Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taki tasowa ta ci abincin. Daga karshe dole suka kyaleta, dan sun san hali. Fitowa Angelina ta yi hannunta rike da abincinta, ta nufi in da matasan sojojin nan suke zazzaune, daidai lokacin Zaynish and Vash suka iso wajen. Sai kallon Zaynish Angelina take yi, amma shi bai san da zamanta ma a wajen ba, yana zuwa yai zamansa a kusa da wutar tare da fito da wayansa, take sojojin wajen dik suka miƙe suka sara mashi har ita Angelina ɗin, sai da ya jinjina masu kai sannan suka koma suka zauna. Wayansa Zaynish ya ya ɗan fara latsawa, da alama shi fa su Angelina basu mashi bama, ba ruwansa da su. Ya mayar da hankali kan abinda yake yi kawai, a daidai lokacin Aunty Ummi ta kirasa, miƙewa yai ya bar wajen, bayansa Angelina ta bi da kallo, sai magana Unays yake yi mata amma bata tanka ba, cikin sanyin murya ya ce. "Nai maki message baki mun reply ba". Ƙasa ta yi da kai, a ɗan daƙike ta amsa da. "Banga saƙon bane"...... Nisawa ya yi tare da ƙara matsawa kusa da ita, ya fara janta da hira, ƙasa ta yi da kai, bata ƙara bi ta kansa ba ta hau cin abincinta a natse. A can gefe kuwa, Leo da Noor ne zaune a cikin ɗakinsu suna cin abinci, Noor ya ce. "Bro zan je in ɗauki Juliet ɗita, ba zan iya cigaba da fushi ba"........ Abinci Leo ya ɗebo a spoon mai zafi sosai ya dannawa Noor ɗin a cikin baki ba tare da ya yi magana. Da sauri Noor ya fito da abincin yana buɗe bakin ta sha iska saboda zafi, akwai zafi sosai, ta ƙona mashi baki matuƙa. A ƙule ya ce. "Yau mugunta kake ji da shi ne?"....... Ɗebo wani abincin Leo ya sake yi, ya shammacesa yana magana ya sake danna mashi a baki. Ai a miliyan Noor ya miƙe yana tufo da abincin waje saboda zafi. Da sauri ya dunƙule hannu zai kai wa Leo ɗin punch a kumatu Leo ya damki hannun nasa tare da ture plate na abincin gabansa, ya jawosa Noor ya faɗo jikinsa, yana ƙoƙarin damke wuyan Noor ɗin. Noor ya juya ya rungumesa yana faɗin. "Wai ni yau me nai maka ne?". Shiru Leo bai yi magana ba, ya janye Noor daga jikinsa kawai yana ja mashi coily hair ɗin nan nasa. Wasa suka ɗan taɓa gwanin burgewa kafin Noor ya kwanto da kansa a kan laps na Leo yana faɗin. "Bro me na yi maka yau kuma?". "Babu abin da ka mun, kawai ina son gwada maka ne, yadda ka ji wannan zafin abincin nan haka mace take, ka kiyaye"........ Awwa sai yanzu Noor ya gane karatun, ya ALLAH, watau Leo ba zai canza ba, halinsa ɗaya da yayansa Lion, wai a haka ma fa Leo bai san tarihin iyayensu da irin cin amanar da ya faru ba, da ya sani kam ban dan me zai faru ba. Miƙewa Noor ya yi yana faɗin. "Sauran mata ne suke saka mutu a zafi tamkar wuta, but my Juliet daban take da sauran mata, bari ma in je in ganta, goodnight bro"....... Da ido kawai Leo ya bisa ba tare da ya yi magana ba, miƙewa tsaye ya yi, har zai fita kuma sai ya ɗan dakata tare da juyowa. A kusa da Leo ya tsaya, a kunne ya raɗa mashi cewa. "Kada ku nemeni, kuma kada ku zo mun ɗauki, yau ni da matata zamu kwana, yau zan yi dis virgin ɗinta, bye bro". Yana kai karshe ya miƙe da