sun zage su wai zasu cuci mutane, gwamnati ta bada kyauta su kuma suna sayarwa". Brother ya faɗa.
"Business kan business ba". Dr James ya faɗa........ Nisawa brother ya yi kafin ya ce. "Mu samu damar canza yanayin duniya shi zai bamu damar yin abubuwa dayawa".....… Dr James ya ce. "Ni kam ya batun ambaliyar da kuke ƙoƙarin kirkirawa waɗan can manyan ƙasashe uku dake ƙoƙarin bijire maku ɗin ne? Ka ce zaku hasasa masu ambaliyar da zai haifar da rugujewar tattalin arziki, zaku fasa manyan dams a sirrance, bayan ambaliya zaku tsokani fararen ƙasar da ke ƙarƙashin ƙasa ku haifar masu da girgizan ƙasa, zaku yawaita ambaliya a duniya, kuma zaku yawaita girgizar kasa, a lokacin kuma ga fari, hakan zai sanya yunwa ya zautar da al'umma, ya batun wannan aiki?".
(ALLAH sarki wannan magana ta tina mun da ambaliyar Maiduguri, mutanen barno muna kara miƙo jaje, ALLAH ya jiƙan waɗan da suka rigamu gidan gaskiya.)
"Aikin yana nan, kasan mu yanzu matsalarmu shi ne mu san yadda zamu yi mu kashe aikin hannu a cikin al'umma, kasan nan gaba kaɗan zamu ƙwace kowani irin aiki daga hannun al'umma, za'a rasa aikin yi, talauci da taadanci zai ƙaru, idan aka rasa aikin yi dole ƴan zaman banza su ƙaru, hakan zai sanya matasa su faɗa harkar shaye-shaye da daba". Ya ɗan nisa tare da cigaba da cewa.
"Zamu iya kwace kowani irin aiki, yanzu muna shirin kashe karatun boko, baya ga shi zamu kashe kasuwanni ta hanyar kawo masu sauƙin tsaro, mu haɗasu da na'urar da zaka ajiye a shago ba sai mutum ya zauna maka ba, mutum zai iya damfararka amma naura ba damfara, hakan zai sanya su yarda da na'urorinmu sosai dan suna ganin sauƙi ne ya samu, daga nan kasuwannin za'a daina ɗaukar matasa zaman shago, a koma masuwancin media da naura, mu kirkiro robot masu dawo da sauran ayyuka a kasuwa, kaga mun kashe kasuwa, ɗan adam baya buƙatar aiki a cikinta".
Kai Dr James ya jinjina alamar haka ne. Cigaba brother ya yi da cewa. "Muna da hanyar kashe dik ayyukan mutane, asibitoci dik zamu kashe aikinsu, yanzu damuwarmu ɗaya ce, shi ne aikin hannu, musamman noma da kiwo, so gara noma yanzu mun ɗauko irin da zamu tarwatsa rayuwar nomarsu da shi, har ma wannan plan ɗin ya isa ga al'umma, to shi kuma kiwo shiyasa muka baka project na ƙirƙirar yadda zamu fara haɗa nama a lab dan mu kashe kiwo a duniya, dik wani aiki zamu kwacesa daga hannun al'umma, zamu azabtar dasu da yunwa ta yadda a lokacin da zamu fito da addinin da muke shiryawar nan dole al'umma su karɓeta, idan basu karɓeta ba yunwa ne zai kashesu".
Bari in ɗan yi maku karin haske. Suna da damar kashe dik ayyukan mutane, a nan gaba kaɗan dik wani aiki zai kwace daga hannun mutane, asibitoci zasu dawo na'urorin artificial intelligence ne zasuna aiki, kasuwanni ma haka, zasu rikita komai, kuma ba nan da nisa bane, gaba kaɗan ne zasu aikata hakan. Kun san meyasa suke dikka wannan? Suna son jigatar da al'ummar duniya ne, a yanzu ai basa iya juya duniya gabaɗaya, akwai ƙasashen da suka bijire masu, to wannan abin da suke shiryawa zai sanya ko'ina a duniya ya girgiza, idan yunwa ta yi yawa, a wannan lokacin da kowa yake neman mafita, zasu fito da wannan addini nasu guda ɗayan da suke son duniya ta koma binta, zasu ce ku karɓi wannan addini ku samu jin daɗi rayuwa ko kuma ku mutu da yunwa da wahala.
