so kasheta, har ya daɓa mata wuƙa a gefen ciki guards ɗinta suka kama shi aka kaisa kotu daga nan aka kaisa gidan yari, tin daga wannan lokaci bai sake sanin in da take ba, shekarunsa 3 a gidan yari ya fito, tin da ya fito kuma nemanta yake yi. Amma allegedly mom ɗinsu ta yi surgery ne aka canza mata fuska dan ta kaucewa shiga hannun Lion, shiyasa yake ta nemanta bai ganta ba, ta yiwu tana kusa da shi bai sani ba, dan ance dik ta yi surgery ta canza halitta, ta koma ƴar yarinya mai ƙananan shekaru kamar 18 years. AKWAI CAKWAKIYA INA FAƊA MAKU, amma gaskiya mom ƴar duniya ce, tana can tana yaudarar samari bayan ya koma ƴar yarinya, da ciwo ace irin wannan uwar ce da su, gara ma su kasheta su huta.
To shi Lion burinsa shi ne yakamata ta faɗa mashi su waye ta sadaukarwa da kwakwalwar daddynsa, dan ya yi alkawarin wlh sai ya karɓo brain ɗin mahaifinsa, gara mashi ya haƙa rami ya binne da ya barshi a jikin wanda aka yi mashi dashensa, to dalilin biyu yasa yake neman mom, ya kamata ta faɗa mashi su waye ta sadaukarwa, na biyu kuma ya shayar da ita gubar da ta shayar da Leo yana jariri! Dan haka dik abin da kuka ga Lion yana yi kada ku ga laifinsa, an kuresa ne, sun sa zuciyansa ya bushe ya ƙeƙashe, sun jefasa cikin manyan gangsters and terrorists ya yi rayuwa da su a prison, ya sha bakar wahala sosai, yanzu wutar fansa ce kawai take ruruwa a zuciyan bawan ALLAHN nan, shi kaɗai yasan wani irin raɗaɗi yake ji, sai ma idan ya tina cewa an dasawa wani banza can kwakwalwar daddynsa yana can yana morarta yana rayuwa, shin aikin alkhairi yake yi da kwakwalwar ko kuwa aikin sharri? Waɗan nan sune manyan ciwukan dake zuciyar Lion, amma kuma bai bari Leo yasan gaskiya ba, ya ɓoye mashi ta hanyar faɗa mashi basu da iyaye sun mutu, ya reni kaninsa cike da soyayya da kulawa, ya sadaukar da lokacin, dukiyansa da komai ɗinsa dan Leo ya zama mutum, babban abin takaicin kuma shi ne dikkansu da mahaifiyarsu suke tsananin kama, ko ɗaya basu yi kama da daddyn nasu ba, sai kaifin kwakwalwarsa kawai suka gado, shiyasa idan Lion ya ga fuskansa wani irin takaici ne yake kama shi, saboda in dai zai ga face ɗinsa to sai ya tina mom ɗinsu, shiyasa ko a cikin gida zaku gansa da face mask dan ma kada ya ga face ɗin nasa idan ya zo gifta mirror.
-----------------------------🔥
"Aryan stop! Stop it i said! Dr and mom dik ɗaya ne, mata dik basu da imani, ita Dr ba ita ta zama sanadin mutuwar Big Bro ba? Ka manta lokacin da na kirata a waya, ban taɓa rokan mutum wani abu a rayuwata ba, amma a kanta na dinga rokonta da ta buɗe Big Bro ya gudu, ta sake shi akwai matsala, me ta ce mun?"....... Nisawa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "She said so kake shi ma ya zama irinka ne? Ba zai sake fita ba! Kamar zan yi hauka ina cikin Washington, I called you and I called Scorpion that time dik baku yi picking ba, ina ji ina gani Big Bro ya mutu mutuwar walaƙanci all because of her! Da ita aka haɗa baki, ita ta bawa wasu damar su shigo su kashesa, in ba haka ba meyasa zata ɗauke wayoyinsa, ta rufesa a ɗaki ta hana shi guduwa? Why?!!". With harsh voice ya kai karshen maganar.
