daga can ƙasa akwai hanyar da ruwan yake sake komawa bakin zakin, ba karamin ƙara gyara gidan wannan design ɗin ya yi ba. Ga wasu shuke-shuken flowers a gefe guda da suka ƙarawa gidan haɗuwa.
A gefen dama akwai guest suite, ɗakunan baki guda biyu tare da toilet da kayan more rayuwa a ciki. A gefen lambu akwai tangamemen garage na parkin motocin wanda tsab zai iya ɗauke motoci 30 ciff, gate na shiga garage ɗin automatic ne, da kansa yake buɗewa da rufewa, har yau akwai jiga-jigan motocin daddy guda biyar ciff a fake, tsadaddun motoci ne da suka haɗa da Maserati Levante Trofeo, Rolls-Royce Cullinan, Bugatti Chiron Super Sport, Mercedes-AMG G 63 sai wata mota mai tuƙa ƙanta, motocin dik an rufesu da car cover.
Sannan akwai katafaren swimming pool a ta gefen ginin ba harabar gidan ba, a ɗan gefe aka ƙawata shi, yana ɗauke da sky blue ruwa mai balain kyau da ɗaukar hankali. A gefen pool akwai glass wall na tennis, basketball, filin wasanni na tennis da basketball har ma da football.
A gaban zakin wani tampatsetsen baranda ne a wajen wanda babban parlo door yake kansa. Kai mu haura ground floor dan wlh ƙawartuwar harabar gidan nan ya zarce in iya faɗa maku shi lokaci guda, sai a hankali.
Mu lula grand entrance hall, babban kofar shiga ground floor, kofar ya haɗu, ga kakkafar tsaro da idan ba mamallakan ginin ba babu wanda ya isa ƙetarawa izuwa ciki, ya fi kofofin CRYSTAL PALACE tsaro da amfani da kimiyar zamani.
Kana shiga kofar akwai wani dogon corridor mai kyau wanda yake ɗauke da fitilar chandeliers a tsakiyar corridor ɗin daga sama, duk tsawon corridor din nan sai da chandeliers ɗin nan ya kusa kai ƙasa saboda tsawo da haɗuwarsa.
Idan ka wuce corridor ɗin sai haɗaɗen automatic door, kana buɗesa da wani katafaren living room zaka fara cin karo, haɗuwar parlon nan ba zai faɗu ba, kusan za'a ce five in one ne parlon, dan haɗaɗɗun luntsuma-luntsumar sofa set kala biyar ne a cikin parlon, kowani set ya haɗu matuƙa.
A cikin parlon akwai door da zai sadaku da tamgamemen mediterranean kitchen, kitchen ne mai siffa ra gargajiya, amma su gas na zamani ne a cikinsa, da alama daddy yana son gargajiya, dan a waje harahar gidan cikin wannan lambu akwai hut da aka ƙawata har guda uku, sai dai bukkar ba'a kewayesu da komai ba face glass, samansu kuma exactly bukar da ake yi a ƙauye, cikin bukkokin kuma haɗaɗu kujeru ne na zama dan shaƙatawa, to da alama yana ɗan son gargajiya.
Iya wannan kitchen ɗin ne a ground floor, sai wani haɗaɗɗen butterfly stair case da ya yi sama izuwa first floor, nan ma akwai babban parlo two in one, sai master suite, katafaren ɗaki mai ɗauke da babban balcony da ke kallon wajen harabar gidan da sauran cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Sai katafaren toilet mai ƙunshe da jacuzzi da shower mai ban sha'awa.
Bayan master suite akwai luxury bedrooms guda uku, ɗaya ɗakin yara ne, biyun kuma ɗaya na matar gida, ɗaya kuma babu kowa a ciki sai kayan alatu da aka zuba. Kowanne ɗaki na da toilet haɗaɗɗe da balcony, ga furnitures made in Dubai masu matuƙar kyau da tsada.
