Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a hankali, na kawo ku gidan nan ne dan cikar burinmu ba dan faɗa da su ba, in kin san ba zaki iya jura ba gara ki koma". Babu wasa a tattare da ita ta faɗa. Zama gefen gadon Suhana ta yi, tana turo baki na rashin kunya ta ce. "Sorry Aunty, it can't happen again"...... "Ya dai fi maki". Madam ta faɗa tana miƙewa. Ita kuwa Seraphina ɗakinta ta koma, ta hau feshe jikinta da perfumes da ya saya mata masu daɗin kamshi, ta haɗu matuƙa sosai. Zama ta yi a gefen bed tana laluɓo wayarta zata kirasa, sai kuma ta fasa, ajiye wayar ta yi a gefen gadon ta miƙe da sauri ta nufi wajen curtains dake wajen door, a bayan labulayen ta ɓuya tana ɗan leƙowa. After like 5mins da tsayuwarta a wajen ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama. Tsayawa ya ɗan yi a tsakiyar ɗakin yana kalle-kalle game da shaƙar kamshinta da ta fesa yanzu, a cikin ransa ya ce. "Awwa yau ɓuyan mun aka yi kenan". Ya faɗa game da sake saurarawa, abinku da jami'an kwarai, tuni ya gano tana ɗakin ta hanya biyu, na farko sautin nunfashi wanda shi ko me yaya baya ɓuya a waje, muddin ka saurara sai ka jisa, na biyu kamshin perfume da ta fesa yanzu, ya nuna alamar yanzu-yanzun nan mutum yana cikin wannan ɗakin, dan kamshin bai ko gauraye da airfreshner dake ɗakin bama. Juyo da kallonsa a kan curtains na wajen door ya yi, a nan ya ji karfin fitar numfashinta ya fi yawaita, kun san su a horon da ake basu ana mugun koya masu amfani da nunfashin mutum, ta haka ne suke iya zaƙulo abubuwa dayawa. Ya gane nufinta yanzu, wai tsoratar dashi take son yi, juyawa ya yi kamar bai ganta ba, sai ta buɗe labulen ta leƙo, ganin yana ƙoƙarin wucewa zuwa bakin gado ne yasa ta yi murna bai gane tana wajen ba, a hankali ta fito, ta ɗan yi taku step uku kafin ta daka tsalle ta mashi kukan kare a kunne......... Da gangan ya nuna alamar ya razana, har da faɗawa saman gadonta. Dariya ta fara yi tana karawa, zuba mata idanun ya yi yana ganin tsantsar kyan da ta ƙara. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ce. "Daddy kai ba jarumi bane, ka cika tsoro, na fika jarumta, da nice ba zan tsorata ba, ka zo in koya maka jarumtata!". Tana murmushi ta faɗa. Shi kam kallonta kawai yake yi, yana jin tamkar ya jawota ya rungume, ta yi wani irin musulmin kyau tamkar amarya. Ganin sai kallonta yake yi ne yasa ta natsu tare da komawa kusa da shi, cike da kisisina yarinyar nan har da tsugunnawa a gabansa, sai ka rasa daga ina take koyo kisisina da kirsa yarinyar nan. "Sannu da dawowa daddy, am...... In..... Ka yi hakuri tsorataka da na yi, dik saboda soyayyarka ce". Tana turo baki ta faɗa. Shi kam izuwa yanzu dik wasu kalaman da zasu fito daga bakinta ya daina mamaki, yarinya kamar wata uwar mata, sai kirsa da kisisina. Uhm rasa abin faɗe ya yi, sai kawai ya bita da ido. Kwanto da kanta a saman laps ɗinsa ta yi, ta riko hannunsa cikin nata, tana turo baki, a shagwaɓe sosai ta ce. "My gentle chaos talk to me mana". Uhm miƙewa ya yi game da kama hannunta, ya miƙar da ita, ya