barci, kuma shi ya tashi ya sake binsu da tofin addu'a dik da yaki kulasu, can dare around 1 ya tashi ya ɗauro alwala, ya haye kan dadduma ya fara gabatar da sallah, bashi ya sake kwanciya ba sai around 4, ya kwanta zuwa 5 ya tashi ya nufi shirin zuwa masallaci, a tare suke sallar dare kullum, yau sun gaji ne yasa suka kasa tashi, kuma basu yi barci da wuri ba, suna ta hiran yaushe gamo da Vir.
Sai da ya yi shirin sallah ne ya zo ya tashesu, Aryan ne ya fara farkawa, a gaggauce suka shirya suka fita izuwa masallacin cikin CRYSTAL PALACE ɗin.
Bayan idar da sallah sun zauna a masallaci, suka yi karatun Alkur'ani mai girma, suka kuma yi askar, a nan ne Lion ya nemi zaɓin ALLAH kan ya koma gidan daddynsa ne ko kuma ya zauna a gidansa? Ya yi addu'a ya roki zaɓin ALLAH sannan ya barwa ALLAH komai, daga nan suka miƙe suka nufi komawa gida.
A nan ne Aryan ya zame daga cikinsu ya gudu wajen Seraphina. A lokacin da ya shigo room ɗin ya iskota tana ƙoƙarin jan zip na sket ɗin uniform ɗinta ta baya. Hannunta dake rike da zip ɗin ya kama game da ɗan jan sket ɗin sama, ya gyara zura rigarta ciki da suke yi, ya saita waist ɗinta kafin ya ja mata zip ɗin sama.
Nisawa ta ɗan yi game da juyowa tana faɗin. "Good morning my gentle chaos". Tana murmushi ta faɗa....... "Morning my cherry, how's your night?".... "Cool and you daddy?". Hannayenta ya riko game da amsa mata da. "Super cool cherry"........ Tana ɗan murmushin one side ta ce. "Ka ci abincin jiya?". ALLAH sarki soyayya, da wannan zance na yana jin yunwa a ranta ta kwana.
Yatsa ya sanya a dimple ɗinta da ya lotsa kafin ya amsa da. "Yeah, na ci"......... Shiru ta ɗan yi game da ɗan sunkuyar da kai, sai ya ce. "Are you okay?". Ya faɗa yana sake hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta.
"My gentle chaos, ina son tambayarka ne!". A sanyaye ta faɗa.... "Please I'm listening"......... "There was a day da ka ce mun ni kaɗai ce nike baiwa Champion na IRON FIST haƙuri kuma ya haƙura, i asked you who's Champion you didn't answer me, ka canza topic na hiran, and day before yesterday i called your phone, someone picked up, i saw his face, exactly wannan mutumin da ya kashe mun mammyna, daddy, my heart is telling me that you're hiding alot for me, who are you? Where are coming from? Who's that man i saw in your house in my fist day living there?". Babbar magana, watau har guru da ta gani a ranar farkon zamanta a gidansu bata manta da shi ba.
Yanzu Aryan ya gane babban kuskuren da ya tabka, ya manta cewa jinin IRON FIST ce ita, akwai brain, komai ƙanƙantar motsi tana lura da shi, gata dai wani lokaci shirme yai mata yawa, but ko motsi ka yi kusa da ita, zaka ga kamar bata ganka ba, amma kar take kallon komai.
Ganin ya yi shiru ne yasa ta cigaba da cewa. "Your face looks like Rimsha's face, also uncle Faryan, kana kama da shi, i try all my best dan in haɗaku da Rimsha, amma you're running out of her, why daddy? Are they your family?". Watau dik motsinsa a kan su Faryan ma ta tariye komai cikin kanta, ta kuma shirya titsiye shi.
