ji kara a ɗan gaba da su kaɗan. Da sauri suka kai kallonsu a wajen, sai kuma suka juya da sauri suka nufi wajen, bakin Arya cike da tarin tambayoyi kan drone da V ta tura, waye ya harbe drone ɗin? Su waye a wajen?.
Da gudunsu irin na sojoji suka isa in da suka ji wannan kara. Tin daga nesa suka fara hango mutane tsaye cirko-cirko a wajen wasu bukkoki. Da sauri suka ƙarisa wajen. Cikin jama'ar suka kutsa, nan suka ga wata mata tsaye, daga ita sai ɗaurin kirji, ga wani namiji a tsaye rike da igiyar ɗaure shanu yana dukan matar sai kuka take yi, jama'ar dake kewaye dasu babu wanda ya tsoma baki a ciki bare su kwaci matar, macen yarinya ce da bata wuci 15 years ba, gata kyakkyawa, irin fulanin nan ne na tashi wanda suke kewaye duniya, yau ka gansu a nan gobe ka gansu a nan, babu dajukan da basa shiga.
Wannan igiyar shanun ya ɗaga, babu tausayi ya fara zubawa yarinyar a jiki yana, ihu ta cigaba da yi tana bashi hakuri, dik da su Arya basa jin yarensu, basa gane me suke faɗe, sun gane hakuri yarinyar take baiwa mutumin, ga yarinyar jikinta dik ya yi ruɗu-ruɗu abinku da farar fata, har da ɗan jini-jini a jikinta, ta ƙanƙame zanin jikinta da ya kwance, ta durkutsa ƙasa tana bashi hakuri bata gudu ba, gashin kanta dake cike da yawa da tsawo ya warware ya zubo mata a fuska da baya.
Ai wani irin tsuma jikin Arya ya fara yi, bata bari a zalunci wani a gabanta, ji ta yi zuciyarta na tafarfasa tamkar an ɗaura dalma a wura, bata san lokacin da ta afko cikin fili ta danki bulalar ba, mutumin yana ƙoƙarin kwace bulalar da karfi yana wani irin huci Arya ta fisge da karfi daga hannunsa ta jefar gefe.
Take jama'a suka ja da baya suna zazzare idanu da alamar razana a kan fuskokinsu, dik yadda aka yi suna mahaukacin tsoron mutumin shiyasa basu shiga sun karɓi yarinyar da yake duka ba.
Cike da faɗa da jahilci ya yi kan Arya zai fara dukanta kenan ta sanya kafa ta takesa sai da ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa. Ɗagowa ya yi ya kalleta, ganin macece yasa ya sake miƙewa ya yi kanta, ai wasu tagwayen maruka da ta ɗaukesa da shi sai da ya ji duniya ta tsaya mashi gum, ya ji ya daina jiyo sautin komai.
Da sauri V ta matsa ta ɗago yarinyar da ake dukan, numfashin yarinyar sai sama-sama yake yi yana ƙoƙarin ɗaukewa, ita kuwa Arya da zuciyar sojojin ta motsa, belt na tactical trouser ɗin jikinta, idanunta ya rufe da jin kishin mace ƴar uwarta, bata ji bata gani ta fara tabkawa mutumin nan wannan tactical belt ɗin namu na sojoji, ta ko'ina ta fara sauke mashi a jiki tamkar wacce aka yiwa wahayin duka. Mutumin yana ƙoƙarin miƙewa tasa wannan shegiyar takalmar tasu ta take mashi kirji sai da ya yi baya-baya ya kwanta, ta take kafafunsa da karfi ta kafarta ɗaya, duka ba na wasa ba ta fara yi mashi, irin dukan zuciya a kusan nan, ya za'ayi ace yana yi wa mace irin wannan dukan? Macen ma yarinya ƙarama wacce bata gama mallakan hankalinta ba, dik ya fashe mata jiki ruɗu-ruɗu da bulala.
Ai tin yana daurewa har ya fasa baki ya fara kurma ihun da ya sanya dajin ta fara amsawa, kafa Arya tasa ta kai mashi duka a bakin nasa. Abinku da ruɓaɓun hakwara tuni bakin ya fashe sai jini, dukansa ya dinga yi ta ko'ina babu sanya. Tin yana kokarin kare kansa har ya kwanta flat a ƙasa yana wani irin numfashi mai nauyin gaske, ɗan banza ya ji bugun sojojin AZURE.