sauri yana ja baya, dan yasan sai Leo ya kai mashi duka ko damƙa. Harara Leo ya bisa da shi, sai kuma ya sauke idanunsa ƙasa bai yi magana ba. Wucewa Noor ya yi ya fice waje. Kai tsaye tantinsu Arya ya shiga, yana shiga V dake kwance ta ɗago kai, ta ji kamshin perfume ɗinsa, Arya na zaune gaban laptop tana cin abinci. Tabbatarwa da cewa shi ne yasa ta miƙe zaune a tsakiyar mattress ɗin. Muryarta a dishashe ta ce. "My Romeo". Bai yi magana ba, ya iso dab ita, hannu yasa ya ɗauketa cak, da sauri ta saƙalo wuyansa tana kwantar da kanta a gefen kirjinsa. Bai ce da Arya ko uppan ba ya fito waje da V, kai tsaye cikin tantinsa ya shige da ita. Bai direta a ko'ina ba sai a saman mattress ɗinsa, ya sauƙeta game da yunkurawa zai miƙe ya sauƙa. Da sauri ta riko damtsen hannunsa, muryarta a raunace ta ce. "I'm so so sorry my Romeo, ba zan sake ba, na tuba"........ Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali. Can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "To sakeni"......... Sake shi ɗin ta yi tare da kwanciya a saman mattress ɗin, ta fashe da sabon kuka. Miƙewa ya yi, ya cire uniform ɗinsa, ya rage daga shi sai shorts guntu wanda bai kai tsakiyar cinya ba, ga shi short ɗin ta matse shi sosai.......... Saman gadon ya dawo, yasa hannu ya ɗagota gabaɗaya ya rungume, sosai take ta faman shessheƙa, in a cool way sosai ya ce. "Ke baki san ke matata bace da zaki ce voice na wani is so sweet? Baki san cewa voice ɗina kawai zaki ji ki yaba ba? Kin manta ina sonki ne? Kin manta zan ji zafin in kika yabi wani ne?". Cikin muryan kuka ta rungumesa taigtly kafin ta ce. "Sorry my Romeo it was a mistake, ba zan sake ba"....... Kai ya jinjina. "Is okay to, for now I forgive you, but in kika sake, you will lose my control and my happiness"...... Ƙara ƙanƙame shi ta yi tana ƙara ce mashi sorry. Ɗago face ɗinta ya yi, ya haɗe fuskokinsu kafin ya haɗe bakinsu, ya fara bata hot kiss mai narka zuciya, ai ƙara shigewa jikinsa ta yi, ta fara shafesa tana turo mashi kirjinta, a gefe guda tana shessheƙa. Ai kwantar da ita ya yi, ya mata runfa da buɗaɗɗiyar kirjinsa, ya fara moving hands ɗinsa a jikinta, cikin salo ya fara ɓalle mata botiran sleeping dress ɗinta. Ita kuwa ta ɗaura hannayenta a saman bayansa, tana yin sama da su, slowly ta dawo da shi ta gaba, kai tsaye ta damki magicstick ɗinsa. Ƴar ƙara ya saka mata kafin ya fara bata komai cikin zafa, dan ta kunna shi ne......... Romancing ɗinta sosai ya yi, ya rabata da kayanta dikka, daga ita har shi suka manta da a filin daga fa suke, yaki suka fito, ko da yake dama su basu ɗauki rayukansu a bakin komai ba, already sun sa a ransu mutuwa zasu yi anytime. In a romantic way ya dinga binta da love and sexy words, ya ɗauke mata hankali kafin ya yi yunkurin shigarta, ko me ya tina kuma sai ya fasa, ya kwanto jikinta yana mayar da numfashi, yana jin tamkar ana buga mashi guduma a tsakiyar kai. Hannu tasa tana ɗan bubbuga bayansa kamar mai rarrashinsa, tana jin bugun zuciyansa na tsanantawa. Shiru ya kwanta a jikinta, after like 10 