Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai da ya yi zaman sauraren abin da suke faɗe har karshe, a wasu hiran nasu ne ma suka sanya ya ji gabaɗaya feeling ya taso mashi, musamman yadda Seraph take cewa amma kuma ai idan suka yi aure shi mijinsu zai taɓa kuma ba zai zube ba, Rimsha ta ce ai Ammie ta ce mata hannun miji malaiku sun saka mashi albarka. Jinjina kai Aryan ya yi a ransa yana faɗin lallai ma Ammie, ko ba malaiku sun saka mashi albarka ba. Gabaɗaya ya shiga wani irin mood, ya kwanta shiru kamar mai saureran ƙira'a, yana jin gabansa har wani zogi take mashi saboda mood ɗin da ya shiga. Ga shi kuma a tsari da dokar IRON FIST babu soyayya kuma babu aure, su sun sayar da rayukansu ne kawai dan gyaran duniya, baku ga shiyasa suke hora kannensu ta yadda ko sun mutu zasu karisa abin da suka fara ba? Shiyasa basa kusantar in da mata suke, sun keɓe kansu, kuma sun cusawa kannensu tsanar mata, dan ga kudurinsu a kan kannen nasu, shiyasa zaku ga Leo baya ko ɗaga ido ya kalli mace, already Yayansa ya cusa mashi ra'ayin cewa mata rauni ne kuma su ɗin kashe buri ne, idan ka haɗa hanya da su dik wani burinka sai sun lalata maka, shiyasa baya yarda haɗa hanya da mace, shiyasa da Ummien Zaynish ta zo gaishesa bai amsa ba, aiki da sadaukarwa kawai yayansa ya koya mashi, shi Leo a yanzu ba'a bakin komai yake ɗaukar ransa ba, ko a yanzu mutuwa ta zo a shirye yake. Wannan dalilin yasa Lion ya ce kada a kawo masu Seraph gida, dan ya ce mace ko ba matarka ko kanwarka ba, ko ma wacece mace mace ce kuma rauni ce ga namiji, dan haka ko inuwar mace baya son ganin a kusa da su, tsabar sun sanya abin a ransa ma wlh basa feeling a kan mace, kamar wasu duwatsu, kuma hakan ya samo asali ne saboda basa haɗa hanya da matan, ku kun san da suna haɗa hanya da mata dan ƙaniyarsu dole su yi feeling, ba ga shi yanzu Aryan daga jin hiransu Seraph ya fara jin shauki ba, abin da Lion yake gudu kenan. Kuma 33 years suke da shi yanzu a duniya, amma kullum burinsu su tsabtace duniya daga ƙazanta, sun shiryawa mutuwa a koda yaushe ta zo, bayan wannan basu da wani buƙata!. E to da matsala. IRON FIST basa soyayya kuma sun haramtawa kansu aure ko haɗa hanya da mace, MUHAMMAD KHAIZA'ANS HOUSE kuma an haramta soyayya sai auren haɗi, kai watau ana badaƙala a littafin nan. (Uhm ina ma Abba ya samo wata ƴar duma-duma kawai ya kai sadaki a aurawa Champion, da na fi kowa murna ɗan banza ba, ALLAHN Rimsha ya kamashi ta hanyar aura mashi mace mummuna, ƙazama, mara kunya kuma mara jin magana mu ga ya zai yi, Abba kuma ya ce in bai zauna da ita har suka haifi yara ba zai tsine mashi.......) Bai san time da Lion ya hauro saman bed ɗin ba sai ji ya yi Lion ɗin yasa hannu zai cire Bluetooth dake kunnensa, ƴar zabura ya yi tare da janyewa baya yana jefawa Lion ɗin harara. Guru ne ya ce. "Guys is time for pray". Tin bai gama rufe baki ba suka miƙe, Aryan sai faman kokarin danne abar yake yi, sai satar kallon Lion and guru yake yi, shi ya rigaru faɗawa cikin toilet. Ganin babu lokaci sosai yasa suka faɗa toilet na sauran ɗaku nan gidan. After some minutes suka fito dikkansu a sanya da arabian throbe mai shegen kyau farare kal. Daidai lokacin shi ma Leo ya fito suka nufi masallacin cikin C-P ɗin dan gabatar da sallar magrib. -----------------------🔥 NIGERIA. Diran magrib su Ummie suka yi a Naija, basu ɓata lokaci wajen kama hanyar gida ba, Zaysh sanye yake da uniform ɗinsa wanda yasa da suka isa unguwar su Ummie kowa ya ja da baya ya bata hanya, kun san kwarjinin soja karshe ne. Kai tsaye gidanta suka nufa, a rufe ta isko gidan nasu, hannu tasa ta fara knocking, amma shiru ba'a zo an buɗe mata ba, haka ta dinga bugawa. Cike da Mama Zaysh ya ce. "Ummie lafiya? Ko dai babu kowa a gidan ne?". Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Akwai, haka take, sai ayi ta bugawa tana ciki sai lokacin da ta yi ra'ayi zata fito ta buɗe"........ Kamar zai sake yin magana sai kuma ya ɗan ja baya ya yi shiru yana bin unguwar da kallo, ita kuma ta cigaba da buɗewa. Sai da suka shari good 20 mins a wannan waje a tsaye kafin amarya ta zo ta fara buɗe kofar tana sababin uban waye mai buga mata gida da daddaren nan. Tana buɗewa ta ga Ummie, wani irin dogon tsaki ta ja tare da cewa. "Awwa juya kece dama? Sai yau aka dawo daga yawon bin mazan kenan? To fatan dai a wannan tafiya kin samo koda ɓatar wata ne"......... Zaynish dake bayan Ummie ta gefe ne ya ɗan matsa kaɗan dan ya ji kamar kunnuwansa suna mashi karya ne! Bin maza kuma? Ya tambayi zuciyansa. "Bani hanya in wuce cikin gidana". Ummie ta faɗa a ɗan taƙaice..... "Da an yi magana sai ki fara gadara da wannan gida, bayan ko kwai baki ajiye a gidan ba, ke fa yanzu ko rabuwa kuka yi mayafinki kawai zaki ɗauka ki fita, ba ɗah ba jika, amma a haka kike ƙoƙarin ɗagawa uwar magaji murya? Mai ɗauke da cikin ɗah na farko a gidan Yaya Faisal, magajin ubansa kuma magajin wannan gida da kike gadara da shi, ni kina bani mamaki ta yadda kika yi sake dik mazan da kike bi baki dage ɗaya ya maki ciki dan ki wuce goro ba.........". Ai bata iya karisar da maganar ba sakamakon bayyanar Zaysh da ta gani a gabanta, da yake kofar gidan akwai bulb ta koina, ga wutar lantarki, haske ta ko'ina. Wani irin ihu amarya ta kurma tare da cewa. "Na shiga uku jama'a, ta kira mun sojoji sun zo su kasheni!!". Ta faɗa tare da kamo addu'ar da bata san me take karantawa ba, da gudu ta juya ta yi cikin gida tana kara ihu. Gabaɗaya fuskan Zaysh ya canza, kun san wani lokaci sojojin nan ba man kai suka cika ba, musamman sabbin yayewa da a lokacin jininsu a tafashe yake, sun fito daga horo babu tausayi ba imani, a wanna lokaci da kansu suke neman balai ya zo su buga da shi, suna jinsu tamkar wasu zakuna. Haba ai bayan amarya ya bi cikin fushi, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta, da sauri Ummie ta bi bayansa dan ta rikesa kada ya daki matar mutum, wannan ma idan ya ce zai daketa a yadda ya fusatan nan yaushe zata yi saura. Ihun amarya yasa jama'a suka fara taruwa a kofar gidan, rufo kofar gidan Ummie ta yi, har tana haɗawa da ɗan gudunta ta bi bayansa. Ai tana shiga ta tsaya turus tana kallon yadda Zaysh yake dukan kofar ɗakin amarya, dan ya shigo ne ya sameta a tsakar gida, a tinaninta ba zai shigo ba, tana ganinsa ta watsa da gudu sai cikin ɗaki, shi kuwa ya bi bayanta, yau sai ta faɗa mashi a yaushe ƴar uwansa take bin maza da ta ambata, cikin fushi ya koma baya ya take kofar tata da karfin gaske har sai da ta jinjiga tamkar zata ɓalle, ya koma baya zai sake duka na biyu ne Ummie ta shigo. Da gudu ta yi kansa tana ƙoƙarin cewa ya dakata, sai dai ina, kafin ta iso ya sake kaiwa kofar duka a karo na biyu wanda ya sanya kofar rugujewa ya faɗa ta ciki. Gabaɗaya ya canza tamkar ba shi ba, a fusace ya dimfari cikin ɗakin, yana taku irin na mazan gaske....... E kam yau akwai rikici a gidan comrade Faisal........