Shiru su Aryan suka yi, dan basu da wani hanya na ƙoƙarin wanke zuciyar Lion kan mata ba azzalumai bane, saboda ta ko'ina macece ta jefasa cikin bakar wahala, ya ɗanɗani zafin dafin harbin mace, dan haka kome zasu ce ba zai taɓa yarda ba. Amma da yake Aryan soyayyar Seraphina ta rufe mashi ido, sai ya yi ƙoƙarin wanketa, yasan idan ya yi shiru har Lion ya gane yana zuwa wajenta to rabasu zai yi, shi kuma ya kai matakin da ba zai iya rabuwa da ita ba, dan haka dole ya tursasa zuciyar Lion ya yarda cewa ba dikka mata bane mugaye, kuma Seraphina bata cancanci hakan ba.
Guru ne ya amsa da. "For sure Dr tana da sa hannu a kisan Big Bro, idan ba haka ba meyasa a lokacin da ka kirata kake ce mata ta buɗe mashi kofa ya gudu akwai matsala taki sauraranka? Meyasa ta rufesa a gida? Ai yana zuwa gidan bata taɓa rufesa ta hanasa fita ba sai wannan rana? Meyasa? Then ta kwashe wayoyinsa ta gudu da su, after mutuwansa ta gudu ta canza gida a lokacin da ka dawo daga Washington saboda tana tsoron haɗuwa da kai!".
Aryan ne ya amsa da. "Wlh bana jin Dr tasan za'a kashe Big Bro, kawai ina ga abin ya zo mata unexpected ne, and ku tina abu ɗaya mana, Dr bata da kowa, bata san kowa a US ba sai mu, and ta san su waye mu, ba zata taɓa yarda ta bi son zuciya ko zancen wasu a kanmu ba, zata ji tsoro, then dik wanda ya zauna da ita yasan macece mai rauni, meyasa idanunku ya rufe a tsanar mata kuke son ɓoye gaskiya ne? Zayra'an ai kafi kowa sanin halin Dr, amma saboda baka son mata shi ne zaka haɗasu kai masu kuɗin goro?".
Cikin fushi Lion ya ce. "Da sa hannunta, a wanan ranar kuɗi sun shiga account ɗinta daga wani account na daban wanda aka sanya mashi matakan tsaro, all IRON FIST members muna da information a kan dik wasu motsinsu kasan hakan, meyasa kake ƙoƙarin kareta bayan kafi kowa sanin cewa da sa hannunta?!!". Cikin tsawa Lion ya faɗa tare da kara shake wuyan Aryan da karfi, zuciyarsa na tafarfasa haka ya buga Aryan da jikin bango da karfi, sun tina mashi da abin da ya wuce, sun ɗaga mashi hankali, ya shiga out of control.
Da karfi Aryan ya ɓanɓare hannun Lion daga wuyansa, shi ma ya shake Lion ɗin yana faɗin. "Babu sa hannunta, kuma kaima kasan hakan, ni ba zan bi son zuciya in ki faɗar gaskiya ba, takan iya yiwuwa kuɗin da ya shiga account ɗinta na wani abin ne daban da wasu family suka tura mata! Baka yi tinanin hakan ba, sai ka tsani Seraphina, ƴarka, domin kawai mammynta tai maka laifi!!". Ya kai karshen maganar tare da buga Lion da jikin bango shi ma.
Guru ne ya ce. "Kun fara kenan, sai ALLAH ne kaɗai zai iya sassauta maku wannan ɗan banzan zuciya da fushin".
