kawo mun wuƙar da bata ci sosai wanda sai na yi ta dirza wuyarsu kafin ta yanzu, ina son su ɗanɗani kalar azabata, ko mutuwa sai ta shaida da sun shigo yankina, sai ta shaida a yankina aka ɗauki ransu".
Take dik ƴan ta'addan dake wajen suka hau ihu suna ɗaga bindigu sama alamar jinjinawa a garesa, Leo da Noor ko a jikinsu, dik da sun kwana sun wuni basu ci abinci ba amma wlh basu jigata ba, bayansu na manne da na juna, suna bin ƴan ta'addan one by one da kallon walaƙanci da ƙasƙanci.
Wani ɗan ta'adda ne ya karisi wajen hannunsa rike da katuwar wuƙa, ya miƙawa ogan nasu, wani kuma daga can gefe ya saita camera dan ɗaukar yadda za'a yankasu a turawa duniya ta gani.
Karɓar wukar ogan nasu ya yi tare da nufar in da su Leo suke, dab kusa da su ya tsaya tare da zaro wukar daga kotarta, ya buɗe hannayensa yana fasa murya wajen cewa. "Dole in sha jininku, kuma nasan jinin naku zai yi daɗi, amma na ji takaicin cewa zan kasheku fa, kuna da kyau sosai, yanzu wannan kyan kawai zai tafi a banza? Gaku matasa da ku! Na tabbata baku bar baya ba, baku bar iri ba, kash wannan abu bai mun daɗi ba".
Da yake hannayensu zuwa cikinsu ne a ɗaure sai Leo ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tare da yin fito mai kamar sauti kafin ya ce. "Kana jan lokacinka fa, bana son ka haura lokacin da na ɗeba maka". Da harshen turanci suke magana.
Wani irin dariyar samudawa mutumin ya yi kafin ya kara taku ɗaya, ya danki golden white hair ɗin Leo tare da ɗaga kansa sama. "Kisan da zan yi maka sai ya fi na brother ɗinka munu"....... Nisawa Leo ya yi tare da yin fito da karfi. Unexpected harbi ne ya ratso cikin wajen kai tsaye sai damtsen hannun ogan nasu.
Wani irin ihu ya kurma tare da ja da haya ya saki wukar hannunsa yana dafe in da ake harbesa. Take dikka ƴan ta'addan suka haɗe kai tare da ɗaga bindigunsu suna ƴan waige-waige. Leo ne cikin ɗaga murya ya ce. "Fire!"....... Haba take wajen ta kaure da harbi.
Watau dama da gangan ya miƙa wuya, sun yi ƙoƙarin sanin in da ainahin tsakiyar sansanin ƴan ta'addan yake da kuma hanyar da za'a bi a je wajen, amma sun rasa ganewa, shi ne suka shigo bakin sansanin nasu, Leo ya shirya cewa shi zai je, idan suka kama shi sai sojojinsu su bi bayansu su ga hanyar da suka bi da su, daga nan sai su dawo su yi shirin gagarumin yaki su yi wa ƴan ta'addan zobe lokaci guda kawai su kamasu, kada ku manta a ƙaida an ce su kama ƴan ta'addan ne ba su kashesu ba, shiyasa suka harbi ogan nasu a wajen dantsen hannu in da ba zai mutu ba.
Sosai Noor ya ji tsoron rasa Leo a lokacin da Leo ɗin ya ce zai je ya miƙa wuya su kamasa, sai ya ce ba zai yarda ba sai dai su tafi tare, shiyasa kuka ga sun shigo su biyu kawai, tarko suka kafa ƴan ta'addan, ga shi yanzu sun kamasu a sauƙaƙe.
Kafin ƴan ta'addan su farga su Zaynish sun kewayesu sun kuma matso izuwa cikin sansanin nasu. Vash ne ya yi shahadar zuwa da gudu zai nufi in da su Leo suke dan ya kwance unexpected aka harbesa. ALLAH sarki burinsa ya zo ya kwancesu kada ƴan ta'addan su fusata su harbesu, ashe shi ne da rabon wahala, bullet bai taɓa shi a in da zai mutu ba, dan a wajen cinya ya same shi.
