izuwa bakin ruwan dake gaban hotel ɗin, cikin takun jarunta da kwazo, zallar kwarewa a iya aiki. Shi kuma guru ya wuce wajen kayan kwalama, ya sayo masu chips and drinks, ya zo ya isko Champion a bakin ruwa yana zaune saman ɗaya daga cikin chair na table da aka shirya a wajen dan kara ɗaukar hankalin jama'a su ziyarci wajen.
Zama suka yi tamkar wasu bayin ALLAH, cikin natsuwa suka zame nose mask dake fuskokinsu, dan dole suka hau cin chips ɗin nan ba wai dan suna so ba. Kana ganinsu ka ga abokai ƴan korea.
Lokaci guda tsaro ya kewaye wajen, wasu manya-manyan jiga-jigan sojoji ne suka kewaye bakin ruwan, wasu mada karti da su, suna wani muzurai, kai ka ce zasu iya hana mala'ikan mutuwa ratsawa ya ɗauki rai. Kallon gefe-gefen ido su Champion suka yi wa jami'an, sai kuma suka haɗa ido.
A lokacin da dattijon ya sako kafafunsa bakin ruwan sai da ko'ina ya yi tsit, a natse wannan dattijo ya tako ya shigo ciki. Ɗaukar drinks a glass cup Champion ya yi tare da kashewa guru ido ɗaya, kamar zai kai drinks ɗin bakinsa sai ya kauce, ya sanya lips ɗinsa ya ɗan taɓa gefen babban yatsansa dake rike da cup ɗin, take wajen ya kawo wani haske blue sau biyu a jere sai kuma ya ɗauke. Tsabar bala'i da kwarewarsu a aiki jikinsu ma da na'urorin isar da saƙo tamkar wasu saƙaguna. Saƙo ya isarwa da Lion cewa dattijon ya iso, tsaro ya yawaita a wajen, idan suka ce zasu yi waya ko typing message in an zo binciken gawa ana iya cewa a nemo masu yin waya tin bayan shigowar ministan ko a nemo masu typing, kun ga zasu shiga alamar zargi, bugu da kari idan aka kalli irin wayoyin da suke rike da shi, da sh ma ana iya amfani wajen kamasu, dan haka ba ruwansu da waya, suna da hanyar isar da saƙo a natse ba tare da barin wata alama ba. Kai ku dama ai tin da aka ce maku duniya dikka nemansu take yi kun san haɗarinsu ya zarce yadda ake zato, fin haka ma zasu aikata.
Lion dake kwance a saman bed na ɗakin da ya kama ne ya samu saƙon Champion, shi ma gefen babban yatsansa ne ta kawo blue light sau biyu. A natse ya miƙe tare da nufar restroom na ɗakin. Jim kaɗan ya wuce WC side. Wani abu kamar powder ya buɗe a leda tare da fito da handkerchief fara daga aljihunsa, sai da ya gyara nose mask ɗinsa kafin ya yaga ledar wannan powder ya zuba a saman handkerchief ɗin, ya sanya hannunsa dake ɗauke da dogayen yatsu sosai, ya jujjuya powder a saman handkerchief ɗin sosai, sannan ya zubar da powder ɗin a cikin WC, ya yi flushing da ruwa. Ya ninke hankey ɗin ya tura a aljihunsa tare da fitowa, sai ya dunkule hannunsa da ya taɓa powder.
Ƙasa gabaɗaya ya sauƙo, cikin takun zallar jarumta kai tsaye ya tinkari wajen. Sai shiga side ɗin jami'an dake tsaron ministar suka dakatar da shi, ɗaya daga cikinsu ne ya ce ya nuna masu card ɗinsa dake nuna cewa ya kama ɗaki a hotel ɗin nan, idan ba haka ba ba zai shiga wannan waje ba, saboda tsaron lafiyan ministar.... KUN GA AMFANIN KAMA ƊAKIN NASU KO? Shaggun kai ne, akwai basira sosai.
Card na buɗe door na room da ya kama ya fitar daga aljihunsa da ɗayan hannunsa ya miƙa masu, ɗayan hannun nasa dai har yanzu a dunkule. Tsabar yarda da kansa a kwarewar aiki har da zame nose mask ɗinsa ƙasa dan ma su ga face ɗinsa da kyau. Duba card ɗin da kyau suka yi kafin su miƙa mashi kayansa, ko sannu bai ce masu na tamkar kurma, ya karɓa ya wuce cikin wajen.
