa, ya faɗa kuma ba tare da ya kalli fuskar Ammie ba, dan dik da yana cikin fushi yana jin nauyin yi mata magana without respect, dan dik da mahaifiyansa Ummie bata gidan, Ammie ta yi iya kokarinta wajen kula da su.
Rass gabansu Harleen ya faɗi, tin da suke basu taɓa ganin irin wannan musifa ba, kai Abba baya son zaman lafiya ko kaɗan, in banda neman jafai irin na Abba, a wannan yanyi zaka ce umarni kake bashi bama ka lallaɓa shi ba tin da ka yi son ranka? Mutumin da in ya birkice kai kanka gudunsa kake yi, amma wai umarni yake bashi da ya kula da Rimsha.
Nuna Aryan da scepter ɗin hannunsa Abba ya yi, a fusace ya ce. "Sai dai ka nemi wani uban ba dai ni Khaiza'an ba muddin ka tsallaka wannan umarni nawa! Babu saki tsakaninka da Rimsha, kuma ka ɗauketa yanzu ku tafi!". In a harsh way shi ma ya faɗa. Babban magana!. Gidan Abba ya rikice fa.
Juyawa da sauri Aryan ya yi, tamkar zai kifa, kamar zai tashi sama ya fice, baya ganin gabansa, kansa na mashi tsananin ciwo, zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje, ga damuwar rashin sanin in da Lion ya tafi, ga wannan bakar labarin wai an aura mashi Rimsha, wai kuma shi ya biya sadaki, innallilahi, da yasan shi za'a aurawa ita wlh ba zai kawo sadakin ba, gaskiya Abba ɗan duniya ne, Harleen kuma an aura mashi Aunty Luna ɗinsa.
Baya ganin gabansa sam, bai san time da ya isa benensu Seraphina ba, yana shiga room ɗinta ya nufi bed. Tana zaune tsakiyar gado, tana rike da waya, hawaye ya gama wanke mata fuska, tana ta kiran mumbersa bata shiga, ta damu, ta yi kuka har ta gode ALLAH, burinta ya zo ya faɗa mata waye wanda ya ɗauki wayansa jiya.
Tana ganinsa ta miƙe, ta nufosa tana faɗin. "Daddy.....". Bata iya ƙarisa maganar ba ta dakata sakamakon ganinsa yana tangaɗi tamkar zai faɗi, ga shi ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi. Kallon kafafunsa ta yi, ko takalma bai sanya ba, tin daga nan ta goge hawayenta, dan tasan ba lafiya, cikin zafa ta matsa mashi hanya ganin yana ƙoƙarin bugeta tamkar bai ganta ba.
Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinta, ya yi kwanciyar ruff da ciki yana ƙara dafe kansa. Ai da gudu ta hawo gadon, ta zo ta ɗago kan nasa, ta ɗaura saman cinyarta, muryanta na rawa ta fara faɗin. "Daddy baka da lafiya ne? Meyake damunka?"......... Shiru bai iya tanka mata ba. Ƙara ƙanƙamesa ta yi, tana ɗan shafa gashin kansa, cikin taushin murya ta sake cewa. "Daddy ka yi magana please, baka da lafiya ne?".
Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauƙe, ya zura hannayensa ta bayanta ya yi tighting ɗinta, yana huci mai zafin gaske. Ganin haka yasa ta cigaba da shafa kansa izuwa bayansa, ta fara faɗa mashi kalamai masu daɗi tana son shawo kansa, ya kwanta shiru a jikin nata yana jin kamar zuciyansa na sauƙa a hankali-hankali, ya zo wajen masoyiya ba.
Watau Jama'a idan ina hango cakwakiyar dake gaba a littafin nan ba, Rimsha ta auri uncle Aryan! How? Ba uncle ɗinta bane? Tambayar dake ranku kenan, to kada ku damu, zan warware maku komai. Ya auren nan zata kasance, daddy na son Seraphina, while ita ma tana tsananin sonsa, Rimsha babbar aminiyarta ce, shin ya za'a kaya, daddy zai auri Seraphina a ranar birthday ɗinta, sun zama kishiyoyi da Rimsha, a gaskiya na tausayawa rayuwar Rimsha matuƙa. A yaushe zasu gane uncle ɗin Rimsha shi ne daddyn Seraphina? Ya zasu yi idan suka gane? Dama ba Ammie bace ta haifi Aryan? Wacece Ummie da Aryan ya kira matsayin uwa? Ina kuma take a halin yanzu? Uhm akwai rikici sosai, zamu ga yadda wasan zai kaya, ga dai Rimsha baiwar ALLAH a can ta suma, ALLAH sarki ai dole ki suma baiwar ALLAH, irin wannan tashin hankali, Aryan fa aka aura maki, tab, idan akwai abin da ya fi suma ma yi zaki yi!.