Faɗuwa ƙasa a wajen ya yi. Zaynish ne ya saita kullin igiyar da aka ɗaure Leo ya harbeta take ta tarwatse, hakan yasa Leo ya samu damar zame hannunsa. A gaggauce ya miƙe ya fara ƙoƙarin kwance Noor. Zaynish ya tsaya masu sosai, dan ya rike wuta ta saitinsu, yaki bada sararin ƴan ta'addan su iso in da suke bare su kashesu, da ya ga motsi ta kusa da su zai yi harbi, har Leo ya samu dama ya miƙe ya kwance Noor.
Suna miƙewa a tare Leo da Noor ɗin suka ɗaga hannu suka yi wa Zaynish jinjina, dan ya yi namijin kokari, musamman yadda ya tsaya masu ya ki bada sarari ƴan ta'addan su samu damar kashesu.
Suna sauke hannunsa daga jinjinawa Zaysh Noor ya danna da gudu izuwa in da Vash yake kwance, dan sun fi kusa. Dai juyi yake yi saboda zafi. Hannu Noor yasa ya ɗaukesa cak ya ɗaura a bayan wuyansa, ya kuma ɗauki bindigarsa dake yashe a ƙasa da ɗayan hannunsa, ya harbawa Leo bindigar Vash ɗin, sannan da gudu ya nufi in da Zaysh yake tsaye, yana da ɗan nisa da su.
Zaysh ya tsaya mashi, ya yi ƙoƙarin hana a kawo mashi hari ta baya da bindigarsa, Leo ma da ya caɓe bindigar Vash sai ya tarewa Noor ɗin samun damar kawo mashi harin baya.
Da gudu ya fitar da Vash waje zuwa in da sauran sojijinsu suke, bindiga ya karɓa wajensu Unays da jakar bullet ya nufo ciki babu ko tsoro, shi ba zai iya barin Leo shi kaɗai da mutanen nan ba, shiyasa ya nufi dawowa ciki. Cikin zafa Zaynish ya biyosa suka dawo.
Musayar wuta suka fara yi da gasken-gaske, dikkansu sojojin babu sa ran komawa a raye a cikin zuƙatansu, idan sun mutu ma dama hakance a ransu cewa in su fito ba lallai su koma ba.
Da ƴan ta'addan suka ji wuya sai suka fara dannawa a guje suna kutsawa cikin daji. Ai rakasu a guje sojijin suka, sun sha alwashin ba zasu bar ko ɗaya ya gudu ba, dik wanda suka gani sai su harbesa a ƙafa su wuce sauran sojojin dake biye dasu kuma suna tattarasu waje guda.
Leo, Noor and Zaynish babu ɗaga kafa suka raka ƴan ta'addan a guje, sun jajirce wajen ganin sun kawo good result a Mission ɗinsu na farko. Wani irin yaki suke yi mai salo na ɗaukar hankali su ukun nan, kamar ba mutane ba.
A garin bin ƴan ta'addan ne suka shiga wajen wani sunkurun daji, fili ne dake cunkushe da bishiyoyi masu cikar ganyayyaki, sun sanya wajen ya yi duhu, ga tarin maɓoya sosai, wanna waje ake cewa fidda ran fita idan ka shiga.
Ko tsoro basu ji ba suka tsaya a tsakiyar wajen suna duba ta ina ƴan ta'adda suka yi. Zaynish ya buɗe bututun bindigarsa yana duba bullet nawa ya rage masu. Fito da karfi Leo ya yi wanda hakan yasa suka raba kansu da gudun gaske cikin zafin nama. Suna raba kansu bullet ya wuce a tsakaninsu. Ai da gudun gaske Noor ya juyo ya nufo su Zaynish, kamar Zaysh ya sani ya ɗan duƙa mashi Noor ya taka shoulder ɗinsa yakara tsawo tare da ɗaga bindigarsa sama ya yi harbi uku a jere izuwa saman bishiyar dake ta kusa da su.