Yana takowa a natse cikin jarunta ya nufi jerin securitys guda shidda take takewa mai kawo abinci a wajen baya, ya ɗauko abincin ministar ne suka take mashi baya dan tsark. Babu shakka ko tsoro Lion ya tinkaresu gadan-gadan. Sai da ya iso tsakaninsu taku biyu sannan ya ɗan kauce masu hanya, kaɗan suka ɗan bugi juna da jami'in dake gefen mai ɗauke da abincin. Sorry ya yi wa jami'in tare da ware tafin hannunsa ya ɗan yi wa jami'in alamar ban hakuri, juyawa jami'in ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai jinjina kai alamar to. Daga nan Lion ya wuce ya nufi in da ake oder abinci.
Su kuma suka wuce suka kaiwa ministar abincinsa. Kunsan waje da ake oder abinci dole akwai fili na musamman dan wanke hannu, nan Lion ya shiga ya wanke hannunsa kafin ya fito ya saka oder abinci, sannan ya koma saman chair daban nesa da su Champion ya zauna yana jira.
After 5 mins sai ga masu kawo abinci sun kawo mashi abin da ya yi oder. Kan babban yatsansa ya danna, take red light ta bayyana sau biyu a wajen, red light alama ce ta zubar jini, saƙo ya turawa su Champion a kan lokacin zubar jini ya yi, dik yatsun hannunsu cike yake da na'urorin dan balai, kuma kowanne sun san saƙon da suke aikawa da shi, kai sun zarce yadda kuke tinani. Ni kaina sun zarce yadda nike tinani, makasa ne masu bala'i basira, kun ga kuwa kama waɗan nan ba abu bane ma mai yiwuwa, amma a haka wai suna cikin list na FIVE MISSION nasu Noor namu! Kuna ganin hakan zai yiwu kuwa? Su Noor zasu iya kamasu? Tsorona ALLAH tsorona rasa ko mutum ɗaya daga team ɗin su Leo, wannan Mission ɗin babbar abu ce, kai na ce yanzu wasan zai fara.
Wannan saƙo na isanwa su Guru ko second goma ba'a ƙara ba ministar ya fara tari, ai sai jini daga bakinsa. Da wani irin masifaffen gudu jami'an dake tsaronsa suka yi kansa, Lion kuwa drink na kankana da yasa a kawo masa ya ɗauka ya ɗan yi sipping ya ajiye kafin ya motsa daga in da yake.
Ganin jinin dake fita ta hanci da ta bakin ministar ne yasa jami'ansa suka yi gaggawar kiran ambulance. Cikin ƙasa da minti biyar sai ga ambulance ɗin ta iso, sai dai kafin lokaci ministar ya jima a lahira, dan Lion bai taɓa haran abu kuma ta rayu ba, baya saɓa saiti, salon kisansa a second goma rai ke yin halinta.
Take wajen ta rikice, nan fa aka ce lallai a rufe hotel ɗin kada kowa ya fita. Miƙewa Lion ya yi tare da nufar wajen da likitocin dake tafe da ambulance ɗin suke. Kusa da wani babban likita ya tsaya, tamkar zai faɗa mashi wani abu, cikin dabara ya cire hankey dake aljihunsa ya karkaɗe masu a wajen. Kafin a ankara dik su uku dake wajen sun fara aman jini ta baki da hanci.
Wucewa ya yi tare da barin hankey ɗin a wajen, wannan hankey ɗauke take da hoton tambarin da suke bari idan sun yi kisa, watau dan ma a san sune kada a sha wahalar zargin kowa ko ɓata lokaci da kuɗaɗe wajen bincike, sun sauƙaƙawa kowa!. Gaskiya waɗan nan balai ne.
Dik da rufe wajen da aka ce ayi hakan bai hana Lion wucewa ya fita daga bakin ruwan ba. Champion da guru sun ma fita daga hotel ɗin, shi kuma Lion ya koma room ɗinsa da ya kama, hankalinsa a kwance ya shiga wanka, tamkar ba rayuka har huɗu ya kashe ba, ga likitoci uku, ga Minister.
Taya kuke tinanin ya kashe ministar? Kada ku manta bai taɓa abincin ministar ba, bai ma je kusa da in da yake ba! Nasan kun fahimci guba ministar ya ci, to how? Nima na ce how?
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP
STEP 1________🔥
14-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
NOTE. FIVE LIONS babu complete ɗinsa, yanzu nike posting ɗinsa, yanzu aka fara!