Sai da su V suka ga numfashinsa na shirin ɗaukewa ne Angelina ta yi zafan afkawa cikin wajen ta riko Arya tana......
*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581*
Likes comments and share fisabilillah.
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-25.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 65 & 66
Sai da su V suka ga numfashinsa na shirin ɗaukewa ne Angelina ta yi zafan afkawa cikin wajen ta riko Arya tana tausanta, ba dan Angelina renon AZURE bace da ba shakka yau ba zata iya rike Arya ba, da kyar ta jata baya daga kan mutumin. Sai huci take yi tamkar zata kama da wuta.
Kama matar V ta yi, ta miƙar da ita tana ƙoƙarin tambayarta me yake faruwa wannan mutumi yai mata duka haka?. Matar sai nishi take yi, hakan yasa V ta ce a bata ruwa, su kawo mata ruwa ta baiwa matar. Dik wajen babu wanda ya kula V, ga shi ita bata jin yarensu, su kuma basa jin turanci.
Sake matar ta yi, ta nufi mutane tana masu ƴar kurma-kurma wajen nuna masu da hannu alamar zata sha ruwa. Darewa mutanen suka fara yi suna ja da baya alamar ba zasu basu ruwan ba, tsoron sojojin ma suke yi.
Baya V ta koma tana mamakin mutanen, daga bayanta ta ji an taɓata, cikin zafa ta juya, tana juyawa taga wannan yarinya da suka haɗu a mission na gudanci Avaris, yarinyar tana rike da kwarya mai ɗauke da ruwa tana miƙawa V ɗin.
Zazzare idanu a kan V ta yi, ta sha kuka sosai yarinyar, idanunta sun yi jajir sun kumbura, karɓar kwayar ruwan V ta yi, ta gagara zare kallonta daga kan yarinyar. Da sauri V ta nufi wajen matar, ta ɗan ɗagota ta fara bata ruwan.
Sosai matar ta sha, sai da ta kusa shanye rabi, sannan ta ɗauke kai tana nishi...... Shiru wajen ya yi, after like 10 mins, kura ya ɗan lafa, wannan yarinya ta zo ya rungume wannan mata suka cigaba da kuka a tare.
Ai Arya na ɗagowa ta kalli yarinyar bata san lokacin da ta baro jikin Angelina tana zazzarewa yarinyar idanu ba, ita ma yarinyar zare mata idanu ta yi ganin Arya, tabbas ta tunasu yanzu. Da gudu yarinyar ta miƙe ta ƙarisa wajen Arya.
Rikota Arya ta yi, ta rage tsawonta wajen durkutsawa a kan gwiwowinta, ta rike kafaɗun yarinyar tana kallon fuskanta. Cikin harshen fillanci na bororin daji yarinyar ta ce da Arya. "Please ki taimaki addata, mijinta mugu ne, dan ta bani abinci shi ne ya ce zai daketa, ta bashi hakuri, shi ne da ta fita yawon neman itacen da zata yi girki ya zo ya cire mun kayana, ya kwantar dani a gadonsa ya hau kaina, da ta dawo ta gansa ta ture shi daga kaina tana ihu, shi ne ya fara dukanta wai zata zubar mashi da mutunci". Tana kuka tamkar ranta zai fita tana magana, dik tana birkice
Dik da Arya bata jin yarensu ta gane nufin yarinyar saboda kwatancen da take yi da hannunta, ta nuna ya cire mata kaya, ta nuna ya kwantar da ita, ta kuma nuna ya hau kanta, sannan ta nuna wancan matar ta ture shi, yanzu Arya ta fahimci fyaɗe kenan ya so yi wa yarinyar sai ALLAH ya dawo da matar tasa, dan ta dakatar da shi tana ihu ne ya hau dukanta, abin da ake cewa borin kunya, tabarmar kunya da hauka ake naɗeta.
Ai wani irin tafarfasa Arya ta ji zuciyarta yana yi mata, a fusace ta saki yarinyar ta miƙe, gadan-gadan ta nufi mutumin, su dama ai aikinsu shi ne dakatar da ɓarna, kansa ta yi, ta zare ƙaramin wuƙarsu na sojoji dake da mazauni a jikin takalmarsu.
Zare wuƙar ta yi, yana wani kyalli saboda kaifinsa, mutumin yana baje a ƙasa yana nishi sama-sama. Ai tana zuwa ta damki mazargin wandonsa, zata yi mashi kaciya part two tin da shi ɗan iska ne!.