Bayansu akwai dining hall, shi ma dik glass wall ne, daga parlon first floor ɗin kana hango cikin dining hall ɗin, katan table da haɗaɗɗun chairs guda 24 ne a ciki, sai show glass da ake zuba cups and plates a cikin dining hall ɗin, ga haɗaɗen decorations, and daga cikin dining hall ɗin kana iya hango wannan haɗaɗɗen lambun na waje mai ɗaukar hankali.
A gefen ɗakin daddy Haiza'an akwai family lounge, wani ɗaki ne na taron iyali tare da TV mai faɗi da sofas masu taushi.
To mu haura last floor muga me a ciki, ni fa ina son in ga na ɗauko maku abubuwan da cigabansa bai zo mana Naija ba, dan ni a tinanina da yadda na ɗauki rubuta littafi ana rubuce-rubuce ne dan ƙaruwar al'umma da wayar masu da kai game da basu ilmin da ALLAH ya hore maka wanda su basu sani ba........Kazalika kuma makaranta a tinanina kuna karance-karance ne dan ku samu ƙarin ilimi, so bai kamata ace kuna karanta abin da muke da shi a Naija ba, abin da already kun san shi sai dai ayi ta maimaitawa, shiyasa dik rubuce-rubucena yake ketarawa ƙasashe, mu zaƙulo abubuwan da baku sani ba dan ku sani ku kara samun ilmi, kunga ko baku je ƙasashe ba kun san me yake wajen, wannan shi ne kun yi karatu mai riba, kun kara samun ilmi!.
Last floor. Tampatsetsen gym room ne a wajen da aka ƙawata shi dan motsa jiki tare da kayan zamani, sai haɗaɗɗen cinema room dan kallon fina-finai mai ɗauke da fitillun chandelier da kujeru masu taushi dan zaman kallon film da family.
Baya ga shi akwai haɗaɗen roof terrace a saman, wani ƙaramin filin shakatawa ne, tare da barbecue station da kujerun hutawa. And daddy yana da home office na musamman dan aiki, tare da shelves da table na zamani....... A can sama kololuwa wajen sauƙar madaidaiciyar private jet ɗin daddy ne, akwai haɗaɗɗen jirgin da kowa zai yi mafarkin mallaka a wajen an faka shi, jikin jirgin ɗauke yake da sunan MUHAMMAD HAIZA'AN da harafin larabci
To nifa my people wannan lambu na daddy ya tafi dani, dan haka ko aiki ne su Lion su ɗaukeni a wannan lambu, dan gaskiya ina son rayuwa a cikinsa, ya haɗu ne.
Jama'a ALLAH ya mana arziki mai albarka, ya bamu lahira mai kyau, amma gaskiya zuciyar CRYSTAL PALACE ta haɗu, haɗuwa fiye da tinani.
------------------------
Kwance Lion yake a saman bed ɗin daddynsa a master room ɗinsa, ya tada kai da laps na wani kyakkyawan mutum wanda kana ganinsa kasan jininsu ne, dan akwai kamanni ta jini a tsakaninsu. Mutumin na sanye da tail coat a jikinsa, yana rike da hannun Lion ɗin, ɗayan hannunsa kuma yana shafa haɗaɗɗen golden hair ɗin Lion cikin tausasawa da nuna tsantsan kauna. Wannan mutumi ba kowa bane face Hussain ɗin daddynsu, ɗan biyun mahaifinsu wanda shi ya reni su Lion ɗin, da Lion ya shiga damuwa ne ya zo gidan daddyn nasa, sai ya ƙira uncle ɗin nasa kan ya zo su haɗu, kun san da cewa uncle ɓoye kansa yake yi? Baya son duniya ta san yana raye, yanzu haka duniya dik sun ɗauka ya mutu ne.
To meyasa yake ɓoye kansa? Ya aikata wani laifi ne?. Muje zuwa alƙalamina zai amsa masu.
"Zayra'an!". Daddy ya faɗa yana riƙo hannunsa a cikin nasa da kyau, shiru Lion bai amsa mashi ba, da alama ya yi barci. Ɗayan hannunsa daddy yasa yana ɗan shafa kansa a hankali, slowly ya ɗago idanu ya fara bin room ɗin da kallo, komai yana nan yadda yake, babu abin da aka taɓa face gyaran da ake yi wa komai.
