kan ƴar naurar, dan scanning me yake damunsa, sai dai ina, na'urar taki bada haɗin kai, da alama abin babba ne, ganin haka yasa Lion ya ce da su Vir su yi sauri su dawo, su kai containers ɗin gidan uncle na bayan gari yanzu su dawo.
Vir kwararren likita ne kamar dai Aryan ɗin, Lion da guru kuma sama-sama ne, ba aikinsu bane, suna dai taɓawa ne. Ɗaura kan Aryan a saman laps ɗinsa Lion ya yi, ya rike hannunsa ɗaya a cikin nasa, yana shafa arab hair ɗinsa da hannu ɗaya, dik after one minute sai ya cewa Aryan sorry my hb (heartbeat)
Shi dai Aryan ya gagara magana, idanunsa a datse, sai wani irin zufa da ya fara haɗawa na wahalar ciwo.
After 1 hour sai ga su Vir sun dawo, ai suna ganin Aryan a kwance cikin hanzari suka yi kansa suna tambayar menene yake damunsa. A natse Lion ya ce. "Vir duba mun shi a hanzarce"...... Kai Vir ya jinjina, da sauri guru ya zago ta gefen gadon, ya zo ya sanya hannunsa ya ɗauki Aryan cak sai saman shoulder ɗinsa, waje ya nufa da shi.
A natse Lion ya sauko kasan bed ɗin, a tare shi da Vir suka rufa masu baya zuwa ɗakin jinyarsu. E&R (emagemcy room) suke kiran ɗakin, a saman haɗaɗɗen gadon dake ɗakin guru ya shinfiɗe Aryan.
Cikin zafin nama Vir ya matsa ya fara ƙoƙarin dubasa, a gefe-gefen Aryan guru da Lion suka tsaya, dik da ba'a gane farinciki ko bakin cikin Lion, baka gane in da ya dosa amma a yau sai da fuskansa ta nuna alamar damuwa na ganin Aryan a wannan hali. Ya tsaya shiru yana kallon fuskan Aryan ɗin, a halin yanzu a duniya abu ɗaya Lion yake mutuwar tsoro, wannan abu ba komai bane face rasa ɗaya daga cikin IRON FIST, a kullum yana addu'ar ALLAH yasa ya rigasu mutuwa, ba zai iya juran rasasu ba.
Shiyasa ya tsaya shiru, dan yasan ciwon ciki wajen ɗa namiji babban abu ne, dik hankulansu a tashe, guru kamar shi zai baiwa Aryan lafiya, dik ya fisu nuna damuwa, shi damuwarsa har ta fito fili, ya ƙanƙame hannun Arya yana ta faman yi mashi hannu.
Gwaje-gwajensa Vir ya yi, after like 10 minutes ya ɗago da kallonsa a kan Lion da guru, dik sun tsaresa da ido suna jiran jin menene yake damu bugun zuciyansu.......... Shiru Vir ya ɗan yi, sai kuma ya ɗan kalli Aryan. Ajiye na'urar hannunsa ya yi kafin ya riko waist ɗinsa da hannu ya mai da kallonsa a kan Lion.
Girgiza mashi kai Lion ya ɗan yi alamar ya ake ciki?. Kashe wa Lion ido ɗaya ya yi yana ɗan ɗake kafaɗa. Hararansa Lion ya yi, babu alamar zai yi magana. Shi kam Vir da yake ya gane damuwar Aryan hankalinsa ya kwanta, sai ya fara yi matsu tsiya, sun ƙagu su ji menene yake damunsa amma Vir yana son ɓata masu lokaci.
Guru ne ya ce. "Please Vir, menene yake damunsa?". Ya faɗa cike da damuwa........ Gyara tsayuwansa Vir ya yi, cike da tsiya ya ce. "Ba wani abu mai wahala bane, mace kawai yake buƙata mu samo mashi"......... Cikin rashin fahimta Lion ya kallesa game da cewa. "Vir!!". Ya faɗa yana tamke fuska.