Nan fa mutanen dik suka watse suka fara ihu, wasu mata ƙalilan ne suka tsaya, basu wuce su 8 ba, suka tsaya suna kallon Arya cike da jarumta. Cikin harshen fillanci suke cewa Arya ta kashe shi, saboda dikkansu ya keta masu haddi, ya masu fyaɗe, ba mutumin kirki bane, ga shi kuma shi ne sarkinsu a wannan tafiya, haka yake amfani da matsayinsa na shugaban tafiyar yana keta haddin mata, dik kuma ƴan uwa tsoronsa suke ji, saboda zafinsa da mugunsa.
Ya dakeka ya hanaka kuka haka yake yi. Arya bata jin me suke faɗe, ita dai ta nufi yin abin da ta yi niyya kawai. Ko kaɗan Arya bata razana ba, ta zare wandon mutumin nan, da wata abar tasa kamar karas saboda ƙanƙanta sai iskanci cike da kai, aikuwa Arya ta gille abar, tai mashi kaciya part two, tin daga ƙasanta ta yanke mashi ta jefar, sai ta yi jefa da wukar tata game da zare hand groves ɗinta ta zubar a wajen. Tana wani irin huci tamar zata kama da wuta, jinin mutumin ya fallatsa har kan hand gloves ɗinta ba iya wuƙar ba.
Shi kuwa wani irin ihun azaba ya zunduma a lokacin da ta yanke, ihu ɗaya kuma ya kurma ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya suma. Abin da Arya ta yi ya yi matuƙar gigita wannan yarinya, ihu ta kurma ita ma game da rikicewa ta rasa ina zata nufa, hakan yasa Angelina ta rikota game da rungumeta tana ɓoye mata fuskarta kan ta daina kallon mutumin ma.
Ganin haka yasa wani matashi dake laɓe yana jiran ganin me Arya zata yi wa mutumin da ta zaro wuƙa ne ya dallah da gudu ya nufi cikin daji. A razane yarinyar ta fara nuna mutumin tana ihun tana faɗin har da shi ma yana cire mata kaya idan Addar tata ta tafi yin ita ce, yana cire mata kaya ya hau kanta, shi ma ƙanin wannan mutumi ne.
Ai da gudu Arya ta bi bayansa shi ma, sai dai bai yi wani nisa ba ya ci karo da Zaynish da ya fito daga bakin ruwa, jin ihu a wajen yasa ya zo duba menene?.
Karo matashin ya yi da Zaysh, ya bugi kirjin namiji, sai ga shi a kasa wanwar, daidai lokacin Arya ta iso gaban Zaysh da gudu tana nishi sama-sama. Kallo ɗaya Zaysh yai mata game da ɗauke kai kafin ya ce. "Lafiya?". A daidai lokacin matashin ya miƙe zai cigaba da gudu kenan Zaysh yasa kafansa ɗaya ya kwashe kafafun matashin a in da ya zube ƙasa.
Ƙamewa Arya ta yi tare da sarawa Zaysh kafin ta kora mashi jawabin abin dake faruwa. Ta faɗa game da nuna mashi ƴar yarinyar da ya yi wa fyaɗen. Kallo ɗaya Zaynish ya yi wa yarinyar, take ya ɗan rintse idanunsa, jikinsa har wani tsuma ya fara yi yana wani jijjiga saboda takaici, a yadda yaga yarinyar nan ha zata wuci 10 to 11 years ba, me ta sani da zasu yi mata fyaɗe?.
Ai Zaysh bai san lokacin da ya damko matashin nan ba, wani irin jibga da ya fara yi mashi ko amaryar Aunty Ummi bai yi mata ba, ya dinga gwara kansa da jikin itatuwa. Sai da ya yi mashi lilis har matashin ya daina motsi, ya fashe mashi baki da hanci a in da ya haɗe mashi jini da majina.
Jifa dashi ƙasa ya yi, ya kai hannunsa ya ware zariyar wandon matashin, ɗago idanu a kan Arya dake tsaye tamkar an sassaƙata ya yi, ta gane nufinsa, da sauri ta juya ta bar wajen, watau kada ta ga sirrinsu na maza, bai san Arya kam yanzu ya gama yi wa wani sabon kaciya ba.