😂 STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP STEP 1🔥 2025-11-19.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________16 & 17 Ihu amarya ta fara kurmawa, ta gudu cikin bedroom, cikin zafa ya bita ciki, tamkar babu hankali a kansa, ko da yake dama a irin wannan lokaci ba man kai suka cika ba na faɗa maku, dan a lokacin su kaɗai suka san ya suke jinsu, bare sun karɓi alluran karshe na fita horo, amarya tana tsakiyar dajin dake kewaye da zakuna, dan kuwa a kanta wannan allura zai fara aiki, kunga kuwa ita ai ta bar tarihi. Duka ɗaya yai wa kofar bedroom ɗin nata ya ruguje, dan shi irin kofar wood ɗin nan ne. Ciki ya shiga, saman gado ta haye tana ihu. Aikuwa taka saman gadon ya yi da takalmarsa, tana ƙoƙarin gudu ya damki gashin kanta, dama ɗankwalinta ya cire tin da ta gudo ta baro parlo. Tsabar razana da tashin hankali fitsari ta saki a zaninta a wajen. Ina ai bai san tana yi ba, waje ya jata da gashin kan nata, yana fitowa ya daddage ya buga mata kai da jikin bango kusa da ɗakin nata. Wani irin azababben ihun da ta zunduma sai da gabaɗaya unguwar ta amsa. Ummie fa ja da baya ta yi, dan wlh ta ji tsoron tinkararsa, ta ce ba shi bane, an canza mata shi, bata tashi sanin haɗarin soja ba sai yau, kun san shi fa soja ko kakinsa firgita zuciya yake yi bare shi da yake horon AZURE kuma sabon passing out daga bar two bama bar one ba, ai amarya sai sorry. Da gudu Ummie ta nufi kofar gida dan ta buɗe jama'a su kawo masu ɗauki, ita da kanin nata yau tsoron tinkararsa take yi. Tana buɗe kofar ta ga jama'a a tsaitsaye a kofar gidan, da sauri ta ce. "Jamilu ku zo ku taimaka mun kada ya kashe amarya!". Muryanta na rawa ta yiwa matasan unguwar magana. Da gudu suka faɗo cikin gidan, daidai lokacin Zaynish ya kwashe kafafun amarya ta zube ƙasa kamar kayan wanki, kun san sojoji sun kware wajen iya kwashe kafafun mutane su zubar dasu a ƙasa. Dik matashin da ya shigo da gudu yana ganin kalar uniform ɗin sai ya ja wata uwar birki, ba ɗan sanda ba ne bare a iya zuwa a sasanta, shi wannan daga nesa idan aka ga kakin kawai canza hanya ake yi in dai akwai tsama a tsakani. Matasa sun fi goma babu wanda ya iya karisawa wajen ya rikesa, wasu ma ai a miliyan suka juya da gudu suka bar gidan. Makwabta mata da sun shigo sun ga mai dukan amarya zasu juya da gudu. Hankalin Ummie ya yi mugun tashi, ga shi ko kaɗan bata da zarrar iya zuwa ta kama shi, kuma ita kaɗai ce in ta kama shi kun san ba zai kai mata duka ba, zai daure, amma ina ta tsorata. Wannan shegiyar takalmar tasu yasa ya fara ball da amarya, daga karshe ya kwance wannan shagiyar tattauran belt ɗin nasu, dukanta ya fara yi tamkar wanda aka saukarwa wahayin duka. Wani irin gigita Ummie ta yi, tsoronta kada ya yi kisan kai. Da sauri ta ce. "Jamilu dan ALLAH ku kama mun shi". Wanda aka kira da Jamilu ne ya ce. "Aunty Ummie kina gani soja ne fa ba police ba, gaskiya ni ban shirya mutuwa ba"...... Da sauri na jefensa ya ce. "Kai ma kenan da kake matsayin abokin ɗan banga, mu kuma mu ce me? Ai kawai sai dai mu ce ALLAH ya jikan amarya idan ta mutu, dama ta ishemu a layin nan". Kuka hawaye bibbiyu Ummie take yi, da kyar ta iya cewa. "Ku kama shi ba zai yi maku komai ba, kanina ne, dan ALLAH ku dakatar da shi"...... Ai ina dik cikinsu