Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai na leƙa korea na ɗauko maku mutum guda, na sake rugawa da gudu na tafi cikin ƙuraishawa watau arabs na sake ɗauko maku ɗaya, sai cikin European suma na ɗauko maku ɗaya, na last ɗin kuma jinin Avaris ne. So kada ku damu da lallai sai kun zaƙulo FIVE LIONS kun haɗasu sun cika biyar ɗin ciff, kada ku damu a hankali zasu haɗa kansu su kuma bayyana maku kansu, dan haka kada ku sanyawa kwakwalwarku pressure, na hutassheku! Dan naga wasu sun damu suna son sanin ZAKUNA BIYAR to ku kwantar da hankulanku.........🙌🏻 Da sabon salon ZAKUNA BIYAR yake tafe, haƙiƙa ZAKUNAN ne guda BIYAR, amma daga yankuna daban-daban na duniya na zaƙulo maku su, ku more karatu, sai ma mun natsa cikin STEP 2, zaku ci karo da surprise!. Vir ne ya amsa da. "Nigeria kuma ana zaune ƙalau?"....... Guru dake faman shiga wajen closet ɗinsu ne amsa da. "I miss mai Grandpa"....... Aryan ne ya ce. "Babu in da zaka je"...... Hararan Aryan ya yi kafin ya shige cikin wajen cleset ɗin nasu. Aryan ne ya ce. "Miss you more bro". Ya faɗa yana kallon Vir. Ɗan sipping americanonsa Vir ya yi kafin ya amsa da. "Today remain 53 days in dawo ai"...... Lion ne ya katsesu da cewa. "Muna da aiki a gabanmu, let's meet in our room". Ya kai karshe tare da ɗaukar laptop ɗin, ya sauƙo ƙasan bed ɗin, Aryan ne ya rufa mashi baya kafin hero ya biyo bayansu. Kai tsaye ɗakin aikinsu suka nufa, a saman table kusa da Computers ɗinsu Lion ya ajiye laptop ɗin, ya saita yadda Vir zai ga aikins da kyau, sannan suka shiga aiki game da fara tattaunawa. Aryan ne ya fara buɗe saƙon Lion kan Avaris, dogon note ya tura masu a laptop ɗinsu kan yanayin rashin tsaron dake arewacin Avaris da ya jima yana haɗa bayanai da hujjoji a kansu. Duba saƙon Aryan ya fara yi, a daidai lokacin guru ya shigo, ya gama shirinsa cikin pj's milk color, gaban nasa computer ya zauna tare da kunnata. Likes comments and share fisabilillah. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-12.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 48 Duba saƙon Aryan ya fara yi, a daidai lokacin guru ya shigo, ya gama shirinsa cikin pj's milk color, gaban nasa computer ya zauna tare da kunnata. Nashi saƙon ya fara dubawa, sai da suka gama suka ɗago kai a kan Vir dake pressing wayansa, ya ɗauke hankalinsa daga kansu, Aryan ne ya ce. "Bro wannan ɓangaren aikinka ne, ya za'ayi hakan ta kasance? Dik wani fitina kenan daga WS ya fito? Su ne ke shirya komai?". Ɗago fararen idanunsa Vir ya yi, irin kallon ƙasan nan yai masu kafin ya ajiye wayansa a gefen pool da kafafunsa ke ciki, yana da sanyin murya sosai, daga yadda yake magana zaku san mutumun ne dake da natsuwa sosai, baya son hayaniya kamar dai IRON FIST ɗin. "Kwarai, sune matsalar duniya bakiɗaya, in har muna son gyara, to dole mu fara tarwatsasu, dik wani ta'addanci da kake gani a Avaris ɗaukar nauyinsa ake yi, ka manta karfin gwamnati ne?"