dan kawai biyan buƙatarka, ai kai mutuwarka ba zata yi kyau ba, wlh 3D bala'i ne, ni ban taɓa jin kalar wannan rashin imani! Ba gara ma ace zina suke yi da yaran ba ma da ɗan sauki, amma kowani watan duniya ku kwantar da yara ku danna masu karfe a cikin ciki, ku wuce mahaifarsu har ku je kan ovaries ɗinsu, ku buɗe jakar da eggs ke ciki ku tura wannan karfe, ko wani iri baku ji a ranku, saboda kun yi hannun riga da tausayi da imani, ba sauɗaya ba ba sau biyu ba, dan bala'i kullum wata sai kun masu wannan abu, ga uban alluran da kuke kashe masu jiki da shi, dan wannan alluran lalatasu zai yi gaba kaɗan, ai kuna masu shi overdose, yana da side effects, yadda kuka san engine buga eggs suka samu ba mutane ba, shegu tsinannu makiya ALLAH da Manzonsa, hmmmm zaku girbi abin da kuke shukawa ne dan ubanku.
Astagfirullah, 3D sun ɓatan rai sun sakani zagi shegu!
Sun jima suna tattaunawa wanda ni takaicinsu ba zai barni in cigaba da kawo maku labarin abin da suke tattaunawa ba, daga karshe Dr James ya ce. "Zo ka mun video dan turawa WS shaidar aikin maganin nan, zo ka ɗaukeni bari mu yi gwaji a kan ɗaya daga cikin jariran nan mu gani".
Na shiga uku ni QUEEN OF SURPRISE, a kan jariran ma zasu yi gwajin cutar dan bala'i? Wannan wace iriyar musifa ce? Tamkar babu zuciya a kirjinsu fa!.
Da okey suka amsa mashi, ya wuce gaba bayan ya miƙawa Dr Kamal wayansa, bayansa suka bi, wancan ɗakin da ake haɗa magungunar suka koma, jim kaɗan suka fito hannun Dr James rike da wata sirinjin allura da kuma ruwan maganin.
Kai tsaye SECTION D suka nufa, dik in da suka wuce sai nurses sun zube ƙasa sun kwashi gaisuwa. Basu amsa kowa ba har suka shiga cikin ɗakin da su sister Zinta suke.
Su Maya na ganinsu suka zube ƙasa dan kwasan gaisuwa. Wucewa ciki Dr James ya yi, ya fara bin yaran yana dubawa ya ga wanne yakamata ya ɗauka dan ayiwa gwajin alluran nan?.
Daidai lokacin darling dake hannun sister Maya ya fara kuka, miƙewa tsaye da shi ta yi, ta fara jijjigasa tana shafa bayansa, ta saɓashi a saman shoulder ɗinta. Ɗago kai Dr James ya yi, zubawa babyn idanu ya ɗan yi, can kuma ya nisa tare da cewa Maya. "Bani shi a nan"........ Bata kawo komai a ranta ba, ta yi sauri ta miƙa mashi shi. Karɓarsa ya yi tare da cewa Dr Mark. "Jawo mun bed ɗinsa nan". Ya faɗa tare da fitowa gaban ɗakin.
Sister Zinta dake zaune ne ta miƙe tsaye, idanunta na ɗan rawa a kan sirinjin alluran dake hannun Dr James, mamaki ya ɗan kamata.
Jawo gadon baby Dr Mark ya yi, a kansa Dr James ya kwantar da babyn, ya gyara cinyarsa zai fara yi mashi allura kenan muryan sister Zinta ya dakatar da shi. "I'm sorry sir, wannan injection ɗin fa?".
Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta, sai ya tina irin abin da yai mata last time, ba ya ce ta zo yana nemanta ba in baku manta ba, to hidiman babys yasa bata samu damar zuwa da wuri ba, shi kuma shegen zuciyar bala'i, tana zuwa ya koreta wai ta ƙara mintuna goma kan wanda ya ce, yana sonta fa, yana son faɗa mata abin dake ransa, sonta kamar ya kashesa, amma guy ɗin nan sai girman kan bala'i, haka ya koreta, tana bashi hakuri ya daka mata tsawar da ya sanyata fita da gudu tana fashewa da kuka, to tin daga wannan rana bai sake ɗaga ido ya ganta ba sai yau, tsabar iskancinsa mai lasisi ne.
"Magani ne". Ya faɗa a taƙaice.
Dik da bata da ilimi ta fannin aikin 3D, amma a nata fannin ta gano wannan ruwan ba magani bane wlh, akwai sinadarin venomous spur toxin da nematocyst stored venom a ciki, wanda kuma venomous spur toxin tasan lalata jiki yake yi, yana kone fata, shi kuma nematocyst stored venom kumburin jiki yake, ya haifar da kuraje, ko yaya za'a kwaɓa sinadarai a irin kwarewarsu ita da Maya confirm zasu iya tantance wasu irin sinadarai ne a wajen, kada ku manta dik sinadaran da ake kawo masu a SECTION C ɗinsu sai sun tacesa sun cire mai karfi daga ciki, kunga kuwa dik wanda zai san wasu sinadarai a wannan hospital ɗin to ya biyo bayansu ne!.
Bata yarda da hakan ba, jikinta na kerma, fuskarta cike da tashin hankali, dik da tsananin tsoron 3D da suke yi hakan bai hanata ce mashi. "Wannan ba magani bane,wannan ai cuta ce!". Muryanta na rawa sosai ta faɗa......... Ai a miliyan Dr Kamal ya ɗago da idanunsa yai mata kallon ƙasan ido, sai kuma ya saci kallon Dr James da ko gezau bai yi ba. A karon farko yau an samu wacce ta ce da 3D wani abu a kan aikinsu.
Kama kafan baby ya yi wajen cinya da nufin ya tsira mashi alluran. Ai sister Zinta bata san lokacin da ta damke hannun nasa dake rike da sirinjin ba, jikinta na tsananta kerma, idanunta cike tab da kwallah ta ce. "Ka duba da kyau, wannan cuta ce ba magani ba, ka bincika da.......". Bata iya karisa maganar ba ta haɗiye saura sakamakon ɗago da eyes ɗinsa slowly da ya yi a kanta, a razane ta sake mashi hannu tare da ja da baya, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne suka fara zubo mata, bata san meyasa take kukan ba, bata san meyasa hankalinta ya tashi a kan wannan allura ba, tana jin wannan baby tamkar jininta ne, meyasa bata damu da sauran jariran ba sai wannan kawai? And meyasa kuma su 3D basu sakawa kowani jariri ido ba sai wannan darling ɗin Maya ɗin?
Sun yi scanning na brain ɗinsa, bai ishesu ba, suka sake ɗeban jininsa, dik bai ishesu ba, yanzu kuma sai sun sake yi mashi wannan alluran? For what reason? Meyasa dik suka rikice suka tashi hankalinsu a kan jaririn da satinsa 3 kawai a duniya? Meyasa? Wannan shi ne tambayar dake cikin kwakwalwar sister Zinta.
Ita kuwa Maya tambayar kanta take yi kan wai ina iyayen jariran nan dikka suke? 55 babys, kuma dikka babys ɗin 3 weeks suke da shi a duniya! Which is mean dikka rana ɗaya aka haifesu! Suna kama sosai, kenan uwa ɗaya ce ta haifesu? How? Meyasa ake basu madara ba nonon uwa ba? Meyasa su da suke matsayin nurses su suke masu wanka ba iyayensu ba? Kai abin da rikitarwa! Babban damuwarta ma a nan shi ne yadda yaran suke kamanceceniya, sai kuga babys 5 kamanninsu ɗaya kamar an tsaga kara, to ya haka? Wannan kamannin da suke da juna ya fi komai ɗaure mata kai.