Tana barin wajen ya zaro wuƙarsu na sojoji dake jikin takalmansu ta jefe, shi ma babu tausayi ya datse mashi abar daga jijiyarta ya jefar. Wani irin azababben ihu da matashin nan ya kurma sai da gabaɗaya dajin ta amsa. Zaynish sai huci yake yi ya bar wajen ya bar matashin a baje a ƙasa.
Ƙarisawa wajen da su Arya suke Zaysh ya yi, dan ya duba ko akwai wata matsala. Nan ya isko Arya ta tasa wannan matar mutumin a gaba tana yi mata bayanin ƴar kurma-kurma game da wannan yarinyar. Matar ta ce. "Wannan yarinyar dai a can yawonmu na fulanin tashi muka tsintota a cikin daji, dikka ƴan uwana sunki ɗaukarta, amma ni a matsayina na wacce na taso a gidanmu ina da ƙanwa kamarta, sai na ce zan ɗauketa, mijina ya ce ba zai ciyar da ita ba, haka na yarda na ɗauketa, muna rayuwa da ita a gida, mijina baya bata abinci, ni nake shiga daji in nemo mata abin da zata ci. (ALLAH sarki shiyasa ranar take kukan yunwa su Arya suka bata abinci a kudanci) Mijina baya sonta, ya sha korarta waje ta kwana a waje ita kaɗai, ga shi bamu san kowa nata ba, mun kasance tare da ita tsawon shekaru biyu muna yawo ƙasashe, tin bata iya yarenmu ba har ta koya, bamu san danginta ba, bamu san kowa nata ba".
Hakika basu fahimci maganar matar dikka ba, amma sun ɗan fahimci wasu, sun gane tsintar yarinyar suka yi, sannan sun gane cewa wannan mutumi mijin matar nan ne, sun gane yana ganawa yarinyar azaba.
Da yake ba komai suka fahimtar ba sai Arya ta miƙe tana faɗin. "V muje". Ta faɗa da nufin su tafi su barsu a wajen tin da sun hukunta mutumin........ Zaynish da yakasance namu ne, ɗan mutan Niger girman Nigeria, tsab yana jin fillanci, sai dai baya jin na bororin daji sosai, shi ma bai gane komai yadda yakamata ba, amma ya fi su Arya fahimta.
A dake cikin bada umarni ya ce da Arya. "Ki ɗauki yarinyar ku wuce da ita sansani, idan mun koma gida zamu miƙata ga gwamnati a nemi iyayenta, waɗan nan suma tsintarta suka yi". Yana gama faɗar haka ya juya. Da sauri Arya ta kama hannun yarinyar, dan dama ta shiga ranta matuƙa, tin da ta fara kallon yarinyar a kudanci ta ji ta kwanta mata.
Jan yarinyar suka yi, suka tafi suka bar matar da mijinta da sauran Fulani a wajen. Sansani suka koma, yarinyar ma ta ƙanƙame Arya sosai, da alama jininsu ya haɗu sosai, sai shasshafa hannun Arya yarinyar take yi kamar taga wani abin. Kai tsaye cikin tantinsu Arya ta shige da ita, ta zaunar da ita kafin ta ɗauko mata ragowat abincin safenta, da alama Arya na son yara, dan kuwa zama ta yi ta dinga baiwa yarinyar abinci a baki, bata ji kyamarta ba sam.
Yarinyar tana cin abinci tamkar yadda dabbobi suke ci, babu wani control, turawa kawai take yi, hakan yasa Arya ta ɗaura ɗamara, ta dinga nuna mata yadda zata yi a natse. Su V dik sun zuba idanu suna kallonsu.
Sai da ta tabbatar yarinyar ta ƙoshi, sannan ta bata ruwa kafin ta ce su je ta yi mata wanka, dan ta yi datti over, sai wari take yi, ga ƙananan kyawawan hakwaranta sun yi jajir saboda rashin yin brush, fuskanta dik a ƙoɗe. Su dai su V kallo ne kawai nasu, yau karon farko a rayuwansu sun ga Arya ta damu da wata, watan ma talaka, ƴar kauye, ƴar datti, kai wannan abu ya basu mamaki matuƙa, basu san so gamon jini bane, Arya irinsu ne mutanen da ake kira RESERVED PERSON, gaskiya irinsu basu da yawa a cikin al'umma, suna da tausayi amma a ɓoye, su komai nasu a ɓoye yake, basa bayyana kansu kai tsaye haka, sai dai jama'a su gane waye su ko su fassarasu yadda suke so, amma su kaɗai suka san ainahin waye su, zaku ganesu ne kawai ta aikinsu a aikace ba su fito fili su faɗa maka waye su ba, dik yaran GAT ita kaɗai ce wannan gifted ɗin.