...... Kai Aryan ya girgiza alamar a'a. Cigaba Vir ya yi da cewa. "A irin karfi da gwamnati ke da shi ta'addanci bai isa ya yi 24 hours a ƙasa basu tarwatsa shi ba, musamman ƙasa irin Avaris, kasar dake da komai, dik wani abin da ake nema suna da shi, ban taɓa ganin ƙasar da ALLAH yake sonsu irin wannan ƙasa ba, har mamaki abin yake bani wani lokaci". One after the other words ɗinsa yake fita cikin natsuwa kamar Lion ne yake magana. Guru ne ya amsa da. "Gaskiya ALLAH yana sonsu fiye da yadda ake tinani, ba dan haka ba shirin da aka yi a kansu wlh da basu yi saura a duniya ba, amma dik abin da aka shirya masu sai ALLAH ya basu kofar kaucewa, kaɗan ne yake samunsu"..... Aryan ya tari numfashinsa da cewa. "Kuma a haka basa godewa ALLAH ba, kullum suna cikin complain, da sun san abubuwan da ake shirya masu wlh da sun tabbata suna godewa ALLAH". Guru ya cigaba da cewa. "Suna da man fetur wanda shi ne yafi sanuwa a duniya matsayin karfin tattalin arzikinsu wanda kuma a zahiri ba shi bane! An ɓoyewa duniya da ƴan ƙasan ainahin tattalin arzikinsu, an barsu da tinanin cewa fetur ita ce abin da suke da shi mafi karfi a cikin arzikin da suke da shi, dik bama wannan ba, WS ta fara ƙoƙarin rushe amfanin fetur a duniya, sun fito da wani tsarabe-tsarabe wai fetur na fidda hayaki wanda zai iya lalata sararin samaniya, wanda kuma ba dan al'umma suke wannan ba, so kawai suke su gyara yanayin sararin samaniyar ne saboda waɗan nan jiragensu da suke son yin gwanjonsu wa duniya, watau jiragen da basa amfani da mai, (wanda na faɗa maku a baya) shi ne suka fito da ƙage wa fetur, suna son dakatar da amfani da shi, kunga a nan ma Avaris zata shiga wahala, saboda sun fi kowa dogara da fetur a duniya, abubuwan hawansu, komai da fetur suke amfani da shi".... Ya ɗan nisa tare da cigaba da cewa. "Amma da yake ALLAH yana son mutanen Avaris me yafaru?".... Aryan ne ya ce. "To ai an ɓoyewa ƴan kasan abin da yafaru"........ Nisawa ya yi tare da cewa. "Ana tsaka da wannan rikici na ƙoƙarin kashe fetur a duniya sai ALLAH ya baiwa Avaris arzikin aluminum da ake haɗa battery na motocin da suke ikirarin za'a koma amfani da su, a wannan gaɓa ma sun so Avaris ta ci wahala, amma sai ALLAH ya basu wannan arziki wanda ƙasashe ɗaiɗaiku ne suke da wannan arziki a duniya, sai me ya biyo baya?"........... Lion ya amsa da. "Sai suka kwantar da maganar hana amfani da fetur, suka kuma shiga Avaris dan kwasan wancan arziki ba tare da ƴan ƙasa sun sani ba". Aryan ya ce. "Hmmmmm Arewacin Avaris tana da manyan ma'adinan ƙasa sama da 30, wanda suka haɗa da, gold shi ya fi yawa ma, amma mutanen Avaris basu sani ba, jahohi 6 suke da gold a Avaris, amma mutane basu sani ba, kuma gold bana wasa ba, yau sama da shekaru 15 suna ɗeban gold ɗin su fitar da shi waje, amma har yanzu bata ƙare ba, sun fitar da kuɗin ƙasan kawai sun kai wata banki a duniya sun ɓoye, su basu taimaki ƴan ƙasa ba, su basu isa su cinye kuɗin ba dikka ba....." Vir ya ce. "Bakin zalunci ne kawai, aikin mu zai bi ta kan wannan banki da suke ɓoye