Yana harbin ya faɗi ƙasa cikin ciyayi, akwai su da saiti, ƴan ta'adda ukun dake kan itacen dik ya harbesu a kai sun mutu. Kansa Zaysh ya yi dan ya duba faɗuwar nan da ya yi bai ji ciwo ba ko. Sai dai kafin ya isa ga Noor Leo ya yi tsalle ya rungumesa suka faɗa ƙasa tare, a take bullets a gere guda biyar suka wucesu fiw.
Cikin zafa suka wani irin mike a tare, sai suka yi deciding da su nemi wajen ɓuya suma, saboda sun gano ƴan ta'addan da suka ɓuya a nan suna dayawa, dole ayi yakin sunkuru yanzu.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1🔥
2025-12-3.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 36 & 37
Cikin zafa suka wani irin mike a tare, sai suka yi deciding da su nemi wajen ɓuya suma, saboda sun gano ƴan ta'addan da suka ɓuya a nan suna dayawa, dole ayi yakin sunkuru yanzu.
A tare suka ɓuya bayan wasu sunkurun ciyayi, suka tsaya shiru ko numfashi basa yi suna son gano ƴan ta'addan. Ai wannan shirun da suka yi ba ƙaramin taimaka masu ya yi ba, domin kuwa sun jiyo numfarfashi da dama a maɓoyan ƴan ta'addan, wasu ma sai haki suke yi, kun san na faɗa maku sai ka sa karfi zaka iya harbi da bindiga, dan yadda bullet ɗin yake fita da karfi jijjiga mutun yake yi, sun sha harbi sun jijjiga shi ne suke ta haki sama-sama.
Can su Leo suka ji wasu muryoyi a ɗan nesa da su suna faɗin. "Nima bullet ɗina dikka ya ƙare". Ɗayan ma ya ce. "Ai dikkanmu babu mai sauran bullet a cikinmu, kawai mu fito mu yi gaba da gaba da su".
Kallon juna su ukun suka yi, Noor ne ya ce. "Dama kwana biyun ban watsa jini ba, bari mu yi wrestling da su mu gani". Ya kai karshe tare da sauke bindigarsa ƙasa, ya yi mata ma'ajiya a wajen, sannan ya miƙe. Dikkansu ma'ajiya suka yi wa bindigunsu suka ɓoyesu, sannan suka mimmiƙe suka fito tsakiyar wajen.
Suna fitowa ƴan ta'addan ma suka fara fitowa, sun fi mutum 25 suka fito. Gyara tsayuwa su ukun suka yi, Leo ne ya ce masu. "Dik ku tabbatar idan kun masu duka ɗaya ba kari!"........ Noor ya amsa da. "Angama"....... Watau matasan sojoji ukun nan suna jin jininsu a tafashe yake, suna ji da lafiya da zafin jini.
Zobe ƴan ta'addan suka matso suka yi masu, kan kace me suka fara wrestling ɗin da suka ce a kansu, wai waɗan da kayan maye ya gama cinye masu quality ɗin jiki ne zasu gwabza da sojojin AZURE, sojojin AZURE ɗin ma sabbin jini yayen bar two, ai ko ƴan bar one in suka yi wa waɗan nan duka ɗaya ba tashi bare ƴan bar two.
Sosai suka gwabza faɗa, Noor kam da mai hali baya canzawa ma ai abin wasa ya mayar da su. Da ya kaiwa wani ɗan ta'addan da ya zo zai kamasa da faɗa mari sai da ya ji ƙamshin lahira, sharara mashi mari ya yi yana faɗin. "Ɗan banza dubeka dik yunwa ta kusa hallaka shi ne zaka zo in karisaka ko? Dik kayan maye ya cinye maka ƙoda da huhu".
