sun karanta Annabi Isa ya haramta!.
Tin da suka gama karantawa suka natsu tsit suna nazartar kalaman Lion, dik abin da ya faɗa gaskiya ce, ba yadda za'ayi ace rana tsaka ƴan ta'adda su bayyana a waje, su kori jama'a a kauyuka su kwacesa su zauna, lallai tsawon shekaru ake ɗauka wajen horasu a kan hakan, tamkar yadda ake hora sojoji, idan an gama horasu sai su bayyana, ba ƴan ƙasar Avaris bane, bakin haure ne, wlh ainahin ƴan ta'addan ba ƴan kasar bane! Suna amfani da ƴan ƙasar ƙalilan daga cikin jahilan da sukaki karatu ne, sai su fake a bayansu suna taddancin, ƴan kasan da ake yi wa kallon ƴan ta'adda lallai karnukan farautar jiga-jigan dake laɓe a bayansu ne, manyan basu fitowa fili su yi aiki kai tsaye ne saboda gudun aga banbancin launin fata da sauyin harshe, shiyasa suna gefe suna koyawa karnukan farautar tasu ɓarna, ban da haka dakikin da bai je makaranta ba yaushe yake iya magana da correct English? Baku taɓa jin ƴan ta'addan suna turanci ba ko? To iyayen gidansu dake koya masu harbi da bindiga da sauransu turanci kawai suka iya! Dole su koyi turanci na magana yau da kullum.
(Can naga wani ɗan ta'adda a media yana video yana cewa we have a lot of informance everywhere, I said eyeee this guy hear English well-well, he pass me da na yi FGC makarantar da ba'a magana da kowacce yare a cikinta sai turanci, ashe ni dik shirme na iya, ga wani a kwana can ya kware ba tare da zaman class ba. ALLAH kai mana kyakkyawan karshe, ba lallai a yanzu ku gane in da na dosa ba, saboda tushe nake son ɗauko maku, but keep reading, zaku gane sosai a gaba!)
Nazarta kalaman Lion for almost 10 mins suka yi, sannan Champion ya hau typing kamar haka. All what you said is true, but ƴan kasar ba zasu taɓa fahimta ba, everything is damage now.
Typing amsa Lion ya yi da cewa. Shiyasa aka shirya masu rikicin addini, rikicin akida da rikicin ƙabilanci dik dan kada a bar hankalinsu ya natsu waje guda har su iya fahimtar gaskiya, kasan ƴan kasar Avaris ba dai ƙwaƙwalwa ba, ko dame kake ji sun bugeka a kaifin tinani da basira, shiyasa ba za'a barsu su natsu har su yi tinani ba dan an san confirm sai sun gane gaskiya, wannan dalilin yasa rayuwarsu aka mayar da shi tamkar season film, kowani sati da sabon season da za'a shiga masu, a kowacce rana da kalar episode da ake buɗe masu suna kallah, an rikita tunaninsu, idan zasu aikata laifi ma baka ga sai sun kawarwa da ƴan kasar hankali sun basu abin da zai ɗauke masu hankali daga kan kasar ba? Saboda sun san ƴan baiwa ne a kasar, in basu ɗauke masu hankali ba lallai ganosu zasu yi. Two days ago ba an je an yi kidnapping wasu mutane a kauyuka ba? Aka yi districting na hankulan mutane, dik suka koma magana a kan wannan case na satar mutanen da aka yi, a wannan lokacin ne suka shigo da sabbin ƴan ta'adda cikin ƙasar, bayan sun shigo dasu ne kuma al'ummar ƙasar nata faman koke kan ɗauke masu mutane da aka yi, shi ne suka fito da batun bayyanar sabon ƙungiyar ƴan ta'adda sai ya ɗaukewa al'umma hankali daga kan ƴan uwansu da aka sace, suka koma batu kan ƴan ta'adda, nan da gobe ko jibi zasu sake fito da wani sabon season ɗin dan su rufe bakin mutane a kan sabbin ƴan ta'addan nan, jama'a su koma tattaunawa a kan sabon season da za'a sake masu, shikenan tsohon season zancensa ya bi iska.
