Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
karfin cewa sorry, zaku shiga hannun nisau ne dan ubanku Abba Khaiza'an, mu zaku gwadawa iskanci? Yanzu lokacinku ne, ku gama shan kamshinku zamu damƙeku ne, Aunty Luna kada ki kyale ɗan air, ki gyara mashi zama, ki ganar da shi mu fa nisa'u ba'a mana wannan shirmen!. Har ta iso gaban bed ɗin bai ɗago kai ba, sai da ta zauna a dab da shi, tasa hannu cike da yanga irin namu na mata, ga natsuwa ta karɓi wayan hannun nasa ne ya wani irin ɗawo dara-daran eyes ɗinsa a slow motion. Ai yana sauke idanu kan face ɗin mace bai san time da ya zarosu waje sosai ba, sai ya ɗan miƙe daga kishingiɗar da ya yi, ya zauna da kyau yana kallonta babu ko kyaftawa. Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Good afternoon oga sir".......... Shiru bai amsa ba, sai ma juya idanu da ya yi, ya kalli door ɗin shigowa, kafin a natse ya dawo da kallonsa a kanta. Ɗan ɗaure fuska ya yi, a dake ya ce. "What brought you here?".. Nisawa ta ɗan yi kafin in a cool way sosai ta ce. "Coming to see your beautiful face, tin ranar baka sake dawowa ba, ka barni da tinaninka a cikin rai, shin ban maka bane? Baka son haɗin Abbanmu ne? Ko akwai abin da baka so a tattare dani ne?". Ta faɗa tana ɗan jujjuya wayansa dake hannunta. Slowly ya ɗan fara yin ƙasa da idanunsa daga kan face ɗinta, ya fara bin sassan jikinta da kallo. Hakika idan ya ce bata haɗu ba ma ya yi karya, yaudarar kansa zai iya idan ya ce ba haɗaɗɗiya bace, kuma wlh idan kuka ganta ba zaku zaci ta kai 20 years bama, ai kun san yadda jikinsu yake da mugun kyau, gata ƴar kwalisa. Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta kai hannu saman soft cheek ɗinsa, ta shafi wajen sajensa dake kwance luff kafin cikin salo mai ɗaukar hankali ta ce. "I love this". Tana shafa sajen ta faɗa, sai kuma ta sake cewa. "Ka zo har gida, ka barni for more then 20 mins a tsaye, kana tinanin ka ci banza ko? You most pay it as soon as possible". Ta dakata da maganar tana kallon face ɗinsa da kyau. Slowly ta mayar da hannunta izuwa kan kyakkyawan wuyansa, ta gangaro zuwa kirjinsa. "Everything of yours is so special"....... Yunkurawa yai zai yi magana kenan ta yi gaggawar mai da yatsanta saman soft lips ɗinsa, ta ɗaura yatsan nata game da cewa. "Shiiiiiiiii". Ta faɗa tana matso da face ɗinta dab shi. "Now is my time, ka gama naka time da ka je gidanmu". Ta faɗa cikin wani irin romantic way, shi kansa maganar nata cikin wani irin yanayi ya fita, wanda sai da ya sanya gabaɗaya jikinsa ya amsa, to shi tin da ba dutse ba ai dole ƙararrawarsa ta buga! Sai ga malam Harleen ya shiga natsuwarsa, wasu malam shiru ne suka shigesa, tsit kake ji. Kara matso da face ɗinta dan shi ta yi, ta zame yatsan nata daga bakinsa, suna iya shaƙar numfashin juna, can ƙasa ta ce. "Meyasa ban yi maka a matsayin mata ba? Faɗa mun in ji"...... Ba sai ga malam Harleen da rarraba idanunsa a cikin nata ba, ya gagara yin magana. Haɗe fuskokinsu waje guda ta yi, ta sanya ɗayan hannunta ta zagayo da shi ta bayansa, ɗayan hannunta kuma ta saƙalo wuyansa, kafin ya farga ta haɗe bakinsu waje guda.......... 