E_____________13
Jim kaɗan ya fito daga toilet ɗaure da towel, a nan ya ji jiniya ta karaɗe ko'ina a hotel ɗin, alamar jami'an tsaro sun ninka yawansu kenan. Body lotion na kamfanin STARS BODY LUSH da hotel ɗin ke amfani da shi ya shafa tare da buɗe drawer, ya ɗauko wasu kaya tamkar shi ya ajiye.
Shirinsa ya yi a natse, gabaɗaya ya canza tamkar ba shi ba, ya cire Chinese face ɗinsa, yanzu ya fito da fuskan European, still dai nose mask na face ɗinsa. Kayan da ya ɗauko ɗin tail coat ne masu balain kyau da ɗaukar hankali launin white, ya yi kyau matuƙa, kai kace meeting zai shiga da shugaban WORLD SYSTEM.
Bayan ya kammala ya ɗauki jacket ya mayar jikinsa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi, sannan ya fito, kai tsaye ya nufi elevator, ƙasa ya sauƙo, nan fa ya ga jami'ai ta ko'ina, already an buɗe hanya saboda jami'an da suka zo sun tsinci hankey ɗinsa mai ɗauke da tambarin IRON FIST, dan haka an san su ne suka yi kissan, ba sai an wahalar da shari'a ba, already an san ba zasu kamu ba, shiyasa kawai aka buɗe hotel ɗin.
Motarsa ya ɗauka ya fito daga hotel ɗin cike da kwarin gwiwa. Ya ɗan yi tafiya kamar na mintuna biyar, sai ya dakata a saman wata babbar gada kusa da wata bene da ake ginawa ba'a gama ba. Fitowa ya yi daga cikin motar hannunsa rike da jakar guitar mai shegen kyau. Saman benen kololuwa ya haura, bene ce mai hawa goma. A nan ya zauna tare da fito da drinks ƴar karama a kwalba, ya ɓalle bakinta, kaɗan ya yi sipping tare da ajiyeta a jefe jikin window ɗin da yake tsaye.
Zuge zip ɗin jakar ƙasa ya yi, a maimakon ya fito da guitar sai ya fito da dalleliyar sniper gun, shegiyar bindiga da bata saɓa saiti, yawancin manyan terrorists sun fi amfani da ita, kat ce ita, ta kware a iya harbin nesa, bullet ɗinta na da mugun gudu, dan bullet ɗinta na gudun 1000km a kowani second ɗaya, shiyasa ba'a iya kauce mata, in an harba sai ta sama ne kawai, dan rufe ido a sake buɗewa ya fi bullet ɗin sniper ɗaukar lokaci.
Tsabar Lion ya yarda da kansa da kwarewarsa a aiki, bullet ɗaya ne a cikin bindigar, kafa bindigar ya yi a jikin window ɗin da yake tsaye, yana facing babban hanya ne, amma ta gaban in da ya baro motarsa, motarsa na baya saman gada, shi kuma sai ya tsaya ta gaba, hanyar kamar round haka take.
Gyara bindigar tsab ya yi, intently ya ɗauki drinks ɗinsa ya ɗan yi sipping tare da ajiyewa kafin ya sanya kansa a mahangar bindigar, ya ɗana kunamarta, after kamar 20 second ya saki harbi wanda ya tafi kai tsaye sai tsakiyar gidan baya na motar jami'an da suka baro star hotel a yanzu, motoci biyar ne a wajen, biyu a gaba biyu a baya sai ɗaya a tsakiya, to na tsakiyar ya harba, wanda kuma ba kowa bane a ciki face IG na ƴan'sanda.
Mayun saiti ake magana, su Lion basu taɓa harbi an saɓa saiti ba, idan suka yi fa dole a tafi! Kwakwalwar kan IG ya tarwatsa, kuma motocin jami'an suna gudu sosai fa, amma ya harba ta fasa kan IG. Yana harbin ya naɗe kafar bindigar ya ɗauketa ya maida cikin jaka, tsabar yarda da kai bai tsaya tantance bullet ɗin ta samu abin hari ko bata samu ba? Shin abin harin ya mutu ne ko da sauran numfashinsa? Dik bai bi ta kan wannan ba, dan yasan in dai ɗaya daga cikin IRON FIST suka yi harbi fa to an gama ne.
Ɗaukar jakar ya yi, ya bar ɗrink ɗinsa a wajen ya nufi ƙasa. Daidai zai sauƙa ya dannawa su Champions alamar ja zubar jini kenan. Ya gama aiki ba. A daidai lokacin da suka samu saƙon nan suna ƙoƙarin shiga wani gida na shaggun tantiran karuwai, idan kuna ji ana karuwai to daga kan wannan gida an rufe kofa.