Are you thinking what I'm thinking kuwa my people?.
Guru ne ya ce. "Exactly abin da ka faɗa, amma kai a tinaninka meyasa Avaris ta tura su Leo Mission na farko a kan tsofaffin kungiyar ƴan ta'addan da suka jima a harkar?".......... A wannan karon da baki Lion ya amsa masu da cewa. "Kwarewarsu Nirash suke son gani, kowani jami'i AZURE ta yaye sai sun turashi aiki wani waje domin su gwada iya kaifin basira da kwazonsa, dan su san in da yakamata su ajiye shi".
Champion ya karɓa da cewa. "Suna tinanin su Leo ba zasu iya mission a kan waɗan can gogaggun ƴan ta'addan bane, saboda suna tinanin su ba ƴan kasar Avaris bane, so da wuya idan suna da kaifin ƙwaƙwalwa"........ Guru ne ya amsa da cewa. "Ai sun yi kuskure in kuwa haka ne, domin kuwa Nirash ai ba renon AZURE kai tsaye bane ma, su karisar mana da aiki suka yi, ko GAT ɗinsu da kansa Nirash zai iya koya mashi aiki a yanzu".
Ni kuma na karisa masu da cewa bugu da kari daga Nirash har Vash ɗin jinin Avaris na gudana a jikinsu ta ɓangare mai karfi! Dan haka kowa sai ya jira!. ALLAH ka bamu irin IRON FIST a duniya, dan ba zan ce a ƙasarmu kawai bama, a ko'ina akwai musulmai, dan haka ALLAH ya bamu ire-irensu ta ko'ina su ci mana uban azzalumai!!.
Lion ne ya ce. "Kada ku taɓa sanya hannu a mission na su Nirash, let them fight, ban yarda ku bibiyi abin da suke yi bama, kamar yadda muka fafata muka kwaci kanmu har muka zama abin da muka zama yau, suma haka zasu fafata"........ Lion yasan halin Champion sarai, wlh Aryan yana mugun son Leo fiye da yadda kuke zato, ba dan blood is thicker than water ba da na ce ya ma fi Lion son Leo, shiyasa ya taka masu birki, dan yasan tsab Champion zai tsaya masu, karamin aikinsa ne, shi kuma Lion yana son su wahala, su gwabza, su zama mazan gaske masu kwatar kansu kamar dai IRON FIST ɗin!!.
Cigaba da tattaunawa suka yi, daga karshe suka yanke shawarar da kansu zasu mayar da Nirash and Vash jibi, suna da buƙatar kaiwa Avaris ziyara, su ɗan yi yawo a cikinta na kwana biyu kafin su dawo, dan aikinsu ma ta cigaba masu. A kan wannan matsaya suka tsaya, daga nan suka tashi wannan zama.
Lion da kansa ta ɗauki zafi wanka ya yi ya kwanta, a cikin 24h bawan ALLAHN nan ya samo waɗan can bayanai a kan WORLD SYSTEM, kunga kuwa dole kansa ta yi ciwo, shi kuma guru wasu drugs ya ɗebo a drawer ya watsa a baki ya bi da ruwa bayan ya yi wanka kenan, sai ya koma kan computers dan ya zurfafa bincike kan mission nasu Leo, shi hankalinsa bai kwanta a kan irin mission da aka basu ba, jami'an baya da AZURE ta yaye guru ya fara dubawa, duk waɗan da aka yaye babu waɗan da aka baiwa mission mai wahalar nasu Leo, to meyasa?. Ga shi gwamnatin Avaris ke shirya wannan mission ɗin, daga hannun Minister tsaro na ƙasa takardan yake fitowa.