Jama'a idan baku manta ba a jikin kowacce mace suna cire eggs sama da goma ba? Kunga kuwa dole za'a samu kamanceceniya tsakanin babys ɗin, dan wasu uwarsu ɗaya ne! Sannan ita sister Maya ai ita kanta ce abin mamaki ko ya kuka ce? Bata taɓa mamakin yadda aka yi dikka nurses na hospital ɗin suke da 18 years a duniya ba, bata taɓa mamakin yadda suke kamanceceniya ba suma, bata taɓa tambayar ina iyayenta ba, dik bata yi wannan ba sai a kan babys ɗin nan saboda ita mayyan son yara ne ba!.
Suna ji suna gani Dr James ya danawa darling wannan allura a jefen cinyarsa. A ƙasa da second 3 wannan kwayar cuta ta yawace jinin jikin jaririn nan.
Lokaci guda wani irin jijjiga jaririn nan ya fara yi, gabaɗaya bakinsa ya gagara buɗuwa ya yi kuka, amma daga gefe-gefen kunnensa wasu hawaye ne masu ɗumin gaske suke zuba, kafafu da hannayensa dik wani irin kerma suke yi tamkar yana jin sanyi.
Kallon Dr Mark Dr James ya yi kafin ya ce. "Dr yana aikin sosai, duba yadda jikin jaririn ya koma green sosai lokaci guda, lallai wannan abin zai yi yadda ake son ya yi wa duniya sosai, ban ƙara tabbatarwa ba sai yanzu dana ga zahiri, lallai na yabawa kaina ni da kaina!!". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan jaririn da gabaɗaya a yanzu jikinsa ta saki, ba kuma mutuwa ya yi ba, ya koma ne babu abin dake motsi a jikinsa face idanu, hawayen dake zuba daga idanunsa sun dakata cak alamar azaban ta ninku kan wanda yake ciki, na tabbata da yana da baki zai ce gara mashi mutuwa a kan wannan gwajin da suke yi a jikinsa.
Gyara hand gloves na hannunsa Dr James ya yi tare da kama kafan jaririn yana ganin tafin kafafunsa na yadda tsantsar jijiyoyin jininsa suka bayyana ruɗu-ruɗu saboda karɓar bakon abin da ya shigo cikin jinin da ya yi, skin ɗinsa ya koma green sosai kafin daga bisani ya fara komawa yadda yake, kana iya ganin yadda jini ke gudana a jikinsa, jijiyoyinsa suna harbawa alamar bakon abin da ya ratsa jininsa yanzu kamar ya fi karfin jinin jikin nasa.
INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KUMA WLH DA RANSA BAI MUTU BA, HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL! Kada ku manta fa cewa suka yi a jikin nama zasu sanya wannan cuta, wanda ya ci wannan nama zai kamu da cutar, to imagine, shi wannan jariri kai tsaye aka danƙara mashi cutar a jiki, ba a jikin wani abu ya ci ba, sinadarin zallar cutar aka zuba a jininsa, ya rab, ya rahman, ya rahim, ya malik, ya kuddus, ya salam, ya mumin, ya muaimin, ya aziz ka kawo mana ɗauki a wannan duniya da muke ciki, duniya mai cike da ruɗani da tashin hankali game da zallar rashin imani, ka rasa a ina zaka yi gwajin sai a jikin jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ya ALLAH! 3D ina zaku kai hakkin waɗan nan jariran? Dik wani jariri da kuka kyankyasa in ma kun sayar ko kun kashe ku sani hakkinsu na kanku, in kuka sayar da su aka je aka yi abin da bai dace da su ba wlh jininsu ya rataya a wuyanku ne azzaluman banza tsinannu!!!.
After kamar 5 mins da cutan ya gama yawo a cikin jinin baby sai me? Take yaron ya koma yadda yake, dama jijjigar shigar kwayar cutar jikinsa ne ta rikita shi, da ya shiga ya saje da jininsa kuma sai ya dawo daidai, cutar ta fara aiki a jininsa, sai nan da sati biyu zasu ga result, darling zai mutu ko kuwa?. Ya ALLAH.