To mu leƙa DOL team mu dawo, dan cakwakiyar CRYSTAL PALACE yawa ce da ita, ga Lion ya tafi bamu san in da ya yi ba. Ku karanta littafin Queen Of Surprise taku ta amana babu cawakiya ai kun san ba zai yiwu ba! Yanzu cakwakiyar zata fara mutanen kirki!.
-------------------------🔥
DOL.
Tafiya suke tsakiyar dokar daji, babu tsoro bare shakka, sun kashe light na hannayensu ma, a cikin duhu suke tafiya....... Zaynish ne ya ce. "Ina da yaƙinin akwai abin da suke shigo da shi, lallai ba iya kaya bane kawai!".
Noor dake jiki dik a mace ne ya amsa da. "Sosaima, ko kaɗan ban yarda da bakin ruwan nan ba"......... Sarai Leo ya fahimci halin da Noor yake a ciki na tsananin feeling, dan ko magana da kyar yake yi, amma bai nuna mashi kamar ya gane ba.
Vash dake faman dannar waya suna tafiya ne ya amsa da. "Na fi zargin suna shigo da makamai". ....... A natse Leo ya ce. "A baya kafin su shahara ne suka shigo da makamai, yanzu ina da tabbacin sun wuce wannan level ɗin, akwai dai abin da suke yi wanda ya saɓawa doka".
Tsalle Noor ya yi, ya haye saman bayan Leo tare da langwaɓar da kansa, yana saƙalo wuyan Leo ɗin yana nishi kaɗan-kaɗan........ Duka Zaynish ya kai wa Noor ɗin a gadon baya yana faɗin. "Ka dai bi a hankali, kada watarana ta hanaka aiki"...….... Kukan shagwaɓa ya saka yana faɗin. "Bro ba ka gansa ba? Wai ina ruwanka dani ne?".
Shi dai Leo cigaba da tafiya ya yi bai tanka masu ba, watau Zaynish ma ya gane halin da Noor ke ciki. ....... "Akwai ruwana da kai mana, dole in saka maka ido kwana biyun nan, dan kada ka biye mace ka lalata mana aiki, yanzu ma jibeka fa? Ka biye mata ko jurar tafiya ba zaka iya yi ba sai an goyaka, dik gaɓɓanka jikinka sun mutu, ga kasala da nauyin wando"........🤯
Wasa-wasa Zaynish mafa ya iya tsiya, baya magana amma idan yana yi da Noor sai kun sha mamaki, sai ma ku zaci bashi bane yai, kuma sai ya yi magana ya fuske tamkar ba shi ya yi ba, bai taɓa murmushi ba bare dariya ko wacce iriyar magana zai faɗa. Vash dai baya tare da su a halin yanzu, yana can yana baiwa aljana hakuri.
A shagwaɓe Noor ya ce. "Ni ku kyaleni in ji da ɗaya mana, my Juliet want kill me with her sweet, na samu da kyar na shawo kaina, na danni kaina, na biyoku shi ne zaku takura mun?". Ya faɗa yana langwaɓar da kansa a gefen wuyan Leo.
"Ai zaka iya komawa ka ƙarisar da abin da ka fara, nasan ita ma tana can tana fama da abin da kake mana a nan, dan haka ka koma kawai, kuma dama ni banga amfaninka ba, ko tafiya da kafafunka baka da kuzarin yi, yanzu idan aka farmakemu fa?". Zaynish ya faɗa yana ƙara kai mashi dundu a gadon baya.
A dake Leo ya ce. "Zaysh ka yi na kuɗinka, in ka ƙara sai ka ci wahala a hannuna, babu ruwanka da my pleasure"....... Sumbata Noor ya mannawa Leo a wuya yana faɗin. "This is my brother, love you more heartbeat". Gyarasa da kyau a bayansa Leo ya yi yana faɗin. "Love you too baby".... Ƙara rukunkume Leo tightly ya yi yana ɗan sakin shirin murmushi.