Shi kuwa Champion wajen Seraphina ya koma, irin wannan dalilin ne yasa Lion ya tsani mata su shigo cikin al'amurransu, da ace a baya ne suka yi irin wannan zama da yanzu Champion yana gaban computer yana kara zurfafa bincike, amma kunga yanzu ya tafi wajen Seraphina ba tare da ya sake bi ta kan case ɗin ba.
-----------------------🔥
Turesa V ta sake yi da karfi tana sanya mashi kukan cewa da zafi, ba zata iya jura ba, take ta fara kuka hawaye bibbiyu, hakan ba karamin ɗaga mashi hankali ya yi ba, da sauri ya kwanto jikinta ya rungumeta, rarrashinta ya fara yi yana faɗin ta daina kuka ya fasa yi.
A ransa ba wai ya fasa bane, yanzu ne dai zai kyaleta, amma he promised him self da zai bata maganin da zai sa ta fita hayyacinta ta yadda ba zata ji zafi ba, gobe sai su yi. Da haka ya daure ya kyaleta tare da rungumeta yana wasanni da sassan jikinta har barci ya ɗauketa ita.
Shi kuma ya zareta daga jikinsa a hankali, toilet ya fara shiga, sai da ya yi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe ya nufi wajen daddynsa, amma sai da ya gyara mata kwanciya ya rufeta da bargo. Tsaye ya isko daddynsa yana waya, a gefen bed ya zauna tare da zubawa daddyn nasa idanu.
Sai da ya kammala wayar, waya ce dama da kamfaninsu kan kayar da za'a fitar zuwa ga abokan cinikayya. A kusa da Noor ya zauna tare da jawosa jikinsa yana tambayarsa ya aka yi ne. Kwamciya a jikin daddyn nasa ya yi, a shagwaɓe ya faɗa mashi dik abin da ya aikata.
A tinaninku daddy zai mashi faɗa ko? To ku dawo tunaninku, ba musulmai suke ba. Cike da farinciki daddy ya ɗago haɓarsa, yana murmushi ya ce ɗansa ya girma ya kuma zama jarumi, har da ce mashi ya gwada jarumtarsa kada ya zama rago, a zuwan farko ya sama masu babys maza, wai kun san yadda daddy yake ji da Noor kuwa? Ai kwarara mashi gwiwa ya yi tamkar abin arziki zai aikata.
Kamar Noor zai yi kuka ya faɗawa daddy ai V ta ce da zafi ya ɗaga mata kafa, kuma shi yanzu yana buƙatar mace. Nan fa daddy ya faɗa mashi ya kara kokari, tamkar shi ne mahaifin V har da ce mashi gobe ya saya mata zoben aure shikenan ta zama matarsa, daga nan daddy ya ce bari ya je ya ganta, yana son sanin wacece daga cikin su huɗun. A takaice dai daddy ya baiwa Noor goyon baya ɗari bisa ɗari.
Da sauri Noor ya riko daddy, yana ɗan turo baki ya ce. "Daddy ka bari sai da safe ka ganta, yanzu ta yi barci kuma bata da kaya a jikinta"....... Fasa zuwa ya yi, ya zauna suka cigaba da hira har dare ya tsala. Sai can ya miƙe ya koma room ɗinsa, saman bed ya haye, a kusa da ita ya kwanta tare da kara ja masu bargo, bai sake taɓata ba saboda kada ya shiga cikin wani hali.
Less short the story. Washegari daddy ya sai zoben zinari wa Aunty Lisa, ya sanya mata, suka yi da daddy Noor kan cewa after tafiyar su Noor Mission za'ayi party ɗin bikinsa da Aunty Lisa, kun san su suna iya yin aure da shekara uku ma kafin ayi party, to shi abin da yasa ba za'ayi shagali yanzu ba yana da gagarumin aiki a gabansa na wannan mission da su Noor za su tafi, kuma su sojoji kun san aurensu yana da lokacin, sannan abu ne da ake ɓoye shi, ba'a cike shelanta aurensu ba, dayawansu auren sirri suke yi, musamman manyansu, dan haka daddy GAT ya ce ko za'ayi party guda ɗaya za'ayi, kuma a nan US za'ayi ba'a Avaris ba, dan a yanzu ma baya son Avaris tasan ya yi aure, sai gaba.
