yasan namiji ne wannan a tsaye, dik wani sauran tausayinsu horo bar two ɗin nan ya kwashe masu shi.
Dikkansu hannunsu ɗaure da tambarin lambobin yabo da jarumta a jikinsu. Ga wani tsantsar natsuwa da kwarjini a tattare da su. Wasu sojoji su 4 ne suka zo da fareti suka fesa masu wani haɗaɗɗen perfume mai bala'in kamshi dan karramawa ta farko a garesu.
Wani irin busa ne mai karfi ya karaɗe hall ɗin wanda yasa kowa ya kara natsuwa tsit, wannan busa alama ce ta karramawa a garesu, kuma alama ce ta sun yi nasara.
Dikkan jama'a idanunsu na kan waɗan nan matasan sojojin ne, musamman family ɗinsu da suka canza masu, sun ga sun zama dakakkun maza, murɗewar jikinsu ya razana zuƙata, ga fuskokinsu kana gani kasan maza ne a wajen! SOJA MARMARI DAGA NESA!.
Bayan busar wannan ƙaho sai recap of their struggle, wani dakakken soja mai zubin rashin imani ne ya tako izuwa tsakiyar hall ɗin, a gabansu ya tsaya tare da miƙawa GAT sd card dake hannunsa cikin girmamawa tare da sara mashi.
Karɓa ya yi ya sanya aka kunna makeken tvn dake wajen, sannan ya bada sd card ɗin aka sanya a tvn. Take video ɗinsu a lokacin horo na biyu ya bayyana, irin gwagwarmayar da suka sha, bakar azaban da suka sha. Wajen da ya fi komai ɗaukar hankalin jama'a shi ne in da suke gwabza faɗa da junansu dan kwarewa a faɗar hannu, ya ilahi, duka sosai suke yi wa juna tamkar ba jikinsu ba, a wani waje tayar mota ce take bi ta kansu, suna kwance flat a ƙasa motar take bin ta tsakiyar cikinsu, kuma basa jin komai, saboda jikinsu ya rigada ya kame, babu abin da zai yi masu.
Da aka hasko wani waje in da Vash ke kaiwa Noor naushi a ciki sai da dayawa daga cikin jama'a suka ɗan datse idanun, slowly suka sake buɗewa, sai suka ga Noor a tsaye tamkar saƙago, bai ji komai ba a kan wannan naushi. Wani waje suna kwasan manyan kayayyaki a gadan bayansu su yi ta gudu iya kurewar gudu, horo na gaske suka yi ba kamar bar one ba, Noor tin da ɗan sauran murmushi a kan face ɗinsa har komai ya kau, ya fuskanci reality, ya zama tsayayyen namiji wanda bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa!.
Wai a haka wurare masu sauki aka nunawa iyayensu, ba'a nuna masu ainahin azaban ba, dan wlh dik wanda ya ga ainahin azaban da suke sha a bar two ba zai yarda ya turo yaransa aikin ba, sai ma da suke lallankwashe kasusuwan juna, kaga tamkar zasu karyesa ne, abin dai ba'a magana sai shiru.
Captain ne ya kashe video ɗin tare da cewa. "A yau kuna tsaye a gabanmu ne a matsayin jarumai masu ƴanci, kun sha wahala, kun sha horo, kun sha yunwa, amma kun tsaya tsayin daka! Kun cancanci wannan rana ta karramawa!".
Har cikin ransu sun ji mugun daɗin kalamansa, kuma a yanzu mugun kaunar Captain suke yi, dan ya tsaya masu, shi ya mayar da su cikakkun maza, saboda jajircewarsa yasa suka yi nasara a yau!.
Time for oath of allegiance ya yi, a nan ne aka umarcesu da su tsaya a gaban mic dake saman stage ɗin, sannan su fuskanci dunban jama'ar dake wajen dan yin rantsuwa ga wannan aiki. Ba musu suka kaddamar da abin da aka ce.
Hannayensu suka ɗaga sama suna masu dunƙulesa alamar karfafawa, haɗe baki suka yi wajen cewa. "A yau muna tsaye a kan kafafunmu gaban dubban jama'a, muna rantsuwa da sunan wanda ranmu ke hannunsa cewa zamu kare ƙasarmu, rayuka da dukiyata, ba zamu taɓa bari abokan gaba su yi mana ƙawanya ba, dik wasu dattin dake a kan kasarmu zamu kawar da shi!". Gabaɗaya sojojin nan voice ɗinsu ya zama Lion voice mai kaifin da babu wasa a cikinta, musamman Leo and Noor, zai Zaysh and Vash, then Juraiz and Units then saura.