jata suka nufi waje ba tare da ya yi magana ba. Shopping na sama suka nufa, sai faman kallonsa take yi, taga ya yi tsantsar kyau yau, wannan suit ɗin ta kara fito da kyansa. Kai tsaye wajen abayas ya wuce da ita, da kansa ya zaɓo mata wani haɗaɗɗen after dress mai balain kyau fari tas da veil ɗinsa. Dress room na shopping ɗin suka shiga, da kansa ya ware rigar ya sanya mata a jiki, ya ce. "Haɗe maɓallan mu gani". Ya faɗa yana mata kallon ƙasa-ƙasan ido. Turo baki ta yi. "Ni daddy ban iya sakawa ba, yadda ka fara haka zaka kammala"...... Ɗago eyes ɗinsa a kan face ɗinta ya yi, da sauri ta ce. "Da gaske ban iya ba, ai kaga ban taɓa sanya irin wannan kaya ba"....... Wani irin musulmin hararar kauna ya dallah mata kafin ya kai hannu saitin kirjinta ya kama maɓallan. Zubawa hannunsa ido ta yi, sai taga yatsunsa suna ɗan rawa, baya son taɓa jikinta. Da sauri ya haɗe mata maɓallai ukun, zuwa flat tummy ɗinta maɓallan suke, sauran gaban rigar a buɗe, rigar ta haɗu sosai. Hannu yasa ya ware veil ɗin rigar, ya yafa mata a kai, sai ya ce. "Ki yi rolling ɗinsa mu je". Ɗan turo baki ta yi. "Ni daddy ban iya rolling ba"....... "Wannan kam nima ban iya ba, amma bari in kira ma'aikaciyar wajen ta zo ta maki". Ya faɗa game da juyawa da nufin ya fita....... Da sauri ta riko hannunsa. "Ni daddy ba sai ka kira wata ba, kada ma ta ji muryanka". "To ba na sanya nose mask ba sarkin kishi? Ai ba wanda zai ga fuskata"....... Make kafaɗa ta yi. "Ni dai dik da haka daddy ban yarda ba". Ta kai karshe game da kama veil ɗin, ta fara rolling tana cewa. "Na iya fa".......Zuba mata idanu kawai ya yi, awww ashe ta iya tsiyace dama. Rolling ta yi mai kyau kamar yadda Rimsha take yi, ta ce. "Daddy na yi kyau?"....... Kawai tsintar kansa ya yi d kashe mata ido ɗaya yana sauke ajiyar zuciya. Waro idanunta ta yi. "Daddy, dama ka iya kashe ido ɗaya?"...... Siririn harara ya dallah mata, bai yi magana ba ya riko hannunta suka fito. Kuɗin rigar ya je ya biya suka nufi waje, suna fita ya rungumo shoulder ɗinta tare da rage tsawonsa, a dan kunnenta ya ce. "Yau fa kin yi kyau over, anya ba zan aureki kawai ba? Na fara jin gajiya a kan wannan shamakin dake tsakaninmu, gara in cire hijabin ta hanyar halatta abin"........ Da sauri ta ɗago kai, cike da farinciki ta ce. "Daddy ka aure ɗin kawai, kada ka jira komai". Dogon hancinta ya ja. "Kafin na yi aure dole akwai tsari, sai na bi wasu hanyoyi shiyasa, but lokaci kaɗan ne ya rage, and yanzu akwai very important abubuwa sosai dake taso mana"...... Yana tina tarzomar da zata tashi ne bayan bayyanar IRON FIST a cikin CRYSTAL PALACE, yasan duniya dik sai ta tsaya cak, akwai kura, wannan dalilin yasa ma bai fara batun auren ba, ga shi yana da tafiya a gabansa mai muhimmanci. Turo baki ta ɗan yi ta zura hannunta ta baya ta zagayo da shi har ta wajen flat tummy ɗinsa. A haka suka sauƙo ƙasa. Shopping na ƙasa ya shiga da ita. Kaya sosai ya fara loda mata, bathrobe da sukai mata gajarta na gidan nan dik ya ɗauka mata masu tsawo, ya sai mata abayas sosai, dan