da shi da kansa ya yi gaba ya buga kansa da jikin glass, wayar hannun nasa ta faɗi.
Ba komai yasa ya yi wannan firgicewa ba face irin murya Harleen sak da ya ji, tabbas ba wai kunnensa bane, irin murya Harleen ne, wlh babu banbanci, kai zai iya rantsuwa wannan shi ne ma.
Amma dan ya tabbatar sai ya lalluɓo wayansa cikin kiɗima, hannunsa har wani kerma yake yi, jikinsa na wani irin tsuma, number Harleen ya kira, at this time sai ya ji wayar busy alamar ana call da ita, hakan ba ƙaramin ƙara gigita shi ya yi ba, lokaci guda ya ji tamkar an yi formatting na brain ɗinsa, ya ji kamar ba shi ba.
Dropping phones ɗin ya yi a saman seat, kifa kansa a saman steering motar ya yi, jim for almost 30 mins ya yi, bai ma san time da aka katse kiran ba, sai da ya wastsake ya dawo cikin hayyacinsa, ya yi ƙoƙarin koran shaiɗanin da ya shiga kansa, dan shi yasan Harleen bashi da power ɗin iya aikata wannan abin, idan har da sa hannunsa, to akwai jiga-jigan dake bayansa waɗan da suka tsaya mashi, wanda sam baya fatan hakan, yana fatan ALLAH yasa kamannin muryan ce kawai.
Da kyar ya iya kunna motarsa ya nufo gida. A tinaninsa zai sami su Lion suna barci, sai ya isko Lion a zaune a parlo rike da laptop yana pressing, ya ɗan yi barci ya farka. Bai yi mashi magana ba ya nufi hanyar wucewa cikin room ɗinsu, jikinsa har yanzu tana wani irin rawa na tsananin ɓacin rai, baya son motsa laɓɓansa da suka yi mashi mugun nauyi.
"Aryan!". Lion ya ambaci sunansa. Shiru ya ɗan dakata da tafiyar ba tare da ya juyo ba. Kallon tsab Lion ya mashi kafin ya ce. "What are you trying to hiding for us?"
Wani irin yawu mai ɗaci ya haɗiye, da kyar ya iya juyowa, nisawa ya ɗan yi kafin ya fara kokarin motsa lips ɗinsa da suka gagara yin magana. Sake binsa da kallon mamaki Lion ya yi, sai kuma ya nufi ajiye laptop ɗin ya miƙe.
Daga cikin laptop ɗin wani golden voice mai sanyi da mugun daɗi ya ce. "What's going on there bro?". Ɗaura laptop ɗin a saman table yai, in a low way sosai ya ce. "Some minutes VIR". Ba tare da ya jira amsarsa ba ya miƙe ya nufo Aryan dake tsaye.
Yana zuwa ya riko shoulders ɗinsa yana sake tambayarsa lafiya yake kuwa?. Faɗowa jikinsa gabaɗaya Aryan ya yi, take sautin numfashinsa ta canza, ya yi ƙoƙarin rike kansa amma kamar ba zai iya ba, zuciya shegiyar aba ce, shi da Lion akwai zafin zuciyar balai, ya gagara magana ko kaɗan.
Sosai Lion ya ji matuƙar mamakin jin bugawar zuciyar Aryan ta canza, tana fita da karfi-karfi irin wanda ya razana da abu haka, abin mamaki IRON FIST da razana? Meya razana mashi ɗan uwa? Lion ya tambayi kansa. Ni kam na ce ba dole ya razana ba, ace ƙaninka uwa ɗaya uba ɗaya ka ji muryansa a irin wannan waje da yanayi, dama can ga abubuwan da ya faru, ka ɓoyewa Lion abubuwa da dama, ka barsa a zuciyarka kai kaɗai saboda son da kake yi mashi, ka shanye zafin kai kaɗai baku raba ba, kuma ace da sa hannun wani naka ai dole ka kuɗime.
