fara'a, sannan ita kaɗai ce mai saukin kai da kaunar ƴan aikinsu, sai Angelina ita ma time to time tana da mutunci.
Dikkansu suna da mugun tsabta, dan wlh ko mai ƙanƙantar datti basa accepting a arear da suke. Dikkansu ba musulmai bane kamar yadda kuka san GAT mahaifinsu ba musulmi bane. In maku yadda zaku gane, idan kuma gansu yadda kuka san irin fashion model ɗin nan, watau irin shahararrun mata masu tallan kaya ko wani abin, suna da tsawo da kyakkyawan jiki, kuma just 13 years suke da shi fa.
Dikkansu gashin kansu dark ash ne haka, mai balain kyau wanda har wani sheki yake yi idan ya ji gyara. Ga idanunsu dara-dara fararen sol, kuma abin dake kara rikita mutane da su irin tiger brown eyes ɗin nan ne da su kamar na daddynsu, idan suka zare maka ido tamkar idanun tiger, jikinsu tamkar madara, da yake suna da tsawo sosai zaka iya basu 15 years in ka gansu.
Dikkansu suna da zane a wajen wuya wanda daddynsu yai masu tin suna ƙanana dan mutane su rinƙa rabesu, tsananin kamar tai yawa ne. Kowacce a gefen wuyanta an rubuta mata harafin farko na runanta, Arya and Angelina da suke da A a farkon suna sai daddynsu ya sanyawa Arya sunanta ARYA, Angelina kuma A kawai dan banbanci, to da wannan zanen ake banbancesu.
Su ɗin ba kamar sauran yaran da kuka sani ba ne. Kwararrun jami'an bincike daddynsu yake da burin su zama, kuma ALLAH ya zuba masu baiwar, yanzu haka suna da 13 years, amma idan suka rike computer sai kun sara masu, suna karatu ne a nan A-C-S dake nan cikin Barrack ɗin, makaranta ce da ake kwankwasan kwararrun jami'an da suka san computer, wanda dik wani aiki da za'ayi sai da su, cikin ƴan mintuna ƙalilan suke iya binciko abu dik nisansa, basu da wasa kuma basa ɗaukar wasa, yanzu trainin suke karɓar a kan computer, sannan suna karɓar horo irin na su Leo, sai dai ba kamar nasu kai tsaye ba, sese-sese dai, su ana basu horon ne dan kare kansu idan suka shiga wajen haɗari.
Bari in yi maku misalin jami'an zaku fi ganewa, su idan za'a je kama riƙaƙƙun ƴan ta'adda ana tafiya dasu ne a motarsu daban da Computers ɗinsu a cikin motar, zasu tsaya ɗan nesa da in da ƴan ta'addan suke, zasu tura drone mai ɗauke da Camera da suke controlling ɗinsa daga in da suke, idan ya isa wajen ƴan ta'addan zasu dinga ganin dik abin da suke aikatawa, daga nan su samu connection da sojoji suna faɗa masu dik wani motsi na ƴan ta'addan tin da suna ganinsu. Nasan yanzu kun gane irin jami'an da nike nufi, masu kaifin ƙwaƙwalwa da basira, kina basu number kika ce su nemo maki mai ita cikin ƴan sakanni zasu faɗa maku a in da yake, to su ana basu horo ne dan su kare kansu idan yaki ta ɓarke ta ritsa da su a wajen kama ƴan ta'addan................ To abin da su Arya ke karanta kenan, kuma su dikkansu uku da, ita kuma Manassa tana ɓangaren Surgeon Generals, watau likitan sojoji, sun mai da hankali sosai, dan suna burin zaman manyan jami'ai. Aikin soja suka so, amma daddynsu baya son su sha wahala shi ne ya sanyasu waɗan nan matsayi.
Uhm yanzu muka fara tafiyar, wasan kwakwalwace zallah a book ɗin nan, ilimi za'a gwada da kwarewa, ga soyayya mai zafi! me kuke tinani? ku biyoni dan samun ilimi kuma!.
------------------------🔥
"Woooow". Angelina ta faɗa tare da miƙewa tsaye gabaɗaya, ta kara zaro tiger eyes ɗinta a kan Leo dake tsaye yana kallon ƙasa. Da sauri ta taɓo Arya tana faɗin. "Bloody, look at this handsome guy, heroic man". .... Kusan a tare dikkansu huɗu suka ɗago kai da kallonsu a kan Leo. V mayyar soyayya da shauki ce ta fara cewa. "Kai anya wannan ba Angel bane? Dik yadda aka yi mala'ika ne". Ta faɗa cikin ruɗu tattare da shauƙi tana wani ɗan rintse ido ta sake warowa.
