Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
face ɗinta, while ita ma shi take kallo, kurawa juna idanu sosai suka yi, gagara rike kanta ta yi har sai da ta kwantar da kanta a saman massive chest ɗinsa, ya matsa kusa da ita ne sosai, ga kamshinsa dake ratsa hancinta, ga shi kuma abin da zuciya ta jima take begen gani ne......... Ɗan motsa eyes ɗinsa ya yi ya bi gashin kanta da kallo, wani irin yanayi ya ji na jinta a jikinsa, sai ya ji kamar komai ya tsaya mashi cak. Ita kuma wani irin daɗin da ta ji har bata san time da ta sanya hannunta dikka biyu ta rikosa ta baya ba!. A daidai lokacin motocin suka gama wucewa, ɗan ja da baya ya yi kamar yana tsoronta haka. Da sauri ta ɗago kai suka haɗa ido, sai ta tsinci kanta da jin kunyansa, hakan yasa ta juya da gudu ta bar wajen. Bayanta ya bi da kallo yadda yake gudu har ta kurewa ganinsa, tana sane sarai da bata karɓi wayarta ba, dan dama na ce maku tarko ta ɗana mashi da wayar, ta yi alƙawarin sai sun yi ta haɗuwa da sunan karɓar wayar nan, in sun zo rabuwa ta tafi ta bar mashi wayar, a haka har ya fara sonta. Da yake ya zura wayar a aljihu ɗazun ne sai ya mance da ita, dan haka yana gani har ta gudu bai tina ya bata ba. Juyawa ya yi ya koma side ɗinsu. Sai da ya koma room ɗinsa, zai hau bed kenan ya ji wayar a aljihunsa, da sauri ya cirota, mamaki ne yakama shi na yadda aka yi ya shagala ya mance bai bata wayarta ba, to me ya shagalantar da shi? Ya tambayi kansa......Ni kam na amsa mashi da kyan V da iya maganarta, ga daɗin murya da shagwaɓa, shi ya mantar da kai me ka je yi wajenta!. Kurawa wayar idanu ya yi yana ta mamaki, a daidai lokacin Leo ya shigo room ɗin bakinsa a ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa. Ajiye wayar a gefen bed ya yi tare da kwanciya yana yi wa Leo barka da dawowa! Toilet Leo ya wuce ba tare da ya amsa shi ba!. Ita kuwa kai tsaye gate na gidansu ta nufa. Tana zuwa ta hau knocking ba wani tsoro, dan dama fitar ce mai wahala, shiga kam tasan maganin jami'an, ita ma ai jami'a ce, dik wata makirci ta iya. Ɗaya daga cikin sojojin wajen ne ya buɗe mata gate ɗin. Mamakin ganinta ne ya kamasu. Ɗaure fuska ta yi tare da sanya kai zata wuce ciki, da sauri sojan da ya buɗe mata ya bata hanya ta shigo. Ɗaya daga cikin sojojin ne ya ce. "From where at this time? Kuma a yaushe kika fita gidan nan?". Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Kana da business dani ne? Dik wanda ya sake mun magana a cikinku ya yi wa kansa, dan zama zan yi a nan har daddy ya dawo yasan na fita! Kun san sauran kuma idan yasan na fita, dan baku iya aikinku ba tin da zaku bari in fita ba tare da izininsa ba, ku rai nawa ne a wajen nan da har ni zan fita baku sani ba?". A dake ta faɗa. Shiru suka yi, dan kuwa ta ɗauresu da magana, sun kuwa san idan GAT yasan ta fita sun shiga uku, ace sojoji sama da goma ke gadin gidan har V ta fita babu wanda ya sani? Ai suka yi sake GAT ya ji wannan magana sun shiga tara ne ma, dan haka suna ji suna gani ta wuce cikin gida tana hararansu, babu wanda ya sake ce mata ko ƙala. Tana shiga parlo ta daka tsalle tana faɗin. "Smart girl, wai ni ko yaushe na koyi waɗan nan wayo ne ma?". Tana cikin surutan nata ne ta ɗago kai sai a kan su Aunty Lisa dake zaune a dining room suna dinner, da yake glass wall ne wajen dining room ɗin sai suna iya ganinta. Da gudu Angelina ta taso ta nufota, muryarta har yana rawa wajen tambayarta