👀 Hot kiss ta bashi na just 5 second, slowly ta fara zame bakinta daga nasa, sai dai ga dikkan alamu munahiki bai so ta cire bakin nata ba, dan har ɗan wani kama lips ɗinta yake yi, ta jisa sarai, amma ta basar ta zame bakinta, dan dama burinta ta kwaɗaita mashi, ta kuma rikita shi sai ta gudu ta barshi ta yadda dole ne ma yai tinaninta har ya biyota gida. Tana zame bakinta ta kalli cikin kwayar idanunsa da suka fara rikiɗewa izuwa ja. "Sai kazo gida"...... Ta faɗa tare da sakesa, ta miƙe tsaye, ai tamkar wawa haka ya zama, sai ya bita da idanu kawai yana kallon yadda take taku tamkar wahainiya, gabaɗaya ya jisa a duniyar sama jannaty. Sai da ta fice ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, ɗan lumshe idanu ya yi yana tariyo daɗin soft lips ɗinta, ya ALLAH, shi kaɗai yasan me ya ji, a ƙasan zuciyansa ya ce zuma, a fili kuma da miskilancin ta motsa sai ya yi gaggawar kawar da tinaninta, har da sa hannu ya fara goge bakinsa yana jan dogon tsaki, shi a dole zai yi avoiding ɗin abin, bayan kuma ƙasan zuciya ta kyatsa har da lashe baki, munahiki bai so ma ta dakatar da kiss ɗin iya haka ba. Ita kuwa tana fitowa ƙasa ta sauƙo, a cikin ranta taka faɗin ta kunnasa kenan, da kansa zai kawo kansa ne ma, tana sonshi so na tsakani da ALLAH, ga shi bata da matsala, wayayyiya ce kuma sosai, bata bari kanta ya kulle. Yadda ta bar su Abba haka ta iskosu, ƙasa ta ɗan duƙa tana yi masu sallama kenan suka ji knocking. Abba dake rike da waya ne ya duba wanene? Can ya gano grandpa ɗinsu Noor ne. Buɗe masu kofa ya yi. Cikin faɗa dattijon ya afko ciki, yana wani muzurai tamkar zai saka duka, cike da sababi ya fara zazzaga masifar ina jikarsa? Ai Aunty Lusi ta faɗa mashi nan ta yo, ya sha alwashin ba zai rabu da Khaiza'an ba, zai sace mashi ɗiya ya lalata. Tin da ya shigo yake wannan balai har ya kariso tsakiyar parlon. Daidai lokacin Faryan da Rimsha suka shigo. A natse Harleen ya sauƙo ƙasa jin banbamin dattijon. Shi kuwa daddyn Noor yana office bai san wani waina ake toyawa ba, shi dai kawai ya ce Aunty Luna ta zo ta bawa Abba hakuri a madadinsa tin da Aryan ya hana shi shiga. Da sauri dattijon ya zo ya rike Aunty Luna yana faɗin. "Basu yi maki komai ba ko?".......... Faryan da ya shigo yanzu ne ya ce. "Ammie ina son yin magana dake". Daidai lokacin grandpa ya nuna family da sandar hannunsa, cike da masifa ya ce. "Ba zan kyaleku ba! Dole hukuma ta ɗauki mataki a kanku, dole a shiga tsakanina da ku! Sai na gwada maku karfin dukiya! Sai na ɗaure dikka zuriarku, mutanen banza kawai". Aunty Luna na kokarin dakatar da shi amma ina, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba. Wucewa Harleen ya yi, ya zauna a saman carpet kusa da Abba tare da miƙe kafafunsa, tamkar bai ga grandpa ba, while ita kuma Rimsha ta nufi sama tana faɗin. "Ammie bari in cire uniform ɗina ina zuwa in baki labarin Seraphinata yau ma". Ammie dai bata da aiki kullum sai sauraren labarin Seraph, dik Rimsha ta addaba masu. Faryan da ya zauna kusa da Ammie tare da kwanto da jikinsa a jikin Ammie ɗin ne ya ce. "Ammie na gaji, zo mu je in baki wani labari".......... Abba ya ce. "Gulma zaka kai mata ko?". Yana ɗan murmushi ya ce. "Kai Abbanmu, ai mu bama gulma, wani labari zan bata fa, ina wannan kawar Rimsha Seraphina ɗin?". Jinjina kai su Abba suka yi, dan dik wanda yake tare da Rimsha yasan labarin Seraphina. "To yarinyar yau saura kaɗan daddynta ya mun duka, wai dan kawai Rimsha ta ce mu yi dropping ɗinta a gida, zamu ɗauketa sai ga daddynta, labarin nike son baiwa Ammie fa Abba"....... Abba na ƙara tsare gida ya amsa da. "Waye shi da har ya isa ya taɓaka? Waye shi? Dame yake taƙama? Autan nawa zai taɓa? Waye ubansa a faɗin US!". On a serious note Abba ya yi magana......... Ni kam da nike laɓe a gefe na ce waye ubansa kuma ya wuce Muhammad Khaiza'an dake wannan magana! Ko ya kuka ce ƴan amana?. Watau