bai taɓa jin Aryan ya nemi alfarma a wajensa ba, abin da yasani shi dai komai nasu na juna ne, komai nasu ɗaya ne, amma yau Aryan yake batun alfarma? Menene wannan da girma haka?.
Shiru Lion bai tankar mashi ba, da yake suna fahimtar shirunsa sai Aryan ya gane yana saurarensa kenan, wlh shi kansa Aryan ɗin zuciyansa a razane yake da kalaman dake shirin fitowa daga bakinsa, amma bashi da wata mafita ne, sai ya daure da cewa. "Alfarmar da nike nema shi ne ina son ɗauko sister ɗinta in kawota nan ta ɗan zauna for some days".
Tamkar fuska tamau Lion ya yi har sai da Aryan ya ji kishi ta kama shi..... "Reason?". Lion ya faɗa a dake..... "Kada ka tambayi reason please, zan faɗa maka gaba, yanzu dai please bro, ba zata jima sosai ba"...... Shiru Lion bai sake yin magana ba, sai ma miƙewa da ya yi zai bar wajen, saboda baya son abin da zai ɓatawa Aryan rai, kuma shima baya son ransa ta ɓaci a wannan lokaci.
Binsa da kallo Aryan ya yi yana tinanin yadda zai ɗauko Rimsha, har Lion zai fita Aryan ya ce. "Our Lion yarinya ce ƙarama, zata........". Maganar tasa ta dakata ne sakamakon juyowa cikin zafa da Lion ya yi, wani irin kallo ya wurga mashi kafin ya ce. "Mace ko jaririya ce zafin cizonta ya fi dafin kunama! Ko yau aka haifeta kada ka kuskura ka jawota cikin rayuwarka!!". Ai Lion an shaka ka warke, kome zaka ce mu mata ba zamu ga laifinka ba, sister Lazy ai sai shiru.
Maganar da ya yi ne yasa su Vir shigowa cikin room ɗin da saurin dan ganin menene yake faruwa, a fusace Lion ya juya ya fice da sauri. Miƙewa Aryan ya yi, ya kwanta a gado cike da tinanin yadda zai yi ya dawo da Rimsha gidan, ya yi rantsuwa da ALLAH sai ya dawo da ita.
Saman bed ɗin su Vir suka hau suna tambayansa menene yakefaruwa tsakaninsa da Lion? Banza da su ya yi, suka tambaya har suka gaji bai yi magana ba, daga karshe ma rufe idanunsa ya yi tamkar mai barci. Dole suka kyalesa suma.
------------------------🔥
KHAIZA'AN'S HOUSE.
Su Abba sun ɗauko Aunty Luna lafiya sun dawo da ita gidan, a lokacin da Rimsha ta dawo daga school sai ya isko Aunty Luna a gidan, ɗan baya-baya da ita ta fara yi tana rakuɓewa.
Aunty Luna watayyar mace, kuma da kallo ɗaya ta ji Rimsha ta shiga ranta, sai ta jata a jikinta, tin bata cire uniform ba ta rikota game da cewa su je ta cire mata uniform ta yi wanka. A lokacin su Abba dik basa nan, ya ce Harleen ya kashi shopping dake saman nan da kansa ya sayawa surukarsa kyauta ta ban girma na maraba da shigowa Khaiza'ans family.
To shi ne suka tafi, Ammie na ɗakinta, Faryan yana shigo da Rimsha suka gaisa da Aunty Luna ya wuce room ɗinsu. Kama hannun Rimsha Aunty Luna ta yi suka nufi ɗakin Rimshar tana tambayarta meyafaru idanunta suka kumbura sosai har haka.
Ai tamkar Rimsha jira take a tambayeta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta yi, sai kawai ta juya ta rungumi Aunty Luna tana cigaba da kuka, anki a fahimta, anki a gane damuwarta, kowa yana ganin kamar zasu yi zaman lafiya da Aryan, ina zaman lafiya tsakanin wuta da audiga fisabillillahi?.
Rungumeta Aunty Luna ta yi suka karisa cikin ɗakinta, a gefen gado ya zaunar da ita game da ɗago haɓarta tana goge mata hawaye tana faɗin. "Sorry my sister, yo shiru ki faɗa mun menene yake damunki? Waye ya taɓaki?".
Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi.
*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*
Likes comments and share fisabilillah.
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-26.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 67 & 68
CRYSTAL PALACE.
Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi. Jawota jikinta Aunty Luna ta yi, ta hau rarrashinta.
Baki ɗauke da sallama Ammie ta shigo ta samesu, dama a jikinta ta ji Rimsha na kuka shiyasa ta zo rarrashinta. Karisowa ciki ta yi, suka haɗu da Aunty Luna suka rarasheta sosai, sai da ta yi shiru, sannan Aunty Luna ta ce Ammie su je waje su yi magana.
Kwance suka baro Rimsha suka fito, a parlo suka zauna Aunty Luna ta tambayi Ammie me ya sa Rimsha take kuka haka? Dan ita wlh Rimsha ta kwanta mata a rai matuƙa, tana jinta tamkar sister ɗinta na jini watau sister Lisa.
Ba ɓoye-ɓoye Ammie ta sanar da Aunty Luna gaskiyar abin dake faruwa. Cike da mamaki Aunty ta ce. "Kan wannan abin ne take irin wannan kuka? Waye shi Aryan ɗin? Ba namiji bane?".
Ammie da tasan waye Aryan ne ta amsa da. "Yayan Harleen ne wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya"...... Shiru Aunty Luna ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Shikenan ina zuwa". Ta miƙe ta fita, ɗakin Rimsha ta koma, nan ta iskota tana waya da Seraphina, ta ce dan ALLAH Seraphina ta zo gidansu yanzu tana son ganinta.
Aikuwa Seraphina kafa sarkin son yawo, sai cewa ta yi gata nan zuwa, amma bata san gidan nasu ba ai. Rimsha ta ce. "Benen dake ɗauke da number 2 shi ne benenmu"....... A lokacin Aryan ya fita, Seraphina ɗin ta yi wanka tana shafa mai.
Aikuwa kafa sarkin yawo, a gurguje ta karisa shirinta ta fito, ta danya wani crazy jeans fari tas, daga sama top baki, sai ta ɗaura winter jacket a saman kayan wanda ya zo mata har gwiwa saboda sanyin da ake zubabawa, kafafunta sanye cikin socks, ta sanya ankel boot a kafafunta.
Kai ba ɗankwali, ta nufi wajen Madam tana faɗin. "Mom ɗaure mun gashina zan je gidansu Rimsha". Cike da mamaki Madam ta ce. "Kin faɗawa daddy ne?". Ɗan zazzare violet eyes ɗinta ta yi, sai kuma ta ce. "Zan kirasa a wata mom, yanzu dai ɗaure mun".
Ba musu Madam ta gyara mata gashin, ta cufke mata a tsakiya game da sake jilar a baya, waɗan nan guntaye na gaban goshin kuma ta ƙara gyara mata su, ta kwantar mata da su da kyau kafin ta feshe gashin da turarukan gashinta.
Tana murmushi ta amsa da ta gode, fitowa ta yi ta kira number Aryan, a lokacin ya gama wannan rikici da Lion kan dawo da Rimsha gidan, yana kwance saman sofa, ya tada kai da cinyar guru suna ta yi mashi magana ya yi banza da su.
Kiran na shigowa ya ciro wayar, ganin my Cherry yasa ya katse kiran ya kirata. Bugu ɗaya ta ɗauka, cike da zumuɗi ta ce. "Daddy zan je gidansu Rimsha tana kirana". ....... Ai sai da ya ji wani irin rass, da sauri ya miƙe zaune. Sai kuma ya ɗan nisa tare da cewa. "To ki je, amma kada ki jima". Ya faɗa mata hakan ne kawai dan kada ta sake zargan wani abu, yanzu idan ya hanata tana iya cewa sai ya bata dalili, dama ga shi ta ce taga yana kama da Faryan, kunga kuwa tsab zata gasgata zarginta.
"Love you daddy, shiyasa nike sonka sosai"........ Ƙasa ya yi da murya sosai, tamkar mai raɗa yana satar kallon Vir da ya tsare shi da ido kafin ya ce. "Love you more Cherry"...... Dik abin da ya faɗa guru na jinsa, amma kamar bai ji ba, shi kuwa Vir baya jinsa amma ya karanci bakinsa tsab, ya gano me ya ce.
Dan haka yana katse kiran sai ya ce. "You love who?"...... Hararansa Aryan ya yi game da miƙewa zai bar wajen ba tare da ya yi magana ba. Damko hannunsa Vir ya yi, ya jawosa da karfi har sai da ya faɗo jikinsa, ya damki arabs hair ɗinsa da karfi kafin ya ce. "Kaima sarautar zaka gwada mana ne?".