yana son ta dinga rufe jikinta. Ita ma zagewa ta yi sai shopping take yi, har da ɗaukar breziya dozen biyu, gani take ta zama ƴan'mata yanzu, musamman da ake ce mata in an ganta kamar mai 16 years, shikenan tana jin kanta ta kai can. Suna tsaka da shopping suna hiran soyayyarsu ne wata mace siririya mai zubin taliyar bua tai masu hello. Kallo ɗaya Aryan yai mata ya ɗauke kai, ita kuwa Seraphina ta fara kallonta daga sama har ƙasa, gata ƴar siririya sai kuma ta ɗauko wasu karuwan kaya, jeans and top ta labka a jiki, ta tara gashin kai a tsakiya ta ɗaure, ta sako jelar gaba, idanunta dara-dara, to a ajiye maganar adawa a gefe kyakkyawar gaske ce sosai, fara tas da ita, sai dai bata da welcome bare kuma goodbye, a shafe take kamar namiji da zani, amma kyan fuska kam akwai shi sosai. Ta kwamo wani uban high heel tamkar wacce ke shirin zuwa taɓa duniyar wata. Yarinyar irin classic lady ɗin nan da boko ya bugasu, wayayyu fiye da misalin nan, a shekaru zata iya kai 25 haka, a nan CRYSTAL PALACE ɗin take, ƴar wani tsohon ƙusa ne na siyasa a ƙasar, dukiya ta yi mubaya'a, suna haya a CP. Seraphina baki abin magana, da ta kare mata kallo sai ta ce. "Wannan fa? Ke babu mirror a gidanku ne?"....... A tinanin yarinyar Seraphina sister ɗin Aryan ce ganinta ƴar karama, sai bata amsa mata ba, ta ɗan matsa dab da Aryan, cikin wani karuwan murya dake maƙale ta ce. "Hii handsome, wajenka na zo, one minute please". Aikuwa nan Seraphina ta ce ba'a haifi mutum ba, da sauri ta matsa kusa da angon nata, ta tamke fuska kafin ta bi yarinyar da wani matsiyacin kallo. Aryan dai tamkar ba da shi aka yi magana ba, ya yi banza da yarinyar. Seraphina dan ta gwadawa yarinyar ita ma A ce sai ta ce. "My gentle chaos mu tafi wajen lotion in zaɓa, daga nan ya isa mu wuce". A shagwaɓe ta faɗa tana riko hannunsa. Tsayar da kallonsa a kanta ya yi, ta marairace fuska tana turo baki. "Kin fasa sayen vest ɗin ne?". Ya faɗa can ƙasa. Kai ya jinjina mashi. "Yanzu na fasa, sai wani lokaci, kawai ka zo mu tafi". Ta ƙara kankame hannunsa. Ɗan rungumo shoulder ɗinta ya yi game da cewa mu je. Zame jikinta ta yi daga nasa ta tsugunna a ƙasa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Ni ka ɗaukeni". Waist ɗinsa ya riko da hannayensa dikka biyu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rage tsawonsa, ya ɗauketa cak tamkar ƴar baby, hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta kwantar da kanta a gefen lion chest ɗinsa. Wucewa da ita ya yi, sun zo dab zasu wuce yarinyar Seraphina ta fidda tongue ɗinta tai mata gwalo, Seraph ta ji haushin yadda yarinyar ta yi banza da ita ta nufi Aryan ne, ta zage sai ta mashi magana, shi ne ta gwada mata capacity ɗinta. Ai tsaye yarinyar ta yi tana ganin ikon god, babyn daddy ta goge mata hadda gabaɗaya. Da suka je wajen lotion zai sauƙeta ƙasa ta ce ina bata san wannan ba, wai sai dai ya riketa ta zaɓi abin da take so, ta ƙara ƙanƙame shi game da kwantar da kanta luff sosai. Uhm soyayya ai dole ya yi abin da take so dan kada ranta ya ɓaci. Ya kuwa