kuɗi a ciki ɗin ma ai, one day one time su jira diran IRON FIST a kansu! Dik sai sun ɗanɗani azaba irin wanda suke ganawa mutanen Avaris, ba zamu ragawa ko mutum guda ba!!". Cikin kunar rai yai maganar, kaman Lion yake, akwai zafin zuciya da saurin hawa, yanzu haka shi da Lion da Aryan ji suke tamkar su gansu a gaban WS, da wani irin azaban da zasu yi masu sai sun san lallai hannun IRON FIST suke! Cigaba guru yai da cewa. "Aryan, bayan gold ma akwai manyan ma'adanai kamarsu tantalite wanda da shi ake yin capacitors a wayoyi, taba da laptops, akwai Tin wanda da shi akeyin solder, kayan lantarki, kwalaye masu hana abu yin tsatsa, suna da columbite da shi akeyin kayan jirgin sama, roba mai jure zafi, alloy, amma yau an wayi gari Avaris bata da jirage guda 10 masu kyau na kanta, ko in ce na ƴan ƙasa, sai kame-kame, idan gwamnatin ƙasar ma zata sayi jirgi sai second hand, idan kaga jirgi mai kyau a Avaris to na ƴan kasuwa ne bana gwamnatin ƙasar ba, ga shi kuma suna da columbite da suke sayarwa ƙasashen dake son cigaba suna haɗa jiragen sama suna keta hazo!". Ya ja dogon numfashi kafin ya cigaba da cewa. "Suna da iron ore wanda da shi ake yin karafuna, siminti, injuna da ginin layin dogo, amma yau an wayi gari Avaria dik wani inji mai kyau idan ka gani daga wajen Avaris aka saya aka shigo masu dashi, basu da kamfanonin haɗa dik waɗan nan, sai dai a ɗebi ma'adanan a sayarwa waje, ƴan ƙasan dik basu san da akwai wannan ba! Baya ga shi akwai lead zinc, akwai lithium, gemstones, sapphire, garnet, amethyst, tourmaline, sannan suna ma da coal dayawa, musamman arewa maso gabas na ƙasar". (Gombewa how far? A Nigeria kuma nasan kuna da arzikin coal sosai! Hakane ko? Ba iya Avaris ba, kuma kuzo ku faɗa mun me kuke yi da naku? Gombawa daku nike fa, Gombe ikon God, kuma kuna da tatalin arzikin ƙasa dayawa fa, to ALLAH yasa ya amfaneku idan kun gano kuna da shi!.) Cigaba guru yai da cewa. "Akwai limestone wanda ake siminti da shi, suna da gypsum, kaolin, bentonite, manganese, phosphate, granite, dolomite, quartz, copper, nickel, graphite, asbestos, uwa uba suna da uranium wanda da shi ake haɗa wutar lantarki, nuclear, nuclear da manyan ƙasashe ke ta faman rikici a kansa, wanda dik ƙasar da ta mallaketa ake mahaukacin tsoronta, amma yau an wayi gari abin da ake haɗata yana a Avaris, amma Avaris bata da ishasshen wutar lantarki ma bare aje kan nuclear wanda kun sani ko family nuclear basu da shi bare asalin nuclear wanda zai iya tashin ƙasa gabaɗaya, abin taƙaici sai dai wasu can su zo su masu dabara su kwashi uranium a fita da shi, su je su wadata ƙasashensu da wutar lantarki, su kuma wadata ta da makamai da suke dawowa su sayarwa Avaris ɗin". Lion ya tari nunfashinsa da cewa. "Kuma makaman da suke sayarwa sojojin Avaris ɗin ai very local ne! Basa taɓa sayar masu masu inganci, alhalin daga ƙasarsu suka kwashi uranium ɗin". Ya kai karshe yana sunkuyar da kai, tin ɗazun shi da Vir sun yi shiru ne saboda tafarfasar da zuƙatansu yake yi, idan suka ce zasu buɗe baki zasu iya haɗiyar zuciya su mutu tsabar takaicin abin da ake yi wa al'umma!. (To mutanen Adamawa state sannunku, na ce ba a Nigeria kaf na ji ku ne kuke da arzikin uranium a ƙarƙashin ƙasarku kamar na Avaris, na ce fatan kuna yin abin da ya dace da shi ko? Fatan kun san da shi kuma kuna ƙoƙarin ganin ko an sayar a gyara maku gari da kuɗin ko?