Tamke fuska shi ma Vir ya yi kafin ya ce. "Da gaske mace kawai yake so, sperm tai mashi yawa a mara, dole ya samu wajen juye, zan mashi alluran da zata sassauta mashi, but ko a nema mashi mata ko kuma a samu matsala, allura ba zata cigaba da rikesa ba, a nema masa mace, idan ba haka ba wlh ya ƙulla da ciwon ciki kenan har sai randa ya samu wajen juye"........ Zazzaro idanu guru ya yi, wata sabuwa in ji ɗan caca. Lion kuwa cewa ya yi. "Hakan ba zai yiwu ba, zai samu sauki ne, ba wata mace!". Ya faɗa game da juyawa ya bar room ɗin, da alamar ɓacin rai a tattare da shi.
Kallon Vir guru ya yi, can ƙasa ya ce. "Bana fatan ALLAH ya haɗa our Lion da wani kaddarar da zai sanya shi neman abu a wajen mace, yanzu dai ga shi ALLAH ya kama our champion, dole ya nemi mace in yana son zaman lafiya, a da ba wanda ya kaisa cika baki a kan cewa mace bata da amfani, bak san cewa akwai wani abin da zaka nema a duniya sai a wajen mace kawai zaka samu ba". ........ Vir dake kokarin haɗa allurar da zai yi wa Aryan ne ya ce. "A ɓangaren lafiya akwai abubuwa da dama wanda dole a wajen mace kawai namiji zai iya samunsu dan lafiyarsa ta ɗaure, shi kansa Lion ɗin zai shiga hannu ne, dan injunan jikin namiji suna cigaba da aiki da kwarinsu ne kawai idan suna samun wasu sinadarai daga jikin mace, but shaaaa, lokacin zai gyaramu ne".
Guru ya ce. "Awww ka yarda bama kan daidai sai lokacin ya gyaramu ko?"...... Yana ƙoƙarin ɗaure hannun Aryan ya nemi vein ya ce. "Muna kan daidai, amma muna yanke hukuncin da bai dace ba, ba'a hukunta wani da laifin wani, amma mu mun yi hakan". Ya faɗa game da yi wa Aryan wannan allura.
Miƙewa guru ya yi tare da cewa. "Bani da bakin magana, wannan hukuncin da muka yi shi ne daidai". Ya faɗa game da juyawa ya bar wajen. Bayansa Vir ya bi cike da tsananin tausayin guru, dan shi ma labarinsa bashi da daɗin ji, shi da Lion sun sha gubar mace ba kaɗan ba, shiyasa kome zasu ce kan mace ba mai ganin laifinsu, ko uncle baya ganin laifinsu, sai dai ya ce sun yi daidai.
Bayan ya yi wa Aryan allura sai ya rage mashi gudun AC, ya kulluɓe shi da duv kafin ya fita zuwa room na Lion. Tsaye a kan daddduma ya isko Lion yana sallah, while guru ma ya ɗauro alwala ya fito, a gefen Lion ya tsaya suka cigaba da sallah a tare.
Cikin toilet Vir ya nufa, alwala ya ɗauro shi ma, ya zo ya jera kusa da su. Suka fara nafilfilinsu. Jama'a dole IRON FIST su gagari kowa a duniya, mutanen dake da kusanci da UBANGIJINSU, kun san girman sallar dare kuwa? Kai dole su fi karfin kowa.
Basu kwanta ba har asuba, suka yi raƙatainil fajir kafin su shirya zuwa masallacin, a tare suka nufi in da Aryan yake kwance. Yana ta zuba barcin wahala, ya sha azaban ciwon ciki bawan ALLAH. Guru zai tashesa Lion ya ce su barshi, haka suka kyalesa suka nufi masallaci. Yau Aryan bai yi sallar asuba ba sai around 6 na safe, da suka dawo masallaci Lion ya tashesa.
