thinking?". Lion ya faɗa tare da kunna wata recorder. Shiru dikkansu suka yi na a ƙallah 2 mins, sannan guru ya ce. "Batu ne a kan rashin tsaron dake Avaris ko?"....... Kai kawai Lion ya ɗan girgiza alamar a'a kallonsa a kan Champion da ya shiga duniyar tinani na daban.
"Yakamata mu sanya ido a kan Avaris sosai, saboda rashin tsaro ya yi yawa, wahala da yunwa sun yawaita, abin mamakin kuma kasar Avaris ita ce ta uku a dukiya da karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa, meyasa kuma take zuwa matsayin sahu na gaba a yunwa, wahala, rashin tsaro, ma'aikata babu albashi, sojoji ba'a biyansu yadda yakamata, dik duniya babu barrack ɗin da ya kai AZURE yaye ɗalibai masu kaifi, fikira da basira, ga horo na musamman da ko ba bindiga zasu iya gwabza yaki, to amma meyasa sojojin basa iya kama ƴan ta'addan? Meyasa komai yake tafiya a juye?". Guru ne ya faɗa cike da damuwa sosai a ransa.
Champion ne ya ce. "Babu wani abin da yake tafiya a juye guru, komai a daidai yake tafiya cikin tsarinsu, sai dai ƴan kasar ne suke ganin kamar komai a juye masu yake saboda an juya tunanin kwakwalensu". Ya faɗa without looking at them, da alama yana jinsu amma ba dikkan hankalinsa bane a kansu.
One thing, da guru da Lion suna da alaƙa mai karfe da AVARIS and AZURE BARRACK shiyasa suke damuwa da ƙasar sosai, kullum aikinsu a kan shawo kan matsalar kasar ne, dan Avaris tana daga cikin top ten ƙasa masu shan bakar wahala a duniya, kuma tana cikin top ten na ƙasashe masu karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa da ruwa, to me matsalar? Abin da kowa ya gagara ganewa kenan, amma alƙalamina zai faɗa maku me matsalar!.
"Zancenka gaskiya ne Champion, amma a tinaninka meyasa Avaris tana da yelwar arziki, ga wadataccen noma, idan ka duba a kididdigar da muka yi suna iya noma abincin da ƙasar zata iya ci ba tare da sun ji yunwa ba, meyasa suke fitowa neman abinci? Manoman dake noma suna fama da yunwa da bakar wahala, meyasa?". Cewar guru.... A wannan karon Champion baya tare da su, so bai ma ji tambayar ba.
Shiru ne ya biyo baya for almost 5 mins, dama shi Lion kullum a karshe yake magana, sai ya gama jin dik abin da zasu faɗ, ya gama jin ra'ayin kowa kafin ya faɗi nasa ɗaya tamkar da dubu. Kamar dai ni Princess Teema, sai na gama jin ra'ayin kowa nike faɗar tawa ra'ayin a karshe!.
Jin room ɗin ya yi shiru ne yasa guru yasa hannu zai taɓa Champion Lion ya dakatar da shi tare da cewa. "Wannan abu ne da yake a tsare! Idan har aka bar Avaris da wadataccen abinci, suka ci suka ƙoshi to the next thing abin da zasu fara yi shi ne nemawa kansu da ƙasarsu cigaba wanda hakan zai haifarwa da WORLD SYSTEM damuwa". Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa. "Kasan a duniya yanzu babu ƙasar dake da haziƙan mutane kuma ƴan baiwa irin kasar Avaris, sun san cewa idan jama'ar kasar suka farka to dik duniya sai sun jira, shiyasa suke kashesu da yunwa dan ma kada su samu kwarin gwiwar yin wani tinani bayan na abinci".
Cike da rashin fahimta guru ya ce. "To amma ta ya za'ayi a shiryawa babbar ƙasa irin wannan wahala da yunwa?".
Watau kun san me mutane? Su Lion karshe in dai a ɓangaren tinani da hangen nesa ne, ga karfin hasashen dake tabbata, wlh dik hasashen da suka yi tabbatacce ne. Ni dai a jikina ina jin Avaris exactly Nigeria tamu ta gargajiya, ku me kuke jinta? Amma mu je zuwa, alkalami ya fi tokobi! Kumun addu'ar in samu cikar burina na warware gaskiya a cikin wannan labari kamar yadda na so, wlh complete storyn nan ina ɗaukarsa tamkar gaske ne sai abin da ba'a rasa ba, tamkar yadda kwakwalwar su Lion take da kaifin hangen nesa da hasashe game da tinani haka ƙwaƙwalwata take, dikkan abin da zai faru da idon basira nike kallonsa, ina fatan dik wacce zata karanta littafin nan daga yanzu ba za'a sake raina mata wayau ba!.