"This is unbelievable V, this is seraph, look at his body, like wow". Cewar Manassa... Angelina ce ta capki zancen da cewa. "Laaa motan daddynmu ne, mu ya zo ɗauka, daddy ba zaizo ba dama".
Waro idanunsu gabaɗaya suka yi a kan motar da ya jingina, lokaci guda suka hau sauke ajiyar zuciya. Arya ce ta ɗan ja siririn tsaki kafin ta ce. "Seraph bai kamata ace yaron daddy bane! Disgusting!". Ta faɗa tare da nuna yatsarta na tsakiya alamar ƙasƙanci.
Manassa ce ta amsa da. "All though wani guru ne! Look at his body, his soft skin, all though ɗan wani shegen ne, but it's very disgusting ace boy ɗin daddy ne, I feel very shameful for him". Cikin sigar rainin wayau tai maganar.
Arya ce ta sake cewa. "Leave all your bags here bari mu sakashi ya zo ya ɗauka mana tin da boy ɗin daddy ne". .......... Su fa daga ganin ya zo ɗaukarsu kenan ɗan aikinsu ne tin da a karkashin daddynsu yake!.
Nufar in da yake suka yi, cikin takun class da yanga, Arya ce a gaba hannunta rike da basketball ɗin nasu. Shi dai tamkar babu shi a wajen. A gabansa suka tsaya, cikin bada umarni Arya ta ce. "You don't know your work, right? Ko dai door ɗin ma mu zamu buɗewa kanmu ne?".
Da yake yana kallon ƙasa ne sai ya kalli Boot dake kafafunsu, a nan ya gane sun iso in da yake, ko kaɗan bai motsa ba, babu alamar ma zai tanka masu. Dikkansu da suka matso kusa da shi babu wacce kirjinta bai buga ba, sunga madarar kyau ga kwarjini, dik sun kasa magana, Arya ce ma da yake akwaita da karfin hali da tsiwa shiyasa ta iya yi mashi magana.
Ganin bai amsa masu bane yasa suka kalli juna, sai kuma suka mai da kallonsu a kansa. V sarkin saukin kai sai ta nufi wajen motar, buɗe kofar tai tare da cewa. "You people should come in".
Wani irin tsaki haɗe da kallo mai wuyar fassaruwa Arya ta dallawa Leo da bai san tana yi ba, a cikin ranta ta ce dole ta faɗawa daddy ya hukunta shi, dan ya ɓata mata rai. Manassa da Angelina da suka kasa yi mashi magana ne suka yi saurin shigewa cikin motar, sai kallonsa suke yi tamkar zasu cinyesa da ido. Ita kuma Arya gyara tsayuwarta tai tare da rike waist ɗinta da hannayenta dikka biyu, cike da gadara ta ce. "Ka kwaso bags ɗinmu mu je".
Still Leo bai motsa ba, yana tsaye. Motsawa tai tamkar zata shiga motar, ganin bashi da alamar zuwa ɗauko bags ɗin nasu ne yasa ta dakata, matsawa kusa da shi tai, dik da mugun kwarjinin da ya yi mata, ga shakka da tsoronsa amma ta daure ta tsaya dab da shi, zuciyarta na bugawa da karfi, amma saboda karfin hali irin nata sai ta miƙa hannu ta ɗago haɓansa tana faɗin. "Kai kurma ne? Ko baka san aikinka ba......".
Gagara karisar da maganar ta yi saboda sharp eyes ɗinsa da ya sauke a kanta. Wani irin rikicewa ta yi, a miliyan ta ja da baya har kamar zata faɗi tai zafin namar rike kanta, zazzare idanunta a kansa ta yi, tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa. Shi kuwa kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, gentle ya raba jikinsa da jikin motar, ya buɗe from side ya shiga, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi wa motar key.
Ganin tsab zai iya tafiya ya bar Arya ne yasa Angelina tai saurin leƙowa ta jawo hannunta, dama basu rufe door ɗinsu ba. Kuma tsabar girman kai irin na Arya taki zuwa ta kwaso masu jakunkunan, watau sai da shi ya zo ya ɗauko ko a barsu a wajen.
Shi kuwa reverse yai, ya juya kan motar, ko a jikinsa, bai ɗago ko sau ɗaya ya kalli in da suke a ciki ba, da sauri Angelina ta rufo kofar. Da gudun gaske ya ja motar suka bar school ɗin.