Ai cikin zafa Aryan ya miƙe ya damko korean hair ɗin Vir, da karfi ya ja yana faɗin. "Dama kwana biyu da ka tafi na huta da sa ido, ka dawo kenan yanzu, zamu fara raba hali"..... Dik cikinsu ba wanda ya kai Vir sa ido kam, ko baya jin me ka faɗa in dai yana ganin bakinsa sai ya san me kace.
Kafa ɗaya kan ɗaya guru ya ɗaura yana ganinsu, dan in da sabo sun saba wannan faɗa...... Damke gashin Aryan ɗin shi ma Vir ya sake yi yana faɗin. "Sai ka faɗa mun waye kake cewa I love you, na dai san ba Abba bane, kuma ba su Faryan bane".
Kwace kansa Aryan ya yi yana faɗin. "Ba zan faɗa ba". Ya wuce ya nufi cikin ɗaki. Miƙewa suka yi a tare suka rufa mashi baya guru ka zolayarsu.
Ita kuwa Seraphina wucewa ta yi ta fito. Elevator ta zo shiga kenan sai ga wani matashi dake benen nasu amma sama da gidansu shi ma ya zo shiga zai sauƙa ƙasa. Kura mata idanu ya yi, ita kuma ta tamke fuska tamau. Ta shiga ciki, ta tsaya a gefe shima ya tsaya a gefe, sai satar kallonta yake yi, a tare suka kai hannu zasu danna down, dan dik ƙasa zasu sauƙa.
Ɗauke hannunta ta yi, ta barshi ya danna. Har elevator ɗin ta sauƙa kasa bata ɗago ta kalli guy ɗin ba, amma ta rike kamanninsa sosai. Fitowa ta yi bayan elevator ɗin ta buɗe, basu da nisa da benen su Rimsha, can ta nufa tana ɗan waigo guy ɗin, abinku da jinin IRON FIST, a cikin ranta tana jin wannan mutumin bashi da gaskiya, ta ce kwayar idanunsa sak na masu laifi ne, shiyasa da suka sauka take ta faman kallonsa.
Tana ganinsa ya nufi wata haɗaɗɗiyar motarsa, ya ja ya nufi main gate na CRYSTAL PALACE ɗin. A cikin ranta ta ce. "Zan ce daddy ya saya mun mota nima". A fili kuma ta kara tamke fuska ganin dik in da ta wuce sai masu wucewa sun kalleta, sun ga ƴar beauty, ita kuma ta tsani kallo kamar uncle ɗinta Lion.
Bene na biyu ta nufa, kai tsaye elevator ɗinsu ta nufa, ta zo dab elevator ɗinsu kenan sai ga wani matashi ya fito daga cikin elevator ɗin. Kallo ɗaya ta yi mashi ta ɗauke kai, shi kuma tin da ya ɗaura ido a kanta har ya fito daga cikin elevator ɗin ita yake kallo. Wucewa ta yi ta shiga ciki tana ɗan rera wakar da ta saba saurare a wayarta tana kalle-kalle.
Elevator ɗin na ƙoƙarin rufe kansa sai taga an sanya hannu daga waje an dakatar da shi. Zubawa masu shigowar ido ta yi, Abba ne da Harleen, sun je shopping na sama basu samu abubuwan da suke so gabaɗaya ba shi ne suka je na ƙasa.
Hannun Harleen rike da uban niƙi-niƙin kaya a manyan ledoji. Hannu ta kai zata danna hawa na goma sai taga Abba ya rigata ya danna. Bin Abba da kallo ta yi, sak kamannin fuskan Aryan babu banbanci, har sai da ta ji gabanta ya faɗi, haka ma Harleen yana mugun kama da Aryan, abinku da jini, shi da Abba basa kama can sosai fa, amma jini yasa taga suna kama.
Rage tsawonta ta yi, ta ɗan durkutsa kafin ta ce. "Good evening sir". Ɗago da kallonsa a kanta Abba ya yi, lokaci guda ya ji yarinyar ta mashi, sai ya ji yana buƙatarta a cikin danginsa, kun san gidansa auren haɗi ake yi, kamar yadda ya ga su Aunty Luna a cikin elevator ya je ya nemi aurensu wa ƴaƴansa to ita ma Seraphina ta mashi, sai ya ji yana buƙatar haɗata da Faryan.