biya mata, a haka ta karisa sauran shopping ɗin, wai dan fa yarinyar ta ji haushi ne yasa ta ce kada ya sauketa, a haka zasu yi shopping, dik in da suka gifta yarinyar ta ganta kwance a kirjinsa. Kai Seraphina duniya, kishi da wanga ɗiya ai balai ne, iya kirsa da kisisina. Har da shafa arab hair ɗin Aryan ta bayan wuyansa tana ɗan turo baki. Shi kam bai kawo komai a ransa ba, kawai dan ya faranta mata yake yi. Bayan sun kammala shopping sai ya ɗauketa suka yi bakin beach dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, a lokacin dare ya fara yi, karfe 11 ta yi. Suna parking a wajen sai ga kiran Lion. Picking ya yi game da karawa a kunne, shiru ya ɗan yi yana sauraron Lion ɗin, after like 20 second sai ya ce. "Kawai ku yi dinner ɗin, sai can dare zan shigo". Buɗe baki Seraphina ta yi zata yi magana ya yi gaggawar rufe mata da hannunsa yana ɗan zare mata idanu. Kai ya jinjina kafin ya ce. "Zan kula". Daga haka ya ciro wayar ya katse. Zai ɗauke hannunsa daga kan ɗan bakin nata ta yi saurin kamawa ta sumbacesa kafin ta ce. "Daddy da waye kake waya?". Buɗe kofar motar ya yi, ya fito ba tare da ya amsa mata ba, sai kuma ya ce. "Wait for me bari in maki oder abincin dare a wancan CRYSTAL RESTAURANT ɗin". Bai jira amsarta ba ya wuce ya nufi wani haɗaɗɗen ɗan karamin restaurant dake wajen. Fitowa ita ma ta yi, ta tsaya a jikin motar game da takure jikinta waje guda, wani irin sanyi na bugata, akwai sanyi sosai. Jikinta na rawa, ta so komawa cikin motar amma babu dama, dan tana fita motar ta rufe kanta, bata san yadda ake buɗeta ba. Unexpected idanunta suka sauƙa a kan beach na wajen, ya ALLAH, zazzare idanunta a kan ruwan ta yi, bata san lokacin da ta raba jikinta da jikin motar ba, da gudu ta karisa wajen tekun tana kallon fitilun dake wajen, ga hasken wata na haska ruwan. Rufe idanu ta yi ta sake buɗewa, a fili ta ce. "Wajen ya haɗu, yaushe zan samu cikar burina na keta cikin teku a jirgin ruwa in je kasar da rana take fara fitowa? Wayyo sea". Lokaci guda wani iska mai sanyi ya busata, hakan yasa ta yi gaggawar takure jikinta waje guda, hannunta suka fara rawa, tana son kallon ruwan kuma tana son komawa wajen motar ta laɓe kada sanyi yai mata illah. Shiru ta takure a wajen tana ganin haɗuwar ruwan. Unexpected daga bayanta ta ji an ɗaura mata abu a saman shoulder, kamshin perfume ɗinsa yasa ta gane shi ne. Da sauri ta juyo ta faɗa jikinsa, ya rufeta da suit ɗinsa da ya cire, ya gyara mata da kyau, dama suit ɗin ya ɗaura mata a shoulder ɗinta. Zuro hannayenta ta bayansa ta yi, ta yi tighting ɗinsa sosai tana faɗin. "Daddy yaushe zaka ɗaukeni mu ratsa teku mu je kasar da rana yake fitowa ta cikin jirgin ruwa?"