Lokaci guda daddy ya ji tamkar Hassan ɗinsa yana raye, idanunsa na mashi kizo lokacin da dad ɗin Lion ya tsaya a gaban parlo, yana ɗaura necktie a wuyansa, cike da tsantsar kaunansu yake cewa. "Hussain ka tashi ka bar mun gida, ka bar mun yara cikin kewa da kaɗaici, ka je na sallameka, kuma kada ka sake zuwa sai na nemeka"...... Mom Lion tana sauƙowa ta ce. "Zaka koran mun ƙani a kanka yake zaune ne?".
"Tuba nike ranki ya daɗe". Dad ya faɗa yana miƙa mata hannu kan ta bashi wayansa dake hannunta......... Rintse idanu daddy ya yi, wani dogon numfashi ya ja game da sauƙewa a hankali, ya fama ciwon dake ransa na tina rayuwar baya. Dawo da kallonsa a kan kyakkyawan fuskan Lion dake ta zuba barci ya yi, cikin barcin ma sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi alamar ya fara samun peace of mind, ALLAH sarki, idan ya tina rayuwar iyayensa in bai zo ya ga second daddyn nasa ba baya samun natsuwa, ganinsa kawai shi ne kwanciyar hankalinsa, shiyasa ya gudu ya bar su Aryan tin asuba.
"Ina sonka sosai Zayra'an, ina sonka fiye da kaina, ba wanda nike gani in ji daɗin rayuwata face kai da ƴan uwanka, ina rokon ALLAH ya bani ikon cika alkawarin dana ɗaukarwa ɗan uwana na kula daku".
Ɗan motsawa Lion ya yi, hakan yasa ya zame hannunsa daga cikin na daddy, ya gyara kwanciyansa da kyau, ya cigaba da barcin da bai samu damar yi daren jiya ba........ Sake riƙo hannunsa gam daddy ya yi tamkar ance za'a rabasu ne, ya yi shiru yana ta kallon fuskan Lion. Slowly ya jingina kansa da jikin headboard na gadon, ya ɗan lumshe idanu cike da tinanika kala-kala.
Barcin good 2h Lion ya yi, daddy na zaune bai motsa ba gudun kada ya tashesa. A hankali ya waro idanunsa da suke jajir saboda barcin bata ishe shi ba. Kai tsaye sai kan fuskan daddy..... "Dad". Ya furta yana miƙewa zaune, kallon farko ya zaci dad ɗinsa ne ba daddy ba. Slowly daddy ya yo ƙasa da kai yana faɗin. "Ka tashi?".
Kai ya ɗan jinjina game da cewa. "What says the time?"...... Laluɓo waya daddy ya yi, ya kunna light ɗin screen.......... 4:00 PM. Iska mai ɗimi daga bakinsa ya furzar game da miƙa hannu ya jawo nasa wayan. "Daddy let me call Aryan, nasan yanzu yana can ya damu da rashin sanin ina nike".
Cikin zolaya daddy ya ce. "Sai yanzu ka tina da shi kaima ai"..... Shiru bai yi magana ba, ya fara laluɓar number Aryan, ya danna kira. Sai dai a lokacin dik suna barci a kan gadon Seraphina, wayar tana silent basu ji ma, message Lion ya rubuta mashi kan yana lafiya kuma yana dawowa yanzu. Wayoyinsu kusan a haɗe yake, sun saita shi ta yadda idan ya turawa ɗaya saƙo dikkansu saura ukun zasu samu saƙon.
Yana tura masu ya zuro kyawawan kafafunsa ƙasan bed ɗin, jikinsa dik a mace ya miƙe tsaye, toilet ya nufa, da kallo uncle Hussain ya bisa har ya shige katafaren toilet ɗin daddynsa, ajiyar zuciya Uncle ya sauƙe game da gyarawa ya kwanta.