Dan haka fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata game da ce mata. "What's your name my daughter?"...... Seraphina baki abin magana tuni ta ce. "Seraphina". Ta faɗa tanawa Abba murmushi.
"Seraphina". Abba ya maimaita sunan kafin ya ce. "Ina iyayenki suke? Ina ne benenku?"...... Abba ya ga ƴar beauty zai je nemanwa Faryan aurenta..... "Mom ɗina tana gida, daddyna ya fita, amma asalin mammyna ta rasu, asalin daddyna kuma ban san shi ba". Ta bawa Abba amsa a natse........ "A wani bene kuke?". Abba ya sake tambaya. Nan ma ta bashi amsa, sai da ta gama bashi information ɗinta sai kuma ta ce.
"Mezaka yi da information ɗina Uncle?"...... "Ki kirani da Abba, zan kawowa iyayenki ziyara ne, zan zo mu ƙullah zumunci, ko baki son zumunci dani?". Abba ya faɗa. Murmushi ta yi. "Ina son zumunci da kai mana Abba". Ta bashi amsa....... "Yauwa ina da yaron da baida aure, baida mata ma". Abba ya faɗa, shi fa Abba tallan yaransa maza ma yake yi, kaman Seraphina ta tambayesa wai yana da yaron da bai da aure, kai Abba duniya.
Seraphina kuma da hankali ya yi mata yawa sai ta ce. "Ni ma ai Abba bani da aure"....... Ai da sauri Abba ya riko hannunta, ya samu daidai shi, irin Seraphina yake so dama. Baki Harleen ya saki yana kallon yadda Abba yake tallarsu a titi, wai ina da yaron da bai da mata, this word pain Harleens heart wlh.
Aikuwa Harleen bai gama mamakin Abba ba sai ya ji yana cewa Seraphina. "Kuma kinga yaron nawa da bashi da auren kyakkyawan matashi, ya gama degree ɗinsa na farko da na biyu, nasan ma zai burgeki"....... Takaici tamkar Harleen ya saka ihu, watau haka Abba ya yi je ya yi sallarsa wajen su Aunty Luna kenan? To ga shi yana tallar Faryan ma, yanzu fisabilillahi ya za'ayi Aunty Luna tai mashi kallon daraja tin da tallarsa aka yi mata?..........🤌🏻😂
Seraphina ta amsawa Abba da cewa. "Abba kaima ai ka burgeni"..... "Yarona zai burgeki fiye dani, zaki auresa ko?"......... Kai ta ɗan girgiza game da cewa. "A'a Abba, ba zan aure shi ba, daddyna kawai zan aura"..... Daidai lokacin suka isa in da zasu sauƙa, kofar elevator ɗin ta buɗe masu.
Da yake Abba ya kalleta yarinya kuma ya ɗauka daddynta mahaifi take nufi, sai bai wani damu ba, ya ce. "Zan zo gidanku In Sha ALLAH". Da okey ta amsa mashi game da tsayawa a gefe ta hau kiran number Rimsha zata faɗa mata ta iso hawa na goma ɗin. Abba da Harleen suka nufi haɗaɗɗen kofar parlonsu, dama daga wajen elevator ɗin wani hadaɗɗen baranda ne kafin ka isa wajen kofar Khaiza'ans House.
Har Abba zai buɗe kofar Main parlo sai kuma ya juyo da kallonsa a kan Seraphina. Cike fa kulawa ya ce. "A nan kema zaki sauƙa ne?". Kai ta jinjina alamar e, sanin cewa gidansa ne kawai a hawa na gomar yasa ya sake cewa. "Wajen waye kika zo?".
Tana ƙoƙarin kara waya a kunne ta amsa da. "Wajen kawata Rimsha"...... Cikin parlo Harleen ya shige da kayan hannunsa, dan tsab Abba zai iya sanyawa zuciyansa ya buga na tallarsu da yake yi wajen ƴan mata.
"Nan ne gidansu Rimsha ai, zo ki shiga". Abba ya faɗa. Ɗan zazzare mashi idanu ta yi, sai yanzu ta gane dalilin da yasa Abba yake kama da daddy gentle chaos ɗinta, a cewarta saboda baban Faryan ne, kun san ta faɗa ai Faryan yana kama da daddynta. Kamar zata ce mashi dama uncle Faryan ne ɗanka da bai yi auren ba, sai kuma ta fasa game da kufansa.