Da yake yasan rauninta, sai ya ce. "Seraphina, you mean daddy yana maki karya? Don't you know that ke matata ce a yanzu? Why zan yi hiding maki some of my life privacy?"....... Shiru ta ɗan yi, tana ƙoƙarin gane me yake nufi da waɗan nan kalamai nasa.
Bai bari ta yi dogon tinani ba bare ta gano raina mata wayau yake son yi, sai ya yi gaggawar sake cewa. "Oh you mean ni mayaudari ne ko? Okey good". Ya faɗa tare da sake hannunta zai juya. Yasan ba zata iya juran irin waɗan nan kalamai nasa ba, ba zata yarda ya yi fushi ba, shiyasa ya ɗaureta ta nan, ai in tasan wata bata san wata ba.
Da sauri ta tari gabansa, muryanta har yana rawa wajen cewa. "Sorry daddy, is not like what you're thinking, kawai baka fahimceni bane, what i mean here is how i called your phone someone picked up, and mutumin da ya kashe mammy na ne, so i wonder yadda aka yi wayanka ya zo hannunsa, then kai da bakinka ka ce ni kaɗai nike baiwa Champion na IRON FIST hakuri kuma ya hakura, to waye Champion? Ina kuma IRON FIST? Kenan ka sansu ne?". A dame ta yi maganar, tana gudun ya ce zai yi fushi ne.
"Okey like that ake tambayar miji abu ko? Baki iya tambaya ba? Wannan zargina kike yi kai tsaye ba tambaya ba, kuma in kina zargina babu aure a tsakaninmu, dan ba'a aure da zargi". Ya faɗa game da raɓawa gefenta zai wuce irin ya yi fushin nan.
Da sauri ta sake tare gabansa, ta riko hannunsa tana faɗin. "Uhmmm uhmmm, daddy..... Daddy..... Daddy, wait mana, sorry please, ba zan sake ba"....... Tamke fuska tamau ya yi. "Go and learn how to talk to your husband sai in sake kulaki". Ya faɗa game da sake yunkurin wucewa ta gefenta..... Turo baki ta yi tare da ƙara ƙanƙame hannunsa, a shagwaɓe ta ce. "Sorry my gentle chaos, ba zan sake ba".
Nisawa ya ɗanyi game da rike hannayenta gam a cikin nasa, cike da kulawa ya ce. "I lose my phone two days back, ina ga shiyasa kika kira wani ya ɗauka, and about champion na IRON FIST, na yi maki kwatance ne da hakan dan ki san kina da kima da daraja a rayuwata, ina sonki sosai, kin san IRON FIST basa karɓar sorry ko a tarihinsu da duniya take da shi, an ce wai in suka kama mutum zasu kashesa ko da sun ce zasu yafe mashi ba ance in ya ce masu sorry suna fasa yafe mashi su kashesa ba?".... Kai ta jinjina tana ƙoƙarin gano ina ya dosa, dik ya gindayar da ita.
"To shi ne nai maki kwatance da IRON FIST ɗin, then about Rimsha, ba yadda ALLAH baya halittar mutum, kin san kowa yana da masu kama da shi guda 9 a duniyar nan, kuma basu haɗa dangi ba, kema kina da naki masu kama dake ɗin, takan iya yiwuwa ALLAH ya haliccemu muna kama da juna ne sosai da su, ni ban sansu ba, ki daina zargin mijinki, ki yarda da shi in ba haka ba aurenmu bai halatta ba".
Shiru ta ɗan yi, tana jin kamar bata gamsu da sauran amsoshin ba, dik ya gindayar da ita, amma amsarsa na cewa ALLAH na halitta mutane biyu iri ɗaya wannan ta yarda da shi, dan bata san addini ba, abin da bata da sani a kai aka sanar da ita karin ilmi take ɗaukar hakan, sai kawai ta rungume shi tana faɗin. "Love you more daddy, ba zan sake abin da na yi ba, for give me?".
