Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a gaban class ɗin nasu hannunsa rike da wata katuwar littafi. Fuskansa babu alamar annuri ko wasa, a saman table dake kusa da smartboard ya ajiye takardan hannunsa, yana sanye da kaki a jikinsa. Rubutu ya ɗan yi a smartboard ɗin da makar kamar haka FIREARMS kafin ya juyo ya kallesu, while dik shi suke kallo. Dikkansu sun fitar da note books ɗinsu, a natse cikin kakkaifar voice ya fara da faɗin. "Firearms, watau rabe-raben makamai, yau zamu fara ne da rabe-raben makamai kafin ku san menene makaman na gaske". Ya ɗan dakata yana rarraba idanu a kansu kafin ya cigaba da cewa. "Bindigogi sun rabu rukuni 5 ne, na farko akwai pistols, watau ƙananan bindigogi waɗan da za'a iya rikewa da hannu ɗaya, sannan ana amfani da su ne daga kusa. Misalan pistols akwai glock 17, beretta M9, colt m1911, SIG sauer P226, jimilla nau'ikan kala 10 na pistols gun". Dafe kai Noor ya yi, a ransa ya ce. "Da sunan waɗan nan makamai kawai idan aka barka sai su kasheka ko ka shiga doguwar suma, kana jin wasu sunaye tamkar na horori wai bindigu, ni dai na shiga uku tin da na shigo aikin soja!". A fili kuwa ya mayar da hankalinsa kan sauraron Captain Onbish da abin da yake faɗe. Leo, Zaynash and Unays sun natsu sosai karatun yana shiga kansu, saboda sun sanya a ransu zasu zama manyan sojoji masu ji da lafiya dan bawa duniya gabaɗaya tsaro su kori ƴan ta'adda, sun yi alkawarin a dik ranar da suka sanya kaki mai ƴanci, ma'ana suka tsallake horo suka zama sojoji, to tabbas ba za'a sake samun wani ɗan ta'adda a duniya ba kasarsu kawai ba, wannan alƙawari ne suka ɗaukarwa kansu. SHIN WANNAN ALKAWARI NASU ZAI CIKA? ZASU YI NASARAR TSALLAKE HORO SU ZAMA SOJOJI?. Cigaba Captain ya yi da cewa. "Na biyu akwai rifles, bindigogi masu dogon murfi, ana amfani da su daga nesa, kuma suna da ƙarfi da daidaito sosai. Suna da nau'ika kamar haka, bolt-Action rifles, kamar mosin-nagant, kar98k, sai semi-automatic rifles, kamar m1 garand, SKS, da kuma assault rifles, kamar AK-47, M16, FN SCAR, G36, F2000, suna da nau'ikandai fiye da 30, amma ana koyar da nau'i 10 zuwa 12 a wannan Barrack ɗin, ba'a cika amfani da sauran nau'ikan ba". (Sai ga jami'ai na musamman ake koya sauran nau'ikan, misali idan suka gama karɓar horo, yanzu haka manyansu suna nan suna kula da dik wani motsinsu, idan suka kammala aiki za'a zaƙulo jarumai kuma ƴan baiwa, sai a sake basu horon da a nan ne zasu zama manyan jami'ai na sirri dana ambata maku a farko, za'a koya masu harbi na musamman wanda ko a ina ne a faɗin duniya komai nisan da suke zasu iya saita mutum su yi harbi kai tsaye.) Ya ɗan dakata ya basu 2 mins suka rubuta abin da yake karanta masu, dan shi ma yana bayani yana ɗan kara rubutawa ne. "Na uku muna da machine guns, bindigogi masu harbi da yawa a lokaci guda, ana amfani da su wajen mamaye wuri, suna harba bullets da yawa a lokaci ɗaya. Sannan suna da nau'ika kamar haka, akwai light machine guns (LMG) RPK, M249 SAW sai