Suka shige ciki a tare. A parlo Abba ba zauna game da nuna mata sama yana faɗin. "Ki je Rimsha tana sama".... "Nagode Abba". Ta faɗa game da hayewa sama tana ɗan murmushi. Shi kuwa Abba ya yi shiru yana tinanin yadda zai je ya gana da iyayenta a nan kurkusa. E kam akwai case, Abba zai je karɓawa Faryan auren Cherry a hannun Aryan.
Tana haurawa sama suka yi karo da Ammie, risinawa Seraphina ta yi ta ɗaga mata gaisuwa, fuska a ɗauke da fara'a Ammie ta amsa mata, sai ta ce. "Ban gane ki ba". Kai ta jinjina. "Seraphina by name, friend ɗin Rimsha, wajenta na zo". Cike da girmamawa ta faɗa.
Da yake dik sun san labarin Seraphina sai Ammie ta ce. "A'a, ai mun san labarin Seraphina, mun sanki a bakinta, shiga ga ɗakinta". Ta kai karshe game da nuna mata ɗakin. Godiya ta yi tare da wucewa ciki. Bayanta Ammie ta bi da kallo tana yabawa kyan yarinyar, sai ta ji ta kwanta mata a rai, a cikin zuciyarta ta ce ina ma ace rabon Faryan ɗinta ce, ALLAH yasa ya mallaketa.
Sai da Seraphina ta shige cikin ɗakin Rimsha sannan Ammie ta wuce ta sauƙo ƙasa. A lokacin da ta shigo Rimsha ta yi shiru, tana kwance ta tada kai da laps ɗin Aunty Luna dake ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Tana ganin Seraphina ta miƙe da gudu ta nufeta tana faɗin. "Welcome my girl". Ta kai karshe game da rungumeta.
Rungumota ita ma Seraphina ta yi, Aunty Luna ta zuba masu ido tana kallonsu har suka raba jikin juna, Rimsha ta kamo hannun Seraphina ta isar da ita bakin bed, ta zaunar da ita kafin ta ce. "Seraphina my Aunty, Aunty Luna my best friend".
Cikin girmamawa Seraphina ta ɗagawa Aunty Luna gaisuwa, fuska ɗauke da murmushin nan nasu mai kwantar da hankali Aunty Luna ta amsa mata, lokaci guda Seraphina ta gano Aunty Luna na kama da uncle na school ɗinsu, amma bata yi magana ba.
Bayan sun gaisa Aunty Luna ta fita ta basu waje, ai sake rungume juna suka yi kafin su fara gulma. Sai ga Ammie da kanta ta shigowa da Seraphina cima irin nasu na larabawa kala-kala masu daɗi da kamshi. A saman carpet ta shirya mata kafin ya juya ta fita. Daga Rimsha ɗin har Seraphina ɗin babu wacce ta ci abinci rana a cikinsu, dan Seraphina ma in baku manta ba ta je yin wanka ne ta fito ta yi lunch ɗin kenan Rimsha ta kirata, so dik basu yi ba, amma ko da Ammie ta kawo masu abinci basu sauƙa sun ci ba, suka yi zaman gulma.
To kafin su kammala gulmar nasu bari mu je wajensu sister Zinta mu dawo, jama'a me kuke tunanin zai faru? Abba ya yaba da Seraphina, Ammie ma haka, ga shi dama Faryan yana so, kun kuwa san idan Abba ya nufi yin abu fa to koma ya za'ayi sai ya yi, me kuke tunanin zai faru? Muje zuwa.
------------------------🔥
WS-HOSPITAL.
Around 2 na dare sister Zinta ta farka daga barci, ga mamakinta sai bata ga Dr James a saman bed ɗin ba, miƙewa ta yi zaune taka kalle-kallen gefe, babu shi babu alamarsa.
Kasa ta sauƙo tana daka hamma, a tinaninta waje ya fita dan bata ji alamar motsi a toilet ba, sai ta nufi waje. Shiru babu alamar motsin mutane a gidan, ta yi matuƙar mamaki sosai, ɗakin dake kusa da nasu ta shiga. Nan ta isko mutum kwance a saman bed.
Har zata juya kuma sai ta fahimci ashe macece kuma sister Maya ce. Ajiyar zuciya ta sauke game da karisawa wajen da sister Maya ke kwance, tattaɓata ta fara yi tana ambatar sunanta. A hankali Maya ta buɗe idanunta, ganin Zinta ce yasa ta miƙe zaune tana faɗin. "Sister lafiya?".