ya aka yi? Ta samu ganin Noor?. Bata fuskanci wata matsala ba ko?. Zazzare idanunta a kan su Aunty Lisa ta yi, cike da mamaki ta ce. "Aunty". Suma sai kallonta suke yi, sai a yanzu suka gane gaskiya Angelina take faɗa masu na cewa ba ita ce suka haɗu da ita ɗazun ba. Kun san me yafaru ne? A lokacin da suka shigo gidan Angelina kawai suka samu a parlo, su Arya sun yi sama. Nan fa suka fara rungumar Angelie suna tambayarta dama nan ne gidansu? Ita kuma bata ganesu ba sai ta fara tambayar su waye su, nan suka zayyane mata komai, ta ce ba ita bace sai dai ko in sister ɗinta V, kuma bata nan sai ta dawo, suka kafe lallai ita ce, Aunty Lisa har da cewa ga ash hair ɗin nan nata, komai sak na wacce suka haɗu, su basu yarda ba, lallai ita ce. Ita kuwa ta kafe ba ita bace, ta ce sai dai su jira V ta dawo dan su tabbatar. Shi ne fa suka yi shiru suna ta mamaki, masu aiki suka yi masu iso kamar yadda GAT ya basu umarni, sannan suka kaisu ɗakunan da ya ce su kaisu, wanka suka yi suka shirya, sannan suka sauƙo dan yin dinner, har yansu basu ga su Arya ba, dan kun san Arya ta tsani shiga cikin mutane, bata son hayaniya, kuma idan ba dole ba bata sauƙowa ƙasa sai in daddynta ya dawo ta zo ta yi mashi oyoyo. Angelie ita ta zauna da su Lisa har yanzu da V ta dawo, Daddyn Noor kuwa yana room da aka bashi, yana jiran GAT ya dawo su ci abinci a tare. A natse V ta kariso wajensu, cikin girmamawa ta gaisa da su kafin ta zauna a kusa da aunty Lisa, nan fa suka fara nuna mata kauna tare da tambayar dama su identical twins ne bata faɗa masu ba tasa sun ruɗe! Tana murmushi ta ce a'a su identical quadruple ne ma ba twins ba! Mamaki yasa su Aunty Lisa rikicewa, suka fara lallai a nuna masu sauran, V ta ce su gama dinner zata kaisu wajensu Arya, dan tasan wlh Arya ba zata sauƙo ƙasa dan su gaisa ba, sai dai ita aje a sameta. Shiru room ɗin ya yi suka cigaba da cin abincinsu a natse, V tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tsananin daɗi, yau ta kwanta a kirjin love ɗinta!. ----------------------------🔥 CRYSTAL PALACE. Mu koma baya mu gani. Tin tana kuka kaɗan-kaɗan har sautinta ya daina fita, take ta ji nunfashinta ya fara sama-sama yana ƙoƙarin ɗaukewa, a zabure ta miƙe tsaye tana ta ƙoƙarin jawo numfashin, amma ina, babu iskan da zata iya ja ta shaƙa. Laluɓe ta fara yi tana ƙoƙarin kama bango ta jingina, amma ta gagara, tangaɗi ta fara yi tana kai hannu ta rike wuyanta ta fara ɓarin abubuwa, dan ji take yi tamkar an shaƙeta ne, take ta fara tari tana zazzaro idanu waje. Kafin wani ɗan lokaci ta sulale ƙasa babu numfashi a jikinta!........ A can cikin gida kuwa, bayan sun kulle ɗakin kai tsaye suka sauƙo ƙasa, wanka Champion ya shiga room ɗinsa ya yi, ya shirya cikin tail coat mai bala'in kyau launin ash color, still dai fuskan sanye da nose mask, ya fito ya isko scorpion a parlo. Miƙewa ya yi suka nufi hanyar fita, da alama barin gidan za su yi. Gab zasu hau elevator Champion ya tsaya, scorpion na kokarin yi mashi magana ya juya da sauri yana faɗin. "My phone, I'm coming". Bai jira amsarsa ba ya wuce ciki da gudunsu na terrorist. Sama ya haura tare da nufar wannan ɗaki. A gaggauce ya buɗe ya shiga, kai tsaye wajen table ɗin da suka zauna ɗazun ya nufa, wayar ya ɗauko tare da nufar kofar fita. Dab zai fita ya kunna wutar wayar. Ganin jini a ƙasa yasa ya ɗan ja baya kaɗan, ya kara haska wajen da kyau. Tabbas jini ne, a ransa ya ce