Khaiza'ans family muggan ƴan mannin hauka ne, sun baiwa banza ajiyar grandpa, tamkar basu san yana wajen ba, sai zazzaga masifa yake yi, ya gama kuri da nuna isansa, ya ce zai kira hukuma tai masu iyaka, dik babu wanda ya kulashi, ya nunasu da sanda, ya kirasu da mutanen banza, amma tamkar basu jisa ba. One thing about Abba, ko in ce Khaiza'ans family, su fa suna kula waɗan da suke ganin sun kai ne, waɗan dake da ilimi, ko musayar yawu zasu yi a cewarsu basa yi da dakiku waɗanda kansu baya ja basa fahimta! Sun raina isar grandpa ne, sun raina izza da taƙamansa, basa son harkar ƙaranta, shiyasa suka baiwa banza ajiyansa, basu da lokacinsa. Dama dai daddyn Noor ɗin da kansa ne to da sai Abba ya tanka, dan daddyn Noor akwai ilimi da sanin yakamata, amma grandpa, gargajiya kawai ya sani sai masifar tsiya da kullatar mutane a zuciya!. Yanzu me laifin auren nan? Banda hajilci irin na grandpa me laifin dan baku addini ɗaya kun yi aure? Musulunci bai haramta ba, dan haka ba zamu haramtawa kanmu ba, idan aka yi auren ma ai in su Aunty Luna na da rabo sai su musulunta. Ganin basu kulasa bane, suna ta sabbagar gabansu ne yasa grandpa jan hannun Aunty Luna, suka nufi hanyar fita yana faɗin. "Talakawa kawai, sai na gwada maku karfin kuɗi, sai na ƙasƙantar daku na walaƙanta rayuwarku, in ja ku a titi, ku jirayi dawowata, har ni zaku ɗaukawa jika ku kawo gidanku? Ku jirani". Suna jinsa, amma babu wanda ya tankasa, suka baiwa iska ajiyansa, har ya fice yana sababi. Yana fita Harleen ya miƙe ya koma sama, Faryan ma ya nufi wajen Rimsha dan ya faɗa mata cewa shi fa ko zai rasa ransa ba zai fasa son Seraphina! Abba da Ammie suka cigaba da tattaunawa kan yadda za'ayi biki, Abba ya ce baya son taro, a sirrance za'a ɗaura aure, a cikin masallacin dake nan CRYSTAL PALACE ɗin, Ammie dai da ta ga da gaske babu gudu babu ja da baya a lamarin Abba kan batun auren nan, kuma tasan halinsa in yai magana ɗaya ko duniya zasu haɗe ba zai canza ba, sai kawai ta bada kai, ta hakura ta biye mashi suka hau tsara yadda komai zai wakana. DEATH OR LIFE! 🔥(DOL🔥) Tsaye Leo yake a gaban wani tapkeken tekun da ka kar iya kallonka ba zaka iya ganin karshen tekun nan ba, ga wasu manyan jiragen ruwan dake shawagi a tsakiyar tekun, bodace ta arewacin AVARIS, teku ce da ta haɗa manyan ƙasashe da dama ana kasuwanci ta cikinta, ana shigo da kaya a sake fitarwa, tana da girma matuƙa, to su suna kusa da ita ne ta cikin Avaris, a nan ɗan nesa kaɗan da ita Leo ya ce su kafa tantuna, saboda wani tinani nasa da ya barwa kansa sani! A cikin ransa yana jin yana mugun zargin wannan ɓangare da dajin da suke ciki, sannan yana zargin wannan tekun, yana da yaƙinin dik wani fitina dake shigowa Avaris daga nan yake farawa, ya yi imanin wannan dajin ita ce matattalar dik wasu manyan ƴan iskan ɓatagarin cikin Avaris, shiyasa ya zaɓa masu wannan waje. Sun kafa tantunansu yadda suka saba, ya yi matuƙar kyau, sun kuma rungumi rayuwar dajin nan tamkar gidansu, basu wasa da aikinsu ko kaɗan, musamman waɗan nan team na room 1 da kuma Arya, basa wasa ko kaɗan. Yana sanye da tactical tshirt da tactical trouser, ya rungume hannayensa a saman buɗaɗɗiyar kirjinsa, ya ɗaure kitson kansa a tsakiya, while pistol gun ɗinsa na waist ɗinsa a mazauninsa. Ya kurawa jiragen ruwan dake shawagi can nesa tsakiyar tekun idanu. A hankali ruwan sama yaf-yaf-yaf ya fara sauƙa a kansa, iska mai ɗan sanyi ya fara kaɗawa, alamar an yi babban ruwa a nesa da su. Lokaci guda hadari ta taso gadan-gadan, iska mai karfi da guguwa suka turnuƙe dajin, tsawa da walkiya ya fara yi. Hakan yasa dikka sojojin suka koma kusa da tantunansu except Leo dake tsaye bai motsa ba. A cikin ransa yana saƙa yadda za'a wayi gari ace sun gyara duniyar nan, sun tsabtacesa daga dik wasu gurɓatattu. Noor ne ya fito daga cikin tantinsu sanye da army trouser da tactical tshirts a jikinsa. Yana fitowa dik sojojin dake wajen suka ƙame tare da fara sara mashi........ "Ina Leo?". Ya faɗa a dake. Arya dake cikin tantinsu ne ta fito da sauri jin ya ambaci sunan Leo, tana fitowa ta ƙame game da sara mashi. Jinjina mata kai ya yi....... Ɗaya daga cikin sojojinsu ya ce. "Sir Leo yana bakin ruwa". Nan ma kai ya jinjina alamar to. Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya ɗan yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin............ Likes comments and share fisabilillah. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-12.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 51 & 52 DEATH OR LIFR (DOL)🔥 Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya ɗan yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin ɗakinsu Arya ɗin. A tsakiyar ɗakin ya tsaya, ya zuba mata idanu, tana zaune saman electric mattress ɗinsu, ta sanya bluetooth a kunne, dik iskar dake tashi bata da labari. Angelina dake zaune gefenta ne ta taɓata game da cewa. "Ke". Ɗago kanta yi daidai lokacin da take cewa. "Kai ma muryanka na da daɗi ai causin.......". Gagara karisa maganar ta yi a lokacin da idanunta suka sauƙa a kan angry face ɗin Noor. Da sauri ta zabura ta miƙe tsaye, wani irin mugun kallo ya dallah mata wanda bai san ya yi ba, in a harsh way ya ce. "Da waye kike waya?"...... Da sauri ta cire bluetooth na kunnenta, hannunta na ɗan kerma, dan gabaɗaya yadda ya ɗaure faska ya razanata, murya na ɗan rawa ta ce. "Wani..... Wan.... Wani brother ɗina ne". Wani kallo da ya wurga mata ne yasa ta haɗiyi yawu gwad...... "Ashe kina da brother kenan?". A faɗa...... Kallonsu Angelina da Manassa suke yi, while Manassa na ta faman rikita hankalin Vash dake cikin tantansu, ta gama ce mashi wai ta gani a in da yake ana ruwan sama, kuma zata kawo mashi ziyara daren yau, dik ta rikita bawan ALLAH, wlh ya yarda aljana ce. "No, he's my Aunty's son, tare muka yi school, mother ɗinsa sister ɗin dad ne.......". Hannun da ya ɗaga mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi ya ce. "Kuma kike cewa he have a sweet voice ko?".. Tsuru-tsuru ta yi da idanu, dan bata zaci ya ji ba, kuma wlh ita ba da wata manufa ta faɗa ba, kawai guy ɗin ya ce mata your voice is so sweet shi ne ita ma ta ce naka ma da daɗi, kun gane irin wannan abin ai? Wai ka ɗan mayarwa mutum magana mai daɗi, ashe sarkin kishi kuma lover boy ɗinmu ya jita. Jama'a watau family ɗin Noor duniya ne, lovers ne, ga kishin balai da iya shagwaɓa. Kai ya ɗan jinjina. "Your voice is so sweet". Ya maimaita yana ɗan jinjina kai....... Zata yi magana daga cikin wayar guy ɗin ya ce. "Vanisha are you okey?". Ta ɗan zazzare idanu a kan face ɗin Noor kafin ta ce. "Nothing Yosif"..... "I hear like kina magana da wani, who's he?"......... Ƙara zazzaro idanunta a kan Noor ta yi. Daidai lokacin su Angelina suka mimmiƙe tsaye suna kallonsu. Wani irin kallo Noor yai mata like ki bashi amsar da waye kike magana!. Ɗan tattauna lips ɗinta ta fara yi. "Yosif bye". Tana faɗa ya katse kiran. Muryarta na ɗan rawa ta ce. "My Romeo.......". Bai jira jin me zata ce ba, waje ya nufa cikin fushi. Da gudu ta rufa mashi baya, a tsakiyar wajen tantin nasu ta tare gabansa, kamar zata yi kuka ta ce. "Please my Romoe, isn't what you're thinking......". In a harsh way ya ce. "How do you know that I'm thinking something? Or you're hiding something for me right?!"