Suna kai karshe aka harba bindigu uku a jere, daddyn Noor daɗi ya sanya ya gagara yin magana gabaɗaya, yaga ɗansa ya zama dakakken namiji jarumin gaske, tamkar ba shi ba!
Cikin wani irin kamewa da takun jarumta Captain ya matsa gaban GAT, sara mashi da karfi ya yi haɗe da gwada zarrar jarumta!.
Miƙewa GAT ya yi, a daidai lokacin dakakken soja mai kama da saƙagon dake bayansu ya miƙo mashi ƴar kyakkyawar akwatin dake hannunsa, karɓa GAT ya yi, ya miƙawa Captain. A wani irin kame Captain ya karɓi akwatin ya juya ya koma gaban sojojin nan. Iyaye sai farinciki suke yi.
Buɗe akwatin ya yi, wasu gold stamp ne guda shidda a ciki. Cirosu ya yi tare da miƙawa sojan dake bayansa akwatin, kowani kambu yana ɗauke da sunan wanda za'a sanyawa. Daga ƙasa ya fara, wanda ya zo na shidda a horon bar two shi ne Juraiz na ɗakinsu Unays. Matsawa Captain ya yi, a wuya ya sanyawa Juraiz kambunsa, take aka yi harbi guda biyu a sama na girmamawa garesa.
Sake matsawa zuwa mutum na biyar ya yi, watau Unays, sanya mashi ya yi shi ma aka harba two bullets a sama. Ya matsa na huɗu Vash, yaro ya zama shirgegen soja mai rai da lafiya. Sanya mashi kambunsa ya yi, ya sake matsala ya sanyawa Zaysh dake na uku kafin ya matsa ya sanyawa Noor dake matsayin na biyu, watau Leo ya tsaya tsayin daka sai da ya mayar da Noor dakakken namiji, dik in da ya sanya kafa Noor sai ya sanya, bai mashi ta daɗi ba amma a karshe yasa ya yi nasara!.
Lokacin da Captain ya zo sanyawa Noor wannan kambu shi da kansa yasan Noor namiji ne a yanzu, sai da ya kare mashi kallo kafin ya sanya mashi kambun, sannan sai da ya sanya hannu ya buga shoulder ɗinsa da karfi alamar jajircewa kafin ya wuce wajen oga Leo dake tsaye tamkar wanda aka sassaƙa! Ya kafe kallonsa a waje guda, wanda da na juya dan ganin wa yake kallo sai da na firgita.
Ya ilahi ya lillahi, wani bawan ALLAH yake kallah wanda dik da yana sanye da Dr nose mask hakan ba zai hana ka san cewa ALLAH ya yi halitta a wannan waje ba, kamanninsa da Leo tamkar an tsaga kara ne, still shi ma kitso ce a kansa na kalba, kitson ma zara-zara kuwa, zanensu ya fito sosai, ya tara kitson a tsakiyan kai ya ɗaure, hannunsa rike da p-cap da ya cire daga kansa. Dik da yana zaune kai daga ganinsa kasan mazajene a wajen, eyes ɗinsa kalar sanyi, irin jade eyes ɗin nan, in kuka gansa zaku zaci yana jin barci, ga idanun very sharp, har sun fi na Leo rikitarwa, dan shi zaku zaci yasa kwalli a idon ne, kuma haka halittarsu yake, kunga ɗan round mouth lips ɗinsa kuwa? Gasu pink color kamar na mata, maza da ja aka sansu, su kuma nasu pink color ne sosai. ALLAH ya yi halitta a wannan waje jama'a!.
Slowly ya mayar da p-cap dake kansa, gabaɗaya ya kafe Leo da kallo shi ma. Zayra'an Muhammad Haizaan kenan, Big Bro na Leo, the same father the same mother, su biyu ne rak wajen iyayensu, Zayra'an zai kai kimanin 32 years a yanzu, tsayayyen namiji ne wanda ya samu horo a AZURE shekarun baya da suka wuce, zakaran da a lokacinsa babu wanda ya iya bugesa, yaki yarda aiki a AZURE shiyasa ya koma Us military, mutumin da yadda kuka ga Leo haka yake, har ma ya fi Leo wasu dabi'u masu gindayar da mutane, zaka iya zaman shekara da shi bai ce maka kala ba, in ma kai ka mashi magana ba lallai ya amsa ba, kaifi ɗaya ne, wlh in ya ce e to fa e ɗin nan ne babu wanda ya isa ya sanya shi canzawa, idan kuma ya ce a'a fa ita ma ta zauna, yana da nuna iko da isa a waje, a cewarsa dik in da ya je shi ne sarki, dole kowa ya yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. A lokacin da ya karɓi horo a hannun GAT ne, lokacin GAT yana matsayin Commander kafin ya samu karin girma.