Ai ya ji marin maza, sai da ya yi wani irin tangal-tangal kamar zai faɗi sannan ya tsaya da kafarsa. Yana ƙoƙarin ɗagowa Noor ya kama wuyansa da hannu ɗaya, ya jasa izuwa wajen bishiya, da karfi ya maka kansa da jikin bishiyan. Noor sai shirin ALLAH, sai ya ɗaukesu dik kamar abin wasa, dukan mata yake yi masu, ya ce idan ya ce zai masu dukan sojojin AZURE dik zasu mutu ba'a mai da su barrack ba.
A cikin ƙasa da mintuna 10 suka lallasa ƴan ta'addan nan, wasu ko motsi basa yi. Noor ne ya ce. "Waɗan nan ɗaukarsu ma ai aiki ne, jibesu fa, ƙazaman banza"....... Leo da ya ɗauko bindigarsa yana ƙoƙarin gyarata ne ya ce. "Babu in da zamu kaisu, dik harbesu a nan zamu yi, idan ma an gane mun kashesu sai mu ce a musayar wuta ne by mistake, kada ku wuce kama ƴan ta'adda biyu mu koma da su, suma dan ana buƙatar bayanai daga bakinsu ne, amma dik saura ku harbe shegu!".
Na'am da wannan shawara suka yi, Zaynish ne ya fara saita bindigarsa ya dinga binsu one by one da suke baje a ƙasa yana fasa kansu da bindigar tasa, babu tausayi bare imani. To a irin haka ina soja zai yi tausayi? Ai aikin soja ba dik kai ba, tin yana gani ana kashewa a gabansa har ya fara kashewa da kansa, ya kashe ya kara kashewa, tin yana kashewa yana tausayi zuciyarsa na ɗan rawa, har ya dawo kisa ta zame mashi jiki, ya saba, zai ɗauki bindiga ya harbi rai kamar ya harbi tsuntsu, ba zai damu ba, ba zai ji komai ba!. JINJINA GA DIK WANI KAKI NA SOJA!.
Bayan sun kashesu tsab Leo ya wuce gaba, tsalle Noor ya daka ya ɗale bayan Leo ɗin, cikin shagwaɓa ya ce. "Bro na gaji, ba zan iya tafiya da kafafuna ba, ka goyani har zuwa wajen sansaninmu my Juliet ta mun massage"....... Hannu Leo yasa ya gyara shi a bayan nasa da kyau, ya tallabosa suka cigaba da tafiya kafin ya ce. "ALLAH ya shirya mun kai".
Zaynish ne ya daki kafaɗar Noor tare da cewa. "Ba zaka canza hali ba!"....... Turo baki ya yi tare da saƙalo wuyan Leo, ya kwantar da kansa a bayan wuyan Leo ɗin yana hararan Zaynish kafin ya amsa da. "Bafa zan canza ba!".
Leo dai bai sake yi masu magana ba, yana ta cigaba da tafiya abinsa, ya rataye bindigarsa a gefen shoulder ɗinsa. Noor dake kwance yana zuba masu shagwaɓa ne ya zabura ya sauƙa daga bayan Leo, tsayawa cak shiru suka yi, take suka ɗauke nunfashinsu suka daina yi. Nan suka ji alamar numfashin mutane biyu daga gefensu.
Tsalle Noor ya yi ya sake hayewa bayan Leo tare da gyara bindigarsa, kafin su Zaynish su gano masu numfashin ya saita ya yi harbi biyu a wajen sunkurun ciyayin dake kusa da su, already ya ga ƴan ta'addan dama. Yana sake harbi biyun nan ya komar da kansa a bayan wuyan Leo ya kwanta yana turo baki da shagwaɓa tamkar bashi ya gama harbi yanzu ba, ya wani rukunkume Leo, kamar zai yi kuka ya ce.