😭💔) Guru ya cigaba da cewa. "Suna da crude oil, watau ɗanyen man fetir wanda a cikinsa ake cire maku su gas da sauransu, baya ga haka kuma suna da natural gas, Iskar gas, suna da bitumen, glass sand, kaolin, gypsum, granite, laterite, manganese, talc, wolframite, lignite". Ya kai karshe yana girgiza kai, takaici tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, ace dikka wannan uban tattalin arzikin, kuma dik masu mugun tsada da duniya take nema, amma ace yunwa kawai ta gigita ƴan ƙasar, basu da abin da zasu ci, alhalin da kuɗin uranium da zasu dinga sayarwa ƙasashen waje kawai zai wadaci ƴan ƙasan dik abin da suke so, sai dai ina........ Abin mamaki da takaici sai su tara kuɗin da har ɗan auta a zuriarsu ya girma ya kare rayuwansa da zuri'arsa kuɗin da suka tara rabi bai ƙare ba, kuɗin da ɗan adam bai isa ya karan da shi ba, kuma kullum ƙara sata suke yi, sai ka rasa me zasu yi da kuɗin! Ka rasa ina zasu kai son duniyar da zamu tafi mu barta, duniyar da tamkar wuni muka zo, babban abin takaici sai su kai kuɗaɗɗen kasashen waje su ajiye, ƙasar da suka ajiye kuɗin ta yi ta juya kuɗin tana amfanuwa, su nan suna sake satar wasu su fitar, wani ma yawan kadarorinsa dake wasu ƙasashe wlh har ya mutu ba'a san in da suke ba, wani ma tsabar ya sata ya sata idan ya sayi wasu kadarori a ƙasashe yana mancewa da wasu su salwanta, wani kuma ya mutu iyalansa ma basu san yana da kuɗi a ƙasa gaza ba! Sun dai sata sun fitar, ya ALLAH ka dubemu da idanun rahma!!. Aryan da jikinsa har wani tsuma yake yi saboda takaici ne ya ce. "Dik wannan tattalin arzikin da ALLAH ya mallaka masu amma ƴan ƙasar basu da wani abin yi, sun zauna basu da aiki kullum sai dai ka gansu a media suna faɗar addini, aƙida ko ƙabilanci, ko yunwar cikinsu basu iya gama maganinta ba, kaga matashi har matashi, mai ji da rai da lafiya, madaki karti, sai ya shiga ɗaki ya saita camera ya hau zagin wata ko shiga faɗar da bata shafesu ba, wasu matasan da basu san ciwon kansu ba ma sai ka samesu da musayar yawu a media a kan kwallon kafa, ko faɗa da mata".. Wani irin numfashi Vir ya ja tare da saukewa a hankali, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa na takaici kafin ya ce. "An kashe masu zuƙata ne, an dasa masu tsoro, an kashesu da yunwa, ai babban makaman da suka rike shi ne rikita al'umma da yunwa, kana jin yunwa kowani irin aiki aka baka zaka yi dan ka ci abinci, sannan wannan tsoro da aka dasa masu ba zai taɓa barinsu ba, and kada ku manta WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa suka fi karfinsa!!". Aryan ya amsa da. "Ai idan ba ga ALLAH