general purpose MGs PKM, FN MAG, akwai heavy MGs DShK, browning M2 .50 Cal, suma sun kai kala 10". Nan ma ya ɗan dakata ya basu damar rubuta wannan karatun kafin ya cigaba da cewa. "Na huɗu muna da shotguns, watau bindiga mai fashewar bullets, suna amfani da pellets ko slug, masu amfani daga kusa. Misali remington 870, mossberg 500, benelli M4, winchester model 1897, a taƙaice irinsu 6 zuwa 10 ne kawai da aka fi sani". "A karshe muna da sniper rifles, bindigar kwantena masu harbin nesa, suna da tsawo da ƙwarewar harbi daga nesa sosai, misalinsu akwai dragunov SVD, barrett M82 .50 cal, M24 sniper weapon system, L96A1, cheyTac M200, su 8 ne zuwa 12 da aka fi amfani da su". "Amma akwai sauran makamai masu harbi irinsu submachine guns SMG kamar MP5, Uzi, PPSh-41, grenade launchers, kamar M203, GP-25, Rocket launchers, RPG-7, AT4, anti-material rifles, NTW-20, denel mechem, flamethrowers, kaɗan ake amfani da su yanzu, kamar M2. nau'ukan bindigogin, a taƙaice gasu kamar haka pistols 10, rifles duk nau'i 30, machine guns 10, shotguns 8, snipers10, gabaɗaya sama da 80 zuwa100 na nau'i bindigogi ake koyarwa a aji na nan GIDAN SOJA, amma ana mayar da hankali kan 25–30 na asali ne wanda kuma shi ne kuma zaku fi mayar da hankali, yau ku rike na'ikan da na faɗa maku, gobe zamu fara duba ne daga kan menene pistols gun da yadda suke, yadda ake amfani da su!". Ya dakata yana sauke numfashi a hankali. Shi dai Noor gabaɗaya sunan makaman ma kawai sun hargitsa mashi lissafin ƙwaƙwalwa ne, wai sunan makaman kawai ma ai sai su sa mutum ya mutu da ransa, dan haka shi wlh ragonta zai dinga nuna masu har a gama horon ya fito bai samu result ba ko za'a barshi ya koma gida. Cike da wannan tinani a ransa har suka kammala class, suka tashi around 1 na rana, a nan ne kuma musulman cikinsu suka nufi masallaci dan yin sallah. Bayan sun fito daga sallah suka wuce hall ɗin cin abinci dan yin lunch. Kamar dai ɗazu group-group suka zauna kowane da ƴan ɗakinsu suka ci abincin su, sannan aka basu hutun 30 minutes kamar ɗazu. Dik wani motsin matasan sojojin nan a kan idanun manyansu suke yi, kun san meyasa ake saka masu ido sosai?. Saboda a yanzu ne ake zaƙulo sojijin ɓangare na musamman, a yanzu ne ake ciro sojoji masu kaifin barisa, suna lura da su ne dan su ga su waye suka fi kaifin basira ta yadda ko sun kammala horo za'a sake basu horo na musamman na sirri dan zama zakwaƙuran kuma su kasance masu iya gano mai laifi da kallo ɗaya, shiyasa ake saka masu ido sosai a wannan lokaci. Karfe 2:30 Captain ya umarcesu da su tsaya bisa tsari, sannan su yi tafiya a kan tsari izuwa wani katafaren fili mai girman gaske wanda shi ma a cikin GIDAN SOJAN yake. Bayan sun isa wajen a nan Captain ya fara karantar da su me ake nufi da discipline da ladabi, yadda zasu kasance masu ladabi da girmama manyansu, bin umarni ba tare da gardama ba, tsabtace kaya da gyaran ɗakunansu, tsari a rayuwa, da tsarkin jiki. Ai ya zame masu dole su yi ladabi da tsabta ne ma, idan