meyakawo blood wajen nan kuma?. ALLAH sarki jininta ne, dan a garin neman iskar shaƙa ta dinga buge-buge har bakinta ya fara jini. Ɗan bin jinin da light ya yi har izuwa wajen da take yashe a ƙasa bata ko motsi. Ɗan waro eyes ɗinsa waje ya yi, da sauri ya kai hannu ɗaya ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa suka yo waje. Kai tsaye ya nufi kasa da ita. Sai cikin mota, kai tsaye ya ce su wuce CPH da ita, dan a bata taimakon gaggawa idan ma tana raye kenan. Kun gane ne, ɗakin binciken nasu sun yi shi ne musamman ta yadda babu wanda zai iya leƙan asirinsu, ko ka samu nasarar shiga a sace ba da saninsu ba to 30 mins ya yi maka yawa ka baƙunci lahira ba tare ma da sun taɓakaba, haɗarin dake cikin ɗakin tamkar haɗarin dake tattare da su ne! Kun gane ai?. Suna zuwa CPH aka ce ba za'a karɓeta ba sai da wannan notebook ɗin nasu na shaidar mazauna CP ne su. Champion ji ya yi tamkar ya harbe likitan dake mashi wannan jawabi, amma sai ya daure da cewa. Scorpion ya je ya ɗauko notebook ɗin a gida, a room ɗinta cikin drugs ɗinta. Da sauri ya juya ya tafi, yau ba dan Lion ɗinsu ne ya ce su kula da yarinyar kuma su bata kome take so ba da babu abin da zai hana Champion bai kasheta ya jefar da gawarta ba, dan ta cika karambani dayawa a cewansa. Haka dai ya dinga tausan kansa har aka kawo note-b ɗin, ya karɓa ya baiwa likita aka karɓeta. In takaice maku sai da ta yi kwana biyu a sume bata san in da kanta yake ba sannan ta farfaɗo da taimakon ALLAH da taimakon likitoci, sai da ta sha ruwa keda 3, kamar ma za'a kara mata jini, sai kuma aka fasa, aka haɗa mata magungunar jini kawai. After two days suka ɗauketa suka koma gida, a cikin wannan sati Champion ya nema mata boarding school, ya shirya mata komai ya ɗauketa ya jefata can ba tare da ya jira dawowar Lion ɗin nasu ba, watau ft, yana kwance a gadon asibiti bai san in da kansa yake ba, saboda raunin da ya ji, ga shi ya rasa jini sosai, sai da aka kara mashi leda biyu, har yanzu dai yana fama da jinya. To shi dai Champion ba zai iya jurar kiriniyar Seraph ba, shiyasa ya yanke nasa hukuncin, dan a kullum basa zaman lafiya a gidan, ta dinga kukar mammy ɗinta, abinci sai an mata ɗure, idan ta fito suka haɗe da zakin nan ta dinga ihu tana suma kenan, dik ta hanasu samun peace of mind a gidan, dan haka ko dan hero (zaki) da take tsoro gara a bar gidan da ita!. In kara takaice maku sai bayan zuwanta school da sati biyu Lion ya warke ya dawo, ko da ya dawo bai tambayi ina take ba, bai bi ta kanta bama, suka shiga sabon babi na aikinsu, dama gagarumin aiki ne a gabansu aka samu wancan matsala su Eagle suka farmasu, kungiyar su eagle sun basu aikin kashe wani ne suka ce ba zasu yi ba, dan su ba kowa suke yi wa aiki ba sai wanda suka yi ra'ayi, to abin da ya haɗa tsama a tsakaninsu kenan, su eagle suna ganin ai sun san sirrinsu sannan su ki yi masu aiki? Shi ne suka nufi kashesu, suka shirya zama da su, a wannan zaman ne Lion shi kaɗai ya yi attending har suka farmakesa, su Champion basu je ba, dan basu cika zuwa waje su ukun a tare ba. Kada ku manta suna da fuskoki da dama, su eagle ba da fuskan Iron Fist suka sansu har suka ƙulla harƙallah ba, da wani fuska ne, shi fuskan Iron Fist suna amfani da shi ne kawai idan zasu yi gagarumin kisan da zai jinjiga duniya! Fatan kun gane?. Seraph dama Jss 1 take a school, Champion yasa aka kaita Jss 2, daga nan ta cigaba. In kara takaice maku har