Dik wata izza da isa a barwa Zayra'an kayansa, bakinsa bata buɗewa ta yi magana sai dai ido ya cika aiki. Idan ya zuba maka ido sai ka tsargu ka yi abin da ba shikenan ba, idan ya zare maka ido da alamar tuhuma in baka yi saa ba sai ka saki fitsari a wando, idan ya yi maka magana cikin tausasawa sai ka rikice saboda daɗin muryansa, idan kuma ya daka maka tsawa in har baka da kwarin zuciya kana iya sumewa! Kyansa yana haukata dayawa, yana rikita maza da mata, shiyasa baya shiga taro, baya zuwa ko'ina saboda idanun jama'a, kada ku manta sun fito ne daga ƙabilun da suka fi kowani ƙabilu kyau a duniya! Kunga kuwa batun kyau ma sai dai ayi shiru, amma suna rikita kwakwalen mata da maza, ko namiji ya gansu sai ya sake juyawa ya gansu bare mace.
Sanya mashi kambun Captain ya yi tare da buga shoulder ɗinsa alamar kwararawa. Daga nan Captain ya karɓo kambun karmawa mataki na biyu, a nan aka sanyawa Ameer da sauran matansan room ɗin nasu dana room 3.
Daga nan ne GAT ya tashi tsaye, cikin takun jarunta ya isa gaban mic da aka tanada dan jawabinsa. Take dik wani soja dake wajen ya ƙara kamewa da alamar girmamawa.
Da kaifaffar harshe ya ce. "Ina yi wa sojojin da suka yi nasara murnar tsallake wannan babban aiki, hakika sun cancanci jinjina ta musamman, jaruman gaske ne, kuma dikkansu sun fito da sakamako mai kyau, sai dai a bisa doka wannan horon bar two da aka basu lallai ba za su karɓi sakamakon horonsu ba har sai sun ƙaddamar da Mission guda biyar, bayan sun kammala shi sun dawo, a nan ne zasu samu sakamakonsu na farko da na biyu, misali idan ace yanzu sun fita da muƙamin lieutenant, idan suka gama wannan Mission ɗin, suka yi shi da kyau, kuma suka yi nasara, suna iya fita da muƙamin General, Major General, har izuwa muƙamina, dan wannan Mission da zasu yi shi zai tabbatar da jarumta da kwarewarsu a aiki, dan haka yau ba rana ce ta yaye ɗaliban soja ba, yau rana ce ta shiga sabon babi, za'a basu hutun sati biyu, zasu je gida suga dangi da iyaye, dik abin da zasu yi zasu yi shi ne a cikin wannan sati biyun, daga nan za su dawo bakin aiki dan shiryawa wannan mission ɗin!". Ya dakata yana kallon iyayen sojojin.
Irinsu Ummie da basu san me Mission yake nufi ba sai daɗi take ji, ita dai ƙaninta ya zama soja tin da ta gansa da kaki. Sauran iyaye kowa fuskarsa ta sauya, musamman daddyn Noor dake da mallakin ɗa namiji ɗaya tilo a duniya, kunga kuwa ba zai so a tura shi wani Mission da manyan ƴan ta'adda a duniya ba. Basu gama dawowa daga tinanin da suke yi ba suka ji GAT na kirga irin mission da zasu yi, ciki har da kirgo kungiyar IRON FIRST wanda jiga-jigan jami'an Amurka sun ƙasa damkesu, amma wai ake kiransu matsayin mission na biyar da su Ko za su yi. BABBAR MAGANA, DA MATSALA KUWA!
Kai wasa ma ake yi. A cewar daddyn Noor, domin shi bai yarda IRON FIRST mutane bane, yadda duniya take maganarsu, an gagara kamasu ɗin ne za'a ce wai su Noor zasu yi mission a kansu, very funny thing. Amma fa a cewar daddyn Noor, dan yana ɗauka Noor da ya sani ne, kunsan sanin da ka yi wa mutum a farko ko me zai zama a haka zaka dinga kallonsa, shi daddy kawai yana kallon Noor a ɗan shagwaɓa rago mai kukan da ya sani yake yi!.