A lokacin wahala ta kai wahala, za'ayi ambaliya dayawa, fari da girgizan ƙasa, ga canjin yanayin sararin samaniya dake iya haifar da faɗuwar jiragen sama, ga cutar da 3D suke kirakiranwa duniya, jama'a basu da mafita a wannan lokaci, wuya zai sa su mance ALLAH, wasu zasu yi imani da wannan addini, yayin da wasu zasu ce ba zasu yarda ba ko zasu mutu.
Jama'a a wannan tafiya aikin hannu ne kawai WS ba zasu iya kwacewa mutane kai tsaye ba, wannan dole su lallaɓaku su sanya aikin hannunku ya zama yana karkashin sarrafarsu, ta yadda ko noma zaku yi dole ku nemi irin yin noma daga wajensu, ko nama zaku ci dole daga wajensu ne, suna son ganin sun mayar da komai naku karkashin ikonsu ta yadda zasu dinga binsu kuna rokonsu, su kuma su faɗa maku buƙatarsu, ko ku bi ko yunwa ta kasheku. To jama'a shawarata a gareku shi ne ku rike sa'naarku ta hannu, ba dan wani abu ba da na ce ku dakatar da karatu ku rike sana'arku domin ku samu saukin wannan yanayi da suke shirin jefa al'umma a ciki, kada ku yarda a sana'arku ta hannu a kawo maku wani abu da sunan cigaba ne ku karɓa ku yi amfani da ita, hmmmmm, kassaraku suke son yi, su damkeku a hannu gam, su samu damar mayar da duniya na bin addini guda ɗaya, a haka zasu cika burinsu na cure duniya su fitar mata da shugaba guda ɗaya da zai rinƙa juyata. Na kara baku shawarar ku rike sana'ar hannunku, ita kaɗai ce ba zasu iya kasheta ta sauƙi ba!.
-------------------
"Jinjina bro, aikinku yana kyau, na matsu in ga an saki NEXAPOX-31 ɗin nan dan inga yadda zata yiwa duniya, na jima ban ji kukan jama'a ba, ina son in ga suna kuka har da na jini". A cewar Dr James.
Brother yana wani irin shu'umin murmushi ya amsa da. "Kafin mu sake NEXAPOX-31 dole sai mun yi abu ɗaya, idan muka tsananta ambaliyar nan, zamu samu damar sawa a rasa noma, a ruwa tsabtatacce, da matsuguni, al'umma zasu rasa wajen zama. Hanyoyin zirga-zirga na ruwa da sama su lalace, ruwan teku na karuwa, biranen gabar ruwa za su fara natsewa, a Nigeria kamar Lagos, a waje kamar Mumbai, Venice, a Avaris kamar Eldoria".
Sosai Dr James ya ji daɗin wannan batu, ransa ta yi fes sosai.
Brother ya ce. "Ya batun project ɗinmu na Oxygen-Free Humans?"...... A natse Dr James ya ce. "Project ɗin yana nan muna aiki a kansa".
Kun tina akwai ɗakin da 3D suka shiga na wasu halittu da suke kyankyasa? Na ce maku tamkar halittun mutane? To waɗan nan halittu ne Bro yake magana a kai, da su za'ayi tafiyar sabuwar addini, su mutane ne masu iya rayuwa a wurin da babu Iska, 3D sun gyara ƙwayoyin halittarsu ne dan rayuwa ba tare da buƙatar numfashi da iska ba, musamman sararin samaniya. Shi ma babban aiki ne.
Ganin sister Zinta na ɗan motsawa ne yasa Dr James cewa. "Bro goodnight, my princess tana buƙatar in kwanta ta shiga jikina sosai, nima ina buƙatar hakan, mu yi magana wani lokaci".
Wani irin kallo bro ya dallah mashi wanda ya sanya shi cewa. "Abin da ka sani ne, kuma na gama aikata komai". Daga haka ya katse kiran, ya kashe laptop ɗin gabaɗaya tare da mayar da shi saman side sofa ya ajiye, ya ɗauki wayansa tare da fito da light control na ɗakin, ya kashe wutar tare kwanciya, ya jawota jikinsa sosai, yana shafa bayanta har barci ya ɗaukesa, ASUBA TA GARI.
------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
Sai around 5 na yamma Aryan ya farka daga barci, ya yi mamakin ganin Seraphina a jikinsa tana zuba barcinta, intently ya zareta daga jikinsa, ya kwantar da ita a gefe, ya juya, dab face ɗinta ya tsayar da nasa, kallon 2 mins yai mata kafin ya matsa ya manna mata sumbata a forehead ɗinta.