Cikin ikon ALLAH ya tashi da lafiyansa, ya yi wanka, ya ɗauro alwala, sallar asuban ya biya tare da zama yana askar. Yana kammalawa around 7 ya fito, a dining room ya isko su guru zaune suna jiransa, dik suna shirye cikin tail coat ɗinsu iri ɗaya mai mugun kyau da tsada, shi kuwa yana sanye da thobe (arabs jallabiya) fari tas.
Wani irin yunwa yake ji, saboda alluran da Vir yai mashi, cikinsa har wani murɗawa take yi, yana zama ya ɗauki spoon, masu serving ɗinsu suka zuba mashi, sai kallonsa Lion yake yi, shi kuwa bai yarda sun haɗa ido ba, dan dik maganar da Vir ya faɗa daren jiya yana jinsu, dan haka bai yarda sun haɗa ido da kowa ba.
Dikkansu sai kallonsa suke yi, aikuwa ya mai da kansa kan abinci. Ana zuba mashi mandi rice ya sanya spoon ya ɗebo, zai kai bakinsa sai ya fasa ya nufi bakin guru ɗan autan IRON FIST da abinci. Ba tare da ya ɗago ya kalli guru ido cikin ido ba kawai ta danna mashi abincin a baki, ya zare spoon ɗinsa, ya ɗebo wani ya kai bakinsa.
A natse ya fara ci yana wani kara yin ƙasa da kai kamar wani maras gaskiya. Kallon Lion da guru Vir ya yi, sun haɗe hannu sun yi folding a kirjinsu suna kallon Champion. Ko sau ɗaya bai ɗago ya gansu ba har ya ci ya ƙoshi, ya ci abinci da mugun yawa yau, dan plate shake tab ya cinye, ya sha ruwa roba ɗaya full, sannan ya ɗauki tissue ya goge bakinsa, yana gamawa ya miƙe, ya dai ki kallonsu ya wuce da sauri ya fice daga room ɗin.
Yana fita ya je ya sanya kaya irin nasu sak, bai sake bi ta kansu ba ya nufi waje, kai tsaye Khaiza'ans House ya nufa. Su kuwa yana fita suka kalli juna, sai kuma suka ɗauki spoons a tare, ba wanda ya ce da ɗan uwansa kala, suka fara cin abinci a natse.
Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga gidan Abba, ya wani uban tamke fuska babu alamar wasa a tattare da shi.
Gabaɗaya family suna dining room suna breakfas, daga in da yake tsaye a parlon yana hangosu a cikin dining room ɗin. Zamansa ya yi a kan sofa yana jiran su kammala, ya fito da wayansa kenan sai ga kiran Seraphina ya shigo wayan.
Picking ya yi game da karawa a kunne. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi kafin ta ce. "Daddy what about school? In tafi da kafa ne?"........ Duba time ya yi. 7:30 ta yi, a dake ya ce. "Baki iya sallama and gaisuwa bane?"......... "Sorry, na manta ne, ina sauri batun school, good morning my husband".
Nisawa ya ɗan yi. "Za'a zo a kaiki, akwai in da zan je yau". Yana gama faɗa ya katse kiran, ɗaya daga cikin guards ɗinsu na benen SSO ya kira. Dama ya taɓa kaita school, dan haka Aryan ya ce mashi. "Jeka kai Cherry School yanzu".. bai jira amsarsa ba ya katse kiran.
A daidai lokacin su Faryan suka fito daga dining room ɗin, wajensa suka nufo, cikin girmamawa suka ɗaga mashi gaisuwa. Harleen ango sai wani kyalli face ɗinsa take yi. Dikkansu amsa ɗaya Aryan ya basu, daga nan bai sake yin magana ba.
Miƙewa suka yi, Hareen ya nufi sama ɗakinsa, shi kuma Faryan ya tsaya a wajen door yana faɗin. "Rimsha ki yi sauri kada ki yi latti"...... Ita kuwa ganin Aryan a parlo yasa ta gagara barin dining room ɗin ta fito, tana shirye cikin uniform, tana tsoron ko numfashinsa ta ji.