ba haka ba su gwammaci mutuwa!!. Sun yi wannan horo na discipline har zuwa karfe 4 na yamma, sannan suka wuce masallaci. Bayan sun yi sallah sun dawo suka ɗaura da horon gwajin ƙarfin hannu, ana koya musu yadda ake riƙe makami da ɗagawa ba tare da gajiya ba, amma ba kai tsaye shi aka koya masu ba, domin yau ne ranar farkonsu ko makaman basu gani da ido ba, kawai gwada karfin hannayen nasu aka fara yi ta hanyar haɗa mutane biyu, zasu rike hannun juna, dik wanda ya kwantar da hannun ɗan uwansa shi ya yi nasara, kai da baka yi kokarin ba za'a sake haɗaka da wasu har sau uku, idan baka yi ba yau za'a ɗaga maka kafa tin da ranar farko ce, daga gobe ka sake aka yi winning a kanka zaka karɓi wani horon ne na daban!. Sun yi wannan horo zuwa karfe 5 na yamma, daga nan aka basu hutun 30min, bayan sun huta suka ɗaura da horon daidaito, aka koya musu yadda za su tsaya da ƙafafunsu ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki. Dik horon da suka yi yau Noor shi yake cariying last, kwata-kwata babu alamar zai yi abin arziki a rayuwarsu na matasan sojoji, shi fata ma yake yi a koresa daga school ɗin shiyasa yaki mayar da hankali. Sarai Captain ya lura da shi, kuma da daddynsa ya karɓa mashi Form ɗin ya kawosa ya faɗawa G.A.T a bashi horo na musamman, dan haka shi kuma ya sanar da Captain cewa ya saka ido kan Noor ya tabbatar da cewa horo na musamman ya bashi, daddyn Noor suna da kyakkyawar alaƙa da GAT, Dan haka ya ce kada ya barsa ya yi lalaci dan renon mata ne shi. Da misalin ƙarfe 6 aka basu horon zuciya, karatu da darussa kan jarumta, sadaukarwa, da ƙaunar ƙasa, aka zafafa masu kan batun kaunar kasa da yin komai a kan ƙasa da aikinsu, aka nuna masu cewa rai ba'a bakin komai yake ba, su kashe ko a kashesu, Captain ya zafafa masu cewa karaya ba halin namiji bane, tsoro ba dabi'a bace, jajircewa ita ce mutum, su tsaya tsayin daka dan kare kasa, ko sun mutu ƙasa zata yi alfahari da su. Sosai zafafan kalaman Captain suka fasa zuƙatan dayawa daga ciki, shi kansa Noor ya ɗan ji kamar zai yi aikin, amma idan ya tuna wannan ɗan banzan wahalar da suka sha yau, kuma a haka ma wai ranarsu ta farko ce, yana tuna wannan zai ce kai shi ina, sai ya ji zafafan kalaman Captain sun goge a kansa. Karfe 7 daidai suka tashi daga horon jarumta, Captain ya basu 5mins su yi alwala zuwa masallacin soji. Haka kuwa aka yi, bayan sun yi sallar mangariba da ishai karfe 8 suka haɗu a dinner hall suka yi dinner, karfe 8:30 suka kammala, a nan ne Captain ya umarcesu da kowa ya wuce room ɗinsu, suna da damar yin wanka su kwanta, kada su manta gobe 4:30 na asuba zasu tashi. Daga nan ya hura usir kowa ya nufi room ɗinsa. Noor ya riko shoulder ɗin Vash yana ta faman haki yana nishi sama-sama alamar shi ya yi matuƙar gajiya, shi ma Vash ɗin nishi sama-sama yake sai faman kwaɓe fuska suke yi. Kai tsaye room ɗinsu suka nufa, sai dai kuma suna shiga suka tsaya turus ganin Leo a tsaye a tsakiyar ɗakin hannunsa rike da waist ɗinsa yana kallon