...... Kai ta fara girgiza mashi, kawai tasan yadda ya fita nan ne zai yi tinanin ko soyayya take yi da wani, shiyasa ta ce isn't what he's thinking, amma ya sake fassarata ta wani sigar. Raɓawa gefenta ya yi zai wuce, a lokacin ruwan saman ta fara karfi sosai. Da gudu ta juya, ta ruga ta faɗa bayansa, ta ƙanƙame shi tightly, hakan yasa dikkan sojojin dake kallonsu suka yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. Tsalle ta yi ta haye bayansa, ta saƙalo wuyansa. Aikuwa cikin fushi ya dawo da ita ta gabansa, da karfi ya yakiceta daga jikinsa, ido cikin ido ya kalleta, ga ruwa na zuba a kansu, a fusace ya ce. "Kada ki sake taɓani, ina baki wannan umarni ne ba amatsayin masoyinki ba, sai a matsayin oganki!!". Yana gama faɗin hakan ya saketa tare da tureta gefe, ya wuce ya nufi bakin ruwa. Abinku da bata taɓa faɗa da shi ba, durkushewa ƙasa a wajen ta yi, kuka ta fara yi, ALLAH sarki bata san komai ba sai soyayyansa, slowly ta kifa kanta a ƙasa, wani irin kuka ne ya kubce mata. Da gudu Angelina da Manassa suka yo waje. Angelina ce ta watsa da gudu ta yi kanta, a cikin ruwan ta je ta rungumota tana bata hakuri. Takaici tamkar Arya dake tsaye a bakin tantin ta rufesu da duka, sun zubar mata da mutunci a cewarta, siririn tsaki ta ja tare da komawa ciki abinta. Daidai lokacin Unays ya fito, ganin Angelina a cikin ruwa ne yasa ya yi gaggawar shiga ciki shi ma, ya isa daidai lokacin da Angelina ta ɗago V, sai dai V na ta famar langwaɓewa tana a barta a cikin ruwan ita kam. Sai hakan ya zamana kamar ta fi karfin Anglina ta gagara ɗagata. Ganin hakan yasa Unays ya ce. "Let me help you, bari in kai maki ita ɗaki". Ya faɗa yana matsowa zai ɗauketa wai irin shi zai taimakawa Angelina ko zai zamu ya sace zuciyarta, taƙi kulashi ne, yana ta neman dama....... Matsawa baya Angelina ta yi tana faɗin thanks.......... Hannu yasa zai cicciɓi V, sai kuma ya tsaya cak, da sauri ya ja da baya daga kusa da ita kallonsa a kan Noor dake nufosu tamkar wani zaki, shi da Leo duns bubbuɗe kamar zakuna, ya nufo wajen yana dallahwa Unays ɗin wani irin mugun kallo mai kama da ka taɓata kaga yadda zan yi da rayuwarka. "Ki ɗauketa kawai". Unays ya faɗa yana ƙara ja da baya game da mai da kallonsa a kan Angelina ɗin. Ta yi mamakin jin ya fasa taimaka mata, ita kanta V mai kukar ta yi mamaki. Slowly ta ɗago kai karaf suka yi 4 eyes da Noor. Ƙara ɗaure fuska tamau ya yi, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya zo ya wucesu tare da Leo. Angelina ta gane karatun, watau Noor ne ya hana Unays ɗaukar V, ya ALLAH kaga wata soyayya da kishi ga fushi a gefe, kai Noor akwai rigima wlh, ya dai yi fushi, amma ba zai bari wani ya kusantota ba........ Sai dai ita V ɗin bata gane ba, ta zaci ya daina sonta kenan, shiyasa take ta faman kuka. Arya kuwa tana komawa ciki ta hau aikinta na duba drone da suka tasa a wannan daji, ta share su V, a cewarta basu da hankali sam-sam. Tantin Leo suka shiga shi da Noor, a saman electric mattress ɗin Leo suka zauna, Noor ya yi ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abu, kallo ɗaya Leo yai mashi ya ɗauke kai tare da faɗin. "What are you thinking?"