Tin da yai mashi wannan alluran sister Zinta and sister Maya jikinsu ya hau tsuma, yana wani irin kerma, sister Maya idanu ya cika tab da kwallah, idanunta a kan yaron. Ana gama mashi alluran ta matso da sauri zata ɗaukesa Dr Kamal ya rike hannunta.
Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, tsaida video ɗin da yake ɗaukar babyn tin shigowarsu yai tare da tura wayar aljihu bayan ya yi saving. Daidai lokacin ta juyo da kallonta a kan Dr Kamal, wani irin zafafan hawaye ta ji ya fara bin ƙuncinta. Tana son zuwa ta ɗauki babyn amma ya hanata, ganin ta fashe da kuka ne yasa ya jawota jikinsa, a lokacin ta samu damar sakin wani irin marayan kukan da ba san dalili ba.
Da gudu sister Zinta ma ta yi kan baby tana son ɗaukarsa. Ajiye sirinjin hannunsa Dr James ya yi tare da cire hand gloves na hannunsa, ya miƙa hannu ya riko sister Zinta, tin da ta ga yadda babyn nan ya yi bayan an mashi wannan alluran ta kara gasgata cewa cuta aka zuba mashi. Kada ku manta dikkansu kullum suna sanye da doctors nose mask.
Da sauri Dr James ya ce. "Dr Mark fita da babyn nan zuwa sashe na musamman dan killacesa". In baku manta ba cutar tana yaɗuwa ne, ba zai yiwu a barshi cikin sauran babys har 2 weeks ya kawo result ɗinsa ba, dole a killacesa.
Jan gadon nasa Dr Mark ya yi, har lokacin babyn na kwance shiru bai motsa ba, kamar wanda akai wa alluran natsuwa fa, ALLAH sarki yana jin bakon yanayi ne a jikinsa, jininsa na karɓar sabon abu, shiyasa ya natsu shiru, ya gagara ganewa jikinsa bawan ALLAH.
Ihu sister Zinta ta fashe da shi tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannun Dr James tana faɗin. "Babyn nan zai iya mutuwa, ku duba jikinsa, ku yi hakuri ku bari mu ceci rayuwansa, mutuwa zai yi, wannan cuta kuka saka mashi ba magani ba, ni ku barni zan taimaka mashi, ku sakeni, wayyo sister Maya darling ɗinmu, ni ku sakeni, zan iya taimaka mashi". Tana magana tana ƙoƙarin kwace kanta daga rikon da yai mata, dik ta kiɗime ta fita hayyacinya.
Dikka sauran nurses dake ɗakin ko kaɗan basu damu ba, dan su an sha gwada cuta a gabansu a kan jariri, sau nawa suna gwada cutuka a jikin jariran? A gaban idanunsu ma an sha scanning na kwakwalwar jariri, idan yai masu abin da suke so, suna mashi tiyata ne, wani yaron su saka mashi wani abin a kwakwalwar wanda alƙalamina ne kawai yasan menene ake saka masu a kwakwalwar kuma shi kaɗai zai warware maku a gaba, wani jaririn kuma idan sun gwada shi cire kwakwalwar nasa suke yi gabaɗaya, babu abin da basa yi wa jarirai, su sister Maya ne sabbin baki a SECTION D, shiyasa zasu damu, amma nan da shekara kaɗan zasu daina damuwa su ma!............😭
Jawota jikinsa Dr James ya yi, ya rungumeta sosai, hakan yasa dik sauran nurses ɗin suka ɗauke kallonsu daga kansu. Jikinta sai wani irin kerma yake yi, musamman Sister Maya da ta gama sarewa, ta gama saddakarwa mutuwa jaririn nan zai yi, idan ta rufe ido sai ta ga idanunsa yana zazzarosu lokacin da alluran ta ratsa jininsa, wannan ya fi komai tsaya mata a rai.