GAT bashi da ishasshen lokacin ɓatawa a US, dama kwana ɗaya yake da niyar yi, saboda tafiyar su Noor, dan haka da safe suka shirya komai da daddy Noor ya ɗauki yaransa suka wuce airport da Aunty Lisa. A lokacin da za su tafi Noor sun rakasu har airport shi da daddy and Aunty Lusi, Aunty Luna bata je ba, tana da meeting mai muhimmanci so ta tafi attending.
A gefe guda da suka je airport sai satar kallon juna Noor and V suke yi, ko kaɗan Noor bai damu dan basu yi abin da ya so su yi jiya ba, dan yasan barrack ɗaya suke ai, kuma shi ma gobe zai koma. Daddy Noor kuma sai albarka yake sanyawa V har ta gagara hakuri sai da ta yi wa Noor message a kan ya faɗa mata me ya faɗawa daddynsa da ya kara sonta sosai har haka? Meyasa yake sanya mata albarka.
Sai bayan sun dawo gida ya duba wayansa ya ga saƙonta, one side smiling ya saki kafin ya rubuta mata reply kamar haka, na faɗawa daddy abin da muka yi daren jiya ne shiyasa ya kara sonki, ya ji zaki haifa mashi jika da wuri....... Da jin haka sai ta ji ta yi danasanin hana Noor kanta da ta yi, dan yadda daddy ya damu yake son jika gaskiya bata kyauta ba da ta zama bata bari sun kama hanya ba, amma da ta tuna ai Noor zai dawo gobe, suna da lokaci a tare, sai kawai ta ji daɗi.
In kara takaice maku labarin nan after one day su Noor dik suka yi wa AZURE diran mikiya, a rana guda dik suka dawo saboda basa wasa da lokaci. Harta Zaynish ya dawo, amma fa kafin ya dawo sai da ya saita gidan Ummie, tin daga kan uwar mijinta, uban mijin nata, wannan shegiyar Auntyn nasu, gabaɗaya kannen mijinta tattarasu ya yi, ya basu capital warning, ya ce masu wlh a kan Ummie ba irin hukuncin da ba zai masu ba, zai iya sanya bindiga ya harbe mutum kuma ya harbe banza! Shi ba sojan Nigeria bane a yanzu, karkashin ikon gwamnatin AVARIS yake! Yakamata su san wannan, dan haka su shiga hankalinsu.
Ko da zai dawo kuma bai bari Ummie ta sanar masu cewa ya koma ba, ya ce mata kada ta gwada masu ya koma, dan zasu iya cigaba da yi mata iskanci, yanzu dai biyayya sama da ƙasa ake yi mata, har amarya da aka sha jinya aka dawo, yanzu zaman lafiya take da Ummie, ai dik wanda ya sha dukan soja so ɗaya ko a mafarki ba zai so ya sake haɗa hanya dashi bama bare duka, mutanen da in suka mareka sai ka ji kamar ba'a duniya kake ba, kunnenka ya daina jiyo sautin komai, dole amarya ta natsu. Yanzu dai Ummie ta samu saukinsu sosai, kannen mijinta mata Aunty sama Aunty ƙasa, marasa kunyar karya, ai komai waje yake samu, yanzu dai dik sun haɗa malaman jikinsu, wata mara kunyar kaunar Faisal ɗin ma wai son Zaynish take yi, ta tattaro kayanta dik ta dawo wajen Ummie, sai ladabi da biyayya take yi mata, har aiki dik ita take yi mata, burinta kawai ta dinga ganin Zaysh da har ya gama zamansa a gidan bai taɓa ɗaga ido ya kalleta ba, magana wannan baya yi wa mutane kuma baya amsa nasu idan sun yi mashi, idan kun ji Zaysh yana magana to da Ummie ne, bayan ita sai Faisal da suke waya, idan ba su ba sannu baya haɗa shi da kowa.