babu wanda ya motsa bare su yi yunkurin kama shi...... Dukan ALLAH tsine uwar mai karya Zaynish ya yi wa amarya, farfashe mata jiki ta ko'ina , har sai da yaga ta daina motsi, sannan ne ya dakata yana cigaba da huci. A fusace ya juyo da kallonsa a kan Ummie, haba ai a miliyan su Jamilu suka yanka kofar gida, sun ga zaki ya juyo, ka ji gudun karti wasu ta saman gini suka dira waje. Ita kanta Ummie kaɗan ya hana ta saki fitsari a in da take tsaye, ba dan tasan ciki ɗaya suka kwanta ba, ko mai wuya ba zai cutar da ita ba da wlh babu abin da zai tsayar da ita itama, tuni zata gudu, amma ta daure ta tsaya. Dimfarota ya yi tamkar wani mayinwacin zaki, a gabanta ya tsaya, with harsh voice ya ce. "Dama irin zaman da kike yi a gidan nan kenan? Meyasa baki sanar dani ba? Ina Faisal ɗin yake? Sai ya faɗa mun idan jaka aka bashi ko ance mashi baki da gata ne!". Tashin sense, yau babu batun Yaya Faisal, Faisal kai tsaye, ba shakka da comrade Faisal na nan yau da shi ma ya gane ALLAH da girma yake. Wani irin kerma da jikinta yake yi ne yasa ta gagara iya rike kanta, kasa ta durkushe tana cigaba da kallonsa har cikin ido, ta gagara bashi amsa. Tsawa ya daka mata da karfi wajen cewa. "Wacece wannan? Kuma ina Faisal ɗin na ce? Sai sun faɗa mun a gidan uban waye kika bi maza? Idan basu faɗa mun sun bani shaida ba billahil lazi sai na lahira ya fisu jin daɗi". Hannu bibbiyu tasa ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatsewa, still kallonsa take yi ta gagara yin magana, allurar tasa ta motsa, baya iya fahimtar a wani hali take ciki bare ya sassauta mata murya, sai ma tsawa da ya sake daka mata tamkar zai kai mata duka, daga karshe ma yasa hannu ya miƙar da ita tsaye, yana cigaba da huci ya ce ta lissafa mashi masu ce mata tana bin baza, da alama wannan kalma ta fi komai ƙona mashi rai. Har lokacin baiwar ALLAH ta gagara yin magana. Jama'a sun cika kofar gidan dam, amma kowa yana tsoron shigowa, wasu matasa ma aka samu suka kira ƴan sanda. Mota biyu ƴan sanda suka zo, take jiniya ya karaɗe umguwar, zaku ce yaki ake yi, jama'a an yi cirko-cirko. Ƴan sanda biyar ne suka diro ƙasa daga bayan motocinsu, da farko sun tsaya a waje, sai su Jamilu suka faɗa masu ai kisan kai za'ayi a cikin gidan, hakan yasa suka danno kai ciki da gudun gaske, a lokacin shi kuma yana tsaye gaban Ummie ya titseyeta kan lallai ta faɗi masu mata ƙazafin zina, yau sai sun bashi hujja ko kuma dik su ci ubansu ne, ba zai ɗauki nonsense ba, yana matsayin position 3 a bar 2 ɗin za'a kawowa rainin wayau? Tab!. Da gudu ƴan sandan suka kewayesa suna faɗin ya natsu ko su harbesa har da ɗaga bindigu su nunnuna shi. Nan fa su Jamilu suka dawo cikin gidan dan ganin gulma, da a basu kabari gara su bayar. Ai a miliyan Ummie ta ware, sai kuma ta fara ƙoƙarin kare Zaynish ɗin, muryanta na rawa a fara ƙoƙarin cewa ƴan sandan su yi hakuri su je rigimace ta cikin gida. Bata kai ga yin magana bama wani ɗan sanda ya ce. "Madam bai yi maki komai ba ko?"........ Da kyar ta iya ƙoƙarin buɗe baki zata yi magana, amma ta gagara saboda rawar da jikinta yake yi. Shi kuwa wani irin juyowa ya yi tamkar bujumin zaki, dikka ƴan sandan sai da gabansu ya faɗi, baya suka ɗan ja suna faɗin kada ya motsa. Kallon tsab ya yi masu kafin ya ce. "Your gun down!". A sigar bada umarni ya yi maganar, dan ya ga dik ya fi ƴan sandan rank, dikkansu constables ne, ko soja dake bar one ya fisu rank bare shi da yake na uku a bar 2, ai ya wuci waɗan nan. Jin yadda ya yi magana cikin bada umarni in a harsh way ne yasa suka ɗan ja baya, sun sha jinin jikinsu, slowly suka yi ƙasa da bindigunsu kamar yadda ya umarta. Ganin basu yi gardama ba sun yi biyayya ne yasa ya ɗan sauko ya yi masu bayanin waye shi, da sun yi gardama lallai da sun ɗanɗani karfin dukan hannun horon Azure yau, dan wlh yadda yake jin kansa tsab zai iya dukan zaratan maza 20 ko sama da haka, shi fa abokin balai ma yake nema yanzu ko zai sosa hannunsa dake mashi ƙaiƙayi, wai baku ga Vash a gida yana can yana ta faɗa da neman masifa bane? Ai haka suke bayan horo, dik su rikiɗe su zama wasu zakuna. Ba karamin girgiza ƴan sandan suka yi ba jin waye shi, sannan ya ce masu zasu iya tafiya babu ruwansu da case ɗin nan. Sai a lokacin Ummie ta ce. "Ku yi hakuri kanina ne, faɗar gida ne, ba wani abin zai mun ba". Tana magana dai idanunta a kansa sosai. Ganin tsananin kamanninsu na buzayen nan ne yasa suka yarda ƙaninta ne, dan dik wanda ya ganta ya gansa, dan ma dai shi wannan gashin nasu ma buzaye ya cika mashi kai sosai, yasa fuskansa ta ɗan rame, amma dik da hakan kamanninsu sosai. Da sauri ƴan sandan suka karɓi umarni tin da sama da su yake, da gudu suka fice a gidan, sam basu lura da an sumar da amarya ba, su a zatonsu iya Ummie ce kawai. Ai suna fita su Jamilu suka bi bayansu, dan tsoron kada Zaynish ya bi ta kansu. Suna fita Ummie ta yi ta mazan kama hannun Zaysh ɗin tin da taga ya ɗan sauƙo, shi ma sai a lokacin alluran ta ɗan sauƙa ya iya ganin firgicin dake kan fuskanta, ɗan rungomo shoulder ɗinta ya yi tare da cewa. "Sorry Ummie, wannan firgita dik na mecece?". Ai da sauri ta rumgumesa ganin dama ya samu ya ɗan sauƙo, sabbin hawaye ne suka fara wanke mata fuska, da kyar ta iya cewa ya je ɗaki dan ALLAH ya basu dama ta kira jama'a a kai amarya asibiti, zai yi mata gardama ta ce. "Zaynish ALLAH idan ka mun gardama zuciyata zata iya bugawa, ka je ɗaki dan ALLAH". Ganin yadda ta firgita sosai ne yasa ya hakura ya wuce cikin room ɗinsa, da sauri ta ɗauko wayarta ta kunna, number Faisal ɗin ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka, da yake bai san me yakefaruwa ba sai ya ce. "My ƴar aljanna yanzu nike son kiranki in ji kun iso ne, dik kewarki ta dameni". Da kyar ya iya danne kukanta, ta harhaɗo natsuwa tare da girmamawa a garesa kafin ta fara faɗa mashi abin dake faruwa, bata ɓoye mashi komai ba. Fusata ya yi, ya fara yi mata faɗa da cewa dama amarya na jifarta da kalmar mazinaciya shi ne bata taɓa faɗa mashi ba? Meyasa dik rashin kunyar da amarya take yi mata take ɓoyewa bata faɗa mashi?. Shiru ta yi tana sauraron faɗar tasa har ya kammala, sannan ne ta ce. "Ka yi hakuri, ban son haɗaka faɗa da matarka ce, amma ka yafe mun mijina"..... Shiru shi ma ya ɗan yi kafin ya ce. "Zaynish ya mun daidai, dan ko ni ne hukuncin da zan yi mata kenan, na sha faɗa mata tai maki biyayya, dan ita ƙaƙaba mun ita aka yi, ke kuma ni na ganki na ce ina so, kuna da bambanci, idan tana son zaman lafiya dani ta girmamaki, watau shi ne idan na fita take maki abin da take so ko? To ku kyaleta a wajen babu wani asibiti da za'a kaita!". Cikin faɗa da iya gaskiyansa yake maganar. Ummie baiwar ALLAH ba zata iya ɗauke kai ba'a kai amarya asibiti ba, da sauri ta hau rokonsa kan ya yi hakuri a kaita. Da kyar ya yarda, sannan ya ce bari ya kira kannensa da kannenta su zo su ɗauketa. Cike da mamaki ta ce. "Kai ka yi nisa ne da ba zaka zo ka kaita ba?"