Ganin yadda jikin Zinta yake kerma sosai ne yasa Dr James rage tsawonsa, ya ɗauketa cak yai waje da ita. A wani ɗaki kusa da na babys ɗin ya sauketa tare da riko hannayenta. Durkushewa ƙasa a wajen ta yi, wani irin kuka mai karfi ne ya kwace mata, a ranta tana jin idan suka barta zata je ta ceci yaron, kuma tana ganin kamar zata iya bashi maganin cutar, dan tasan chemicals, amma ina sun tafi da shi in da babu wanda ya sani, a can zai rayu na tsawon sati biyu, sai cutar ta gama game jikinsa, ta lalata shi, da wuya ma ya kai sati biyun, dan shi kunga kai tsaye aka danna mashi cutar ba daga jikin nama ko wani abin ya samu ba.
Tsugunnawa a gabanta Dr James ya yi tare da riko hannayenta a cikin nasa, ɗago fuskarta da ya yi jaga-jaga da hawaye ta yi, ta kallesa kafin ta ce. "Sir please ka bari in je wajen babyn, mutuwa zai yi!".
"Is okay, ba zai mutu ba, wani gwaji muke yi, zamu dawo maki da shi a raye kin ji?". In a low way sosai ya faɗa. Soyayyarta na kara ratsa mashi zuciya sosai........... Da yake sun yarda da 3D sosai sai ta ce. "To yaushe zaku dawo da shi?"........ Zubawa kyakkyawan fuskanta idanu ya yi, a sanyaye ya ce. "Kwanaki biyu kawai, wani magani muke nema na wata cuta dake ƙoƙarin shigo mana, to muna kokarin haɗa wannan maganin ne mu ka ce bari mu gwada a jikinsa, amma babu abin da zai same shi, so be patient".
Ta ji daɗin kalamansa, kuma ta yarda da shi, dan haka sai ta dakatar da kukanta, tana shessheƙa ta yi ƙasa da kai kamar mai tinanin wani abu. Hannunta ɗaya ya saki tare da riko haɓarta, ya ɗago suna kallon juna, in a cool way ya ce. "Smile, babynku zai dawo, naga kuna son babyn sosai, kaman ɗanki ko?"...... Munafuki yasan meyasa suke son yaron, domin yaron jinin IRON FIST ne, in baku manta ba su Maya ɗin ma ai kannen Lion ne ko? Kunga kuwa ai wannan baby jininsu ne, ba banza ba suke son shi.
Ƙasa da idanunta ta yi, tana ɗan ɓoye fuska saboda kunyar ganin idanunsa take yi, cikin muryan kuka ta ce. "E muna son babyn sosai, yana da kyau sosai, ina jinsa har cikin raina"...... Kara ɗago haɓarta sosai ya yi, still taki ɗago idanu ta kalli nasa idon........ "To kada ki damu very soon zaki samu naki babyn, kina so ko?".
Da sauri ta gyaɗa mashi kai, sai kuma ta ce. "Ko na samu nawa babyn zan rike darling, ina son shi sosai". ........ A cikin zuciyansa ya ce thank God da tinanin yi wa yaron alluran cutar ta zo kansa, ba dan haka ba wannan yaro zai kawo mashi matsala, yanzu zai mutu kowa ya huta, ka ji yarinya wai tana son gwada mashi ta fi son darling a kan ɗan da zata haifa mashi, tab ashe gara da ya ɗauko hanyar kashe yaron kowa ma ya huta.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Yaushe zan haifi nawa babyn?"....... Ɗago idanunsa a kan face ɗinta da kyau ya yi, ya kurawa kyakkyawan fuskan nata idanu, can ya ɗan nisa kafin ya ce. "Idan mun tashi aiki ki sameni a office, yau ma ki ɓata mun lokaci". Ya kare maganar cikin alamar gatse....... Da sauri ta ce. "Ba zan ɓata maka ba". Sake haɓarta ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, da sauri ta miƙe ta biyo bayansa, ɗakin jariran suka komo.