After 2 hours, Lion ne tsaye a tsakiyar master room na daddyn nasa, yana sanya botiran tail coat na jikinsa, ya rabb, kayan sun zauna a jikinsa matuƙa, tamkar dan shi aka yi su, yai wa kaya mugun kyau, ya tara kitson kansa ya ɗaure, jade eyes ɗinsa sun ciza sosai, kyawawan soft lips ɗinsa sun ciza pink matuƙa, fuskansa ya yi very fresh sosai, ya ƙara kyau da cikar haiba da kamala.
Uncle dake zaune a kan gado yana kallonsa ne ya ce. "Zayra'an please ka dawo gidan nan da zama, tsawon shekaru 10 kenan yanzu ina binka kaki yarda, meyasa baka son zama a nan ɗin?"..
Shiru ya yi bai amsa ba, har Uncle Hussain ya fidda ran zai amsa mashi ma sai kuma ya ji in a low way ya ce. "Nothing, kawai bana son gidan ne".
"Please, even because of Nirash, ku dawo ku raya gidan nan, ku sake raya ruhin Haiza'an ɗina, ku farfaɗo da gidan"....... Nan ma shiru for good 3 mins ya yi kafin ya ce. "Zaka dawo mu zauna a tare a nan ɗin?"....... Rass uncle Hussaini ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya daure da cewa. "Zan yi tinani, amma idan na aminta zan dawo mu zauna gabaɗaya zaka dawo?".
Kai kawai ya jinjina ba tare da ya sake yin magana ba. Shiru uncle yai yana tinanin yadda zai dawo gidan su haɗe waje guda, da kuwa abin zai yi making sense. Katse mashi tinani Lion ya yi da cewa. "Bye uncle"....... "Bye my beloved son". ....... Daga haka bai sake magana ba ya fice waje, ya bar uncle, dik lokacin da yake so zai iya tafiya, shi dai ya koma benensu.
Yana fitowa waje wasu karfin jami'an SSO suka nufosa da gudun gaske, hannu ya ɗaga masu tin ma basu ƙariso ba, baya son hayaniya da gayya, baya cikin wani good mood sosai. Sauƙowa kasar wannan baranta ya yi, ya nufi gate na fita, da kafa zai koma benensu ba sai ya ɗauki mota ba, dama da kafa ya zo. Kafin ya fito sai da ya sanya wannan haɗaɗɗen nose mask ɗin nasu a face ɗinsa, sannan ya fito ya nufi benensu, a cikin ransa yana jin kamar zai iya dawowa gidan nasu da zama.
Dik in da ya zo ƙetarawa sai waɗan nan jiga-jigan jami'an sun kame tamkar basa numfashi sun sara mashi, bai ɗago ya kalli kowannensu ba, bai tanka kowannensu ba, ya wuce kai tsaye ya nufi benensu.
----------------------🔥
KHAIZA'ANS HOUSE.
Sai da aka zubawa Rimsha ruwa 3 bottle kafin su samu kanta ta farfaɗo, da kuka ta farfaɗo tana faɗin. "Abba yanzu uncle Aryan ɗin ne mijina?".... A lokacin Abba baya kusa, sun baro room ɗinsa da ita, Faryan ya ɗauke zuwa room ɗin Ammie.
Rungumota Ammie ta yi, ta hau rarrashinta tana bata baki, sai dai ina Rimsha taki yin shiru, in short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana wannan kuka na ta shiga uku, dik Abba bai san tana yi ba, a rana ta huɗu ne ta kama Monday, a wannan ranar da asuba Faryan ya ce ta shirya ya kaita school.
Jin cewa aurenta ba zai hanata school bane yasa ta ɗan saki jiki, burinta dik ta je makaranta su haɗu da Seraphina ta faɗa mata abin da aka yi mata, dik tayi sanyi baiwar ALLAH, daga umm sai uhm-uhm ta zama, bata hira, ta takura kanta sosai, amma yau da zata je school har da ɗan murmushinta.