Hannunsa ɗaya ya ɗaura a kanta, ɗaya kuma bayanta, yana shafa ash hair ɗinta da ya sha gyara sosai wajen Madam, sai sheƙi da kamshi yake yi ya ce. "Kada ki sake yin wani bincike a kaina, dik abin da baki gane ba just go straight and ask me, zan baki amsa". Yasan halinta sarai, tsab zata ce zata yi bincike a kansa da kan waɗan nan amsoshin da ya bata, shiyasa ya yi saurin taka mata burki.
"Okey daddy, but daddy yaushe zaka kaini tsakiyar teku a cikin jirgin ruwa, mu je garin da rana yake fara fitowa, ya fito a kan idona in gansa?"...... "Very soon zan kaiki, muna yin aure dai zamu tafi honeymoon a cikin tsakiyar teku, daga nan mu wuce garin da rana yake fara fitowa".
Ƙara ƙanƙamesa ta yi, shi kuma ya rage tsawonsa ya ɗauketa cak suka fito parlo, a dining hall ya direta, already an shirya mata breakfast Aisha na zaune tana jiranta, Madam ta haɗa mata wannan daddaɗar kunun alkama mai madarar, ta shirya mata a saman table. A saman chair ya zaunar da ita, da kansa ya zuba mata abincin, ya zauna kusa da ita, ya dinga feeding ɗinta a baki har sai da ya tabbatar ta ƙoshi, sannan ya bata kunun kaɗan, ya ɗauki tissue ya goge mata baki.
Time ya duba a wayansa 7:05, hannunta ya riko suka koma room ɗinta, ya ɗauka mata rucksack ɗinta game da rikota da kyau suka fita waje, Aisha ta rufa masu baya. Kai tsaye ƙasa suka sauƙa, motarsa da ya bari a gidan jiya ya ɗauko, ya juya kan motar game da cewa ta shiga su tafi, da sauri Aisha ta shiga gidan baya. Ita kuma turo baki ta ɗan yi, a shagwaɓe ta ce. "Daddy I am a Queen of your heart, tin da Queen nike ka zo ka buɗe mun door".
Wani irin kallon ƙauna ya bita da shi kafin yasa hannu ya buɗe mata motar, yana buɗewa ta shigo tana ɗan murmushi. Harararta ya ɗan yi kafin ya tada motar su wuce school. Yana parking a school ɗin ya juyo da kallonsa a kanta. "Ayi karatu sosai". Ya faɗa daidai lokacin da Aisha ta ɗauki jakarta ta fice ya basu waje.
"Okey daddy, ka dawo da wuri ka ɗaukeni"........ Harararta ta yi. "Ni driver ɗinki ne?"..... Damke hannun door na motar ta yi kafin ta ce. "Kai bawa nane ai daddy, my driver, ka kawoni kuma ka zo ka ɗaukeni, you're my guard". Ta kai karshe game da jan hannun kofar zata fita da gudu dan kada ya damketa.
Sai dai ina, tana gama faɗa ya danna locks na motar ya rufe. Nan fa kofa taki buɗuwa. Da sauri ta juyo, hannayenta tasa ta kama kunnenta, a shagwaɓe ta ce. "Sorry daddy, wasa nike yi".
Shiru bai yi magana ba, yana dai kallon kyakkyawan face ɗinta, slowly ya matso dab da ita, har suna iya shaƙar numfashin juna. Zazzare mashi idanu ta fara yi, ya ɗan fito da tongue ɗinsa ya lashi soft lips ɗinsa kafin ya ce. "Love you forever and ever my cherry, take good care of yourself, ki yi karatu sosai".
Kai ta jinjina mashi alamar to, bata iya yin magana ba, sumbatar cheek ɗinta ya yi, ta ɗan rintse idanu tana sauke numfashi a hankali. Janye jikinsa baya ya yi ya koma saman kujerarsa, ya buɗe mata motar. Da sauri ta fita tana faɗin. "Love you more daddy, sai ka dawo".