Miƙewa Abba da Ammie suka yi suka fito, while ita kuma Auntu Luna tana room ɗinta kwance tana barci, bata farka ba, dama in baku manta ba yar daddyn Noor basa tashi barci safe da wuri, fatan kun tina Noor a AZURE BARRACK a lokacin da Captain ke tashinsa da ruwan sanyi.
Abba yana ɗan dogara scepter ɗinsa ya kariso saman sofa, ya zauna game da mai da kallonsa a kan Aryan. Cikin girmamawa Aryan ya ɗaga mashi gaisuwa. Amsawa ya yi fuska ba yabo ba fallasa. Gaisuwa ya ɗagawa Ammie ma, tana murmushi ta amsa.
Shiru ne ya ɗan biyo baya, Abba na jiran jin me Aryan zai ce mashi, dan wannan zaman da ya yi da biyu, while Faryan na jiran Rimsha dake zaune a dining room ta gagara fitowa, ta yi ƙasa da kai, ko kallon in da Aryan yake bata iya ɗago ido ta yi ba, ɗan kwarin gwiwar da Seraphina ta bata jiya har take jin zata iya ganin Aryan tai mashi magana ma ya gudu, tana ganinsa yanzun nan ta ji komai ya gudu, tsoronsa ya ninku a ranta.
"Abba na zo ɗaukar yarinyar nan ne in koma da ita gidana". Aryan ya faɗa a dake....... "To Alhamdllh, abin da nike fatan ji kenan, ai gata ta shirya zuwa school yanzu, ka yi dropping ɗinta a school, idan an tashi sai ka ɗauketa ku wuce gidan naka ko?"...... Kai kawai ya jinjina, miƙewa tsaye ya yi tare da wucewa ya nufi kofa kafin ya ce. "Ta sameni a mota yanzu".
Rimsha dake jinsu ne idanunta suka cicciko da kwallah, gani take yi shikenan rayuwarta ta zo karshe idan ta je gidansa. Ƙoƙarin danne hawayen nata ta yi, ta mike ta fito wajensu Abba. Cike da farinciki Abba ya ce. "Mamana jeki mijinki na jiranki a mota, ALLAH yai maki albarka kin ji? Ki yi hakuri da halinsa watarana komai zai wuce".
Faryan da ya fi kowa sanin halin Rimsha ne ya yi mugun tausaya mata, sai yake jin kamar kada ya barta ta bi Aryan, bai tashi sanin yana son Rimsha ba sai da aka aurawa yayansa ita, da ace yasan ta halatta aure a tsakaninsu wlh da shi zai aureta ba Aryan ba, yadda suka saba, su yi kallo tare, su je yawo tare, a ɗakinsa take hira, ta kwanta a jikinsa, dik wani shirme ta kwaso yana biye mata, idan tana farinciki yana farinciki, idan tana cikin damuwa tare suke raba kuncin, wlh yana son Rimsha matuƙar so, bai san haka ha sai yanzu.
Masu tambayata alaƙar Rimsha da Aryan na hakikanin gaskiya idan kuma yi hakuri ai zaku ji, tin da kuka ga ya aureta ai kun san akwai auren kenan a tsakaninsu, Abba ai ba mahaukaci bane da zai aurawa kawu ƴarsa, tin da kuka ga ya yi hakan to ku san ba kawun nata na ainahi bane, keep reading zaku ji komai a gaba.
Ta zo wuce Faryan dake tsaye, suka kalli juna ido cikin ido, wani irin sabon sonta ne ya ƙara ratsa shi, idan suna hira a baya ce mata yake yi mai irin halinki zan aura Rimsha, dan ina son mace mai shagwaɓa, ALLAH ya yi ba rabonsa bace da ya aureta.
"Uncle Faryan wai ka ji Uncle Aryan ne zai kai ni school yau". Tamkar zata fashe da kuka ta faɗa. Hannunta ya riko suka nufi waje, zuciyansa babu daɗi sam, suna fita ya ce. "Babu komai Nisha ɗita, ki bi umarninsa kin ji? Komai zai wuce, ki gaishe mun da Seraphina". Ya faɗa lokacin da suke shiga elevator.