Suma sun canza fuska daga na korea da suka sanya ɗazun zuwa na Asia, cike da takun jarumta suka shiga wajen, sai tashi sauti ake yi ta ko'ina, maza da mata an sha an bugu sai rawa ake yi. Ai suna shigowa mata suka fara tururuwan zuwa jikinsu. Sai dai dik wacce ta dimfarosu sai ta ja da baya, domin kuwa kwarjininsu firgita zuƙata suke yi, bare yadda suka ɗaure fuskan nan, dik wacce take a cikin maye sai da ta wastsake idan ta nufosu.
Ko sau ɗaya basu ɗaga ido sun ga kowa ba, suka nufi sama, dan karuwan dake ƙasa ma ai iskancinsu kaɗan ne tin da da kaya masu ɗan nauyi a jininsu, karuwan dake saman daga pant sai bran da iya nipples ɗinsu ya rufe suka sanya.
A farko haurawa sama suka tsaya suka kama ɗaki ɗaya a zuwan zasu kwana da ƙaruwai, tsabar sun shahara har da yin oder karuwai guda shidda, guru uku Champion uku kenan, watau mace ɗaya ta masu kaɗa. Tsala-tsalan ƴan'mata suka zaɓa tare da bada lokacinsu, wai karfe 1 na dare matan su samesu a ɗakin. Daga nan suka karɓi card suka wuce room ɗin bayan an basu farashi sun biya.
Suna shiga suka fara rage kayan jikinsu, guru ya hau fito da wasu chemical daga aljihun jacket ɗin jikinsa, cikin kwarewa ya fara haɗa Chemical ɗin, shi kuma Champion ya wuce ya shiga toilet. Yana shiga ya haye sama, wajen fan da ake yi a tsakiyar pop dake baiwa toilet iska ba irin iskan Ac ba, kun san iskar Ac bata kaɗe warin abu sai dai zuba sanyi, shiyasa a manyan wurare basa amfani da ita, sun fi yin amfani da wata sabuwar technology na wannan fanka da ake yinta a tsakiyar pop, tamkar babban bolb na wutar lantarki haka, kuma idan kuka kallah in ba kun lura ba zaku zaci Ac karama ce, da tsari dai suke yinta.
Ita Champion ya hau kwancewa bayan ya kasheta. Daga kan yadda yake aiki zaku san ba yau bane farau a kwance irin wannan fanka, ya kware, dan a take ya ware notikanta dikka ya ajiye, sannan ya buɗeta, a hankali ya sauketa ƙasa, ya cireta gabaɗaya, sai ga hanya ya huda a wajen tamkar in an cire cilling ɗaya a ɗaki.
Yana sauƙeta sai ga guru ya shigo rike da Chemical ɗin a hannunsa, miƙawa Champion ya yi. Karɓa ya yi tare da matsawa ya bashi hanya. Hayewa sama guru ya yi, cike da kwarewa da yarda da kai ya shige ta cikin wajen, sannan ya zuro hannunsa ya karɓi chemical ɗin tare da wata ƴar karamar kwalbar acid, daga nan ya fara jan jiki cikin cilling ɗin ya tafi. Shi kuma Champion ya dawo cikin ɗakin ya kwanta a saman bed ɗinsu yana jiran dawowar guru.
To mu ɗan yi duba kan yadda aka yi Lion ya kashe Minister. A daidai lokacin da ya buge wannan jami'i, in baku manta ba ai ya ware hannunsa dan bawa jami'in hakuri ko? Bayan ya bashi hakuri sun juya zasu wuce ne hannunsu ya gogi na juna, da gangan Lion ya ɗan matsa ya shafi hannun jami'in.
A lokacin da suka kaiwa Minister abinci wannan jami'i shi ya sauke kayan abincin daga saman plate, ya jerewa minister a gabansa, sannan shi ya fito mashi da spoon daga kwali, da wannan hannu nasa da suka shafi juna da Lion. Karfin gubar da Lion ya yi amfani da shi ko taɓa cup aka yi da hannun da aka taɓa gubar aka goge hannun, idan wani ya sha abu da cup ɗin sai ya mutu, dan balain karfi gareta, a shegen kaifin kwakwalwarsa ya auna cewa wannan jami'in idan sun isa wajen Minister shi ne yake ta hannun dama, dan haka shi zai yi serving Minister, shiyasa ya bugesa da gangan.