Shiru Lion ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Wannan abu ne mai sauƙi, manyan ƙasar sun zauna meeting na sirri da manyan ƴan kasuwa dake shigo da kaya, sun umarcesu da ɗaga farashin kayan abinci ta yadda talaka ba zai iya sayan foreign food ba, daga nan su kirkiro fitinar ƴan ta'adda suna shigowa sai a rufe wasu bodojin ƙasar". Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa.
"Idan suka ɗaga kayan abinci suka kuma rufe boda sai su ƙarawa takin noma kuɗi ta yadda takala dole ya ci bashi a lokacin yin nomansa, dan kuɗin da ya lissafa zai kashe a farko yanzu komai ya tashi ya ninka kuɗinsa, kuma dole ya saya dan yana buƙata, kafin ya gama noma bashi tai mashi yawa ta yadda yana cire amfanin gona dole ya biya mutane bashinsu, idan ya noma buhu goma ne, to buhu 6 zai tafi a biyan bashi, saura huɗun ba zasu ishesa ya ci a gida da iyali ba bare har a je ga lissafin ajiye wani kuɗin dan noman shekara mai zuwa, kaga kafin wata shekara ta zago ya sake cin bashi dan ciyar da iyalinsa, lokacin noma ya sake cin bashi dan nomawa, idan last year ya samu ragowar buhu 4 to this year in ya biya bashi da kyar ya tsira da buhu 2, a haka ake haifarwa da ƙasa mugun yunwa da wahala, shiyasa zaka ga kaya a wajen Avaris da mugun arha, amma a cikin ƙasan ya ninka kansa sau biyar".
"Kaga buhu biyu bai wuci ya ci na ƴan kwanaki ba, sun kare, kaga bashin da zai sake ci wannan shekara da ta fi ta wancan shekara kenan, idan ya ci ya gama noma abincin da ya noma ba zata isa ya biya bashi bama bare ya rage na ci, daga nan zai fara gudun biyan bashi, ya ci ba zai biya ba saboda babu yadda zai yi, idan ya biya bashi da abincin da zai ci a gida, yunwa ta mamaye ƴaƴa da ƴan uwansa, daga nan yunwar take farawa har ta mamayesu ta ko'ina, ga bashi da rashin madogara, makarantun yara ya tsaya, rashin sana'a, abubuwa su caƙuɗe, yunwa tasa dole yara su fara ɗauke-ɗauke, daga nan shaye-shaye". Lion ya dakata hankalinsa a kan computersa.
Champion ne ya ce. "Wannan ma naga ba zanga-zanga rashin tsaro suke yi ba bayin ALLAH, zanga-zangan yawan faɗuwar tamkoki mai da ake samu ne a kwanakin nan yana masu ɓarna, yana kashe masu al'umma sosai, shi ne suke zanga-zanga kan gwamnati ta biyasu gidajensu da wata tankar mai ta ƙona".
Guru ne ya kalli Champion da ya ajiye wayar dake hannunsa yanzu, dama tin ɗazun da kuka ga ya yi shirun nan sauraren wayar da Seraphina take yi da Rimsha a yanzu yake yi, yanzu ta sake kiran Rimsha tana faɗa mata tana tsoron gidan, kuma ita kaɗai ce, tana kuka tana faɗa mata. Gabaɗaya sai ya ji hankalinsa ya tafi kan ya je ya ganta, yanzu da suka gama wayar ne shi ma ya ajiye wayan nasa ya mai da hankali kan aikin da suke yi.
Bai san dik abin da yake yi Lion na sane da shi ba, su fa mata haramum ne a wajensu, sun haramtawa kansu, kada ku ɗauka da wasa ake yi! Da gaske suke yi, yanzu idan har Lion ya kama Champion kan macece take ɗauke mashi hankali zai rabasu ne, saboda ba zasu tsayar da aikin da suka fara ba, kuma ga shi kunga zancen Lion ya fara tabbata, mata suna da ɗaukewa mutum hankali, kunga tin ɗazun maganar arziki ake yi shi kuma Champion ya tafi jin gulma na hirar su Rimsha, sun ɗauke mashi hankali.