A nan ya isko su Dr Kamal ma sun rarrashi Maya, tana zaune shiru, Zinta na shigowa ta je ta rungumeta tana faɗin. "Ke Sir James ya ce babu abin da zai samu darling ɗinmu, wai maganin cuta suke gwadawa, zai dawo lafiya lou". Cike da farinciki sister Maya ta amsa da. "E haka sir Kamal ya faɗa mun, na ji daɗi"..
Kallon juna Dr James and Dr Kamal suka yi kafin su juya su bi bayan Dr Mark, su kaɗai suka san me a cikin ransu shegu, sun san wannan babyn kam ya tafi kenan, sai dai wani! Amma sun kwaɗaitawa yara wai zasu dawo da shi, harda wani wai maganin cuta suke gwadawa, waɗan nan shegu akwai makiran mutane!.
Suna fita suka je in da Dr Mark ya killace babyn nan, har lokacin yana kwance shiru, guard ɗaya suka sanya ya yi gadin yaron, daga nan suka fita suka koma office ɗinsu, Dr James ya karɓi wayansa, ya turawa WS video ɗin da suka yi wa yaron a lokacin da suke mashi alluran, ya ce nan da 10 days zasu samu result ɗinsu. Hakika sun yabawa wannan cuta, dan tin daga kan yadda jaririn nan ya yi wani irin jijjiga zaka san ba ƙaramin cuta bace, abin ya ratsa jininsa kuma ya fi karfin jininsa, sun yabawa Dr James sosai, sai suka ce zasu tura kafun alƙalami dala miliyan 100 yanzu, idan suka ga result zasu cike saura, dan dala miliyan 500 suka sayi cutar kawai ban da maganinta, shi ma maganin ciniki daban zasu yi.
Ai ba ƙaramin kuɗi suke samu a kirkirar cuta ba, su kansu WS da suka sayi cutar ba karamar riba zasu ci ba, a kan maganin zasu fanshe kuɗinsu. Hmmmm ALLAH yasa shiruna ya zame mun alkhairi, bari in ɗan yi shiru, gaba da kallo, dan in na buɗi baki a gaba hmmmmm!.
-------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
A daddafe Seraphina ta yi barci yau, da kyar da suɗin goshi saboda rashin jin a wani hali daddynta yake ciki, washegari ta shirya tsab, sai dai har 8 ya cika Aryan bai zo ba, ta kira numbersa ya fi sau dubu, amma bata shiga.
Haka ta tafi school da kafa da yake basu da nisa, amma har kuka sai da ta yi, bata saba tafiyar kafa ba, sai da ta shari 20 mins a tafiyar 5, tana tafiya a hankali tana ruwan hawaye. Wani waje ma ta samu ta zauna, Aisha nata rarrashinta dik da bata san me takewa kuka ba, amma taki yin shiru. Sai da suka fi 10 mins a zaune kafin ta miƙe suka cigaba da tafiya.
Sun kusa isa school daga bayansu suka ki ana masu horn, juyawa suka yi a tare, nan suka ga uncle ne, kashe motar ya yi, ya fito da sauri. Sai ga shi a gaban Seraphina, cike da kulawa ya ce. "Good morning baby flower". Cikin salo mai ɗaukar hankali ya faɗa. Sai kuma ya ce. "Oh God, meyasame kika yi kuka haka?".
Tamkar jira take yi a tambayeta, haba kuka ta fashe da shi har da shessheƙa. Kallon Aisha yai. "What happened to her?"....... "I don't know, tin da muka fito take kuka".
Dawo da kallonsa a kanta ya yi, hannunta ya riko tare da janta zuwa wajen motarsa, ya sanyata ciki kafin ya tada motar sai da ya tabbatar ya rarrasheta, ita dai Aisha sai kallonsu take yi, ya ɗauko wani heart design cushion mai balain kyau white color ya damƙa mata a hannu, sannan ya ɗauko chocolate ya damƙa mata shi ba. Ba shi ya tada motar nan ba sai da ya tabbatar da ta yi murmushi, sannan ya tada suka ƙarisa cikin school.