A shagwaɓe V ta ce. "Daddy's boy mu idan an ɗauko mu a mota ba'a gudu saboda ina tsoro, please go slowly".
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
5-11-2025.🔥
https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP/
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
E_____________6
A shagwaɓe V ta ce. "Daddy's boy mu idan an ɗauko mu a mota ba'a gudu saboda ina tsoro, please go slowly".
Ai ina bai ma san suna yi ba, bai canza daga yadda ya fara tafiyar ba har koma wajen barrack ɗin, a kusa da wasu zaratan sojojin da suka kame kam ganin motar GAT ya tsaya. Slowly ya sauke glass ɗin motar, cikin mutuntawa ya sara masu while suma ƙoƙarin sara mashi suke yi a tinaninsu GAT be tin da sun san shi yake ɗauko yaransa.
Tambayarsu ya yi ina ne gidan GAT, kallon juna su V suka fara yi, sun ji daddaɗar murya, Angelina ce cike da mamaki ta matsa kunnen V, raɗa ta fara yi mata. "Buddy watau baya magana da mata ne shi? Kin ga yana tambayar wasu gidanmu, but yaki yi mana magana".
V da ta gama marairacewa ne ta amsa da. "I felt so bad my love, ni ban yi mashi laifi ba, but why yaki yi mana magana?"......... Dik basu ji daɗin yadda yaki ya yi magana da su ba, musamman V, Angelina and Manassa, sun fola mashi matuƙa, ya haɗu amma dan iskanci ya cika mashi ciki ko kallon in da suke bai yi ba.
Suna nan suna gulmansa shi kuwa har mashi kwatance, dan haka ya figi motar da gudu, V tamkar zata yi kuma, ta sake cewa ya tafi a hankali ita da Manassa suna tsoro, ba'a gudu da su a mota, amma Leo tamkar babu shi a motar, bai tsaya ba har ya isa kofar katafaren ginin gidan GAT wanda tin daga nesa zaka hango wasu jiga-jigan sojoji wanda tamkar yakin duniya na uku za'a tafi, yanayin tsarin ginin ya yi matuƙar kyau sosai, bene ne hawa uku.
Horn yai, a take wasu shirga-shirgan sojiji suka wangale katafaren gate ɗin, ba ɓata lokaci ya kutsa da su ciki. A katafaren parking lot na gidan ya faka motar, yadda kuka san gabaɗaya sojojin barrack ɗin a gidan suke, gidan cike yake da ƙosassun sojoji, ta ko'ina suna shawagi.
Yana kashe motar ya ɗauki daddumarsa ya fito da sauri, bai sake bi ta kansu ba ya nufi gate, yana zuwa ya kame ya sarawa sojijin dake bakin gate ɗin, a matsayinsa na matashin soja kunga dole ya girmamasu tin da yanzu manya suke a kansa, sai sun kammala horo ya ga da irin result da zai fito, a nan ne zai san ya fi su matsayi ko sun fishi.
Ɗan jinjina mashi kai suka yi, daga nan ya fice rike da key ɗin motar a hannunsa, kai tsaye ya wuce office na GAT dan ya mayar mashi da key ɗin motar kamar yadda ya bashi.
Su Arya kuwa, yana kashe motar ya fito V tai saurin fitowa ita ma, bayansa ta bi da kallo tana yaba jiji da kai irin na guy ɗin nan, har sai da taga ya fice daga gidan, sannan ta juya, tana juyowa suka haɗa ido da Angelina da Manassa dake tsaye suna kallonsa suma, Arya ce kawai bata fito ba, saboda ya ɓata mata rai.
Da sauri V ta wuce ciki tana murmushi, a ranta tana ayyana yadda zata sace zuciyar guy ɗin, sai kuma ta turo baki da ta tina baya kallon mutane ma. Angelina ce ta rufawa V baya cike da tinanin haɗuwarsa suka nufi ciki, ita kuma Manassa ta jawo hannun Arya tana tausanta, da kyar ta yarda suka fita, kai tsaye wani katafaren down parlo suka shiga, komai na cikin parlon ligh ash ne mai ɗan banzan kyau, ya ji komai na more rayuwa, ga wani fitinannen kamshi da yake tashi mai tsananin kwantar da hankali.