mins, slowly ya miƙe, ya sauƙo ƙasa, kayansa ya mayar jikinsa tare da matsowa bakin mattress ɗin, ya tsuguna a gabanta, in a cool way ya ce. "I'm coming, ki yi barci, yau a tare zamu kwana". Yana kai karshe ya miƙe ya fita. Yana fita bai zame ko'ina ba sai ta bayan tantunansu, a nan ya isko Leo, Zaynish, Vash suna tsaye, wayar hannunsa ya duba time 11 na dare ya yi, gaba Leo ya yi, suka rufa mashi baya, dik cikinsu Vash ne kawai yake rike da bindiga, su kam banda ƙananan wuƙaƙen dake jikin takalmarsu na aiki babu abin da suka ɗauka sai torchlight ɗinsu mai bala'in hasken nan. Cikin tsakiyar dokar daji suka kutsa ba tare da sanin kowa ba, suna tafiya suna tattaunawa kan aikin da zasu je yi, ma'ana aikin da ya fitar dasu a daren nan. A can kuwa sauran sojojinsu suna zaune bakin wuta suna ta hira, while Arya na ta kokarin ganin ta yi aiki tuƙuru, Angelina ma ta dawo ta kunna laptop ɗinta tana duba gabas da dajin, dik da cikin duhu ne tana sauraran sauti da motsi, while Manassa na kwance rike da waya tana zubawa Vash tsiya, dan shi ma suna tafiya yana dannar waya ne, sai hakuri yake baiwa aljanarsa da ta ce zata kashe Manassa da ya kula. Dik ya tashi hankalinsa, ya dinga bata hakuri, har da cewa shi tai mashi dik abin da zata yi mashi, amma ta kyale Manassa bata san komai ba, ita kuwa ta kafe lallai sai ta nakasa Manassa. V dai tana tantin Romeo ɗinta kwance tana tinanin love moment da suka sha, dik ya tashi kanta da salonsa, idan ta tina his soft lips, his romance, his sexy words, ya rabb, sai ta jita a wata duniya na daban. Shi kuwa Unays ya zage sai ya kafa gwamnatinsa a zuciyar Angelina, sai tashin kanta da love words yake yi, ita kuwa tana can tana tinanin yadda zata samu even contact ɗin Zaynish ne. Uhm akwai dirama. CRYSTAL PALACE. 4:30 na washegarin ranar da Abba ya kai sadaki, ranar Alhamis kenan. Zaune familyn Khaiza'an's suke a parlo, Faryan, Harleen, sai kuma Rimsha dake zaune kusa da Faryan ta tada kai da cinyansa tana chatting da Seraphina, suna ta hira kan school, yau sun mayar da hankali kan hirar karatu ne ba hirar shirme ba, Rimsha tana son jan Seraphima ta musulunta, tana bata tarihin Annabi Muhammad (SAW) Faryan yana latsa nashi wayan shi ma suna chat da Seraphina, dan bai hakura ba kuma ba zai hakura ba, while Harleen yana aiki a laptop ɗinsa, kun san Harleen pilot ne, matuƙin jirgin sama. Abba baya nan, sun fita da Aryan, ƙafa ta matsawa Abba sosai, kun san yana da problem na kafa, sai da aka dasa mashi karafuna, to dama dik karshen wata ana zuwa asibitin ƙashi a duba mashi, wannan wata bai je da wuri ba, kafar ta dame shi shiyasa ya kira Aryan a gaggauce suka tafi, dalilin kenan da yasa kuka gansa yana dogara sanda, matsalar kafa ce. Knocking na door aka yi, hakan yasa Rimsha ta mike, a tinaninta su Abba ne ya dawo, ta nufi jikin door ɗin, ba tare da ta duba camerar door ɗin ba ta sanya fingerprint ɗinta, kofar ta buɗe. Tana buɗewa sai ga kaki sun shigo cikin parlon, ƴan sanda ne su biyar, a gaba ACP ne da sauran yaransa. Razana Rimsha ta yi, da