Wanka ta yi wa yarinyar a cikin tantin da suka kafa da sunan toilet, da kanta ta ɗebo ruwa a bakin teku, ta wanke mata wannan uban gashin kan nata dake da mugun yawa, tsantsi da tsawo, dan har ya ɗan zarce mazaunanta a tsawo, ga shi bakinkirin da shi har yana wani curlyn.
Da shampoo na SB-LUSH (Stars body lush shi ne na taƙaita maku da SB-LUSH) sai kamshi shampoo ɗin gashinta yake yi, take ya ɗauki kyalli. Arya ta naɗeta da towel ɗinta suka fito suka koma cikin tantinsu, ta shafe yarinyar da mayukansu masu daɗin kamshi, sannan ta ɗauko doguwar rigar dake tsaya mata a cinyoyi ta sanyawa yarinyar, ya kai mata harƙasan gwiwa.
Zaman gyara mata gashi Arya ta yi, tana tajewa yarinyar tana kuka saboda zafi, haka Arya ta dinga ce mata sorry har ta gama gyara mata, sannan ta shafa mata mai, ta ɗaure mata a tsakiyar kai game da kitse mata jelar, ta yi mata rolling na jelar jikin tibka.
Take yarinta kyanta ya fara fitowa, ta ji gyara, kamanninta da Leo ya ƙara bayyana, bare ma idanun nan nasu. Wajen kwanciyarta Arya ta kwantar da yarinyar. Baiwar ALLAH, tata ci ta ƙoshi, ga wanka da aka wanke mata dauɗa, aka rabata da dattin gashinta, sai ta ji duniya sakayau, wani niimantaccen iska na shigarta, tuni ta ɓige da barci.
Ita kuwa baiwar ALLAH Arya sai ta jawo laptop tana faɗin V ta zo ta faɗa mata kilomita nawa ne tsakanin daga nan zuwa in da aka harbe drone ɗinta. Jawo laptop dinta V ta yi, ta fara kora mata bayani.
Nan Arya ta fahimci suna da mugun nisa daga in da suke da in da aka harbe drone ɗin, rucksack ɗinta ta jawo, ta fito da ɗan karamin drone mai kama da fly, irin ƙananan ƙidajen nan, ba zaka taɓa cewa camera bane, wlh zaka zaci ƙuda ne, na sirrinsu ne, sai abu ya yi tsamari suke tura irinsa. Shi ta saita ta yi connecting na camerar da laptop ɗinta, sannan ta sakesa game da fara controlling ɗinsa ya nufi in da aka harbe na V.
While Leo yana zaune bakin ruwa shi da Noor, suna waya da Captain Onbish, kun san yi mugun sabo da Captain a lokacin training, shi ne ya kira Captain ɗin yana son latsa shi ya ji ko akwai wani ƙarin haske da zai samu kan manyansu na soja, dan yanzu ba sojojin ruwa kawai yake zargi ba, har da nasu sojojin.
Sun jima suna waya da Captain, sai kara kwarara masu gwiwa Captain yake yi, daga karshe Captain ya ce. "Ban taɓa son wasu sojoji da na horar irinku ba, ba zan so mu rasa haziƙan sojojin irinku ba, Nirash ka kula sosai, arewaci ya sha banban da kudanci, sannan shawarar da zan baka ta ƙarshe, wannan daga zuciyata ce a matsayin aboki ba shugaba ba, lallai ba umarnin kowa zaka karɓa ba a lokacin da kake tsakanin mutuwa ko rayuwa, a wannan lokaci ka ɗauki umarni mai kyau ka watsar da mara amfani, sannan kada ka yarda da kowa a bakin aiki, kowa yana iya cin amanarka a bakin aiki, dayawan mutane abin duniya na canzasu a lokacin da baka tsammata ba, dayawan manyan sojojinmu masu gaskiya an kaisu ƙasa ne tare da sa hannu da haɗin bakin na jikinsu, gaskiya ta yi ƙaranci, dan haka team 1 ku kula matuƙa, ku riƙe amanar junanku, kada ku yarda da kowa".