Guru ne ya ce. "Gaskiya kwana biyun nan ana samun fashewar tankar mai a Avaris sosai, kuma tana sanadin rayuƙa da dama, to motocin man ne dik sun mutu, amma manyan ƙasar sun kasa sayan sabbi". Champion ya ce. "Kuma kansu zasu yi wa idan sun sayi sabbin ma, amma ba zasu saya ba".
Nisawa Lion ya yi tare da ɗaukar cube ya fara murɗawa, ya koma baya ya jingina da jikin chair da yake kai a zaune, sannan in cool way ya ce. "Da balain son kuɗin nan nasu kuna tinanin zasu taɓa yarda su karɓi asara ne? Kada ku manta fa idan man ya zube asararsu ce, to zasu yarda haka kawai su yi asara ne?".
Shiru su Champion suka yi suna nazarin kalamansa. Katse masu shirun ya yi da cewa. "Shi kansa faɗuwar tankan man plan ne ga ƴan ƙasa"...... Champion ya ce. "Confirm, suna sake tankar ne saboda abubuwa biyu, na farko ko su juya akalar tinanin al'umma zuwa kan wannan case ɗin su aikata wani babba laifi, ko kuma su faɗar da ita domin kashe mutanen dake yankin, da gayya suke faɗar da ita, ko direbobinsu basu sani ba, dik shiri ne, in ba haka ba ba ta yadda za'ayi su dinga tabka asara haka, yadda suke mugun son kuɗin nan".
Guru ne ya ce. "Na fi tinani suna yin hakan ne domin su ɗauke hankalin ƴan ƙasa su aikata wani babban laifi".
"Dalilai uku yasa suke hakan, na farko dan ɗauke hankalin ƙasa, ko zasu fitar da dukiyar ƙasa kamar su gold zuwa wani waje, ko zasu shigo da wasu manyan mutane cikin ƙasar, ko kuma zasu fitar da ƴan matan da suke sacewa ana kaisu waje dan kasuwanci da su ta hanyar karuwanci". Cewar Lion.
Jan numfashi Lion ya yi tare da sauƙewa a hankali kafin ya cigaba da cewa. "Idan sun shirya jefar da tankar mai, akwai wata chemical da ake cewa hydrochloric Acid, suna saita daidai in da suke son tankar ta fashe ne, sai su yi diluting ɗinsa da ruwa, su zuba ruwan da zai daidata chemical ɗin ya kuma ɗauki tsawon lokacin da zai isa wajen can ɗin, sai su zubawa tankar mai ɗin ta daidai in da suke son ya fashe, idan drivernsu ya ɗauki motar lafiya lou zai tafi da ita, wannan chemical ɗin tana cin wajen da aka zuba ɗin a hankali, sai ya isa in da suka tsara unexpected zai ga tankar ta fashe mai ya fara zuba, za'ayi duban duniyar nan a rasa dalilin fashewar tankar, dan chemical ɗin sam bata nuna alama, haɗewa sa ruwa take". Ya dakata yana sauke ajiyar zuciya.
"Yanzu me mafita?". A cewar guru. Champion ne ya amsa da. "Yakamata mu tsaya tsayin daka dan tsabtace Avaris, gurɓacewarta ta yi yawa over, ga cin hanci ta yawaita"........ Guru ne ya amsa da. "To jami'an Avaris ai dole ake tilasta masu cin hanci, shi ma wannan shiri ne domin jami'an su zama karnukan farautarsu, dole suke tikasta jami'an Avaris da su yi masu biyayya ta hanyar azabatar da su da karamin albashi, idan suka basu albashin da ba zai iya ciyar da su ko na sati biyu ba, kunga yunwa zata sanya dole su fara karɓar cin hanci dan ciyar da family ɗinsu, dole a wannan lokaci zasu karɓi dik wani aiki da na sama da su ya basu dan su samu abin da zasu baiwa ahali, yunwa ita ce babban makamin da shuwagaban Avaris suka rike wajen sanya kowa ya bautawa buƙatunsu, talaka na fama da yunwa an kawo mashi aiki da zai samu 10k dole zai karɓa ko dan yaran da ya baro a gida suna jiran baba ya dawo ya kawo aci abinci". Ya kai karshe cikin tsananin takaicin abubuwan dake faruwa a duniyar yau.
Nisawa Lion ya yi tare da cewa. "Ba laifin shuwagabannin Avaris bane, suma umarni ake basu ta yadda idan basu yi ba za'a kashesu, WORLD SYSTEM ita ce matsalar duniya gabaɗaya, kowani shugaba ya hau mulki dole zai bi umarninsu ne in har yana son ransa".