Kai kawai ya jinjina mata game da miƙo mata rucksack ɗinta, ta karɓa tare da wucewa, bayanta ya bi da kallo, imagine kawai yake yi ranar da za'a ce ita matarsa ce, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ransa. Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya tada motar ya nufi gidan Abba.
-------------------------🔥
After sometimes. Tana shiga class ta isko Rimsha ta kifa kai a saman table kamar tana kuka, da sauri ta kariso cikin class ɗin tana ambatar sunanta. Rimsha na jin muryarta ta yi gaggawar ɗago kai game da miƙewa, ta zo da sauri ta rungumeta, a lokacin babu kowa a class ɗin.
Zaunar da ita a saman chair Seraphina ta yi, ta rarrasheta sosai kafin ta tambayeta meyake faruwa, Rimsha bata ɓoye mata komai ba, ta faɗa mata an aura mata uncle ɗinta. Mamaki ne ya kama Seraphina na jin tana kuka wai dan an aura mata Uncle ɗinta, ita fa Seraphina bata san cewa ma haramun ne ka auri Uncle ɗinka na, a wautarta har mahaifinka zaka iya aura, bata da ilimi da sani ƙan ɓangaren wa yakamata ka aura, a ɗan dake ta ce. "Ke baki son shi ne?".
Cak Rimsha ta tsayar da kallonta a kan Seraphina, kana ganin idanunta zaka san tana cikin tsananin tashin hankali.... "Na ce ke baki son shi ne?". Seraphina ta sake tambaya.... Nan fa komai ya ɗaukewa Rimsha na ƴan dakiku, sai kuma ta ja dogon numfashi, muryanta a dashe ta ce. "Idan na ce bana son Uncle Aryan na yi karya, dan a koyaushe in zan yi addu'ar miji ina kwatance da irin qualities ɗinsa, amma dik wannan bashi bane, ni irinsa nike fata ba shi ba, kuma ban taɓa addu'ar mai halin mugunta irinsa ba, bana son halinsa, mugu ne sosai, tsoron kallon fuskansa nike sis, zuciyata bugawa take yi tana rawa muddin yana gida, ko ban haɗu da shi ba idan na ji ya zo gida hankalina in ya kai dubu tashi yake yi, wlh ni gara ace mutuwa na yi da ace na wayi gari na ji wannan bakin labari wai shi ne mijina".
Siririn tsaki Seraphina ta ja kafin ta ce. "Meyasa sai mai irin qualities ɗinsa kike addu'a? Ba ga shi ba? Kika sani ko addu'ar taki ce ALLAH ya amsa maki ta hanyar baki shi? Kika sani ko shi ne alkhairi a gareki? Kada ki bani kunya sis, is he not a man? And ke ba mace bace?"........ "Uhm, sis ba zaki gane bane, Uncle Aryan bakin mugu ne, ban tsanesa ba, amma na tsani halinsa matuƙa".
"Sai ki canza shi, ke ba mace bace? Ki canza shi da salonki, ki koya mashi dik irin halin da kike so ya zama, ki koya mashi ya zama mai taushi"...... Ganin Seraphina ba zata gane irin mugunta Aryan bane yasa ta kifa kanta a saman table kawai, ta fara rera sabon kuka.
Rungumeta Seraphina ta yi, ta dinga bata baki, da kyar ta samu ta yi shiru, ganin Rimsha fa ta rigata ta tsorata da Aryan, tana tsoronsa tamkar mutuwarta ne yasa Seraphina ta ce bari ta kyaleta zuwa wani ɗan lokaci sai ta ƙara bata shawari, yanzu ba zata taɓa fahimtarta ba.