Tin ɗazun ƙoƙarin karyata kansa Aryan yake yi, yana ƙoƙarin tursasawa zuciyarsa ta yarda kamanni ne kawai ba wai murya bane iri guda, amma abinku da shaiɗan, ya hana mashi yarda da hakan, ya hana zuciyansa sukuni.............. Rage tsawonsa Lion ya yi, ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye room ɗinsu ya kaisa, a saman gado ya kwantar da shi, ya dawo parlo ya ɗauki laptop ɗinsa da waya.
A tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da cewa. "Vir goodnight, my heartbeat is not feeling well"........ Ai Aryan ya wuce bugawar zuciyar Lion, dan wani irin son da yake mashi baki ba zata iya faɗa ba, shiyasa wani lokaci yake ce mashi shi ne bugawan zuciyansa, idan babu shi zuciyansa ba zata buga ba!.
Vir dake zaune saman bed ne ya amsa da. "I want to see him". A sanyayye yake magana, wani haɗaɗɗen korean guy ne, fari kal tamkar madara, kuna ganinsa ba tambaya kun san korean ne, kyakkyawan gaske ne, lips ɗinsa purple color, while gashin gerarsa tamkar zasu haɗe gasu bakinkirin yana wani sheki, kashin kansa tamkar wanda aka kifawa huka, amma ya bayan wuya yana yana da ɗan tsawo har ƙasan wuyansa, ta gaban goshi kuma a daidai saitin gerarsa gashin ya tsaya, nasa ɓangaren shi ma ya haɗu.
Babban aminin su Leo ne tin na yarinta, yanzu haka wani Mission suke yi yasa yake ƙasan Russia baya tare da su, tsawon shekaru uku aikin zai ɗaukesa, yanzu saura mashi watanni biyu kawai ya dawo, a tare suke aiki, amma wannan aiki da ya tafi Lion ne ya tura shi, kuma aikin sirri ne, a gaba zaku san wani irin aiki ne, muje dai zuwa.
"No goodnight". Lion ya faɗa. Ba tare da ya jira amsar Vir ba ya katse video call ɗin, ya kashe laptop ɗin tare da ɗaurawa a saman laptop table dake gefen bed ɗinsu. Saman bed ɗin ya hau, ya riko hannun Aryan yana kallon kyakkyawan fuskansa da take cike taf da damuwa, kura mashi idanu Lion ya yi na ƴan tsakanni kafin ya ce. "To much of pressure, all for what?". Ya faɗa yana ɗaura ɗayan hannunsa a saman gashin kan Aryan.
Nisawa Aryan ya yi tare da riko hannun Lion sosai. "Bro give me sleeping pills or injection now". Ya faɗa a lokacin da ya ji kansa na barazanar tarwatsewa.
Sauƙa ƙasan bed ɗin Lion ya yi. Waje ya fita, jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da sirinjin allura. Zuwa ya yi yai mashi, sannan ya fita zuwa mayar da alluran, kafin ya dawo Aryan ya yi barci. A maimakon ya kwanta yai barcin shi ma, sai ya zauna ya tofa wa guru da Aryan ɗin addu'ar barci, sannan ya sauƙo ƙasa.
Waje ya fito ya koma ɗakin aikinsu dan ya binciki Aryan sosai, meyake damunsa? Meyasa ya gagara yin magana? Ya gagara yin barci sai da allura? Bugawar zuciyarta ta canza, meyafake faruwa?. Gara ya bincika da kansa ya gani.
After some times.
Aryan ne tsaye a parlon gidansu Seraphina, hannunsa rike da waya, yau ya yi balain kyau cikin hoodie farare tas, ya sanya hular kayan a kansa, daga ta ciki kuma ya sanya p-cap, ya zura hannu ɗaya a cikin aljihu, ɗayan hannun yana pressing phone, sai tashi daddaɗar kamshi yake yi.
Madan ce ta fito, a mutunce suka gaisa kafin ta wuce cikin kitchen. Yana tsaye a wajen Aunty Safiyya ma ta fito, gaisuwa ita ma ta ɗaga mashi, dikkansu ba tare da ya ɗago ya kallesu ba ya amsa, amma all they're movement yana sane da shi, kallonsu ne kawai bayayi.