...... Can ƙasa ya ce. "Very soon, after our marriage". Ɗago kanta ta yi, suka ɗan zubawa juna ido, sai kuma ya rabata da jikinsa game da sanya mata suit ɗin nasa. Ya kama hannayenta suka nufi wajen haɗaɗɗun kujerun da aka tanada kusa da beach ɗin dan cin abinci. A nan suka zauna saman kujerun dake kallon juna, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya mallaketa ya gama, a daidai lokacin kuwa Abba na can suna plan da Ammie kan a cikin satin nan zai kawo ziyara gidansu Seraphina, Ammie ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari saboda dama Seraphina ta shiga ranta. Sai shagwaɓa take zuba mashi tana ƙarawa, shi kuwa yana ta biya mata, a wannan dare ya shirya masu abubuwa dayawa, dan har wajen CP zasu fita. Ƙayattatun abinci aka kawo masu wajen, da kansa ya dinga ciyar da ita, sai santi take yi tana karawa, sai da ya cika mata ciki tab, sannan ya ci ɗan kaɗan, ya tashi ya kama hannunta suka nufi cikin mota, daga nan suka nufi ainahin main gate na CP ɗin, sai murna take yi yau zata fita waje, shi kuwa sai farinciki yake yi na ganin tana murna. ------------------------------🔥 D-------O--------L🔥 Around 1 na rana, bayan sun yi sallar azahar sun yi lunch, suka zauna Noor yana ɗaukar karatu wajen Leo, while Zaynish ya haɗa kayansa ya nufi bakin ruwa dan yin wankin kakinsa, ya ce ba zai iya baiwa ƙananan sojoji su yi mashi ba, saboda shi in mutum ne yai mashi wanki yana ganin baya fita, ya fi so ya yi da kansa. Vash yana zaune a kan wani dutse yana shan mangoron da sojojinsu suka ciro a wata bishiya da ta nuna gwanin ban sha'awa. A can kuwa, Arya da su Angelina suna ɗaki, Manassa na zaune gefen mattress rike da drink a cup a hannunta tana sha, while Angelina na rike da laptop, yanzu ta mayar da hankali kan aiki sosai, saboda Zaysh baya ɗaukar wasa. Shigowa cikin room ɗin V ta yi, tana ɗan ɗingisa kafa, ba jimawa ta farka daga barci ta yi wanka, tana sanye da kaya marasa nauyi. Kallo suka bita da shi, suna shirin yin magana sai gani suka yi ta ɗauki wayanta ta nufi waje, bayanta suka bi da kallo. Kusan a tare suka miƙe Manassa rike da cup na drink ɗin suka biyo bayan V dan su ji meyasameta, sun ga idanunta sun yi jajir sun kumbura tamkar ta sha kuka, ga shi tana ɗingisa kafa, abinku da shagwaɓɓaɓiya sai shagwaɓe fuska take yi. A bakin tantinsu suka isko V tsaye tana ƙoƙarin kara waya a kunne, Arya rike da hannun Jehan, Manassa ta zauna a wannan dutse dake bakin tantin nasu tana kora drink ɗinta, Angelina ta tsaya gefen Manassa ɗin, suka tsaya jiran ta kammala waya. A natse murya can ƙasa ta ce. "Hello friend". Ta faɗa tana ɗan matsawa daga kusa da su Angelina, taga miss call ɗinsa sama da 20 ne daga daren jiya zuwa yau, shi ne ta ce bari ta kira ta ji menene, wannan causin ɗin nata ne. Daga can ɓangaren ya ce. "Ina kika shiga ne beb, tin jiya ban jiki ba, dik na damu, na yi kawarki sosai, na yi kewar daddaɗar muryar nan taki"........ "Sorry friend, nima ai na yi kewarka kuma na yi kewar daddaɗar muryanka ɗin, aiki ne ya sha kaina, ya su Aunty Bee?". "Suna lafiya to ya aiki?"