Haka suka kasance har sauran ɗalibai da uncle suka shigo, ya fara karantar da su, sai dai dik abin da yake koya masu sam baya shiga kan Rimsha, tana nan cikin ƙuncinta, Seraphina ta yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali, amma abin ya ci tura, dole kawai ta haƙura ta kyaleta zuwa su fita break, Uncle ɗan kwalisa kuwa sai satar kalle mana Cherry yake yi, yana son a tashi break ya zo ya faɗa mata ya yi kewarta.
A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana isa gidan Abba bai iskosu ba, Abba da Faryan basa nan. Bai yi wa Ammie magana ba ya fita ya koma gidansu Lion.
-------------------------🔥
D--------O--------L
Manasa ce ta fara lura Arya bata cikin sansani, to da yake sun san halinta da son ruwa sai ta ce bari ta dubata a wajen ƙoramun nan kan ta zo ta yi breakfast. Fitowa ta yi da nufin ta je wajen. Bata yi wa kowa magana ba ta wuce. Tin daga nesa ta hango Arya kwance saman dutse, da sauri ta ƙarisa wajen tana ambatar sunanta.
Sai da ta taɓata ta gane ta suma ne. Hannu tasa cikin ruwan ta ɗebo, ta yayyafa mata a fuska. Dogon numfashi ta ja game da saukewa a hankali, slowly ta waro idanunta waje, sake sauke ajiyar zuciya ta yi kafin ta yunkura ta miƙe. Cike da mamaki Manassa ta ce. "Bloody lafiya kike sume a nan?".
Banza da Manassa ta yi, ta miƙe ta kwashi kayanta ta nufi cikin sansaninsu. Shiru Manassa ta ɗan yi tana mamakin halin Arya sosai. Juyawa ta yi tana kallon koramar dake zubo da ruwa daga sama. Daga bayanta ta ji ance. "What are you doing here?".
Ko bata juyo ba tasan muryan, a natse ta amsa da. "Waiting for my special person"........ "Are you sure?". Vash ya faɗa yana ƙarisowa in da take...... "Very sure". Ta faɗa game da juyo da kallonta a kansa. Nisawa ya ɗan yi, cikin zafa ya haye kan dutsen. A gefenta ya zauna suna fuskantar ruwan, hira mai cike da respect ɗin juna suka fara yi, bai fito da soyayyarta a fili ya bayyana ba, ya dai biye mata yana bata amsar tambayoyi. Ita kuma tana tinanin da sun koma sansani ta ɗauki wayarta zata mashi aljanar da ta saba ta ce taga ya kula wata a bakin ruwa.
Mu ɗan yi baya kaɗan a ɓangarensu Leo. A lokacin da suka kammala breakfast, team 1 dik suka haɗu a tantin Leo, sai suka kwance mutanen da suka zo da su jiya. Sun yi mamakin ganin fuskokin mutanen, fuskoki mai cike da kamala da mutunci. Vash da Noor ne suka caje jikinsu kaff.
Abin da suka gani ya yi matuƙar gigitasu, ID card nasu, ya tabbata navy ne, ya rabb, sojojin ruwa ne da wannan aika-aikan, no wonder suka iya faɗa irin na soja, ashe dik ɗaya ne. Kallon juna team 1 suka yi, cike da takaici Noor ya ce. "Wannan wani irin cin amanar ƙasa ne? Wani irin zalunci ne wannan? Ya ake son al'umma su yi da ransu?".
Zaynish ya amsa da. "Dama ai dik abin da ya shigo kasar nan in ma mai kyau ko mara kyau to da sa hannun sojojin ruwan dake kan aiki, ba ta yadda za'ayi wani abu ya keta bakin ruwa ya shiga cikin ƙasa basu sani ba, hakan ba zai yiwu ba, suna sane da komai!".
Shiru Leo bai yi magana ba, saboda tsananin takaici, wai ace da jami'ai ake haɗa bakin wajen yin wannan ɓarna.
Can Leo ya ce. "Ku karɓo mana alluran barci daga wajen Manassa, ko kuzo da ita ta zo tai masu, zuwa dare zamu san hukuncin da zamu yanke masu".