Ɗaga Aryan cak Lion ya yi ya buga shi da jikin wall glass na wajen restroom ɗinsu har sai da glass ɗin ta tarwatse watsa-watsa, cikin tsawa Lion ya ce. "Waye take da shi da zai tura mata kuɗi? All our family ni kaɗai nike tura masu kuɗi! Tana da ƴan uwa da ahali ne a nan? And ita da take ƴar kauye cikin daji a yaushe family ɗinta suka samu damar rike account mai tsaron da ba za'a iya bibiya ba? Ka daina rainawa kanka wayau Aryan!!". Ya faɗa tare da dunkule hannu ya daki show glass na littafansu cikin fushi, take glass ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse kaca-kaca.
A daidai lokacin Aryan ya tashi tsaye, zuciyansa na tafarfasa ya nufi Lion gadan-gadan, glass table ɗinsu ya ɗauka ya makawa Lion a gadon baya yana faɗin. "Baka son gaskiya, saboda ka tsani mata shi ne a kansu baka taɓa kyautata masu zato, ba zaka yi tunanin kirki a kan wannan al'amari ba, ko bata da ƴan uwa za'a iya tura mata kuɗi". Ya faɗa ne kawai amma shi kansa yasan ba haka bane, lallai kuɗin da aka tura account na Dr daga babban account mai tsaro ya fito, shi kansa Aryan ɗin yasan da kamshin gaskiya a batun Lion, amma soyayyar Seraphina yasa lallai sai ya wanketa a gaban Lion.
Da karfi Lion ya juya ya shakesa, ya ɗagasa sama, sannan ya buga shi da ƙasa kafin ya ce. "Ba zan yi tinanin alkhairi ba in dai akan mata ne! I hate them and also you now, i don't want to see your face!!"........ Wani irin azaba Aryan ya ji, hakan yasa ya ɗan rintse idanu, da kyar ya iya miƙewa, cikin fushi ya sake ɗaukar flower decoration ɗinsu ya bugawa Lion a kai ta baya, nan Lion ya juyo suka fara gwabza faɗa tamkar mayunwatan zakuna.
Shi dai guru rungumo hannayensa a kirji ya yi yana kallonsu, saboda yasan bafa zasu rabu ba, shi kaɗai bai isa ya rabasu faɗa ba, idan suna yi sai sun jigata dan kansu sun hakura, amma batun rabasu ma bata taso ba. Cikin ƙanƙanin lokacin suka wargaza ɗakin kaca-kaca, suka fashe dik wasu glass dake wajen, suka lalata komai, sun jiwa kansu ciwo sai jini suke zubarwa, Aryan yaki yarda da maganar Lion shi me Lion yaki yarda da maganarsa, kowa gani yake shi ne mai gaskiya.
Yau sun jima suna faɗa saboda magana ce kan abin da ya shafi zuciya, sai da guru ya ga Lion ya ɓaɓɓako Tv ɗinsu daga jikin bango zai bugawa Aryan dake baje a kasa yana numfashi sama-sama ne ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar dannawa da gudu ya rike Tv, suna cikin fushin nan zasu iya kashe junansu ne ma basu sani ba, kun san zuciya bata da hankali wani lokacin.
Ƙoƙarin kwacewa Lion ya fara yi dan har yanzu zuciyansa tafarfasa yake yi, sanya karfi guru yai, suka fafata, da kyar ya kwaci Tv ɗin saboda Lion ɗin ma ya jigata babu karfi sosai a jikinsa, so ya samu damar kwacewa kafin ya yi ta mazan shigar da Lion cikin wajen balcony ya rufe glass door ɗin. Da gudu ya zo ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa ya fita waje. Yana fita ya rufe kofar har da sanya key, a daidai lokacin Lion ya rugurguza glass door na wajen balconyn ya dawo cikin ɗakin, sai huci yake yi, kun san ance idan rai ta ɓaci sai hankali ya gushe to haka ne.