....... Ɗan juyawa ta yi zata amsa da lafiya idanunta suka sauƙa a kan Noor dake tsaye ta bayan tantinsu, ya yi folding hands ɗinsa a kirji, kallonta kawai yake yi, fuskanta a tamke tamau, dik ya canza. Ya shiga cikin tantinsa ne yaga bata ciki, to sanin bata jin daɗi yasa ya ce bari ya dubota, sai ya bi ta bayan tantin nasa zai shigo nasu kenan ya ji tana cewa ta ki kewar daddaɗardl muryan friend, shi ne ya tsaya a wajen. Ai jikinta take ya hau rawa, ta wani irin mugun shan jinin jikinta, da sauri ta zare wayar daga kunnenta, tana ƙoƙarin yi mashi magana ya matso cikin zafa ya kwace wayar, wancan karon ma da ya raga mata dan bai san me mata yake nufi gabaɗaya ba, aikuwa yanzu ya sani, dan haka bai ga dalilin da zai sa wani ya nemi shiga harkarsa ba, yanzu auren sunnah ma suka yi bana zobe ba, kuma ya je duniyar sama jiya ai sai shiru. Jikinta na rawa ta sake mashi wayar tana kallonsa. Bin kan screen ɗinta da kallo ya yi, sai ya kara wayan a kunnensa, a daidai lokacin Friend yake ce mata. "Da gaske voice ɗina na maki daɗi beb?"........ Wani irin tsananin takaici ne ya turnuƙe zuciyansa, a fusace ya ce. "Who the hell are you?!". Zuba mashi idanu su Manassa suka yi, zallar kishi ne malam a kan fuskansa, har idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir. Kit Friend ya katse kiran, dan a tinaninsa oganta ne a wajen aiki. Bin kiran Noor ya yi, amma ba'a ɗauka ba, cikin zafa ya ɗago da kallonsa a kanta. Hannu ɗaya ya zura cikin aljihun combat trouser dake jikinsa, ji ya yi tactical tshirts dake jikinsa ma zafi take haɗa mashi tsabar ya fusata, abin takaicin yai mata warning a farko ranar, amma yau ta sake yi. Cike da zafin kishi ya ce. "His voice is so sweet, and you missed him so much, who's he?!". In a harsh way ya faɗa, hakan ya ja hankalin sauran sojojinsu dake sansanin, amma dik sai suka yi ƙasa da kai tin da ogansu ne a wajen. Gagara bashi amsa V ta yi, idanunta suka ciko da kwallah, hannunta sai kerma suke yi........ "Okey you love his voice, you missed him? You love him right? You want to marry him?". Cikin zafin kishi ya faɗi maganar, bai ma san me yake faɗe sosai ba. "Please stop it, stop saying that, It's not what you're thing......". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar..... Wani irin mugun kallon da ya dallah mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya maka wayar tata da ƙasa, take ta tarwatse raga-raga. Hannu bibbiyu ta sanya ta toshe bakinta jikinta na tsananta kerma, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne ya fara zuba tamkar an buɗe tap, da kyar ta iya ɗagowa ta kalli rikitatcen face ɗinsa da gabaɗaya ya canza, har ja fuskar tasa ta yi tsabar fushi. Sai ma in ya tina ta ce i missed you and i missed your sweet voice, ya rabb, sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya. Muryarta na rawa ta fara ƙoƙarin sake yi mashi magana ko zata dace. Cikin zafa ya ɗaga mata hannu game da cewa. "Don't say anything here!!". Ya faɗa yana pointining ɗinta da hannunsa. Ba shiri ta haɗiye abin da take son faɗe, jikinta ya tsananta kerma sosai wanda yasa ta gagara iya rike kanta dama ba lafiya ba, sai kawai ta durkushe ƙasa a wajen, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi. Da gudu Angelina ta kariso in da take, durkushewa ta yi ta rungumi V a jikinta tana satar kallon Noor dake ta uban huci