mutanen Avaris suka koma ba wlh babu abin da suka isa yi wa shugabanninsu! Saboda WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa zasu iya fito na fito da shi, suna gani ana zalunntarsu amma ba zasu iya yin komai ba, sai dai su yi ta banbami suna cika baki a media!". Iska mai zafin gaske Lion ya furzar daga bakinsa, wai yana matsayin leader na IRON FIST kuma ace a ƙasarsa, ƙasar mahaifinsa ake wannan ɓarna? Ya ALLAH, shi kam zai iya haɗiyar zuciya saboda takaici, lallai lokacin yin aiki ya yi, lokacin kawo karshen dik wani azzalumi ya yi. Dama ina baku manta ba IRON FIST sun tafi hutu ai! Tin da suka kashe ministar ba sun ce sai bayan shekara ɗaya ko biyu zasu sake yin aiki ba? To shiyasa kuka ji sun yi shiru suna ta bincike kawai, yanzu lokacin komawa bakin aiki da gaske ya yi, Seraphina zata rage ganin daddy Aryan, dama san suna hutu ne yasa yake da ishasshen lokaci!. Da kyar Lion ya iya cewa. "Gano WS babban abu ne, aiki ne ma matuƙar wahala, amma zamu tsokanesu ta yadda da kansu zasu bayyana kansu!"..... Kallon juna suka yi, basu gane in da Lion ya dosa ba, suna son karin bayani, hakika sun san gano WS ba abu bane mai sauki, dan WS ɗin na farko ba mulki suke yi, basu a cikin siyasa, su mutane ne dake rayuwa kaman sauran mutane, kila ma suna kusa da kai a halin yanzu, suna rayuwa very simple, amma suke naɗa masu mulki, abin mamaki, su fa basa son hawa gujerar mulki, da suna son hawa da sun hau, su dai suna gefe, amma dik wata kafunci da zalunci suke shiryasa, idan kuna jin ana faɗin masu naɗa masu mulki to su ne. Tsabar ɓadda kama ma suna tafiya ba security, ba ɗan sanda, babu sojoji, ba zaku taɓa tinanin su bane, kuma suna ko'ina, kunga kuwa kamasu abu ne mai matuƙar wahala, dik duniya harta shugabannin da suke ɗaurawa a kan mulki babu wanda yasan kamanninsu, kai haɗarin mutanen nan ya zarce yadda kuke tinani, su ne mutanen da ko kana kan mulki in baka bi umarninsu ba a cikin ƙasa da 5 mins zasu iya kasheka, baka isa ka guje masu ba, suna koina, suna da ido dake ganinka a dik in da kake, wlh haɗarinsu ya fi na nuclear, sai dai mu ce ALLAH ya karemu ya kawo mana karshen dikkan wasu azzalumai! Aryan da ya fi kowannensu fahimtar Lion ne ya ce. "Kana nufin siyasar Avaris zamu shiga?"....... Vir ya amsa da. "Ta hakance kawai zamu tsokanesu su bayyana kansu, dan a halin da ake ciki ka kuskura ko magana ka yi a kan shuwagabannin Avaris ɓatar da mutum ake yi, idan kana da rabon rayuwa a daka maka warning a sanya maka tsoro!". Jinjina kai dikkansu suka yi, dan kuwa haka ne, suna gani a media ta kasar, suna bibiyar dik wani motsin Avaris sosai......... "Ba zamu shiga siyasar Avaris ba, amma dik wani gurɓatacce shugaba zamu tugesa, zamu farkar da matasan Avaris mu cire masu tsoro, hakan zai yi matuƙar tayarwa da ws hankali, dole zasu nememu da kansu dan su ga bayanmu! Kunga daga nan zamu kamasu a sauƙaƙe". Cewar Lion ɗan baiwa mai basira da wayon kama azzalumai, kai Lion ne ya cancanci sunan Smart fa!. Jinjina kai suka yi, lallai haka ne, wanna shawara ta yi, zasu kamasu a sauƙaƙe! A natse Vir ya ce. "Ya batun bank ɗin can?"