Ɗayan room dake kusa da nasu guru ya kai Aryan, ya kwantar da shi saman gado tare da shiga cikin drugs room ɗinsu, cikin gaggawa ya ɗauki wata allura, jikinsa har yana rawa wajen fara ƙoƙarin haɗa alluran nan, yana jiyo Lion na ƙoƙarin ruguje door room ɗinsu, dama su biyun nan zuƙatansu na da wuyar sarrafuwa idan ta kwaɓe masu, shi ma Aryan ɗin dan Lion ya dakesa da laptop ɗinsu a kai ne yasa ya shiga wani irin yanayi tamkar ya suma, kun san duka a kai akwai wahalar iya jurewa, ban da haka da yana cikin hayyacinsa wlh ba zai hakura ba shi ma, zai ce sai dai a yarda shi ne mai gaskiya, to thank god ya shiga coma mood.
Yana gama haɗa alluran ya fito da gudun gaske, kai tsaye room ɗinsu ya koma, yana zuwa daidai door Lion ya ruguje kofar zai fito. Cikin zafin nama guru ya shammacesa ya dankara mashi wannan allurar a gefen wuya, da sauri Lion ya dafe wajen tare da juyo da kallonsa a kan guru, ɗayan hannunsa yasa ya damki wuyar guru, ya shakesa da karfi, yana ƙoƙarin yin magana amma ya gagara, take idanunsa suka fara rufewa a hankali, ya fara ganin abubuwa bibbiyu, kan kace me wata yana ta fara rufe mashi gani.
Jim kaɗan ya saki jikinsa gabaɗaya zai faɗi ƙasa tare da zame hannunsa daga wuyan guru. Jifa guru ya yi da kwankon alluran hannunsa, cikin zafin nama ya tare Lion ɗin, sannan ya zare alluran dake wuyan nasa ya jefar kafin ya gyara shi da kyau, ya ɗaukesa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya fito da shi zuwa ɗayan ɗakin dake gefe ba wanda Aryan yake ciki ba, ɗakinsu da suke kwana su uku kam yau ma sun fashe komai kamar yadda in ta kwaɓe masu dama suke ruguje komai, sai sun huce ake sayan sabbin kaya, amma idan suka yi faɗa, oooooo kai kace abokan gaba ne ƴan duniya.
Room da Aryan yake a ciki guru ya koma dan ya duba ba dai ya samu matsala a kan nasa bane. Yana shigowa room ɗin daidai Aryan na dirowa kasan bed ɗin, da alama ya dawo normal. Fuskan nan tasa tamkar wanda aka bawa bakar labarin cewa wuta zai shiga, yana wani irin huci ya ce. "Ina Zayra'an?"....... Hannu guru ya harɗe a saman kirji kafin ya ce. "Aryan kada ace idan rai ya ɓaci sai hankali ya gushe mana! Ka sani cewa Zayra'an ba zai taɓa saurarenka ba, ba zai yarda da abin da zaka faɗa ba, kuma kai da kanka kasan kan batun case na Dr Lion ya fika gaskiya, mun san bata da ƴan uwa a nan, sannan ƴan uwanta na can a daji suke, ta ina ta samu kuɗi daga irin wannan shahararren account da sai manyan gangster's ko terrorists or manyan ƴan siyasa suke amfani da shi? Mun yi iya yinmu mun gagara bin diddigin mai wannan account ɗin, ka yi lissafi mana".
Hannu Aryan ya ɗaga mashi. "Is enough, koma dai menene Seraphina bata cancanci ya mata hakan ba"..... Kallon tuhuma guru ya wurga mashi kafin ya ce. "Aryan anya kuwa? Meyasa ka damu da Seraphina haka?"....... "Because she's my daughter!". Cikin tsawa ya faɗa. Gyara tsayuwa guru yai yare da ɗan karkata kansa, ya ɗan ɗaga mashi gera guda kafin ya ce. "After that kuma fa?".
Wani irin kallo Aryan ya wurga mashi kafin ya ce. "Get out of my room!!". Cikin fushi ya faɗa.