"I miss my Juliet over, nasan yanzu tana can tana kukan rashina .......". Bai karisa maganar ba ya dakata tare da ɗaga bindigarsa ya saita gabansu ya yi harbi. A tinaninsa alamar da ya gani ta mutum ɗaya ne a wajen, sai dai yana harbin ta samu mutum ɗaya shi kuma ɗaya ya fito da gudun gaske, kafin su harbesa ya iso in da suke.
Kan su juya ya yanka Zaynish da wukar dake hannunsa. Da karfi Leo ya juyo da Noor dake bayansa, Noor ya saita bindiga ya harbi ɗan ta'adda ya faɗi mushe. Cikin zafin jini Noor ya sauƙo ƙasa daga bayan Leo, da sauri ya zo ya rike Zaysh yana faɗin sorry.
A wajen damtsen hannu yai mashi wani irin wawan yanka da ta shiga sosai. Rigar jikinsa Noor ya cire tare da sanya karfi ya yageta, ya kama hannun Zaysh ya ɗaure mashi dan su samu jinin ya taƙaita zuba, saboda ba karamin jini ne yake zuba daga wajen ba, kunga daga yaki ya fito, ya jijjiga jininsa sosai, dole jini ya zuba a wannan yanka sosai.
Ɗaure mashi gam ya yi, sannan Leo ya ɗaukesa a bayan wuya suka cigaba da tafiya. Abin like wow, suna tafiya Leo and Noor suna hira kuma suna kashe ƴan ta'addan dake gudowa daga wajen sassaninsu in da sojojinsu ke ɓarin wuta, suna tsarewa su nemi wajen ɓuya, da sun fito zasu ci karo da su Leo, sai su harbesu, kuma ko a jikinsu basu tashi hankali ba, a natse suke tafiya suna hiransu.
In takaice maku labari sai da suka kwana suka wuni suna musayar wuta, Vash da ya sha harbi a kafa Leo ya umarci wani soja ɗaya da ya ɗaukesa ya mayar da shi sansaninsu surgeon devissio watau my surgeon lioness Manassa ta dubasa ta ceto rayuwansa kada a tsaya ɓata lokaci bullet ɗin ta yi ɓarna, komai na iya faruwa idan aka barshi ya jima, yana ma iya rasa kafarsa yazama sai an yanke mashi kafar nasa, shiyasa Leo ya ce a mayar da shi sansanisu da wuri dan basu san adadin lokacin da zasu ɗauka a wannan ɓarin wutar ba.
To a haka suka kwana suka wuni babu cin abinci babu ruwan sha, musayar wuta kawai suke yi, har sai da suka tabbatar komai a arear ya daina motsi, sun kashe dikkan ƴan ta'addan sannan suka fara shiga lungu da saƙo na sansanin ƴan ta'addan suna dubawa ko akwai waɗan da suka ɓuya, su kamosu su masu yankar rago.
Basu bar mutun ko ɗaya da rai ba sai guda biyun da suka harba a kafa, da ogansu da wani, su kawai suka bari da rai dan su mayar da su barrack.
A ɓangaren su Arya kuwa, kamar yadda su Leo suka kwana suka wuni musayar wuta suma haka suka kwana suka wuni musayar hawaye, sun shiga damuwa, ko abinci basu ci ba, sun zauna jugum-jugum har zuwa lokacin da sojan can ya dawo da Vash ɗauke a saman wuyansa. Da gudu su Arya suka fito jin cewa ga soja ya dawo ɗauke da wani soja.
Ai ba wanda ya kai Manassa kiɗima da ganin Vash aka harba, domin kuwa shi ne mutumin da ta haɗu da shi a safiyar ranar da zasu tafi bakin daga. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ta yi kansa tana tambayar me ya same shi ba?.