wajen da Noor ya ɓata da taɓo ɗazun. Leo ya tsani datti komai ƙanƙantarta, baya zama wajen ƙazanta, wlh idan ya ga ƙazanta a waje ya dinga shirga amai kenan, yana da bala'in kyankyani sosai, zuciyansa ta yi ta tashi idan ya ga ƙazanta. Ganin yana tsaye yana kallon wajen ne yasa Vash and Noor suka ɗan sha jinin jikinsu, shi kuma Zaysh ya wani ɗale kan gadonsa yana ɗaure fuska tamau irin shi ma no respect ɗin nan. Wucewa Noor ya yi zai nufi toilet sanyayyar sexy voice ɗin Leo ya daki dodannin kunnuwansu da cewa. "Come over here". Sosai sun ji shakkarsa, amma Zaynash da ya yake dake ne ya ce. "Yana kiranku ai sai kuzo". Ya faɗa ba tare da ya kalli Leo ba, saboda shakka da tsoronsa, kuma gatse yai masu, ina irin ubanku na kiranku ai sai ku je. Zazzare ido Noor ya yi, da sauri ya saki Vash yana faɗin. "Yanzu zamu goge wajen mancewa na yi"....... Da sauri Vash ya amsa da cewa. "To dama meyasa baka goge ba?". Mamaki ne ya kama Noor, wai ba su suka ce kada ya goge ba ɗazun? Yanzu kuma sun juya mashi baya. Wucewa Vash ya yi da sauri ya nufi wajen bed ɗinsa. Jakansa ya zaro zai kwashi kayan wanka irinsu lotions da soap ya wuce toilet, bai bi ta kan Noor ba, sai da ma ya ciro katon biscuits mai daɗi ya fasa ya ɗan ci rabi, ya mayar da sauran cikin kayan motsa bakinsa, daga nan ya miƙe tare da kwasan kayan amfaninsa ya wuce toilet. Back to their age, Zaysh kamar Leo haka yake 23, Vash bai wuci 22 ba, Noor 20, Amma kansu kusan ɗaya, Leo dai ya fisu tsawo ne, Pamira people suna da tsawo sosai!. Yanzu Noor yagama gane dikkansu suna tsoron Leo, sai ya kudurta a ransa sai ya ƙullah alaƙa da Leo su shaƙu sosai ko dan su Zaysh su daina raina mashi wayau. Mopper room ɗin nasu ya ɗauko, ya zo ya goge ko'ina tsab, ya kara share masu ɗakin kafin ya nufi wajen bed ɗinsa, shiru suka zazzauna cike da al'ajabin farkon ranarsu a GIDAN SOJA, wannan abu ya tsayawa Noor a rai, ba su taɓa zatan haka ba. Ni kuwa na ce abin da baku taɓa zata ba ai yana nan dayawa kuma yana kan hanyar iso ku, GIDAN SOJA ya zarce yadda kuka ɗauka mutanen! har gobe dai inai maku fatan kammala horo lafiya har ku fara aiki!. Suna zaune shiru har Leo ya fito daga wanka sanye da bathrobe white kala mai shegen kyau, ya haɗe kitson kansa waje guda, yana ɗaure da karamar white towel a saman kan nasa, lokaci guda kamahin soap and shower gel ɗinsa ya buɗe ko'ina a cikin ɗakin nasu. Mamaki ne ya kama Noor dake saman bed ɗinsa, a fili ya ce. "Wannan kamshi tamkar na soap ɗin Companynmu". Basu ji me ya faɗa ba, dan haka babu wanda ya tanka shi. A saman bed ɗinsa Leo ya zauna tare da kawo jakarsa, ya fito da lotions na companyn STARS LADIES BODY LUSH. Kayan kamfanin kala biyu ne, na maza ya kasance da sunan STARS BODY LUSH, na mata STARS LADIES BODY LUSH. Fito da su Leo ya yi, a natse ya fara murza mayukan a jikinsa, take kamshinsu ya kara bule ko'ina a ɗaki, kura mashi ido Noor ya yi yana mamakin yadda aka yi kayan kamfanin daddynsa ya shiga duniya har nan. Like wow, yanzu