Jikinsa babu kwari sosai, ƙasa ya sauƙo, kai tsaye ya nufi benensu yana ɗan ciza laɓɓa game da duba wayansa, nan yaga saƙon Lion, ai take ya ji kwarin jikinsa, da sauri ya ƙarisa gidansu. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga room na Lion. Zazzaro idanunsa ya yi a kan Vir dake kwance saman katafaren bed ɗin Lion, ya tada kai da cinyar Lion ɗin, yana sanye da pjs, hannunsa rike da waya yana danna.
Lion ma dannar wayansa yake yi. Guru na making call, yana zaune saman side sofa, ya ɗaura kafafunsa a kan throw pillow ɗin dake gabansa.
"Saukar yaushe?". Aryan ya faɗa yana ƙarisowa cikin ɗakin. A kansa dik suka sauke kallonsu, take Lion ya gano yana cikin damuwa, amma ya ɗan ɗauke kansa game da cigaba da dannar wayansa. Vir ne ya amsa da. "Saukar ɗazu"........ Hayewa saman bed ɗin Aryan ya yi, zai yi magana kenan suka ji sallama again.
Da sauri suka kai kallonsu bakin door suna mamakin waye kuma zai shigo masu gida. Ɗan zazzare idanunsu dikka suka yi a kan Uncle Hussain except Lion da yai mashi kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Ciki Uncle ya shigo, da sauri Vir ya miƙe ya tarosa yana faɗin. "Welcome Uncle".
Hannun Vir ya rike yana faɗin. "My son South Korea ta karɓeka fa, ka ƙara kyau matuƙa"..... Dik da fuskan IRON FIST basu san me murmushi ba, Vir ya nuna alamar ya ji daɗin ganin Uncle, dik da bai murmusa ba, ya ɗan saki fuska yana kara riko Uncle ɗin.
Guru dake zaune saman side sofa ne ya miƙe tsaye yana faɗin. "Uncle yau kai ne a gidanmu?"......... "Hunaish ba dole in zo ba, tin da kun mun ya ji". Ya faɗa daidai lokacin da yake zama saman bed.
Dik hayewa gadon suka yi dan jin dame uncle ya zo masu ne. Zuba masu idanu sosai Uncle ya yi na, kallon 2 mins yai masu, dik sun zuba mashi idanu suna except Lion da tin da ya ɗauke kai bai sake ɗagowa ba, ya cigaba da dannar waya.
Ganin kallon ya yi yawa kuma Uncle ya yi shiru ne yasa guru ya ce. "Uncle talk now"........ Nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Nazo ne da maganar komawarku gidan Haiza'an"....... Slowly Lion ya ɗan ɗago da kallonsa kaɗan, sai kuma ya sake sauke idanunsa. Vir ne ya ce. "Uncle komawarmu gidan dad ba zai yiwu ba, kasan in muka koma can dole za'a san bayan dad na raye, dole kuma ɗayan biyu zai faru, ko dai duniya ta san mu ne IRON FIST, ko kuma mu ajiye aikin SSO".
A dake Uncle ya ce. "Dama dole zaku shaidawa duniya kune IRON FIST, lokaci ya yi da zaku maye gurbin Haiza'an a idanun duniya! Ku yi fito na fito da kowa, ku sanya tsoro da gaggarwa a zuƙatan mugaye".......... Guru ne ya ce. "Uncle a yadda muka tsara komai ai kaga da sauran aiki a gabanmu ko? Ka bari mu ƙarisa sai mu koma gidan dad ɗin".
Vir ya ce. "Ga aikin shirin dakatar da ambaliyar da ake ƙoƙarin sakewa, ga aikin........". Hannu Uncle ya ɗaga mashi wanda yasa ya yi shiru, a dake cikin izzar sarautarsu Uncle ya ce. "Bar dik wannan zance, so nike kawai ku koma gidan Haiza'an, lokacin ɗaukar fansa ya yi, bana son in mutu baku cika mun burina ba". Ya kai karshen maganar yana kallon Lion da ko sau ɗaya bai ɗago ya gansu ba tin da suka fara magana, kuma babu alamar zai sanya baki a maganar tasu.
Guru ya ce. "To amma Uncle tare da kai zamu koma ko?"........ "Tukun nan dai".......... Vir ya ce. "In dai zamu koma can to dole mu ajiye aikin SSO, dan IRON FIST fito na fito zata yi ba da iya gwamnati ba, da duniya bakiɗaya ne"......... A taƙaice Uncle ya ce. "SSO da IRON FIST wanne ya fi amfani ga al'umma?".