..... A natse ya ce. "Bana garin ne, na je tsakanin Adamawa da Taraba". ...... Zazzaro ido ta yi kafin ta ce. "Ma ka je yi can?". "Wani abokina ne ya ce mu je haƙar gold a wajen, ya ce ana samun alkhairi sosai a wajen, akwai sabon wajen da aka gano yake da gold a wajen, to shi ne na ce bari in jarraba tin da aiki ya gagara samuwa, ki tayani da addu'a ƴar aljanna, ki mun addu'a in yi farar tafiya"..... Dik da bata so tafiyar ba dan tasan yadda ake mutuwa a wajen harkar gold ga wahala, amma hakan bai hana ta daure ta zuba mashi addu'a sosai ba, ya ji daɗi ya dinga amsawa da amin, sai da ya zuba mata kalaman kauna sosai, sannan suka yi sallama yana faɗa mata zai turo kannen amarya yanzu, kuma yana umartanta da ta shige ɗaki yanzu, sannan ta gaida mashi da kaninsa Zaynish ta kuma bashi hakuri da abin da ya faru. Da okey ta amsa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga haka suka yi sallama ya katse kiran, gagara komawa ɗaki ta yi, haka ta samu fili a wajen ta zauna har lokacin da ƴan uwan amarya suka zo suka ɗauketa, basu yi wa kowa magana ba, dan already Faisal ya faɗa masu cewa akwai zaki jarumin jarumai a gidan, su kula su kuma haɗe malaman jikinsu waje guda, idan ba haka ba jikinsu ya faɗa masu ma, shiyasa basu yi magana da kowa ba suka ɗauketa suka fita, hegiya ta ji maza ta sume. Ita kuma Ummie da aka tafi da amarya sai ta bi bayan Zaysh izuwa ɗakinsa dake gidan, kuma yana ma da ɗaki a gidan uncle ɗinsa, kawai Ummie ta matsa mashi su sauƙa a gidanta da safe sai suje gidan uncle ɗin ne, baya son zama a gidanta yanzu da ya kara girma, a da dai lafiya lou ya zauna lokacin yana yaro. Zaune ta iskosa yana danna waya, ya sanya sim card ɗinsa ta nan gida Naija, da alama wani abin yake son yi. A kusa da shi ta zauna zata fara magana kenan taga yasa waya a kunne, cikin sanyin murya suka gaisa da uncle ɗin nasa, sannan ya faɗi mashi ya dawo, sun iso lafiya. Watau Zaysh ɗan halak ne na gasken-gaske, dik da halin da matar uncle ɗinsu ta jefasu a ciki hakan bai hana shi yana yabawa uncle ɗin nasa kuma yana kara gode mashi ba, and kome zai yi sai ya fara sanar mashi kafin ya yi, tamkar uba haka ya ɗaukesa dan yasan ba laifinsa bane, ba shi ya muzguna masu ba, matarsa ce ta yi komai. Bayan sun gama gaisawa da uncle sun yi sallama ne ya miƙe tsaye, da sauri Ummie ta rike hannunsa tare da cewa. "Ina zaka je?"....... A taƙaice ya amsa da. "Wanka". Sakesa ta yi tare da miƙewa tana faɗin ya zauna bari ta haɗa mashi ruwa. Da a'a ya amsa mata, ya kara da cewa ita da bata da lafiya, ta zauna shi bari ya haɗa da kansa tin da shi ai ba bakon gidan bane. Zama ta yi tana sauke numfashi a hankali-hankali, shi kuma ya fito ya ɗebi ruwa a bokiti ya wuce toilet dan ya yi wanka. -------------------------🔥 C-P. Basu dawo gidan ba sai da suka yi sallar ishai, sannan suka shigo. One by one suka tsala wanka, suka shirya cikin sleeping dress iri guda, sannan suka shiga ɗakin aikinsu. A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya kunna wani video na zanga-zanga da ake yi a ƙasar AVARIS, natsuwa dik suka yi suna kallon video mai tsawon mintuna 33, sai da suka gama kallo tsab sannan ya tsayar da video tare da cireta gabaɗaya. "What are you

Chapter 27 of 95