Kuka ta fashe da shi a cikin elevator game da juyowa ta rungumi Faryan, ita kaɗai tasan kuncin da zuciyarta zata shiga a wannan lokaci. Kafin elevator yai ƙasa da su ya dinga rarrashinta har ya samu ta yi shiru, ya ciro hanky ya bata ta goge hawayenta. Karɓa ta yi da sauri.
Kafin elevator ɗin ya buɗe kansa tuni ya goge hawayenta da sauri, ya riko hannunta suka fita. Zaune cikin mota suka isko Aryan yana waya. Ya ɗaure fuska tamau. Gidan gaba Faryan ya zo zai buɗe mata, wani irin kafurin kallon da Aryan ya dallah mashi bai san lokacin da ya saki hannun marfin gidan gaban ya buɗe mata na baya ba.
Hanky ɗin da ya bata ta rufe fuskanta da shi tana sakin sabon kuka can ƙasa dan ma kada Aryan ya jita. Cikin mota Faryan ya sanya, yana ɗaga mata hannu yana mata bye-bye. Tana kallonsa tana ƙoƙarin danne kukanta. Aryan ya figi motar da gudun gaske suka bar side ɗin.
Juyawa Faryan ya yi yana jin kuka na shirin kwace mashi, lallai ya yarda yanzu yana matuƙar son Rimsha, kawai sai ga hawaye a idanunsa, yana tausayawa halin da zata shiga. Cikin elevator ya koma, yana shiga parlo bai yi wa kowa magana ba ya haura sama da sauri ya shiga ɗakinsa ya rufo kofa, ciwon so ta motsa.
Su Abba basu lura da yana kuka ba, suna ta hira da Ammie, shiri ne kan zasu je neman auren Seraphina, Abba ya ce da sadaki zai tafi, Ammie ta ce a'a ya fara zuwa ya ga yanayin ahalinta tukun nan, to tsarin da suke yi kenan.
Shi kuwa Aryan yana figar motar nan bai zame ko'ina ba sai benensu, a tinaninta school zai kaita, sai taga akasin haka. Yana parking a benensu ya fito abinsa. Da sauri ta fito ta bi bayansa, kai tsaye cikin elevator ya nufa.
A hanzarce ta shiga ita ma dan kada ya rufe ya barta, a can gefe ta takure, ko numfashi mai kyau yarinyar nan bata yi tsabar tsoronsa, shi kuwa ya tsaya tamkar wani soja, ya zura hannaye a aljihu. Elevator na tsayawa ta buɗe, fita ya yi ta bi bayansa, kai tsaye ya nufi door nasu.
Sai da naurar wajen kofar ta yi scanning ɗinsa ko yana ɗauke da wani mugun abu, sannan yasa fingerprint ɗinsa ta buɗe. Ciki ya shige, da sauri ta bi bayansa, da yake ginin CRYSTAL PALACE dik iri ɗaya harta decorations na cikin gidajen, HEART OF CRYSTAL PALACE ne kawai ya fita daban, sai bata wani ga canji ba.
Sai dai suna shigowa Hero ya fito da gudu, ganin Aryan ya daka tsalle ya hayesa yana gurnani. Wani irin zabura ta yi, ta ja da baya tana ƙoƙarin guduwa ta fita muryan Aryan ya katseta da cewa. "Ga room ɗinki!". Ya faɗa game da nuna mata ɗakin dake fuskantar in da suke ba tare da ya juyo ya kalleta ba.
Sama ya nufa hero na kara ɗale mashi jiki. Ai a miliyan ta nufi ɗakin da akace nata, wani irin kuka ne ya kubce mata, tana shiga ta garƙame kofa, sai ta tsaya jikin kofar tana ta faman haki sama-sama, wani sabon kukan ta fashe da shi tana tinanin yadda zata yi ta sanar da Seraphina in da aka kawota, ga shi ba zuwa school yau kenan, wayarta na gida, ya zata yi? Ta yi iya kukanta babu mai rarrashi.