Shiru Zaysh bai sake yin magana ba, sai dai ya kama kunnen Noor ya murɗa da ɗan karfi. Turo baki Noor ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shi kuwa Vash hankali ya yi nisa, ya shiga damuwa sosai ta yadda har zufa yake haɗawa, saboda aljana ta ce zata kashe Manassa a daren yau, ga shi sun barosu a sansani, ya ALLAH.
Hannu Noor ya miƙa ya taɓo Vash yana faɗin. "Vash lafiya?"...... A ɗan firgice ya ɗago, nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Akwai matsala bro"...... Dikkansu dawo da hankalinsu a kansa suka yi, cikin sanyin murya Noor ya ce. "Matsalar me?"......... Wayansa Vash ya miƙo mashi kan ya duba ya ga matsalar.
Karɓa ya yi, suna cigaba da tafiya farinwata tankar ta fito sosai yanzu, hakan yasa ta ƙara haskaka masu hanya sosai. Fara bin chat ɗin Noor ya yi, wani waje ya yi murmushi, wani waje ya haɗe rai, har dai ya iso kan in da take cewa daren yau zata kashe Manassa, ya duba reply da Vash yai mata, na zunzurutun magiya da ban hakuri, ya damu sosai.
Hakan ne ya ɓatawa Noor rai, sai ya ce gaskiya ba zai iya barin Vash a cikin damuwa ba, dan haka zai faɗa mashi gaskiya, miƙa mashi wayan ya yi yana faɗin. "Aljanar zata kashe kanta kenan?".
Cike da mamaki Vash ya ce. "Me kake nufi?"....... "Manassa da ita kake wannan chat ɗin ai, tin ranar na san da haka, na ɗauka zata cigaba da zolayarka irin na masoya ne kawai shiyasa na rufa mata asiri, ban zaci zata jefaka a damuwa ba, tin da haka ne bari in faɗa maka ita ce".
Ina Vash bai yarda ba, sai ya fara girgiza kai alamar kai ba ita bace, a dake Noor ya ce bari in tabbatar maka. Wayansa ya fitar, ya kira number V, bugu ɗaya ta ɗauka, dama ta koma ɗakinsu ta ɗauki wayar. Tana ɗauka ta shagwaɓe murya da cewa. "My Romeo, har yanzu baka dawo ba".
Ai wani sabon feeling ɗinta ya ji, a sanyaya ya ce. "Ina dawowa yanzu, ina son ki mun wani abin ne yanzu"..... Ƙara shagwaɓe murya ta yi wajen cewa. "Me kenan?"......... "Jeki ari wayar Manassa yanzu, kada ki faɗa mata me zaki yi da ita, ki karɓo ki zo cikin tantina ke kaɗai akwai abin da zaki mun da shi"..
Da okey ta amsa tare da miƙewa ta fita, jim kaɗan ta dawo game da cewa. "Ga wayar a hannuna"....... Hannu ya miƙa ya karɓi wayar Vash kafin ya sanya wayansa a H-free ta yadda Vash zai ji komai kafin ya kaluɓo number Vash ɗin. "Shi ga contact ki saka wannan number da zan kira maki yanzu". Da okey ta amsa. A natse ta shiga.
Number Vash ya fara kira mata ta fara shigarwa kenan sai ta ce. "Akwai number a wayar, gata ta fito da saving my flower"....... Ɗago idanu ya yi ya kalli Vash kafin ya ce. "Shiga Whatsapp ɗinta ki nemo mun member". ....... Da sauri ta shiga, sai ta ce. "Number ce a sama, da ita take chat yanzu".
"Okey to shiga kan number ki yi clicking voice, a cikin voice ɗin ki ce I am mrs Noor ya wadatar"....... A natse ta aiwatar da abin da ya ce, bata tambayesa me dalili ba, saboda tasan haka kawai ba zai tsaya wannan dogon magana ba.