Da Ummie tai mashi maganar aure zai ce ta zaɓa mashi mata kowacece in dai ita ta zaɓa mashi zai aureta. To kannen Faisal sun ji haka shiyasa suka makalewa Ummie dan ta zaɓawa Zaysh su, suka kirkiro halin kirki na karya, ladabi tamkar kaza a cikin miya. Shi dai Zayah har ya gama hutunsa ya koma kallo wannan bai haɗa shi da su ba, da zarar ya fito ma zasu gudu cikin ɗaki, suna tsoron haɗa hanya da shi, sai dai su dinga leƙansa ta window har ya fita, idan yana gidan amarya bata zama a waje, tana ɗaki, sai ya fita take fitowa ta yi aiki da sauri ta koma ciki.
Da ya koma Ummie ta ce masu ya yi tafiya ne zuwa Niger zai je ya ga gida ya dawo, bata faɗa masu ya koma ba, ya kara bunƙasa mata shagonta, yasa an kawo mata abays daga Egypt, Dubai and Turkey sosai da kuɗin da su Noor suka bata, ya gyara mata kasuwancinta kafin ya koma. A takaice kun ji yadda Ummie take ciki. Idan na ce zan tsaya rubuta maku komai labarin ba zai gudu sosai ba, ainahin labarin yana gaba, yanzu dik sharar fage ce, so ba zan tsaya ɓata lokacina a kan abubuwan da basu da muhimmanci sosai a labarin ba, fatan kun gane?.
To a yanzu dai dikkan sojojinmu sun dawo barrack, sun kuma dukufa a kan aikinsu, shirye-shiryen tafiya mission suka fara yi ba kama hannun yaro, a cikin kwana biyu da ya rage masu su tafi sai da suka shiga practical, aka kara horar dasu, sannan aka faɗa masu mission ɗinsu na farko.
Daga nan suka dawo suka ƙara shiri, tin da Noor ya dawo basu haɗu da V ba, saboda gagarumin aikin dake gabasu, ko waya basa yi, ita ma bata damu ba, saboda shirin da suke yi ita ma, zasu fara aiki a yanzu, za'a gwada kwarewarsu, shiyasa ita da Arya and Angelina suke ta faman shiri, ita kuma manassa idan baku manta ba na faɗa maku ita Surgeon ce, ba jami'a bace, idan kun ji Surgeon General ko Surgeon Brigadier yana nufin likitan dake kula da rundunar dake karkashin Brigadier ko General ɗin ne, to ita Manassa Division Surgeon ce, watau likita mai kula da majinyatar runduna na musamman, ita zata yi aiki ne a medical corps na soja. Dan haka dole zata tafi Mission da su Noor, saboda sune runduna na musamman, dik idan sojiji zasu tafi mission ana haɗasu da kwararrun surgeon saboda in sun ji rauni, an harbesu ko sun faɗa wani waje sun ji ciwo sai ayi jinyarsu, so a taƙaice ita Manassa ba jama'a bace, likitar sojoji ce.
A wannan rana irin ta yau dikkan jami'an da aka yaye zasu tafi Mission ɗin da aka sanyawa suna DEATH OR LIFE (DOL) kenan a taƙaice. Gabaɗaya sojojin da suka yi imani da cewa mutuwa ba'a bakin komai take ba sune a tsaitsaye a cikin hall na AZURE. Tabbas Noor ya yi mamakin ganin V a cikin tawagarsu, bai yi zato ba, ita ma bata taɓa zaton da su zata tafi ba, sai kallon juna suke yi daɗi tamkar su kurma ihu.