gudu ta juya ta koma ciki tana faɗin. "Uncle Faryan police". Wannan magana da ta yi karaf a kan kunnen Ammie dake ɗaki tana shan americano, tana zaune saman sofa. Jin Rimsha ta yi kukan sunan ƴan sanda yasata ajiye americanon ta miƙe tsaye, tana sanye cikin arabian dress, ta yi rolling veil a kanta. Ƙasa ta nufi tana ɗan sauri dan ta zo ta gani. Police a gudan Khaiza'an? Abin da ko a mafarki bai taɓa faruwa ba. A tsakiyar parlo ƴan sandan suka tsaya, ACP yana kallonsu Faryan ya ce. "Kai ina Muhammad Khaiza'an yake?"....... Dik cikin parlon babu wanda ya amsa mashi, saboda rashin yi masu sallama da basu yi ba. Cigaba da abin da suke yi suka yi tamkar basu san da halittar ƴan sanda a wajen ba. Wani irin ƙasƙantaccen kallo ACP yai masu kafin ya ce. "Wai ba daku muke magana bane?"....... Ɗago kai Faryan ya yi, ya kalli TV dake magana, a ɗan natse ya ce. "Rimsha rage volume na TV ɗin nan, karen ciki na mana haushi dayawa". Kuma da gaske wani bakin ƙare na haushi a cikin TV ɗin. A tsorace ta miƙe ta je ta rage volume ɗin, shi kuwa Harleen ya ajiye laptop ɗinsa a gefe ya jawo waya ya fara latsawa. Daidai lokacin Ammie ta sauƙo ƙasa. Kallo ɗaya tai wa ƴan sandan ta ɗauke kanta tare da ƙarisawa in da su Faryan suke, ta zauna a saman sofa tana mai da kallonta a kan Rimsha da jikinta ke ta faman kermar tsoro. "Ku wasu irin dabbobi ne? Baku ji ana magana ne? Kuna wasa da wuta ko? Hukuma ce a gabanku!!". ACP ya faɗa a kadarance. Ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya Faryan ya yi, ya jawo Rimsha jikinsa yana faɗin. "Baby zo ki ga me kawarki ta rubuta mun, wai tana sona saboda ina kama da daddynta". Ya faɗa yana murmushi. Rimsha dai hankalinta sam bai kwanta ba, tana tsorace da ƴan sandan nan, kallon wayar kawai take yi, amma hankalinta baya jikinta, hasalima bata ga me Seraphina ɗin ta rubuta ba. Wani irin tsawa ACP ya daka masu. "Ku dabbobin ina ne nace? Kun san zan iya jefaku a cell ko?".......... Jikin Rimsha ne ya tsananta kerma, ta ƙara ƙanƙame Farya. Ammie ce ta ce. "Faryan naga alamar wannan Seraphina ɗin tana burgeka, ka fara biyewa Rimsha ko?". Murmushi Faryan ya yi. "Ammie yarinyar ta haɗu fa, kin ganta kuwa, kamar ki sace ki ajiye ki yi ta kallo, kyakkyawar gaske ce"........ Cikin zolaya Ammie ta ce. "To ya tsaya a iya haka dai, kada ka bari Abbanka ya jika"...... Gabaɗaya Khaiza'an's family sun mance da wasu ƴan sanda, sun baiwa banza ajiyarsu. A fusace ACP ya sake cewa. "Lallai dikkanku sai kun yi danasanin wannan abin fa kuka aikata!"...…... Miƙewa Faryan ya yi, ya nufi kitchen yana faɗin. "Ammie bari in duba idan waɗan nan robot ɗin sun kammala abinci". "Faryan zo mun da ruwa mai sanyi". Harleen ya faɗa yana ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ya cigaba da dannar waya. Watau idan kana neman shahararrun ƴan rainin wayau to ka zo gidan Abba, takaici ne zai kasheka. "Rimsha je ki ɗauki mun Americano na da na baro a ɗaki in karisa shanyewa". Ammie ta faɗa tana kallon Rimsha da tsoro ya gama cikata, dan dik family Abba ita kaɗai