Wucewa ta yi ta bi bayan Madam ita ma, still yana tsaye Aisha ta fito sanye da uniform, sket baki zuwa gwiwa, da riga fari mai dogon hannu, sai socks farare kal-kal, gashin kanta a ɗaure gida biyu, ta sanya mashi ribon, tana rike da school back ɗinta.
Har ƙasa ta durkusa ta gaida shi, ita ma ba tare da ya ga in da take ba ya amsa, miƙewa ta yi ta koma saman sofa ta zauna, a daidai wannan lokaci sai da Suhana ta fito, sanye take da kayan barcin da suka fitar da surar jikinta, ta ji mugun daɗin ganin Aryan a tsaye, a tinaninta zata ja ra'ayinsa da surar jikinta ne, dan ALLAH yai mata halitta mai kyau ba karya, ta yi zubin shahararrun karuwai masu yin surgery su cike nan da can ɗin nan, sai dai ita bana surgery ɗin bane, kyauta ce daga ALLAH, goodbye and welcome dik a cike masha ALLAH.
Sai dai bata san IRON FIST jikin mace ba shi ne a gabansu ba, idan sun yi ra'ayi matan da suka ninkata a komai zasu samu, kai in suna so kowacce dare da irin matan da zasu kwana, amma wannan ba ita bace ɗabiarsu ba, su da maza da mata dik kallon abu guda suke masu, dik kyan mace da wani surarta wlh basu kallonta kamar mace, tamkar namiji suke kallonta saboda tin ainahi basu sanya abin a ransu ba, sun cirewa kansu feeling da sauransu.
Ko Seraphina da Aryan yake kauna soyayyar tsakani da ALLAH yake yi mata ba dan surarta ba, saboda ya fara son Seraphina ne tin babu komai a kirjinta, tin tana JSS1, kawai jinin ɗan uwansa ne yasa yake sonta a farko, daga nan ta rikiɗa izuwa soyayya, amma bayan haka wlh dik kyan surarki tamkar bango haka suke ganinki.
A gabansa ta tsaya, tana wani yauki da yanga ta ɗaga mashi gaisuwa. Shiru babu alamar ya ga wata halitta wai Suhana a wajen. A daidai wannan lokaci Seraphina ta fito sanye da uniform irin na jikin Aisha, da alama makaranta guda ya sanyasu.
Matsawa Suhana ta yi tana ƙoƙarin ɗaura hannunta a saman nasa tana faɗin. "Meyasa baka son amsani ne? Ko kana tsoron faɗawa so......". Bata iya karisarwa ba ta ɗauke wuta ɗiff saboda wani marin da ya ɗauke fuskanta da shi!.
Take ya sulale ta baje a ƙasa bata numfashi, yarinya ta sha marin IRON FIST, ALLAH yasa idan kika farfaɗo kada ki rasa kunnuwanki ki daina ji gabaɗaya, dan ba karya kin sha irin marin wanda IRON FIST suke yi wa maza! Kin maru ba karya.
Sosai Seraphina ta razana, da gudu ta juya ta koma cikin ɗaki jikinta na kerma, dan ita ta san dukan Aryan, abin ba'a cewa komai. Bayanta ya bi cikin zafin nama, dama lokaci na kurewa ita kaɗai suke jira. 7:20 ta yi.
Zaune ya iskota a gefen gado tana hawaye without any reason. Cike da mamaki ya ce. "Are you okay?". Zabura tai ta miƙe tsaye, jikinta na kerma ta ce. "Daddy please don't slap me, i promise you that ba zan sake yin laifi ba, for give me". A ruɗe take maganar, ga hawaye tamkar an buɗe tap.
Ƙarisowa in da take ya yi, ya ciro hankey daga aljihunsa, hawayen ya goge mata tare da damƙa mata hankey ɗin a hannu, sannan ya riko hannunta suka fito parlo ba tare da ya yi magana ba. Duƙawa ya yi ya ɗauki bag ɗinta da ta jefar a ƙasa ta gudu, ya nufi waje da ita.