Minister na karɓar wannan cokali da aka fitar mashi daga kwali ya fara cin abinci kenan gubar ta ratsa jininsa, dan gubar tana da karfin gudu ne fiye da yadda kuke zato, cikin ƙanƙanin lokaci ta kewaye jininsa gabaɗaya har ya fasa ɓargon ƙashi, spoon biyu ya ci bai kai na uku ba ya fara aman jini. To kun ji yadda aka yi, shi kansa jami'in da ya yi serving abincin ya mutu, saboda ya tattaɓa sassar jikinsa da hannun, musamman fuska, ya shafi fuskansa, a take gubar ta huda jikinsa shi ma.
------------------------------
Kwanciyar 5 mins Champion ya yi sai ga guru ya dawo. Miƙewa Champion ɗin ya yi, ya dawo cikin toilet ɗin, a natse ya mayar da fankar ya ɗaure, suka wanke hannayensu a toilet ɗin tare da shiryawa suka fito waje. Reception suka nufa, card ɗin suka miƙa masu tare da cewa akwai sayayyar da zasu je su yi, zasu dawo nan da 30 mins.
Manager ya amsa da to tare da karɓar card ɗin. Daga nan suka wuce suka fita. Basu zame ko'ina ba sai gida, dan sun gama aikin da zasu yi a wannan waje, wasu manyan mutum suka shirya aiki a kansu. Kun san manyan mutane idan zasu yi meeting suna samun wajen da ba za'a taɓa zaton suna wajen bane, koda ace mutanen kirki ne mutanen, suna ɓadda kama dan meeting, yanzu kunga ai babu wanda zai zargi mutumin kwarai zuwa gidan karuwai! Kunga zasu samu damar yin meeting ɗinsu a natse.
Wasu manya ne su uku suke zaman tattaunawa kan yadda za'a kawo karshe IRON FIST, manyan ɗaya daga ciki ma babban soja ne, sai Minister na tsaro da wakilin shugaban ƙasa. Shi ne fa suka shiga ta cilling ɗin nan, a tab fankarsu na toilet ɗin ɗakin da suke meeting ɗin guru ya zuba acid a cikin wannan chemical ɗin, take hayaki kaɗan-kaɗan ya fara fita, shi ne ya dawo suka tafi, wannan hayaki nan da mintuna goma zata kewaye ɗakin nasu, kafin su farga ta kewayesu, in kuma suka shaƙa ko sau ɗaya ne zasu fara aman jini, daga nan minti uku ya yi yawa su wuce lahira.
Su guru suna kula da dik motsin gwamnati a kansu fiye da yadda gwamnatin ke nemansu, dik wani take-taken jami'ai a tafin hannunsu suke, dik wata ƙullah-ƙullah da shirya yadda za'a yakesu da ake yi suna sane, wannan meeting ɗin sun san da za'ayi shiyasa suka fito da shirin gamawa da su, wai a hakan gwamnatin ta yi dabara, sun zo gidan karuwai meeting, a tinaninsu ai babu wanda zai zaci suna wajen, har da ɓadda kama na sanya fuskan boge dik dan kada a ganesu, basu san a tafin hannun su Lion suke ba.
Shiyasa hankulansu a kwance da suka haɗa komai suka fita, nan da 10 mins dai gidan karuwan ma zai rikice.
A yayin da dik wannan yake faruwa ƙasa na can ta rikice, dik wani babba ana kiransa da ya koma gidansa yanzu, saboda IRIN FIST sun fita aiki. Suna ɗaukar lokaci kafin su fita aiki, idan kuma suka fita fa to a tashi ɗaya suke zubar da mutane 10 zuwa 15, in sun gama suka lafa zasu ɗauki lokaci basu yi wani aikin ba.
Kwance a gida suka isko Lion, ya yi wanka yana shirye cikin sleeping dress, dogon wando da riga mai dogon hannu saboda sanyi, yana kwance saman katafaren bed ɗinsh mai girman gaske wanda suke kwana su uku ɗin. Hannunsa rike da waya yana latsawa, while makeken TV dake manne a bangon room ɗin nasu na magana, labarai ne na yadda ƙasa ta rikice a ƙasa da mintina 10, an rasa babban IG na ƙasa, anrasa babban baƙonsu daga India, ga babban soja da minister ɗin tsaro da aka rasa, uwa uba wakilin shugaban ƙasa, kunga kuwa dole ƙasa ta rikice, dare ya zama tamkar rana, hankula sun tashi.