GAT ya kammala jawabinsa da kiran sunayen manyan ƴan ta'adda da zasu yi mission a kansu, daga nan ya ce Leo shi ne shugaban da zai jagoranci wannan runduna tasu, su 12 ne kenan a tawagar, from room 1 to room 3, kunga mutane 4 ne a kowani ɗaki, su 12 kenan. GAT ya naɗa Leo a matsayin Commander wannan runduna, dole su yi mashi biyayya da karrama shi, Noor assistant, daga nan ya umarci da a kawo stars ɗinsu, kowa iyayensa su sanya mashi star ɗinsa a gaban riga.
Yana gama magana aka saki bindigu uku sama da karfi. Sannan Captain ya ɗauko stars ɗin a cikin box, iyaye one after the other aka fara kiransu suna zuwa dan sanyawa yaransu. A room 1 iyayen Vash aka fara kira. Wani kyakkyawan matashi ne ya taso ya kariso wajen, dik in da ake neman namiji wannan ya kai. Dr Aryan Muhammad Khaiza'an kenan, babba likita kuma natsastsen matashi mai jini a jika. (Ku lura, sunan mahaifin Vash da mahaifin Leo kusan iri ɗaya ne, amma ba ɗaya ba, na Leo Haiza'an, na su Vash Khaiza'an)
A gabansa ya tsaya tare da karɓar star ɗin, ya sanyawa Vash a gaban riga, da karfi Vash ya sara mashi kafin su rungumi juna cike da kauna da kewar juna. Daga nan Vash ya bisa suna sauƙa ƙasa dan kara ganin juna.
Iyayen Zaysh aka kira a mataki na gaba da su zo. A natse Ummie ta tashi ta nufi wajen, jikinta sai rawa yake yi, dan har ga ALLAH a tsananin tsorace take da sojojin dake wajen, kun san su ko kakinsu mugun kwarjini ne da shi. Tana zuwa ta karɓi star ɗin, da kyar ta iya jurewa, Captain ya nuna mata in da zata sanya mashi! Sakawa ta yi tana ta kallon fuskansa, gabaɗaya yanzu tsoronsa take ji, kwarjininsa ya firgitata, dik ya canza kamar bashi ba. Sara mata ya yi kafin su rungumi juna kirjinta kamar zai fashe saboda tsoro da faɗuwar gaba, take ta fara ruwan hawayen tsantsan farinciki, yau ALLAH ya cika masu burinsu ya zama soja. Daga nan ya bita suka sauƙa ƙasa dan su gana da kyau.
Sai daddyn Noor da aka kira, cike da farinciki da alfahari ya taso, wasu jiga-jigan guards suka take mashi baya har zuwa in da Noor yake a tsaye, aka bashi star ya sanya mashi, sannan suka rungumi juna, sai da daddy ya girgiza jin jikin Noor a jikinsa, ya ji namijin gaske, ai a take ya ji zuciyansa ta wastsake, ya ji lallai Noor zai iya wannan Mission ɗin!. Da sauri daddy ya ja shi suka nufi wajensu Aunty Lisa da tin shigowarsu GAT yake ta kallonta, ya ga ƴar kyakkyawa, da alama su Arya zasu samu second mother idan da rabo!
Lokacin da aka kira family ɗin Leo Big Bro ɗinsa ya miƙe ya fito sai da kowa ya kallesa ya sake kallah, dan ma dai yana sanye da winter jacket mai ɗan tsawo zuwa gwiwa da ta rufe kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa, amma dik da haka an kafesa da idanu. A gaban Leo ya tsaya a dake tare da karɓar star ɗin ya sanya mashi sannan suka rungumi juna. Dik wanda ɗan uwansa ya sanyawa star ɗin nan sai an buga bindiga sama alamar girmamawa!.
Kama hannun Leo ya yi suka koma gefe dan ganawa, saboda an gama dik wasu important abin da za'a ayi saura ci da sha, suna da damar ganawa da ƴan uwansu.
To mu koma baya kaɗan, tin da su Leo suka shigo hall ɗin nan su V suka rikice. Tana sauke idanunta a kan Noor bata san time da ta miƙe tana faɗa masu su tayata ganin shin da gaske na jikin robar mansu take gani ne ko bashi bane. Arya ce ta jata ta zaunar da ita dan kada ta tara masu jama'a, sannan ta ce shi ne mana, amma ta natsu taga jama'a a nan ai. Da kyar ta natsu, ba ita kaɗai ba har su Angelina da kyar suka natsu saboda gigicewa da suka yi a ganin Noor and Leo, ita kanta Arya ta gigice da ganin Leo, ya kara kwarjini da zarra, da ta kalli face ɗinsa sai da ta sha jinin jikinta, sai da gabanta ya faɗi.