Vash ne ya ce. "Amma yakamata ace mu ajiyesu har su farfaɗo sai mu tambayi su waye suka basu aikin?"........ Shiru Leo ya ɗan yi, sai kuma ya girgiza kai. "Ba zasu faɗa maku ba, dan suma basu san wanene ainahin mai ɓarnar ba, suna karɓar umarni ne kawai daga sama kuma cikin waya, dan haka babu wani amfanin neman information a wajensu"......... Noor ya ce. "Su ɗin karnukan farauta ne kawai".
Sun gamsu da waɗan nan kalamai na Leo, dan haka sai suka yarda da shawaransa, a kan haka suka tsayar da matsaya, daga nan suka rufe babin zancen suka ɗauko maganar shirya plan kan yadda zasu je wajen wannan hayaƙi su duba menene.
Sun tsara nan da kwanaki biyu zasu je su duba menene a wannan waje, kan wannan matsaya suka tsaya, sai Leo ya ce su fita su ɗan yi kewaye a arear wajen ko akwai wani abin da zasu samu. Zaynish da Vash suka fita, shi ne Vash ya tsaya wajen Manassa a bakin ruwa, while Zaynish ya tafi bakin babban tekun nan dan saka idanu, shi ya damu sosai da yadda ake shigo da gurɓatattun kaya, a cewarsa bai ga anfanin hukumar sojan ruwa ba, a rana idan ka tsaya a bakin tekun nan sai ka ga jiragen ruwa sama da 10 sun iso, wasu suna nesa, wasu sun juya, to yanzu sun san wasu daga cikin abubuwan da ake shigo dasu, yakamata su san abubuwan da ake fitarwa.
Tamkar Zaynish ya shiga cikin zuciyar Leo, in baku manta ba Leo yana yawan tsayawa a bakin tekun nan, to kullum tunaninsa me ake fitarwa cikin waɗan nan manya-manyan jiragen ruwan? Ina ake kai abin da ake fitarwa? Wasu lokutan yana ganin tankokin man fetur ne, wasu tankokin da rigister gwamnati, wasu kuma yana zargi babu, wasu kuma na ƴan kasuwa ne, dik bama wannan ba, manyan containers da ake fita da su kullum me a cikinsu? Kullum yana wannan tunani, shi ne ya tsara su je su fara binciko me ake shigo da shi kafin ya tsara binciko me ake fita da shi. Leo yana da kishin ƙasa da kishin kai sosai.
Zaynish and Vash suna fita Leo ya ware gashin kansa, ya ɗauko comb ya miƙawa Noor, karɓa Noor ya yi ya fara taje mashi gashin, abinku da renon mata, take Noor ya tsara mashi kitaon balba masu balain kyau, ya zuba mashi mayukan gashi a kai, sai kamshi gashib take yi, ta ƙara zama golden white sosai.
Yana tsaka tara jelar kitson ya ɗaure ne ya ce. "Bro kaki ka faɗa mun zanen me a bayan wuyanka, ina son sani, kuma kasan me?"....... Kai Leo ya girgiza alamar aa... "Waɗan nan zane suna mun kaman na sansu a wani waje, ina jin kamar zanen password na wani abin ne da na taɓa sani, kaman kuma zanen wani tambari". Ya faɗa daidai lokacin da ya gama ɗaure mashi jelar kitson, sai yasa hannu a saman lallausan fatan bayan wuyan Leo ɗin, ya fara shafa zanen yana son tina a ina ya san shi.
"Yadda ka ga zanen nan haka nima na gansa, na sha faɗa maka ban san na menene bane, ban ma taɓa ganin zanen me bane, ni da kawai ana ce mun a bayan wuyana akwai zane kamar tabo, kamar da wuta aka yi mun, to ban sani ba". Leo ya faɗa game da juyo, har ga ALLAH bai san zanen me bane, shi dai kawai ana ce mashi akwai zane a wuyansa, bai taɓa gani ba, kuma bai taɓa sha'awar ya gani ɗin ba.