Tin da ya fara magana Leo ya yi shiru yana saurarensa, da ya kammala okey thank you sir kawai ya ce mashi, suka yi sallama. Shiru Leo ya ɗan yi yana tinanin kalaman Captain bayan ya katse kiran, lallai ya samu ƙarin haske bana wasa ba. Captain bai fito ya faɗa mashi me a karkashin ƙasa ba, amma waɗan nan maganganun sun fi wa Leo komai, watau dik wani soja da za'a kashe da haɗin bakin sojoji na kusa da shi.
Kuma haka ne, ya za'ayi a kashe soja ba tare da haɗin bakin na kusa da shi ba? Impossible ai, ya samu karin haske a nan, sannan Captain ya ce ba kowani umarni kai tsaye zai yi amfani da shi ba, which's mean akwai umarnin zalunci kenan. Kun san wani abu ne jama'a, a lokacin horar da soja ana basu tsastsaurar wahala a kan bin umarni, ana sanya masu tsananin tsoron rashin bin umarni, ana nuna masu rashin bin umarni azabar tafi ta mutuwa, zaka ce gara mutuwa, shiyasa zaku ga soja idan manyan su suka bashi umarni, ko kuma zai yi zai tsaya a kan wannan umarni.
Kun san azaban da akewa soja idan yaki bin umarni? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, hakika soja zai gwammaci mutuwa da hukuncin taka umarnin manyansa, ya rabb, azaba sai ta zautar da shi, tsoron wannan hukunci yasa yake binsu a kan komai, yana mantawa azaban lahira ta zarce ta duniya. Idan mutum yana da hankali hakika ba zai taɓa zagin ƙananan sojojin dake karɓar umarni daga sama ba, su tamkar juyasu ake yi, komai ba su suke yi ba, gangan jikinsu yake yi da kuma bin umarni! Laifin yana sama.
Bayan sun gama waya ne ya dubi Noor dake faman kallon ruwa. A natse sosai ya ce. "Brother ina son Captain sosai". Ba tare da Noor ya juyo ba ya amsa da. "Sosaima, yana da kirki matuƙa, da alama kuma yana da gaskiya"....... Kai Leo ya jinjin alamar haka ne.
Shiru ya ɗan biyo baya kafin can kuma Leo ya ce. "Zan zama mutum na farko da zai kawo abubuwa dayawa a hukumar soja, zan canza tarihi, zan zama silar canzawar doka ta duniyar hukumar soja"....... Noor dake da buri irin nasa ne ya amsa da. "Zamu zama tare! Amma yanzu ya zamu yi da sojojin can da muka kama?".
Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Da farko na so faɗawa Captain sai na manta, amma bari in faɗawa yayana ya bani shawara, ni ina tinanin in sakesu dan basu da amfani a garemu". Ya kai karshen maganar game da ciro wayansa, ya laluɓo number da aka yi saving da my champion, ya dannawa Aryan kira, dan yasan shi ne kawai a cikin IRON FIST zai sauraresa a gaggauce ya bashi amsa, Lion ai sai ya mashi kira 10 bai ɗauki ɗaya ba, daga karshe in ya tashi saƙo zai ajiye mashi a Whatsapp, shi kuwa guru da waya ma bata wani damesa ba, zaka kira sau uku baka jisa ba, Vir ya fi su dikka rashin damuwa da waya, dik kuma ba zasu faɗa mashi yadda zai yi ba, zasu ce ya girma da kansa, ya yanke hukuncin da ta dace, dan suna son gobensa ta yi kyau ta yadda ko babu su zai tsayawa kansa.
Shi kuwa Arya komai yaya sai ya taimaka mashi, ko da shawari ne...... Bugu ɗaya Aryan dake kwance saman gado ya tada kai da cinyar Lion ne ya ɗauka game da cewa. "Hello boy".
Kara natsuwa Leo ya yi kafin ya ce. "Bro dama shawara nike son ka bani"...... Satar kallon Lion Aryan ya yi, saboda yasan Lion ɗin ya hanasu tsoma baki kan Mission ɗin. "I'm listening". Aryan ya faɗa. Nan Leo ya kwashi dik abin dake faruwa ya faɗa mashi.
Nisawa Aryan ya ɗan yi, su IRON FIST wannan ai a wajensu ba abin mamaki bane, su da suke tare da ainahin manya masu ɓarnar, Leo ne bako yake ganin cin amanar ta yi zafi dayawa har da sa hannun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 81 Chapter of 95