Da sauri Aisha ta taso ta rufa mashi baya suka bar Suhana a baje a sume. Ganin ba dukanta zai yi bane yasa ta saki jiki, ta ƙanƙame hannunsa tana sauke ajiyar zuciya. Bai ce mata ko ƙala ba har suka shiga cikin mota, haka bai ce mata ko kala ba har suka nufi haɗaɗɗen school na cikin CRYSTAL PALACE ɗin.
A parking lot na wajen ya tsayar da motar, da sauri Aisha ta fita ta basu waje, ɗan ɗaure fuska ya yi, on a serious note ya kara ja mata kunne a kan karatu, ba ruwanta da kowa, banda abubuwan da ya hanata, daga karshe ya ce mata. "Kinga yanzu ni mijinki ne, idan kika kuskura kika yi shirmen da kika yi a junior set ɗin nan zaki shiga wuta ne, kuma dakuwa zaki yi ne a hannuna, dan yanzu ni kaɗai nike da mallaki kuma da iko dake!".
"Daddy dama yanzu ka zama mijina?". Tana murmushi ta faɗa. Hararar kauna ya ɗan wurga mata kafin ya ce. "Bar shiririta, ki yi karatu sosai, ni mijinki ne mana yanzu, kinga yau ce first day ɗinki a school ɗin nan, dan haka ki yi karatu sosai"....... Wani irin daɗin da ta ji ne yasa ta faɗo jikinsa. Ɗan ɗaure fuska yai tare da cewa. "Tashi mun a jiki bari in ta fi"......... "Kai daddy kai fa ka ce sai ka zama miji zan dinga kwanciya a jikinka, to yanzu ba ka zama ba?".
Nisawa ya ɗan yi. "Haka ne, to yanzu dai tashi ki wuce kada lokaci ya kure".... Wai shi ya faɗa mata shi mijinta ne dan kada ta yi shirmen da ta yi a baya, kun ji kuma ta yadda ta fassara shi yansu kuma, kai shi dai yana cikin alkhairi dumu-dumu, Seraphina sai shirin ALLAH, rashin uwa babban musifa ce, ga rashin karatun addini, ai fin haka ma zata aikata, jama'a uwa rahama ce, rahamar da babu biyunta, a kullum ina ƙara faɗa maku, uwa number one ce!! Idan babu ita a rayuwar bawa hakika sai kunga banbancin rayuwarsa da waɗan da suke da uwar.
Tana murmushi ta ɗago kai. Sumbata ya mannawa cheeks ɗinta tare da cewa. "Ki yi karatu sosai"....... Da okey ta amsa, miƙewa daga jikinsa ta yi, sumbatar ita ma ta manna mashi kafin ta buɗe kofa ta fito. Tana fita ta rufe kofar kenan sai ga motar Faryan ya kawo Rimsha.
Ai cikin zafin nama Aryan ya tada motarsa ya bar wajen da gudu, dan ALLAH yasa motarsa na gidan Abba daban, motarsa na IRON FIST daban, so ba zasu ganesa ba. Ita kuwa Seraphina zata wuce Rimsha ya sauke glass ta kwala mata kira tin basu gama parking ba. Ai tana juyowa taga Rimsha bata san lokacin da ta dawo wajen motar da gudu ba.
Faryan tin bai yi parking ba idanunsa a kanta, yana kashe motar ya riga Rimsha fitowa. Cikin sanyin murya da salon soyayyarta ya fara yaba kyan da uniform ɗin yai mata. Sosai ta dinga murmushi tana faɗin uncle Faryan na gode.
A haka Rimsha ta fito ta samesu, hannunta ta kama tana faɗin. "Uncle zamu yi latti, ba kuna chatting ba?".... Kai ya jinnina mata alamar e, daga haka ta ja hannun Seraphina suna ɗaga mashi hannu suka wuce. Kullum tana chatting da Faryan, Aryan kuma yanzu baya zama sosai saboda yana aiki tuƙuru na son gani ya gano wanene yake yi masu wannan abin? Ina mom ɗinsu Lion take? Abin da ya ɗauke mashi hankali kenan yanzu yasa baya bibiyar chat na Seraphina.