Da gudu wani soja ya shiga cikin tantinsu ya ɗauko wani tampol ya zo ya shinfiɗa a ƙasa a wajen. Shinfiɗe Vash a kai sojan ya yi, a lokacin ko motsi Vash baya yi, ya suma kuma ya rasa jini. Kansa Manassa ta yi, tsabar ta ruɗe ma ta manta da cewa ita ce surgeon ɗinsu.
Arya kuwa, da gudu ta shiga cikin ɗaki ta ɗauko jakar Manassa. A gaban Vash ta zo da gudu ta zube gwiwowinta, zuge zip na jakar ta yi, gabaɗaya ta zazzage abin dake ciki a ƙasa tsabar kiɗima. Sai a lokacin Manassa ta farga da ashe ita ce surgeon ɗinsu, ai cikin zafin nama ta kwaso kayan aiki irinsu scapel, jikinta na kerma, tana hawaye ta fara ƙoƙarin ceto kafarsa.
Da yake Arya tana da ilimi a kan aikin na Manassa sai ta taimaka mata. Wani abu da Arya, tana da mugun tausayi ne yarinyar, idan ta ga wani a cikin wani hali tana rasa hankalinta gabaɗaya, ba ruwanta da koma waye, kawai idan ta ga mutum a damuwa zata tsaya mashi ne sai in da karfinta ya kare. Yanzu haka ta tsaya tsayin daka a kan Vash har zai da ta ga ya fita daga haɗari, sannan ta samu damar jan dogon numfashi, sai ta koma babin tinanin sterious ɗin nata.
Ganin Vash ya fita daga haɗari ne yasa kowa ya hau sauke ajiyar zuciya, musulman cikinsu suna ta Alhamdllh. Ita kuwa Arya matsawa dab da shi ta yi, hannunta har yana rawa wajen sanyawa ta ɓalle botiran rigar jikinsa, tsabar an shiga tashin hankali basu lura da uban gumin da yake haɗawa ba.
Buɗe gabar rigar ta yi, ta ɗauko kwalin wani drugs a cikin kayan aikin surgeon Manassa, ta yage kwalin, ta cire drugs ɗin ciki ta hau yi mashi fifita tana addu'ar Leo ɗinta ya dawo lafiya, dan tin da ta ga Vash da rauni ta ƙara karaya.
Ita kuwa V tana barcin safe a lokacin, daren jiya bata rintsa ba, sai yanzu take barci. Angelina na ganin abin dake faruwa ta dannawa daddynsu kira tana ruwan hawaye....... A lokacin da kiran ya shiga yana tsaye a tsakiyar ɗaki rike da waist ɗin Aunty Lisa dake kokarin ɗaure mashi maɓallan uniform ɗinsa, a taƙaice dai tana shirya shi zai fita office.
Ya tallabo waist ɗinta ta baya wajen mazaunanta, suna kallon juna ido cikin ido cike da tsantsar so da kauna, sai murmushi take yi. Sumbata ya bata a cheek ɗinta kafin ya ce. "Miƙo mun wayata ana kira". Da sauri ta juyar da kallonta zuwa saman bed ɗinsu dake shinfiɗe da tsadaddun bed sheet, ga wani fitinannen kamshi dake tashi.
Watau auren nan ya karɓesu fa, dikkansu suna kula da juna, Aunty Lisa ta kara kyau matuƙa, har wani murjewa skin ɗinta ya ƙara yi, while shi ma daddy GAT hakan ce, har wani sheki skin ɗinsa yake yi, ga kumatu da ya yi, hankulansu a kwance, yana nuna mata soyayya matuƙa, ita ma tana nuna mashi.
Yanzu haka ya cika alkawarinsa na sama mata aikin jaridar da ta kwallafa rai a kai, idan ya fita aiki ita ma zata fita nata aikin, amma tana riga shi dawowa.
Ɗauko wayar ta yi ta miƙo mashi. Ganin Angelina ke kira yasa ya katse kiran ya kirata. Aunty Lisa na ƙoƙarin juyawa ta bar wajen ya kamota da ɗayan hannunsa a lokacin da yake cewa. "My daughter be patient please, meyakefaruwa?"........… Tana goge hawayenta ta faɗa mashi an harbi sojansu ɗaya ne.