Shi kuwa Aryan a wannan lokaci yana zaune a tsakiyar gadon Lion yana danna wayansa, ya sauƙe numbersa dake na family, yana chantting ne da handsome VIR namu, korean guy mai capacity. Tambayansa ya karfin jiki Vir yake yi, dan jiya Lion ya faɗa mashi Aryan baya jin daɗi.
Baki ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa Lion ya shigo cikin room ɗin, hero na biye da shi a baya yana wani takun ƙasaita, da alama sun shirya. Sanye Lion yake da hoodie fara kal a jikinsa, ya ɗaure kitson kansa a baya, hannunsa rike da laptop ɗinsa.
A gefen Aryan ya zauna tare da ajiye laptop ɗin a saman gadon. Slowly Aryan ya ɗago idanu kai tsaye sai kan dara-daran eyes ɗin Vir ta cikin laptop ɗin Lion. Zazzaro mashi ido Aryan ya yi cike da mamaki, kuma fa chatting suke yi, watau ashe yana chatting da shi, shi kuma yana video call da Lion.
Kashe mashi ido ɗaya Vir ya yi, yana zaune gaban wani tabkeken swimming pool mai shaƙe da ruwa game da green light da ya sanya ruwan rikiɗa izuwa green mai ɗaukar hankali, hakika filin ya matuƙar haɗuwa, babu riga a jikinsa, hakan yasa kyakkyawar kakkarfan korean gorgeous body ɗinsa a waje, gashin kansa a kwance luff, ga wani haɗaɗɗen americano a gefensa cikin glass cup yana sipping.
Ya kashewa Aryan ido ɗaya kafin ya ce. "Meyake damunka likita bokan turai?"........ Harara Aryan ya dallah mashi kafin ya amsa da. "Ban faɗa maka ta chat bane?"........ "Chat daban ganin ido daban, yanzu faɗa mun, amsa mun tambaya dan yanzu nine likita kai patient".
Gyarawa Lion ya yi ya kwanta yana kallonsu, a daidai lokacin guru ya fito daga toilet sanye da robe fara kal a jikinsa, yana rike da wata ƙaramar towel yana goge hair ɗinsa da ba zan kama maku kalarta ba, saboda bana son ku san waye guru yanzu, nasan ina faɗar suffarsa kaɗan zaku iya gano wanene.
Zuba mashi idanu Lion ya yi yana karewa dik wani motsinsa kallo, dik ɗagowar da zai yi sai sun haɗa ido, hakan yasa guru ya ce. "Kallon fa?".
Hararansa Lion ya yi ba tare da ya yi magana ba....... "Zan je Nigeria gobe watakila". Guru ya sake faɗe idanunsa a kan Lion....... Wani irin mugun kallo Lion ya dallah mashi kafin ya amsa da. "Babu in da zaka je!".
Karin haske, guru mahaifinsa ɗan Nigeria ne cikakke, ɗan Nigeria ɗin ma ɗan arewa, arewan ma Hausa Fulani ne babansa, mahaifiyarsa ce kuma ƴar wata ƙabila can na je na zaƙulo maku wacce labari zai zo ku ji tarihinta, dan bakaramin power suke da shi ba a wannan littafi, kun san ba zan taɓa yin tuya in manta albasa ba, ba yadda za'ayi ace Nigeria bata da power kaso 60 zuwa 80 cikin ɗari a littafin nan. Karin wani haske ZAKUNA BIYAR littafi ne da ya shafi duniya ba Nigeria kawai ba! Dan haka ZAKUNA BIYAR da ake ta nema sun kasance ne daga yankuna daban-daban suka haɗu dan gyara duniya!.
Akwai jinin Nigeria tamu ta gargajiya,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 58 Chapter of 95