ya yarda da cewa Leo ba karamin kai bane, dan ba kowa ya isa amfani da kayan kamfaninsu ba , saboda balain tsadarta, abu mai kyau da inganci ai dole ta yi tsada!. Robar lotion da Leo yake shafawa a yanzu pic ɗin Noor ne a jiki, dan kyansa yasa su suke yi wa Companynsu tallah, a robar mata hotunan sister ɗinsa ne a jiki, ai na faɗa maku Noor yana da kyakkyawar jiki kamar madara, ga kyan fuska, amma Leo tsabar iskanci bai gane Noor bane a jikin hoton, dan bai taɓa bi ta kan hoton jikin ba!. Suna gani Leo ya kamma shirinsa cikin pj's tsab, ya haye gado ya kwanta, sannan ya jawo littafinsa na nazarin makamai na lacture ɗin da suka yi ɗazun ya fara karantawa, ya sanya Bluetooth a kunne yadda ma kada ya ji wani motsi ko magana. Shiru ɗakin ya yi, suna son yin gulma suna tsoron ya ji su, haka suka yi tsit, daga karshen kowannensu ya tashi ya yi wanka, suka zo suka shirya yare da hayewa gado, kwanciya suka yi suka hau barcin gajiya, jiki dik tsamin wahalar horo, shiyasa suna kwanciya ba jimawa sai barci, amma ban da Zaysh, shi bai rintsa ba, sai da ya bari suka yi barci sannan ya diro ƙasan bed ɗinsa, ya fito da........ Masu tambayata batu kan Dr and ƴarta ku dai kara hakuri, zamu waiwayi wajen a next page In Sha ALLAH, akwai dalilin ɗan janyewa!. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. 3-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________4 Wayarsa kirar Infinix hot 12, wayar ta ɗan sha jiki kaɗan, screen ɗinta ta gefe ta ɗan tsage, amma lafiya lou yana kallo. Sauƙowa kasan bed ɗinsa ya yi, a nan ya fahimci Leo bai yi barci ba, wucewa ya yi ya nufi hanyar toilet... A saman WC ya zauna tare da laluɓo wata number da aka yi saving da my Ummie ya danna kira. Yana yi yana duba time. Bugu ɗaya aka ɗaga, sanyayyar muryar mace ce ta karaɗe kunnensa da cewa. "Bloody sai yanzu ka tina da ni ko?". Da sauri ya hau girgiza mata kai yana faɗin. "A'a Ummie, tin da safe na so kiranki amma ban samu dama ba, mun fita training ne yau"........ Sanyayyar ajiyar zuciya ta sake sauke kafin ta ce. "ALLAH sarki, ka ce kasha wahala kenan?"...... "A'a Ummie, babu wata wahala, ke dai ki cigaba da tayani da addu'a kawai, in fito da kyakkyawar result, in zama babban soja dan kiji daɗin rayuwarki, zan cika maki burinki matuƙa". "In Sha ALLAH ina tayaka da addu'a bloody na, ka kara dagewa ka ji? Ina kewarka sosai".......... "Ni ma ina kewarki sosai Ummie na, ki kula da kanki kin ji?"........ "In Sha ALLAH zan kula, kai ma ka kula, kaga kai kaɗai nike gani in ji daɗi ko? Kai kaɗai ka rage mun a duniya"...... "Haka ne, amma nima ai kin san ke kaɗai ke gareni ko?". "E haka ne". Ta bashi amsa a taƙaice, da alamar barci a voice ɗinta. "To shikenan ina yayana?". Ya faɗa yana gyara zamansa......... "Yayanka yana barci, nima tinaninka ya hanani rintsawa, na damu ina son jin ya ka wuni, na kira layinka sau ba adadi amma baya shiga". "ALLAH sarki, ai na kashe wayar ne dan in samu damar yin abin da yakamata, yanzu dai ki je kin