Ita kuwa V matsawa jikin Angelina ta yi tana ta faman santin kyan Noor, wai a hoto ma ashe an rage mashi kyau, tuni ta manta da tana son Leo, to taga first love, wanda ta fara so a rayuwanta tin buta wuci 8 years ba, kuma kun san so ba ruwansa da kyau, dik da Leo ya fi Noor kyau ita dai Noor ne ya fara shiga ranta, dama saboda tinanin ba zata samu ganinsa bane yasa ta bada kofar Leo ya shiga zuciyanta.
Angelina ɗin ma sai tayata santin kyansa take yi, dik sun rikice, Arya dai tana zaune a natse, tamkar babu abin dake damunta, daga karshe ma ta ɗan yi ƙasa da kai ta daina kallon Leo saboda tsananin sara mata da kan nata yake yi idan tana kallonsa.
Bayan an gama karramasu sun koma gefe da ƴan uwansu, manyan baki sun fara cin abinci ne V ta ce. "Angelie ni zan je in gana da love ɗina, ALLAH zan je in yi mashi magana". Riketa Angelie ta yi tare da cewa. "Baki da hankali ko? Bari daddy ya kamaki zaki sani ne, ai kin san ya hana boys ɗinsa su kulamu, kuma muma ya hanamu kulasu ko?".
Tana turo baki ta ce. "Wannan ba boy ɗin daddy bane, baki ji me aka ce bane? Kwararrun jami'an ESS ne, emagemcy secret service. Dan haka shi ba boy ɗin dad bane". ........ "Amma ai kin san kowani kaki yana karkashin GAT ne ko?!". A cewar Arya dake jinsu, ta yi maganar a natse sosai cikin dakewa ga class.
Marairace murya ta yi tamkar zata yi kuka, a shagwaɓe ta ce. "Please bloody, ku barni in je in gansa, in ba haka ba zan yi ciwo, ko kuna son in kamu da ciwo ne?"........ Da sauri suka girgiza kai, har suna haɗa baki wajen cewa a'a basu son ta kamu da ciwo. "To please ku kare mun wajen daddy bari in je in gansa in dawo, two mins kawai".
Da yake suna bala'in son juna sai suka aminta, har da cewa zasu ce da daddy ta je toilet ne, kuma ta yi sauri ya dawo, da okey ta amsa tare da lallaɓawa ta zame jiki ta fice. A lokacin Noor yana tare da Auntys ɗinsa a can waje gefe da hall ɗin, daddynsa kuma ya nemi zama da GAT dan ya ga yadda za'ayi a cire Noor a wannan mission kawai ya koma da ɗansa gida, gara mashi ya je ya yi aiki cikin Us army kusa da gida!.
Tin daga nesa ta hangosa kewaye da mata, haba take ta ji ranta ya ɓaci tin ma bata san me alaƙarsu ba, bai ma san da ita ba wai tana kishinsa, har da yin sauri ta kariso wajen. Excuse ta yi mashi a natse. Da sauri su Luna suka kai kallonsu a kanta, shi kuwa Noor yana rike da Auntynsa da yake bi wajen haihuwa watau Aunty Lisa, ya rike hannunta sai hira suke yi, ya yi kewansu sosai, so bai ɗago ya kalli V ba!.
Aunty Lisa ta fi kowa saukin kai, da sauri ta ce. "Like wow, fine girl, pleasure look at this beautiful lady, wajenka ta zo ko?". ...... Sai a lokacin ya ɗago ido, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai tare da girgizawa Aunty Lisa kai game da cewa. "No Aunty, I don't even know her, this is my first time seeing her".
Da sauri Lisa ta saki hannunsa tare da riko hannun V, tana yaba kyanta musamman ash hair ɗinta dake ta faman kyalli, ga wannan na gaban goshi da ya kara fito da kyanta, cike da kulawa ta ce. "Fine girl lafiya?"...... Mamaki ne ya kama Noor ganin har da sake hannunsa ta kama wata, sai ya ja baya tare da komawa kusa da Aunty Luna yana hararar Lisa ta kasan ido, irin like zamu haɗu dake ne, amma bai to magana ba.