Kun san wani abu? A daidai wannan lokaci da suke ta faɗar su kuma Abba da Ammie suna can zaune suna shirin zuwa gidan makota tambayawa su Aryan auren yaransu, da Aryan, da Faryan and Harleen, Abba ya ce sun girma dik aurar da su zai yi, dan haka ya ga wasu ƴan mata uku a makwabta, ɗaya ma ƴar siyasa ce, yana ganin tana da kyawawan halaye, zata dace da Aryan, kun san su waye yake magana a kai? Su Aunty Luna Aunty's ɗin Noor, su Abba ya gani, ya yaba da hankalinsu, kun ga shi ba'a auren soyayya a gidansa, dan haka gobe zai je nemanwa su Aryan aure, dama so yake su tsayar da magana da Ammie gobe ya kira Aryan maza su zo su shirya su tafi aje a kaisu ƴan'matan su gansu idan sun yi masu.
Bafa idan ƴan matan sun yi wa su Aryan ɗin ba, a'a, idan dai su Aryan ɗin sun yi wa ƴan matan, shi Abba ba ruwansa da su Aryan basa so ko yaran basu yi masu ba, shi dai yardan ƴan matan kawai yake so, to jama'a wacece zata ga Champion namu na amana ta ce bata ciki? Ai kowacce makale mashi zata yi, akwai dai dirama, wai kaman Champion ɗin namu ne za'a kai mace ta gani ta zaɓa, lallai su Aunty Lusi anyi kasuwa mai tsadar gaske. Watau idan na hango cakwakiyar dake gaba a cikin littafin nan har wani ɗan juya mun kaina yake yi.
Sanin cewa suna cikin fushi ne hasa guru ya juya ya fita, bai sake magana ba. Cikin fushi Aryan ya wuce toilet zuciyansa cike da tunanin Seraphina baiwar ALLAH kuma marainiyar ALLAH. Ni kam na ce daddy Aryan ko dai ko dai? Ka faɗi gaskiya fa!.
----------------------------🔥
WS-HOSPITAL.
Safiyar yau ta fara masu ne da yanayi na musamman, sun tashi cike da farincikin da basu san dalili ba saɓanin yadda suka yi barci jiya da takaicin sister Lazy. Shiryawa suka yi tsab cikin kayan aikinsu, suka fito zuwa wajen aiki, sun mance ma da batun sister Lazy na jiya, saboda su mutane ne da sam basa rike abu a ransu, da sun yi barci sun tashi zasu mance komai abinsu.
Daidai zasu shiga side ɗinsu watau side C sai ga su Dr James a jere su ukun kamar yadda suka saba tafiya. Jikinsu na rawa suka sussunkuya suka gaishesu, dik in da zasu wuce sai an sunkuya an kaishesu saboda su ne manyan kwararrun likitocin.
Ko kallon in da suke basu yi ba suka wuce suka shiga section D. Da kallon su sister Maya suka bisu har suka shige ciki, ajiyar zuciya sister Zinta ta sauke kafin ta ce. "Kwanaki biyun nan Dr James suna yawan zuwa section D, ko dai wani project suke yi ne? Kullum da safe sai sun shiga wajen, suna kuma ɗaukar awanni kafin su fito".
Maya ce ta amsa da. "A tinaninki menene a section D and section E?".......... Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "I think akwai babban aiki a wajen, dan kinga su uku ne suke shiga wajen, project ne babba a wajen, musamman section E ɗin nan da yake killace a gefe guda, ga tsananin matakan tsaro har da kofofi masu amfani da lantarki a wajen, kai ina son sanin me a cikin wajen?".