Dan kuwa Aryan kam ɗakin Lion ya shige, nan ya iskosu tsaitsaye suna fito da makullan motoci daga cikin drawers na wajen bed ɗinsu. A kallah makullan motoci 55 suka fitar, kuma dik makullah iri guda.
Tara makullah waje guda suka yi, guru ya keashesu dikka, Lion da ya tsare Aryan da ido ne ya ce. "Ina ka je?"...... Ba tare da ya kalli in da Lion yake ba ya ce. "Wajen Abba"...... Shiru ne ya ɗan biyo baya, guru ya katse masu shirun da cewa. "Mu je ko?".
Gaba Lion ya yi, suka rufa mashi baya, basu zarce ko'ina ba sai cikin motar Lion, daga nan suka nufi HEART OF CRYSTAL PALACE. Suna yin parking na motarsu Lion ya fara fitowa yana danna wayansa. Yana fitowa suma suka fito, gabaɗayansu fuska a tamke tamau kamar hadari.
Jingina da jikin motan nasu suka yi, after kaman mintuna 10 da tsayuwansu sai ga wasu jiga-jigan maza madaka karti, murɗaɗɗu masu kiran ƴan dambe sun shigo cikin gidan daddy. Jiga-jigan maza 40 ne ciff suka shigo gidan, dik suna sanye da white jeans and tshirts baki shi ma, fuskokinsu sanye da face mask, while hannayensu sanye da hand gloves, nose mask ɗinsu ma fari ne, boot na kafafunsu, a taƙaice daga sama har ƙasa wankan farare ne.
Baka iya ganin komai a jininsu sai idanunsu, kansu sanye da p-cap mai ɗauke da tambarin Lion a gaba. WHO ARE THEY?.
A gabansu Lion suka tsaitsaye, suka kame tamkar basa numfashi sannan suka sara masu. Miƙa masu makullan motar guru ya yi. Ɗaya daga cikinsu ne ya karɓa, fara rarrabe makullan motocin sannan ya fara mimmiƙawa kowannensu. Dik ya raba masu saura makullai 5. Miƙa mashi hannu guru ya yi, ya miƙo mashi ragowar makullan.
Cike da bada umarni Aryan ya ce. "Ku fito da motocin". Nufar wani tangamemen gate dake gefen kambun dad suka yi, a jere suka nufi wajen cikin takun dake nuna cewa jaruman maza ne.
Su Lion suna tsaye babu wanda ya ce da wani ƙala har waɗan nan guards ɗin suka fara fito da motoci a jere one by one. Wasu irin kafuran motoci ne wanda FIVE LIONS da kansu suka zaɓi irin design na motocin. (Kamar yadda ɗangote ya bada design ɗin irin motocin dake jido mashi kaya wanda dik Nigeria shi kaɗai ne mai irinsu dan shi ya zaɓi design ɗinsa)
Kaff faɗin US babu masu irin waɗan nan motoci sai su, a gaban kowani mota an rubuta FIVE LIONS da tambarin hoton kan zaki da ke firgita zuƙatan mutane ya sanya kakkarwa a jikin azzalumai. Zaku rantse da ALLAH motocin nan basu da tayoyi tsabar haɗuwarsu, kun tina irin motocin da suka je suka ɗauki Seraphina a ranar da gobara ya tashi a gidansu? To daga cikin waɗan nan 50 cars ɗin aka ɗaukesu aka yi amfani da su wancan rana, basa da kara sosai, sai in an kunna jiniyarsu, suna da jiniya sosai idan an kunna.
A harakar gidan dad aka faka masu, wasu kuma har waje aka fitar da su, motocin tamkar yanzu aka fito dasu daga leda saboda shekinsu, da yake suna rufe da car cover datti baya taɓasu.
Cikin ɗaya daga cikin motocin IRON FIST suka shiga, sannan guru ya umarci direbobin da su tashi motocin, Lion ya ce ayiwa motocin service, lokacin fara aikinsu ya yi! Dan haka su kutsa cikin US su ɗan yawata....... Tashin sense, akwai tada tarzoma kenan yau.