Guru ne ya ce. "Wai to su ɗin su waye ne?". Champion ya ce. "Mutane ne kamar kai"....... Lion ya amsa da. "Haɗarinsu kuma ya fi nuclear, su ɗin ba mulki suke yi ba, ba shugabanci ba, hasalima basu a siyasa ko sarauta, su akewa laƙabi da masu naɗa mai mulki, su suke zaɓar shugaban da suke so ya yi mulki a kowace ƙasa, kuma dole ya yi masu biyayya ya aikata dik abin da suka sanya shi, idan ba haka ba, su kashesa ko su ɓatar da shi, su ɗin su ne ke juya duniya a yau, sai abin da suka so mutane su sani suke sani". Ya ɗan dakata yana fito da bayanai a kansu a cikin computer dake a gabansa, bayanai ne da ya sha wahala, ya shafe tsawon lokaci yana haɗasu, dan shirya mission na musamman a kansu.
Champion ne ya ce. "Suke juya sojoji ta sigar da babu wanda zai sani har su kansu sojojin, suke juya manyan da suka amsa sunansu manya, suke juya harta talaƙawa, dik wata ƙasa a duniya da kuke ganin kamar suna da power ko su ke juya duniya to ku sani suma umarni suke karɓa daga wannan team na WORLD SYSTEM ɗin, wannan WORLD SYSTEM ɗin su ke tsara komai da suke son ya gudana a kowacce ƙasa, baku ji sunansu ba? WORLD SYSTEM, su biyar ne, amma mutum ɗaya ya fi dikkan shuwagabannin manyan kasashe girma da karfin iko game da haɗari, kowa a karkashinsu yake ba tare da kowa ya sani ba".
Lion ne ya ce. "Sune a next mission namu"........ Shiru room ɗin ya yi, dukkansu suna tinani daban-daban, lallai kuwa sun ɗauko dala ha gammo, mission kan WORLD SYSTEM, na yarda da gaske su Lion sun sayar da ransu, basu tsoron mutuwa, sun shirya mata a koda yaushe. Yanzu wasan zai fara, su Noor zasu yi mission a kan IRON FIST, su kuma IRIN FIST zasu yi mission a kan WORLD SYSTEM, kungiyar da suka fi haɗarin ma haɗari.
Ni dai na shirya tsab dan bin kowani team a wannan tafiya, dik wacce ta shirya ta haɗo kayanta mu wuce, batu ake na gaskiya da gaskiya, reality amma a novel, get ready my people, wannan karon bamu zo da wasa ba!.
Sun jima suna tattaunawa a kan wannan matsalar, har zuwa 12 na dare, sannan suka miƙe suka nufi dining room. Dinner suka ti sama-sama saboda dare ya yi, shi Lion ma green tea kawai ya sha, Champion ya sha Amercano, guru ya ɗan sha coffee, daga haka suka nufi room na Leo.
Sun sha madarar mamakin ganin idanunsa biyu, ya dukufa a kan laptop dole-dole sai ya ɗan samu wata makama a kan IRON FIST, aiki tukuru yake yi, dik wasu kisan da IRON FIST suka yi sai da ya bankaɗo bayanai, amma babu wata makama ko alamar da za'a iya gane su. Dik kisan da zasu yi sun subarwa da mutum jini, bugu da kari sun fi yin kisa da poison ko Chemical, kansa ya ɗauki zafi sosai, ruwa roba biyar ya shanye amma bai iya gano komai ba, idan ya binciko wani kisa nasu sai ya miƙe ya fara kewaye a cikin ɗakin yana tinanin yadda aka tsaya komai, ya kewaye room ɗinsa ya fi sau hamsin, amma dai babu wata haske, tin yana aiki a kan gado har ya sauƙo ƙasa.
Brothers ɗin nasa suna shigo ya ɗago ido a kansu, da sauri ya miƙe ya koma saman bed yana kallonsu. Ɗan kallon juna suka yi kafin su karisa in da yake, cike da damuwa ya ce. "My love please come and help, my brain is about to tarwatsewa wlh".
Champion zai yi magana Lion ya rigasa da cewa. "Babu wanda zai taimaka maka, da kanka zaka yi komai". Daga nan ya kafawa su Champion dokar kada su kuskura ko da sunan wasa su taimakawa su Leo a kan wannan mission da zasu tafi, su je su yi faɗa da kansu su yi nasara, idan har zamu taimaka masu kenan babu amfanin su kaisu AZURE ai, su kam waye ya taimaka masu a lokacin nasu mission ɗin? Ba su suka kwaci kansu ba? Dan haka su Leo su kwaci kansu suma.