Aryan da tin da suka fara magana bai tanka bane ya amsa da. "IRON FIST suna sama da kowa da komai"....... "To daga yau IRON FIST kuke ba SSO ba! Dole ku ajiye aikin SSO, ku fito fili ku ceci duniya! Lokacin ya yi da zaku haɗe family dik waje guda, dik ku koma gidan Haiza'an da zama, ku haɗa kanku, ku natsu ku cika mun burina"...... Tashin sense, e lallai kam Uncle ya zo da babbar magana fa.
Tsit ɗakin ya yi, ganin haka yasa uncle ya ce. "Zayra'an baka ce komai ba". Dik suka mayar da kallonsu a kan Lion da yake faman pressing phone. Shiru Lion bai yi magana, almost 3 mins, har sun fidda ran zai tanka, can ƙasa cike da izza ya ce. "Ba ka yanke decision ɗinka na?". Ya faɗa tare da miƙewa, ya nufi balcony.
Binsa da kallo suka yi suna mamakin yadda Lion yake sak daddynsa, banbancinsu kawai daddy yana da jumurin juran abu, shi kuwa Lion ina.
Nisawa suka yi game da dawo da kallonsu a kan Uncle da ya ɗan sha jinin jikinsa, dan ya gane nufin Lion, kuma dama yasan halin kayansa, wannan nuna iko da isar tasu a waje gado ce, watau Uncle ya nuna mashi iko tin da bai nemi shawararsa ba ya yanke cewa zasu koma gidan dad, shi ne Lion ya yi banza da su, kuma ba zai koma ɗin ba, in kuna son shiri da Lion har ya yi abu to ku nuna mashi cewa shi ne sarki a wajen, akasin haka to wlh ba zai yi abin da kuke so ba, Uncle yasan da hakan, ba'a tilasta jinin Haiza'an a kan abu, lallaɓasu ake yi, ka nuna masu power zasu baka mamaki ne, ba power kakansu Lion ya nunawa daddyn Lion ya ce lallai ya bashi hakuri bane yasa ya bar mashi masarautar? To su haka suke, in suna waje sune kawai masu power, komai ikonka dole ka durkusa masu.
Miƙewa Uncle ya yi, ya bi bayan Lion ɗin, yana tsaye a balcony, ya zura hannaye a aljihu yana kallon yanayin cikin palace ɗin. A gefensa ya tsaya cikin sanyin murya ya ce. "My decision is it not yours?"....... Shiru babu alamar Lion zai tanka, ya gano Uncle ya zo da kalaman yaudara ne, ba zasu fahimci shi bane, akwai dalilin da yasa baya son komawa gidan dad ɗinsa.
"Zayra'an talk to me now"...... Shiru babu alamar Lion zai tanka, dik yadda uncle ya so shawo kansa abin ya ci tura, Lion ko kaɗan bai tanka ba, babu ma alamar zai yi magana, rarrashin duniyar nan Uncle ya yi, amma Lion ko ɗagowa ya kallesa bai yi ba, da alama sarautar ce yau ta motsa mashi. Da Uncle ya gaji sai ya dawo cikin ɗaki, ya nufi waje yana faɗin. "Aryan ku shawo mun kan murɗaɗɗen ɗan uwan nan naku, yau ya koma Haiza'an ɗin sak". Ya kai karshe game da ficewa.
A tare Aryan da Vir suka yo ƙasa kafin guru ya rufa masu baya, suka isa in da Lion yake tsaye, idanunsa a kan cikin CRYSTAL PALACE ɗin. A gefe-gefensa suka tsaitsaya game da zubawa PALACE ɗin idanu suna kallonta, Aryan ya ce. "Our Lion me ya ɓata maka rai?". Sun fahimci ransa a ɓace.
Shiru dai babu alamar zai yi magana. Vir ne ya ce. "Uncle ne ko mu?". Still bai motsa ba. Guru ya ce. "Baka son mu koma gidan dad ne?"....... Still dai babu alamar zai kulasu. Suka yi iya yinsu Lion bai motsa daga in da yake ba, yadda kuka san sassaƙa bawan ALLAHN nan aka yi, wasa-wasa har mangrib suna tsaye a wajen Lion bai ko kalli in da suke ba.