Babu kowa a parlo, dan haka sama suka haye, wani katon parlo ne a saman mai ɗauke da manyan ɗakuna guda huɗu, ɗaya na daddynsu, ɗaya na su, biyun ɗaya na masu aikin dake kula da su, komai dare suka buƙaci abu masu aiki zasu kawo masu, shiyasa suke a kusa da su, ɗayan ɗakin kuma babu kowa, in case dan baki aka yi shi.
Kai tsaye room ɗinsu suka shiga. Ya ilahi, room na ƴan'matan nan ya yi bala'in haɗuwa, komai 4 ne a cikin ɗakin, yana da girma sosai, beds ɗinsu guda huɗu ne, biyu ta left side na ɗakin, biyu ta right, a tsakiyar kuma glass door na balcony, daga side na left door na toilet yake, right side door na closet ɗinsu yake, komai na cikin room ɗinsu sky blue ne, ko'ina tsab-tsab, da alama suna da bala'in tsabta sosai, ga wani kamshi mai daɗi da yake tashi.
Left side Arya ta nufa, a saman bed dake shinfiɗe da tsadadden bedsheet na alfarma pink color ta zauna, hannayenta biyu ta sanya ta dafa kumatunta tana wani irin huci ƙasa-ƙasa, a ƙasan zuciyarta ita kanta yaba kyan Leo take yi, amma ji da kai yasa taki yardan shi mai kyau ne. A gefenta Manassa ta zauna tare da dafa shoulder ɗinta, a natse ta ce. "Sorry bloody, I feel your pain".
Angelina dake ƙoƙarin karisawa right side ne ta ce. "It hot me too". Ta karisa magana tare da zama a gefen bed ɗinta. Watau da Arya da Manassa sun fi shiri, su ne a left side, da Angelina da V su kuma beds ɗinsu a right, su sun fi shiri, suna da saukin kai sosai.
Wani irin nisawa Arya tai tare da miƙewa tsaye, cikin fushi ta ce. "Arya! Me Arya? This stupid zai walaƙanta? Wlh sai ya yi danasanin sanina, in dai boy ɗin daddy ne, sai na gigita rayuwansa, sai ya yi kuka, nasa ya durkusa ƙasa a gabana ya ban hakuru". Ta dakata tana huci, sai kuma ta sake cewa. "Calm down Arya, calm down babyn daddynta"...... Watau ita da kanta ma rarrashin kanta take yi, kai Arya duniya. Da gudu su V suka yo kanta, rurrungumeta suka yi suna faɗin calm down, calm down.
Sun ɗan jima a haka kafin su saki juna, a natse suka hau cire uniform ɗin nasu, babu kunyar juna suka cire kaya a gaban juna, ya rage daga su sai pant, kuma breast ɗinsu ya fara girma da zama na matasan ƴan'mata, but they don't care suka tsaya ba riga a gaban juna. Da yake V bata kaisu tsawo, sun ɗan fita kaɗan, sai breast ɗinta ya fi nasu cika, ta ɗan fisu ƙiba, harta mazaunanta ya fi nasu cika, ga shape kam kamar su suka bawa kansu, cikinsu tamkar babu hanji a ciki.
Dikkansu suka ɗauki white bathrobe suka sanya a jikinsu. A daidai lokacin wasu matasan ƴan'mata su biyu suka shigo room ɗin bakinsu a ɗauke da excuse.
V ce kawai ta amsa masu, karisowa ciki ƴan'matan suka yi suka hau tattare uniform da su V ɗin suka cire, kai tsaye laundry suka kaisu, sannan suka sake gyare ɗakin fes kafin su shiga wajen closet ɗinsu.
Su kuma one by one suka yi wanka, dik wacce ta fito a tsakar ɗaki take ajiye bathrobe ɗin ta hau shirinta, waɗan nan ƴan'mata suke tattare komai.
Cikin wasu gajerun jeans trousers suka shirya, sai ƴan rigunar da suka tsaya masu a waist ɗinsu launin white, komai nasu iri ɗaya, fitowa suka yi, Angelina ta gyarawa V gashin kanta, ta shafa mata man kamfanin STARS LADIES HAIR CREAM, kayan gyaran gashinsu mugun gyara gashi yake yi, yana ƙara mashi tsawo da sheƙi, STARS LADIES LUSH zaɓin dik wani ƙasaitacce ko hamshaƙiyar mace mai ji da kanta! Dan ɗan karen tsada ne da shi, kuma kun san abu mai kyau dole ya yi kuɗi ai.