Kuma Lion yana da gaskiya, kunga abin da ake jiran su goge su maye gurbinsu kenan wayau IRON FIST, idan suka fara tayasu aiki ta ya za'ayi su jajirce su zama mazan gaske? Ai kunga gara a barsu su ci ƙwaƙwa su tsira da kansu. Lion ya ce ko mutuwa suke yi babu wanda zai taimaka masu, bama zai bibiyu mission ɗin nasu ba, su je su fafata su zama mazan gaske, kuma da gaske yake yi wlh, dan ya gana su Champion ma bibiyar Mission ɗin nasu Leo, ya ce su fafata da kansu, suma su shiga tsananin rayuwa ko mutuwa, daga nan ne dik wata sauran tausayi zai bar ransu, zasu zama mutane in ji Lion.
Da haka suka yi wa Leo goodnight bayan sun karfafa mashi gwiwa, suka wuce izuwa room ɗinsu. Hankalinsu a kwance suka kwanta, Lion ya ce ya basu nan da kwanaki biyu su yi tinani a kan WORLD SYSTEM, shi ma zai yi nashi tinani, after two days zasu sake yin zama a kansu dan yanke hukunci kafin su fara ainahin bincike a kansu!.
Suna kwanciya ba jimawa Lion da guru suka yi barci, shi kuma Champion ya ɗauki wayansa ya duba layin Seraphina ko tana online, sai ya ga bata nan, ya kirata sau ɗaya da bata ɗauka ba ya fahimci ta yi barci, hakan yasa ya kashe wayarsa shi ma ya yi barci, ya so ne ya jita, dan kukan da ta yi ɗazun abin ya tsaya mashi a rai, ta faɗawa Rimsha ita kaɗai ce a gidan kuma tana tsoro.
Kai inna biyewa rubuta komai fa zamu jima ba'a kai in da muke so ba, dan haka After some days.
A ƴan kwanakin nan da suka wuce abubuwan da suka faru sun haɗa da Aryan ya ɗauko madam Rohisha da ƴar marainiyarta ya dawo da su wajen Seraphina, ya kuma nema masu school da suka gama dan komawa su yi senior set a can, ya kuma nema masu izinin dawowa gida su dinga kwana ba boarding ba, ya yi sa'a aka bashi, ya yi matuƙar murna sosai, dan baya son kwananta a school, gara mashi a C-P ɗin nan, dik time da ya tashi ya shigo ya duba lafiyarta.
A gefe guda kuma su Noor soyayya ta kara kulluwa a tsakaninsa da V, yanzu sai shirin komawa barrack yake yi, nan da kwanaki uku zasu koma, kuma har yau basu haɗu da Leo ba, Leo ɗin ne ya ce bashi da lokaci, saboda yana nema kashe kansa a kan bincike, ba dare ba rana yana aiki ɗaya, har rama guyen nan ya yi, Zayra'an na ganinsa amma bai ce ko uppan ba, shi daɗi ma ya ji na ganin yadda kanin nasa ya dukufa kan aiki babu wasa babu kama hannun yaro, ko abincin kirki Leo baya ci, idan ya zauna a gaban computer sai ya samu wani ɗan haske yake matsawa, kansa tamkar zai fashe saboda ciwo, amma ya dage.
Shi ma Noor ya dage da aiki babu kama hannun yaro, hakan yasa jiya suka yi faɗa da V, ta ce ya daina sonta, baya bata ishasshen lokaci, sati ɗaya baya da suka fara soyayya wuni suke yi manne da waya suna hira da juna, yanzu kuma idan ya yi mata message da safe sai ya shiga aiki, baya sake bi ya kanta sai can yamma, wayarsa ma kashewa yake yi, yana kara hora kansa da motsa jijiyoyinsa, a taƙaice dai basa waya sai dare, daren ma daga karfe 8 zuwa 10 suke waya sai ya ce mata goodnight, ko ta so ko bata so ba zai kashe wayar ya shiga aiki ne abinsa.
Ba wai dan baya sonta ba, sai dan aikin dake gabansu yanzu ya zarce wasa, dole ya mayar da hankali idan ba haka bama Leo zai rabasu da ita ne, ita kuma bata gane ba, sai fushi take yi da shi, ya yi mata bayani amma bata gane ba, ita dai kawai lokacinsa take so, shi kuwa ya ce ta yi hakuri ba zata samu lokacinsa yanzu ba.