Ta shirya tsab cikin uniform ɗinta, har ta rame uniform ɗin yai mata yawa. Faryan na tsaye a parlo ta fito rike da rucksack ɗinta, karɓa mata ya yi yana faɗin. "Mu je in kaiki da wuri, Abba na jirana zamu je mu ɗauki amaryar Yah Harleen".
Kallonsa ta yi, muryarta a dashe sosai ta ce. "ALLAH yasa tana da kirki"....... Da amin ya amsa game da riko hannunta, suka nufi waje yana kara yi mata nasiha, yana tausan zuciyarta, yana faɗa mata kalamai masu daɗi, yana tunatar da ita ALLAH ya ce Annabi ya ce, a haka suka nufi school ni kuma na nufi DOL kafin mu dawo mu bisu school ɗin.
--------------------🔥
D-O-L
Nutso take yi a cikin ruwan cike da farinciki, yana tsoma gashin kanta can kasan ruwa tana ɗagosa ruwan dake biyo gashin ya ƙara wanke mata fuska, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba. Shi kuwa tamkar gunkin da aka sassaƙa haka yake tsaye a cikin ruwan ware kitson kansa dan ya wanke golden hair ɗinsa.
Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana ɗan juyawa, ɗagowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi...........
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-22.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️
E_____________ 59 & 60
DEATH OR LIFE. (DOL)
Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani.
Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba'a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za'a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen.
Al'ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za'ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?.
Amma shi rigakafi za'a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za'a biku ko'ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za'ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye.
Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama'ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza.
Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka.
Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buɗe container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai ne a cikin wannan container, waɗan da basu san me Tramadol ba, wani maganani ne da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta, amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, in kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai.
Leo sai da ya ɗan girgiza ganin waɗan nan uban tulin kwalin Tramadol ɗin nan, katon container irin wannan cike da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buɗe container.
Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiransa da maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwandon sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fahimci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!.
Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba.
A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu, amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki.
Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe lokaci guda ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake in na ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali!.
Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al'umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al'umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuɗi. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando!
Idan kuwa kinƙi dakatar da shi to fa ɗan karfin da yake da shi ɗin zaku rasa, dan in yana da sauran shan ruwa a gaba bai mutu ba, to at the end abar tasa mutuwa zata yi ta daina aiki, kinga kuwa bai samu power ba wanda yake da shi kun rasata. Wata ma sai kuga ita ke sayawa mijin man power, su man power manya, zakuwa ki ga man power. Wlh mata tin wuri idan zaku tattara mazajenku ku turasu gudun motsa jiki da gym kullum dan su samo power ɗin asali is better for you, gym yana sanya jikin namiji ya yi karfi, dik wasu matattun jiyoyi zasu miƙe, yana ƙara girman gaban da kukewa haukar neman har kuke kai kanku ga halaƙar in da zaku rasa ɗan wanda kuke da shi. To maza, gym yana ƙara girman gaba da kuke so ɗin, ba sai kun sha man power ba zaku samu ingantaccen power da babu mix, sannan gym yana ware ƙasusuwan gaɓɓai yasa su yi kwari sosai, yana ƙara lafiya da daidaita zuciyar ɗan adam, kai in taƙaice maku kai da kanka in ka fara zaka ji jikinka ya canza, ya yi maka daɗi da sauransu.
Mata ku tura mazanku gym ko dan su dinga ɗaukarku kamar ƴan baby suna jefawa gado kamar matan novel, da zarar yana gym komai girmanki zai ɗaukeki cak, to kashinsa ya yi kwari, amma yanzu kun kyalesa dik man gyaɗa da gishiri ya kashe dik wani karfin da yake da shi, ga wata musifa wai man power, ba dole a samu tangarɗa ba!.
(Kuma mata masu shan hips and breasts enlargement yake kome? Ku jira, zan bangaɗo maku dame ake haɗasa, naku na nan tafe, ai nai alƙawarin sai fa na faɗi komai dake cutar da bayin ALLAH!)
Container na gaba kuma maunguna ne irinsu diazepam, rohypnol, valium, magungunan bacci da kwantar da hankali a cewarsu, ana shigo da su
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 75 Chapter of 95