kwanta, sai da safe zamu yi waya tin da kin ji ina lafiya"......... "To shikenan, kada ka manta da alwalar barci da kuma addu'a, sannan ka dinga cin abinci sosai, ka kuma mai da hankali a kan aikinka, kada ka manta da karatun Alqur'ani da littafan addu'oi". Tin da ta fara magana yake jinjina mata kai har ta kai karshe, sannan ya amsa da okey In Sha ALLAH zai yi dik abin da ta ce. Albarka ta sanya mashi daga haka suka yi sallama ya katse kiran. Shiru ya ɗan yi tare da kurawa wayar tasa idanu, can kuma ya shiga gallery ɗinsa, ya fito da wani hoto nasa shi da wata kyakkyawar mace, fara tas mai kyan fuska, sai murmushi take yi cikin hoton, ga ta da dimple mai ɗaukar hankali irin nasa. Shiru Zaynash ya yi yana tinanin mafita a garesa, ya so faɗawa Ummie cewa aikin soja akwai matuƙar wahala, amma ya gagara, dan baya son fara bata wani damuwa daga tafiyarsa, idan kuma bai faɗa mata ba ta ya zai dinga samun kwarin gwiwa? Zai iya idan ba'a karfafa shi kuwa?. Waye Zaynash? Mu ɗan ji tarihinsa kaɗan. Zaynash maraya ne da bashi da uwa kuma bashi da uba, sai yar uwarsa guda ɗaya mai suna Ummie, wacce suka yi waya a yanzu kenan! Ummie ita ta reinesa tin yana karami, mahaifansu sun rasu tin yana da shekaru huɗu a duniya, ita kuma tana da shekaru 13 a lokacin, haka ta renesa, daga cikin ƴan uwa babu wanda ya kula da su, saboda mahaifinsu bai mutu ya bar komai ba sai kangon gida da ko kofa babu da kuma gona, haka Ummie ta juri yunwa na cikinta, ta juri dik wata wahala wajen renonsa, ta shiga kalubale da dama saboda shi, sau uku ana ƙoƙarin keta mata haddi dik saboda neman abincin da zata bashi ya ci a lokacin da yake kukan yunwa. Sun rayu cikin kunci da talauci, ba makarantar boko sai ta islamiya, ita ma islamiyar makocinsu ne mai makarantar yasa ya ɗaukesu kyauta. Sun mai da hankali har Ummie ta haddace Alqur'ani mai girma, kakarsu wacce ta haifi babansu ita ma tana gidan nasu ne, amma da yake ta tsufa sosai sai yazamana bata iya taimaka masu da komai sai dai ma su su taimaka mata, dan haka Ummie ke ciyar da su. Shi kuma Kanin babansu ɗaya tilo a duniya yana can wani gari yana rayuwa, tin da ya tafi neman kuɗi bai dawo ba. To a haka dai suka rayu har Ummie ta zama budurwa. Da yake suna da balain kyau kamar ƴaƴan larabawa hakan yasa samari suka fara tururwar zuwa neman aurenta. A lokacin bata yarda ta kula kowa ba, ta cigaba da karatun islamiyarta har ta zama Ameera a islamiyar tasu, malamin ya ɗauketa tana karantarwa a wajen dik wata yana biyanta kamar 5k a kuɗin Naija. Da wannan 5k ɗin take amfani ta haɗa da ɗan aikatau na mutane da wanki a gida da takewa mutane, ta haɗa kuɗin ta sanya Zaynash makarantar boko dake ɗan babban gari kusa da su, ta ce ya yi karatu zai taimaka masu a rayuwa tin da shi namiji ne. Zaynash yana primary 4 a school uncle ɗinsu kanin babansu ya zo garin ganin gida bayan tsawon shekaru. Ya jajanta halin da suke ciki, ya kuma yaba da ƙoƙari irin na Ummie, daga nan ya ce zai tafi da su birni su yi