Zinta ta amsa da. "Sis babu kowa fa a gidan nan yanzu, ina suke to?"..... "Ban gane babu kowa a gidan nan ba?". Ta faɗa tana zare idanu. Shaida mata da kyau sister Zinta ta yi lallai babu kowa a gidan nan, zabura ta yi ta sauƙo ƙasan gadon tana tambayar ina suka je?.
Sister Zinta ta ce. "Ke, ki natsu, ina ganin wani abin suka je yi, ko sun je cikin hospital ne? Mu je mu dubasu"..... Na'am da wannan zance Maya ta yi, sai ta haɗe natsuwarta waje guda, ta miƙe suka fice a tare.
A bakin gate suka isko guards masu gadin gidan suna zazzaune babu alamar barci a idanunsu, zasu fita guards ɗin ɗaya ya ce. "Ina zaku je Madam?"....... "Cikin hospital". Sister Zinta ta basu amsa.
"Sorry Madam ba'a ce mana zaku fita ba, dan haka ku koma"...... Kallon juna suka yi, sister Maya ta juya da nufin su koma, ita kuma sister Zinta da yanzu ta daina jin tsoro da shakkar kowa tin da ta amarce da Dr James sai cewa ta yi. "To idan na zo fita ka hanani in gani". Ta faɗa tana riko hannun sister Maya.
Miƙewa tsaye guard ɗin ya yi game da cewa. "Sorry Madam, ba'a bamu izinin cewa akwai wacce zata fita mu buɗe mata kofa ba". ..... Sosai sister Zinta ta tsorata da ya miƙe tsaye, wani kato da shi a murɗe. Amma saboda yanzu bata jin magana sam-sam, bata shakkar kowa bare tsoro sai ta ce. "Wannan kai ya shafa, ni dai hanya zaku bani in wuce ko kuma in buɗe da kaina in wuce".
Rikota sister Maya ta yi tana faɗin. "Sis please ki kyalesu mu koma ciki"..... "Ba zan kyalesu ba sis, sai na je na duba mijina, kika sani ne ko yana tare da sister Lazy!". Cikin masifa ta faɗa, yanzu ta fara iya harda masifa yarinyar nan, da shiru-shiru abinta.
Mamaki ne ya kama Maya ganin yadda take masifar, har da ɗaure fuska tamau. Shi kuwa wannan bodyguard ɗin ya tsaya tsayin daka kan ba zata wuce ba, domin kuwa a bakin aikinsa yake. Da ta matsa mashi ma sai ya yi mata ɗaukar amarya, cak ya dagata, bai direta a ko'ina ba sai a tsakiyar parlonsu, ya juya ya fito.
Zata bi bayansa sister Maya da ta shigo yanzu ta riketa tana faɗin ta yi hakuri koma menene ai Dr James ɗin zai dawo, ba sai ta titseye shi ba idan ya dawo, kin aminta ta yi, ta kwace kanta zata sake fita Maya ta riketa tana sake bata hakuri. Shi kuwa bodyguard tini ya koma bakin aikinsa.
A daidai wannan lokaci kuma 3D suna tsakiyar hospital ɗin, dan SECTION E a tsakiyar gabaɗaya ginin yake, amma ba zaka taɓa zaton shi ne a tsakiya ba har sai in ka san taswirar ginin da kyau, a yadda aka tsara haka ne, amma jama'ar cikin asibitin suna ganin kamar SECTION E a karshe yake.
Da ace sister Zinta ta fito a wannan lokaci, to hakika da zata haɗu da 3D rike da jariran da suka ɗauko daga SECTION D, saboda sun fito zasu shiga SECTION E, a daidai saitin hanyar da zai kaisu gidansu suka tsaya Dr James yana duba wani baby da hancinsa ke bleeding, sun ɗauko five babys kamar yadda suka saba, suna tsaka da tafiya ne Dr James ya ji jini na zuba a hannunsa, shi ne suka tsaya duba menene matsalar, to daidai wannan lokaci su sister Zinta suka so fitowa guard ɗin can ya taresu.
Sosai hancin jaririn yake zubar da jini, wannan jaririn ne da sister Maya take ɗauka a lokacin da aka ɗauke mata darling, sai ta maye gurbin darling da shi, to shi suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 83 Chapter of 95