Sai da aka kira sallah ya juya ya nufi cikin ɗakin, Vir zai rikosa Aryan ya dakatar da shi ta hanyar kama hannunsa...... "Kyalesa yana kan dokin zuciya ne, sai ta sauƙa, Uncle ya nuna mashi kamar ya isa da mu ne, ya ce zamu koma gidan dad"..... Vir ne ya ce. "Ba dan ma uncle ne ya nuna mashi wannan isa da mu ɗin ba ai da yau mutum ya ji a jikinsa, amma kasan Uncle dole mu yi hakuri da shi".
"Mu je lokacin sallah ya yi". Vir ya faɗa. A tare suka fito zuwa other rooms na floor ɗin, dan su yi gaggawar shirin zuwa masallaci. Yau dai kafin su shirya Lion ya tafi, sai a lokacin kuma ya faɗowa Aryan ashe bai yi sallah la'asar ba, hakan yasa ya ce su je zai yi sallah a gida bayan ya biya bashin wanda ake binsa.
Vir da guru suka wuce suka bi bayan Lion. Shi kuma Aryan ya shinfiɗa dadduma ya tada sallah a gida.
After 3 hours.
*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581*
Likes comments and share fisabilillah.
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-24.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 63 & 64
After 3 hours.
Zaune suke a saman chair na dining, dinner suke yi a natse, babu wanda ya ce da ɗan uwansa ƙala, dik kuma suna kallon abin dake gabansu face Lion dake kallon waya kuma yana dinner.
After some minutes suka kammala dinner, kusan a tare suka ajiye spoons, basa da yawan cin abinci, kai suna iya 24h basu ci abinci ba, kuma basu damuwa, idan sun zo ci ɗan kaɗan suke ci su tattare sauran.
Suna ajiye spoons Lion ya miƙe, cikin room ɗinsu ya shige, bayansa suka bi da kallo har ya shige, Vir ya ce. "Yau Lion ya koma sak daddy, sarautar ta motsa har damu ma yi za'ayi"......... Aryan ya ce. "Ai da sauki ma tin da uncle ne ya taɓosa, kasan uncle kuma ba yadda muka iya da shi, sai dai mu ɓata rai a cikin zuciya".
Miƙewa guru ya yi yana faɗin. "Ina zuwa, ina da aiki"...... "Aikin me?". Vir ya faɗa yana miƙewa shi ma..... "Aiki kan malaman secondary school da Champion ya haɗani da su". Ya faɗa tare da shigewa cikin ɗakinsu. Kallon Aryan Vir ya yi. "Me malamai kuma suka yi?".
Tamke fuska Aryan ya ƙara yi game da miƙewa tsaye, cike da takaici ya bashi labarin dik abin da ya faru kan Seraphina da kuma Rimsha, shi ne yasa guru ya yi mashi bincike kan daga ina matsalar ta samo asali, dan ya ji ƙishin-ƙishin cewa da sa hannun gwamnati, to yana son tabbatarwa kafin ya ɗauki mataki, shiyasa guru yake aikin sirri a kai. Shiru Vir ya yi, can kuma ya ce. "You mean ɗiyar Dr Hushaima tana raye?".
Kai ya jinjina alamar e. "Where's she?". Kara tamkar fuska Aryan ya yi. "Kasan tin asali Dr da Lion basa shiri ai, ba zai bar Seraphina a kusa da shi ba".... Tamke fuska shi ma Vir ya yi kafin ya ce. "Ya za'ayi Dr ta yi shiri da Lion bayan azzaluma ce, ta cuce shi ta cutar damu, ai ko ni bana goyan bayan ya taimakawa Dr, amma kuma ina goyan bayan ya taimakawa rayuwar Seraphina tin da ita bata da laifin komai, laifin wani baya shafar wani ai".
Ɗan rage tsawonsa Aryan ya yi, ya dafa table ɗin gabansa, soyaya ta rufe mashi idanu, baya son laifin Dr sam, a ɗan dake ya ce. "Wace hujjace ta tabbatar maku cewa Dr tana da laifi? Vir ka daina bin bayan Lion a lokacin da baka da hujja a hannu"...... Kada ku manta sarai Aryan yasan biyan Dr akayi maƙudan kuɗaɗɗe, ya ga alert ɗin a wayarta, amma in baku manta ba ya ɓoye maganar alert ɗin bai sanarwa Lion ba, kunji yana son kareta saboda yana son Seraphina.