Miƙewa ya yi game da ɗaukar belt ɗinsa, ya sanya a jikinsa da kyau, a wannan lokaci Manassa ta shigo da allura, Noor ya nuna mata mutanen, zata masu alluran Leo ya ce. "Na awa nawa ne?".
Cike da gimamawa ta ce. "Awanni 12 sir Zaynish ya ce mun". Jinjina kai ya yi alamar haka ne, Noor ya taimaka mata ta yi masu alluran, sannan ta fita. Ƙarisa shiryawa Leo ya yi, suka fita a tare da Noor, suka kutsa cikin daji, suna tafiya suna hira, suka yi nisa da sansaninsu, daga ta bayan sansaninsu can suka isa bakin ruwa, a nan suka zazzauna saman wasu manyan duwatsu dake kewaye da wajen, ga wasu bishiyoyi dake kaɗa iska mai daɗi kuma mai sanyi, Leo ya ɗibi wasu duwatsu ƙanana yana jefawa a cikin ruwa one by one suna hira.
A can sansani kuma Arya ta shirya cikin ainahin kakinta, ta ɗauki breakfast ɗinta, wake ne da kwai guda ɗaya. Ta zauna gaban laptop ɗinta, tana ci tana sake bincike a kewayen da wannan hayaki yake fitowa, har yau dai wannan hayaki yana nan yadda yake bai daina fitowa ba, sai ma karawa da ya yi, kuma abin mamaki har yau drone ɗinta yaki matsawa gaba ta ga menene a waje. Sai ta juya drone ɗin tana kewaye a arear wajen ko zata ga wani abin da zai sanya ta iya fahimtar me a wajen.
Filin wani irin kurman fili ne da ba zaka taba fahimtar me a wajen ba, ga alamar igiyar lantarki mai karfin gaske, bugu da ƙari a dab wajen tsuntsaye basa rayuwa sai da gefe kusa da tekun, idan kuwa haka ne to fa lallai gurɓatattun abubuwa ake narkawa a wajen masu guban gaske. Shiru ta yi tana tinanin yadda zata samu fly ta tura shi wajen ta gani.
A daidai lokacin ta kammala cin abincinta, sai ta miƙe ta fito waje bayan ta ajiye plate ɗin a gefe, bayanta V da Angelina suka biyo, a lokacin Manassa na bakin ruwa tare da Vash suna hira.
Cikin daji ita ma ta kutsa dan kewaye tana tinanin yadda zata yi ta samu nasarar sanin me a wannan waje?. Suna tsaka da tafiya Angelina and V sai gulman sojojinsu suke yi. V ta ce. "Sir Zaynish ɗin nan akwai miskilanci, baya magana sai haɗe rai kaman sir Nirash".
Angelina ta ce. "Kada ki yarda, kome sir Zaynish ya yi kyau yake kara mashi, kuma ya kai ya yi ɗin ne". Tana ɗan harararta ta ce. "Ko dai kina ciki ne?"...... "Sai ma kin tambaya? Ai sir Zaynish nawa ne". Dariya V ta saki kafin ta ce. "Tab ki ɗauko babban aiki, amma zan sayaki"........ Rungumeta Angelina ta yi. "Shiyasa nike sonki baby".
V ta ce. "Drone da na tura yamma maso gabas na dajin nan fa ɗazun an harbe drone ɗin, naga ba signal ɗinsa ya ɗauke"....... Cikin zafa Arya ta dakata da tafiya, da sauri ta ce. "Kuma shi ne baki sanar mana ba? An harbe drone ɗin? Kenan akwai wani motsi a wajen?". Watau ita Arya idan ba batun aiki ba bata sanya baki a ciki.
V zata yi magana suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 80 Chapter of 95