Zuba masu idanu Faryan ya yi har suka kurewa ganinsa, nisawa ya yi tare da cewa. "Yah ALLAH ka mallaka mun wanna baiwa taka, ta tafi da zuciyata tafiyar da ba zan iya dawo da shi ba, ALLAH kada ka jarabceni da rasata ko kasako wani tseƙo a tsakani".... Ya jima tsaye yana addu'ar kafin ya shiga mota ya tafi, kuma abin mamaki har yau bai faɗawa Seraph yana sonta ba, shi dai yana ta faman ƙoƙarin su shaƙu da juna, zasu sha hira sosai kamar masoya, amma bai taɓa faɗa mata yana sonta ba.
Suna shigowa cikin school Rimsha ta ce. "Ke my star lady do you know something?"........ Kai ta girgiza alamar a'a. "Uncle Faryan sonki fa yake yi! So sosai ɗin nan ma, please ki so shi kin ji?"..…..... Da yake ita Seraphina ta ɗauka so daban kuma aure miji ma daban, a tinaninta zaka iya soyayya da wani, wani kuma zaka iya cewa mijinka ne, dan bata ma san yadda ake ɗaura aure ko yadda auren yake ba, dan haka ta ɗauka wannan kalma ta miji kamar uba yake nufi, boyfriend kuma shi ne yaren da ta fi ganewa.
San haka sai ta ce. "Ki bari ya faɗa mun da kansa". Ta faɗa tana gyara goya jakarta a baya. "To shikenan zai faɗa maki ai nasani, da gaske yake sonki". Jinjina kai kawai Seraphina ta yi.
Kamar daga sama Seraph ta ji an ɗan taɓa bag ɗinta ta baya. Slowly ta juya dan ta ga wanene? Sai ta ga mutum ya juya yana tafiya, yana sanye da wandon jeans daga ta ƙasa, daga sama kuma jacket fara tas, kafafunsa sanye da boot, ya sanya hukar jacket ɗin a kansa, ya zura hannayensu a cikin aljihu, dik da ya juya mata baya hakika ta gano ɗan kwalisa ne koma wanene.
Zuba mashi idanu ta yi har sai da Rimsha ta taɓata tana faɗin. "Ke me kike kallo haka?"...... Firgigit ta dawo cikin hayyacinta, zata yi magana Rimsha ta ciro wani ɗan teddy da aka manna a jikin jakar Seraphina ɗin tana faɗin. "Ya ALLAH, my star lady wannan teddy ɗin ya haɗu".
Da saurin Seraphina ta waro idanunta a kansa, lokacin guda ta saki wani ƙayataccen murmushi kafin tasa hannu ta karɓi teddyn, ɗan daidai da shi, an yisa yana haɗe da hannayensa waje guda, yana rike da wani heart da aka rubuta you're so pretty a jiki, teddyn fari tas, shi kuma rubutun baki, irin kyautar nan na masoya.
"A ina kika samu wannan haɗaɗɗen teddy ɗin Nisha?". Seraphina ta tambaya..... Rimsha dake ta faman smilling ne ta amsa da. "A bayan bag ɗinki na gani an manna".
Da sauri Seraphina ta sauƙo da bag ɗin nata, sai ga wani parin takarda ya faɗo, ɗauka ta yi ta buɗe. "Please bless my morning with your cool smile blossom". Shi ne abin da aka rubuta a jiki. Wani irin murmushi ne ya kubce mata wanda yasa wushiryarta ya bayyana.
"Wait for me Nisha, I'm coming".... Ta faɗa tare da juyawa da ɗan gudunta ta bi bayan mutum da ta ji ya taɓata ɗazun. Sai dai ga mamakinta ko alamarsa bata gani ba, waige-waige ta fara yi tana neman ta ina zata gansa.