....... Zuba mashi idanu suka yi, alamar suna jiran karin bayani, Lion ne ya ce. "Zamu gane wace bank ce kuma a wace ƙasa take". ....... Aryan ne ya ce. "Awww bank da suke kai kuɗin Avaris ko?"........ Jinjina kai Vir yai. Lion ya ce. "Zamu gane, kuma zamu kwashe dik kuɗin Avaris dake wajen, In Sha ALLAH zamu gina ƙasar Avaris da shi!". Kai suka jinjina alamar shawarin ya yi. Aryan ya ce. "Wani plan ne a ƙasa a kan aikin?"........ Lion ya ɗago da idanunsa a kan Vir wanda shi ma shi yake kallo, while su Aryan dikka Vir ɗin suke kallo. Kyafta masu idanu sau biyu ya yi kafin ya ce. "Next week zan shigo, ina zargin wannan bank ɗin yana tsakanin ƙasashen nan guda, France, America ko England!". Shiru suka ɗan yi, can Lion ya juyo da karfi ya sauke kallonsa a kan Aryan, in a cool way ya ce. "Aryan daga wani bank aka sakawa matar can (mom ɗinsu) kuɗi? Me sunan bank ɗin?". Yanzu tinanin ya faɗo mashi a kai. Shiru Aryan ya yi, sai yanzu shi ma ya ji yana zargin wannan bank ɗin. Yana ɗan zazzare idanu kaman mai wani tinani ya ce. "Wani bank ne wanda ban taɓa jin sunansa bama a duniya sai a wannan rana, kuma tin daga wannan rana har yau ban sake jin sunansa ba, sunan ma isn't complete name, just alphabet ne kawai, something WS-STSW-BANK, haka sunan yake". IRON FIST akwai ƙwaƙwalwa, tsawon shekaru bai manta sunan bank ɗin ba. Wani pen dake gefensu Lion ya ɗauko, ya jawo wani book dake gefe, WS-STSW-BANK ya rubuta a kan littafin, ya cire WS farko, ya WORLS SYSTEM, ya cire STSW na biyu, ya rubuta STARS WORLD BANK, ya haɗa a ƙasa ya rubuta WORLD SYSTEM STARS WORLD BANK! Sun sha madarar mamakin ganin yadda a cikin sauƙi ya fitar da sunan, ya ALLAH, watau brain kyauta ne daga ALLAH da ya baiwa IRON FIST, Lion gifted ne!!. To yanzu sun gano sunan bank ɗin, saura su gano a wace ƙasa take!. Wani numfashi Lion ya ja wanda kana ji kasan na takaici ne, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Any danger is from ws, dik wani balai ma daga can yake fitowa, watau bank ɗin ma nasu ne kenan, da kyau!". Aryan ne ya ce. "Ni yanzu damuwata ɗaya ne, su Nirash, sun tafi Mission, kuma a Arewacin Avaris, wanda dani da ku dik mun san dik wani motsinsu ana sane da shi, kada ku manta ƴan ta'addan ɗaukar nauyinsu ake yi, kunga kuwa ba za'a bar wasu sojoji su kawo karshensu ba, saboda moriyar abin da ws suke ci". Guru ya ce. "Su Nirash basu san komai ba, yakamata mu taimaka masu, dik wani motsinsu ƴan ta'addan suna gani, kunga sun shirya masu tin ma kafin su zo"......... Vir ne ya ce. "Su Nirash jinin IRON FIST na gudana a jikinsu". Lion ya ce. "Dik cikinku kada wanda ya kuskura ya taimakawa su Nirash, ku kyalesu, muma a lokacin da muka yi Mission ai bamu san ƴan ta'addan na ganinmu ba, da muka ji wahala ne muka yi experiencing ɗin suna ganinmu har muka nemanwa kanmu mafita, dan haka su Nirash sune