Dikkan jami'an babu alamar wasa a tattare dasu, dikkansu a shirye suke tsab wa mutuwa. Zasu tafi wannan mission na farko ɗin ne a karkashin ikon Brigadier General na ƙasa, shi zai kula da mission ɗinsu na farko, dan haka yasa ƙananan sojoji suka fara shirya masu rucksack ɗinsu, watau wannan jaka katuwa ta sojoji, wannan jaka da kuke gani tana ɗaukar abubuwa fiye da tinaninku, a matsayinsu na masu tafiya Mission ga abubuwan da aka shirya masu a cikin wannan jaka.
Combat uniform na yadi nai karfi da kwari, akwai tactical shirt wasu rigunar aiki ne ta musamman, sai jacket ɗinsu saboda sanyi. Bayan uniform akwai combat trousers da ake basu, yana nan kalar kayan sojiji, amma shi wando ne mai tarin aljihuna fiye da uniform ɗinsu. Akwai manyan gloves ɗinsu dan kariya ga hannuwa daga yankar wuƙa, zafin ɗaukar bindiga musamman a lokacin yaki idan bullet na fita daga bindiga yana masu zafi a hannunsu, to wannan kakkarfar gloves ɗin zai taimaka masu sosai.
An baiwa kowani soja body armor, ballistic vest ɗai-ɗai, body armor rigar kariya ce daga bullet, kazalika dik an basu plate carrier dan sanya ƙananan wuƙarsu na soja, ƙaramin bindiga and wayarsu na na ujila da sauran abin da ba'a rasa ba. Kowani soja an bashi helmet wasu ballistic helmet, waɗan nan huluna ne na soja dan kariya ga kai daga wajen buguwa da sauransu.
Sannan dikkansu an basu camouflage, wasu kuma ghillie, kaya ne dan ɓoyewar sojoji a lokacin yaki, kamar ciyawa haka aka yi kayan, idan sun sanya ba zaku taɓa cewa mutane bane, musamman idan suka kwanta, sai ku zaci shuka ce a wajen, dik dabarun yaki ne. Dik an basu tactical belt dan ɗaukar ƙananan kayan aiki da holster.
Sannan dikkansu sojojin an basu service rifle, wasu assault rifle, bindigu ne wanda dayawan sojoji dasu suke amfani. Sannan mutum uku daga cikinsu watau manyan cikinsu an basu pistol gun, Leo kuma sidearm, ƙaramin bindiga ne da zasu iya rikewa da hannu ɗaya dan kariya ta kusa ko faɗar gaggawa, uku daga cikinsu da aka bawa sun haɗa da Leo, Noor and Zaysh, su ne position one to 3 ɗin.
Sannan an basu rocket propelled grenade, kayan ne da aka yi dan lalata manyan abin hawa masu ƙarfi, in case ko ƴan ta'addan suna da motocin yaki ko abin hawa su ce zasu gudu, to zasu yi amfani da wannan dan lalata shi. Sannan kowani soja an bashi optics wasu kuma scopes dan hangen nesa, saboda ya taimaka masu wajen inganta daidaito harbi ko ganin nesa, zasu iya duba nesa ko su hango me abokan gaba suke yi. An kuma basu bipod dan ya rinƙa daidaita bindigarsu a lokacin harbi.
Kowani bindigarsu an mashi suppressor, na Leo , Noor and Zaysh kuma an masu silencer, hakan yana rage amon karar harbi da flash light da yake kawowa, hakan zai taimaka kada abokan gaba su riskesu da wuri. An basu wasu mahaukatan flashlight, mutane ukun nan kuma weapon light, wasu irin light ne masu balain haske wanda in suka haska sai waje dik ya zamto tamkar rana, baku ganin torchlight na sojoji ne? Hasken balai garesa, ga shi da haska nesa sosai, in suka dalla shi sai ya kashe ido.