To shi ne tun jiya ta yi fushi da shi, ya yi rokon duniyar nan a Whatsapp ta sauraresa taki yarda, daga karshe ma ta rufe wayarta, yanzu haka tin jiya bai ji voice ɗinta ba, dik ya kiɗime ya fita hayyacinsa, ga aikin da ta sha gabansa. Ya kira number Angelina da yake da shi, yasa ta bata waya amma ta ce ace mashi ya manta da ita, kada ya sake nemanta, Noor bai tashi sanin a sati ɗaya da ƴan kwanaki da suka yi suna soyayyar nan mugun sonta ya shigesa ba sai yau.
Gabaɗaya yau ya gagara yin aikin ma, wlh sai kai komo yake yi tsakanin ɗaki da waje, ya rasa me yake yi mashi daɗi, jikinsa dik a mace, ita kawai yake tinani yake son jin muryarta, daga karshe ya yanke shawarar komawa AZURE gobe mai maimakon jibi, ya ce tin gobe zai koma dan ya samu ganinta ko hankalinsa zai kwanta.
Jama'a kunga irin abin da Lion yake gudunwa IRON FIST kenan, shiyasa suka haramtawa kansu soyayya, da gaske ne idan kana soyayya wasu abubuwan ba zaka mai da hankali a kansu ba, kuma su a yadda suke ɗin nan dik yarinya da suka so ma sun cutar da ita ne, saboda sun san a kowani lokaci mutuwa zasu yi, bare yanzu da suke ƙoƙarin ɗauko mission ɗin da duniya dik ta gagara, abin dake ɓoye a cikin duhu suke shirin bangaɗowa duniya shi, kuma kun san gagarumin haɗari zasu jefa kansu, ga dai Noor, soyayya na neman hanasa abin dake da muhimmanci a kansa, ta yi fushi da shi ta jefa zuciyansa a cikin wahala da tinani, tasa ya gagara yin aikin dake gabansa, har yana tunanin zuwa wajenta gobe.
A gefe guda kuwa Aunty Lisa na can tana abin da ta ga dama da zuciyar our daddy GAT ɗinmu, tasa bawan ALLAH ya zama yaro ɗan 20 years, sai juya shi take yi yarinyar nan, shi kuwa sai biye mata yake yi, ya zauna ya gama zuba mata sexy and romantic words yarinyar nan sai ta ce mashi. "Daddy all this fa westing of time ne". Kuma ƴar kaniya har kwana mafarkinsa da kalaman nasa take yi, amma take cigaba da mashi abin da take so.
Yau dai da ta kawo shi har wuya, ya yi ya yi su yi video call taki yarda, sai ya katse kiran tare da miƙewa ya koma gida, a take ya nemi bizar zuwa US, ga shi two days ago su Arya suka yi passing out ɗinsu, dama ya ce idan suka fita kafin su fara aiki zai kai su yawo, dan haka sai ya shirya masu tafiya gabaɗayansu.
Da yamma jirginsu ya ɗaga sai US, bai sanar da su Arya ga in da zasu je kai tsaye ba, kazalika bai sanar da Aunty Lisa yana zuwa ba, while Noor bai san V na hanya ba, ya bari sai da suka yi dirar mikiya a airport sannan ya kira daddy Noor ya faɗa mashi suna US yanzu.
Ai da sauri daddy ya umarci ƙaninsa uncle ɗin su Noor da ya ɗauki motoci da guards aje a ɗauko mashi bakinsa a airport. Noor bawan ALLAH yana ɗaki yana ta faman shirye-shirye kan cewa gobe zai wuce AZURE ya je ya ganta, ya gama shirya rucksack ɗinsa, yana kwance a saman bed rike da waya yana ta faman neman numberta.
A daidai lokacin suka danno cikin gidan, da yake su kullum suna cikin yin baki daga ƴan siyasa, sarakuna, manyan ƴan kasuwa sai basu wani damu dan sun ji manyan baki sun zo ba, dik suna cikin ɗakunansu, Aunty Lisa na kan gado tana aikin wana hankalin GAT a Whatsapp ɗinta bata san ga shi ya shigo gidansu ba. Aunty Luna na kwance cikin bargo tana shirin yin barci, Aunty Lusi tana waya da wani abokinta, kunga Noor kuma yana ɗakinsa, kwanan nan da yake yasa aiki a gaba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 95