rayuwa a can. Bai yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukarsu su koma can ba, suna zuwa can kuma wani fitina ta tashi ta tsaya na matarsa, ta ce waɗan nan ƴan kauye ba za su zauna mata a gida ba, an yi juyin duniyar nan taki yarda, a na haka kakansu ta faɗi ta rasu, dalilin kenan da yasa matar tasa ta hakura su Ummie suka zauna, imani ya ɗan shigeta ganin mutuwar tsohuwar a gabanta. Su Ummie sun yi zaman shekara ɗaya a gidan amma cikin rashin daɗi da takura, ga kuntatawa da Auntyn tasu matar kawun nasu take masu, dik ta sallami ƴan aikinta su Ummie suka zama masu mata bauta, sun ci kwakwa matuƙa kafin kanin Auntyn tasu da ya dawo daga bautar ƙasa ya ga Ummie ya ce shi fa ya yi mata, yaga tsantsar kyau, Auntyn tasu ta so hana auren amma ALLAH ya yi sai anyi, Ummie ta auri wannan bawan ALLAH. To shi ma dai ba wani kuɗi yake da shi ba, yawon neman aiki yake yi, ɗan makaranta ne. A lokacin Zaynash ya kammala primary, dan zuwansa babban gari ya cigaba da karatu, uncle ɗinsu ne yake biya mashi kuɗin makaranta. In taƙaice maku labari har yanzu Ummie tana cikin talauci da kunci ga takurar dangin miji musamman wannan Aunty tasu, dik ta shafe mata bakin fenti a family shi ne yasa basa sonta ko kaɗa. A lokacin da Zaynash ya kammala secondary school sai ya ce shi makarantar sojoji zai tafi, ya zaɓi hakan ne kuma bisa ra'ayin Ummie, tana son ya zama babban soja dan kawo karshen ta'addancin dake faruwa, saboda ƴan bindiga ne suka kashe iyayensu, suka shiga har gida suka yi masu rashin mutunci, sannan suka yi garkuwa da su, da ba kuɗin fansa shi ne suka kashesu suka baiwa karnika gawarwakinsu. In kara takaice maku yanzu auren Ummie da mijinta shekara biyu kenan, bata taɓa haihuwa ba, hakan yasa dangin mijin suka kara sakota a gaba, zagi da cin mutunci kala-kala suke yi mata, kannensa da Auntynsu matar uncle ɗinsu sun hanata shan iska, da ta yi magana ace juya bata haihuwa. Dalilin kenan da yasa Zaynash ya kara mai da hankali dan ya zama babban soja ya ga ya fitar da Ummie daga cikin kuncin da take a ciki, yana balain son ƴar uwarsa kamar yadda take mutuwar son shi. Dama da zai zo GIDA SOJA uncle ɗinsa ne ya yi mashi komai, amma sai da ya sayar da gidansu na kauye da konarsu, sannan ya cika ya kawosa nan, dan AZURE ba dik kai ba, makaranta ce na ɗan wane da wane, uncle ɗinsu ya kashe makudan kuɗaɗɗe kafin Zaynash ya samu wannan makaranta, and da kyar Auntynsu ta bari uncle ɗin nasu ya yi mashi komai ɗin, ita kuma Ummie kuɗi kimanin 50k a kuɗin Naija ta bashi, wannan dalilin yasa ya baya son kawo mata abin da zai ɗaga mata hankali, ya yi alkawarin daurewa dan ya ga ya cinwa narasa. Amma fa bai tsammaci haka GIDAN SOJA yake da wahalar gaske ba. A TAKAICE KENAN RAYUWAR ZAYNASH, DAN HAKA DIK YADDA ZAKU GA YANA GASA DA SAURAN YARA DAN YA ZO NA FARKO KADA KU GA LAIFINSA, BURINSA NE HAKAN DAN TSAMO ƳAR UWARSA DAGA WAHALA, SHIYASA YA DAGE!!. -------------------------🔥 Ya jima sosai zaune a wajen

Chapter 6 of 95