A haka Rimsha ta kariso ta sameta, riko hannunta ta yi tana faɗin. "Lafiya kike kuwa?". ...... Kai ta ɗan girgiza game da cewa. "Mu je kawai"....... A tare suka juya suka cigaba da tafiya, ta ƙanƙame teddy ɗin a kirjinta, ya yi mugun yi mata kyau.
Suna barin wajen ya fito daga maɓoyansa yana sakin haɗaɗɗen murmushinsa irin na Noor ɗinmu na amana, watau familynsu Noor ba dai iya soyayya ba, yanzu zasu sace zuciya, ba'a takara dasu a fagen soyayya, dan mutum zai sha ƙasa ne. To waye ya faɗa mashi a nan school ɗin take kuma? Ga dikkan alamu ya yi bincike a kanta ne, kuma saboda ita ya nemi karantarwa a makaranta, abin da kunsan sun fi karfin hakan, amma saboda su tin ainahi sun iya bautawa soyayya shiyasa zai iya sauƙa izuwa kowani irin mataki dan ya samu soyayyarta. E KAM AKWAI BABBAN CASE! UNCLE ƊIN NOOR DA ZAFINSA YAKE TAFE. MU JE ZUWA.
A ɓangaren Aryan kuwa, yana barin school ɗin gidan Abba ya nufa bayan ya ajiye motarsa a gidan Lion. A wannan lokacin kuma Abba ya dawo daga gidansu Noor ransa a matuƙar ɓace. Ya je su sake ganawa da familyn Noor, in baku manta ba ai da ya je na farko daddyn Noor baya nan ko? To shi ne yaga yakamata ya koma ya gana da shi.
Sai dai yana koma ya isko kakan Noor na wajen uba, wani masifaffen dattijo, shi daddyn Noor kun san bashi da matsala, da Abba ya faɗa mashi buƙatarsa sai daddy ya ce ai wannan ba wata matsala bane, in dai su Aunty Luna suna so shi bashi da wata damuwa dan basu addini guda. Abba ya ji daɗin hakan sosai.
Sai kuma me? Wannan dattijon ya ce idan sama zata haɗu da ƙasa ba zai haɗa jini da wani addini ba idan ba mutane marasa addini irinsa ba!. Daddyn Noor ya yi ƙoƙarin faɗa mashi cewa ai hakan ba wani matsala bane, amma wannan dattijo ya ce daddyn Noor yai mashi shiru, har da karawa da cewa daddyn Noor bai san ciwon kansa ba, shi komai yana da sauki a kai, to shi ba zai ɗauki wannan iskancin ba.
Na faɗa maku daman cewa Abba yana da mugun zafi, da zuciya, aikuwa sai ya ce da dattijon. "Da a cikin lumana babu cin mutuncina ko cin mutuncin addinina ka ce ba zaka bani aure ba, da zan hakura, amma tin da iko da karfi zaka gwada mun, ka zagi addinina, wlh, narantse da sarkin da ya busan rai sai mun haɗa jini daku, waɗan nan yara sai mun auresu, zan gwada maka mun fika ji da kai da izza, ba'a haifi wanda zai kalli Muhammad Khaiza'an ido cikin ido ya gaggaya mun magana ba!!".
Aikuwa dattijo ya hau shi ma, ya fara surfa balai, wai ko ya mutu idan daddyn Noor ya haɗa jini da su Abba bai yafe mashi ba, Uncle da daddyn Noor sun yi ƙoƙarin tausan dattijon, amma ina, yaki hakura, daga karshe dai suka yi baram-baram da Abba, har marinsa Abba ya kusa yi Uncle ya rikesa yana bashi hakuri.
Daddy Noor ya ja Abba waje, ya dinga bashi hakuri, ya ce mashi. "Kasan yanayin tsufa, amma ka bari zan shawo kansa a hankali"...... Cikin fushi Abba ya ce. "Ka shawo kansa ko kada ka shawo kansa dik ya rage naku! Aure ne a wannan gida sai mun yi, ko kuso ko ma ku ku ƙi!!". Babban magana!..... Daddy Noor ya ga ikon ALLAH, kai Abba akwai zuciya da saurin fushi, baya ɗaukar nonsense....... To daddy Noor, a matsayinka na uba ko ka bada auren ko kada ka bada Abba namu na gargajiya sai ya ɗaura wannan aure, yau ake yinta a CRYSTAL PALACE.