Aikuwa a jere motocin suka tashi suka nufi main gate CRYSTAL PALACE. A daidai wannan lokaci ita kuwa Lazy tana driving motarta tana nufo CRYSTAL PALACE. Watau akwai kura fa jama'a, FIVE LIONS zaku kewaye US da motocinsu, lokacin da kowa zai sansu ido da ido ya yi, ya Seraphina zata yi? Ya Khaiza'ans family zasu yi? Su waye iyayen IRON FIRST Vir da guru? Su waye su? Waye yake baiwa IRON FIST maƙudan kuɗaɗen da suke amfani da shi? Waye uncle Hussain? Menene a cikin containers da suka kama? Shikenan su 3D sun hakura da wannan babban project da IRON FIST suka kama ko dai zasu biyo sahu? Tambayoyin su dayawa fa, mu je dai zuwa.
----------------------🔥
D----O-----L They embraced death without fear, fully prepared for it, brave men, with the blood of heroism, the blood of love for truth, and the blood of justice flowing in them. Their ambition was to cleanse the world of the filth of society.
Washegari da asuba bayan sun yi sallah Leo is tara sojojinsu dikka, ya sanar dasu hukuncin da ya yanke kan kowa ga da wanda zai yi aiki, ya basu matsayin umarni, sannan ya ce. "Yakamata mu samu kalma guda da zamu dinga gane junanmu a koma ina ne". Ya faɗa yana kallon sojojin nasu.
Noor ya ce. "Yeah, tin daren jiya na yi wannan tinani"........ Leo ya ce. "Okey ku kawo shawara mu ji"....... Unays ya ce. "Fito is okey ba?". Kai Leo ya girgiza alamar a'a, sai ya ce. "Fito bai yi ba".
Vash ya ce. "Kukan kare ya yi?"..... Nan ma kai Leo ya girgiza. Juraiz ya ce. "Kukan kaza zaraka".... Nan ma kai Leo ya girgiza alamar a'a. Shiru wajen ya yi, dik suna tinanin abin da ya dace, Noor ya ce. "Bro mun baka gari kawai ka kawo naka".
"No, naku nike so". Leo ya bashi amsa. Dik sojojin sun kawo nasu amma Leo bai karɓa ba, Zaynish da dama shi a ko yaushe shi ne karshen magana a waje, sai ya yi dogon nazari kafin ya yanke hukunci, shi ne na karshen da ya ce.
"Awuuuuuuu ya yi, saboda a dajin nan akwai karnukan daji masu kukan Awuuuuuu sosai, so ko mun yi ba wanda zai zaci wani sign ne, amma kukan gaza ko kare dik za'a gane wani sign muke badawa tin da babu kaji da karnukan gida a nan, za'a gane mutane ne"...... Kai Leo ya jinjina game da yi wa Zaynish alamar jinjinawa da hannu ɗaya, wannan shawara ta yi.
Leo ya ce. "Ku koyi wannan sauti, idan kun jisa a sigar rauni yana nufin abokin aikinku yana buƙatar taimako, idan kun jisa a sigar faɗa yana nufin abokin aikinku yana nemanku kun ɓace mashi"..
Kai suka jinjina alamar to, daga nan ya ce dik su yi sautin su ji. Nan fa suka hau maimaitawa, jinjina masu kai ya yi, sannan ya miƙe game da yi wa Zaynish alama da ido kan ya biyosa, hanyar bakin ruwa suka nufa. While Noor da Vash suka miƙe a tare suka nufi cikin tantinsu. Sauran sojojin suka mimmiƙe suka koma in da suka saba zama, masu yi masu girki suka koma wajen girki.
A saman wasu duwasu Leo da Zaynish suka zauna a hakin ruwa, suna fuskantar juna, Leo ya ce. "Mun samu umarni daga sama yau da asuba kan mu je wajen hayakin a sirrance mu duba menene, dan haka ku shirya zamu yi tafiyar yamma, mu huɗu". Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya ce. "Akwai abin da Captain ya faɗa mun yanzu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 92 Chapter of 95