Maya ce ta ce. "Idan kika koma aiki a karkashin office ɗinsa zaki iya sani fa, mu dai dage da aiki tukuru"....... "I wish hakan ya faru". Sister Zinta ta amsa da hakan....... "Me ya tsayar daku a nan?". Daga bayansu suka ji muryan sister Lazy. Da sauri suka wuce cikin section C ba tare da sun yi mata magana ba, ita kuwa fuuuuu ta zo ta wuce section D in da su Dr James suka shiga, tana wani hura hanci, ga hancin nata ya yi siriri sosai, ga shi dogo, ko ta hurasa baya huruwa, watau sister Lazy kyau ɗinta har yai yawa ya zama mata muni, kunganta kamar Aljana danginsu ifiritai, idanunta wlh in ta zarosu sai mutum ya ji hantar cikinsa ta kaɗa, manya-manyan ne idanun nata, gasu farare tas kamar audiga, sannan a waje suke, gashin idanunta tamkar an kara kuma a tsaitsaye suke, bata da lips in ji sauran nurses, saboda ƙanƙantar bakinta, yadda kuka san babyn roba dai haka take, ALLAH na tuba kyan yai yawa har ya mai data kamar aljana. Su kuwa su sister Maya komai nasu daidai ne gwanin birgewa, sai idanunsu suma kamar nata ne manya-manyan farare kal kamar audiga.
Cikin section D sister Lazy ta shiga, a nan ne waɗan nan tarin mahaifa dake cikin kwalabe suke in baku manta ba, bata bi ta kan mahaifan ba ta wuce izuwa wani kofa dake fuskantar kofar shigowa. Tura kofar ta yi ya shiga. Ɗaki ne mai girma sosai a wajen, cike yake da gadajen tiyata da a kallah zasu kai gado 30 zuwa 50, ɗakin yana da girma sosai, tsayawa zayyana maku abin da ɗakin nan ya kunsa ba zai yiwu ba, kawai mu je ciki, dan abin babba ne.
Kowani gado dake a cikin wannan ɗaki akwai mace guda ɗaya dake kwance a kansa, kuma ƴan mata ne da basu wuci 18 to 20 years ba, dikkansu kuma kamar barci suke yi ne ko suma, kai da alamar alluran barci aka yi masu, kowacce yarinya ka ɗaga ido ka kallah zaka san me ake nufi da kyan ɗan adam, wlh kamar su suka yi kansu, kyawawan gaske.
Su Dr James suna tsaye a tsakiyar room ɗin, suna dudduba ƴan matan da kyau, sun canza kayan jikinsu izuwa surgical gown and gloves, alamar sun shirya aiki kenan.
Dik macen dake kwance a kan wannan gadon gabanta a buɗe yake babu kaya, daga ta sama a rufe da patient gown, amma ƙasansu a buɗe. Dikkansu eggs retrieval za'ayi masu.
Cikin kwarewa dikka Doctors ɗin suka ɗauki kayan aikin da zasu buƙata, kowannensu ya nufi gadajen dake layin farko a jere, gadajen line by line ne a jere, so suna bin komai daki-daki. Ita ma sister Lazy kayan aikinta ta ɗauko watau jota and pen ta nufi wajen bed ɗin da Dr James yake, su Dr Kamal ma kowannensu da PA ɗinsu kamar dai Dr James da sister Lazy.
Ɗauko wani needle suction tube watau bututun ƙarfe su yi, kai bari mu bi Dr James mu ga yadda yake yi, ba sai mun bisu dikka ba, yadda yake yi haka kowannensu yake yi.
siririn bututun ƙarfe ya ɗauka tare da ɗaukan wani siririn na'ura ya ɗaura a kan cikinta, take computer dake manne jikin gadon da yarinyar ke kwance ta kanta ya kawo wuta, kai tsaye cikin cikin yarinyar ne ya bayyana a kan screen na computer, ɗan zubawa computer waɗan nan dara-daran idanun nasa Dr James ya yi. Sai da ya ɗauki 3 mins yana kallon yanayin cikinta tare da ɗan junjuya naurar dake kan cikin nata yana duba lungu da saƙo kafin nan ya gyara kafafun yarinyar dake kwancen, ta gabanta kofar virginity ɗinta ya zura wannan bututun ƙarfe mai karfin da ya ɗauka, dik da yarinyar tana barci sai da ta ɗan tsuke fuska alamar akwai azaban zafi kenan, imagine, yarinya budurwa ka zura mata wannan siririn bututun ƙarfe a gabanta har izuwa cikin cikinta, dole akwai azaba mana.