A fusace Abba ya baro benen yana wani irin huci, zuciyarta ta ɗauki zafi, tin da ya shigo gida bai yi wa kowa magana ba, su Harleen sun kewaye shi suna tambayar lafiya? Amma ina, bai amsa kowa ba. A daidai wannan lokaci Aryan ya shigo parlon cikin fushi shi ma.
Domin kuwa yana gab da shigowa gidan ya haɗu da daddyn Noor, bayan sun gaisa daddy yake ce mashi. "Na zo kara baiwa Muhammad Khaiza'an hakuri ne a kan abin da ya faru, idan ba damuwa ka mun sallama da shi"...... Cike da mamaki Aryan ya tambayi abin dake faruwa, daddy ya zayyane mashi komai, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, shi ne Aryan ya ce daddy ya bar masu kofar gida tin kafin yai ball da shi. Dole ya juya da koma.
Shi kuma ya shigo cikin gida da fushi. Yana zuwa ya tsaya a tsakiyar parlo, kowa sai da ya sha jinin jikinsa da suka gansa a wannan yanayi. Cikin kunar rai ya ce. "Abba na faɗa maka bana son auren ana dole ne? Ba ga shi yanzu ka je ka ja an taɓa mana ƙimarka ba! A kan wata mace zaka ja wasu banzaye su faɗa maka magana! Ko so kake mu kashesu ne? Kasan zuciyarmu ba zata iya ɗaukar wani ya gaya maka magana ba meyasa zaka kai kanka wajen ƙasƙantattun mutane?!".
A fusace Abba ya ce. "Aryan sai ka auri wannan yarinya, dan sai na gwada masu ba'a ja dani!". Cikin dokin zuciya ya faɗa....... "No Abba! Ba zan auri kowa ba". Cikin fushi ya faɗa....... Da karfi Abba ya ce. "Zaka aureta Aryan!!"........ A fusace shi ma Aryan ya ce. "Ba zan aureta ba na ce maka, wai Abba rayuwata ce ko naka? Kai zaka zauna da ita idan ka aura mun ita ne? Ko zan mutu idan ban yi aure a wancan gidan ba sai dai in mutu, amma aure ba zan yi ba!!"..
A fusace Abba ya miƙe tsaye, jikinsa har yana wani irin kerma, ya nuna Aryan da sandar hannunsa, cikin tsawa ya ce. "Ko kaki ko ka so sai ka aureta, sai na gwada masu ba kowa ake taɓawa b!!".
Juyowa Aryan ya yi, suna fuskantar juna, cikin fushi, zuciya game da zugan shaiɗan ya ce. "Abba ba zan aureta ba!! Dik gidan nan ma babu wanda zai yi aure! Na kafa wannan doka! Ko kaki ko ka so Abba, ba shawaranka nike nema ba, wannan umarni na ne!! Babu wanda zai shigo da mace cikin gidan nan, ka faɗa mun auren me ya tsinanawa zuri'armu in banda wahala? Ka ce ka hana soyayya saboda an cutar da kai ta dalilinta, ka aurawa su babban yaya abin da basa so, me ya haifar? Wancan banzar (Mom Rimsha) ta zo ya shiga jikin yayana, ta kashe mana shi, mahaifiyar Vash, yaya yana zaune a gidan nan, ta ce sai sun je yawon ƙasashe shaƙatawa, a nan ya je suka yi haɗarin jirgi suka mutu, ka faɗa mun me mata suke tsinana mana a rayuwarmu idan ba balain da suke jefamu a ciki ba? Dole ne sai mun rayu da mace? Ka faɗa mun dole ne? Kai da kake tare da Ammie.......". Bai iya karisa maganar ba Faryan ya yi tsalle ya rufe mashi baki, dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 95