tsawon shekara biyun nan suka wuce, Seraph ta kammala Jss 3, tana da shekaru 12 kenan yanzu, Lion bai taɓa tambayar ina take ba, da alama ma ya manta da ita a duniya, amma Champion yana zuwa wajenta a school time to time, yana kai mata kayan abinci idan ya dedeci lokacin karewarsu. Amma ku zo mu ɗan bi rayuwarta a makarantar ko kaɗan ne mu gani kafin mu yi skipping. GOLDEN ROOTS ACADEMY, shi ne sunan school da Champion ya sanyata. Boarding school ne wanda daga jss 1 ake fara kwana a makaranta zuwa Ss3. Ranar da ya kammala shirya mata komai ya ɗauketa a mota ya wuce kai tsaye da ita school ɗin. A ranar sai kuka take yi tana tambayar ina zai kaita? Kuma ina mammy ɗinta? Bai ko kalli in da take ba, yana driving cikin zafin jini abinsa. Tin da suka shararo titin da ya sadasu da school ɗin ta yi tsit tana kallon hanya har suk shiga ciki, katafaren makaranta ce na gani na faɗa, ƴaƴan manyan kai ne kawai a cikinta, shinfiɗaɗɗiyar titi ce ta ratsa ko'ina a school ɗin. Kai tsaye parking lot ɗinsu ya nufa. Yana parking ya fito tare da buɗe side ɗin da take ciki. Sanin cewa baya yi mata magana yasa ta fito da sauri, jakarta dake ciki ya ciro tare da buɗe bayar motar ya ɗauko echolac ɗinta, ba tare da ya sake kallon in da take ba ya wuce gaba abinsa. Da sauri ta rufa mashi baya suka nufi office na director. Yana zuwa ya wuce ciki kai tsaye, kafin ta karisa shigowa sai gani ta yi yana ƙoƙarin fitowa, zata bi bayansa wani kyakkyawan farin fata dake zaune a saman office chair ɗinsa ne ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Da sauri ta dakata, alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba musu ta je, tana tafiya tana waigo Champion har ya kurewa ganinta. Cikin harshen turanci director ya ce ta samu waje ta zauna bari Madam Rohisha ta zo ta ɗauketa su tafi side na ɗalibai!. Muryanta na rawa ta ce. "Uncle where is my Mammy? Do you know where she is? Will you take me to her?". A kiɗime take magana, ya fahimci akwai firgici da tashin hankali a tattare da ita, dik tana ruɗe, ga idanunta a kumbure luhu-luhu! Lokaci guda mugun tausayin yarinyar ya kama shi, miƙewa ya yi daga kujeransa ya dawo in da take, cikin tausasawa ya fara rarrashinta har ya samu ta ɗan natsu. A daidai lokacin Madam Rohisha ta shigo bakinta a ɗauke da excuse, wata haɗaɗɗiyar mata ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, tana da ido masu zurfi da kyakkyawan dogon gashi, gata da kyan jiki, sanye take da arabian dress, ta yi rolling kanta da veil alamar musulma ce. Tana ɗaura dara-daran eyes ɗinta a kan Seraph ta ji yarinyar ta yi mugun tafiya da imaninta, gata kyakkyawar gaske. Ai cikin azama ta karisa gareta. Director ne ya miƙe ya bar wajen, ya koma saman kujeransa, ita kuma Madam ta zauna kusa da Seraph tare da riko hannunta tana ƙoƙarin tambayarta sunanta kenan director ya katseta, a natse ya fara bata bayanin wacece Seraph, watau marainiya ce da bata da uwa kuma bata da uba, dan haka ta kula da ita. Sosai Madam Rohisha ta ji kalamansa, ta kuma yi alkawarin ɗaukar Seraph a matsayin ƴar cikinta, daga nan ta kama hannunta, ta ja mata echolac ɗinta da ɗayar hannunta, sai ta ce Seraph ta ɗauki dakarta, daga nan suka fice izuwa side na mata, watau wajen kwanansu kenan!. Farko kenan a rayuwar Seraph a school, dan haka zan yi labarin ne bisa ɓangare biyu, idan na waiwayo wajen Seraph to muna baya ne in da take rayuwa a school, idan na koma wajensu Leo muna gaba ne kafin in yi skipping, kun gane ai?. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP STEP 1________🔥 12-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________11 Ɗakin da yakasance mallakin ɗaliban aji biyu Madam ta kaita, tin da suka shiga Seraph ke faman kallon ɗakin kamar ta ga wani abin daga wata duniya. Bed guda huɗu ne a cikin ɗakin, uku yara na kwance a kai, ɗaya babu kowa. A nan Madam Rohisha ta kaita, sannan ta kira dikkan ƴan'matan dake kwance a saman gadonsu kan su zo ga bakuwa sun yi. Su ukun dik suka sauƙo, ƴan yara ne da basu wuci Seraph ɗin ba. A wajen gadon suka zazzauna suna kallon Madam cike da kulawa, ita ma cike da kulawa ta ce. "Wannan bakuwa ce, ku kula da ita sosai, Aana kinga kin fi su girma ko? Ki kula da su"...... Wacce aka kira da Aana yarinya ce da zata iya kai 13 years, su kuma kun ga a lokacin 9 to 10 suke, ba'a cika 10 ciff ba. Kama hannun wata kyakkyawar yarinya Madam ta yi, ita ma ba zata wuci 11 years ba, cikin sanyin murya ta ce. "Rimsha, wannan ita ma kamar ke take, she don't have anyone, bata da Father and Mother, take care of her kin ji? Ki kwarara mata gwiwa". Da sauri Rimsha ta ɗago kai, dan ta san zafin rashin iyaye, mahaifinta ya rasu, mahaifiyarta babu wanda yasan in da take, a hannun kakanninta take rayuwa sai uncles ɗinta da suka tsani ganinta. Sanadin mahaifiyarta mahaifinta ya rasu, shiyasa dangin mahaifin nata suka tsaneta, kakaninta da suka haifi babanta ne kawai suke kaunarta sai kuma wani Uncle ɗinta ɗaya Ustadz mai zuna Faryan, amma saura dik basu sonta, sun ɗaura laifin mahaifiyarta a kanta, wai in sun ganta mahaifiyarta kawai suke tinawa da ta yi breaking heart na ɗan uwansu har rai ya yi halinsa. Sun tsani ta zo kusa da su, ganin tsanar ta yi yawa ne yasa kakanta ya kawota boarding school dan ta rage zafi, in ta daina ganinsu watakila komai zai warware a zuciyanta. Ta kuwa yi sa'ar shiga hannun Madam Rohisha, malama mai kyan zuciya, ita ta dinga karfafata tana lallashinta har ta mantar da ita bala'in tsanarta da dangin babanta suka yi, gata yarinya kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, uwarta European ce, kun san turawa idan suka aureka, da zarar baka da kuɗi haɗa kayansu zasu yi su gudu su barka, ko da kana sonsu kamar ka mutu, su dai zasu gudu ne, amma abin mamakin a nan shi ne ita Rimsha mahaifinta nada mahaukatan kuɗi, dan kakanninta yanzu haka haya suke yi a C-P, kun kuma san dik wanda yake haya a Crystal Palace kuma ai kunga kuɗi kuwa ba'a magana, sai dai sun rasa dalilin da yasa mahaifiyarta ta gudu ta bar daddynta, har yau kuma suna nemanta basu ganta ba, abin da ɗaure kai. (Wani rawa kuke tinanin Rimsha zata taka a labarin nan? Kun san bana yabo ko magana a kan wanda bashi da matuƙar muhimmanci a labarin nan, okey mu je zuwa.) Kama hannun Seraph Rimsha ta yi tare da cewa. "Zan kula da ita sosai Madam". Sosai Madam ta ji daɗi tare da yi masu fatan alkhairi, sannan ta tashi ta fice ta basu waje. Saura yara biyu miƙewa suka yi suka koma wajen beds ɗinsu ba tare da sun yi wa Seraph magana ba, ita kuma Rimsha ta tayata suka shirya kayanta a cikin lokar wajen gadonta, suka shirya komai Rimsha na ɗan janta da hira tana karfafa mata gwiwa. Fuska ɗauke da fara'a Rimsha ta ce. "Your face is shining like a star, can I call you star lady or star girl?"