Tana kan gyara mata gashin kan nata ne V ta ɗauki robar lotion guda ɗaya, a fili ta ce. "I wish ko sau ɗaya ne zan gansa, Angelina I really like this guy, mura ne"....... Siririn tsaki Angelina ta ja. "V ban san yaushe zaki daina wannan dream ɗin naki ba"....... Shiru ta yi dan babu wanda zai iya fahimtar zuciyarta sai ita kaɗaita. Shiru ɗakin ya ɗan yi na ƴan mintuna suna karisa shiryawa.
Bayan sun kammala gyara gashinsu da shafa mayukansu, sai suka ɗaure gashin kamar yadda suka saba, su rabashi kashi biyu, su ɗaure ta sama su kuma kitsa jelar, sai ƙarshen bakin jelar ma su ɗaure da rebon kalar kayansu kafin su watso jelar ta saman shoulders ɗinsu, dikkansu kuma suna da wasu gajerun gashi ta gaban goshi wanda yake kwance masu luff tamkar an kifa hula har zuwa daidai kusa da idanunsu, dik bayan sati suna rage mashi tsawo dan kada ya yi tsawo sosai ya kamo na baya, musamman da suke amfani da STARS LADIES HAIR SHAMPOO AND HAIR CREAM, a take gashinsu yake ƙara tsawo over, dik da kowani sati suna rage tsawon gashin nasu, amma a haka yanzu ya kusa kai waist ɗinsu tsawonsa.
Sun yi bala'in kyau cikin shigarsu, kamar ka sacesu ka gudu, sai tashin kamshi suke yi, ƙasa suka sauƙo a natse, dining room ɗinsu suka nufa. Already an shirya masu komai dan yin lunch. Zazzaunawa suka yi a saman chairs, dikkansu a tare suka fito da chain dake wuyansu, suka rufe idanu dan yin addu'a, bayan sun kammala suka ɗan manna chain ɗin a gaban goshinsu kafin su miƙa hannu suka ja plates ɗinsu da already aka yi saving ɗinsu. Kowa ya ja plate ɗinsa ban da Arya da tai shiru tamkar mai tinanin wani abin.
Angelina ce ta katse mata shirun da cewa. "Bloody Is there any problem?". Wani iska mai zafi ta furzar daga bakinta kafin ta amsa da. "Angelina, this guy made me feel ashamed, I will never forgive him, I will teach him a lesson, he will know that he touched Arya, the first daughter of GAT".
Da sauri dik suka miƙe suka yi kanta, rurrugumota suka yi, suka haɗe baki wajen tausanta, dakyar suka samu ta sauƙo ta fara cin abinci. Cikin nishaɗi game da class suka ci suka ƙoshi kafin su miƙe su koma sama. Suna shig room ɗinsu kowacce ta fito da haɗaɗɗen laptop ɗinta mai shegen kyau, sannan kowacce ta haye saman bed ɗinta, Arya ta shiga practical a kan aikinsu, V ta shiga karance-karance labaran soyayya abinta, dan ita mayyar soyayya ce.
Dr Manassa kuma ta makale Arya wai tana son koyan aikinsu, Arya na koya mata, ita ma kuma tana koyawa Arya ɗin irin nasu aikin.
Kowace ta natsa cikin abin da take yi sun maida hankulan su gabaɗaya kan laptop dinsu. Can V tayi yar kara mai cike da nishaɗi tana fadin. "Arya come and see, I tried something kuma da alama zan yi nasara................... Mayun computer ba!
Da sauri suka ɗago da kallonsu a kanta, Angelina ce ta fara saukowa kasan gadonta da gudu ta nufi gadon V. Tana zuwa ta haye tana faɗin. "Me kika samo mana........". Bata iya karasa maganar ba ta dakata cak a lokacin da idanunta suka sauka akan laptop dake gaban V. Zazzaro ido sosai tayi cike da mamaki ta ce. "V what am I seeing? Wannan ba hukumar su daddy bane? Akansu zaki fara aiki? Zaki musu kutse cikin kundinsu! Shi zaki datsa? meyasa to? Baki da hankali ko? Bari idan manyan jami'ai suka kamo ki fa kinsan hukuncin ki ko? Tin baki je koina ba kin fara datsa kundin su daddy? To me zaki yi a cikin da ki ka shiga?". Cike da tashin hankali da ruɗu ta faɗi waɗannan maganganu. Hakan ya sa su Arya sukai gaggawar dirowa kasa daga saman gadonsu, gadonta suka haye su ma.