tamkar zai kama da wuta. Gabaɗaya takaicinsu ya gama cika Arya, ji take tamkar ta shake V da ta zubar masu da mutunci take baiwa namiji hakuri a kan laifin da bata aikata ba, yaushe ta ce tana son friend?. Ita dai Manassa abin da kowa ya sani ne, watau komai normal, bata wani damu ba, dan faɗa tsakanin V da Noor ai ba sabon abu bane, zama su shirya ne babu wanda ya sani, ranar da suka yi wancan uban faɗa waye ya taɓa zatan zasu shirya? Ba sai ga shi ko kwana ɗaya ba'ayi ba har sun shirya! Dan haka su rataye kansu idan sun ga dama ita babu ruwanta. Noor ne ya cika baƙin kishi, ga ɗan banzan saurin fushi, ya koyi saurin fusatar Leo, in ban da haka yanzu me abin fasa mata waya daga jin tana magana da wani? Ko damar yin magana yaki bata, shi sarkin zuciya. Siririn tsaki Arya ta ja tare da juyawa da sauri ta bar wajen, dan zata iya kai duka idan ta cigaba da tsayawa. Manassa dai hannu ta miƙa ta ɗauko drink ɗinta dake ƙasa ta cigaba da sipping, dan ita faɗar ma sugar yake mata, ai in basa faɗar basu cika masoya ba. Juyawa Noor ya yi cikin fushi zai bar wajen. Da sauri muryarta na rawa ta ce. "Please, my heartbeat, just listen to me, give me one chance to tell you who I truly am, don't be upset with me for a mistake I never made, let me hold your trust close to my heart". Ai ko kallon in da take bai sake yi ba, da sauri ya wuce gudun kada ya kai mata duka, dan wlh ya rike kansa ne, ba dan haka ba time ɗin da take cewa friend voice ɗinka da daɗi da sai dai ta ji hakwaranta a ƙasa ya zubar mata saboda balain kishi. Ita ma bata ji, gata mai aboki, ai taga aboki yau kam. Wucewa ya yi ya barta a wajen, ta rungume Angelina tana wani irin kuka mai ban tausayi, dama ga ciwon da ya ji mata. Shi kuwa cikin tantinsa ya koma, ya zauna a gefen mattress yana huci. After like 5 mins ya miƙe cikin zafa ya fito. Suna nan in da ya barsu, Arya da Jehan ne kawai suka koma ciki. Su ya nufo gadan-gadan, yana zuwa ya ɗauki V cak sai saman buɗaɗɗiyar kirjinsa, cikin zafin jini ya wuce cikin tantinsa da ita, ba zai iya barinta tana kukan nan ba dan yasan bata da lafiya, kada wani ciwon kuma ya kamata. A saman mattress ya kwantar da ita, a tsawace ya ce. "Ki mun shiru, idan na sake jin koda tarinki ne sai kin gane kuranki". Babu wasa a tattare da shi ya faɗa. Hannu tasa ta toshe bakinta game da haɗiye kukan nata, tana kallonsa cikin ido, ya dallar mata harara kafin ya miƙe ya fice ya barta kwance, sai shessheƙar kuka take yi. Lamarin Noor da V sai su wlh, ga balain kaunar juna ga zafin kishi, ga kuma faɗa, kai suna bani ciwon kai. After some hours. Bayan sun yi sallar mangrib da ishai, sojojin dake sansanin suna hakin wuta, har team one suna tare a bakin wuta except Leo dake cikin ɗakinsa, V tana ɗakin Noor kwance zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da ta sha ga ciwon da angon nata ya bata jiya, sai zazzaɓi ya rufeta, har yanzu kuma Noor yana kan dokin zuciya, yaki sauraranta, da ya kawo mata abincin dare ma tana son yi mashi magana ta faɗa mashi tana jin

Chapter 89 of 95