ce matsoraciya. Gagara miƙewa ta yi, ta kankame Faryan da ya dawo ya zauna a kusa da ita yanzu yana miƙawa Harleen ruwan da ya ɗauko mashi. Riko hannunta Faryan ya yi, tamkar zata yi kuka can ƙasa ta ce. "Uncle, I'm very scared"......... Ƙasa sosai yai da murya wajen cewa. "Don't fear anyone except ALLAH, get up and go bring what Ammie sent you to get". Da gudu ta miƙe ta nufi sama tana waigo ƴan'sandan da suka yi kasaƙe suna ganin ikon God...... Harleen ne ya ce. "Kai Faryan kara gudun Ac ɗin nan ka zo mun da small chop". Ai a ƙule ACP ya ce. "Me kuka ɗauki kanku ne ahalin Khaiza'an? Dame kuke taƙama ne?"....... Dik cikin parlon babu wanda ya ɗago ya kallesu bare su tankasu, sai ma cewa Harleen yai. "Faryan zo mun da bluetooth". Watau ya toshe kunne kada su dame shi. Ɗaya daga cikin ƴan'sandan dake baya ACP ne ya ce. "Kufito mana da Muhammad Khaiza'an, shi muka zo tafiya da, in kuma baku fito da shi ba zamu bincike gidan gabaɗaya, kuma ba zamu ragawa kowannenku ba, dik zaku tsinci kanku a bayan kanta!". In a harsh way ya faɗa yana wani zazzare masu ido, bai san nan gidan dik tantirancinka sun fika iyawa ba, kuma su ba duka ba zagi, kai bama magana zasu sanya zuciyarka bugawa ne. "Wai ba daku muke magana bane?!!". ACP ya faɗa cikin ɗaga murya wanda ya sanya Rimsha dake sauƙowa yanzu ta razana ta saki plate and cup na hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse, Americanon ya malale a ƙasa. Jikinta na rawa ta ɗago da kai ta sauke kallonta a kan mugun watau Harleen, dan tasan ko kowa bai yi mata magana ba shi sai ya yi saboda bala'insa daban ne a gidan nan bayan Aryan. Ga mamakinta sai ta ga ya harareta ya ɗauke kai bai yi magana ba, take ta haɗiyi yawu gwad jikinta na ɗan kerma. Tana ƙoƙarin raɓawa gefen glass ɗin ta isa wajen Faryan ACP ya damki hannunta tare da sanya mata pistol gun ɗinsa a forehead ɗinta, a dake ya ce. "Ku fito da Khaiza'an ko in fasa kanta!!". Wai irin zai razanasun nan. Miƙewa Ammie ta yi tana faɗin. "Ku kawo mopper a goge Americanon nan, sannan ku zo da tsintsiya dan kwashe glass ɗin, Faryan bari in ɗan kwanta in huta". Ta kai karshen maganar tare da nufar sama, ta raɓa gefen ACP ta yi wucewarta........... Saura kaɗan Rimsha ta saki fitsari a wando saboda tashin hankali, jikinta ya tsananta kerma, kallonta a kan Uncle Faryan dake girgiza mata kai alamar kada ta tsorata. Harleen kuwa ko a jikinsa yana cigaba da cin small shop da Faryan ya shigo mashi da shi, suka baiwa bansa ajiyar su ACP, kuma ga shi su ACP ɗin suna shakkar shiga cikin ɗakunan gidan su duba ko Abba yana nan, su da kansu sun san da wuya idan Abba yana gidan, amma sun jajirce sai Khaiza'an's family sun kulasu. Ganin babu sarki sai ALLAH ne yasa suka ce zasu tafi da Rimsha, idan har suna sonta Khaiza'an ya kawo kansa station. Still dai babu wanda ya kulasu, ACP ya kamata suka nufi waje. Take ta fara kuka hawaye bibbiyu. Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga motar Aryan ya danno kai, sun dawo da Abba, an je an gyarawa Abban karafunan kafafun nasa. Tin Aryan bai gama parking ba Abba yasa hannu zai buɗe kofar motar saboda ganin Rimsha a hannun ƴan'sanda ya ɗaga mashi hankali. "Abbaaaaaa......" Aryan ya faɗa yan jan sunan. Harara Abba ya dalla mashi kafin ya buɗe mota ya fita, da alama har yanzu bai huce ba, Aryan kuma babu alamar zai karɓi wannan umarni, ba zai yarda ya auri Aunty Lusi ba. Fitowa Abba ya yi, yana dogara sandarsa ya isa gaban ACP. Da karfi Rimsha ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta nufi Abba, amma ACP ya ƙanƙameta, bai saketa ba. Lokaci guda kuma ya saketa a razane yana kallon Aryan dake tinkarosu tamkar wani zaki, gabaɗayansu babu wanda hantar cikinsa bai kaɗa ba, ACP har da haɗiyar wani yawu da karfi gwad. Da gudu Rimsha ta nufi Abba, tana zuwa ta faɗa jikinsa, riketa ya yi yana cigaba da kallon ƴan sandan. "Me haɗinku da jikata? Me tai maku zaku kamata?". Abba ya tambaya...... Da kyar ACP ya saita natsuwansa game da ɗauke kallonsa daga kan Aryan dake gab da ƙarisosu kafin ya ce. "Lush family ne suka shigar da ƙara a kan Khaiza'an, batu ne na cin zarafin ɗan adam, ka tilasta masu yin abin da basa so, ka kawo kuɗi ka basu dan kasayesu, cin hanci kenan, kasan kuma corruption haramun ne a ƙasar nan"..….. Abba ya gane karatun, watau grandpa ɗinsu Noor ne da wannan ɗanyen aiki. A daidai lokacin Aryan ya ƙariso wajen, fuskansan nan tamau babu alamar wasa, a dake ya ce. "A yaushe CRYSTAL PALACE ta yi lalacewar da ƴan sanda zasu iya shigowa cikinta?!"...... Shiru ƴan sandan suka yi, dan sun san ba kai tsaye suka shigo da nufin kama wasu ba, sun yi wa jami'an dake bakin main gate karyar cewa ziyara zasu kaiwa ɗan uwansu a Lush family, shi ne suka samu hanyar shigowa, dan jami'an bakin gate sun duba number Lush family dake jikin littafin CRYSTAL PALACE ɗin, sun kira table phone nasu, suna tambayi cewa suna da baƙi kala kaza ne? Dama grandpa ne ya ɗauki wayan, sai ya ce e suna da baki, shi ne fa suka basu hanya bayan sun cajesu basu ɗauke da komai sai bindigar aiki. A tsarin CRYSTAL PALACE da yanayin tsaronta babu wani jami'in da ya isa shiga cikinta ya kama wani, babu wannan mahaluƙin, idan akwai mai laifi a cikinta to sai dai a tuntuɓi jami'an dake tsaron CRYSTAL PALACE ɗin, su da kansu zasu yi bincike, idan ya tabbata mai laifi ne, da kansu zaku kama shi, idan kotu ne su miƙa shi kotun dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, idan hukunci ya dace da shi su zasu yanke mashi, shiyasa na ce maku manyan kai ne ke zama a cikin CRYSTAL PALACE, akwai tsaro, dokoki da ƙaidoji, babu wani abin da ya isa zama barazana ga mutanen ciki, karfin ikon CRYSTAL PALACE ya zarce yadda kuke tinani. Tsuru-tsuru ƴan sandan suka yi. Aryan ya daka masu tsawa, hakan yasa ACP ya ce. "Dama Lush family ne suka shigar da ƙasa kan Khaiza'an, shi ne muka zo tafiya da shi.......". Bai iya ƙarisa maganar ba sakamakon gigitaccen marin da Aryan ya ɗaukesa da shi, wai Abba aka zo kamawa. In a harsh way Aryan ya ce. "Ba'ayi mahaluƙin da zai iya taka gidan Khaiza'an da suna kama shi ba!". Da farko