Kowannensu burin shi kawai yaga me ta aikata, yarinyan akwai ƙwaƙwalwa na faɗa muku, akwai baiwa ne, dik cikinsu ita da Arya sun fi su kaifin kwakwalwar sosai, sauran ma ƴan baiwa ne, amma na Arya da V daban ne.
Zazzaro ido Angelina da Manassa suka yi, ita kuwa Arya cikin gaggawa ta kai hannu kan laptop ɗin, da sauri ta rufewa bibiyar V kafin ta ce. "You're not serious at all, kin bar komai a buɗe, bari GI (General na sashin secret service ɗin, shi ne GI, General Ibrahim) bari ya ankara da an kutsa cikin hukumarsu su bibiyeki zaki gane ne!". Ta ɗan dakata tana harararta kafin kuma ta sake cewa. "Me kika shiga yi a kundinsu?".
Turo baki ta ɗan yi, wai bata ji daɗi ba an mata faɗa, kuma bata ji daɗi ba da Arya ta gyara mata, so take ace ta kware a kan komai ba sai an taimaka mata ba. A shagwaɓe sosai ta ce. "Guy ɗin ɗazun fa zan bincika, ina son sanin wanene shi? A wani sashi da wace tawaga yake? And Ina son pics ɗinsa".
Wani irin faɗuwar gaba Arya ta ji jin V ta ambaci Leo, Amma ta daure da cewa. "Uhm ba wani tsiya bane, for sure karan farautan daddy ne!".
V dake aikin kara kutsawa cikin kundin ne ta amsa da. "Impossible Arya, this guy doesn't looks like Daddy's boys, I think wani guru ne, but let me see"............. Zuba mata idanu dik suka yi, ta cigaba da kutse...... Silent for like 3 mins ne ya biyo baya, lokaci guda V ta fasa kara mai cike da murna tare da cewa. "Yes! I got it, I am Vanisha General Thomas, the daughter of her dad, guys clap for me".
Tafa mata ɗin suka ɗan yi kafin Arya ta ce. "Who's he?". Ta faɗa cike da matsuwar son jin wanene shi!..... Jawo laptop ɗin da kyau V ta yi, a bayyane ta fara karanta masu waye shi. "NIRASH MUHAMMAD HAIZA'AN, sabbin jami'an dake kan horo, number ɗauka 1". Ta ɗan dakata tare da ɗagowa ta kalli Arya.
Manassa da Angelina kam sun mutu a kallon pic na Leo dake gaban screen na V, dan ta fito da hotonsa da dik wasu bayanansa tana dubawa, sai suka kura mashi ido, dikkansu sai santin kyansa suke yi, musamman hajiya Arya, gabaɗaya zuciyarta ta susuce, tin ɗazun dauriya ce kawai take yi, amma ko ido ta rufe fuskan Leo a kusa da ita take gani, musamman yadda ya ɗago idanu ɗazun ya kalleta, ya ilahil alamina, ya tashi kan ƴan'matan GAT.
"Ainahinsa ba ɗan nan bane, ɗan Us ne, New York City, yana da mark a sunansa, which means jami'i ne na musamman a tawagarsu! But mark ɗin ma da alama jiya ko yau aka sanya mashi, in zan canka daidai daddy yana gwada shi ne saboda yana tinanin ɗan baiwa ne!". A cewar V kenan, ta karisa koro masu bayanai a kansa, cike kuma da nata hasashen da kwakwalwarta ya bata.
Manassa ce ta ce. "Meyasa kika ce daddy na gwada shi?"...... V dake ƙoƙarin ciro hoton Leo ne ta amsa da. "Saboda ya je ɗaukarmu mana, kin taɓa ganin daddy ya tura wani ya je ɗaukarmu ne? For sure dad yana gwada guy ɗin nan ne".
Arya dai ta yi shiru, ita kaɗai tasan me ainahin abin dake cikin zuciyarta, amma ta ji takaicin da ya kasance Leo ba boy ɗin daddynta bane, bata so haka ba, yanzu Leo yana kan horo ne, kila ya fito da result mai girma da ba z kaskanta a gaban daddynta bama bare har ta walaƙanta shi, takan iya yiwuwa ma ya fito a sashe na musamman.
Ganin ta yi shiru ne yasa suka fara tambayarta meyake faruwa?. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu komai. V ta ce. "Bloody I wish mu samu number guy ɗin nan, da na mana kutse cikin wayansa mu sato hotunansa"...... Da sauri Angelina ta amsa da. "Let daddy comeback, zamu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 95