magada IRON FIST ko bayan ranmu! Su zasu zauna a kan kujeran da muke, saboda haka babu wanda zai taimaka masu, su yi faɗa su kaɗai, su sha azaba su kaɗai, su kwaci kansu su kaɗai! Su zama mazan gaske". Vir ya amsa mashi da cewa. "Suna gama wannan Mission ɗinma zamu turasu horon SSO kafin mu basu horon IRON FIST"....... Kai Lion ya jinjina alamar haka ne, dama abin dake ransa kenan, ya sha alwashin mayar da su Leo tamkar su, su zasu zama magadansu!. Sun jima suna tattaunawa suna tsara yadda zasu ɓullowa wannan al'amari. A can kuma Abba nata shirye-shirye wannan coming Friday nan da kwanaki uku kenan zai ɗaura auren Aryan, Harleen, ko sunƙi ko sunso, haka ko daddyn Noor yaki ko ya so su Aunty Luna sai sun zama surukansa ta karfi da ya ji...... Ni kam zanga yadda za'ayi wannan aure, ga Aryan a nan har Seraphina ɗin ma ya watsar saboda wannan shegiyar zuciyar tasu ta gado, Abba ya ja mana aiki. Shi ma daddyn Noor yana ruwa, ko yaki ko ya so sai ya baiwa Abba auren yaransa, ga kakan Noor ɗan zafin rai shi ma kuma ɗan hau, ni ban san yadda za'a kaya bama a wannan al'amari. Sai around 1 na rana suka tashi tattaunawar, a nan ne kuma Aryan ya ɗauko wayansa dan ya kira Faryan, sai a lokacin ya tina da Seraphina, siririn tsaki ya ja, ya so sherata amma sai ya ji ba zai iya ba, sonta ya rigada ya mamaye zuciyansa. Su Lion sun miƙe sun nufi room ɗinsu dan wanka da shirin zuwa masallaci, while shi kuma Aryan yana zaune, sun katse video call da suke yi da Vir. Number ɗinta ya shigar zai danna kira sai ya tina ashe ta fara zuwa school, ɗan dafe kansa ya yi da ya tuna ashe yau bai kaita school ɗin ba, siririn tsaki ya sake ja kafin ya shiga binciken kwanaki biyu me take yi a waya. WhatsApp ɗinta ya fara shiga, dan ya yi connecting da wayansa, dik wani chat ɗinta suna sauƙa a wayansa. Kunna voice nata ita da Rimsha ya fara yi yana sauraro, wani wajen ya ja dogon tsaki, wani wajen ya haɗe fuska, unexpected ya isa in da Rimsha ke zugata kan ya kyale daddynta ta rungume Uncle Faryan, ai bai san lokacin da ya wastsake ya zabura kamar zai miƙe daga kujerar da yake ba, sai kuma ya koma ya zauna, cigaba da saurara ya yi. Jin takaici na shirin sanya zuciyarsa fashewa ne yasa ya dakatar da voice ɗin, abin da ya bashi takaici kuma yadda daren jiya Seraphina tai wa Rimsha voice cewa. "Nisha ki faɗawa Uncle Faryan ina son shi, daddy ya daina kulani, tin safe da ya kaini school bai sake zuwa ba, zan yarda da maganarki kawai in kyale daddy in so Uncle Faryan". Ya ALLAH wani irin huci da Aryan ya fara yi, kishin ta motsa. Fita chat ɗin ya yi, ya shiga chat ɗinta da number Faryan da ya gani. Ai yana shiga ya fara cin karo da kalaman soyayya da Faryan ya dinga tashin kanta da su, ga shi shi kuma ba iya soyayyar nan yai ba. Ai wani irin zafin kishi ne ta motsa, jikinsa har yana rawa wajen fita ya laluɓo number Faryan, sai dai wayar a kashe ko da ya kira. Da sauri ya miƙe tsaye, har ya manta bai kashe computer ɗinsa ba.

Chapter 59 of 95