Aryan ya so nuna masu ID card ɗinsa na SSO, sai kuma ya fasa, dan basu kai ya tsaya nuna masu waye shi ba, gara ya jibgesu ba'a matsayi nagaba da su a wajen aiki ba, su rubuta a tarihinsu farin kaya ya jibgesu. Abba sarkin izza, aikuwa ya ce Aryan ya ƙara masu, dan shi an walaƙanta shi da har ƴan sanda suka shiga gidansa. Kallon Abba Aryan ya yi. "Abba ka je ciki kawai". A tausashe ya faɗa...... Hannun Rimsha Abba ya riko suna nufi elevator yana faɗin kada Aryan ya raga masu, ya masu hukuncin da gobe ko sunan Khaiza'an suka ji sai sun saki fitsari a wando. Shi kuwa Aryan Abba na shiga ciki ya ɗauki waya da nufin ya kira jami'an SSO dake benensu, sai ya ga wayar Lion ce a hannunsa, ya ɗan yi mamaki, sai can ya tina ashe ɗazun da ya kwanta jikin Lion suna hira wayoyinsu na haɗe waje guda, da ya tashi ne ya manta ya ɗauki na Lion kenan, dama wayoyin iri ɗaya babu abin da ya rabasu, sai ka kunna hasken wayar zaka ga wallpaper kowa da kalar tasa. Kiran jami'an ya yi, ya ce su zo su wuce mashi da ƴan sandan nan, su ajiyesu zuwa dare zai nemesu. Bai faɗawa jami'an SSO ga in da yake ba, ƙasa da minti biyu sai gasu sun yi diran mikiya a wajen, suka wuce da su, su ACP idanu ya raina fata, ga shi yana tsoron ɗaga murya kada ya jawa kansa, dan jami'an dake tsaron CRYSTAL PALACE gabaɗaya jami'an SSO ne, amma ba kowa yasan hakan ba, saboda kada ku manta jami'an sirri ne. And yasan dokar CRYSTAL PALACE, ya yi wa jami'an karya ya samu ketowa ciki, idan ya ɗaga murya zai ji a jikinsa ne. Gara ya yi shiru kawai...... A yayin da dikka wannan abin yake faruwa ita kuwa Seraphina tana can cikin ɗakin Mom ɗinta, ta tada kai da cinyar Madam, Madam ɗin tana gyara mata kyakkyawan silky ash hair ɗinta, tana rike da waya, suna hira da Madam tana ɗan dube-dube a wayar. Madam ta ce mata. "Baby daddy baki jin magana, kullum sai na ja maki kunne a kan kada ki dinga irin waɗan nan maganganu da daddynki amma baki ji ko?"...... Ta faɗawa Madam dik yadda suka yi da Aryan jiya ne, shi ne Madam take mata faɗa, ta nuna mata illar maganganun, ta kuma gwada mata cewa da kunya aka san mace, tai mata faɗa sosai fa, kuma ta yi alkawarin ba zata sake ba. Cikin shagwaɓa ta ce. "Yauwa mom, kin tina mun, yau tin safe ma daddy bai zo ba, har na je school na dawo, sai wani katon mutumi ya turo wai ya kaimu schy, ga shi na dawo bai zo ba, bari in kirasa video call". Ta faɗa tana turo baki, yau Aryan bai zo ya kaita asibiti ba, ya je amsa kiran Abba har suka tafi hospital, sai dai ya turo ɗaya daga cikin jami'an SSO ya zo ya kaita, kuma ya dawo da ita a lokacin tashi. Madam zata yi magana sai ta ga Seraphina ta danna video call tana murmushi, ɗan kawar da fuskarta Madam ta yi tana faɗin. "Ki dai natsu, kada ki yi wa daddy shirme, ki mashi magana a kame cikin natsuwa". Da okey ta amsa........ A daidai lokacin kiran ya shigo wayan Aryan, jawo wayar Lion dake kwance saman bed ya yi, a tinaninsa wayansa ne, ganin video call yasa ya ɗan yi mamaki, sai kuma ya zaci ko Leo ne, amma sai ya ga an yi saving

Chapter 68 of 95