"Na yi na tura". Ta faɗa.….... "Okey to goge voice ɗin yazama tamkar ma baki shiga kan chat ɗin ba". Da okey ta amsa kafin ya aiwatar da abin da ya ce, daga nan ya ce mata. "Je ki mayar mata da wayar, yanzu zan dawo ba jimawa, wait for me don't sleep"........ "Okey my Romeo, love you more"...... "Love you too". Kit ya kashe kiran tare da miƙawa Vash wayansa dan ya duba voice ɗin.
A hanzarce ya karɓa, aikuwa yana dubawa ita ce, tabbas ba aljana bace Manassa ce, aikuwa ya ce zai yi mata tsiya shi ma, ba zai bari ta gane ya gane ita ba aljana ba ce, su cigaba da tafiya haka, ranar da zai damketa yana nan zuwa, zata san ta taɓo jinin Champion na IRON FIST, yadda ta dinga bashi wahala yana magiya ba zai kyaleta haka ba.
Daidai lokacin suka isa bakin tekun nan amma ta can nesa da tantinsu, wani ɓangare ne da ake sauƙe ƙaya, amma ba ainahin in da ake sauƙe kayan bane, nan wani gefe ne kamar na sirri wanda ba kowa yasan ana sauƙe kaya a wajen ba, watau idan jiragen ruwan suka kusa isowa madakata in da ake sauƙe ƙaya, sai su ratse hanya, su ratso gefe can nesa daga in da ake sauƙe ƙaya, sai su dakata a wannan waje, kuma jiragen ruwa basa wannan ratsen sai tsakar dare, suna tsara tafiyarsu yadda sai dare zasu kusa isa madaka in da ake sauƙe ƙaya.
Tin da suka doso wajen wasu mahaukatan karnika suka fara haushi da karfi-karfi, alamar securitys dogs ne, waɗan da aka horar da su dan gadi, kun san su dik yadda suka ji motsi sai sun yi haushi. Aikuwa suna wannan haushin wasu kartin maza suka fara firfitowa daga cikin jiragen ruwan dake faffake a bakin ruwa, wasu ma ba'a sauƙe lodin kayan dake kansu ba.
Maza ne mada karti da a ƙallah zasu kai 30, dikkansu yawancinsu babu riga a cikinsu, suna murɗe sosai, dama kun san tsaron irin wannan waje sai masu rai da lafiya game da jini a jiki ake baiwa, dan kome zai zo su iya tarewa.
Hannayensu rike da gabza-gabzan torchlight masu masifar haske, suna wani bubbuɗewa suka fito da nufin su ga su wanene?......... Ganin haka yasa Leo ya ce. "Is time for game"...... Yana faɗar haka tin bai rufe baki ba Noor ya diro ƙasa daga bayan nasa. Da gudun gaske suka dare suka rabu.
Dik suka kama wajen ɓuya, wasu suka ɓuya bayan kwantainars, wasu kuma bayan jiragen ruwa. Haske ko'ina waɗan nan karti suka fara yi suna wani irin numfashi irin na gardawa. Kewaye lungu da saƙo suka fara yi da haske, while dik in da suka yo sai sojojin AZURE sun kauce sun ƙara ɓuya.
Wani shirgegen ƙato ne ya zo ya wuce saitin in da Noor ya laɓe, ya wuce gaba yana haske-haskensa. Ai yana wucewa Noor ya fito, dik da baya jin kuzari a jikinsa, haka ya bi bayan mutumin, yana zuwa ya sanya hannunsa ya shaƙo wuyan mutumin ta baya, ya matse da hannu ɗaya tare da sanya ɗayan hannun ya toshe mashi baki.
Fafutuka ya fara yi yana neman yadda zai kwaci kansa, sa dai ina, renon AZURE ba wasa ba, sai da Noor ya kaisa ƙasa, sai da Noor ɗin ya tabbatar baya numfashi, sannan ya sakesa tare da karɓar light ɗin hannunsa, ya kasheta game da turata cikin aljihu kafin ya damƙi ƙafar mutumin, ya ja shi a ƙasa tamkar kayan wanki, bakin ruwa ya kaisa ya jefar sannan ya dawo ya laɓe.