Dikkansu an shirya masu night vision goggles ta yadda ko a cikin duhu tana amfani da ƙarfin intensification na haske, komai duhu in dai yana fuskansu zasu iya yin aiki kuma zasu iya ganin abu!. Sannan dik an sanya masu ɗan karamin thermal imagers, na'ura ce ta gano zafi ko a cikin duhu, idan abu mai zafi ya nufosu zai yi alerting nasu da sauri.
Sannan dikkansu an mallakawa kowannensu handheld radio dan sadarwa ga juna, ƴan rundunan zasu dinga amfani da shi saboda sanarwa ga juna halin da suke ciki, an yi masu connecting na shi dikka, in ɗaya ya yi magana dikkansu zasu ji, kuma zasu dinga karɓar umarni daga ogansu Leo, fatan kun ganesa?.
Dik da wannan sai da aka kara masu da headset with boom mic, shima dik na sauraran juna ne da magana da su kai tsaye, gudun ko ta kwana ne, ida wancan baya bada abin da akeso sai su ɗauki wannan.
An basu data mai karfi dan satarwa, an saita wayoyinsu da na'urorin su Arya. Dikka waɗan nan abubuwa fa wannan shegen rucksack ɗin nasu ya kwashesa, ga kayan sakawansu still a ciki, jakar ta cika dam, sai da aka sanya masu belt aka iya rufe jakar, ta yi mugun nauyi, amma a haka zasu ɗauka a bayansu. Mazan fama ba, soja ba dik kai ba!.
A ɓangaren Manassa an zuba mata Individual first aid kit mai shaƙe da kayan farko na taimakon gaggawa, a cikin akwai irinsu bandages, tourniquet, hemostatic agent da sauransu dan ceto ran soja da gaggawa. Sannan an sanya mata combat medic kit, kayan aikin likita masu yawa sosai kuma masu amfani da za'a buƙata a gaggauce dan jinyar raunin filin daga ƙananan zuwa matsakaita a yayin mission.
Dikkansu an basu water bladder dan su samawa kansu ruwa a koma ina suke, kuma ruwan zai zama mai tsabta har su sha su yi abin da zasu yi. Dik an basu ƙananan sleeping system mai caji da rana dan in suna barci wani motsi ya zo komai nisan shi wannan ya ankarar da su. An basu entrenching tool na karfe wanda ake haɗa shi da notika, idan sun isa wajen da zasu kafa tantina suna iya haɗa shi, kamar shovel haka yake, dan su tona rami aka basu.
Sannan dikkansu an basu gas mask wasu kuma cbrn mask, mask ne dan kare numfashi daga iskar guba, iskar sinadarai ko biological hazards dake yanki, takan iya yuwuwa akwai gurɓacewar yanayi a in da suka nufa, wannan mask zai hanasu shaƙar gubar. Sannan an basu cbrn suit mai kama da jacket, yana kare gangar jikinsu daga iskan sinadarai ko gurɓacewar yanayi. An basu cbrn hands gloves, da kuma ear protection dan kare kunne daga ƙarar makami, suna sanya shi kada su rasa jinsu saboda karar bindigu.
Su Arya jami'an computer na musamman kuma an shirya masu compass & maps gps unit a laptops ɗinsu, kuma dik abin da aka basu mai caji da rana ne, dan shi rana a ko'ina akwaisa, lantarki kuwa kun san babu, shiyasa aka masu masu amfani da rana kamar solar kenan. Sannan an haɗa masu gps enabled devices, wannan zai taimaka masu wajen daidaita matsayi daga nesa sosai. An shirya masu na'urar hangen sama, ga su unmanned aerial vehicles, ƙananan drones dan hango sama daga nesa, ga portable drone controllers dan sarrafa uvn na waje.
Uwa uba an haɗa masu counter drone systems wanda zai iya gano drones na abokan gaba idan sun turo masu, su suna iya turawa abokan gaba ƙananan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 95