Abin da zai baku mamaki kuma dik wani Camera dake babban hanya su Lion suna da shi a computers ɗinsu, sun datsi camerorin gwamnati ba tare da sun sani ba, yanzu haka manyan ambulance sai gudun cetan rai suke yi a birnin, kuma suna ganin dik abin da yake faruwa, su kaɗai sun girgiza ƙasa bakiɗaya, suna nan cikin kwanciyar hankali su kuma. Kai su Lion fa basu fito ba sai da suka shirya!.
Suna shigowa guru ya nufi toilet dan yin wanka, Champion kuma ya nufo in da Lion yake kwance. Yana zuwa ya kwanta kusa da shi tare da ciro wayansa, a sanyaye ya ce. "Yanzu nike samun wannan sako ta email".
Ya faɗa yana nuna mashi hoton da ya gigitani, hoton daddyn Noor dake tsaye a bakin ruwa shi yake nunawa Lion.
Kallo ɗaya Lion ya yi wa hoton ya ɗauke kansa ba tare da ya yi magana ba. A dake Champion ya ce. "ARM company ne suka buƙaci da a kashe masu wannan mutumi, amma ni ina ganin wannan matsala ce tasu ta cikin gida, kasan kayan kamfanin BODY LUSH ta samu karɓuwa matuƙa a duniya, ta buge kowani product, shiyasa hankulan sauran Company ya tashi suke son a kawar masu da shi!"....... Kai daddyn Noor ɗin namu ake farauta fa! Ko da yake dama yadda kayan kamfaninsa ta yi suna dole ya samu makiya ta ko'ina bawan ALLAH.
Shiru wajen ya ɗan yi for almost 2 mins, in a cool way Lion ya ce. "Ba zamu yi wani aiki yanzu ba, sai nan da 2 years, sai duniya ta ɗan yi shiru an manta da labarinmu, dan haka ka mayar masu da aikinsu"........ Sanin cewa basa magana biyu yasa Champion ya yi cancel wannan aiki, ya mayar da saƙon cewa ba su da lokaci yanzu, daga nan ya toshe wannan email ɗin nasu, dik da cewa su ba'a isa a bibiyi email ɗinsu ba saboda mayun computer ne su, amma suna toshewa time to time saboda tsaro.
Shiru suka kwanta kowa yana latsa wayansa, gabaɗaya hankalin Champion ya koma kan tinanin Seraph, ya fara kewanta, ya kwana biyu bai je ba. While shi kuma Lion ba zaka taɓa sanin a wani hali ma yake ciki ba, ga shi dai yana ta latsa waya.
A haka guru ya fito sanye da bathrobe fara tas a jikinsa, a tsakiyar room ɗin ya tsaya yana ƙoƙarin goge gashin kansa da karamar towel fara dake hannunsa. Miƙewa Champion ya yi ya sauƙo ƙasa, toilet ɗin ya shige dan yin wanka shi ma.
Ganin Lion ya kura mashi idanu yasa guru cewa. "Ya dai my guy? Na maka kyau ne yau kuma?"...... Hararansa Lion ya yi ba tare da ya yi magana ba, kuma bai ɗauke kallonsa ba. "Wai ka kyasa ne ka biya sadaki?". Guru ya faɗa cike da iskanci da tsiya a maganar tasa.
Wani irin mugun kallo Lion ya dallah mashi bai dai ce komai ba, kuma babu alamar zai yi magana....... Towel dake hannunsa ya jefawa Lion a kan fuska, ya nufi gaban closet ɗinsu yana faɗin. "Idan ranka ya biya ka faɗa mun".
Intently Lion ya same towel ɗin daga face ɗinsa tare da cigaba da kallon guru ta glass wall da ya raba room ɗin nasu da wajen closet ɗinsu, babu dai alamar zai yi magana.
Shiru ɗakin ya yi, jim kaɗan guru ya fito sanye da sleeping dress irin na jikin Lion ɗin, sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufo bed ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa dake gefen Lion ɗin. Sai a lokacin Lion ya ɗauke kallonsa daga kan guru ya mayar kan Champion da ya fito yanzu, shi ma yana sanye da bathrobe fari tas, hannunsa rike da towel yana goge gashin kansa.
Wai kun san wani abin mamaki da su Lion ne? Tsananin son juna suke yi, ba zasu iya juran rasa mutum ɗaya daga cikinsu ba, amma kuma su sun iya raba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 95