A daidai lokacin shi ma Zaynish ya muɗe wuyan wani da ya zo ta kusa da shi, aikuwa yana dab zai haskasa Zaysh ya yi kukan kura ya danke wuyansa, ya murɗe ya karyeta. Yana karyewa Noor ya sake damke wani, shi ma murɗe mashi wuya ya yi ya karya. A tare Leo da Zaynish suka damki wasu biyun, dikkansu murɗe masu wuya suka yi suka karya. Daidai lokacin shi ma Vash ya damƙi wani shirgegen ƙato, ya murɗe mashi wuya.
Faɗar ta koma yaƙin sunkuru, suka dinga yi masu ɗauki ɗaiɗai har sai da suka kashesu tas, sannan suka kutsa cikin kwantainars ɗin. Har lokacin karnukan suna haushi, sun bi dik wanda suka kashe sun ɗauke torchlight ɗinsa sun kashe. Nufar in da suka ɗaure karnukan a jikin wata bishiya Leo ya yi, ya je da nufin ya kashe karnukan, amma sai ya ga suna da mugun kyau sosai, irin manya-manyan karnukan nan ne masu tulin gashi a jiki, ga su farare tas, hakan yasa suka burgesa, su biyu ne, ɗaya gashin jikinsa har yana jan ƙasa, ɗaya kuma bai ƙarisa kai na wancan ba, bujumaye da su tamkar zakuna.
Shafa kawunansu ya yi, hakan yasa suka yi shiru, sai ya wuce ya kyalesu da nufin idan sun gama abin da ya kawosu zai kwance karnukan su wuce da su.
Gaban wani ƙaton kwantaina suka tsaya, hannu Leo ya sanya wajen jikin container, sai ya ga alamar gari-gari. Tsanin dake jikin container ya kama ya hau, Noor na rike da light yana haska mashi, ya haye zuwa wajen da aka sanya sarƙa aka ɗaure container sosai. Ƙasa ya sauƙo, suka shiga cikin wata jirgin ruwa, a nan ya samu almakashin tsinka sarƙa.
Dawowa ya yi, Noor na haska mashi haske ya sake hayewa sama, karfi yasa ya datse sarkar, sannan ya sauƙo, Zaynish da Noor suka haɗu suka buɗe marfin container. Dallah light a ciki suka yi. Kaya ne shirye a cikin kwalaye, an shiryasu datsan-datsan. Leo ya ce Zaynish ya sauƙo da kwali ɗaya su gani.
Ba musu ya sauƙo da shi, suka farka bakin suka buɗe. A tare suka ɗago suka kalli juna, wasu irin sinadarai ne na haɗa ƙananan boma-bomai, shegen tsada ne da waɗan nan sinadaran. Kai kawai Leo ya jinjina, bai yi magana ba, ya ɗauki almakashin ya matsa zuwa container na gaba, ya datse sarkar da aka rufeta. Zaynish da Vash suka buɗe marfin, while Noor yana ƙoƙarin rufe kwalin sinadarin boma-boman nan, a matsayinsu na sojoji dik wannan karatu sun san shi, hmmmmm su suka san me aka shirya a wajen, shiyasa kuka ga Leo ya girgiza kai kawai.
Suna buɗe container na biyun kuwa kwalayen drugs ne a cike a ciki. Leo ya ce Vash ya sauƙo da kwali ɗaya. Da sauri ya sauƙo da shi. Buɗe kwalin suka yi, wasu irin magunguna ne wanda aka ɓuye ainahin manufar drugs ɗin, aka ɓuye ainahin daga ina suke, a jikin kwalin maganin an rubuta made in Avaris, amma sai ga shi sun kama maganin a bakin tekun shigo da shi ƙasar, kunga kenan dama daga waje ake shigo da su aka ɓoyewa ƴan Avaris gaskiya, aka ce a ƙasar ake haɗa masu.
MAGANIN ME?. Mu haɗu a page na gaba dan jin wani irin magani ne? Gaskiya mutanen ƙasar Avaris suna ganin rayuwa, daga ganin wannan magani ba gaskiya aka ƙullah ba, saboda an rubuta cewa a ƙasar ake haɗa maganin a jikin kwalin, to ga shi kuma ashe daga waje ake shigo da shi, ya ALLAH! Ana cutar da su dayawa, ALLAH sarki, idan gaskiya maganin ya ƙunsa ba za'a ɓuye daga in da ake haɗa shi ba!.
Littafin nan jinsa nike tamkar true life story, kamar rayuwar gaske......😭💔
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-22.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 70 Chapter of 95