Ta gansa sarai, amma ta share kamar bata gani ba, saboda ita dai V ta tafi da imaninta..... Jin ya kira su da Aunty yasa V ta ce. "Good evening aunty"...... "Evening my love, kema a nan barrack ɗin kike? Wajen pleasure ɗinmu kika zo ko? Ya sanki ko?". Cikin rawan jiki take tambayarta, dan tana ganin kamar Noor ya santa kawai kunyansu yasa ya ce bai santa ba.
V da tsiya sai ta ce. "Yeah Aunty, he knows me, kuma shi ne ya ce in zo in gaisa da Aunty's ɗinsa, amma kada na nuna kaman nasan shi, wai yana kunyanku ne"......... Ai a miliyan Noor ya juyo da kallonsa a kanta, ɗan turo baki ta yi, bata ma san time da ta ɗan hararesa ba, sai da ta ga ya waro idanunsa sosai a kanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idon kirjinta na bugawa da kari, gabaɗaya kwarjininsa ya rikitata.
Wani irin fara'a ne ya bayyana a kan fuskokin Aunty's ɗin nasa gabaɗaya, dan su suna tsananin son abin da yake so, a tinaninsu yana son V tin da ya ce ta zo ta gaisa da su......... Cike da so da kauna suka jawota jikinsu, Aunty babba watau Aunty Luna ce ta ce. "Pleasure ɓoye mana ita da kake son yi ko?". ...Lisa ta amsa da. "Baka son mu ganta ko?"...... Lusi ta ce. "Gata makurar haɗuwa, zo mu je wajen daddy mu kaita ya ganta shi ma"......... Luna ta sake cewa. "Pleasure gaskiya na yi matuƙar farinciki, gata natsastsiya, a ina ka samota?"......... "Dik ba wannan ba, mu kaita wajen daddy kafin mu dawo mu ji daga in da ya samo ta". Cewar Lisa. Na'am da hakan suka yi, da sauri suka ja hannun V zasu wuce.
Noor da mamakinsu ya hanasa yin magana ne ya yi saurin riko hannun V ɗin dan ya dakatar da su. Sun goge mashi hadda, shi da bai taɓa kallon yarinya ba wai za'a kaita ta gaisa da daddy. Muryansa a sanyaye ga shi yanzu voice ɗinsa ta fashe ta zama lion voice, in a cool way ya ce. "Aunty please stop it, ni fa ban san wannan yarinya ba".
Da sauri Lusi ta ce. "Idan baka son mu kaita wajen daddy ne ma to mun hakura ba zamu kaita ba, amma batun baka santa ba bai ta so ba!"......... Saboda ya dakatar da zancen yasa ya ce. "Okey na ji na santa, ba sai kun kaita wajen daddy ba to".
Fara'arsu ta ninku, fuska cike da murmushi suka dinga yabawa V suna yi masu addu'a kasancewa tare har abada, da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya ce. "Ni bari in je wajen daddy".... Da sauri Aunty Lisa ta rikisa tare da cewa. "Ya za'ayi bakuwarka ta zo kuma ka tafi ka barta, ku tsaya a nan mu bari my je wajen daddy muna zuwa".
Basu jira amsar shi ba, suka wuce gaba. Har sun ɗan fara tafiya Lisa ta dawo da sauri, a kunne ta fara yi wa V raɗa kamar haka. "Kinga ɗan autanmu ne shi, muna ji da shi, ki kula da shi sosai, nasan tin da ya zaɓoki har ya ce ki zo ki gaisa da mu to kin ciri tuta kuma kin fita daban, please kada ki bari ransa yana ɓaci, dan muna son shi fiye da kanmu, anjuma zamu dawo kuma zamu zo har gidanku kin ji?"...... Kai kawai V ta gyaɗa alamar to.
Juyawa Lisa ta yi zata tafi Noor ya yi saurin damko gashin kanta, da yake saƙo ne su akwai wasa sosai a tsakaninsu, kuma yanzu ji yake ma shi ne babba tin da ya zama namijin gaske, dama can ya rainata. Buge mashi hannu ta yi tana hararansa kafin ta ce. "Sai ka fara yin budurwa baka faɗa mun ba, bayan ka ce nice zan zaɓa maka mata, zamu haɗu ne, zaka zo ka sameni, ba dan ka yi sa'a yarinyar ma makurar haɗuwa bace ai da na rusa wannan soyayyar, kuma ka kula da ita na faɗa maka". Ta faɗa tana dallah mashi harara cike da kauna da zolaya kafin ta wuce da ɗan gudunta saboda ya kawo mata damka!.
Shiru wajen
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 95