....... Seraph dake ta ƙoƙarin tura kayanta cikin drawer ne ta amsa da. "Why not? Also your face is shining like mine, if you call me Star lady, I will call you star baby"...... "Most of people here are calling me beauty, but now when I saw you I realized that I didn't deserve that name"....... "Why?". Seraph ta tambaya. "Because you're the really definition of beauty"....... Siririn one side smelling Seraph ta saki, bata sake cewa komai ba, suka cigaba da aiki a tare. A haka suka kasance, cikin ƙanƙanin lokaci suka yi mugun sabo da juna, Seraph ta fara sakin jiki da Rimsha, sauran dake ɗakinsu basa shiga harkarsu, kuma basa takura masu, kowa yana harkar gabansa ne, su je class tare su kuma dawo a tare, sun zama tamkar ƴan uwan juna, Madam Rohisha ta zama tamkar mahaifiyarsu. Dik karshen wata Champion yana kawowa Seraph ziyara haɗe da kayan cima na kwalam, sai dai bai taɓa haɗuwa da ita ba, office na director kawai yake zuwa ya basa ya fita. Idan an yi hutu yana turawa ne a ɗauketa a kaita wani gida, ita kaɗai kamar mayya haka take rayuwa a cikin wannan gida na tsawon hutu, da an buɗe school ya sanya a dawo da ita...... Yau ta kama Monday, kuma farkon sabon watan da suka shiga. Shirye suke cikin uniform ɗinsu. Mini sket ne zuwa gwiwa baki, da riga fari zuwa waist ɗinsu mai dogon hannu, kayan ya yi mugun yi masu kyau, sun fito sosai, a dokar makarantar ana ɗaure gashin kai ne gida biyu, jelar gashin a ɗaure da bakar rebon kalar sket ɗin uniform, sai kuma a zuba jelar a gefen shoulders ɗinsu, haka kuwa suke yi, yana ƙara fito da kyansu, sai santin ash hair ɗin Seraph kowa yake yi!. Suna rike da hannun juna ita da Rimsha, sun fito daga hostel zasu wuce class. Lokaci guda Seraph ta tsaya cak tamkar mai tinanin wani abu.Taɓata Rimsha ta yi tana faɗin. "Star lady meyasa kika tsaya a nan? Mu je mana!"...... Da sauri Seraph ta juyo da jikinta gabaɗaya ta kalli bayanta. Wani irin firgici ne ya bayyana a kan fuskanta, muryanta na rawa ta ce. "Uncle meyasa ka zo nan?". Champion dake tsaye a bayanta ya zura hannaye a cikin aljuhun jacket ɗin jikinsa yana kallonta ne ya ɗan ɗauke kansa daga kallon nata. Mugun tsoronsa Seraph take ji. Da sauri Rimsha ta juyar da kallonta a kansa ita ma. Yana dai sanye da face mask a face ɗinsa, kuma da alama ba ainahin fuskansa bane wannan. Baya-baya Seraph ta fara ja tana son gudu ta bar wajen, dan zamanta a school ɗin nan har ta fara mancewa da su a rayuwarta kawai ya dawo, bata buƙata. Idanunsa a kanta ko kyaftawa babu, yana ganin yadda take ta ja da baya. Sai da ya bari ta ɗan yi nisa, tana ƙoƙarin juyawa da gudu ta bar wajen ya yi taku ɗaya ya damƙota ta ciki-ciki, dama yana ankare da motsinta. Ihu ta fara ƙoƙarin kurma mashi ya dakatar da ita ta hanye toshe mata baki, sannan ya ɗagata sama ya wuce da ita. Da gudu Rimsha ta nufi office na Madam Rohisha dan ta sanar mata da cewa wani ya ɗauke mata star ladynta. Shi kuwa bai direta a ko'ina ba sai a cikin motarsa, a gidan gaba ya sanyata tare da shiga driving side. Tana kokarin fita ya rufe motar tare da cewa ta natsu, ya yi maganar ne a natse sosai. Tsoronsa yasa dole ta natsu tsit. Zuba mata ido ya yi na ƴan mintoci, sai sharan kwallah take yi, violet eyes ɗin nan nata sun kara cizawa saboda kukan, pink lips ɗinta sai kerma suke yi alamar tsoro. "Me alaƙarki da hoton wannan dattijon da kika taɓa a ɗakin aikinmu before in kawoki nan?". Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da

Chapter 19 of 95