Yana zura karfen idanunsa a kan computer dake gabansa, yana kallon hanyar da yake bi ne, kada ya saɓa aiki, kai tsaye ovaries nata ya nufa da karfe, wlh yarinyar nan sai tsuke fuska take yi cikin barci, ga shi dai an mata alluran barci, amma har cikin ranta tana jin azaban aikin da ake mata.
Kofar follicle ɗinta ya buɗe tare da zura needle suction tube ɗin ciki, tsotse ruwan dake cikin follicle ɗin nata ya fara yi, follicle ɗin kamar jaka haka yake, ruwa ne da kwan ke zama a cikinsa a cikin jakar, dan haka sai an tsotse ruwan idan ana son kwan.
KAI JAMA'A KU CE ALLAHU AKBAR, billahil lazi dik wanda bai bi ALLAH ba ya yi asara duniya da lahira, kun san matakan dake akwai kafin ciki ya shiga mahaifar mace? Kun san irin halittar da UBANGIJI yai a cikin mace kuwa? Kai ku kara cewa ALLAHU AKBAR, UBANGIJINMU baya saɓa komai, dikkan likitocin duniya dik kwarewarsu basu isa su gano wani lamari na UBANGIJI da ya tsara a cikin mace ba, shi kansa kwan haihuwa UBANGIJI yai mashi follicle in da zai rayu ya ji daɗi na ɗan lokaci, a haka wasu zasu ce ALLAH bai da adalci? Kai na sake cewa ALLAHU AKBAR, ALLAH buwayi gagara misali!!
Wannan ruwa na cikin follicle shi embryologists watau kwararrun likitocin mahaifanmu su Alhaji Dr James zasu zuƙe su shiga tube na gwaji zuwa laboratory inda zasu nemo kwan a karkashin microscope, to shi dai Dr James ya zuƙe.
A taƙaice karamar tiyata yai mata, ya shiga ovaries ɗinta da wannan karfe ya ciro kwayayyen da ovaries ɗinta suka saki, kwayaye sun kai 10 a cikin wannan ruwa ya kwaso, sai da ya kwashe tas, sannan ya zaro bututun da gabaɗaya ya yi wanka da jininta. A cikin wani karamin kwalba ya zuba kwayayyen haihuwar da ruwan tata tare da sanya hannu ya ɗauko audiga bayan ya rufe kwalbar, a gaban nata ya sanya audigar dan tsotse jinin da ya biyo baya kasancewarta virgin.
Daga haka ya ɗan haɗe mata kafafunta waje guda kafin ya matsa zuwa gado na gaba, ya gama da nata aikin, kwayayyen kuma suna barinsa a wajen gadon kowace da suka cire mata har sai sun kammala cire masu dikka, sannan su tattare kwayayye su wuce da su.
Haka suka bi dikka yaran dake kan gadon suka masu wannan azabben tiyatan suka ciro kwayayyen haihuwarsu, abin mamakin kuma kowacce yarinya kwai sama da 10 suke cirowa daga jikinta, a ƙaida kuma mace tana sakin kwai guda ɗaya ne a wata, sai waɗan da ALLAH ya kaddara suna da rabon samun twins sai su saki kwai biyu, haka masu rabon samun ƴan uku, to amma ya aka yi waɗan nan yara suka bada kwai sama da 10 a lokaci guda? Abin da mamaki gaskiya.
Amma ni bari in yi maku bayani yadda zaku fi ganewa. A jikin mace akwai ovaries, a hausa kamar ace ƙwanƙwason mace kenan, to ovaris side guda biyu ne ai, ciki ya raba kenan, ki duba a jikinki akwai wata ƙashi dake ta gefen ciki wajen kwankwaso ko?
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 95