"Lion bai taɓa hasashen banza ba, bai taɓa yanke hukunci ba tare da ilmi da dogon nazari ba! Dik hukuncin da ya yanke zallar gaskiyarsa ce a kai, dan haka Dr tana da sa hannu a kashe big brother, in ba haka ba meyasa taki buɗe mashi kofa a lokacin da muka sanar da ita rayuwansa na cikin haɗari? Kada ka manta dik iyayenmu sun rasu, manyan brothers ɗinmu dik an kashesu! Saura mu kaɗai muka rage, big brother shi ya tsaya mana bayan uncle, taya kake tinanin ba zamu ji zafin mutuwansa ba?". Har yana ɗan huci ya kai karshen maganar. Nasan kowa ya matsu ya ji tarihinsu, to kada ku damu, zaku ji komai dallah-dallah, ku kara hakuri saura kaɗan.
Shiru Aryan ya yi, hakika yasan sun azabtu a kashe big brother da aka yi, sun kai zuciya nesa ne, amma ba dan haka ba, ALLAH ne kaɗai yasan ɓarnar da za'ayi, shi kansa karfin hali ne yake son gwadawa na kare Dr, ban da haka ai yasan babu hanyar da ya gwada tana da gaskiya.
Ganin ya yi shiru ne yasa Vir sake cewa. "Ga shi a dalilinmu an kashe daddyn Vash, daddyn Rimsha, daddyn Humaira, daddyn Seraphina, all because of IRON FIST, amma still yanzu kana son Lion ya amsa cewa zai fito tamkar yadda dad ya yi? Kana son mu sake rasa uncle ne? Kada ka manta duniya dik ta ɗauka cewa Hussain ya mutu, baya raye, so kake allura ta tono garma?".
Sai a lokacin Aryan ya samu kwarin gwiwar yin magana, nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Uncle ba zai taɓa yin abin da zai cutar damu ba, kada ka manta shi ya umarci da mu ɓoye kanmu a farko, sannan shi ya renemu a irin wannan siga domin mu girma mu ɗauki fansa, ka taɓa tinanin meyasa uncle ya zaɓemu bayan muna da brothers dikkanmu? Ka taɓa tinanin meyasa iyayenmu dik basu renemu da kansu ba suka haɗawa Uncle mu? Suka miƙawa uncle yai mana irin wannan reno?".
Nisawa Vir ya yi, a wannan gaɓa Aryan yana da gaskiya, amma dik da haka akwai buƙatar ƙara lokaci kafin su bayyanawa duniya kansu da manufarsu, a natse ya ce. "Even do! Yakamata mu ƙarisa wasu abubuwan da muka fara a ɓoye kada a rusa mana su". Cikin wannan sanyin murna nasa Vir ya faɗa...... "Da wannan dan wannan, but......"......... "But what?". Yana hararansa ya tari numfashinsa.
Hararansa Aryan ɗin ma ya yi game da cewa. "You want to push me against the wall"........ Hannunsa Vir yakama suka nufi cikin ɗakin Lion ba tare da ya sake magana ba. Nan suka isko Lion kwance saman gado, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kansa, ɗayan hannunsa a kan cikinsa, guru na sanye da bathrobe, da alama daga wanka ya fito, yana tsaye tsakiyar ɗakin suna fuskantar juna da Lion.
Cikin zolaya guru ya ce. "Wai meyasa kake kallona ne?". Yana kallon Lion ya yi maganar. Aryan ne ya amsa da. "Yaga alama ce a jikinka mana". Vir ya amsa da. "Ba dole ya dinga ganinka ba ɗan autan IRON FIST".
Wucewa closet ɗinsu guru ya yi, bai sake yin magana ba, su kuwa Vir ya shiga toilet dan yin wanka, Arya ya zauna gefen Lion tare da riko hannun Lion ɗin, cike da kulawa ya ce. "Bro please a huce haka, talk to us, Uncle fa ya tafi". Tamkar babu Lion a wajen. In takaice maku har suka yi barci Lion bai furta word ba, tamkar wanda aka ɗinkewa baki, yana dai binsu da ido, har suka gaji da magiyar ya yi masu magana suka kyalesa, dama sun san wlh in dai ya yi wannan shiru kome za'ayi ba zai yi magana ba, sai san da yaga dama, ba'a saka shi kuma ba'a hana shi, ganin damansa kawai yake bi, amma dik da haka suna gwada lallaɓa shi da yi mashi magana idan ya fara wannan shirun dik da sun san ba zai amsa ba.
A haka suka kwanta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 79 Chapter of 95