....... Nisawa ya ɗan yi. "My Jeliet, na wuceta tana kuka, zuciyana tamkar ba zai iya ɗauka ba". Wani kallo Leo ya wurga mashi like baka da aikin yi, daga nan yai shiru bai yi magana ba. A daidai lokacin Arya ya faɗo ɗakin bakinta ɗauke da excuse, sai da ta faki idanun Leo ta dallah mashi harara kafin ta ƙame ta sara mashi. Noor ya ganta sarai, a cikin ransa ya ce. "Ban san me yake tsakaninsu ba, kullum sai Arya ta harari brother ɗina, anya ba son shi take yi ba?". Shi kuwa Leo yana zaune shiru bai motsa ba bare ya ɗago ya kalleta, a dake ta ce. "Sir, there's something you should come and see!". Kai kawai ya ɗan jinjina ba tare da ya ɗago ba. Juyawa ta yi ta fita, amma kafin nan sai da ta dallah mashi mugun harara. Tana fita ya miƙe tsaye, kayan jikinsa ya fara ragewa, shi kuwa Noor ya gyara ya kwanta cike da tinanin V a ransa. Pjs jade color kalar idanunsa Leo ya sanya a jikinsa, ya tara kitson kansa ya ɗaure da kyau kafin ya sanya winter coat a saman pj's ɗin, sannan ya sanya beanie, beanie wata hular sanyi ce irin mai laushi sosai ɗin nan. Bayan ya kammala ya fita ya nufi room nasu Arya. A lokacin Angelina ta yi ta maza ga ɗauki V sun shige cikin tantin nasu. Zaune ya isko Arya gaban laptop ɗinta tana duba dajin da kyau. Jin kamshin perfume ɗinsa yasa ta ɗago kai, zuba mashi idanu ta ɗan yi, while shi kuma yana kallon gaban screen na laptop ɗinta. Gently ya taƙo ya ƙariso, dik ɗakin natsuwa tsit suka yi, Manassa da Angelina suka zubawa Leo idanu, V na kife saman mattress ɗin har yanzu tana kuka. Hakiƙa Manassa ta ce Leo yana yi mata yanayi da Vash, musamman idan zai yi magana, sai ka zaci Vash ne yake motsa baki yake magana a wajen, dimple ɗinsu iri ɗaya, sharpe na eyes ɗinsu iri ɗaya, dan dai idanun Leo jade ne, kuma kamar sleeping eyes haka suke, na Vash kuma a waje suke gulu-gulu, amma shape ɗin ɗaya. Saitin in da Arya take ya tsaya, slowly ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, zubawa dajin idanu ya yi for 2 mins, sai kuma ya ce. "Wannan ai hayaki ne". Ɗagowa da kallonta a kansa ta yi, sai taga ba ita yake kallo ba, shiru ya ɗan sake yi, can kuma ya kai hannunsa saman mouse ɗinta, ya ɗan yi ƙoƙarin yin gaba da drone ɗin, amma sai abin ya ci tura, ya yi iya yinsa abin yaki yiwa. Slowly ya dawo da kallonsa a kan, while ta tsaye ƙashin wuyan nan nasa da ya fito sosai da kallo, kunga ya sunkuyo kanta ne, so tana iya kallon wuyansa sosai. Ganin ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta wani irin rass gabanta ya faɗi, gagara kallon cikin idanunsa ta yi, cikin zafa ta yi ƙasa da idanunta. "Meyasa drone ɗin yaki yin gaba?". Ya faɗa in a cool way. Sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta saita natsuwarta kafin ta ce. "Nima ban san meyasa ba, amma na fi tinanin akwai gagarumin abin da dake bayan dogayen bishiyun da hayakin ke fitowa daga wajen ne". Tana magana muryanta na ɗan rawa, dan gabaɗaya ganinsa a dab ita ya rikitata, har take jin kamar numfashinta zai ɗauke. Daidai lokacin Zaynish ya shigo hannunsa rike da bindigarsa, yana sanye da army waterproof jacket, ya yi kyau matuƙa, a kusa da Leo ya ƙariso ya tsaya, zuba mashi idanu su Angelina suka yi, a dake ya sarawa Leo kafin ya rage tsawonsa, ta ɗan sunkuyo yana kallon wajen. A daidai lokacin Noor ma ya shigo, dan jin Leo shiru. Yana shigowa V ta miƙe zaune tana kallonsa, shi kuwa tamkar bai san da zamanta a wajen ba, a ɗayan gefen Leo ya tsaya, ya zamana Arya da Leo suna Tsakiya. Zubawa hayakin wajen idanu suka yi. Hayaki ke bakinkirin yake tashi a tsakiyar dokar

Chapter 63 of 95