To abinku da soja, ko a jikinsa, wace iriyar mutuwa ce basu gani ba, sai kawai ya yi ƙoƙarin kwarara mata gwiwa, ya tunatar da ita cewa sun rigada sun yafe rayuwa ne kafin su fara wannan aiki? Ai rayu ba wata aba bace su a wajensu, so ta daina damuwa. Tina mata da komai da ya yi ne yasa ta shanye kukan, ta kwarara zuciyarta tare da yi mashi godiya.
Daga nan ya tanbayi ina sauran Angels ɗin nasa, ta faɗa mashi suna waje suna aikin cetan ran Jami'in, a ɗan dake ya ce. "Awww wai ba mutuwa ya yi ba dama kike wannan kukan daughter?"...... Da e ta amsa tare da faɗa mashi yadda komai ya wakana. Girgiza kai ya yi, a cikin ransa ya ce mata koma yaya ba zasu taɓa rabuwa da raunin zuciya ba, shi ai ya ɗauka ma an kashe sojan ne a gabanta yasa ta birkice, shiyasa yai mata uzuri dan bata taɓa kallon mutuwa a gabanta ba, to ashe ma ba haka bane.
Ƙara karfafa mata ya yi kafin su yi sallama ya ajiye wayar, ya kara jawo Aunty Lisa jikinsa, sai da suka zubawa juna soyayya sosai, ya yi kissing ɗinta sosai sannan ya saketa game da kama hannunta suka nufi parlo. A nan suka yi sallama ya nufi waje ita kuma ta zauna a saman sofa.
A ɓangarensu Arya kuma, in ƙara takaice maku labari a washegarin ma sai can yamma su Leo suka bar sansanin ƴan ta'addan nan, sai da suka yi kwanaki biyu a hanya kuma kafin su dawo sansaninsu. Suna dawowa suka kira barrack kan azo a ɗaukesu MISSION IS DONE!. Take suka hau shirin komawa. A ranar da suka dawo Manassa ta yi treating hannun Zaynish da ya sha yankar wuƙa.
A wannan rana daɗi kamar Arya ba zata mutu ba, sai satar kallon Leo da bai san tana yi ba take ta faman yi. Noor da V kuwa a tare suka kwana manne da juna wajen da suke hura wuta dan jin ɗumi, suka ɗaure ƴan ta'addan da suka zo da su a jikin bishiyar dake kusa da su. In ƙara taƙaitawa kwanansu ɗaya da dawowa jirgin da ta kawosu ta dawo ta ɗaukesu, amma a wannan karon sai da suka yi tafiya cikin daji kafin su samu wajen da yakamata jirgin ta sauƙa, suka naɗe tantunansu, suka tattara komai suka koma barrack.
Ko da suka koma hutun satin biyu aka basu dan su sake shirin shiga Mission na biyu, ba'a faɗa masu me result na mission na farko ba, so ake yi sai an haɗa Mission ɗin guda biyar dikka.
Mission ɗinsu a kudancin ƙasar bashi ne the most important ba, mission ɗinsu a arewacin ƙasar shi ne ma dalilin wannan missions ɗin a labarin nan, dan haka zan yi skipping ɗayan mission ɗinsu na Kudancin nan mu je arewaci, saboda in na biyewa rubuta komai zamu ja lokaci, gara mu rubuta the most important ɗin.
Kamar yadda suka yi mission na farko haka suka saka yi mission na biyu, sun kuwa yi lafiya sun dawo lafiya babu wanda ya rasa ransa. Daga nan ne aka sake shigar dasu ɗakin horo na musamman, saboda zasu tafi mission a kan Arewacin ƙasar dake cike da jiga-jigan ƴan ta'addan masu haɗari, sai aka ware watanni biyar za'a sake horar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 95